Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda ya ke , ta rage wannan farin
a hankali ta dago hannun ta ta daura saman face din shi , nan ta ji jikinshi ya rage sanyin da gareshi jiya

wani kyawatencen murmushi ta saki ta na janye hannun ta ta ce " Baby , da ga gani ka na samun sauki , na fada maka wani abu ? Gaskiya ba na jin dadin kwana idan ba ka nan " ta kai karshen ta na turo dan bakin nan nata

a hankali ta juya ta kai hannu ta bude basket din da ke geffen ta , ta ciro wani dan karamin bowl da spoon , sannan ta cire Plate din da ke rufe da bowl din ta meda cikin basket din kafin ta juyo ta na kallon shi ta fara shan Fruit salad din da ke cikin bowl din , ta na ci ta na yi mishi hira , har wani dan jinkirtawa ta ke kamar ya na amsa mata

sannu sannu sai da ta share yinin ranar a cikin dakin shi ta na zuba mishi surutu , sai wajen kiran sallar Azahar sannan ta tashi ta ce mishi za ta dawo da yamma sannan ta baro dakin


▪ROUKSAR


zaune ta ke kassan bishiyar nan , Aymane na zaune geffen ta wannan karan bai rufe fuskar shi ba
ta yi irin zaman bokaye , ta na sanye da wasu kaya bakake da veil baki ta rufe fuskar ta shi
ga wasu kwallaye gaban ta sai hayaki ke fitowa da ga cikin su
a hankali wata guguwa ta fara tashi ta mamaye ta , har veil din ta ya fadi gashin ta ya fara tashi sama

sai motsa lips din ta ke yi da sauri sauri idanun ta sun koma farare kal
a hankali ta daga hannu sama , ta na haka kawai wata ball fara kal kamar lamps ta fado cikin hannun ta
lokaci guda ta juya da hannun ta daura shi saman bishiyar bayan ta , nan take Ball din nan ta shige cikin bishiyar

da sauri Rouksar janye hannun ta , ta yi baya ta na sauke nunfashi da karfi har da dafe saitin zuciyar ta da hannu guda

wata yar iskar dariya Aymane ya bushe da ita ya na fadin " Good job , kin yi aiki mai kyau "

wata nanauyar ajiyar zuciya Rouksar ta sauke kafin ta ce " Aymane , wlh idan wani abu ya same ni ba zan yahe maka ba , maci amana kawai "

" za ki iya fadin duk abun da ki ke so , ni dai ba zan ja da baya ba a kan kudiri na , na gode da taimakon ni , idan kuma ki ka ce za ki yi wani abu against me , kar ki manta da hannu kadai zan iya kawo karshen ki " ya kai karshen ya na dafe bishiyar bayan shi da hannu ya na sakin mata wani makirin murmushi kafin ya bace ya bar ta a wajen

wata yar karamar kara Rouksar ta saki kamar za ta yi kuka kafin ta bace ita ma , dama an ce macuci shi ya san makontar macuci , yanzu Aymane ya saka rayuwar Rouksar a hatsari , dan ko da kuwa branch guda ce ta bishiyar nan ta fado , to sai Rouksar ta ji a jikin ta bare a ce za a cire bishiyar baki daya , Allah ne kadai ya san abun da zai faru , amma ni dai na san ba al'heri ne su ka aikata ba


▪BAYAN SALLAR ISHA


a hankali Inaya ta ke fitowa da ga cikin corridor ta na sanye da wata Abaya Pink color me mugun kyau , ta yafa veil din a kai ba ta yi Rowling din shi ba ,



❤⚘ E X I L E D ⚘❤ P R I N C E ⚘❤


(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥





( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )





STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊






BOOK ________3 👑✌






P A G E 11 🌹🕊




ta na tafiyar ta cikin konciyar hankali da murmushi a fuskar ta
bakin ta da sallama ta shigo parlourn nan ta tardo RIANNA rungume da Tesnim da ke kuka kassa kassa

a rude Inaya ta karaso wajen ta na fadin " Aunty Tesnim me ya faru ki ke kuka ? "

cikin nitsuwa RIANNA ta ce mata " kar ki damu baby , momy ce a ka kai likita jinin ta ya hau saboda halin da Malik ke ciki , amma kar ki damu za ki iya tafiya wajen Malik "

