Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga hannu sama , kamar da ga sama wata katuwar sword baki kirin mai mugun tsawo ta fito cikin hannunta da ta daga sama
move guda ta yi da hannunta ta raba macijin nan gida biyu da takobin hannunta
nan take wata bakar guguwa ta tashi ta mamaye sa-san macijin nan kafin ta bace bat tare da macijin kamar ba a taba yi ba

ya na bacewa ko Malik da Diya su ka turo kofar dakin su ka shigo kamar an koro su , lokacin da guards din nan su ka shigo dakin guda cikin su ya juya da sauri dan ya je ya fadawa Malik abun da ke faruwa

cak Malik da Diya su ka tsaya su na kallon Inaya tsaye da wannan sword a hannun ta ga idanun ta sun koma bakin kirin ba karamar razana Diya ya yi ba har ya fara karanto kalmar shahada

a hankali Malik ya daga kafa ya karaso cikin dakin , kafin ya yi taku biyu wannan sword din hannun ta ta bace bat , kaya jikin ta su ka koma kamar da farko , a hankali ta fara lumshe idanunta , ta fara yin kassa allamun sumewa za ta yi

da sauri Malik ya tako ya riko kugun ta ya janyo ta jikin shi , ya daura hannunshi saman kumatunta ya fara bubugawa a hankali ya na cewa " Cutie , Cutie ! "

wani irin dogon nunfashi Inaya ta ja , a razane ta ware idanun ta ta na sakin kara
da sauri ya rungume ta jikin shi ya na fadin " calm down ba abun da ya faru "
ta na jin Muryar shi ta sauke wata nanauyar ajiyar zuciya

a hankali ya dago ta da ga jikin shi ya talabo face din ta da hannayanshi ya ce " shikenan ? "
a hankali ta gyada mishi kai ta na sakin wani dan karamin murmushi
lips din shi ya kai saman forehead din ta ya manna mata kiss kafin ya raba ta geffen ta ya nufi MALIKAT AL'UMU ya riko hannayan ta ya ce " momy , ki na lafiya ? "

a rude MALIKAT AL'UMU ke fadin " Nawfel , mafarki na ke yi amma ko ? "
cikin sigar rarrashi ya ce mata " calm down momy , ba abun da ya faru , ki kontar da hankalin ki "

da sauri ta katse shi da cewa " Nawfel ta ya za ka ce na kontar da hankalina , yarinyar da ta girma gaban idona ta koma maciji , ni , ni , ni ban ma san yadda zan kwatanta maka , wacece yarinyar nan da ka kawo matsayin matar , wlh mutum ba ce aljana ce " ta fada da allamun ta fita cikin hayacin ta

a hankali Malik ya juya ya kalli Inaya da ke tsaye kamar an dassa ta a wajen
wata yar karamar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juyo ya kalli MALIKAT AL'UMU ya ce " momy , ba abun da ya faru , ki kontar da hankalin ki please "

a hankali MALIKAT AL'UMU ta sauke ajiyar zuciya ta na lumshe idanun ta , ya na jin ta sauke ajiyar zuciya ya juya ya kalli Tesnim da ke konce a wajen

hannu ya kai hannu wajen yar drawer da ke bakin gadon , ya dauki bottle din ruwa guda , ya bude ya zuba kadan a hannunshi ya yarfawa Tesnim

wata razananiyar kara ta saki ta na dawo cikin hayacinta kafin ta mike da sauri ta fada jikin MALIKAT AL'UMU ta na sakin kuka kamar mahaukaciya

a hankali ya daura hannun shi saman face din Tesnim ya na fadin " Tesnim , ki kontar da hankalin ki please "

slowly ta ware idanun ta , ba su sauka ko ina ba sai cikin na Inaya
wata yar karamar kara ta saki ta na lumshe idanunta da karfi ta kara kankame MALIKAT AL'UMU

cikin sanyin murya Malik ya ce mata " Tesnim , ki kontar da hankalin ki ki fada min abun da ya faru "

ba tare da ta bude idanun ta ba ta shiga ba shi labarin abun da ya faru tun shigowar Inaya dakin har zuwa lokacin da ta suma

a hankali Malik ya juya ya kalli Inaya ta ce " minene a cikin bishiyar da ki ka ce a cire ? "
cikin ko in kula Inaya ta ce mishi " a ciki ne ta boye ruhin momy , da ba a cire ta ba momy ba za ta tashi ba , kuma ita ce ta saka poison cikin fruits din da ka sha , shi ya sa su ka kasa samo mishi antidote saboda na tsafi ne , ni tun da na sauke ido saman yarinyar nan na ji ba ta konta min ba " ta kai karshen ta na turo dan bakin nan nata

kare mata kallo da kyau Malik ya yi kafin ya juya ya kalli Diya da ya yi mutuwar tsaye bakin kofa
da sauri Diya ya girgiza mishi kai allamun bai sani ba

tun kafin Malik ya juyo MALIKAT AL'UMU ta ce mishi " Nawfel , wacece yarinyar nan ? aljana ce ba mutum ba "

cikin nitsuwa Malik ya mike ya juya ya kalli Diya ya ce " ka sa a shirya min jet yanzu zuwa US "

gyada mishi kai Diya ya yi kafin ya juya ya bar dakin
ya na fita Malik ya juya ya kalli MALIKAT AL'UMU ya ce " Momy , matata ba aljana ba ce mutum ce , dama jira na ke ji tashi , tun da yanzu kin tashi ba zan kwana cikin garin Saudiya ba , i'm tired , na gaji , kullum neman kashe ni a ke yi , har wanda ke jini na bai kyale ni ba ba na tunanin wani zai iya kyale ni saboda wannan banzan Mulkin , na hakura da kujerar Malik , ba zan iya jure wani abu ya samu familyna a dalili na , su je su yi abun da su ke so da kujerar ni dai ba zan sake hawan ta ba "

wani cool murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta mika mishi hannu
ba musu ya daura hannun shi saman nata ya dawo ya zauna
a hankali ta matso da bakin ta saman forehead din shi ta manna mishi kiss ta na fadin " ina matukar alfahari da kai , na sani hawa kujerar nan bai taba zama burinka , amma ba yadda ka iy ta na cikin kaddararka , ba zan tsayar da kai ba , tashi ku tafi , amma idan ku ka isa ka kira ni ka ji ? "

a hankali ya gyada mata kai kafin ya rungume ta
ita ma rungume shi ta yi ta na sa mishi Albarka , da ga haka ya raba jikin shi da na MALIKAT AL'UMU , ya mike tsaye
da sauri Tesnim ta rungume shi ta na kuka ta ce " please Akhie , kar ka tafi ka bar ni , mu tafi tare ma don Allah "

cikin sigar rarrashi ya ce mata " i'm sorry Tesnim , but ba zan iya ba , idan mun sauka zan kira ku "
ya na gama fadar haka ya sa hannu ya raba jikin shi da na Tesnim ya juya ya fara takawa ya karaso gaban Inaya ya riko hannun ta sannan ya juya kadan ya kalli MALIKAT AL'UMU
wani dan karamin murmushin geffen fuska ya sakin mata kafin ya ce " i love you momy "

" i love you my Nawfel " ta fada idanun ta na cikowa da ruwa , babu yadda ta iya dole ta bar shi ya tafi dan kwara a ce ya na nesa da ita a raye da a ce ta rasa shi har abada

da ga haka ya juya ya fara takawa ya na rike da hannun Inaya su ka bar dakin
su na fita Tesnim ta saki wani marayen kuka ta fada jikin MALIKAT AL'UMU

bangaran su Malik kuwa kai tsaye building din su ya koma da ita , su ka wuce floor na hudu
sai da su ka shigo bedroom din su sannan ya saki hannunta , ya ce " ki jira ni ina zuwa "

ba musu ta karaso bakin gadon su ta zauna , jikinta duk ya yi sanyi ta ma rasa abun da za ta ce
ta dan jima a haka kafin ta ga Malik ya fito da ga cikin dressing room ya na sanye da jeans black color da t-shirt purple , ya na janye da wasu trolley guda biyu

tun kafin ya karaso cikin dakin ya ce mata " tashi mu tafi "
a hankali ta mike kamar za ta yi kuka ta ce mishi " baby ! "
cak ya tsaya ya juyo a hankali ya kalle ta , sakin trolley din ya yi ya dawo gaban ta ya tsaya ya na fadin " me ya faru kuma ? "

nan take ta saki kuka ta na fadin " ni ma ban sani ba , ji na ke zuciya ta kamar ta kama da wuta , ba na son mu tafi " ta kai karshen hawaye na zubo mata

a hankali ya kai hannayan shi saman face din ta ya fara goge mata hawayenta ya na fadin " ba ke ki ka ce ki na son mu tafi honey moon ba ? cen za mu tafi , bayan mun huta za mu dawo , kar ki damu kin ji ? kuma ai ga wayar ki nan na dauko idan mun je za ki iya kiran su Nesrine da mama da Abdoul duk za ki iya kiran su , yanzu dai mu tafi kar jirgin mu ya tashi , kin ji My Cutie ? "

wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta gyada mishi kai allamun Eh
bai ce mata komai ya juya ya riko trolley din su ya na ce mata su tafi
ba musu ta bi bayan shi su ka baro part din baki daya ,
su na fitowa ta ga wasu manyan motoci guda biyu jere bakin part din , ga Diya kuma tsaye bakin kofar ta tsakiya

su na fitowa ya saki trolley din hannun shi , ya riko hannun Inaya su ka nufi Motar ta tsakiya , da sauri Azim ya nufi trolley din nan ya janyo su

har zai saka su cikin motar da ke baya , Malik ya ce ya saka a cikin motar tsakiya dan da mota guda zai tafi , ba musu Azim ya dawo wajen motar tsakiya ya bude bayan ta ya saka trolley din

Malik kuwa da kan shi ya budewa Inaya gidan gaba ya ce ta shiga , ba musu ta shiga sannan ya rufe kofar

har ya nufi wajen driver Diya ya riko hannun shi ya na fadin " yanzu da gaske tafiya za ka yi ka bar familyn ka , ka bar ni ? " ya fada ya na marairaice fuska

a hankali Malik ya dawo gaban shi ya tsaya ya na fadin " dama na fada maka , ba zan zauna cikin kassar nan ba , ya kamata na tafi tun wani abu bai sake faruwa ba "

cikin nitsuwa Diya ya katse shi da cewa " kujerar Malik fa , ya ka ke so mu yi da ita ? wa zai ci gaba da kula da kassar Saudiya , please kar ka tafi kowane problem ya na da solution , amma guduwa ba ita ba ce solution din ka ba "

" no Diya , ba guduwa na yi ba , ka gan ta ko ? " ya fada ya na nuna mishi Inaya ta cikin glass din motar
sannan ya ce " idan wani abu ya same ta ta dalilin wannan kujerar ba zan iya yahewa kai na ba , su je na bar musu gadon mahaifina , duk wanda ya ke so ya hau na ba shi izini ko da kuwa kai ne , da ga wannan ranar ku manta da wani Malik mai sunan Nawfel a cikin kassar nan dan ba zan sake dawowa cikin ta ba "

da sauri Diya ya fada jikin shi ya rungume shi ya na fadin " don Allah kar ka tafi , at least ka bari har takwaran ka ya shigo duniya ka gan shi kafin ka tafi please ko dan saboda ni kar ka tafi " ya fada kamar zai yi kuka

dan bubuga bayan shi Malik ya yi ya na fadin " I'm sorry Diya , but i can't stay here , rayuwarta ta fiye min wannan dukiyar da Mulkin , dole na tafi ko dan na ci gaba da ganin ta a raye ba tsakanin rai da mutuwa ba "

a hankali Diya ya dago da ga jikin shi ya kai hannu ya na goge hawayenshi , tun kafin ya ce wani abu Malik ya ce mishi " sai watarana " ya raba ta geffen shi ya nufi mazaunin driver , ya shiga sannan driver ya ba shi key din motar ya tada ta
da kan shi ya tukka motar ya bar wajen da mugun gudu

ya na barin wajen shi ma Diya ya juya ya nufi part din shi kamar zai yi kuka

sai da su ka nufi hanyar fita masarautar sannan Inaya ta ce mishi " baby , uncle na yi maka magana "

ba tare da ya juyo ba ya ce " uhm me ya ke cewa ? "

" tabbas ka tafi , amma za ka dawo , dan wannan kujerar a rubuce take cikin tarihin rayuwar ka , ka gudu amma ba ka tsira ba dan yaki yanzu ka fara yin shi , nan ba da jimawa za ka dawo "

ba tare da ya kalle ta ba ya ce " i'm sorry Dad , but ba abun da zai medo ni cikin wannan masarautar , zan sauya tarihin rayuwa ta , kuma za ka gani "

dai'dai lokacin da motar shi za ta bi ta kofar fita masarautar Inaya ta ce mishi " za ka dawo , ni na fada maka "
bai ce mata komai ba ya ci gaba da tukin shi ya nufi hanyar airport , ga shi kuma glass din motar bakake ne ba wanda ya san wa ke cikin motar

🤧🤧🤧🤧 shikenan yanzu Malik ya bar Daular Saudiya ? ya bar kujerar Malik har abada ? yanzu wa zai hau kujerar ? shikenan Aymane ya samu abun da ya ke so
duk masarautar babu wanda bai samu labarin Malik ya yi hijira da matar shi , lokacin da RIANNA ta ji labarin sai da ta samu , sai da ta yi kamar ran ta zai fita , ita kan ta MALIKAT INAS ta sha kuka , shikenan yanzu ta rasa yaronta guda da ya yi mata saura
bangaran Aymane kuwa Meli na kawo mishi labarin Malik ya yi hijira , farin ciki wajen shi kamar zai tsuntsuwa ya tashi sama , shikenan burin shi na zama Malik ya cika , dama Malik ne ya hana burin shi cika yanzu kuma ba ya nan ba wanda zai iya shiga tsakanin shi da kujerar Malik

bangaran su Malik kuwa , kai tsaye Airport ya nufa
ya na isa ya shiga private jet din shi , sun yi good 30 minutes a na shirya tashin jirgin , kafin ma ya tashi Inaya barci ya dauke ta , a haka har jirgin su ya daga ba ta da labari su ka bar kassar Saudiya
SAI DAI NA CE ALLAH YA TSARE KU , ALLAH YA KARE KASSAR SAUDIYA DA GA SHAIRIN AYMANE 🤧🤧
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment