Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dankareren maciji , ya na fido Tongue din shi waje ya na kukan macizai

wani kyawatencen murmushi Rouksar ta saki kafin ta ware idanun ta da su ka koma tamkar na macijin nan da ke cikin jelar gashin ta
a hankali ta kai hannu saitin kan macijin nan
nan take ya fito da ga cikin jelar gashin ta , ya nade a saman hannun ta , ya daura kan shi tsakanin yatsun ta biyu

a hankali ta matso macijin nan saitin face din ta ta ce " My baby , yau ina ji a jiki na ranar nassara ce , Burin mu zai cika , kar ka gaji da ni ka san abun da na ke bukata a wajen ka "

ta na gama fadar haka macijin nan ya yi wani kuka ya na fiddo tongue din shi , kafin ya juya
a hankali ta matso da hannun ta ta kai shi sama kadan da tray din fruits din
bude bakin shi Snake din na ya yi , nan take poison din shi ya fara fitowa da ga cikin hakwaren shi , ya fara zagaye Tray din nan duk fruits din da ke a sama sai da ya zuba musu poison
sai da ya gama sannan ya rufe bakin shi ya na kukan macizai

wani kyawatencen murmushi Rouksar ta saki kafin ta matso da Snake din nan ta kai saitin bakin ta ta manna mishi kiss a saman jikin shi ta na cewa " na gode baby na , za ka iya komawa ka huta "

wani dan karamin kuka ya yi mata kafin ya yi wata irin burra ya koma cikin jelar gashin ta nan take ya bace a ciki

ya na bacewa Rouksar ta juya ta nufi kofar fita kitchen ta na karasowa bakin kofar glass din ya zuge sai ga wasu mata hudu tsatsaye geffen door din
a hankali ta daga kafa ta fito , ta karaso gaban matan nan ta tsaya ta ce musu " ga Fruits cen Tesnim ta Shirya wa Malik , ku dauka cikin abincin da za ku kai wa part din shi , yanzu nan kafin su Kamala zaman fada " ta na gama fadar haka ta yi gaba abun ta ta na taku kamar ita ce Malik
ba musu matan su ka shiga kitchen su ka fara shirya abincin da za su kai wa part din Malik su ka hada da tray din nan na fruits da Rouksar ta shirya sannan su ka tafi



▪MALIK



kai tsaye part din shi ya koma ya Inaya , amma a floor na Uku ya tsaya , a parlour
zaunar da ita ya yi saman sofa sannan ya zauna geffen ta ya ce " my Cutie are you okay ? "

marairaice mishi fuska ta yi ta na turo dan bakin nan nata ta ce mishi " baby ina ga fa yunwa na ke ji "

a hankali ya kai hannu ya ja mata kumatu ya na fadin " sai da na ce miki ki tsaya mu yi breakfast amma ki ka ce no , ba ga shi ba yanzu wa gari ya waya ? "

kukan shagwaba ta fara yi mishi ta na fadin " uhm uhm ni baby yunwa na ke ji '

da sauri ya ce mata " Shikenan , shikenan Me za ki ci na kawo miki a nan "
cike da shagwaba ta ce mishi " ni fruits ma sun ishe ni "
" an gama ran ki shi dade " ya fada ya na kokarin tashi
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " I love you my baby "

ba tare da ya juyo ba ya ce mata " i love you my Cutie " ya fada dai'dai lokacin da ya shiga dining room
tsaya wa ya yi ya na bin table din da kallo
cen ya ga wani bowl da ga tsakiya cike da fruits , kusan shi kuma wani tray ne shake da fruits an yan'yanka su

a hankali ya kai hannu ya dauki Fork guda biyu , ya daura saman tray din sannan ya dauke shi ya juya ya dawo cikin parlour

gaban ta ya karaso ya ajiye tray din a kassa sannan ya zauna ya ce mata " To Sarauniya ta , sauko mu ci ko ? "

