Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a ke yi wa tambarin a jiki , Idan namiji ne a wuya a ke yi mishi , mace kuma cikin hannu " ta kai karshen ta na janye hannun rigar ta na dama ta na nuna mishi bayan hannun ta , Tak tak irin zanen da ke cikin wuyan shi

" To amma Ammie bayan yaran Malik sauran yaran masarautar a na yi musu shi ? "

" a'a Gaskiya , yaran Malik kadai a ke yi wa shi , yanzu idan ka duba Aysher , Manisha , Djamila ka dai san yaran papi din ka ba sai na fada maka su ba , duk mu na da wannan tambarin , amma for exemple yanzu kamar Muntaz ko Hafsat ka ga mothers din su su ne Diyan Malik Abdoul latif kennan su jikokin Malik ne , a na ba su wani bracelet na Gold mai dauke da tambarin tun su na baby kuma ba a son ya fita da ga cikin hannun su , Saboda shi ne masarautar Saudia , tun lokacin Malik ABDOULAZIZ ya kafa wannan tambarin , a sanni na Sword din ta na nufi irin yakin da su ka sha kafin su kafa wannan masarautar ta Saudiya "

gyada kan shi kawai Malik ya yi ba tare da ya ce komai ba ya fada duniyar tunanin shi
bari dai mu takaice labarin , inin ranar Malik a part din MALIKAT INAS ya yi shi , Sallat ce kadai ke fitar da shi , a nan su ka yi maganar Auren RIANNA da Aymane ya ba da shawarar a yi auren Ranar Friday tare da na Tesnim da Abdoul , ba musu su ka amince da maganar shi
sai wajen sallar isha ya baro part din amma sai da ya biya wajen MALIKAT AL'UMU ya yi mata magana a kan auren Tesnim da Abdoul ita ma ba ta yi mishi musu sai ma farin ciki da ta nuna , ita ma dai MALIKAT AL'UMU ba ta kyale shi ba sai da ta tsokane shi iya son ran ta kuka kadai a bai yi mata ba
bai baro part din ta ba sai wajen Sallar Isha , ya tafi Mosque , da ga nan kuma ya kama hanyar part din shi



▪ROUKSAR


cikin bacin rai Damba ke kallon ta irin kallon nan na sai na kashe ki
cike da fargaba ta ce mishi " Damba ka yarda da ni , Sau uku ina saka poison din na a cikin abincin da a ka kai wa yarinyar nan "

cikin bacin rai ya ce mata " Kar ki raina min hankali , Idan kin saka mata poison din ya a ka yi ba ta mutu ba , ga shi yanzu wacen sakaran yaron ya fadawa Malik gaskiyar yadda a ka yi ya kashe Malik , kuma ya fara bincike a kai ya kamata yarinyar nan ta mutu tun kafin ya gano wanda ya saka shi , yadda laifin mutuwar ta zai ratayu a kan shi bayan na Malik "

kamar za ta yi kuka Rouksar ta ce mishi " Damba , na fada maka ni da kai na na saka mata poison har sai uku , kuma ina da tabbacin t........ " Kut maganar ta yanke ta na zaro idanu ta na kallon Damba

" Lafiya ki ka yi shiru ? " Damba ya fada ya na tsare ta da ido

wasu yawu ta hadiye kafin ta ce " Damba , ni dai na san sau uku ina tura abincin part din Malik da sunnan MALIKAT AL'UMU ta turo shi kuma duk da poison a ciki , kuma ina da tabbacin Yarinyar nan ta ci abincin "

cikin rudu Damba ya ce mata " me ki ke son ki ce ? "

" Damba , poison di na ba karamin poison ba ne , dan ko magani ba shi da shi , kuma yarinyar nan ta ci shi har sai uku ba ta mutu ba , hakan na nushi Aljanun ta sun tashi "

da sauri Damba ya katse ta da cewa " ki na nufin ita da Malik sun ...... "

bai kai karshen maganar shi ba Rouksar ta katse shi da cewa " they had sex " ta kai karshen baki sake

Girgiza mata kai Damba ya yi ya na fadin " no ! no ! no ! no ! " ya fadi na karshen da karfi ya na juyawa ya kai wa bishiyar bayan shi wani mugun bugu har sai da hannun shi ya fara zubar da jini

a razane Rouksar ta ce " Shikenan , Shikenan , shikenan ta kare mana ta kare mana ta kare mana , ko rabin shirin mu ba mu kai ba ga shi har ya baci "

