Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kujerun parlorn kememe yaki Zama a kujerar, 'yanaga kadawo dawuri? Koko sauran kayan ka kazo kwasa? Aida bakaxo ba saika yi waya idan yaso maba bireba yakawo maka sauran kayan inji Alhaji muktar yayinda ko kallon AK baiyi ba, shiko wani takaici yakara turnuke shi ganin iyayan shi sun daina sanshi da tausayin shi duk akan wata shegiyar Aisha, 'dukda haka bata baci ba zan yarda kayi kwanan karshe a cikin gidana, naba mamarka makullin daya daga cikin gidajena kaje chan ka zauna insha Allah nakusan kawo maka iyalin ka, 'nifa banda kudin dazan iya zuba kaya a cikin gidan, inji AK
Cikeda mamaki Mamie ta kalle shi wai AK ne baida kudi, 'Karka damu ai ninaga zan iya nasa muku duk wani abunda zaku bukata a matsayina na Uban Amarya uban Ango kuda akaima Auran gata? Lefenka ma ake hadawa bana bukatar ko kwandalar ka, ahtoh daddy yafadi yayinda AK ya wuce daki kai tsaye cikin takaici.


AK ya tare a dankareran gidan su Wanda ya hadu ya hadu ya hadu harya gaji da haduwa, gidan ba gidan sama bane four bedroom ne manya manya sai katotan parlor Guda daya a tsakiyar dakunan yayinda kowane daki yanada bayi harda parlor kowani daki saida a zuba furniture's hadaddu parlor kuwa Royal kujeru ne har set biyu sky blue da Orange, sai barayin dinnin dinda aka kewaye shida transparent glass komai na wurin white ne gskia dady ba karamin kudi ya zuba a gidan ba, hmmmm sai Wanda yagani bari inyi shiru kada ace zan zuba karya🀭.


Mamie ce ta aika gidansu Aisha aka amso measurements din kayan ta da size din takalmi da undis nan aka hada mata lefen ta mai rai da lafiya akwati set daya yayinda aka dinka kayan ciki sosai bayan an kwana biyu Mamie da kanta tazo da direba inda ta dauki Aishar basu zame ko'ina ba sai babban boutique English wears taita jidan ma Aishar a cewarta so takeyi ta rikita AK tanaso taga yazo ya durkusa yana musu godiya akan aura mishi Aishar da akayi kunya ta cika Aishar inda take ji kamar ta nutse a kasa, kaya ne naban mamaki masu daukar hankali ko kunya Mamie bataji ba nanta dinga gayama Aishar kissar mallake miji cikin dabara saikace ba sirikarka ba, itako Aishar jinta takeyi a sama duniyar ta fes, tun daga ranar Kullum da safe zatazo ta dauke ta takaita wurin gyaran jiki na amare, hmmmm Allah sarki Naira, cikin kwanaki Uku kachal Aisha tayi masifar kyau naban mamaki tayi fresh color dinta yakara fitowa gashin nan ba'a magana yayinda akaita dura mata maganin mata a zuciyar Mamie kuwa sotake AK yayi har kukan Agwagwa Ranan 1st 9ytπŸ˜‰oooh su Mamie iyayan Zamani, ranar karshe Kunshi akakai Aisha akai mata baki daja, hmmmmmm Kara gyara mata kanta akayi inda Mamie ta hadata da turaruka masu matukar kyau da motsa Sha'awa, sai wurin la'asar suka dawo nan take shaida ma Ramata akan daddy zaizo karfe Tara na Dare shi da kanshi zaikai Amarya dakin ta ba'a bukatar yan rakiya idan yaso bayan an kwana biyu sai aje aga daki, Hmmmm zo kuga bakin Aisha har saida yakusa yagewa saboda murnar zata kwana da masoyin ta ayau, tunda yamma Ramata ta hada mata ruwan wanka na turare kala kala, nanfa Aisha abun naima yasamu taita durzan fatan jikin ta a cewarta ayau zata fara hada jiki da Rabin Ranta muradin ta AK, shiru kakeji kamar an aiki bawa garinsu yayinda Ramata take shirin binta bayin sugani ko wani wabu yafaru ne ko nakuda takeyi ai ya isa ace ta haihu Yanzu inji Ramata, haba har ana shirin shin sallar Isha'e, Aisha kuwa badan taso ba ta fito kassncewar ruwan yakare kuma fatar jikinta yafara zafi durza yasha bana kadan ba, 'harara Ramata tabita dashi, aina zaci bcci kikayi a bayin, Kota kansu batabi ba tafara kwalliya mai daukar hankali tana rera wakar soyya cikin nishadi.

"So bai karewaaaa
"So bai chanzawa aaa
"Wanda nake kauna "da'eman fa bazai "chanza baa gani gaka, harda rufe fuska a dole tanaba kanta kunya, bilki kuwa daga uhmm sai uhm uhm, suna ganin ikon Allah, turare taita sawa kala kala saida bilki ta kwace kwalbar a hannun ta, nan tasaka wani dankareran red lase dinda yagaji da haduwa cikin kayan lefenta Mamie ta bata dazu tace shi zatasa idan za'a kaita, lefenta tuni ankai mata gidanta ko ganin shi basuyi ba a cewar Mamie Sa gani achan gidan, wow bilki ke cewa ita kanta yayar Tata tamata ba kadan ba ko makiyin ki wlh Anty Aisha idan yaganki saiyace shegiya amma fa tayi kyau, mayafin kayan tasa Wanda keda digo digon baki tareda flat shoes tasha dankunne ta sarka da zobe harda agogo da warwaro sak Amaryar masu kudi sunan da bilki tasa mata kenan a lokacin, 'Ramata da garbati sai santin ta sukeyi saikace ba ita ba lallai kudi sunyi, nan sukaita mata nasiha da fada mai shiga zuciyar mai sauraro inda Ramata keta kukan rabuwa da murnar Aurarda Aisha, itako Aishar batama San sunayi ba dukta kosa daddy yazo inda Rabin fadan dasuke mata ke shiga kunnan ta ya fita ta dayan kunnan jefi jefi tana Satan kallon agogo wurin karfe Tara saura, maiya tsaida Daddy? Itafa takosa akaita taga mijinta, 'toh Kidai rike maraicin ki kinsan wacece ke basai na tuna miki ba mu talakawa ne lis bamuda gata saina Allah, ke ai ko ba,ai miki fada ba ya isa kima kanki ganin irin Rayuwar da mukeyi har a unguwan nan, hakuri Aisha, Hakuri bazan daina maimaita miki ba, kiyi hakuri, girgiza kai kawai takeyi cikin mayafi sai a lokacin ne ta matso jaririn kwallar rabuwa da yan'uwanta bilki kuwa kuka takeyi kamar zata suma saika rantse itace Amaryar dukta kankame Aisha, aikowa akayi daddy yazo daukar ta, inda dakyar garbati ya sashi shigowa suka gaisa sama sama da Ramata daketa zuba godiya da kuka, rike hannun ta bilki tayi inda ta bude mata bayan motan ta zauna yayinda daddy ke zaune gaban mota shida driver dinshi, Inda akace bilki zata kawo mata kayan da akai mata anan zuwa jibi insha Allah,motar na tashi ta tsinci kanta da muguwar faduwar gaba tareda fargaban yanda daren nasu nayau zai kasance itafa tsoro takeji Allah yasa AK ya bita a hankali saboda tataba ji Wata yar'islamiyyar su tana bada labarin 1st 9yt dinta idan tace har saida ta suma, hmmmm nan takara rikicewa tana Addu'ar Allah yasa mijinta yabita a hankali.



Bakaramin rikitata gidan nata yayi ba ko'a duniyar mafarki bata taba gani da zuwa irin gidan nan Wanda harya gaji da haduwa ba bare kuma ace nata ne, ooh Allah kenan Dare daya yakanyi Bature, da Addu'a ta shiga gidan kamar yanda Ramata ta umarce ta, wani sanyi AC neya ratsa su yayinda gogan ke kwance nashe nashe yana shan madarar shanu mai kyau cikin kwanciyar hankali yake kallon American movie dinshi sanye da kananan kayan shan iska su matukar yimai kyau, mikewa yayi tareda gaishe da daddy cikin fa'raa da murna kamar bashi ba, shi kanshi daddy yayi mutukar mamakin sauyin AK, kodai ya dangana ne? Inji daddy, idan ma bai dangana ba dole zaiyi kuwa, a zuciyar shi yake fadi yayinda AK da Aisha ke zaune a kasa daddy nakan kujera, nasiha yayi musu mai shiga jiki tun bare AK yaita tausasa shi har saidaga karshe yatashi ya Mike tareda kallon Aisha, 'zan aiko miki da waya na tambayi mamarku tace bakida waya zansa miki number na a ciki, zan dinga jin yanayin zaman naku ko kallon banza yaimiki Wanda zuciyar ki bata amince dashi ba kiyi gaggawan sanar dani, Allah yaimiki Albarka yabaku zu'ri'a dayyiba, kaikuma ina jiranka ka aiko min da gawarta domin yanzu mun Riga Munsa kafar wando daya ni dakai, 'subhanallah daddy Dan Allah kayi hakuri nayi nadamar abunda naimuku kaida Mamie insha Allah babu Wanda zaiji kanmu katayani ba Mamie hakuri idan an kwana biyu zamuzo sai in Kara bata hakurin, cikin jin dadi Dady yace, 'a'a kuyi zaman ku kada kaje ko'ina ku huta Sannan kuzo, fita daddy yayi yayinda AK yatafi mai rakiya, tunda suka fita takara gyara mayafin kanta a cewarta angon ta ne zai yaye mata kamar yanda akeyi a Al'adance, shiko AK tun shigowar ta parlon turaren ta yagama susuta shi wani irin turare ne wannan? Kai waya bata? Gskia kamshin shi yamasa jiki a mace ya shiga parlon.




*Mrs Sadik RumahπŸ’…πŸ»*
[13/11, 03:04] Frd Group Yareema: πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*


*Written by Anty Mamie*



*Dedicated to sister Husnah*



20



Tanajin motsin shigowar Sa takara natsuwa dakin shiya wuce kai tsaye Kota kanta baibi ba, inda shiru shiru babu ango babu labarin Ango kafarta harta fara tsamin gajiyar Zama gawata yinwa datake ji rabonta da abinci tun rana saboda zumudi batama wani ci sosai ba a cewarta yau zataci kazar amarci, har karfe sha'daya darabi shiru tana zaune a wuri daya inda sai a lokacin hankalinta yakara tashi toh kodai ya manta an kawo mishi Amaryar sane? Gashi taga yakara mata wani masifar kyau dukda ta cikin mayafi ta kalle shi, shiko gogan yana kwance nashe nashe akan gado sai chatting yakeyi a Facebook tareda frnds dinshi hankali kwance inda kamshin turaran ta daya shaka duk yabi ya hanashi sukuni, tsaki yaja a karo ba adadi tareda mikewa, gskia dole in nema matar mutunci in Aura mutum shi kadai kullum Ga Sha'awa hakurina yafara karewa shekara talatin da biyu ba wasa ba, ya furta parlon ya wuce ta inda ya dinga bin wutan gidan yana kashe wa haryazo kanna parlon, kashe kayan kallo yayi harya kashe wutan parlon ta Mike ganin baisan da halittar taba, 'Yaya AK, tafadi cikin hanzari ta Mike,Yaya..tasamu kanta dajin nauyin shi inda lokaci daya ya tsaya yana Kare mata kallo hadeda kunna wutan parlon, 'ya akayi? Menene? Jarabarki ta motsa ne?? Ooooh ba haka kikai tsammani bako? Kin saba jin namiji kwance akan cinyarki wace irin Amarya ce wannan? Banda iskanci harkin fara nema na uwar mai zan miki Wanda ba'a taba miki ba? Look bari in kankara miki warning na farko yafadi yana nunata da yatsa, nidai ba mazinaci bane asalima ko yatsar Wata macen ban taba rikewa ba ma'ana ni tsarkakekke ne tas Alhmdlh, sannan ni bantaba cin diyar Wata ba, duk Randa kika Kara mun magana kiyi kuka da kanki kada kisake kiyima kanki wani kallo na daban a cikin gidan nan, kisama ranki kinzo a lokacin bayi, rayuwar bauta zakiyi idan nace miki yar'aiki toh kinsamu promotion, noooo noooo ke baiwace black monkey kawai wawiya mazinaciya mai fuska biyu simi simi kamar mutuniyar Arziki idonshi harya fara rinewa yayinda Aisha kafarta Sam takasa daukarta hawaye daya nabin dayan jikinta na wani irin rawa yayinda zufa yagama wanke ta dukda sanyin AC, takowa yayi har gabanta murmushi kwance akan fuskar shi wuyanta ya shako hadeda dago kanta yana mata kallon kiyayyah, congratulations na tayaki murnar samun namiji Irina Wanda babu kamarsa amma kamar yanda zaki fara ganin babu kamana a mugunta, congratulations daga rana tayau kunyi bankwana da farinciki a duniyar ki, ina tayaki murnar sabuwar rayuwar bauta, kakari tafara cikeda azaba nan yayi wurgi da ita kan glass cup dinda yagama shan fresh milk bakaramin bugewa tayi a kanta ba, juyawa yayi sannan yakara dawowa, 'Akwai mai gadi na dattijon Aziki ina neman Alfarman kada ki bata tsohon mutane domin mijin marigayiya ne ance kefa jarabar taki har tsofaffi baki bari ba, kiyimun Alfarma iskancin ki ya tsaya a waje banda yan aikina wlh wlh zan iya kashe ki har lahira Randa na kamaki dawani a gidan nan, sannan inada masu bama flowers ruwa damai wanke mun mota, congratulations a dalilin ki kinsa sun rasa aikin su bazan barki da gattin samari masu jini a Jika a cikin gida ba kamar naba kura Ajiyar nama ne, 'kanshi yadaga Alamar yana tunani chan yadawo ya tsuguna yadago fuskarta da hawaye yagama wankewa, 'bazan taba baki damar kizama karuwar gida ba kada kazantar zunibin kiya halakamu baki daya, idan jarabar kita motsa kinsan inda zaki GA kwartayan ki, Wuceta yayi hadeda rufe bedroom dinshi harda Sa mukulli a cewarshi kada taimasa fyade tunda ankawo ta cikin maza babu abunda bazata iya ba.

Anan ta kwanta kanta dukya kulle tarasa abun yi inda sai wurin biyun Dare ta Mike taci kuka harta gode Allah taita shiga sauran dakunan harta gane dakin ta saboda ganin hadaddun akwatunan lefen ta, komai na dakin dark purple ne yayi matukar kyau amma Sam bai burge taba Yanzu dama ba Auran soyya tayi ba? Mai AK ke nufi?? Dukda taji matukar takaicin abunda yaimata amma soyyar shi nanan daram dam a zuciyar ta.

Tun daga ranar tafara aikin bauta a gidan, AK ya kori matasa masu gyara gidan a cewarsa ankawo kura cikin garkin nama kudin sallama yabasu sosai nan aikin gidan yadawo kanta mace da wankin mota harda gyaran flowers idan tatashi tun asuba bata Kara komawa bcci, idanko tayi lattin wanke mai mota ranar hmmm bakaramin duka zata Shaba, idan yadawo ya taddata tana bcci kuwa ruwan sanyi mai kankara zai dinga watsa mata tijara iri iri babu Wanda bata gani ba nan tasa mai suna *farin mugu na* ta tsani AK amma a iya bakin ta, kullum muguwar kaunarshi ke samun masauki a Ranta duk yanda tayi kokarin fito na fito da zuciyarta abun yaci tura, Babu Wanda yasan halinda take ciki sai bilki itama ranan tazo gidan ta taradda Aisha da AK a kitchen inda yayi fatali da indomie Wanda shine yasata dafa mai a cewarsa kanme zata dafa mai haka babu kifin gwangwani shiba matsiyaci bane shida kudin shi aita masa mugunta akan abincin dayake siyowa, batada aikin yi saidai taci ta cika Masai da kashi mai wari sai uban kiba datake narkawa a kugu,ana haka bilki ta shigo indai Ranta yai mugun baci har saida ta tanka mai, 'karya kakeyi ka kiramu da matsiyata tunda munada wadatar zuci sannan kashin ma ni'ema ce mutum yace shi baya kashi mana sai uban takama da iyayin Gayu kamar kaidin baka kashi...... Rufe mata baki Aisha tayi inda bilki ta dinga ruwan masifa, AK kuwa baibi ta kanta ba a cewarsa ita ba sa'ar yinsa bace wacce tasata ita zata girbe mata abunda tasata ta shuka mai, Aikuwa bilki taita masifa ta wanke Aisha Tass inda Aisha taita bata hakuri akan kada a gayama Ramata da garbati dakyar bilki ta yanda saboda rashin lafiyar da Ramatan keyi akai akai tun bayan Rasuwar babansu kullum yau ciwo gobe lafiya.

