Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta hakanan take san abunta.πŸ™πŸΌπŸ˜*


*Dedicated to sister Husnah Amarya*


17


Kan Ya'u akayi ina rai yayi halinsa tuni nan aka dauki kabbara Allah sarki ya'u ashe yanada rabon ganin Auran diyarsa Allah ya dauki Ransa a wurin daurin Auran yar'sa, jama'a nata jimamin lamarin tun bare jarumtar da Alhaji muktar yayi, liman yabada sanarwa da la'asar za'ai mai salla akai shi makwancin shi nan danan wani yaro ya ruga gida batareda bata lokaci ba Amarya taci kwalliyar ta babu laifi tayi kyau tasha lallan gargajiya inda babu wasu yan biki masu yawa sai makwaftar da gulma ce yakawo su harda masu kawo mata gudunmawar maganin mata na Ni'emah maganin matsi kuwa ankawo mata shi babu iyaka wasu saboda cin fuska kawai zasuzo suna mata bayanin yanda zatayi matsi bilki ceke tanka musu yayinda Ramata ta kwabar musu kada kowa ya tanka sunaso ayi rigima ne kuma yau ranar farinciki ne, shinkafa jaluf akayi mai kyau sai faten tsaki, Amarya kuwa kawayan ta basu wuce mutum biyu ba suma Abokanan karatunta ne suka samu labari dukda bata gayyaci kowa ba suko sunzo, 'Aisha ta Auri AK Dan gidan Alhaji muntari Naira, abunda yaron keta shela kenan harya isa gidan, Kai zonan mai naji kana cewa bafa masan iskanci, inji Wata makwafciyar suda ta damki hannun yaron tana shirin ingiza keyarsa waje, Wlh wlh yanzu aka daura Auran Aisha da AK wannan baturan daya dawo kwanaki, yasin idan nayi karya Allah tsinan, 'mikewa Aisha tayi bako kunyar Amare tareda jawo hannun yaron cikin daki, 'ummah kinji fa abunda yake cewa, tafadi tana washe baki nan kallo yakoma kanta, koda karya yakeyi yagama faranta mata ayau tunda ya danganta AK a matsayin mijin Auren ta, nan mata akaita surutu ana karyata zancen, 'yo duk matan garinga hauka yayi dazai Auri diyar unguwan nan, haba Malam banda ma haka GA yara masu komai a unguwa kai dalla wuce kada in zabga maka Mari, inji wasu matan da abun yafara kaisu bango, 'yauwaaa sannan babanku Ya'u mai shayi yafadi ana tunanin kamar Maya rasu, 'salati aka dauka gaba daya nan kowa yagama yarda ya'u ya rasu, Ramata kuwa tunda aka fara maganar kallon kowa dai'dai takeyi tarasa abun cewa koda aka fadi Rasuwar ya'u ko motsi takasa yi nan aka dinga bata baki, ana haka Garbati ya shigo tareda rokon jama'a akan subar musu dakin yanasan ganawa da Mahaifiyar Sa, 'zaure suka koma wasu kuma na zaune kofar gida a cewarsu sai sunga abunda zai ture nadin buzu, 'kallon Aisha yayi yayinda ya kalla bilki, 'ki harhada duk wani abunda Musa yakawo na Aure harda kayan fitan bikin dayayi ta cire wannan na jikinta a hada da sauran a kawomun, sannan mama........babanku ya rasu koh Garba? Ta katse shi tana kallon cikin idonsa, Allah ya gafarta masa mukuma Allah yabamu juriya da tawakkalin rashin nasa, 'jikin shi yayi sanyi yayinda tunda abun yafaru sai lokacin Yaji hawaye nabin kumatun Sa na tausayin mamar tasu da kannan shi, Wata irin mace ce ita mai dakewar zuci? Bata taba bayyana sirrin Ranta, hannunta yakamo zaiyi magana, 'tashe kuje a suturta shi akai shi gidan shina gaskiya, kukuma ku share hawayen ku Addu'a zamu cigaba dayi, 'mikewa yayi zai fita saiya waigo tareda kallon Aisha wacce ta hade kanta da guiwa tana kuka kasa kasa, 'An Daura Auranki da Abdulkareem Dan gidan Alhaji muktar akan sadaki dubu hamsin, dukda tana cikin tashin hankali saida ta dago ta kalli yayan nata idonta taf hawaye, murmushin ke neman subce mata nanta maida kanta akan cinyar ta samun kanta tayi da mika tawassali tareda godiya ga Allah Ashe AK Santa yakeyi?
Ashe ba ita kadai take dakon soyyar shiba?
ashe zata Kara tsintar farinciki a Rayuwar ta lokacin data cire ran samun murmushi a duniyarta sai gashe bayan lokaci mai tsawo ta manta daduk kuncin ta dukda Rasuwar mahaifin ta nanan daram a gefen zuciyarta amma murnar Mallakar AK ya shafe duk wani kunci a tattare da ita, mikewa tayi kamar mahaukaciya tareda girgiza bilki datake gabzan kuka, 'Auta Auta kinji mai yaya yake cewa? Auta Dan Allah ki mareni Auta ki jijjiga ni dukda nasan ba mafarki nakeyi ba inaso in tabbata bani kadai naji Abunda yake cewa ba, cewa fa yayi nazama matan Aure kuma AK na Aura, yaya AK na,
Auta Ashe AK zan Aura? Ashe sona yakeyi? Ashe shine ya Hana Musa Aurena yayinda kaddara taso ta shiga tsakanina dashi, Ummah, tafadi tareda rarrafawa tana rike kafan Ramata dake binta da kallo itada bilki gani sukeyi tadan samu matsala akanta ubanta fa akace ya rasu yanzu amma tana murnan Mallakar namiji ko kunyar idonsu bataji, 'ummah kice wani Abu mana, kinji, kinji umman mu, Kuka tafara yi mai sauti inda kadan yarage Ramata tayi kanta da bugu ganin ta zube a wurin tana kuka mai taba zuciya taji tausayin diyar nata yagama mamaye ta datasan matsayin ta a wurin AK din datafi haka yin kukan babu Wanda ya lallashi wani cikin su Ramata kuwa babu koda digon hawaye a idonta.