a hankali Inaya ta karaso ta dafa shoulder din Tesnim ta na cewa " ki yi hakuri kin ji Aunty Tesnim ? ba abun da zai samu momy in sha Allah "

wani murmushin karfin hali ta na gyada mata kai ba tare da ta ce komai ba
kamar da ga sama su ka jiyo Muryar Abdoul ya shigo wajen ya na sallama
Tesnim na ganin shi ta tashi da gudu ta nufe shi ta fada jikin shi ta na sauke ajiyar zuciya
a tare Inaya da RIANNA su ka saki wani dan karamin murmushi , kafin Inaya ta tako a hankali ta raba ta geffen Abdoul ba tare da ta ce komai ba ta fice abun ta dan ita ma yanzu ta na da burin kasancewa da nata masoyin

a haka ita ma RIANNA ta mike ta bi bayan Inaya amma ita wajen MALIKAT AL'UMU za ta je

su na fita Abdoul ya dago Tesnim da ga jikin shi ya ce " To rigimamiya , sake ni kare ki karaya min baya "

noke mishi kafada ta yi ta na turo dan bakin nan nata ba tare da ta ce komai ba
a hankali ya rage sautin Muryar shi ya ce mata " mu tafi garden to ? "
da sauri ta gyada mishi kai kafin ta sake shi a hankali ta na sunkuyar da kai

hannu ya kai ya riko hannun ta kafin ya juya su ka bar part din a tare
😂😂😂✌KU BARI NA BI BAYAN SU TUKUNNA , MUN NEMI INAYA DA GA BAYA 🤣🤣🤣

a tare su ka baro part din MALIKAT INAS su ka nufi garden
su na shigowa ya ce mata " me ya faru ki ka ce ki na son ganina ? " ya fada ba tare da ya kale ta ba su na ci gaba da tafiyar su

cikin sanyin murya ta ce mishi " kawai ina son kasancewa tare da kai "
wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " hmmm fada min gaskiya dai , da ga gani akwai abun da ke damun ki , za ki iya fadamin kin sani ko ? "

dan jinkirtawa ta yi kafin ta ce mishi " ban san abun mu ka yi musu , sun raba ni da Abbi , ga Malik cen konce rai a hannu Allah , yanzu kuma sun komo kan momy , yanzu da jimawa a ka tafi da ita likita ni na san doctor karya kawai ya ke mana , ba wani jini ta da ya hau , yanzu ga ta cen konce ko motsi ba ta yi " ta kai karshen kuka na kubce mata

shiru Abdoul ya yi ya na kallon ta ta na kukan ta , gwara ya bar ta ta gama kukan ta ta fitar da abun da ke cikin zuciyar ta da ga baya ya shiga rarrashin ta

sai da ta gama kukan ta kafin ta juyo ta wurga mishi hararra ta na fadin " ba za ka rarrashe ni ba sai ka kyale ni na yi ta kuka "

wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " to ba ga shi yanzu kin yi shiru da kan ki ba , ni fa ban iya rarrashi ba , bayan auta ba na jin zan iya rarrashin wata macen a duniya "

" Har ni kenan ba za ka iya rarrashina ba ? " ta fada ta na marairaice mishi fuska kamar za ta yi kuka

wani dan karamin murmushin geffen fuska ya yi mata kafin ya ce " zan iya mana , amma ba kamar yadda na ke rarrashin auta ba "

" kamar ya kenan ? "

a hankali ya juya ya kali dama , ya kalli hagu ya ga babu kowa sai su kadai sai kuma guards din da ke tsaron wajen amma hankalin su ba ya saman su

a hankali ya juyo ya kalle ta , ya sakin mata wani cool murmushi kafin ya tako ya matso dab da ita , ya na kallon cikin idanun ta ya zagayo da hannun shi a hankali a kugun ta ya janyo ta jikin shi , ya matso da face din shi dab da ta/ta yadda su na iya jiyo nunfashi juna

a hankali ta bude baki a tsorace ta ce mishi " me ka ke shirin yi ? "
daga mata gera guda ya yi ya na cewa " rarrashin ki zan yi mana , ko ba ki so ? "
" haka a ke rarrashin mutum ? ni ka sake ni tun wani bai gan mu "
noke mata kafada ya yi ya na fadin " sai da nace miki ni fa ban iya rarrashi ba , ke ce ki ka matsa , dan haka yanzu ki bari na yi rarrashin ki yadda na iya "

