Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murji junan su da kyau
sai da ya fara jiyo kiran Sallar asubahi sannan ya hakura ya kyale ta sannan su ka shiga wanka a tare , su ka fito su ka shirya shi ya kama hanyar mosque ita kuma ta yi sallar ta cikin dakin
Malik kuwa ko da su ka Kamala Sallat sai da ya wuce wajen Momyn shi da Ammie
sai wajen karfe 7 ya koma part din shi , ko da ya shigo part din su ya tardo ta konce saman gado ta na barci

bai bi ta kan ta ba ya shiga toilet ya yi wanka sannan ya fito ya shirya cikin manyan kayan shi na Malik sannan ya bar dakin , amma kafin ya fita sai da ya manna mata kiss a saman forehead din ta sannan ya tafiyar shi Fada

Bakin shi da sallama cen kassan makoshi ya shigo fadar
su na ganin shi duk su ka mike tsatsaye su na sunkuyar da kai cikin girmamawa
bai bi ta kan su ba ya nufi Chair din shi ya zauna ba tare da ya ce musu komai ba
a hankali kowane ya koma ya zauna
su na zama ko Inaya ta shigo fadar ta na sallama , ta na sanye da wata muguwar gown pink color har kassa ta daura Alkyabar MALIKAT AL'UMU da ya daura mata ranar naddin shi sai qamshi ta ke saki

a tare duk mutanan Fadar su ka yi mamakin ganin ta har shi kan shi Malik , wadda ya bari yanzu ta na kwana ya a ka yi ta samu lokacin yin wannan uban shirin da ga gani kuma wannan shirin ba na mintina ba ne

a hankali ta daga kafa ta fara takowa cikin Fadar
a hankali duk wanda ke zaune ya mike ya na kallon ta cike da tambaya
ba ta bi ta kan su ba ta nufi Chair din MALIKAT ta zauna cikin nitsuwa
ta na zama ko wane ya koma ya zauna ya na bin ta da kallo wajen ya yi tsit

kamar ko Malik ya san abun da su ke tunanin cikin nitsuwa ya ce musu " Why ku ka tsare ta da idanu haka , ba ku taba ganin MALIKAT ta shigo fada ba ? "

a tare duk su ka saki murmushi su ka kauda kai cikin girmamawa Diya ya sunkuyo ya ce mishi " ba komai ran ka shi dade , bare kuma ina ga za mu bukaci ra'ayin mace a tare da mu dan wannan karar ta shafe ta , Azim za ka iya shigo da su "

Gyada mishi kai Azim ya yi kafin ya juya ya fice fadar
ya na fita ya dan matso da kan shi kusan Inaya ya ce mata " me ki ke yi a nan ? "
ba tare da ta kale shi ba ta ce " Why za ka tafi ka kyale ni ? "
" ba dawowa zan yi ba ? "
" hmmm irin na jiya ko ? "

har ya bude baki zai yi magana Azim ya shigo fadar
a hankali Malik ya gyara zaman shi dai'dai lokacin da wani namiji ya shigo fadar da mata a bayan shi su na sallama

a tare su ka karaso tsakiyar Fadar sannan su ka zube saman guyiwowin su kai a sunkuye su ka gaishe da Malik cikin girmamawa
gyada musu kai kawai Malik ya yi ba tare da ya ce komai ba

sai da su ka Kamala gaisuwar su sannan Diya ya ce " Ranka shi dade , wannan sunnan shi Hadi Ahmed , wannan kuma matar shi ce Zulaihat , shekaran jiya ta kawo karar ta na rokon mai martaba Malik ya shiga tsakanin su ya raba auren "

ya na gama rufe bakin shi Rafik ya ce " Yarinya , why za ki ce a raba auren ku , wani laifi ya yi miki ko kuma ba ki son shi ? "

shiru Zulaihat ta yi ba ta ce komai ba , sai ma kuka da ta fara yi kassa kassa

cikin sigar rarrashi Diya ya ce mata " Zulaihat , ba kuka za ki yi ki , ki bude baki ki fada mana dalilin ki na cewa a raba auren ku , kin san ba karamin abu ba ne raba aure "

a hankali Zulaihat ta fara girgiza kai cikin kukan nata ta ke cewa " Don Allah ku raba da shi , wlh ba na son shi "

" ba ki son shi ki ka yarda ki ka aure shi , ko kuma cilas ta miki a ka yi ? " Diya ya fada