"no , ba zan yi wannan aikin a banza ba , dole na zama Malik din Saudiya , ta ya a ka yi sihirin da na yi mishi ya kare da sauki haka ?

cikin rudu Rouksar ta ce mishi " wani sihiri kuma Damba ? "

wani dan karamin tsaki ya ja ya na fadin " na hana shi kusantar mace , duk lokacin da ya kusanci mace , zai ji dick din shi na yi mishi zafi kamar za ta kama da wuta , amma ga shi sihirin ya kare , dole na san abun yi , ba zan bar Nawfel saman kujerar nan ba "

da sauri Rouksar ta katse shi da cewa " To yanzu ya za mu yi ? ka na dai ji fa yarinyar nan poison di na ta sha ba ta mutu ba , ka na ganin za ta bari wani abu ya samu Malik ? "

ba ta gama rufe bakin ta ba Damba ya juyo a zafafe ya damko wuyan ta ya na cewa " duk ai laifin ki ne , tun yaushe na ce ki kashe yarinyar nan , Har part din MALIKAT AL'UMU ta koma da zama amma ki ka kassa yin komai a kai "

cikin wata disashashiyar murya ta ce mishi " Damba sake ni " ta fada dan ba karamar shaka ya yi mata ba sautin ma da kyair ya fito

da kyau ya waro idanun shi ya ce " No Rouksar ba za ki sa shiri na ya baci ba , Idan na fadi ki tabbata ke ma za ki fadi , Idan har ta dalilin ki ban zama Malik ba sai na ga bayan ki da hannu na "

kamar kiftawa Rouksar ta lumshe idanun ta ta sake bude su , sun koma kamar na maciji , cikin abun da bai kai dakika Biyar ba , duk fatar jikin ta ta koma irin ta maciji hannayan ta su ka bace bat , nan take ta koma wani dankareren Maciji Green color wanda griman shi ya ma fi bishiyar da ke bayan Damba

Damba kuwa tun lokacin da ya ga idanun ta sun sauya ya janye hannun shi da ga saman wuyan ta , ya koma baya kadan ya ja tsaki

sai da macijin nan na Rouksar ya yi wani razanannan kuka sannan ya bace bat , sai ga Rouksar ta dawo tsaye gaban Damba amma har yanzu idanun ta na maciji ne

cikin wata razananiyar murya mara dadin ji ta ce mishi " Kar ka manta ko ni wacece Damba "

ba ta gama rufe bakin ta ba Damba ya matso kusa da ita ya na kallon Ta cikin ido ya ce " kar ki manta ko ni wanene Rouksar " ya na gama fadar haka idanun shi su ka juye kamar yadda a ke juya PAGE din littafi su ka koma na maciji kafin su dawo dai'dai

wasu wahalalun yawu Rouksar ta hadiye kafin ta meda idanun ta dai'dai ta dan ja da baya

a hankali shi ba Damba ya ja baya ya ce " ya dai fi miki , nan gaba ki san irin maganar da za ki fadamin , gwara ki je ki samo yadda za ki yi ki kashe yarinyar nan " ya na gama fadar haka ya bace bat

ya na barin wajen Rouksar ta saki wani kukan kura sannan ta bace bat ita ma
NI YANZU ABUN NAN YA FARA BAN TSORO , NA MA KASSA GANE MANUFAR WANNAN DAMBA , KAMATA YA YI YA CE KASHE MALIK WHY ZAI CE TA KASHE INAYA ?



▪INAYA


zaune ta ke cikin parlourn su saman carpet , ta na sanye da kananan kayan barcin ta ta saki gashin ta ya zubo mata har saman shoulder sai tashin qamshi ta ke
ga bowl a gaban ta cike da popcorn , ga tray kuma a gefe shake da fruits da Juice , sai kallon Tv ta ke cikin konciyar hankali

ta na a haka Kofar lift ta bude Malik ya shigo parlourn ya na sallama kassa kassa
wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta amsa mishi sallamar shi
sai da ya karaso tsakiyar parlourn sannan ya tsaya ya bude mata hannayan shi

murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta mike da sauri ta nufe shi da gudu
sai da ta zo dab da shi sannan ta tsaya ta na kallon shi
" Lafiya ki ka tsaya ? " ya fada cikin sanyin murya

turo dan bakin nan nata ta yi ta juya mishi baya ta ce " ni na manta fushi na ke da kai "

a hankali ya sauke hannayan shi ya ce " Cutie me ku ma na yi za ki yi fushi da ni ? "

