Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta furta ganin yanda Aisha keta tsala kuka kamar zata suma, samarin kuwa tuni sukayi cikin gida hannun su rikeda Leda da Alamar siyya sukayi da mamar tasu.

A babban parlon dake kasan gidan sukai masauki kassncewar gidan gidan sama ne, parlon ya tsaru sosai, a gefen kujera Ramata ta zauna yayinda hajiyar tayi tayi ta zauna kan kujera taki, Wata dattijuwa ceta shigo parlon rikeda farantin ruwan sanyi da lemu tanama hajiya sannu da zuwa, amsawa tayi tareda mika ma Ramata ruwan aikuwa ta Amsa ta sha sosai tareda kwanto Aisha tabata tasha nan tayi shiru tana Ajiyar zuciya da Alama zafi neya dameta dama.

Basu bar gidan ba saida hajiya taimata Albishir din bata aikin wanke wanke da gyaran kitchen da tsakar gida, tunda sunada mai musu girki sannan ba abincin kowa suke ciba, cikin Ikon Allah tafara zuwa tareda samun Alheri mai tarin yawa inda kusan anan take saman musu abincin da sukeci a gida, kassncewar idan abinci ya kwana basa ci, nan hajiya taba Ramata izinin dauka tunda dama Almajirai ake dunduma ma, dukda ranar juma'a ana girki na musamman da yamma Almajirai na layi amsar sadakan abinci mai rai da lafiya, nanfa duniya tadawo masu ya'u da Ramata harma da yaransu sabuwa sunyi fes sunyi kyau sosai sun murmure Aisha kuwa sai wayo takeyi tayi bulbul da ita gwanin ban Sha'awa takawa takeyi ko'ina.




*Mr's Sadik Rumah💅🏻*
[14/11, 00:13] ‪+234 814 511 8251‬: 🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*


*Written by Anty Mamie*


*Dedicated to sister Husnah*


*Woooo page biyu harda Read more har biyu🤩dukda haka some one must complain😨😰lemmi c*😏

10




Alhaji muktar babban Dan kasuwa ne kuma ma'aikacin gwamnati inda yake aiki a NGO yayinda yake zaune a unguwan shanu, tareda matarsa hajiya Bilkisu wacce sukai Auran saurayi da budurwa cikeda soyya, Alhaji muktar Dan Asalin jahar katsina ne matar shi kuma yar Yola ce bafulatana kyakyawar mace sun hadu dalilin wani zuwa Yola dayayi cikin ikon Allah har sukai Auran soyya tareda Arzikin yara biyu duka maza, Abdulkareem shine Babba Wanda akafi Sani da AK, sai Abdulhakeem tun akansu haihuwa ta tsaya musu chak dukda a duniya babu abunda suke Sha'awa kamar Tara yara masu yawa Wanda burin hajiya Bilkisu wacce suke kira da Mamie bai wuce ta ganta da diya mace ba, hakan yasa kullum Addu'ar ta kenan samun mace,
Alhaji muktar mutum ne mai tausayin talaka hakama matar tasa, ba karamin kyautata ma talakawan unguwan yakeyi ba hakan yasa a karo da dama yaso barin unguwan talakawa na hanashi ganin yanda suke karuwa dashi matuka dukda yanada gidaje masu dumbun yawa a garin kullum arzikinsa karuwa yakeyi saboda yanda yake wanke dukiyar shi inda yaso yakoma GRA cikin manyan gidajan shi nachan ya koma da iyalan shi amma yan'unguwa sunyi kememe sun hanashi, babu yanda basuyi dashi ba akan yashiga harkar siyasa yaki, a cewarshi bata burge shi.
zuwan su Ramata gidan yasa hajiyar sakewa da Aisha a cewarta yarinyar na burge ta gata kyakyawa gata yar'duma Duma bakaramin gashi Aisha keda shiba inda tayi gadon shi wurin dangin uwa harna uba, kyawawàn halin Ramata neyasa Mamie takara janta a jiki itada diyarta domin tasha gwadata ta hanyoyi da dama kuma cikin ikon Allah bata kamata dawani laifi, soyyar da Mamie kema Aisha yasa AK shiga lamarin ta indai yana gidan tohfa tana hannun shi har fita kofar gida yakeyi da ita yanai mata wasa kassncewar kullum zaka ganta fesfes an tubke mata gashi gwanin ban Sha'awa, hakan yasa Ramata na zuwa Mamie ke amsarta taita mata wasa itama, shakuwa sosai ke tsakanin AK da Aisha, inda a yanzu a'kalla takai shekara hudu a duniya wayau da surutu kuwa ba'a magana komai Yaya AK, hakan yasa Mamie ke tsokanar AK Take cemishi Angon Aisha, na Aisha wasa wasa shima yafara kiranta da matarshi, inda babu Wanda yayi zargin wani Abu, shakuwar AK da Aisha ba'a magana inda hajiya har kaya siyan mata takeyi hakan yasa Alhaji ma yafara sake mata ganin iyalin Sa na kaunar yarinya shima ta shiga Ranshi, nan Ramata tasa Aisha awata islamiyya anan unguwan tana zuwa safe da yamma, A'nanan har babanta yasata awata makarantar gwamnati tafara zuwa Boko cikin lokaci kadan takara wayau sosai, a kwana a tashi saiga wani cikin ya kuma bullowa a jikin Ramata nan taita rainon abunta har Allah ya sauke ta lfy ta haifi diya mace inda a wannan karan hajiya Bilkisu akaima takwara a cewarsu basuda kamarsu a kaf unguwan bayan mai unguwa, bazasu manta Alkairin su a garesu ba, sunji dadin karan da akai musu nan suka Kara rike juna da Amana.

Abunda masu karatu basu Sani ba shine ya'u Nada wani mugun hali tun a kasarsu nijar babban mashayi ne kuma dan'chacha ko bayan daya Auri Ramata babu abunda yafasa a halinshi talaucin daya mamaye sune yasa ya ajiye shaye shayen a gefe ganin baida kudin dazai siya tareda ma Ramata Alkawarin dainawa yayi gaba daya tunda yara sun fara girma baiso yabar musu abun kunya, ganin yanda kudi ke shigo mishi yanzu gakuma matarshi kusan ta dauke mai hidimar ci Dasha na gida hakan yasa yadawo da tsohon halin shi, tun yanayi a boye har Ramata ta farga hankalinta ba karamin tashi yayi ba, inda zata tasa shi a gaba taita masa magiya tana rokon Sa tana kuka, haka zaikara mata Alkawarin daina wa, Wata rana idan ya bugu tana magana zai lakada mata duka a daki tanaji tana gani zai jibge ta haka zata hadiye kukanta a cewarta bataso kukanta ya tona asirin uban yaranta, haka yaran zasu makure a bango suna kuka ganin yanda ake jibgar mamarsu, washe gari haka zaizo ya tsugunna yana bata hakuri da nadama, amma hakan bazata chanza zani ba. babu yanda batayi dashi akan su nema hayan gida kusa dasu koda wani daki dayan ne tunda garbati ma yafara Zama saurayi, dakin yamusu kadan ga Aisha tafara girma rai biyar dakin bazai dauke suba amma kememe ya shafa ma idon shi toka dukda yanada kudin yin hakan a yanzu ganin biyan kudin hayan dakin da zai kama kamar barnan kudi ne gara yasha kudin shi yayi tatil haka zai shigo yana rangaji tareda zage zage tun yan unguwa basu farga ba har aka fara ganewa inda sanaar shayin ma yadaina garbati keyi yanzu shi saidai ya kwanta a gida idan Ramata tatafi aikatau yaita baccin Asara, wasa wasa abun nashi yai tsanani inda akaita kaima mai unguwa karar shi, hakan yasa ya kirashi yai masa nasiha sosai, hakuri yaita badawa, inda har cewa yakeyi asiri akai masa daga kasarsu a cewarshi wai sun sami labarin rufin asirin shine, Jama'a saidai suce Allah shi kyauta, Daya daina na kwana biyu zai dawo ruwa tsundum harma yafi Nada.





Shakuwar AK da Aisha ba'a magana, inda AK bai hadata da komai ba hidima yake mata baji ba gani a lokacin ya mallaki hankalin kanshi yazama kyakyawan saurayi sosai, babu abunda yafi kauna kamar ka danganta shida Aisha tun bare idan kace mai mijin Aisha hmmm har kowa yagane hakan ita kanta Aisha dadin hakan takeji komai Yaya AK bakinta baitaba rabuwa da sunan shi, a lokacin yafara shirye shiryen barin kasar zuwa Egypt yin jami'ar shi dukda baiso hakan ba a cewarsa wazai kula maida Aishar Sa, dakyar iyayan suka lallaba shiya tafi, inda Aisha ta rikice lokacin tafara Zama budurwa itama har abinci saida ta daina ci dukta rame nanfa iyayan suka fara tsoran shakuwar dake tsakanin su. A kwana a tashi babu wuya komai na tafiya daidai banda halin ya'u dake Kara birkicewa dukya rikice yakara tsufa abun na damun iyalan Sa tun bare Aisha da a makaranta har gori ake mata haka zatai ta kuka tun bata saba ba harta saba mai unguwan yaso korarsu a karo da dama tuno Laifin wani baya taba shafar wani saboda darajar matarshi da yaran shi Wanda suka samu shaida mai kyau a unguwan shiyasa ake daga mai kafa, inda Aisha tazama Silent kasancewar batada kawaye a cewar su babu Wanda zaiyi harka da diyar mashayi, nan kewar yayanta yakara cikata saidai ta kwanta a daki taita kukan kewar AK Wanda a lokacin tagama yarda shine farin cikin ta, tagama yarda idan bada shita rayu ba toh rayuwar Tata batada wani Amfani, tagama yarda sanshi takeyi soyya Mara iyaka inda Ramata tun tana biye mata suna labarin harta fara tausaya ma diyar Tata ganin dala da gwauron dutsen data dauko ma kanta ko'a duniyar mafarki AK ba sa'an ta bane hakan yasa Ramata tadage dayimata Addu'a Allah ya yaye mata larurar data Dora ma kanta.
Ta fannin mamie kuwa komai na tafiya daidai duk sanda zasuyi waya da AK baida abun tambaya sai Aisha, tun bata damuwa abun yafara damun ta nan ta taka mai birki bataso zargin da takeyi yazama gaske, ganin yanda Ranta baisan hakan yasashi daina tambayar badan Ranshi naso ba, Mamie babu abunda suka Fasa yima Ramata da yaranta dukda sanin halin ya'u saidai mommy taita bata hakuri da tattausan kalamai.



A kwana a tashi lokaci na ta tafiya tun Aisha nasa ran dawowar AK harta dangana saidai soyyar shi nanan daram a Ranta tareda Alkawarin bazata taba mai kishiya a Ranta ba, yayinda ta bangaran shi kuwa iyayanshi kekai mishi ziyara a cewar su gara ya zauna wuri daya saiya gama komai da komai tas na karatun shi domin yana hada Degree gara ya karasa gaba daya zasu dinga zuwa tareda kanin shi Abdulhakeem Wanda a yanzu shima yake shirin komawa chan karatu.

A lokacin ne makerin budurwa yagama kawata halittar Aisha fiyeda tunanin mai tunani tahada duk abunda ake bukata a wurin mace, Allah ya wadata tada zaunannan baya 'duwawu' ga tudu kamar ka Dora Kofi ya zauna daram🤭 ga hips masha Allah ga kirjin nan ya cika yayi dam Tubarkallah, da taimakon shafaffen cikinta shape din halittar ta yakara baiyana, ko hijab tasaka idan tana tafiya komai na jikinta saiya dinga kadawa, kiban jikinta a wuri biyu yake hakan ba karamin tsokale ma samarin unguwan ido yakeyi ba uwa uba Allah ya zuba mata natsuwa ta musamman kullum cikin dogon hijab zaka ganta hakan yasa yan iskan samari saka fara samata ido, inda Ramata ta farga Kullum cikin yimata Addu'a da nasiha takeyi hakan yasa take Kara suturta kanta kokadan bata shigan banza.


*Bakar rana........coming soon*










*Mr's Sadik Rumah💅🏻*
[14/11, 00:14] ‪+234 814 511 8251‬: 🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*


*Written by Anty Mamie*

*Dedicated to sister Husnah*


11


Tunda Aisha tazama cikakkiyar budurwa a lokacin tanada ilimin Addini Daidai gwargwado, Boko kuma tana SS1 Makarantar gwamnati, nanfa samari suka yo mata chara, yawancin marasa jin unguwan ne duk Wanda yasan unguwan shanu yasan ba laifi akwai marasa ji saidai Allah ya shirya kawai, hakan yasa bata kula kowa ganin duk babu na kwarai koma akwai babu hurumin shi a gefen zuciyarta, nanfa suka Kara samata ido wasu harda zagi idan tafito, tana diyar mai shayi da rake amma tana girman kai, wasu suce rufa mata Asiri zasuyi danta samu ana Santa diyar Dan kwaya, hakan yasa tasa katon audiga tareda toshe kunnan ta, Ramata kuwa Kullum cikin hannunka mai sanda take mata yayinda yayanta garbati abun yafi damun shi fiyeda kowa amma ya zaiyi? Wasu yan'iskan ma cewa sukeyi darajar shi takeci mai akai da diyar mashayi dan cha-cha?
Ya'u kuwa ko'a kwalar rigarsa hidimarsa yakeyi.
Cikin masu takura mata akwai wani Saurayin dake zaune a cikin gidan su Wanda yake dan'sara suka ne yayi suna a unguwar wurin rashin ji, duk inda ka ambaci *Virus* tohfa harta yaro yasan da zaman shi a unguwar, maguwar Sha'awar Aisha yakeyi tunda ya kyalla ido yaga surarta, hakan yasa yaita mata tayin soyyar Sa babu yanda baiyi ba ko darajar magana baya samu dukda yana aiko mata da kananan kyauta kozata kula shi saidai ta kori Dan sakon tareda sakon, Wata rana da yamma tadawo daga islamiyya Virus na zaune a kofar gida ganinta yasa yatare karamin kofar shiga cikin gidan, tsayawa tayi dataga bayida niyyar matsa mata kallan shi tayi, 'zan wuce, 'kallon ta yakeyi sama da kasa tareda lashe baki kamar tsohon maye, 'ki wuce mana, tareda Dan bude mata hanya kadan, rabawa tayi ta gefen shi cikin natsuwa ta manne da bango gudun kada jikinsu yataba juna Virus kuwa dayake bahaka yaso ba yaso yadan ji dumin ta koda Dan gogarshi ne tayi hakan yasa kafun takarasa wucewa taji PA's ya bugan mata gefen duwawu har yana Danna hannun shi, wooooooooo kafun yarufe baki aiko Yaji saukan Mari a gefen fuskarshi, karamai wani tayi tana huci Ranta yayi mugun baci ta kudiri aniyar duk abunda zai faru saidai yafaru tagaji da rainin wayaun su, hannun ta aka kama daga baya, 'zoki wuce, inji Ramata wacce tafito duba sanwar data Dora a zaure, babu musu tabi bayanta sukabar Virus na hucin ganin babu namijin daya isa yayi mishi haka amma yau saboda ya latsa duwawun mace yasamu mari biyu abun takaici kuma a gaban yaransa dake zaune a gefe, aikuwa masu dariya damai kirari nayi masu bashi hakuri nayi nan yakara kulewa tareda Alkawarin daukar fansa.

Kuka takeyi da takaicin rayuwar data tsinci kanta a ciki bakowa yakara jamusu abun gori ba I'lla baban su daya kasance mutumin kwarai babu Wanda zai watsa musu shara, nan tayi mai isarta yayinda Ramata batabi ta kanta ba itama dazata samu mai lallashin nata so takeyi, Aisha kukan fili takeyi itako tadade tanayin na zuci, batada yancin shiga cikin mata sa'an ninta iyaye koda kuwa sha'ani ne na cikin unguwan inko taje an dinga ya'da mata habaici kenan saikace itace keyin cha-cha ko shaye shayen🤷🏻‍♀ gidansu AK ne kawai basu chanza mata ba.