Ankai ya'u gidanshi na gaskiya saidai muce Allah ya gafarta mashi idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani, yayinda Garbati yace baza'ai zaman makoki ba sanin babu abunda za'ai a wurin sai gulman mamacin hakan yasa kowa ya watse badan rai yaso ba, 'Mamie ceke tsaye a parlor sai zufa takeyi dankwali rike a hannun ta tunda abun yafaru yan'gulma suka gaya mata komai tareda cikama wandon su iska gudun kada Alhaji muktar yadawo ya samesu a gidan, bakaramin tashin hankali ta shiga ba inda har kukan bakin ciki saida tayi ta kudiri aniyar saidai tarasa Auranta akan Auran Aisha amma Sam danta bazai taba Auran Yar'duniya ba, shigowar Alhaji muktar neya Kara tunzura ta da hanzari ta tarbe shi bakin kofan falo inda taita ruwan Masifa tana zagin Ramata akan asiri sukayi banda aikin Asiri ina AK ina Auran Aisha? Ance kwarya tabi kwarya ko cikin kwaryar bakowace kwarya bace tadace da dangatan danta ba, Aikin banza aikin hofi wlh saiya Saki karuwan nan bazan Zama abun nunawa a gari ba yarinyar da ubanta ke neman ta, 'kallon ta Daddy yayi tunda tafara haukan ta baice mata komai ba kanshi na Sara mishi babu abunda yake bukata sai bcci a lokacin dukda ana neman karfe biyar na yamma, wucewa zaiyi ta tare mishi hanya akan saitaji dalilin tozarcin daya jamusu, 'cikeda takaici ya kalle ta sama da kasa, 'wai bilki baki San mahaifin yarinyar nan ya rasu bane yau? Karona farko tun Auran su dataga yamata irin kallon nan, 'toh sai me? Nice na kashe shi? Ina ruwana dawata Rasuwar shi? Allah na tuba ai gara daya rasu koba komai an rage mugun iri a doran kasa, bai dameni ba wlh yau yau sai an sakar musu da diyarsu, 'hankade ta yayi saida tafadi akan kujera bayasan biye mata bare yadauki mummunan hukunci cikin fushi, yanufa dakin sa yayinda yarage kayan jikin Sa, wai maiyasa mata wani zubin sukeda Karamar kwakwalwa ne? Idan tanada magana dashi aiba haka ya kamata ta tunkare shiba yaushe bilkin ta chanza Halinta ne? Shi za'a kawoma iskanci a cikin gidanshi aiko zaiyi maganin ta daga ita har yaron nata Aure kuma zaiga ubanda ya isa ya raba shi muddin yana raye.