Haka AK da Aisha ke Rayuwa har ayau shekara Uku da Auransa, dawowa gida yayi da yamma misalin karfe biyar kamshin girkin Aisha dukya cika gidan tun a tsakar gida yabude kofofin hancin shi tareda shakar kamshin abincin daya gama Kara masa yinwar Sa dukda bayacin girkin nata sai idan taimasa shida Abokanan Sa Wanda saita jera abinci kala biyar duk ita kadai a cewarsa kada ta kuskura taba wani yaimasa girki tunda ya taba taradda bilki tana tayata ranan tasha azaba wai ana jagwalgwala masa abincin daya kashe kudi akai, dukda baci yakeyi ba saida ya gasa ta, 'Shigowa parlon yayi daidai da daukewar farin cikin daya dawo gidan dashi dalilin wakan da take rerawa mai matukar dadin gaske cikin muryarta mai sanyi da zaki yaji tana cewa.

'AK ne Raayina
"AK sona yakeyi yana bala'en jidani,.
" na rubuta sunan AK akasa ruwa aka goge wlh kosun goge basu goge sanshi a zuciya ba.......ido biyun da sukayi baki sake batasan sanda ta tsuguna tana bashi hakuri harga Allah batasan yadawo ba cikin mamakin Sa ya juya yatafi a ranar baimata komai ba, a cewar Sa hukuncin Laifin ta zai iya kashe ta saboda hakoran bakinta ya kamata ya banbare a cewarsa kada yafara kisa akanta shiyasa ya kyale ta saboda bata taba bata masa rai irin na ranar ba wai AK Santa yakeyi yana ba'laen jida ita kalmar Nance tafi komai kona masa rai inda Yaji Aishar tagama cutar dashi.




*Cigaban labari*


Leemah ce zaune gaban Malam liman yana shaida mata wani matashi anan bayan unguwar su yazo ya same shi akan yana Santa da Aure inda Malam liman yace bazai ma diyarsa dole ba amma yaje ya nemi soyyar ta yabashi izini, sanar mata yayi akan zatayi bako daga yau zai dinga zuwa da yamma saboda bayasan tadin Dare su daidaita idan yamata toh idan baimata ba kada ta cuci kanta babu mai mata dole, Amincewa tayi lokaci daya tun bataga bakon nata ba ta amince zata iya Auran shi saboda wani kudiri Wanda ita kadai tasan abunda ke ran nata.






*Mrs Saddiq Rumah πŸ’…πŸ»*

[13/11, 03:06] Frd Group Yareema: πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?*πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€