A hankali ta girgiza musu kai allamun a'a
cikin Tsawa Mohammed ya ce mata " ki bude baki ki yi magana ba shiru za ki yi ba , ki na son ki batawa Mai martaba lokaci "

ya na gama fadar haka ya jiyo Muryar Inaya ta na cewa " Ba tsawa za ka yi mata ba , Kamata ya yi ku bi ta a hankali " ta na gama fadar haka ta mike a hankali ta fara takawa kowa na kallon ta ya na jiran ya ga abun da za ta yi

a hankali ta karaso gaban Zulaihat ta Zube saman guyiwowin ta da murmushi a fuskar ta ta ce " yar uwa , kar ki ji tsoro ki fadi abun da ke cikin ran ki , kin ji ko ? "

gyada mata kai kawai Zulaihat ta yi ba tare da ta ce komai ba
wani cool murmushi Inaya ta saki sannan ta ce " Shikenan yanzu fada min ba ki son shi ? "

girgiza mata kai ta yi ta na cewa " da ba na son shi ba zan yarda na aure shi ba "

" to minene matsalar , why za ki ce a raba auren ku bayan ki na son mijin ki "

" Ina son shi amma gaskiya ba zan iya zama tare da shi ba , ba zan iya zama da mutumin da zai iya daga hannu ya dake ni , wanda zai iya halaka ni babu ko tsoron Allah a idanun shi ni gaskiya a raba auren nan "

" Inallillahi , ki na nufin Dukan ki ya ke ? "

gyada mata kai Zulaihat ta yi kafin ta ce " kullum sai ya sa hannu ya dake ni , ko da ban yi mishi laifi ba , har ya kai na rasa cikin shi da ke a jiki na saboda Dukan da ya ke min , Idan na fadawa yan gidan mu , sai su ce na yi hakuri mu rufawa juna asiri , ko karar nan da na kawo babu wanda ke da labarin ta saboda na san za su yi kokarin hana ni , Don Allah ina rokon ki , ki yi wa adalin shugaban mu magana ya raba ni da shi , duba ki gani irin azabar da ya ke min "
ta kai karshen ta na sa hannu ta warware veil din da ke a kan ta
ga shaidar belt nan konce a kan fatar ta , saman shoulder , saman wuya har a kirji , sun ni jazir kamar jini zai fito

cike da takaici Inaya ta ce mata " ki yi hakuri na yi miki Alkawari ba ke ba shi a yau , kuma zai fuskanci hukunci dai'dai abun da ya yi miki "

a hankali Zulaihat ta meda veil din ta ta yafa ta na yi wa Inaya godiya

a hankali Inaya ta mike ta juya ta na kallon mutanan fadar da su ka tsare ta da idanu
" na san dukkan ku kun ji abun da ta fada , shin wane hukunci zai fi dacewa da mutumin da zai iya daga hannu ya daki matar shi bayan ba ta yi mishi laifi ba , har ya kai ta rasa babyn da ke jikin ta , Tabas maza sun fi mata karfi saboda a haka Allah ya hallice su , amma ba ya bawa maza wannan karfin ba dan su dinga cin zarafin mata sai dan su dinga kare su , namijin da zai iya daga hannu ya daki mace , macen ma mai ciki sam bai kamata a kira shi da namiji " ta na gama fadar haka ta fara takawa a hankali ta koma saman chair din ta ta zauna

mutanan wajen ban da kallon ta ba abun da su ke yi har shi kan shi Malik , sam maganar ta ba ta yi kama da shekarun ta ba , da ga ji ka san akwai hankali tare da ita

a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya kafin ya juya ya kali Diya , ya ce " Ka sa a rufe shi a yi mishi bulala dari ko wace safiya , ya kuma rubuta mata takardar ta sannan ku ba ta abun da za ta kula da kan ta "