" Tun fa safe da ka futa ba ka dawo waje na ba sai yanzu , ka san irin kewar ka da na yi kuwa ? "

a hankali ta karaso wajen ta ya sa hannayan shi ya rungumo ta ta baya ya kontar da kan shi saman shoulder din ta sannan ya ce mata " Ni ma na yi kewar ki sosai My Cutie "

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " shikenan na ji , yanzu ka je ka yi wanka sai ka dawo mu kali Film ya na da dadi sosai "

a hankali ya dago hannun shi ya janye gashin da ya zubo mata a saman shoulder sannan ya kai lips din shi ya manna mata kiss ya na cewa " an gama ran ki shi dade , bayan haka ku da bukatar wani abu ? "

girgiza mishi kai ta yi kafin ta ce " no hakan ma ta isa "

sakin ta ya yi kafin ya ce mata " shikenan jira ni , ina zuwa " ya na gama fadar haka ya fara takawa zai bar wajen

da sauri ta riko hannun shi
cak ya tsaya ya juyo a hankali ya ce mata " Cutie me ya faru ? "

a hankali ta tako ta tsaya gaban shi da hannu ta mishi allamun ya sunkuyo
ba musu ya sunkuyo da kan shi ya rage tsawon shi
dan bakin ta ta kai saitin kunnen shi ta yi mishi rada

a hankali ya zagayo da hannun shi guda a kugunta ya janyo ta jikin shi ya ce mata " Ummm da gaske ki na so na yi miki ? "

gyada mishi kai ta yi a hankali ta na shagwabe fuska
lips din shi ya kai saman forehead din ta ya manna mata kiss sannan ya ce " okay bari na yi wanka , sai na dawo na yi miki , mai dadi ma kuwa " ya na gama fadar haka ya sake ta ya juya ya nufi corridor

da kallo ta raka shi har sai da ya shiga sannan ta koma ta zauna , ta kai hannu saman sofa ta dauki wani pillow sannan ta sauko shi kassa ta konta

after one hour , ya fito da ga cikin corridor ya na sanye da kayan barcin shi Red color ma su mugun kyau , ya saki wannan lalawsan gashin kan shi sai tashin qamshi ya ke , Hannun shi rike da laptop din shi gudan kuma ya na rike da wayar shi

a haka ya karaso cikin parlourn ya nufe ta ya zauna kusan ta , ya mike kafafun shi sannan ya daura laptop din shi a saman cinyoyin shi ya bude ya fara latsawa

sai da ya share good 30 minutes a haka kafin ya kai hannu ya dauki wayar shi ya fara latsawa na dan lokaci sannan ya kai ta a kunne
cikin nitsuwa ya ce " Na tura maka Lambar wata mota ina son sanin da sunnan wa a ka yi register din ta "
ya na gama fadar haka ya sauko wayar ya katse kiran , shi kadai ya san da wa ya ke wayar dan ni ban ji komai ba , 🤔🤔🤔 lambar wace mota ce ya tura mishi ma ?

ya na katse kiran ya kashe laptop din shi , ya rufe ya meda shi gefe ya daura wayar a sama sannan ya juya ya kale ta
Har ta yi barci , sai nunfashi ta ke saukewa a hankali a hankali

ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya ya konta geffen ta ya sa hannu ya janyo ta jikin shi sannan ya kai lips din shi saman forehead din ta ya manna mata kiss sannan ya sauko saman lips din ta ya manna mata kiss

maimakon ya yi barci kawai sai ya tsaya ya zuba mata wadanan hazel eyes din nashi , kamar ya meda ta cikin jikin shi ya ke ji

ya na a haka kawai ya ga ta saki wani cool murmushi murya kassa kassa ta ce " baby kallon ya isa haka , rufe idanun ka ka yi barci "

dan zaro idanu ya yi ya na kallon ta ya ce " dama ba barci ki ke ba ? "

shiru ta yi ba ta amsa mishi ba ,
da allamu dai aljanun nata ne su ka yi mishi magana 🤣🤣🤣🤣
a hankali ya lumshe idanun shi , ba jimawa barci ya yi gaba da shi