har ta bude baki za ta yi magana ta ji ya cabko lips din ta na kassa ya fara kissing din ta
dum ta ji zuciyar ta ta buga da mugun karfi har wani zaro idanu ta ke ta na kallon shi , shi ko bai ma san ta na yi ba dan ya lumshe idanun shi
( 🤣🤣😂😂 wayyo na so malam na nan ya ga aikin yaron shi )

a hankali ya zame bakin shi da ga cikin nata , ya bude idanun shi
ba su sauka ko ina ba sai cikin nata , ganin irin da kallon da ta ke yi mishi ya sa shi tunanin ko ba ta ji dadin abun da ya yi mata

a hankali ya saki kugun ta ya ja baya kadan murya kassa kassa ya ce " I'm so so sorry , ban yi dan na bata miki rai ba "

a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta gyada mishi kai allamun shikenan
ya na ganin haka ya juya ya fara takawa zai bar wajen
da sauri ta rigo hannun shi ta na cewa " ina kuma za ka je ? "
ba tare da ya juyo ba ya ce mata " ina ga ya kamata na tafi "
" why ? please ba na so ka tafi " ta fada ta na marairaice mishi murya

slowly ya juyo ya sakin mata wani dan karamin murmushi ya ce mata " ki yi hakuri , akwai wani aiki da na ke son na yi yanzu , kuma kin ga dare ya yi ya kamata ki je ki konta ki huta., gobe zan dawo "

a hankali ta sake mishi hannu kafin ta ce " shikenan , amma sai ka meda ni in da mu ka fito " ta kai karshen cikin shagwaba

wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce mata " an gama ranki shi dade "
yar karamar dariya ta yi mishi ita ma kafin su juya a tare su ka koma part din MALIKAT INAS



▪AFTER SOME DAYS ⛅



▪INAYA



a hankali ta turo kofar dakin da Malik ke konce ta na sallama kassa kassa
ta na shigowa sojojin nan su ka nufi hanyar fita su ka fice
a hankali ta karaso bakin gadon shi ta tsaya ta na ci gaba da kallon shi
nan take idanun ta su ka ciko da ruwa kamar za ta yi kuka ta ke ce mishi " baby , wai me ya sa har yanzu ba ka tashi ba ? don Allah ka tashi mana , ina kewar ka over , ko barci na kassa yi saboda yawan tunanin ka da na ke , don Allah ka tashi ko dan saboda ni " ta kai karshen hawaye na zubo mata

a hankali ta lumshe idanun ta , ta kai hannu ta fara goge hawayen ta
cak ta tsaya ta kassa yin wani kwakwaran motsi
a hankali ta sauko da hannun ta , kafin ta bude idanun ta lokaci guda sun koma farare kal ko digon baki babu a ciki har wani haske su ke yi kamar lamps

a hankali ta ja wani irin dogon nunfashi kafin ta yi gaba kadan kamar an ingiza ta
nan take Kayan jikinta su ka koma farare kal , veil din ta ya fado kassa , a hankali jelar gashin ta ta fara komawa white ta tashi sama kamar ana busar da ita

a hankali ta bude baki ta yi magana cikin wani harshen da ban taba ji ba , da ga ji kuma ba na mutane ba ne

slowly ta dago hannu ta daura saman forehead din Malik , ta fara motsa lips din ta a hankali kamar ta na karanto wani abu
lokaci guda wata guguwa ta tashi cikin dakin fara kal ta zagaye su ita da Malik

sai da ta dauki wajen good two minutes a haka kafin Malik ya ja wani dogon nunfashi har sai da kirjin shi ya yi sama
a dubu dari ya ware idanun shi dai'dai lokacin da ya furzo jini da ga cikin bakin shi da wasu kananan ball guda biyu green color , nan take su ka yi cikin guguwar ta bace bat lokaci guda
ta na bacewa kowa lamps din dakin su ka fara mutuwa su na kunna kan su
slowly Inaya ta janye hannun ta da saman forehead din shi , ta lumshe idanun ta kawai ta Zube a kassa sumamiya
ta na faduwa ko launin gashin ta ya koma kamar yadda ya ke , da Abayar ta ma ta koma pink color din ta

ta na faduwa ko sojojin nan su ka dawo da gudu cikin dakin saboda sun ga lamps din su na kunnuwan su na mutuwa da kan su kar a je wani abu ke faruwa a ciki