Bayan an kwana biyu, zaune suke a'dan tsukukun dakin su cikeda jimamin rashin dawowar ya'u gida kusan kwana biyu kenan babu shi babu labari, shiba wayaba bare a kira duk inda akesa ran ganinshi bayanan hakan yasa suka dangana tareda zubama sarautan Allah ido, garbati ne ke zaune gefen mamar tasu da Aisha yana cin tuwon masara miyar kuka Auta kuwa tana gefe daya tazuba uban tagumi sai tausar su yakeyi akan baban nasu zai bayyana gobe da sassafe zai Kara dubashi ko za'a Dace, dakyar ya lallaba sukaci tuwon suma tareda musu sallama zuwa makwancin shi a lokacin yabar dakin su ganin rashin dacewar hakan shiyasa yakoma dakin abokinshi dake unguwan yana kwana, sallama yayi musu yayinda yawuce a lokacin sunada matsalar wuta gashi lokacin zafi ne babu halin kulle kofa dukda sunsan akwai hatsari barin kofar a bude tohya zasuyi? Gashi kofar gidan nasu dan kwano ne akeja ake kullewa.

Wurin sha'dayan Dare dukansu sukayi bcci ga azabar sauro da zafi hakan yasa Ramata ke daure da zani a kirji Auta ma haka, Aisha kuwa vest ce sai underwear a cewarsu zafi bazai kashe suba.

Kafarta yake shafawa a hankali, nan yafara kokarin tube mata Riga,cikin bcci taji ana shirin cire mata kaya gashi ana shafa mata jikin ta, aikuwa kwanciya yayi sosai a jikinta jin nauyin shi yasata sakin ihun da Ramata ta farka, nanta dinga zuba ihu daduk karfin ta aikuwa kafun kace kwabo muryarta ta karade ko'ina, magana yafara cikin maye, meeeeyeee......ha.ka, Raaaa.. a'a
Mikewa tayi ganin ana shirin keta ma diyarta haddi akan idonta Kwanan samiran dake gefenta ta kwada masa akai, sannan ta tuna da tuchlight dinda ke gefen katifar su, ihu Ramata keyi akan akawo musu dauki kwarto ya shigo aikuwa tana kunna tuchlight din idonta ya sauka akan Ya'u dake shirin cirema Aisha underware harya fara yaga mata vest din jikinta, bin bango tayi tana salati tareda dafe kirji tuchlight din hannun ta yafadi kasa hakan yayi daidai da karasowar virus da ihunsu ya tashi kowa na gida, ihu yasaka jama'a uba kecin diyarsa shiyasa aka hanamu dandane ashe cikin zafin nama ta tattaro duka karfin jikin ta tahau buga mai duk wani Abu dake kusa da ita, virus kuwa ihu kawai yakeyi yana shela a unguwa ya gansu turmi da tabarya, diyata? Duk karuwan gari sai diyata? Wlh kashe ka zanyi Ya'u Allah ya la'ance ka Allah ya hanaka farinciki Aisha sumewa tayi ganin ubanta neya yaga mata suturar jikinta yayinda Auta bilki tayi mutuwar tsaye numfashi na sama da kasa.........




*Mrs Sadik Rumah💅🏻*

[14/11, 00:14] ‪+234 814 511 8251‬: 🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*