Gogan kuwa yana chan yana harkokin Sa a cikin gari gaba daya gidan nasu baya mishi dadi yanzu ya gwammace yabata lokacin Sa wurin business dinshi hakanan yau ya tsince kanshi da Muguwar faduwar gaba harsaida ya gayama wani Abokin shi inda yabashi shawarar yaita Addu'a kila Alkairi ne zai Same shi, hankalin shi gaba daya ya karkata kan gida hakan yasa shida saura ya doshi unguwan nasu tunda matasa suka hango motar shi nan akaita ihu ana daga masa hannu, Ango Angooo Angoooo kawai kakeji suna fada suna shewa, mamaki yayi toh dawa sukeyi? ango? Kodai sunyi tsammanin wanine bashi ba? Dariya yayi harda Jan tsaki yakara murza zaman hularshi a kanshi, 'oooh mutane da rigima sukeyi kaji wai Ango nida ko budurwa bantaba yiba naiman rigima kawai yawancin suma ban sansu ba, 'yafadi shi kadai, yana isa kofar gida tunda yayi horn kafun mai'gadi ya bude mai tuni wasu sun biyo motarshi a baya inda akan dole ya bude musu glass din motar cikeda mamaki, 'Ango kasha kamshi Dan Alaji yaushe za'a hada mana walimar maza tunda Auran yaxo bawai an shirya bane, 'walimar maza? Ya tambaya cikin mamaki, 'au eh mana wacce akeyi bayan an daura Aure mana, koda yake jeka huta muna nan munanan muna Sa ido Dan Allah kada a manta damu Dan Alaji, wooooo sai Ustaziya yasin Allah barku tare, 'dayaga abun yazama hauka Jan motarshi ciki yayi cikeda Al'ajabin samarin unguwar tasu, haka yafito ya rufe motar jikin shi dukyayi sanyi, mai'gadi kuwa sai kirari yake masa tareda Addu'ar Allah ya sanya Alkairi, 'wucewa yayi baiko bi takanshi ba inda yana shiga parlor ya tadda Mamie ta buga tagumi da hannu biyu biyu cikin yini guda harta Dan fada saboda tashin hankali, 'subhanallah Mamie lfy? Ya tambaya yayinda ya zauna kusada ita, kallon shi takeyi idonta ya rine yayi jajir, 'AK kasan abunda babanku yaimana? Kaji labarin tozarcin dayayi mana? Toh an daura maka Aure yau bayan sallar juma'a kasani idan baka Sani ba kabude kunne kajida kyau kazama mai mata mai iyali, tafadi tareda gyara zamanta harda buga cinyarta, 'dariya yayi har saida fararan hakoran shi suka bayyana, haba Mamie wlh kema kin iya tsokana Auran lfy saikace yaro, 'riko hannun shi tayi tareda kafa mishi ido babu Alamar wasa take kallon shi nan jikin shi yayi sanyi ganin yanayin nata, 'Abdulkareem nataba maka irin wasan nan? Wlh yau aka daura Auran kada Aisha diyar mai shayi, Mikewa yayi zumbur hadeda goge kunnansa harda Dan bugawa a tunanin shi baiji dakyau bane, 'eye? Yafadi yayinda yayi jifa da hular kanshi Mai kikace? Mikewa Mamie tayi hadeda maimaita mai abunda tace, 'chab haba wasa yakeyi duk matan duniya?jada baya baya yakeyi, Idan hukuntani yakeyi saboda naki Auran diyar Aminin Sa toh yanzu na yarda, Mamie Yammata nawa nema a gidan? Sun kai hudu? Wlh idan dukansu yakeso in aura na yarda akan abunda kike danganta nida shi, wlh ina sansu, ko Auran kauye ne aimun na Amince, kowacece na yarda Mamie ina Dadyn? Yafadi yana waige waige waiko zaiga Dadyn a wurinda suke, *Ina Dadyn?* yafadi cikin razanannan ihu har saida jijiyoyi suka furfuto akansa idonshi kamar zasu fado kasa sai zaro su yakeyi sunyi jazur, 'shi maiyasa bai aurota ata biyu ba? Maiyasa baiyi sadakatul jari'ar da itaba bayan yataba Aure? Tunda yataba Aure maiyasa dasai yakara da bazawara why me??
Why?
Why?
Auran fari infara da bazawaran titi?
Haba!
Haba!!.
Bazawara duk mazan gari sun Santa fa, Ustaziyaar banza? Kirarinta fa kenan, wai Ustaziya saboda yanda takeda fuska biyu, Ustaziya koko yar'duniya? yafadi yana yarfa hannunsa duka biyun saikace zai Mari mamin, saidai shi Dadyn ya aureta wlh sakinta zanyi Dan bata auru ba sai zaro mata ido yakeyi itako baki da hanci tasaki tana kallon ikon Allah yayinda take girgiza kanta cikin bacin randa bata taba tsintar kanta a cikin saba, ji takeyi kamar ta rufe shida duka, Dan ubanka AK ni zakaima bakin ciki? da tsufa na kake mun fatan kishiya? Yaron nan bakada mutunci kishiya kakemun fata da tsufana diyar cikina yarinyar Dana raina da hannuna? Lallai ko kishin mamarka bakayi kakemun fatan babanku yakara Aure? Tafadi da Alamar maganar ba karamin zafi taimata ba.