▪MISALIN KARFE 2 NA DARE


a hankali ya fara jiyo wayar shi ta na ringing
slowly ya ware idanun shi ya na karanto adu'ar tashi da ga barci
ya na bude idanun shi sai cikin nata , ba karamar razana ya yi ba , bare kuma cikin bacin nasu ya juya da ita ta dawo saman shi ko ni ce sai na ji tsoro

" wayar ka " ta fada mishi cikin sanyin murya
ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kai hannun shi ya dauki wayar shi ya kali screen din
wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya dauki kiran ya kai wayar a kunne ko sallama bai yi ba ya ce " General why za ka kira ni a irin wannan lokacin , ba za ka bari safiya ta yi ba ? "

shiru ya yi ya na sauraron abun da General ke fada mishi
sannan ya ce mishi " General ka na jin abun da ka ke fada , yanzu fa ? "
yanzu ma shiru ya yi ya na sauraron abun da General ke fada mishi sannan ya amsa mishi da cewa " Okay i'm coming " ya na gama fadar haka ya sauko wayar ya katse kiran sannan ya latsa wayar na dan dakikai sannan ya kashe ta ya ajiye gefe

a hankali ya juyo ya kali Inaya , cikin sanyin murya ya ce " Cutie ? "
" uhm " ta fada ba tare da ta dago kan ta ba
" zan fita amma ba zan jima zan dawo " ya fada ya na kai hannu saman bayan ta ya na shafawa a hankali

da sauri ta dago kan ta da ga saman Chest din shi kamar za ta yi kuka ta ce mishi " Baby , yanzu fa ? ni gaskiya babu inda za ka je " ta kai karshen ta na meda kan ta saman chest din shi ta kankame shi da kyau

cikin sigar rarrashi ya ce mata " please Cutie , ki bari na je wlh ana jira na "
girgiza mishi kai ta yi ta na cewa " ni gaskiya babu inda za ka je cikin daren nan "
" Shikenan tashi mu tafi tare "

a hankali ta dago kan ta, ta ce mishi " da gaske ? "
gyada mata kai kawai ya yi kafin ya ce " sauka yanzu "
ba musu ta sauka da ga saman jikin shi ta koma gefe ta zauna
ta na sauka ya mike ya fara takawa ya nufi corridor ya bar ta nan zaune

jim kadan ya fito Sanye da jallabiya Fara kal mai dogayen hannuwa
hannun shi kuma ya na rike da wata Abaya Fara kal ita ma , da veil din ta
wajen ta ya karaso , ya mika mata hannu
ba musu ta daura hannun ta saman nashi ta mike tsaye
ta na mikewa ya bude abayar hannun shi ya saka mata ita , sannan ya yafa mata veil din ya riko hannun ta su ka nufi lift a tare

kai tsaye part din su ka baro
su na fitowa sai saman wata dankareriar mota baka kirin , Azim na tsaye wajen motar ya na jiran Malik
Da sauri Azim ya bude mishi gidan baya , a hankali Inaya ta daga kafa ta shiga cikin motar sannan shi ma ya shiga Azim ya rufe musu kofar ya yi sauri ya shiga wajen mai zaman banza

ya na shiga Driver ya tada motar su ka bar wajen
motar na barin wajen Inaya ta konta da kan ta saman shoulder din ta ce " Baby ina kuma za mu je ? "

" nowhere " ya fada a takaice
da ga haka ba wanda ya sake cewa komai har sai da su ka karaso Word rooms din masarautar

su na isowa tun kafin Azim ya sauko ya bude mishi kofar ya bude ta da kan shi ya sauko ya yi gaba
da sauri ita ma Inaya ta sauko ta bi bayan shi
ya na shigowa word room din ya ga wasu sojojin biyu tsatsaye a bakin kofar , su na ganin shi su ka sara mishi
bai bi ta kan su ba ya karaso cikin dakin , nan ya ga Hakim Konce saman gado an yi mishi bandeji a kai da hannun daman shi , dayan hannun ya na sanye da catheter a na yi mishi karin jini

cikin rudu Malik ya dago kai ya kali General da ke tsaye dayan geffen gadon ya ce " How ? Ta ya hakan ta faru ne ? "