*Written by Anty Mamie*



*Dedicated to sister Husnah.*


12



Kafun kace kwabo mutane sun yanyame zauran gidan, nan aka damki ya'u dukanshi sukeyi Kota ina matasan unguwan, suna cewa duk iskancin su bazasu taba naiman jinin suba karshan iskanci yakare uba ya nema yarsa ya'u tuni yadan dawo hankalin Sa saboda bugun daya kesha jini ta hanci ta baki babu kyan gani kanshi a fashe duk jikin shi ciwo, 'wlh na dauka Ramata ce, Allah na tuba shegiya, shegiyyaaa giya giya Allah ya tsine miki yar iska ta kassarani Allah ka dauki raina Dan girman Allah ku kashe ni banda Amfani nadauka Mamarta ce taya zan naima abunda na Haifa? Bantaba zina ba ya za'ai infara akan diyar cikina? Allah ka shiga tsakanina da giya kaimana hisabi Kin gama dani kinji dadi giyaaaaaaaa, Babu Wanda ya saurare shi, Ramata kuwa kirjinta ta dafe nanta sulale kasa sharaf, matan makota ne suka suturta ma Aisha jiki dukda ba'a tsirara take ba nan aka Kara rikicewa a tunanin su mutuwa Aishar tayi danko motsi batayi, ruwa aka shiga watsa musu yayinda Ramata taja Ajiyar zuciya mai karfi Aisha kuwa ko Alamar motsi batayi ba, Auta bilki kuwa tana manne da bango kamar mutum mutumi itama ruwan sanyin aka shiga yayyafa mata domin batada banbanci da wacce ta suma, ana haka ne Garbati ya karaso a rikice dagashi sai gajeran wando saboda rudewa, dakyar aka iya bambare ya'u daga hannun matasa, nan Abokanan garbati suka shiga lallaba su, kememe sukace sai sun kashe shi mutumin da akace an ganshi turmi da tabarya shida diyar cikin Sa ina maganar sassauci? Karku raina mana hankali mana malam, cikin dabara Abokanan garbati sukaja hankalin su da sunan bada hakuri yayinda Garbati yaja ya'u batareda sun Ankara ba saboda garin yayi duf kowa da tuchlight yake rike, ya'u kuwa babu abunda yakeyi sai tsine ma giya da cha-cha tareda yima kanshi Allah wadaran sai a lokacin yasan illar shaye shaye wato duk abunda musulunci zai Hana toh bakaramin Rahama bane a garemu muddun zaka kusance shi kuwa sai Allah ya nunama kyakyawan jarabawa akan haka, Allah ya tsine miki giya, kabarsu su kashe ni, 'suna barin wurin Virus ya karaso da abokansa yan Sara suka harda fetur da taya wai zasu kona ya'u bakaramin takaicin rashin samun Sa sukayi ba, yayinda wasu sukace a fito musu da Aisha, nan virus yace su kyale ta batada laifi, Laifin baban ne dayake mata mugunta hartaki yin Aure Ashe shike kwasar romon tunda budurwa ce su barta kawai, a zuciyar shi kuwa wani kudiri ne na daban akan hakan dayayi tunda yaga Aisha da underwear yasa ma Ranshi koda gawarta cefa saiya dandana.


Watsewa akayi babu Wanda yabi takan Ramata da yaranta kowa ya koma gida ana ruruta abunda ya faru dama Wanda bai faru ba kowada kalar labarin Sa akan lamarin, dakyar bilki ta tattaro jarumtar ta yayinda ta dibo ruwa a Roba da tsumma taita shafama Ramata da Aisha a jiki saboda rashin mafitan abun yi shiyasa tace bari ta gwada kila a Dace, Saida gari yafara wayewa Ramata ta farfado nan akai jugum jugum Aisha kuwa babu ko Alama, saida tayi yini daya Sannan aka samu kanta, babu mai iya magana cikin su kamar kurame yayinda zaman gida yagama Auran dukansu babu mai iya leka waje, unguwa kuwa anyi gulma harta takashi🤭 a'haka Rayuwa ta kasance musu babu labarin ya'u babu kuma Wanda yadamu yasani cikinsu bare ya tambaya ko maganar basu Kara tadowa ba, hidimar gidan garbati ne ya dauka gaba daya harta gidansu AK Ramata ta daina zuwa inda Mamie ta tako takanas tazo musu jaje rareda Alkairi mai yawa inda Alhaji muktar ma yabada kudi masu yawa akan abasu.