*Mrs Sadik RumahπŸ’…πŸ»*
[13/11, 03:03] Frd Group Yareema: πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*



*Written by Anty Mamie*


*Ina kuke yan hannun dama na🀝🏻godiya Mara iyaka sister futu marubuciyar Ramlat, tareda Asiyar Bachaka marubuciyar Danasani keya, leemat muna jiran sabon novel.Nagode sosai da kaunar ku a gareni.*


*Dedicated to sister Husnah*


18


Babu abunda zai hanani sakinta yanzun nan kuwa, juyawa yayi yayinda sukayi ido Biyu da Alhaji muktar Wanda hayaniyar su yafito dashi daga daki duk abunda suka tattauna akan kunnan shi, AK na shirin Gilmawa Yaji daddy na fadin, 'bazan hanaka sakinta ba kamar yanda ban naimi shawarar Aura maka ita wurin kowa ba haka bazan tilasta maka Zama da ita ba tunda ka nuna ban isa dakai ba shikenan nikuma zan nuna isata a inda na isa, kallon Mamie yayi ita mai zugakan tareda Aisha zasuyi zawarcin kasan da sanin datse igiyoyin Auran Aisha daidai yakeda mutuwar Auran Bilkisu mamarka, a razane Mamie ta kalla daddy yayinda takarasa wurinsa, wai wace bilkin kake magana Alhaji? Ban gane ba badai ni Bilkisu ba? menene hadin Aurena Dana AK? Jama'a aimun Adalici mana Lallai Alhaji kamar bakai ba nice fa bilkin ka yar'fulanin ka shakara kusan Arba'in muna tare ko daga mun murya baka taba yibafa, tafadi jikinta na rawa yayinda hawaye daya nabin daya a idonta....'yauwa sannan kana sakin Aishar ni zanyi sadakatul jari'ar da ita insha Allah bazaku maidani karamin mutumin banza ba dattijon banza Wanda bai isada gidanshi ba kunji na rantse muku, AK kuwa mutuwar tsaye yayi cikeda takaicin Daddy Anya daddy ne kuwa? Idan shine kuma maiya same daddy a'yau? Daddy na shirin barin wurin mamie ta fada a kirjin shi tareda sakin kuka mai cin rai, Ashe zaka iya Rayuwa batare dani ba? Ashe akwai Ranarda ko'a mafarki Zaka iya dangantani da kishiya? Wlh ban zuga AK ba harga Allah mijina babu abunda yarinyar nan ta taba mun Allah yabasu zaman lfy tunda abun yazama haka wlh kowa ya gyara Auran shi bazan bari Aurena ya mutu ba saboda na wani, 'dariya taso taba daddy dakyar ya iya gimtse dariyar Sa, 'haba mamie wlh an cutar dani kada kimun haka, inji AK dayake tunkaran iyayan nashi, 'wlh Abdulkareem kowa yaje ya gyara Auran shi bazan koma gida yin zawarci da tsufa naba bayan haka inasan tsohon mijina ban hadashi da komai ba a duniya dukda ina sanku banda kamarku amma sanku bai isa ya kashe mun Aure naba tareda rugujemun soyyar shekara Arba'en danayi ba, Kara Rungume ta Daddy yayi a jikin Sa cikeda kaunar matar tashi, Yauwa yanzu ne bilkin shi tadawo bilki amma da dukta rikice an birkita mishi mata, Sakinta yayi yayinda ya tunkari dakinsa, 'Dadyn su Abdul na tuba Dan Allah kayi hakuri mai gidana, tafadi harda daga muryar ta, baiko waiwayo ba bayaso ya nuna mata ya sauko dawuri saiya Dan Kara gasata nan gaba bazata Kara jayayya da hukuncin saba, 'AK barin wurin yayi yayinda ya shiga dakinsa da hanzari ko ganin Gabansa baiyi sosai cikin minti Uku yafito da karamar jakar kaya a hannun Sa, 'Yau saika haifi da'mai bakin ciki? Inji Mamie tana kallon AK na saukowa daga steps, 'ina Zaka? Muddun ka dauki hukunci akan Yarinyar nan bazan taba yafe maka ba Abdulkareem kaji na gayama wlh Aure da ita kasama ranka kamar kafara ne mutu ka raba kaida ita muddun ina numfashi idan ba haka ba kuwa bazan yafe maka ba, Aure baifi Aure ba, 'tuni AK yabar gidan cikin motarsa kamar zai tashi sama kanshi kuwa kamar zai fashe tuni zazzabi da ciwon kai mai zafi ya rufe shi dakyar ya iya karasawa 17th hotel tareda kama daki na kwana uku, cikin rawan sanyi ya zube akan gadon dakin kuka ya fashe da karfi kamar mace yana dukan gadon a hankali, 'why Aisha? Why cikin mata maiyasa saike? Maiyasa kika koya mun muguwar tsanarki? Maiyasa? Dukda na guji rayuwarki maiyasa kika sake shiga duniyata tareda zaban Rayuwa dani? Kin cutar dani Aisha wlh bazan yafe miki ba bani kadai zan rayu da bakin ciki ba dukanmu mun rasa abunda mukeso daga rana tayau dukanmu zamu rayu cikin kunci wlh zan dandana Miki kunci kwatankwacin Wanda kika Sani a ciki, maiyasa zanga Aibun ki? 'Yah Rabbi ka sassauta min Aisha a cikin zuciyata, ka rage mun ita ta dameni, kuka yakeyi yana rawan sanyi jikin shi kuwa kamar garwashin wuta saboda zafin zazzabi.

Mamie kuwa wanka ta dauka tareda tsara girki mai matukar dadi cikin gaggawa ada ta kudiri niyyar babu Wanda zaici abincin Dare a gidan saboda Auran AK harsai an mata abunda takeso shiyasa tun kafun daddy ya farga batayi girki ranar ba ta shiga cikin hanzari tayi, Abdulhakeem kuwa yana makaranta achan Egypt gidan babu kowa sai masu aiki da Mijinta hakan yasa ta tunkari dakin shi domin Kara lallashin Sa sai kamshi take zubawa mai tsayawa arai.




