Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"

" Tabbas akwai abun da ya bace mana , wai ina officer din da ka tura yin investigation ? har yanzu shiru ? "

" ka san wani ? "

girgiza mishi kai Eliot ya yi ya na fadin " no sai ka fada "

" Get out ! " ya fada ya na matse gera
" no , babu in da zan je sai ka fada min , kowa ya San abun da ke faruwa ban da ni kun bar ni cikin duhu "

mikewa tsaye Jimy ya yi ya dauki wayarsa ya nufi kofar fita ya fice ya bar Eliot nan tsaye
da sauri ya bi bayansa ya na rokon shi ya fada mishi amma ya share shi


▪ NIGERIA ( JOS STATE )


yau dai ta kama week-end duk samarin gidan su na gida , ba wanda ya farka da ga barcinsa karfe 8 , duk karfe 10 su ka tashi , Ashur sai da ya kai har karfe 12 dan jiya ya share dare ya na hira da masoyiyyarsa
Sana kuma ta na tare da Danish , ta na kula da shi , shi kansa Danish sai wajen karfe 10 ya tashi ,
bayan ya tashi ta yi mishi wanka ta shirya shi sannan su ka fito a tare ta na rike da hannunsa su ka yi breakfast tare da sauran mutanan gidan


- 05 PM -


wassan ball su ke yi cikin harabar gidan , sun yi Team biyu , har da Tracksuit din su color guda na team din su , da Ashur , Abeeram , & Talal , Team din su red color ne , Captain , Abdoul da Ramadan Team din su kuma ash color ne , Danish shi ne arbiter , Sana da Ma da Chef su na zazzaune saman chair su na kallon su , yanzu dai Team din Red ke wining 2 da 1

gaskiya abun ya yi matukar kawatar wa , duk da ni ba wani wassan ball na ke kallo ba sai da su ka burge ni , har sauran sojojin Captain sun yi tsatsaye su na kallon su

su na tsaka da wassansu kawai su ka ga wata budurwa ta bangad'o karamar kofar gidan ta fado da gudu ta na kuka ta na waiwaye
cak kowanan su ya tsaya ya zuba mata ido har ta karaso wajensu
idonta a rufe ta nufe Captain ba tare da ta sani ba , kawai sai ji ta yi ta bugi mutum da karfi har ta yi baya za ta fadi

da sauri Captain ya kai hannu a kugunta ya taro ta kar ta fadi
ta na jin an taro ta ta ware idanunta a dubu dari
kai tsaye ko cikin nashi su ka sauka ,
nan take ya tsargu da kallon ta , specially kananan sexy eyes din ta farare kal , kwayarsu blue kamar tashi , ba karamin burge shi su ka yi , har wata bugawa ya ji zuciyarsa ta yi

ya na a haka ya jiyo Muryar Talal ya na fadin " Captain me ya faru ? "

sai a lokacin ya dawo hayacinsa , ya gyara mata tsayuwarta sannan ya janye hannunta da ga bayan kugunta
ya fara kallon ta da ga sama har kassa , budurwar kyakyawa ce gaskiya , at least za ta kai 22 years , ta na da tsayi , dan ta kusa kai wa shoulder din Captain , skin din ta fara kal amma Su Abeeram sun fi ta haske , a gefensu wannan sai a ce mata black amma fara ce , gashin kanta duk ya na tirje brown color smooth da shi , ta na sanye da wata Gown ta atanfa amma duk ta yage , musaman wajen hannu kamar an sa hannu an yage ta da karfi dan har gabanta ya yage kadan ya yi saura a ga breast din ta , fuskarta duk ta yi red kamar an dake ta

da sauri Ma ta mike ta karaso wajen ta na fadin " Captain me ya faru ? wacece ? "

har ya bude baki zai yi magana su ka ga wasu samari hudu sun fado gidan da gudu da alamun yarinyar nan ce su ka biyo

ta na ganin su ta saki kara da kuka a tare , ta boye bayan Captain ta na fadin " don Allah ku taimake ni , wlh cutar da ni su ke son yi , don Allah "

kallon sojojinsa Captain ya yi , kafin ya musu alamun su kamo samarin da kai
ai ko samarin na ganin sojoji sun nufo su su ka juya da gudu za su tsere , amma sojojin nan su ka bi bayansu su ka fice gidan da mugun gudu

sai da su ka fita sannan Ma ta riko hannun Yarinyar , cikin sanyin murya ta ce mata " ki kontar da hankalinki ba abun da zai faru da ke "

sai a lokacin ta sauke wata nanauyar ajiyar zuciya ta fito da ga bayan Captain ta fara bin wajen da kallo
ta na ganin Maza ne a wajen , ta yi sauri ta sunkuyar da kai ta na sa hannu ta ja rigarta ta rufe kirjinta

wani dan karamin murmushi Ma ta saki kafin ta ce " Sana , zo ki tafi da ita bedroom din ki , ta yi wanka , cikin kayanki sai ki ba ta guda ta saka "

da To Sana ta amsa mata kafin ta karaso wajen ta riko hannunta su ka nufi cikin gidan , ba ta yi mata musu ba ta bi bayanta su ka shiga cikin gidan


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment