Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wando three cuter da T-shirt , ya na rike da remote ya na kallon Tv cikin konciyar hankali

ya na a haka ya jiyo karar mota ta shigo gidan , ko dan yatsa bai daga ba dan bai damu ba

ya na zaune Ma ta shigo parlourn ta na sallama
ba tare da ya kalle ta ba ya amsa mata sallamarta ya na fadin " welcome Ma "
godiya ta yi mishi kafin ta ce " na ji dadi da ka ke nan , please je ka dauko yarinyar nan a cikin motata , da ta yi tsaye jiri ke debe ta ta fadi "

" okay " ya fada a takaice kafin ya ajiye remote din hannunsa saman table ya tashi ya nufi kofar fita ya fice
Ma kuma ta karaso cikin dakin ta zauna saman sofa ta ajiye ledodin hannunta na maganin yarinyar da ta buge saman table , da kayan da ta sayo mata a mall

ta na zama Captain ya shigo dauke da wata kyakyawar budurwa cak kamar baby , ta zagayo da hannayanta a wuyansa
kai tsaye doguwar sofa ya nufa ya kontar da ita sannan ya koma in da ya tashi ya zauna ya dauki remote ya ci gaba da kallon Tv

a hankali ta mike zaune ta sauko da kafafunta kassa ta na dafe kai
gaskiya yarinyar kyakyawa ce , Skin din ta chocolate , da ga gani wannan ba da ga karamin gida ta fito ba , ta na da kananan Sleeping Eyes farare kal kamar madara , kwayar cikinsu Black ce , da wani dan karamin hancinta kamar an ajiye shi tsakiyar face din ta , a shekaru za ta kai 19 years haka zuwa 20 , ta na da shape gaskiya kamar coca cola
babu veil a kanta saboda dress din da a ka yi mata , hakan ya sa gashinta duk ya na a waje , an yi mata kananan kitso ga shi kuma gashinta na da tsayi gaskiya Masha Allah kawai za a ce

cike da kula Ma ta ce mata " sannu , ya jikin naki ? "
murya a disashe ta ce " da sauki "
wani dan karamin murmushi Ma ta yi kafin ta ce " ki yi hakuri kin ji , ban san ina ne gidanku ba shi ya sa na kawo ki gidana har ki samu sauki , na mayar da ke gidanku "

gyada mata kai ta yi a hankali alamun Okay
" shikenan , yanzu fada min ya sunanki ? "

shiru ta yi ba ta ce komai ba ta na kallon Ma , sai da ta dauki lokaci sannan ta girgiza mata kai ta na fadin " ban sani ba "

" shikenan , yanzu za mu dinga kiranki da Sana Mahnoor , okay ? "
wannan karan sai da Captain ya sa baki ya ce " Sana Mahnoor ? sunan bai yi tsayi dayawa ba ? "

girgiza mishi kai ta yi ta na fadin " Sana , ya na nufin Resplendence, brilliance , Mahnoor kuma Light of the moon , Sana Mahnoor na nufin kyakyawan hasken Wata , ko ba ka ga ta na da kyau ba ? "

" a bar shi kan Sana din zai fi " yarinyar ta fada da kanta

" shikenan Sana , yanzu mu je ki konta zan kai miki abinci ki ci , sai ki sha maganinki ki konta ki huta " Fadin Ma ta na mikewa tsaye ta dauki ledodin da ta shigo da su
gyada mata kai Sana ta yi kafin ta mike tsaye a hankali
lokaci guda ta ji jiri ya debe ta , da sauri ta dafe hannun sofar dan kar ta fadi

karasowa Ma ta yi gefenta ta riko hannunta , ta taimaka mata su ka nufi guest rooms
shi dai Captain kamar babu shi a wajen ya na kallon Tv din sa , bai ma san abun da ke faruwa ba

kai tsaye daya da ga cikin Guest rooms ta kai ta , da ya ke ta san kullum sai butler sun gyara gidan
sai da ta zaunar da ita bakin gadon sannan ta ajiye mata ledar maganinta saman bedside drawer , ta kayanta kuma saman gadon gefenta

ta ce mata " ki shiga ki yi wanka yanzu an kawo miki abinci , sai ki ci ki konta ki huta "
gyada mata kai kawai Sana ta yi ba tare da ta ce komai ba
da ga haka Ma ta juya ta fice bedroom din , ta ba ta waje dan ta huta

bayan Ma ta fito parlourn ta tardo babu kowa alamun Captain ya yi tafiyarsa
ba ta wani neme shi ba ta nufi kitchen dan ta ce wa Chef ya shirya wa Sana abinci da ga haka ta nufi part din ta

bangaran Sana kuma , bayan Ma ta fito ta tashi a hankali ta na jan kafa ta nufi kofar da ta ke tunanin toilet ne

ta tanka dai-dai ko , toilet din ne , kawai ta shiga ta yi wanka ta fito cikin bathrobe
ta dauki ledodin da Ma ta ajiye mata ta nufi dayar kofar ta dressing room ta shiga
Jim kadan ta fito sanye da wata gown ta material , babu veil a kanta

ta na fitowa ta ga tray din abinci ajiye saman table din gaban sofar da ke cikin bedroom d'in
ba ta kawo komai a ranta ba ta karaso wajen sofar ta zauna ta kai hannu ta janye plate din da a ka rufe mata abincin da shi , ta fara ci cikin konciyar hankali

bayan ta kammala ta dauki gorar ruwan da ta gani saman tray d'in ta nufi bakin gadon ta zauna
ta dauki ledar maganinta ta fiddo drugs din da za ta sha , ta sha
da ga nan ta Haye saman gadon ta konta ta kashe lamps din dakin baki daya

yinin ranar ta yau baki Daya Sana a bedroom din ta yi ta , ta na konce saman gado sai lokacin Sallat ya yi sannan ta tashi ta yi , in lokacin cin abincin ya yi kuma Chef ya shigo rike da tray din abincinta ya ajiye mata ya fice , ya koma , in ta ci ta sha maganinta sannan ta koma ta konta


- 07 PM -


a tare duk samarin gidan su ka shigo gidan su na sanye da jallabiya alamun da ga masjid su ke har da Danish
Abeeram na dauke da shi saman wuyansa , sai tirje mishi gashinsa ya ke

ko da su ka shigo Ashur ya nufi stair da sauri ya haye
sauran kuma su ka karaso cikin parlourn su ka zauna saman sofa
sai a lokacin su ka lura da Sana da Ma , su na zaune cikin parlourn

murya cen kassa ta ce musu " sannu da zuwa "
a tare duk su ka amsa mata su na yi mata wani kallo na rudu
kamar ko Ma ta san kallon me su ke yi mata , sai ta ce musu " sunanta Sana , ita ce yarinyar da na ke ce muku mun yi accident jiya "

" Ah okay , Captain har yanzu ba ka da labarin in a na cigiyar yarinyar da ta bata jiya ? " fadin Talal

girgiza mishi kai Captain ya yi ya na fadin " No , ban ji komai ba "
har Ramadan ya bude baki zai yi magana kawai su ka ga Danish ya sauko da ga jikin Abeeram ya nufi Sana , ya Haye saman laps din ta ya na fadin " momy na yi kewar ki sosai " ya fada ya na rungume ta

Dam ta ji zuciyarta ta buga ta na zaro idanu , ba dai yaronta ne ba ta ji ya kira ta da momy
da sauri Ma ta kai hannu ta na kokarin janye shi da ga jikin Sana ya na fadin " No my baby , ba momynka ba ce , please kyale ta ta huta "

kankame ta tsam Danish ya yi kamar zan kwace mishi ita
daya bayan daya samarin wajen su ka fara kokarin raba Danish da Sana amma ina ya matse ta sai kuka ya ke ya na fadin momynsa ce
ita dai Sana ta yi zugum waje guda ko motsi ba ta yi , sai da su ka gaji su ka koma su ka zauna su na kallon su , musaman Captain , a ganinsa kamar Danish ya san Sana sosai , shi ya sa ma ya makale mata , dole ya yi investigation a kan yarinyar nan da kansa

su na a haka su ka fara jiyo wani dadaden qamshi ya fara tashi cikin parlourn
kallon juna su ka fara yi cikin rudu su na son su san da ga ina qamshin nan ya ke fitowa
a hankali su ka fara jiyo takun mutum ya na sauko stair

a tare duk su ka kai kallonsu wajen stair din
Ashur ne ya ke saukowa cikin nitsuwa , ya na sanye da trouser green color na Jeans , da T-shirt White color , ya daura wata jacket green da ga sama ta jeans kalar wandonsa , da fararen sneakers a kafafunsa , ya gyara gashinsa ya mayar da shi baya ya daure , sai tashin qamshi ya ke

ko da ya karaso cikin parlourn Ramadan ya ce mishi " Ashur , ba dai hira ka fara zuwa ba ? "

murmushi mai dan sauti Ashur ya yi kafin ya ce " me ka gani ? "
" na san kai Handsome guy ne amma na yau shirin na musaman ne , fadi gaskiya ina za ka je ? " Fadin Talal