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta sauko kassa ta zauna su na fuskantar juna sannan ta kai hannu ta karbi fork din da ya miko mata ta na yi mishi godiya
a tare su ka kai fork din su cikin tray din , ita ta dauki Apple shi kuma ya dauki Strawberry , su ka kai baki a tare

a hankali ta fara taunawa , ta na kallon shi
cak ta tsaya ta na zaro idanu , da sauri ta hadiye Apple din bakin ta ta ce mishi " baby kar ka hadiye , kar ka hadiye "

tsayawa ya yi ya na kallon ta , ita ba ta san tun kafin ta fara magana ya hadiye


❤⚘ E X I L E D P R I N C E⚘❤


(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥





💔💫 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )💫💔





STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊



【THE ROYALTY LOVE 👑🕊❤】




BOOK ________3 👑✌





______________________ 💔💫💔💫💔💫💔💫💔💫____________________





《 P A G E 7 🌹🕊 》






a hankali ya bude baki ya ce " Me ya faru ? " ya kai karshen ya na daga mata gera guda
marairaice mishi fuska ta yi ta na fadin " sai da na ce maka kar ka hadiye "

har ya bude baki zai yi magana kawai sai ya shiga cough , idanun shi su ka koma jazir
a rude Inaya ta koma geffen shi ta na fadin " baby lafiya , me ya faru ? "
a hankali ya bude baki murya a disashe ya ce mata " take me water "

bai gama rufe bakin shi ba ta tashi da gudu ta nufi dining room , ta na isa bakin dining table ta kai hannu ta dauki glass da jug din ruwa , ta zuba ruwan cikin glass sannan ta juya da Sauri ta dawo cikin parlourn

tun kafin ta karaso gare shi ya saki glass din ya fadi kassa , wata razananiyar kara ta saki kafin ta nufe shi da gudu har sai da ta taga glass din ba ta sani ba
da gudu ta Zube saman guyiwowin ta ta talabo kan shi ta na bubuga kumatun shi ta na fadin " baby , baby me ya same ka , ka bude idanun ka don Allah , baby ! " ta kai karshen da karfi

ina ko jin ta ba ya yi idanun shi su na rufe , jikin shi ya yi zafi , sai wata rawa ya ke , ga wata zufa da ta karayo mishi a Fuska kamar an watsa mishi ruwa
ta na a haka kawai ta ga wani fari abu kamar kunfa haka ta na fitowa da ga bakin shi

dan zaro idanu ta yi ta na kallon shi , ba ta san lokacin da idanun ta ke cikowa da ruwa ba ita kawai sai faman jijiga shi ta ke ta na fadin " baby ka tashi don Allah in wassa ka ke min ka daina " ta kai karshen ta na sakin kuka

amma ina ko motsi bai yi ba
a dubu dari ta sake shi , ta mike da gudu ta nufi lift ta shiga ta baro part din
gudu ta ke cikin fitar hayaci ga kafafun ta sai zubar da jini su ke yi amma sam ba ta jin komai , duk wanda ya gan cikin wannan halin kowa sai ya tambayo kan shi me ya sa ta gudu haka , ga shi kuma sai zubar da jini ta ke

a haka ta ke gudu har ta karaso cikin parlourn MALIKAT INAS babu ko sallama
a dubu dari MALIKAT INAS da RIANNA su ka mike su na kallon ta har su na hada baki su na tambayar ta lafiya

bayan haki ba abun da Inaya ke yi dan maganar ta ki fitowa
bin ta da kallo RIANNA ta yi nan ta ga ko shoes babu a kafafun ta ga shi kuma duk jini
a razane ta ce " inallillahi , baby me ya same ki haka ? "

ta na gama fadar haka Inaya ta saki wani kuka mai cin rai hawaye na zubo mata bibiyu ta na nuna musu hanyar fita parlourn ta na fadin " yaya Zayd di na , Aunty RIANNA mu je ki cece shi don Allah "

cikin rudu MALIKAT INAS ta ce mata " baby ki kontar da hankalin ki ki fada mana abun da ke faruwa "

" Ammie , Yaya Zayd ne , ban san abun da ya same shi ba kawai mu na shan fruits na ga ya fara tari , shi ne ya ce min na je na kawo mishi ruwa kafin na dawo na tardo shi konce ba ya motsi wani farin abu na fitowa da ga bakin shi , Ammie don Allah mu je ki duba shi kar wa......... wani Abu ........ " ba ta kai karshen maganar ta ba ta sulale a kassa sumamiya a wajen

sam RIANNA ba ta bi ta kan Inaya ba ta nufi hanyar fita parlourn da gudu ta fice dan ganin dan uwan ta
da sauri MALIKAT INAS ta Zube saman guyiwowin ta ta talabo kan Inaya ta na dan bubuga kumatun ta , ta na kiran sunan ta
amma ko motsi Inaya ba ta yi ba
wani dan karamin tsaki MALIKAT INAS ta ja kamar za ta yi kuka ta ke furta " inallillahi wa'ina illaihi raji'un " har sau uku
ta ma rasa me za yi dan duk ta bi ta rude

ta a haka kawai ta ga wasu nurse guda biyu sun shigo parlourn su na sallama cikin girmamawa su ka gaishe ta sannan su ka nufi Inaya

har sun sa hannu za su daukar ta MALIKAT INAS ta ce musu " wait , ina za ku kai ta wa ya aiko ku ? " ta tambaye su dan ita yanzu ta daina yarda da kowa indai abun da ya shafi familyn ta ne

Cikin girmamawa daya da ga cikin su ta ce " Ranki shi dade Gimbiya RIANNA ce ta aiko mu ta ce mu kai word room "

" shikenan ku dauke ta mu tafi " ta fada ta na kokarin tashi
ba musu nurse din nan su ka sa hannu su ka dauki Inaya su ka nufi hanyar Fita part din da ita MALIKAT INAS na bayan su
su na fitowa ko sai saman Motar ambulance , su ka saka Inaya a ciki

ashe fitar da RIANNA ta yi da waya a hannun ta , tun kafin ta isa part din Malik ta tura Text a aiko mata da ambulance a part din Malik da part din MALIKAT INAS

kai tsaye Word room su ka nufa da Inaya da mugun gudu
ko one minute ba su ba su ka iso , da sauri Nurses din nan su ka fito , su ka fito da Inaya da ga cikin motar saman wani gado su ka nufi word room din da ita
( yanayin word rooms din kamar wata yar karamar likita ya ke har da reception )

su na shigowa da Inaya ko , wasu Nurse su ka shigo Malik konce saman gadon Jinya RIANNA na biye da bayan su

cikin daya da ga cikin word room din nan su ka nufa da Inaya , Malik kuma su ka wuce kai tsaye A&E ROOM da shi

RIANNA da MALIKAT INAS kuma su ka tsaya a reception
a hankali RIANNA ta matso kussan MALIKAT INAS ta na fadin " Ammie wai me ya faru da su ne haka ? "

" ni ma ban sani ba RIANNA , ban sani ba , don Allah kar ki fadawa MALIKAT AL'UMU abun da ya faru har sai mun Doctor sun shawo kan abun da ya same shi "
MALIKAT INAS na gama fadar haka Wata doctor ta fito da ga dakin da a ka kontar da Inaya ta karaso gaban MALIKAT INAS
ta ce " barka da wannan lokacin ran ki shi dade "

da sauri RIANNA ta ce mata " doctor me ya same ta ? "

" ku kontar da hankalin ku , suma ne ta dan yi , jinin ta ne ya dan hau , ga shi kuma ta samu rauni a kafafun ta har ta zubar da jini shi ya sa , amma ba abun da ya same ta " Ta na gama fadar haka ta juya ta bar wajen

a hankali MALIKAT INAS ta sauke wata boyayyar ajiyar zuciya ta na fadin " Allah na roke ka ka sa shi ma sumar ce ya yi ba wani abu ba "

cikin nitsuwa RIANNA ta ce mata " ba na tunanin Suma ce ya yi Ammie "

" why ki ka ce haka ? wai ni INAS , na ma rasa ya zan yi , sun kassa bar min Ahali na lafya , ya Allah me ya sa ka halice ni a cikin gidan sarauta , yanzu ga shi su na neman su raba ni da yaro na saboda wannan banzan Mulkin , ni wlh su je su rike amma su bar min Ahali na " Fadin MALIKAT INAS hawaye na zubo mata

da sauri RIANNA ta rungume ta cikin raunin murya ta ke cewa " ki kontar da hankalin ki Ammie in sha Allah ba abun da zai same shi " ta fada cikin sigar rarrashi

su dai din da ke reception kallon su kawai su ke tun da ba su san abun da ke faruwa ba


▪AFTER SOME MINUTES


sannu sannu sai da su ka share one hour zaune a reception , babu doctor din da ya fito da ga A&E room bare su tambaye shi abun da ya samu Malik

su na a haka kawai su ka ga wasu doctor guda biyu sun fito
da sauri RIANNA ta mike ta nufe su a rude ta ke tambayar su lafiyar Malik
cikin nitsuwa daya da ga cikin su ya ce mata ta yi hakuri su biyu shi office din shi dan ba zai iya yin maganar a tsaye ba , da ga haka ya raba ta geffen ta ya wuce ya nufi office din shi

juyawa RIANNA ta yi ta kali MALIKAT INAS kafin ta fada mata abun da doctor ya ce
ba musu MALIKAT INAS ta tashi ita da RIANNA su ka bi bayan doctor din nan
da sallama a bakin su su ka shigo office din shi , nan su ka tardo shi ya na zaune saman chair din shi , ga kuma gudan doctor tsaye ya na rike da wani file ya na duba

cikin girmamawa Doctor ya ce musu bismillah su shigo
karasowa su ka yi cikin office din , su ka zauna saman chair din da ke fuskantar doctor din sannan RIANNA ta ce mishi " Doctor Mike me ya samu dan uwa na ? "

a hankali doctor ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " ranki shi dade , ba na daya da ga cikin likitocin da ke aiki da bugun zuciyar mutum dan tantance ya na raye ko a mace "

da sauri RIANNA ta katse shi da cewa " Doctor Asheem ka daina yi min wani zancen daban , amsar tambaya ta za ka ba ni , me ya samu dan uwa na ? "

" ran ki shi dade Poison ya sha , mun yi kokarin cire poison din da ga cikin jinin shi amma abun ya ci karfin mu , yanzu haka maganar da na ke zuciyar shi ta daina bugawa baki daya , amma Brain din shi na aiki that's why na ce ba na daya da ga cikin likitocin da ke aiki da bugun zuciya "

" Inallillahi wa'ina illaihi raji'un , Inallillahi wa'ina illaihi raji'un ya Allah ka raba mu da mugun ji , RIANNA don Allah ki ce min abun da ya fada karya ce " MALIKAT INAS ta fada kamar za ta yi kuka

cikin nitsuwa doctor din da ke tsaye ya ce mata " sai dai ku yi hakuri ranki shi dade , babban abun tashin hankalin shi ne mun kassa gano wane irin poison ne bare har mu samo mishi antidote "

Doctor Asheem ya amshi zancen da cewa " Indai ba mu samo mishi antidote ba nan da Next week , sai dai mu kai shi US a yi mishi wankin jini , a cire poison din "

" wankin jini fa doctor ! " RIANNA ta fada ta na dan zaro idanu

gyada mata kai doctor ya yi ya na fadin " Ita kadai ce solution din da ta rage mana , dan gaskiya ban taba yin karo da irin wannan poison ba , tsawan shekara goma yanzu ina aikin likita yanzu "

" ina ya ke ? ina son ganin shi " MALIKAT INAS ta fada ta na zubar da hawaye

gyada mata kai doctor din da ke zaune ya yi kafin ya ce mike ya na fadin " bismillah mu je na kai ku bedroom din da ya ke konce "

ba musu RIANNA da MALIKAT INAS su ka mike su ka bi bayan doctor din su ka bar office din
kai tsaye dakin da a ka kontar da Malik su ka nufa
a hankali doctor ya tura kofar ya shiga ya na sallama cen kassan makoshi ya na ce ma su RIANNA bismillah

a hankali RIANNA da MALIKAT INAS su ka shigo cikin dakin su na sallama kassa kassa
su na shigowa idanun su su ka sauka kan Malik da ke konce saman gadon jinya , ya na sanye da wata doguwar riga fara , an saka mishi irin machine din nan da ke taya nunfashi , ga wasu Machine da ban san ko na minene duk saman jikin shi , har wasu wayoyi na ga sun fito da ga cikin rigar shi
Fatar jikin shi ta kara haske his face turned pale , kamar babu rai a jikin shi

