Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dogon tsaki ya ja kafin ya sauko da kafafunsa kassa , ya mike tsaye ya dauki wandonsa ya mayar sannan ya nufi kofar dakin
nan ya ga Lee tsaye ya na jiransa
tun kafin ya yi magana Lee ya riga shi cewa " Boss , ya kamata ku zo ku gani "
gyada mishi kai Boss ya yi kafin ya juya su ka karaso cikin parlourn , nan ya ga sauran tsatsaye gaban Table din nan ta tsakiya su na kallon Tv

gaban su ya karaso ya tsaya ya na fadin " me ya faru ? "

Money ya dago hannu ya na rike remote ya kunna mishi Tv
a hankali ya juya ya kalli Tv din , dai'dai lokacin ko ta kunnu , a na shirin labarai wata yar jarida zaune a kan chair rike da wasu takardu ta fara magana da harshen Chinese ta na fadin " a safiyar yau ne mu ka samu labarin tashin Bomb a bakin kofar Kowloon Harbourfront Hotel , a bisa binciken jami'an tsaro bomb din ya tashi ne tsakanin karfe 12 na dare da mintina 59 , happily Bomb din ba wani mai girma ba ne , explosion din ba ta yi wani babban tasiri ba , sai dai sun samu gawar wata ma'aikaciyar hotel din , duk yadda a ka yi wanda ya ajiye Bomb din ta cikin hotel din ya ratsa ya wuce , departement of defense ya na son kowa ya kontar da hankalinsa , ko wanene ya tada Bomb din za su kamo shi su ba shi hukuncin da ya dace , sai magana ta gaba ........ " tsit kawai na ga Tv din ta mutu

wani dan karamin murmushi Boss ya saki ya na tapi da hannunsa
cike da izza ya ce " Yesss , Step one finished "

" Boss , yanzu minene shirin mu na gaba " fadin Yung

dan jinkirtawa ya yi kafin ya ce " Marshal Fayd Yeonjun , ina investigation din da na ce ku yi a kansa ? "

Lee ne ya matso ya nufi sofa ya tsugunna , ya kai hannu kassan sofar ya fiddo dasu takardu ya karaso gefen Boss ya tsaya , ya ajiye takardun saman table
ya ce mishi " Boss , kamar yadda ku ka ba da Umarni na yin bincike a kansa , a binciken da na yi Marshal Fayd Yeonjun ya bar American Army shekara uku baya , bayan ya bar Army ya koma kassar Nigeria da ke cikin Africa a jahar Jos , a cen ya na aiki a matsayin Captain cikin Nigerian Army , a yanzu dai shi ne kadai abun da na sani a kai "

" Sauran yan uwansa fa ? "

" Boss , ban san ya da yan uwa ba , amma zan koma na sake bincike a kai "

" Talal , Abdoul-Aleem , Ramadan , Ashur , Abeeram shi ne sunan yan uwansa , su na da Big bro mai sunan Fahd , shi da Fayd tare su ka yi karatu a US , bayan Fahd ya samu master din sa a marketing ya dawo Nigeria in da sauran yan uwansa su ke zaune hannun kanwar mahaifiyarsu bayan rasuwar iyayensu , Fayd kuma ya tsaya a US , ko ni da ke zaune na fi ka masaniya a kai Stupid kawai " ya fada ya na wurga wa Lee wani mugun kallo

da sauri Lee ya sunkuyar da kansa ya na fadin " I'm sorry Boss "

tsaki Boss ya ja kafin ya kalli sauran ya ce " ku yi a hankali dan a yanzu wassan zai fara , ba na son a samu mistake ko da guda ne , Money , Yung , Sniper , ku shirya tafiya UK kamar yadda mu ka tsara nan da one month "

" Amma Boss kudin da mu ka sato fa last months ? " Fadin Doctor

wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya juya ya nufi bedroom din sa ya shiga ba tare da ya ce komai ba
jim kadan ya fito rike da wata bag ya tilla tsakiyar table din , nan take kudin da ke ciki su ka fito su ka bazu tsakiyar table din