Washe gari kuwa karfe goman safe ta shirya cikin shiga ta Alfarma yayinda itada masu aikinta dake dauke da manya manyan kuloli shake da Abincin sadaka Wanda tun daran jiya tasasu dafawa da asuban farin yau, Abinci ne mai rai da lafiya haka aka daddauki kulolin da kwalayan lemuna da ruwan gora katon katon kai tsaye gidan Rasuwa suka nufa hakan datayi ba karamin Kara soyyar ta yayi a zuciyar Alhaji muktar nanda nan tausayin matarshi ya shige shi ganin yanda take matukar tsoran rabuwa dashi, 'Cikeda mamaki Ramata ta tarbe su hannu biyu biyu a kasan Ranta kuwa taji dadi sosai sai a lokacin hankalinta yadan kwanta kwana tayi da tunanin yanda Rayuwar marainiyar yar'ta zai kasance a gidan Alhaji muktar tareda kallan da Mamie zatai musu, samun kanta tayi da washe baki hadeda godema Allah a fili, mikewa Aisha tayi tana gaishe da mamie har kasa ta tsuguna cikeda kunya zata bar dakin Mamie ta rike hannun ta tareda zaunar da ita kusa da inda take, 'gaisuwa Tai musu na rashin da sukayi sosai itada ja'maar gidan ta sannan tace musu Alhaji muktar yace akara musu gaisuwa mika ma Ramata Envelope tayi cikeda kudi a cewarta Alhaji muktar neyace abata, kememe Ramata taki Amsa da ada ne Amsa zatayi amma yanzu bataso suga kwadayin su tunda anzama sirikai kada ace sun siyarda yar'su, dakyar da sudin goshi aka samu Ramata ta Amsa harsaida mutane sukasa baki a cewarsu ta Amsa a matsayin sadaka ba'a maida kyauta, nan yan'unguwa akaita shigowa kwasar abinci mai raida lafiya tunda sukaga shigan kayatattun kulolin Abinci da Hajiya bilki nan akaita shigowa har babu wurin Zama kamar an bada sanarwan jama'a, Mamie tayi minti ashirin a gidan yayinda ta Mike zata tafi, riko hannun Aisha tayi tace ta biyo ta zasuyi magana, kiran Ramatan tayi har waje suka shiga bayan motan ta saboda jama'a dake wucewa, 'Aisha kokuma ince diyata tunda yanzu anzama daya, Dan Allah ki gani kiki gani, duk abunda zai shiga tsakanin kida AK kiyi hakuri kada ki biye mishi ki daure kuba Mara da' kunya Yanzu kowa jira yake aga yanda zakuyi kada ki biye mishi duk abunda zai miki kiyi hakuri kodan saboda ni kinji diyata? Harda rikema Aisha Hannu wacce kunyar duniya tagama rufeta, duk abunda ke damunki ki gayamun ki daukeni a matsayin uwa keda AK mutu ka raba insha Allah nanta roki Ramata Alfarman Kara tausasa Aishar inda sukaita godiyar jin dadin Abunda hajiya Bilkisu tayi nan duka bakin cikin Ramata ya yaye koba komai Aisha tayi dacen surukai ta fannin AK mai sauki ne dama ganin yanda AK din ya tsani Aishar da furicin dayayi a gabanta babu ko kunyar ta a matsayin Mahaifiyar Aishar shike hanata sukuni.

Aishi kuwa dukta kosa ayi sadakan bakwai akaita gidan mijinta masoyinta ji takeyi kamar ace ta tashi ta naimo shi ta bishi, gawata azabar soyyar shida ta Mike mata kullum cikin murmushi zaka ganta batada damuwa ko kadan Yanzu ko bcci takeyi sunan AK take kira mafarkin AK babu Wanda batayi harsai Ramata ta girgiza ta ko bilki, abun yafara damun Ramata inda cikin takaici tafara tankama Aisha, Kidai yi a hankali wlh ba baki nai miki ba muddin kika nunamai soyyar nan zaki sha bakar wahala ace ayi mace ba kunya wannan wace irin Rayuwa ce kika daukan ma kanki dakon soyyar wahala? 'Ummah wlh yayi AK na sona kila fiyeda yanda nake sanshi, 'haka ya gaya miki? Yaushe kika ganshi? Koko sako ya aiko miki na soyyar taki? Kidai yi a hankali banasan hauka da rashin kamun kai, 'Idan Ramata tayi furucin nan Haushi Aishar keji sosai, hakan yasa tafara lallaba Auta bilki akan ta leka mata kofar gidansu AK ko zatagan shi tanaso taga ko yana lfy kwana biyu tarasa sukuni tanasan sanin lafiyar mijinta? Kai tsaye bilki tace mata bazata jeba aiko nan taita dukan bikin cikin takaici, 'wlh Anty kozaki kashe nine babu inda zanje ni wlh haushi yake bani ma ace ko gaisuwa yakasa zuwa yayi mana sirikin shiya rasu haba Dan Allah, 'ke mai kika Sani? Gaisuwa banda Wanda mamarshi taxo tayi a madadin shi? Harfa masu Aikin gidan su sunzo mana gaisuwa da tarin Alheri mai yawa, 'Ramata dake girki a zaure tashi tayi cikeda takaicin Aishar shiga dakin tayi mafici ta dauka ta buga ma Aishar, sannu dadi miji saikije gidan nasu ki bishi, fitar min a daki Mara kunya Kifa kiyaye ni Aisha wlh ranki zai baci akan yaron nan, turo baki Aishar tayi tana gunguni, mutum da mijinsa sai a hanashi jin yanda yake? Gskia baai mata Adalci gara tayi tayi tabar musu gidansu.