RIANNA na ganin shi kuka ya kubce mata da gudu ta juya ta fice dan ba za ta iya jure ganin shi cikin wannan halin ba

MALIKAT INAS kuwa a hankali ta fara takawa ta karaso bakin gadon ta kai hannu saman kumatun shi
ai ba shiri ta janye hannun ta ta na furta " inallillahi , doctor ya na ji jikin shi da sanyi haka " ta fadawa Doctor dan ba karamin sanyi jikin shi ya yi ba kamar wanda ke cikin fridge

shi dai ba shi da abun da zai ce mata gaskiya , dan shi kan shi ya ji babu dadi cikin zuciyar shi ganin halin da Malik ke ciki

❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤


(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥





( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )





STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊






BOOK ________3 👑✌






P A G E 8 🌹🕊





▪AFTER SOME MINUTES


▪INAYA



a hankali ta ware idanun ta ta na karanto kalmar shahada , da ga nan kawai ta shiga kiran sunan yaya Zayd

da sauri RIANNA da ke zaune saman sofa ta tasso ta komo bakin ta zauna ta kai hannu saman face din Inaya ta na cewa " sannu baby ya jikin na ki ? "

cikin sanyin murya Inaya ta ce mata " aunty RIANNA ina yaya Zayd di na ? "

" Kar ki damu baby , ba abun da ya same shi kin ji ko ? " RIANNA ta fada cikin sigar rarrashi
a hankali Inaya ta mike zaune ta na kokarin tashi ta ce " Aunty RIANNA zan je na gan shi " ta kai karshen ta na kokarin sauko kafafun ta kassa

da sauri RIANNA ta ce mata " no baby kar ki sauko " ta fada saboda raunin da ta samu a kafa , kar ta ji zafi idan ta taka

ko sauraron ta Inaya ba ta yi ba ta sauko da kafafun ta , ta mike tsaye ta na fadin " Aunty RIANNA ni zan je na ga yaya Zayd di na "

da sauri RIANNA ta taro ta ta na fadin " Baby yi a hankali , akwai zafi ? "
a hankali Inaya ta fara takawa ta na fadin " Aunty RIANNA don Allah ki kai ni wajen yaya Zayd di na "

" baby don Allah dawo ki zauna , ba ki jin zafi a kafafun ki " ta fada cikin sanyin murya

girgiza kai Inaya ta yi ta na cewa " Aunty RIANNA ni babu abun da na ke ji , ni kawai ni kai ni wajen yaya Zayd di na , ni kai ni wajen yaya Zayd di na " ta kai karshen ta na sakin kuka

ajiyar zuciya RIANNA ta sauke ta na kallon Inaya da ke faman kuka , ta rasa abun da za ta yi , ba ta tunanin Inaya za ta iya jure ganin Halin da Malik ke ciki , ko ita kassa jurewa ta yi bare Inaya

babu yadda ta iya haka ta mike ta riko hannun ta , su ka baro dakin , kai tsaye room din da a ka kontar da Malik su ka nufa
da Sallama a bakin RIANNA ta shiga cikin room din ta na rike da hannun Inaya

a hankali MALIKAT INAS ta dago kai ta kali saitin kofar ta na amsa mata sallamar
ta na ganin ta tare da Inaya ta saki wani dan karamin murmushin karfin hali ta ce " baby har kin tashi ? "

gyada mata kai kawai Inaya ta yi ta na dan karamin murmushi kafin ta tako a hankali ta karaso bakin gadon da Malik ke konce ta kai hannu ta taba kumatun shi
ba tare da ta janye hannun ta ba ta ce " Ammie , jikin shi ya yi sanyi sosai kamar ice "

Shiru MALIKAT INAS ta yi dan ba ta da abun da za ta fada mata ita kan ta ta rasa dalilin da ya sa jikin shi ya yi sanyi Haka bayan kuma doctor sun ce ya na raye bai mutu ba

su na a haka kawai su ka ga Inaya ta janyo chair a hankali ta zauna bakin gadon , ta riko hannun shi ta daura saman kumatun ta ta na wani dan karamin murmushi , kafin ta sauko shi ta kai bakin ta saitin kunnen shi ta ce mishi " kar ka damu baby na , ba abun da zai same ka

Please Login or Register in order to submit comment