daga musu kafadu ya yi ya na fadin " ni ma ban sani ba , sai na dawo " ya kai karshen ya na nufar kofar fita

da sauri Abeeram ya mike tsaye ya na fadin " Ashu tsaya mu tafi tare "
juyowa ya yi ya ce mishi " yi hakuri Benji , zan biyo muku da ice cream " da ga haka ya sa kafa ya fice

ya na fita Ma ta kai hannu saman kan Danish ta ce " my Baby , please sake ta ta sha iska mana "
girgiza mata kai Danish ya yi

sai a lokacin Sana ta sauke wata nanauyar ajiyar zuciya , ta saki wani cool murmushi ta ce " Danish , sake ni mana na yi nunfashi " ta fada murya a sanyaye

ba musu ya sake ta ya na zaune saman laps din ta ya na murmushi
hannu ta kai saman face din sa ta matso ta manna mishi kiss a forehead ta na fadin " you're so cute , ka sani ko ? "

gyada mata kai ya yi alamun Eh
ta na shirin magana Captain ya riga ta cewa " Baby , tashi mu je mu konta dare ya yi "

girgiza mishi kai Danish ya yi ya na fadin " No uncle , ni yau tare da momyna zan kwana " ya fada ya na kontar da kansa a kirjin Sana

a hankali Sana ta dago kai ta kalli Ma
wata yar karamar ajiyar zuciya Ma ta sauke kafin ta ce wa Captain " Fayd , bar shi kawai tare da ita tun da ya makale mata "

" Ma , amma bai san ta ba , ta ya zai makale mata haka , har da kiranta momy ? " Fadin Abdoul

daga musu kafadu ta yi alamun ba ta sani ba , dan ba ta da amsar da za ta ba su
shi dai Captain ya yi zaune ya zuba musu ido , kamar ya na son ya tantance wani abu



☆ *GIDAN BARISTER AABID * ☆


zaune duk su ke a part din Amarya har da Barister , sun dawo da ga masjid shi da yaronsa , shi ne su ka tsaya a nan parlourn
Rehan ta na konce saman sofa ta na latsa wayarta cikin konciyar hankali
haka ita ma auta , Amarya kuma ta na cen kitchen ta na shirya musu Diner

su na zaune a haka Rehan ta ga kira ya shigo wayarta da sabuwar number
babu ko tsoro ta mike zaune ta dauki kiran ta kai wayarta a kunne ta na sallama kassa kassa

amsa mata sallamarta Ashur ya yi kafin ya daura da cewa " Ina bakin gate "ya fada kafin ya katse kiran

dan zaro idanu ta yi ta mike tsaye
cikin sanyin murya Barister ya ce mata " lafiya ki ka mike tsaye haka ? "
wasu yawu ta hadiye kafin ta kalle shi , ita ta manta da ya na cikin parlourn
" umm Daddy , dama classmate d'in da na ce muku zai dinga zuwa koya min shi ne ya zo , ya ce min ya na bakin kofa " ta fada cikin dan tsoro

gyada mata kai ya yi kafin ya ce " shikenan , je ki ce mishi ya shigo , ki taho da shi na gan shi "
wani kyawatacen murmushi ta saki kafin ta ce " shikenan Daddy " ta fada ta na juyawa da sauri ta fice parlourn dama ba karamin hijab a jikinta

da gudu ta nufi gate ta na tsalle kamar wata karamar yarinya
da sauri Gateman ya mike da ga saman chair din sa ya na fadin " Hajiyah karama ? ina kuma za ki je a wannan lokacin ? "

" no ba fita zan yi ba , dama akwai wani cikin mota nan waje , Daddy ya ce ka bude mishi kofa ya shigo "

da to kawai ya amsa mata kafin ya nufi babbar gate din ya fara bude ta
ko da ya bude idanunta su ka sauka cikin na Ashur , dama bakin kofar gidan ya yi parking motarsa

wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya tada motar ya shigo da ita cikin gidan , sai dai bai nufi parking space ba , nan gaban gate din kadan ya tsaya , ya kashe motar ya sauko

a hankali ta tako ta tsaya gabansa ta na fadin " na zata yau ma ba za ka zo ba "
" i'm sorry , wani uziri ne ya rike ni " ya fada ya na dan sosa sajensa