*Written by Anty Mamie*


*Dedicated to sister Husnah*



21



Da yamma misalin karfe biyar na yammacin ranar talata wani karamin yaro neya shigo gidan Malam liman inda yake shaidawa ana sallama da halima inji Ahmed, kassncewar tasan da Zuwan bakon nata bata wani bata lokaci ba ta zurkuma zumbulelan hijab dinta sky blue Wanda ke Jan har kasa, fuskarta da kwalliya ba laifi, sanarda mama tayi zuwan bakon nata inda ta fita ta same shi jikin Wata katuwar bishiyar dake kofar gidan nasu, ba laifi yana da kyau daidai misali saidai zata fishi tsawo da haske domin baki ne maidan jiki, hakan bai dami halima ba koda kuwa mummuna ne futuk ba matsala bane a wurinta, zaune yake akan Mashin dinshi Roba Roba yayi wankan manyan kaya sai zuba kamshi yakeyi, nan taimishi sallama hadeda gaishe shi, batareda bata lokaci ba ya shaida mata kudirin Sa a akanta domin a shirye yake yagama komai, Ahmad ya kasance cikin soyyar ta tunda dadewa sanin dokar gidansu yarinya saita gama secondary ake mata Aure shiyasa yaita shirin shi a hankali kassncewar yanzu tana gafda gamawa yabashi karfin gwaiwar tunkararta da Maganar inda bawani kwana kwana ta Amince nan take, ba karamin dadi hakan yaimasa ba, cikin lokaci kadan suka fara soyya mai tsafta daban Sha'awa a kwana a tashi har iyaye suka shiga Maganar, kawayanta su meenah kuwa babu irin surutun da basuyi mata ba ko kadan bata Dace da Ahmad ba ai gara ta Auri daya daga cikin Alhazawan da suke holewa tare idan ma Auran takeso, mutum ya tashi a talauci ya koma talauci kai kenan Kullum babu wani cigaba, nanta warware musu kudirin ta gameda Auran nashi aiko abun yamusu dadi nan suka hau mata kirari, 'hoooo dakin hutu yar'gidan malamai muna yinki ilimin nan naki ba'a dakin hutu kawai ya tsaya ba eyehh kanki fa Naja kina wutaaaa diyar Malam, muma munbi ki munbi sahu irin naki zamuyi Alkur'an.
Ansa bikin halima nanda Wata Uku masu zuwa, inda Ahmad mutum ne mai matukar ibada kullum cikin rokar Albarkan dake cikin Auran da zaiyi yakeyi baida aiki sai sadaka da istahara kullum akan Allah ya kauda fitina tareda basu kyakyawan zu'ria bakaramin San halima yakeyi ba itama ba laifi tana Dan jinshi sama sama koba komai yana bata kulawa na musamman Ga kyauta akai akai, hankalin mahuta ba karamin tashi yayi ba sanda yasamu labarin Auran halimar inda dakyar ta lallashe shi akan cewa Aure ne na lokaci kadan bawai Zama zataje tayi ba babu yanda batayi ba akan ya fahimce ta ina Sam ya kasa kishi ya rufe masa ido, nan yadan Saki Ranshi kadan ganin kulawar da take bashi yamafi Nada tana matukar sakin mishi jiki tareda Alkawarin ko bayan Auran babu abunda zai Chanza.



Mahuta ne kwance a dakin shi inda kishi ya turnuke shi bayajin zai iya barin wani ya lasar mishi zumar dashi kadai yafara lasa kuma yake kan lasa, inaaa bazai taba barin wani ya huta da kayan hutun shiba, wayar shiya dauko a gefen shi batareda bata lokaci ba ya shiga messages dinshi number Ahmed dayasa a nemo masa yaketa kallo nan ya yanke shawarar abunda zaiyi.

Ahmad ne zaune a cikin Abokanan shi suna fira shigowar messages yaji awayarsa nan ya dauko wayar tareda dubawa salati ya Saki kanshi har sarawa yakeyi.


*Ina tayaka murnar Auranda zakayi, Abun takaici a matsayin kana kimtsatse baka dace da mace irin halima ba, halima tamu ce ta irinmu ce masu gidan hutu, wlh wlh wlh Nina fara cin halima tun tana shekara sha Hudu tazama katifa ta kullum saina hau ruwan cikin ta inda sau biyu tana zubar da cikina.*



Tambayar da Abokanan shi ke masa neya sakashi tattaro natsuwar Sa, Lafiya maiya faru haka?
'Ba komai ba komai ina zuwa bari intafi gida sai munyi waya, Kassncewar a Mike yake tun sanda yaga sakon hakan yasashi tafiya gida kai tsaye ranar ko wurin halima bai jeba sai sake sake yakeyi daga karshe ya tattara komai ya watsar a cewarsa mace mai natsuwa irin halima dole tasamu masoya dayawa masu Sha'awar Mallakar ta, ya ajiye hakan akan wani kesan rabasu domin ya mallake ta.

Halima kuwa sai rawan kai akeyi tanata yad'awa zatayi Aure sai banke banke take bankawa babu Wanda Ahmad ya gayama abunda ke faruwa.





*Mrs Saddiq RumahπŸ’…πŸ»*
[13/11, 03:06] Frd Group Yareema: πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*


*Ina farin cikin gayyatar ku bikin kanwata wacce nake jida ita chan cikin zuciyata Husnah Wanda za'ayi a cikin satin nan insha Allah a garin Kano, muna bukatar Addu'ar ku akan Allah yabasu zaman lfy mai dorewa tareda zuri'a dayyibaπŸ™πŸΌ* Zaku iya jina a cikin satin nan amma banyi Alkawari ba sai yanda ta kasance idan nasamu lokaci toh Ga page har biyu namuku yau.


*Written by Anty Mamie*


*Dedicated to sister Husna Amaryar gobe mai farin jiniπŸ˜πŸ’ƒπŸ½*


22


Wasa wasa fa Karamar magana tazama Babba mahuta baida aikinda ya wuce turama Ahmad texts din yanda yake holewa da halima tareda shaida masa akan ya bincika gaskiyar maganar, tun abun bai damun Ahmad har ya shaida ma Abokanan Sa inda nan suka kwantar masa da hankali akan kishi ke damun mahuta mace kamar halima mai ilimi da natsuwa diyar malamai jikan malamai sharrin mutane ne kawai, nan ya yanke shawara akan zai gwada halimar inda idan suna waya jefi jefi zai dinga sako maganar batsa Wanda ada baya mata hakan kwata kwata, abun mamaki sai yaga bata damu da hakan ba ko kadan bata taba nuna masa rashin dacewar hakan ba, saima nunawa datayi tafisan irin firar akan kowace fira dayake mata, nan zaita gaya mata yanda zai mata idan sunyi Aure, haka zatai ta biye mishi babu kunya hankalin Ahmad yayi mutukar tashi ko a mafarki bai taba tunanin zata biye mai ba, nan yakara bullo mata dawani salo idan yazo tadi kafun yatafi saiya San yanda zaiyi ko hannun ta ya rike nan ma bata Hana shiba😳, ana haka Wata rana mahuta ya turo masa dawani text dinda yakara birkita shi inda yake cemasa.

*Gskia ango Amaryar ka tabude dayawa nayi mamakin budewar ta dukda kasancewar nikadai ke shiga ramin nata, waiii zurkumi, wlh wlh jiya na durje ta tun safe muke Abu daya har yamma, hahahaa koda yake kafi kowa sanin bata gida jiya da yamma har zuwa Dare muna tare ka kirata da la'asar ina jin sanda take gaya ma kada kazo bata gida inda a wurina take yin haddar da aka turata a gidansu, na goge mata tsaf tareda dasa mata karatuna a kanta. Idan namata karya kada Allah yasa inga Annabi, Nina fara cin halima*


Bakaramin tashin hankali ya shiga ba ganin furucin da akai na karshe, wanene zai iyama kanshi wannan fatan? Wani riba mahuta zai samu idan yaimata karya GA manya manyan rantsuwar dayakeyi Anya babu Alamar gskia a lamarin nan kuwa?? Harda cewa kada Allah yasa yaga Annabi hmmm Da zazzabi ya kwana ranar nan ya yanke shawarar hakura da halima dukda ya dage dakaima Allah kukan Sa Ga sadaka dayake yi akai akai cikin lokaci kadan tafara sire masa, dukda haka ya kudiri aniyar kureta.

Ahmad da halima ne a waya inda yake kashe tada maganganun batsa hankalinta ba karamin tashi yayi ba Sha'awar shi takeyi sosai takosa taji yanda zumar shi yake, ganin yasamu yanda yakeso a wurinta hankalinta yayi sama, 'matata wlh ina tsananin bukatar ki har nakejin bazan iya jura sai an kawoki gidan muba lokacin yamun yawa bby ki taimake ni

Please Login or Register in order to submit comment