General na shirin magana Inaya ta shigo dakin , da sauri ta kama Hannun Malik ta kontar da kan ta saman damtsen shi ta na boye Fuskar ta

wani cool murmushi General ya saki kafin ya sara mata
sannan ya kali Malik ya ce " wani ne ya kai mishi hari a cikin cell din shi "
" He is Die ? " Malik ya tambaye shi

General bai ce mishi komai ba ya kai hannu ya daga mishi rigar shi , nan ya ga wani bandejin a cikin shi da allamun wuka a ka caka mishi
" i'm sorry Sir , he is Die " General ya fada ya na janye hannun shi ya meda shi a baya ya rike su

cike da takaici Malik ya ce " How ku na zaman me da har za a kai mishi hari cikin cell har a kashe shi , zaman me ku ke ? General Abdallah Tell me ya ka ke so na........ "

bai kai karshen maganar shi ba Inaya ta katse shi da cewa " baby kontar da hankalin ka , bai fa mutu ba "

ba shiri General da ya sunkuyar da kai tun lokacin da Malik magana ya dago shi ya na kallon Inaya , shi ba katse Malik da ta yi ba ya sa shi dago kai , babyn da ta ce mishi tsakani da Allah shi da ita wa za a ce ma baby

ya yi nisa cikin duniyar tunanin shi ya jiyo Muryar Malik ya na fadin " please Cutie keep quiet "

marairaice mishi fuska ta yi ta na cewa " Please baby ka tsaya ka ji mana "

dan karamin tsaki Malik ya yi ya na kauda kai gefe cikin bacin rai , yanzun hanyar shi guda da zai kamo wanda ya saka a kashe Malik ta mutu ya zai yi

ya na a haka kawai ya ji Inaya ta janye hannun ta da ga cikin nashi
slowly ya juyo ya kale ta irin kallon nan na me za ki yi
cikin girmamawa ta ce " na ce maka bai mutu ba , Ka ba ni izini ranka shi dade na gwada maka "

a hankali ya gyada mata kai allamun ya ba ta izini
wani cool murmushi ta saki kafin ta tako a hankali ta karaso gaban gadon Hakim ta tsaya ta na kallon shi na dan dakikai

nan take idanun ta su ka koma Farare kal ko digon baki babu a ciki har wani haske su ke kamar torch

Dum General ya ji zuciyar shi ta buga har wani baya ya yi ya na karanto kalmar shahada ya na dafe saitin zuciyar shi kamar dan shi ya ke fuskantar ta

cikin rudu Malik ya ce mishi " General Lafiya ? "
Ina fa General babu bakin magana zuciyar shi sai duka uku uku ta ke yi ya na kallon Inaya babu ko kiftawa

a hankali ta dago hannun ta , ta daura saman cikin Hakim inda a ka yi mishi Dressing ta dan danna kadan ta lumshe idanun ta
wani irin dogon nunfashi Hakim ya ja har sai da kirjin shi ya yi sama kafin ya koma ya shiga yin nunfashi da karfi ya bude idanun shi slowly

da sauri Inaya ta bude idanun ta sun koma dai'dai , ta ja da baya ta na dafe saitin zuciyar ta ita ma zuciyarta na bugawa da karfi

da sauri Malik ya taro ta ya na cewa " Cutie are you okay ? "
a hankali ta juyo ta kale shi kafin ta gyada mishi kai da ga haka ta fada jikin shi ta rungume shi

sunkuyar da kan shi ya yi ya manna mata kiss saman forehead din ta sannan ya dago ya kali General ya ce " ku ba shi kulawar da ta dace , Idan wani abu ya same shi a wannan karan kai zan tuhuma , Mu hadu a fada Gobe tare da Azzam " ya na gama fadar haka ya sa hannayan shi biyu ya dauki Inaya cak kamar baby ya juya ya fice word room din

su ka bar General nan tsaye ya na faman zaro idanu ya kassa tantance abun da ya faru anya gaskiya ne ko dai mafarki ne ya ke bai sani ba


❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥





( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )





STORY & WRITTEN BY : MEERAH 👑🔥






BOOK ________3 ✍📚🔥







P A G E 3 🥀 ❤





bangaran su Malik kuwa , kai tsaye motar su ya nufa da ita su ka koma part din su
ko da su ka koma part din su maimakon su koma barcin su , kawai su ka shiga sabon aiki , ni dai ina da ga gefe ina kallon su , su ka

Please Login or Register in order to submit comment