" an gama ran ka shi dade " Diya ya fada cikin girmamawa sannan ya dago kai ya kali wasu dogarai , da hannu ya musu allamun su dauke Hadi
da sauri dogarai uku su ka karaso wajen su ka dauke shi , sai kara ya ke ya na ba da hakuri wai su kyale shi a haka har su ka fice fadar da shi su ka nufi prison

su na fita Malik ya ce ma Zulaihat " gobe za ki iya dawowa ki karbi takardar ki "

ya na gama rufe bakin shi Rafik ya ce " amma ranka shi dade ta ya za mu raba auren su bayan ta na son shi , may be shi ma ya son ta kuma watarana zai iya yin nadamar haka har ya daina daga hannu saman ta , gargadi ya kamata mu yi mishi "

a hankali Malik ya juyo ya kali Rafik ya ce " wane irin gargadi za mu ba wa mutumin da zai iya kashe babyn shi tun kafin ya shigo duniya , a bar ma zancen bugun ta da ya ke yi , kisan kai fa ya yi , ko kuma sai ita ma ya kashe ta zai yi nadama ? "

dan sunkuyar da kai Rafik ya yi ya na cewa " An yi min afuwa ran ka shi dade "

Malik bai ce mishi komai ba ya juya ya kali Zulaihat ya ce " Tashi ki je a mayar da ke gidan ku "

cikin girmamawa Zulaihat ta shiga yi mishi godiya ta na jero mishi aduo'i shi da Inayar shi mutanan fadar su na amsa mata da ameen sannan ta tashi ta fita

ta na fita Malik ya juyo ya kali Inaya , Da ta yi cak waje guda ta tsare waje guda da ido
cikin rudu ya juya ya kali saitin da ta ke kallo , nan ya ga ashe Miram ta ke kallo , sai faman kauda kai ya ke ya kassa kallon ta

a hankali Malik ya juyo gare ta ya kai hannu saman nata cikin rada ya ce mata " Cutie me ya faru ne ? "

wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juyo ta kali Malik cikin rada ta ce mishi " baby , wannan mutum shi ya yi kokarin kashe saurayin da mu je gani asibiti cikin dare "

Dum Malik ya yi zuciyar shi ta buga da mugun karfi har wani lumshe idanun shi ya yi ya na fadin " ya rahman " cikin zuciyar shi

ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya ya kali General Abdallah da hannu ya mishi allamun ya zo

ba musu General ya mike ya karaso gaban Malik ya tsaya ya sara mishi
da hannu Malik ya mishi allamun ya matso
a hankali General ya juya ya kali mutanan fadar kafin ya juyo ya daga kafa ya karaso dab da Malik ya sunkuyo

cikin rada Malik ya ce mishi " Ku yi bincike a kan lambar motar da na tura maka ? "
gyada mishi kai General ya yi kafin ya ce " eh ran ka shi dade mun yi , yanzu ma na ke cewa idan mun fita , na tarda ka part din ka dan mu yi maganar "

" no fada min , da sunnan wa a ka yi register din motar "

a hankali General ya saci kallon Miram kafin ya ce " ranka shi dade , da sunnan Miram ne , a cikin daren kuma na tura dan leken asiri kofar gidan Miram , a cikin daren kuma ya ce min ya ga shigowar wani mutum gidan Miram cikin motar , kuma bai yi ten minutes ba ya fita da motar sai dai mutum biyu su ka fita a cikin motar "

dan lumshe idanun shi Malik ya yi kamar mai jin barci sannan ya ce ma General zai iya tafiya
ba musu General ya koma saman chair din shi ya zauna

ya na zama Malik ya kali Inaya ya ce " Cutie tashi ki je wajen Momy ta ce ta na son ganin ki "

gyada mishi kai Inaya ta yi kafin ta mike , cikin nitsuwa ta fara takawa ta fice fadar

ta na fita ya juya ya kali Diya , da sauri Diya ya dan sunkuyar da kan shi dan jin abun da zai fada
ni dai ban ji abun da ya rada mishi ba , ya na gama maganar shi ya mike tsaye
da sauri mutanan wajen su ma su ka mike tsatsaye , cike da izza ya fara takawa ya nufi Hanyar fita fadar ya fice abun shi
ya na fita Kowane ya koma ya zauna , sannan Diya ya tako gaban Miram ya ce " Miram mai martaba na son ganin ka a part din shi "

cikin rudu Miram ya ce " To , why zai ce sai a part din ba zai iya yi min maganar a nan ba ? "

" ni ma ban sani ba kawai ya ce min na fada maka ya na jiran ka a part din shi , a floor na karshe " Diya na gama fadar haka ya juya ya koma saman kujerar shi ta wazirin Malik su ka ci gaba da aikin su
cike da Shakku Miram ya mike ya bar fadar ya nufi part din Malik



▪INAYA


bakin ta dauke da sallama ta shigo parlourn MALIKAT AL'UMU
nan ta tardo Tesnim da Rouksar zaune a parlourn su na hirar su
Rouksar na ganin Inaya ta tsuke fuska ta kauda kai gefe kamar ba ta gan ta ba ko sallamar ta ba ta amsa mata ba

Tesnim kuwa da fara'a a fuskar ta ta ce " My sister-in-low , sai yau ki ka tuno da ni ? "

wani dan karamin murmushi Inaya ta saki ta na karasowa gaban Tesnim sannan ta zauna saman sofa a geffen ta ta na fadin " Aunty Tesnim ina kwana ? "

" lafiya lau Baby , ya ki ke ? yanzu kin ba zuwa waje na ko ? " Tesnim ta fada ta kai karshen ta na yi wa Inaya hararrar wassa

yar karamar dariya Inaya ta yi kafin ta ce " Sorry Aunty Tesnim , Momy ta na nan ? "

" eh , bari na je na ce mata MALIKAT Inaya na son magana da ita " ta fada cikin zolaya har da yar karamar dariya kafin ta tashi ta bar wajen ta nufi corridor

ta na barin wajen Ita ma Rouksar ta mike za ta bar wajen
cikin nitsuwa Inaya ta taro ta da cewa " ina kuma za ki je wajen ki na zo "
cak Rouksar ta tsaya ta na zaro idanu , har wani mugun bugawa zuciyar ta ta yi , ta kassa gaba ta kassa baya

a hankali Inaya ta mike ta karaso gaban ta dab da ita sannan ta ce " yau ba za ki gwada min wadanan idanun naki na snake ? "

dan karamin tsaki Rouksar ta yi kafin ta kauda kai gefe ta na cewa " fadi abun da ya kawo ki "

" nothing , kawai na zo ne ki gan ni , kamar yadda ki ke gani ban mutu ba " ta kai karshen ta na kashe mata ido guda sannan ta yi wata yar karamar dariya

Rouksar na shirin magana ta jiyo Muryar MALIKAT AL'UMU a bayan Inaya ta na fadin " MALIKAT Inaya , dariyar me ki ke yi haka ? "

a hankali Inaya ta juya da murmushi a face din ta ta ce " Nothing , good morning momy " ta kai karshen ta na fara takawa ta nufi MALIKAT AL'UMU ta rungume ta

murmushi mai dan sauti MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta ce " shikenan yanzu sake ni kar ki karaya min baya "

" sorry momy " Inaya ta fada ta na sakin MALIKAT AL'UMU

ta na sakin ta ko Tesnim ta fito da ga cikin corridor ta na fadin " momy zan je garden "

da sauri Inaya ta bi bayan ta ta na cewa " ni ma zan je "
a hankali Tesnim ta tsaya har sai da Inaya ta karaso wajen ta , ta riko hannun ta su ka fara takawa a tare
da kallo MALIKAT AL'UMU da Rouksar ta raka su har sai da su ka fita sannan MALIKAT AL'UMU ta juyo ta kali Rouksar ta ce " ke ba za ki je ba ? "

girgiza mata kai Rouksar ta yi kafin ta raba ta geffen ta ta wuce corridor
juyawa ita ma MALIKAT AL'UMU ta yi ta koma cikin corridor ta shiga bedroom din ta

bangaran su Inaya Inaya kuma a tare su ka baro part din MALIKAT AL'UMU su ka nufi garden su na tafe su na hira kamar wasu Friends



▪MALIK


tsaye ya ke cikin parlourn shi ya cire Alkyabar jikin , ya na tsaye gaban glass ya na kallon yadda ruwa ke zuba ta kassan Dutsen nan
ya na a haka Kofar lift ta bude , Miram ya fito ya na sallama , Ya na bin wajen da kallo kamar bakwauye , ba karya parlourn ya hadu bai ma taba ganin parlour mai kyawon wannan ba

a hankali ya karaso wajen Malik ya tsaya dan nesa kadan da shi da ga baya ya na fadin " barka da wannan lokacin ran ka shi dade , na ji an ce ka na nema na "

gyada mishi kai Malik ya kafin ya ce " Eh ina son mu yi wata magana , amma karaso ka gani "

ba musu Miram ya karaso geffen Malik ya tsaya ya na kallo ta cikin glass din
" wajen nan ya na matukar burge ni " Malik ya fada cikin sanyin murya
wani kyawatencen murmushi Miram ya saki kafin ya ce " Gaskiya ne Ranka shi dade , wajen ya na da kyau sosai "

gyada mishi kai Malik ya yi ya na fadin " kudin da ku ka fitar last week a sani na ban ba da izinin fitar da su ba , me ku ka yi da su ? "

wasu wahalalun yawu Miram ya hadiye kafin ya ce " Um ran ka shi dade dama , dama Kudin mun....... "

bai kai karshen maganar shi ba Malik ya katse shi da cewa " Miram bude baki ka yi min magana , ina ku ka kai two hundred millions ba tare da sani na ba "

nan take wata muguwar zufa ta karayo wa Miram har da sa rigar shi ya goge

" Miram a sani na duk wasu kudi da a za fitar da ga bank din masarautar nan a na bukatar sa hannun Malik , ni kuma a sani na ba ka kawo min wata takarda ka ce na sa hannu za ku fitar da two hundred millions ga kuma abun da za ku yi da su , ko kuma ka na tunanin ba zan gano an fitar da kudi ba ? , Miram duk abun da ke faruwa cikin masarautar nan ina da masaniya a kai , kawai dai na yi shiru ne na ga gudun ruwan ku , ni ba ma a kan kudin nan na kira ka ba , tambaya guda zan yi maka kuma ina jiran ka fada min gaskiya ko kuma ka fuskanci fushi na "

cike da fargaba Miram ya ce " wace tambaya ce wannan ran ka shi dade " ya fada murya har kerma ma ta ke zuciyar shi na duka uku uku

shiru Malik ya yi bai ce mishi komai ba , ya na kallon Gaban shi
sai da ya share wajen good ten minutes a haka kafin ya bude baki cikin nitsuwa ya ce " Where is Najoua ? "



❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥





💫🌸 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) 💫🌸





STORY & WRITTEN BY : MEERAH 👑🔥


【THE ROYALTY LOVE 👑🕊❤ 】




《BOOK ________3 ✍📚🔥》





___________________ 🌸🕊🌸🕊🌸🕊🌸🕊🌸🕊🌸🕊___________________







{ P A G E 4 ______ 🥂 ❤ }






wata irin muguwar faduwa gaban Miram ya yi har wani dishi-dishi ya gani lokaci guda
murya na kerma ya ce " ran ka shi dade wacece kuma Najoua " ya fada a rarabe

a hankali Malik ya furza iska da ga cikin bakin shi , ya lumshe idanun ya daura hannun shi saman forehead din ya murza a hankali kafin ya sauko shi
cikin zafin nama da dunkule hannun shi ya juyo ya kai wa Miram wani mugun bugu a fuska har sai da kan shi ya bugu da glass din nan

juyawa Malik ya yi ya daura hannun shi saman glass din gaban shi
nan take wajen ya fito kamar Finger print Ya yi scanning hannun , sannan wajen ya bude kamar Window , wani iska mai sanyi ya shigo ga qamshin ciyayi
hannu ya kai ya damko bayan wuyan Miram ya kawo shi gaban Window din nan ya yi kamar zai tila shi ya ce mishi " za ka fada min inda Ka boye ta ko sai na tila ka a wajen nan "

kamar zai yi kuka Miram ya ce " don Allah ran ka shi dade , ban san abun da ka ke magana a kai ba "

a hankali Malik ya saki wuyan Miram ya yi gaba zai fada ya na sakin wata razananiyar kara
da sauri Malik ya riko rigar shi ya na cewa " wannan karan bazan taro ka ba , za ka fada min a ina ka boye Najoua !! " ya kai karshen da dan karfi

" zan fada , zan fada " Miram ya fada kamar zai yi kuka
cikin zafin nama Malik ya janyo shi baya da karfi har sai da ya fadi , sannan ya sa hannu ya rufe Window din nan sannan ya juyo ya kali Miram da ke konce a kassa ya na jan nunfashi da karfi

sai da ya kare mishi kallo da kyau sannan ya kai hannu cikin aljihun shi ya ciro wayar shi ya fara latsawa ya na fadin " tell me where is Najoua ? "

cike da tsoro ya ce " ta na gida na da ya ke a Riyadh "

Malik bai ce mishi komai ba ya raba ta geffen shi ya wuce ya shiga corridor corridor
ya na shiga kofar lift ta bude wasu sojojin guda uku su ka shigo parlourn
kai tsaye Miram su

Please Login or Register in order to submit comment