" ku yi a hankali wajen kashe kudin nan , in ku ka yi abun da zai janyo hankalin jami'an tsaro kanku , daya bayan daya zan iya kashe ku " ya kai karshen maganarsa ya na juyawa ya koma cikin bedroom din sa ya turo kofar ya rufe

a tare su ka saki wani kyawatacen murmushi su ka nufi table din
su ka fara tattare kudin su ka mayar cikin jakar su na tunanin wace irin masha'a yau za su yi , kowane dai na fadin ra'ayinsa , wani ya ce nightclub , wani ya ce restaurant su fara cin abinci , wani ya ce shopping
haka dai su ka tsaya bata lokaci , Boss kuma ya koma ya konta
Ni kuma na dauki takarduna na nufi Nigeria


MY BOOK IS ONLY N300
VIA
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank

Dm +22798999753 for evidence



🥂 𝑮𝑰𝑫𝑨𝑵 𝑴𝑨𝒁𝑨🥂



💙💦 ( ᴛʜᴇ ᴍᴀғɪᴀ' s ʜᴏᴜsᴇ ) 💦💙




___FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ___



🔥👑 𝐌𝐀𝐋𝐋𝐀𝐊𝐈𝐍ᴍᴇᴇʀᴀʜ 👑🔥


The writer of
Taurin zuciya
Exiled Prince ( love meets power )
Two lights ( Yar jarida )
Taurin Zuciya ( Return )
Fairat
Soyayyar gaskiya ( TRUE LOVE )
and now 𝐆𝐈𝐃𝐀𝐍 𝐌𝐀𝐙𝐀 ( 𝐓𝐇𝐄 𝐌𝐀𝐅𝐈𝐀'𝐒𝐇𝐎𝐔𝐒𝐄 )


FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY




اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️




🅂🅃🄴🄿 ____ 8 ✍ ❤ 🔥




☆ *NIGERIA ( JOS STATE )* ☆


- 09 PM -


*CAPTAIN FAYD*


a hankali ya ke sauko stair din gidan ya na sanye da kayan barcinsa white color
a nan parlourn ya tardo duk sauran yan uwansa zaune , Talal , Ramadan , da Abdoul-Aleem su na rike da laptop su na aikinsu , Abeeram da Ashur kuma su na game da Danish

Danish na ganin Captain ya mike da gudu ya nufe shi ya na dariya
wani dan karamin murmushi Captain ya saki , sai da Danish ya karaso gabansa ya sa hannayansa biyu ya dauke shi , ya na fadin " My Baby , me ya faru har yanzu ba ka yi barci ba ? ka manta na fada maka gobe za ka fara tafiya Primary ? "

" Na sani uncle , Uncle Ashur ne ya ce mu yi game kafin na tafi barci " Ya fada cikin shagwaba

a hankali Captain ya juya ya wurga wa Ashur wani mugun kallo
ya na shirin magana Ma ta shigo parlourn ta na sallama a sanyaye
a tare duk su ka dago kai su na amsa mata sallamarta
da sauri Abeeram ya mike ya nufe ta ya rungume ya na fadin " Ma , ina ki ka shiga yau tun safe na ke ta neman ki , har kiran ki na yi " ya fada cikin yar shagwaba

wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " sorry My Baby , wlh hatsarin mota mu ka yi shi ya sa hankalina bai kawo kan wayata ba "

a tare duk su ka mike tsatsaye jin abun da ta ce
da sauri Captain ya sauke Danish ya nufe ta ya na fadin " Ma , ba ki dai ji ciwo ba ? "

girgiza mishi kai ta yi ta na fadin " No ban ji ciwo ba , But yarinyar da mu ka buge ta ji ciwo sosai a kai , tun safe mu ke Asibiti sai yanzu ta farka , doctor ya ce ta yi amnesia saboda bugun da ta samu a kai , yanzu haka ta na Asibiti , gobe na ke sa ran na je na dauko ta na dawo da ita nan na ci gaba da kula da ita har ta samu sauki na mayar da ita gidansu "

Talal ne ya ce " Ma , me zai hana Captain ya ba da cigiyar ahalinta ? "

" Yeah , na san Tabbas in dai familynta su ka ga ta yi kwana daya biyu ba ta dawo ba za su fara kai cigiya police station , ta haka za mu samo ahalinta " Fadin Ashur

wata yar karamar ajiyar zuciya Ma ta sauke kafin ta ce " shikenan , zan je na konta wlh duk na gaji "

da sauri Abeeram ya ce mata " Ma , mu je na yi miki tausa "
wani cool murmushi ta saki ta kai hannu saman face din sa ta na fadin " No my baby na gode , koma ka ci gaba da game din ka , in ku na bukatar wani abu ina cikin part di na "

da to kawai Abeeram ya amsa mata kafin ya koma gefen Ashur ya zauna ita kuma ta nufi stair ta Haye ta koma part din ta

sai da ta bar wajen sannan Captain ya riko hannun Danish su ka nufi sofar da Talal ke zaune ya zauna
da sauri Danish ya kwace hannunsa ya nufi Abeeram su ci gaba da game din su

cikin nitsuwa Talal ya ce wa Captain " ka na da labarin Bomb din da ta tashi a Hongkong ? "

" Yeah , na ga News din " ya fada ya na fiddo wayarsa ya fara latsawa

" ni a tunanina an yi hakan ne kawai dan firgita mutane , hankulansu su tashi " Fadin Ramadan
amsa mishi Captain ya yi da cewa " No , da wata manufa a ka yi tashin Bomb din ...... "

katse shi Abdoul ya yi da cewa " A ka je Mistake ne kawai ? kun ga an ce mota ce ta tashi da bomb , a ka je just ya yi parking din ta a wrong place , ta tashi da kanta "

" Gawar ma'aikaciyar da a ka samu ciki fa ? kamar yadda Captain ya fada , da wata manufa a ka tada Bomb din , a ka je akwai Radiation cikin Bomb din duk wani wanda ke wajen at least har zuwa 5 km sai ya kamu da Radiation din , a ka je kawai dan dauke hankalin jami'an tsaro ne , kun ga in hankulansu ya karkata kan tashin Bomb din , za su samu damar aikata abun da su ka so cikin ruwan sanyi , ko ma tashin wani Bomb din ne " Fadin Talal

wata yar karamar ajiyar zuciya Captain ya sauke kafin ya ce " Possiblity din su na da yawa , idan na je China zan kara fadada Investigation din "
da ga haka ya mike tsaye ya nufi Abeeram ya mikawa Danish hannu ya ce " Baby , let's go sleep , dare ya yi "

ba musu Danish ya mike ya riko hannun Captain sannan Captain ya dauke shi cak kamar baby ya nufi stair
da sauri Danish ya ce " Good night Uncles "
a tare duk su ka amsa mishi da cewa " Good night our Baby "
da ga haka su ka Haye stair Captain ya wuce da shi bedroom din sa



☆ *WASHE GARI ⛅* ☆


▪REHAN 🎀


cikin nitsuwa ta ke tafiya cikin harabar universitynsu , ta na sanye da rigar material , sai wani dan karamin Hijab zuwa kirji , da medical glass din ta , ta na rataye da bag din ta

ta na a haka ta fara hango su Aryan da Karim da Bill , zaune saman wani banci su na hira
kai tsaye wajen su ta karaso ta na sallama
cen kassa su ka amsa mata sallamarta su na yi mata wani banzan kallo

cikin nitsuwa ta ce musu " please , Ashur yau bai zo university ba ? na duba class din su ban gan shi ba "

" lafiya ki ke neman shi ? " fadin Bill cikin tsare gida

hararrar shi ta yi sama da kassa kafin ta ce " ajiya na ba shi , shi ne zan karbi abuna , in ba ku San in da ya ke ba ku fada min na kama gabana "

" in kin san hanyar gidansu za ki iya tafiya ki karbi ajiyarki " Fadin Aryan

tsaki kawai ta ja ta juya ta bar wajen
sai da ta bar wajen sannan Karim ya ce " wai me ya sa ku ke son takurawa yarinyar nan , kawai dan ta ki karbar soyayyarku ta ce Ashur ta ke so ? "

wani dan karamin tsaki Bill ya ja kafin ya mike da ga saman bancin ya bar wajen
mikewa shi ma Aryan ya yi ya na fadin " sai na yi maganin Yarinyar nan ku jira ku gani " ya kai karshen ya na bin bayan Bill
shi dai Karim ya na zaune ya zuba musu ido har su ka bar wajen

bangaran Rehan kuma bayan ta bar wajen kai tsaye class din su ta koma , da ya ke yanzu lokacin break ne babu kowa cikin class din
wayarta ta fiddo wayarta ta shiga kiran layin Ashur , tun jiya ta ke kiransa amma wayarsa a kashe , duk hankalinta ya tashi kar a je wani abu ya same shi

sai da ta yi mishi wajen kira goma amma wayarsa na kashe , ji ta yi kamar ta yi kuka , ga shi ba ta san gidansu ba da sai ta je ta duba in ya na lafiya

ta na a haka kawai ta ji an kwace mata wayarta da karfi
a razane ta dago kai dan ita ba ta ji shigowar mutum a wajen ba

wata budurwa ce tsaye gabanta , ta na sanye da wani pencil skert da T-shirt , sai wani dan karamin veil a kanta , ta sha make up kamar wadda ke shirin tafiya wajen biki , a shekaru za ta kai 21 years haka
Rehan na dago kai ta saki wayarta ta fadi kassa

dan zaro idanu Rehan ta yi ta mike tsaye ta na fadin " ke ba ki da hankali ? lafiya za ki sakin min waya ? "

cikin ko in kula ta daga kafa ta taka wayar Rehan da karfi
a hankali ta dago yatsa ta nuna Rehan ta ce mata " Kin san Allah Rehan ? tun ba mu saka kafar wando guda ba ki fita da ga harkar Ashur , dan ya fi karfinki , ba ki isa ba na tsaya takara da ke "

wani dan karamin Rehan ta ja kafin ta fito da ga cikin table din ta sa hannayanta biyu ta ture ta , ya dauki wayarta a kassa , duk screen din ya watse ya yi daya daya

a fusace ta ce mata " ki bar ganin ke wata ce cikin makarantar nan Zee , ba ki da ikon yi min kashedi , kuma a sanina Ashur ba karamin yaro ba ne , ya mallaki hankalin kansa , ya na da hankalin tantance abun da ya ke so da wanda ba ya so , da a ce bai fara kula ni ba da ba abun da zai sa na shiga hanyarsa , dan haka ni ya kamata na yi miki kashedi , ki ka sake ki ka shiga tsakanin mu sai na gwada miki ke karamar yar iska ce , non-sens kawai " ta na gama fadar haka ta dauki jakarta ta fice class din ta bar Zee tsaye waje guda

sai da ta bar wajen sannan ta ce " Lalle ma yarinyar nan , kin shirya wassa da wuta kenan , shikenan mu je zuwa , za ki ga abun da zan yi miki "

bangaran Rehan kuma kai tsaye parking space ta nufa , ta shiga cikin motarta ta baro universityn duk da ba su sauka ba

kai tsaye gidansu ta nufa ,
ko da isa ta yi wa gateman horn ya wangale mata gate din gidan , ta danna hancin motar cikin gidan , ta nufi parking space ta yi parking motar , sannan ta kashe ta ta sauko

da gudu ta nufi part din Hajiyah ta na sakin kuka kamar wata karamar yarinya
babu ko sallama ta fado part din ta na kuka
Hajiyah na zaune saman sofa ta na sanye da wata Abaya green da hijab a jikinta ta na kallon Tv

da gudu Rehan ta nufe ta ta fada jikinta ta na sakin kuka
cikin rudu Hajiyah ta ce mata " Titi ? me ya faru ? lafiya ki ke kuka haka ? "

slowly ta dago kanta ta kai hannu ta goge hawayenta ta na fadin " ba komai Momy , kawai wata yarinya ce ta bata min rai "