Alhaji muktar neya sauko daga dakin shi misalin karfe sha'biyu na rana yana shirin fita, kwalama Mamie dake kitchen tareda yan aiki suna girki kira yayi, 'amsawa tayi hadeda shigowa parlon nasu Zama kusa dashi tayi, Dadyn su Abdul harka shirya Ashe, 'Eh zan Dan fita nisa zanyi sai yamma zan dawo insha Allah, Allah ya dawo dakai lfy mai'gidana Angona ni kadai ta furta cikin murmushi, mikewa yayi sannan ya kalleta, 'danki bai dawo daga gudun hijirar dayayi bane? 'Uhm bari kawai lamarin AK sai a hankali wlh haryau babu labarin shi mamaki yake bani sati daya babu shi Anya Alhaji ko za'a bada cigiyar sane? Duka wayoyinsa a kashe office ma yadaina zuwa, 'bawata cigiyar katon Saurayin dazan bada yanda ya dauki kafa yabar gida toh zai dawo da kafarsa, idan yadawo kice ya gaggauta barin mun gidana nima, Ga mukullin gida na Wanda ke Malali GRA ba'a Dade da kammalawa ba ki bashi ya tarkata yanasa yanasa chan zasu zauna kafun in kai masa matarshi insha Allah.





*Mr's Saddiq RumahπŸ’…πŸ»*
[13/11, 03:03] Frd Group Yareema: πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*

*Alhmdlh nadawo nagode da Addu'ar ku masoya, Gskia banyi niyyan posting yauba but Alkawarin danayi shiyasa kuka jini masu kirana suji lfy ina godiya sosai😍, Zaku cigaba dajina insha Allah daga yanzu*


*Written by Anty Mamie*


*Dedicated to sister Husnah*


19



Ak kwance yake akan gadon dakin hotel dinda yakama a yanzu gadon baida banbanci Dana asibi saboda tun daga ranar daya sauka a dakin ciwo yaita yi kamar bazai kai labari ba family doctor dinsu yakira nan aka Dora mai ruwa babu yanda likitan baiyi akan zaifi samun kulawa a Asibiti Sam yaki yarda yayinda yaima doctor din kashedi mai tsauri akan bayasan iyayanshi Susan inda yake harsai sun neme shi, kimanin kwana Tara kenan yana kwance a dakin dukya fige ya rame sai uban farin daya Kara likitan ne atare dashi yayinda yagama zarkada masa Allurar karshe daya gama Amsa a ranan kashedi yaimasa akan yarage tunani domin yana gafda kamuwa da ciwon zuciya banda hawan jinin dayake dashi a halin yanzu, godiya yaima doctor din nan yafara hada yanasa yanasa a cewarsa ko mutuwa zaiyi gara ya mutu a gaban iyayan shi ba'a dakin hotel ba dukda bawai ya yafe musu cutarshi da sukayi bane😑aa zaidai koma ne kila a yanzu sunyi nadama sun kuma San zafin rashin Sa a kusa dasu, misalin karfe Tara na Dare ya shigo falon nasu yayinda yake tafiya kamar Wanda kwai ya fashe ma aciki hannun shi rikeda jakar gudun hijirar Sa, Daddy da Mamie na zaune a parlor suna kallo cikin nishadi kallo daya zakai musu ka tabbata basuda damuwa, sallamar sane yadawo dasu nan Mamie ta Mike da sauri ta tarbe shi tana salatin ganin yanda ya rame shiko gogan Kara murtuke fuska yayi adole fa anmai laifi, wani irin ciwo kayi haka ka ganka kuwa? daddy kuwa kallo daya yaimasa ya kauda idonshi ya cigaba da kallon shi, 'Ciwo kayi ne AK ka ganka kuwa? Kanaso ka halaka kanka akan abunda bai taka Kara ya karye bako? Tafadi rikeda hannun shi har bakin

Please Login or Register in order to submit comment