" shikenan , mu je ciki , Daddyna ya ce ya na son ya fara ganin ka " ta fada ta na takawa ta nufi part din Amarya
ba musu ya bi bayanta

da sallama a bakinta ta shigo parlourn ta na fadin " Daddy gashi nan "
sai da ya cire sneakers din sa sannan ya shigo ya na cikakiyar Sallama cen kassan makoshi

a tare Barister da Nasser su ka amsa masa sallamarsa fuska ba yabo ba fallasa
a hankali Ashur ya karaso cikin parlourn , wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya nufi Barister Aabid ya mika mishi hannu

wani dan karamin murmushi Barister ya saki kafin ya riko hannunsa su ka yi musbaha
sannan ya bawa Nasser Hannu shi ma su ka gaisa
da ga nan ya ce wa Barister " fatan na same ku cikin koshin lafiya ? "

murmushi mai dan sauti Barister ya yi kafin ya ce " Alhamdoulilah , bismillah zauna " ya fada ya na nuna mishi sofar da ke gefen tasu shi da Nasser
ba musu ya zauna ya riko hannayansa
" Rehan , je ki kawo mishi ruwa " Fadin Barister
gyada mishi kai ta yi kafin ta nufi kitchen da sauri ta shige

[19/04 13:28] 🪷🩷:

MY BOOK IS ONLY N300
VIA
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank

Dm +22798999753 for evidence



🥂 𝑮𝑰𝑫𝑨𝑵 𝑴𝑨𝒁𝑨🥂



💙💦 ( ᴛʜᴇ ᴍᴀғɪᴀ' s ʜᴏᴜsᴇ ) 💦💙




___FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ___



🔥👑 𝐌𝐀𝐋𝐋𝐀𝐊𝐈𝐍 ᴍᴇᴇʀᴀʜ 👑🔥


The writer of
Taurin zuciya
Exiled Prince ( love meets power )
Two lights ( Yar jarida )
Taurin Zuciya ( Return )
Fairat
Soyayyar gaskiya ( TRUE LOVE )
and now 𝐆𝐈𝐃𝐀𝐍 𝐌𝐀𝐙𝐀 ( 𝐓𝐇𝐄 𝐌𝐀𝐅𝐈𝐀'𝐒𝐇𝐎𝐔𝐒𝐄 )


FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY




اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️




🅂🅃🄴🄿 ____ 10 ✍ ❤ 🔥





sai da ta bar wajen Sannan Barister ya ce wa Ashur " kamar na taba ganin ka a wani wajen , tsaya ! kai ba dan uwan Captain Fayd Mohammed ba ne ? "

gyada mishi kai Ashur ya yi ya na fadin " Eh , ni K'anansa ne , sunana Ashur Mohammed "

wani kyawatacen murmushi Barister ya saki kafin ya ce " Masha Allah , yaron Madina ne kenan "

" kun san Ma ? " Ashur ya tambaye shi ya na dan daga gera
gyada mishi kai Barister ya yi kafin ya ce " Yes , na san ta , a shekarun baya ta neme ni a kan wata kara da ta ke son kai wa gaban kotu , to ban samu dama ba , ko yanzu ina da lambar wayarta sai dai in ta sauya number , kuma mu na yawan haduwa wajaje daban daban , amma ban taba ganin ka , dama dama Captain da Doctor Talal su na san su "

murmushi mai dan sauti Ashur ya yi kafin ya sunkuyar da kai
ya na a haka ya jiyo Muryar Nasser na fadin " amma kai ba bahaushe ne ba ko ? dan ba ka yi kama da hausawa ba gaskiya , har haussar taka ba daidai ta ke ba "

" No , mahaifin mu na kassar Korea ne , mahaifiyarmu ce bahaushiya , da ita da Ma yaya da kanwa ne , that's why "

dan gyada kai Barister ya yi , dama ya jima ya na son ya san labarin su , ya san Ma sosai , kuma ya san ba ta taba yin aure ba bare ta samu yara , ya na tune lokacin da Hajiyah ta ba shi damar kara aure , ya tunkare ta da maganar amma ta nuna mishi ba ta shirya aure , ya hakura ya kyale ta

su na zaune a haka Rehan ta dawo parlourn ta na sallama , ta na rike da tray , da glass din juice a sama da plate din snacks
ta karaso ta ajiye saman table din da ke gefen Sofar da Ashur ke zaune , sannan ta medo mishi table din gabansa

da murmushi a face din sa ya yi mata godiya sannan ta koma gefen Auta ta zauna

ci gaba da tambayar sa Barister ya yi da cewa " amma ku uku ne kadai ko ka na da wasu yan uwan ? "

gyada mishi kai Ashur ya yi ya na fadin " Mu seven ne , akwai Big bro din mu da ke zaune a U.S , amma in sha Allah monday ya na dawowa , da ga shi sai Fayd , Talal , Abdoul-Aleem , Ramadan , Me and Abeeram , Autan mu "