" dan ta bata miki rai shi ne za ki tsaya ki na kuka ? har da baro makarantar ? " Ta fada ta kai hannu saman face din ta

fiddo wayarta ta yi da ga cikin jakarta ta nunawa Hajiyah ta na fadin " duba ki gani abun da ta yi wa wayata , dama da kyair na samu Daddy ya saya min ita , yanzu ta zo ta fasa min ita , na san ko wajen gyara na kaita ba za ta dawo kamar da farko ba , ga shi kuma tun jiya na ke kiran Ashur wayarsa na kashe , ni wlh mutuwa kawai zan yi na huta " ta kai karshen ta na kontawa saman sofar ta tada kai da hannun sofar ta na kuka a hankali

wani dan karamin murmushi Hajiyah ta saki kafin ta dafa shoulder din ta ta ce " yanzu fada min , ki na kuka ne dan wayar ta baci ko dan Ashur bai amsa kiranki ba ? "

babu ko tsoro ta ce " Ashur , jiya fa ya ce zai zo ya koya min karatu , amma bai zo ba har na gaji da jiran sa , har abinci na shirya mishi fa momy , yanzu kuma ina kiran shi bai dagawa , bare kuma yanzu ba na da wayar da zan kira shi ma "

murmushi mai dan sauti Hajiyah ta yi kafin ta dauki wayarta da ke gefe ta kira layin Barister
kara biyu kiran ya yi ta ji ya daga ya na sallama
amsa mishi sallamarsa ta yi ta na fadin " sannu da Aiki Dear "

" Yawwa , fatan komai lafiya ? " ya tambaye ta

dan kashe murya ta yi ta na fadin " Alhamdoulilah , Dear please ina son na fita , akwai kayan da na ke son na je na sayo , na yi maka magana ko ka manta ? "

murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " Hmmm , madam a dinga fadin gaskiya dai , ba wasu kaya kawai ki na son fita ne "

" pleaseeee , ba zan jima ba " ta fada ta na marairaice fuska kamar ya na a gabanta

" na ji shikenan , amma ki kiyaye hanya na San ba wani driving ki ka iya sosai "

wani cool murmushi ta saki ta na fadin " na gode sosai my Love , Sai ka dawo zan shirya maka abun da ka fi so "

dariya kawai ya yi ya katse kiran
murmushi ita ma ta yi kafin ta sauko wayar ta kalli Rehan da ke zaune ta zuba mata ido ta na kallon Ikon God
yo ita Hajiyah ina ruwanta da Rehan , ko gaban Amarya in ta na son yi wa Barister magana haka ta ke yi mishi , shi ya sa Amarya sam ba ta jituwa da ita , sai ta ga kamar ta asirce Barister ita ko ba ta kissa ce kawai da kisisina irin ta mata

" Tashi ki wanke face din ki , mu je na saya miki sabuwar waya " ta fada ta na mikewa tsaye

da sauri Rehan ta sauko da ga saman sofar ta na fadin " da gaske momy ? "
gyada mata kai kawai Hajiyah ta yi kafin ta fara takawa ta nufi stair
wata yar karamar kara Rehan ta yi kafin ta nufi stair din da gudu ta Haye ta na dariya
murmushi mai dan sauti Hajiyah ta yi ta ci gaba da takawarta har ta haye ta shiga part din ta ta sauya kayan jikinta