Aisha kuwa saida aka dade sannan tafara fita hijab dogo har kasa take sawa kamar da nan za'ai ta mata habaici da gori a unguwan, nan aka Sa mata suna *Ustaziya ko Yar'duniya* yayinda ta dauki kaddarar tada hannu biyu bata taba tankawa ba makaranta daina zuwa tayi Boko da islamiyya akan dole inda ko Kare baya naiman ta samari kuwa ko'yan iskan ma sun daina zuwa a cewarsu ita kakarsu ce a bariki dakyar da sidin goshi mai unguwa yabarsu sukara Zama tareda kashedi mai girma idan makamancin hakan yakara faruwa za'a hukunta su tareda koransu gaba daya, sanarwa yabada duk Wanda yaga ya'u a unguwar azo a gaya mai baice kowa ya dauki hukunci a hannu ba.









Mr's Sadik rumah💅🏻
[14/11, 00:15] ‪+234 814 511 8251‬: 🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*


*Written by Anty Mamie*


*Dedicated to sister Husnah*


13





Bayan shekara Uku da faruwan hakan ne cikin Ikon Allah da Al'ajabi tayi wani Saurayi daga sama wai yazo kuma ba wasa ya kawo shiba Aure yazoyi bayasan bata lokaci, sunan shi Musa yanada mata daya da yara Uku baida Wata Sana'a I'lla iyaka shago dayake dashi yana saida kayan masarufi harga Allah baimata ba amma hausawa sunce da babu gara ba dadi hakan yasa batareda dogon nazari ba ta amince a lokacin tanada shekara ashirin a duniya nan Ramata taita farinciki baki yaki rufuwa kashi sittin na damuwarta ya yaye domin tagama sama Ranta Aisha bazata taba samun mijin Aure ba kila Aure kuma sai a lahira idan anayi saboda bakin fentin da Ya'u ya goga musu ita kanta Aisha bata taba tunanin samun mijin Aure ba koma zata samu batasa ran anan kusa zata samu ba harga Allah tacire Auran AK a Ranta tasan kozata mutu tadawo ita dashi har abada saidai babu na biyun shi zatai Aure bana soyya ba.


Mamie ce ke kaiwa da kawowa bakinta yaki rufuwa yayinda da kanta take shigo da farantan abincin da suka gaji da haduwa domin tarban dan'lelen ta, farin saurayi sosai kakkarfa mai kwantaccan bakin gashi dake daukar ido yayinda gefen bakin shi bakin gashin ke zagaye da karamin bakin nashi Wanda Ake kirada *Quarter mullion* hancin shi siriri masha Allah idon shi basu cika girma ba yan daidai sannan basuyi fari kar ba duk inda ake naiman Handsome indai kaga Saurayin nan tohfa an Dace, fara'a ne kwance a fuskar shi Rabon shida Nigeria harya manta he feel Alive gashi cikin gidansu yayinda ya matsu yaci abinci akwai tarin tambayoyin da yake shirin yima mamin nasa, zaune suke gaba daya harda Dadyn su anata cin abinci tareda basu labarin nasarorin daya samu a tafiyar dayayi yasha Addu'a babu adadi wurin iyayan nashi cike daso da kauna nan Dadyn su yai mishi Albishir din fara Aiki a ma'aikatar su NGO tareda mukami mai girma saboda darajar kwalinshi saidai muce masha Allah, gakuma kasuwancin shida yakeyi Abubuwa sunmai yawa yana naiman mataimaki tunda tsufa yafara kamashi ba kamar daba, duk AK ne zai amshe su a'haka firar nasu na ranar ya Kare batareda yasamu damar yima Mamie tambayar da yakeso ba.

Washe gari Allah Allah yakeyi a hadu cin abinci cike yakeda da zumudin dahar mamakin kanshi yake, wanka yayi cikin kananan kaya misalin karfe Tara ya sauko breakfast lokacin Daddy ya Dade da tafiya office, tsakurar abincin yayi sama sama yayinda yake Jan Mamie da fira har akazo inda yakeso, 'wai Mamie ina mai muku wanke wanke ne Ramata Kota daina zuwa dawuri ne

Please Login or Register in order to submit comment