su na shigowa idanun su su ka sauka kan Malik da ke kallon ceiling ya na kifta idanun shi a hankali , ga kuma Inaya konce a kassa

a tare duk su ka juya su ka bar dakin dan kiran Doctor
ko two minutes ba su yi ba da fitar su , su ka dawo tare da doctor Asheem , MALIKAT INAS da RIANNA

da gudu RIANNA ta nufi Inaya , ta Zube saman guyiwowin ta , ta talabo kan ta ta na kiran sunan ta , ko motsi Inaya ba ta yi ba

a hankali ta mike ta nufi Malik da Doctor ke dubawa ta na ganin idanun shi bude ta saki wani kyawatencen murmushi ta na fadin " Akhie , da gaske kai ne ? Alhamdoulilah Allah na gode maka "

a hankali Malik ya bude baki ya na kallon RIANNA ya ce mata " wacece ke ? "

dum RIANNA ta ji gaban ta ya fadi har wani dishi-dishi ta gani lokaci guda baki sake
da sauri MALIKAT INAS ta karaso bakin gadon ta kai hannu saman forehead din shi kamar za ta yi kuka ta na fadin " Nawfel , ba ka gane mu ba , ni ce fa ? Ammien ka , don Allah in wassa ka ke ka daina "

" please su waye ku ? a ina na ke ? " Ya sake fada a hankali cikin nitsuwa ga shi ko murya a disashe

nan take MALIKAT INAS ta fara ruwan hawaye kar dai a ce Malik amnesia ya yi
ita dai RIANNA ta yi mutuwar tsaye dan ko kifta idanun ta ta kassa yi
da sauri Doctor Asheem ya ce mata " ranki shi dade ki kontar da hankalin ki , hakan na yawan faruwa idan mutum ya shiga doguwar suma , ba amnesia ce ba ya yi kawai bai gama dawowa cikin hayacin shi ba , dan haka ku kontar da hankalin ku , ku bar shi ya huta zuwa gobe in sha Allah zai dawo dai'dai "

" ka tabbata doctor ba amnesia ce ba ya yi " RIANNA ta fada ta na dawo da kallon ta kan Doctor

wani dan karamin murmushi ya sakin mata kafin ya ce " ku kontar da hankalin ku ba amnesia ba ce , yanzu ku bashi waje , Idan ku ka ce za ku matsa mishi za a iya samun matsala , gwara ku bar shi ya huta zuwa gobe sai ku dawo ganin shi "

a hankali RIANNA ta juya ta kali Inaya da ke konce a kassa ta ce wa doctor " ya kamata ku duba mana ita "

cikin zolaya doctor ya ce " may be ita ma ya tambaye ta ko wacece ita , ta kassa jurewa shi ne ta suma "

wata yar karamar dariya RIANNA ta yi kafin ta kai hannu ta dauki Inaya cak kamar baby , dama ba wani nauyi gare ta ba sannan ta juya ta kali MALIKAT INAS ta ce " Ammie , zan mayar da ita part din mu "

gyada mata kai MALIKAT INAS ta yi ta na cewa " shikenan , ina zuwa ni ma "
da to kawai RIANNA ta amsa mata kafin ta juya ta fice dakin ta koma part din MALIKAT INAS

ta na fita MALIKAT INAS ta dan sunkuyar da kan ta , ta shiga karantowa Malik adu'a sannan ta tofa mishi ta manna mishi kiss saman forehead ba tare da ta ce komai ba ta juya ta fice dakin

ta na fita shi ma doctor Asheem ya fice , daya bayan daya sojojin nan su ka dawo cikin dakin , duk abun da su ke Malik ya na jin su amma ba shi da bakin yin magana sai kifta idanun shi kawai ya ke , sai da ya share wajen good one hour a haka kafin ya lumshe idanun shi a hankali allamun barci ya ke ji

bangaran MALIKAT INAS kuwa , ba ta koma part din ta ba sai da ta tafi wajen MALIKAT AL'UMU
bakin ta da sallama ta shigo dakin , nan ta ga MALIKAT AL'UMU konce saman gado idanun ta a lumshe