" Masha Allah , ba dan karatu za ku yi ba da na ce ka zauna mu yi diner , amma ba zan rike ku ba , Rehan tashi ku tafi ko ? "

gyada mishi kai Rehan ta yi kafin ta mike ta na fadin " bari na dauko jakata da littafaina sai mu tafi garden " ta fada ta na nufar stair ta Haye

Mike wa tsaye Ashur ya yi ya na fadin " Na gode Uncle "
murmushi mai dan sauti Barister ya yi kafin ya mike tsaye ya mika mishi hannu
a hankali Ashur ya tako ya riko hannun su ka yi musbaha , Barister ya ce mishi " ni ne da godiya , ka kula da ita , in ba ta maida hankali ka ja mata kunne , sannan....... "
ya kai karshen ya na kai bakinsa wajen kunnen Ashur , cikin rada ya ce mishi " duk lokacin da ka shirya sai ka turo magabatanka a sa muku rana "

dan zaro idanu Ashur ya yi ya na kallon Barister
wata yar karamar dariya Barister ya yi kafin ya ce " kar ka manta lawyer ne ni fa , mun iya bincike , na san ba a banza ka yarda ka koya mata ba , haka ita ma ba banza ta ce ka koya mata ba , na gane komai , ina jiran ku kawai " ya fada ya na komawa ya zauna

murmushi mai dan sauti Ashur ya yi ya na sunkuyar da kai , ya kai hannu bayan keyarsa ya fara sosawa wai shi ya ji kunya

ya na tsaye a haka Rehan ta sauko stair din rike da jakarta ta nufi Ashur ta ce su tafi
da to kawai ya amsa mata kafin ya yi wa Barister sallama su ka fice parlourn

sai da su ka fito harabar gidan sannan ya ce mata " Daddynki ya iya shishigi dayawa , har abun da ba a fada mishi ba ya sani "

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " Lawyer ne fa , dazu da safe momy ta saya min sabuwar waya , tak irin wadda ya saya min har colors din da komai , amma sai da ya gane sabuwa ce , ba wadda ya saya min ba "

" me ya samu wayarki ? " ya tambaye ta dai'dai lokacin da su ka iso cikin garden
ba ta amsa mishi ba sai da su ka zauna saman chair din da ke cikin garden din sannan ta ce mishi " girlfriend d'inka ce ta taka min ita "

" my girlfriend ? " ya fada cikin rudu ya na dan zaro idanu

gyada mishi kai ta yi ta na kokarin ciro books din ta da ga cikin jakarta ta na fadin " Zee , ta ce min kar na yi kokarin shiga tsakaninku , tun safe na ke kokarin kiran ka na fada maka na hakura ka yi zaman ka tun da girlfriend d'inka ba ta so , amma lambarka ba ta shiga , har ta shigo ta same ni ina kokarin kiran ka , shi ne ta kwace wayar ta taka ta , ta kuma ce min kar na sake shiga hanyarka " ta kai karshen murya a sanyaye kamar za ta yi kuka

iska mai zafi ya furza da ga bakinsa , dama su Aryan sun ja mishi kunne a kan Zee , sun fada mishi za ta iya komai a kan abun da ta ke so , musaman da ta makale mishi , yanzu a ka je ta cutar da Rehan fa ? dole ya yi mata kashedi tun ba ta bata mishi komai ba

a hankali ya sauke ajiyar zuciya , sannan ya matso da chair din sa dab da table din tsakiyarsu
ya kai hannu ya riko nata , cikin sanyin murya ya ce " Rehan , ba komai tsakanina da yarinyar nan , da farko ta ce ta na so na , kuma na san na fara kula ta , amma ban taba ba ta damar da za ta yi tunanin ina jin wani abu a kanta , asali ma ni tun lokacin da na san halinta na janye hannuna , a lokacin ne mu ka hadu ni da ke , ki yarda da ni duk abun da za ta fada miki ba gaskiya ba ne "

" ni dama ban ce karya ta ke ba , amma kai ma ba zan iya sanin in gaskiya ka ke fada min ba , kuma ai ba sai ka yi kokarin kare kanka ba saboda babu komai a tsakanin mu , kawai ka zo koya min karatu ne " ta fada ta na janye hannunta da ga cikin nashi

" Na sani , amma ba na son ki yi tunanin da wani abu tsakanina da Zee , kuma za ki na iya tafiya ki tambayi yan uwana , ba na taba yi wa mutanan da na

Please Login or Register in order to submit comment