a tare su ka sauko stair din bayan Rehan ta wanke face din ta , Hajiyah kuma ta sanyo wasu kayan na Atanfa ta yafa wani veil ta na rike da jakarta , su ka baro part din

kai tsaye parking space su ka nufa , su ka shiga motar Rehan
Rehan ta yi tukin su ka baro gidan , su na tafe su na hira kamar wasu abokai
ko su ka baro gidan supermarket su ka nufa , ta kai Hajiyah shagon da Barister ya saya mata wayarta

sai da ta zabi wayar da ta burge ta , kirar Iphone 14 pro Max , mai pink color , a ka buda mata icloud da sauran gyare gyaren da a ke yi wa wayar , Hajiyah ta biya kudin su ka baro shagon
da ga nan su ka shiga sauran shagunan , su ka yi shopping ba kadan ba sannan su ka koma gida

bayan sun koma gida yanzu ma Rehan part din Hajiyah ta koma , ta dauki tsohuwar wayarta ta mayar da sim card din ta a cikin sabuwar , da ya ke duk abun da ke cikin wayar ta ta yi copy din shi a cikin laptop din ta ya sa ba ta wani damu da a gyara wayar da fitar da abubuwan da ke ciki

sai da lokacin Sallat ya yi sannan ta tattara kayanta ta koma part din Amarya
ta yi sa'a ko babu kowa a parlourn gidan kawai ta nufi stair cikin sand'a ta Haye kamar wata barauniya ta na rike da ledodin kayan da su ka yi shopping

kai tsaye bedroom din ta ta nufa ta shige ta medo kofar , ta shiga dressing room ta jera kayan da su ka sayo cikin closet din ta , sannan ta zabi wasu kananan kayan , wandon jeans da t-shirt
ta fito ta shiga toilet da su

wanka ta yi tare da alwala sannan ta saka kayan a cikin toilet din , ta fito ta nufi sallayarta , ta dauki hijabinta ta saka ta fara gabatar da sallarta

bayan ta kammala kuma ta tashi ta haye saman gadonta , ta dauki sabuwar wayarta
da laptop din ta da ke ajiye saman bedside drawer ta fara copy din abubuwan da ke cikin laptop din zuwa ga wayarta , abun da bai da anfani kuma ta goge shi baki daya har cikin laptop din



[19/04 13:17] 🪷🩷:

MY BOOK IS ONLY N300
VIA
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank

Dm +22798999753 for evidence




🥂 𝑮𝑰𝑫𝑨𝑵 𝑴𝑨𝒁𝑨🥂



💙💦 ( ᴛʜᴇ ᴍᴀғɪᴀ' s ʜᴏᴜsᴇ ) 💦💙




___FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ___



🔥👑 𝐌𝐀𝐋𝐋𝐀𝐊𝐈𝐍 ᴍᴇᴇʀᴀʜ 👑🔥


The writer of
Taurin zuciya
Exiled Prince ( love meets power )
Two lights ( Yar jarida )
Taurin Zuciya ( Return )
Fairat
Soyayyar gaskiya ( TRUE LOVE )
and now 𝐆𝐈𝐃𝐀𝐍 𝐌𝐀𝐙𝐀 ( 𝐓𝐇𝐄 𝐌𝐀𝐅𝐈𝐀'𝐒𝐇𝐎𝐔𝐒𝐄 )


FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY




اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️




🅂🅃🄴🄿 ____ 9 ✍ ❤ 🔥




☆ GIDAN SU CAPTAIN ☆


Yau ma kamar yadda su ka tsara shi da Ashur , Ashur ne ya tafi Headquater a madadinsa , shi kuma ya tsaya a gida
sauran ma su ka tafi wajen aikinsu , Abeeram kuma ya tafi University , dama Universitynsu guda da Ashur just ba bangare guda su ke ba
haka Danish , yau Captain ya fara kai shi Primary school dan haka gidan babu kowa sai shi kadai

Zaune ya ke cikin parlourn gidan , sanye

Please Login or Register in order to submit comment