a hankali INAS ta karaso wajen gadon ta janyo chair ta zauna ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " Moussina , yaron mu fa ya tashi , yanzu haka da ga room din shi na ke , amma doctor ya ce bai gama dawowa cikin hayacin shi , sai gobe zai iya zuwa ya gan ki , ina Fatan da kin jin Muryar shi za ki tashi " ta kai karshen ta na sakin dan karamin kuka

da sauri ta kai hannu ta fara goge hawayen ta ta na cewa " na san duk cikin jarabawar ubangiji ce , kuma in sha Allah sai mun lashe wannan jarrabawar , kamar yadda yaron mu ya tashi haka kema za ki tashi in sha Allah , za mu ci gaba da yin addu'a Allah ya tsare ahalin mu baki daya , dan ina ga makkiyan mu su na da yawa , Idan mun san wasu , wasu kuma ba mu san su ba , kawai kariyar ubangiji ya kamata mu nema , bari kar na cika ki da surutu zan tafi amma in sha gobe zan dawo , ki kula min da kan ki " ta na gama fadar haka ta kai lips din ta saman forehead din MALIKAT AL'UMU ta manna mata kiss kafin ta tashi ta baro dakin


bangaran su Inaya kuma , da sallama a bakin ta RIANNA ta shigo parlourn MALIKAT INAS
nan ta tardo Tesnim zaune waje guda ta yi zugum allamun ta tafi duniyar tunanin ta , har sai da RIANNA ta kai Inaya bedroom din ta , ta dawo cikin parlourn ta zauna geffen ta ta na yi mata magana ba ta sani ba

a hankali RIANNA ta kai hannu ta dafa shoulder din ta ta na fadin " Tesnim lafiyar ki kuwa ? "

a razane Tesnim ta dawo cikin hayacin ta ta juya ta kali RIANNA ta ce " ummm , wani abu ki ka ce ? "

" tunanin me ki ke yi haka tun dazu ina yi miki magana kin kyale ni " RIANNA ta tambaye ta ta na yi mata irin kallon tuhuma

girgiza mata kai Tesnim ta shiga yi ta na cewa " ba komai , ya jikin momy ? "
wani kyawatencen murmushi RIANNA ta saki kafin ta ce mata " Malik ya bude idanu "
wata yar karamar kara Tesnim ta saki ta mike tsaye da ta na fadin " da gaske Malik ya tashi , bari na je na gan shi " ta fada da sauri ta na shirin takawa

da sauri RIANNA ta riko hannun ta ta na cewa " to uwar zumudi dawo zauna , doctor ya ce kar wanda ya yi mishi magana sai gobe dan bai gama dawowa cikin hayacin shi ba , in kuma ki ka je , zai tambaye ki ke wacece , da ga nan ki sume mana kamar dai baby " ta kai karshen ta na yar karamar dariya

a hankali Tesnim ta koma ta zauna ta na murmushi ta ce " Allah na gode maka , na san tun da Malik ya tashi , ita ma momy za ta tashi da ga ta ji Muryar shi "

" in sha Allah " RIANNA ta fada ta na murmushi
da sauri Tesnim ta fada jikin RIANNA ta rungume ta , ta na sakin murmushi mai dan sauti kamar ta na dariya
su na a haka MALIKAT INAS ta shigo ta same su
wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta karaso cikin dakin ta zauna saman sofa one seater ta na kallon su ta ce " tun da yanzu komai ya yi sauki , ku shirya gobe za ku koma dakunan mazajen ku "

a tare Tesnim da RIANNA su ka juya su ka kali MALIKAT INAS har su na hada baki wajen cewa " no gaskiya Ammie sai momy ta tashi "

tsuke fuska MALIKAT INAS ta yi ta na fadin " ba na son shirme , ba shawara na ke ba ku ba , umarni ne , da aure a kan ku amma ku ke nan zaune tare da ni , ko ita baby da na bata dama wlh tare da Malik za ta dinga kwana a cen likita , dan haka kuma ku shirya ku tafi wurin mazajen ku , in ku na son ganin Momy ai ku na iya tafiya ganin ta har ku biyo ku gan ni , ai duk cikin gida guda mu ke "

ta na gama rufe bakin ta Tesnim ta ce mata " amma fa Ammie....... "
ba ta kai karshen maganar ta ba MALIKAT INAS ta katse ta da cewa " ku rufe min baki , wlh duk wadda na gani cikin part din nan gobe a irin wannan lokacin

Please Login or Register in order to submit comment