Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gabana ba idan kuma zaki tsaya kallan dramar soyya toh Nina tafi saimun hadu a gida, fita Daddy yayi Ramata tabi bayanshi da garbati cikeda kunya Aisha tayi tayi AK ya saketa rantsewa yayi akan bazai saketa ba sai Mamie tabata hakuri harda rikema Mamie gefen zani inda Aisha keta kukan abun kunyar da AK kemata gaban surukai saikace yara. Mamie kuwa murmushi takeyi ganin sababbin Romeo and Juliet a gabanta.







Mrs Sadik Rumah πŸ’…πŸ»


πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*



*Written by Anty Mamie.*



*Dedicated to Sister husnah*



35



Mikewa takesan yi Amma ya'hanata wai saitace ta yafe mishi inda Mamie cikeda dariya take tayashi ba Aisha hakuri dukda batasan abunda ke tsakanin suba amma ya zatayi? Ya hanata koda motsi ne cewa tayi ta hakura ganin idon Mamie gakuma kunyar yanda ya kankameta koba komai Mamie bata chanchanci musu a wurinta ba hakan yasa Mamie mikewa tareda janye mayafinta yayinda taimusu fada sama sama wucewa tayi sanin daddy na jiranta a waje inda Aisha tafito Rakata nan Mamie ta dinga janta a jiki tareda nuna mata akan takula da Mijinta wannan wata sabuwar damace Allah yabata idan laifi yaimata duk mace mai aji basaita gayama mijinta yamata laifiba zai gane Laifin Sa cikin hikima da dabara ake komai a'haka sukayi sallama inda tabi daddy Wanda yaketa mamakin karfin Hali da rashin kunyar AK saikace ba shine yagama ihun bayasan Aisha oooh yaran yanzu basuda kunya yaro anama gata kakasa ganewa kadan ma kagani, inji dady yafadi yana murmushi. AK kuwa sabuwar sha'gwaba yake xubama Aisha kamar yaron goye ita abunma kunya yake bata gaba daya bata sakan masa fuska inda yakicin Abinci wai itace zata bashi a baki sai shege mata yakeyi ita kuwa cikin rashin sabo sai janyewa takeyi bataso tabashi fuska harga Allah tana matukar kaunar mijinta amma bata shirya Amsar'sa a yanzu ba saiya gane kuransa tukunna nan gaba yasan darajarda takeda shi.



Commissioner of police ne zaune gaban sanata inda Yaketa bashi hakuri tareda Alkawarin daukan mataki cikin gaggawa nan sanata ya Saki bakin Aljihu saboda komai yatafi daidai zai iya yafe komai banda cima iyalinsa fuska, mahuta kuwa azaba yakesha kanshi kamar ya fashe likita ya duba lafiyarsa tareda Dora shi akan magunguna bayi yashiga yadade yana gasa jikinsa bakaramin bugu yaci a hannun AK ba nan yashafa maganin zafi duka jikin nasa inda yaci abincin da mommy ta tasashi a gaba shayi kawai yasha saboda bakin nashi dake mishi azaba magani yasha nan yaita bccin wahala.


Kai tsaye su meenah gidansu leemah sukaje inda Mama ta tarbesu hannu biyu biyu Cikeda mamakin ganin yanayin su babu Alamar mutunci kaya a yage kamar an kwato su daga bakin kura yayinda yayyan leemah maza wadanda ke Kano sunanan da iyalansu tun biki basu koma ba gida yacika gwanin ban Sha'awa Malam liman nanan shima cikin daki take shirin jansu su kimtsa jikinsu amma suka nuna bashine ya kawosu ba,nan kowa yafara tambayan lafiya kallo daya zakai musu kasan basa cikin natsuwa, izinin Zama Malam liman yabasu ba musu suka zauna aka basu ruwan sanyi sukasha saida Malam ya tursasa musu cin abinci nan sukaci kadan badan sunso hakan ba dukda suna tareda uban yinwa amma kwarjini Malam din yake musu basa iya Musa mishi, bayanin Abunda ya kawosu suka farayi tiryan tiryan inda kafun meenah tarufe bakinta taji saukan murfin kwanon'sha Wanda mama ta buga mata tana huci, ooooh bakin ciki kukema diyata ganin tayi Aure a gidan Arziki cikeda kwanciyr hankali shine saboda fitsara kuka wanke kafafunku ba kunya kukema diyata Dana dage wurin bata tarbiyya kazafi wlh mai rabani daku sai Allah, sirikanta mata ke riketa inda duk abunda ta rarumo take jifansu Meenah dashi Malam liman kuwa tunda suka fara magana baice komai ba har zuwa yanzo inda ya tsawatarma mama dakyar ta natsu tana kuka tareda Allah ya isan sharrin da akaima diyarta, kallon su meenah yayi inda yabasu umarnin su cigaba da bayani meenah kuwa duk a tsorace take baki na zuban jini cikeda azaba take shirin barin gidan inda yayyin leemah suka dakatar da ita, feenah ce takarasa bayanin tana kuka ganin tashin hankali da suka jefa kansu daga wayewar garin yau, ana hakane Motocin yan'sanda suka dinga Dira a kofar gidan saikace sansanin yaki inda batareda bata lokaci ba akayi musu sallama damai gidan wasu rikeda bindigogi cikin sanyin jiki Malam liman da yayyin leemah suka fita waje inda kai tsaye aka tasa keyar su a cewarsu saisun fitoda yar'su da sirikinsu dasuka boye sakamakon sunje gidan AK mai'gadi ya shaida musu bakowa a gidan shiyasa sukazo nan a tunanin su Malam dinne yaboye AK da leemah, Salati Malam yadinga nanatawa tareda kiran sunan Allah yayinda jiri ke dibarsa nan unguwa ta cika makil inda matasa da dattawan unguwan sukace indai suna raye bazasu bari aci mutuncin Malam ba hayayyakoma yan'sandan sukayi ganin ba sarki sai Allah haka yasa suka hakura Malam yashiga daya daga cikin motar matasan unguwan da suka shirya binsu domin ganin yanda zata kasance cikeda tashin hankali mama take inda kukan da takeyi tuni ya tsaya tama rasa abunda zatayi taji dadi a Ranta.



Rikici akayi sosai a station sunan Allah kawai Malam ke kira jin Laifin da ake zargin AK dashi wato na cirema yaron sanata Wanda Saurayin leemah ne a sakamakon yaje duba Ajiyar cikinsa dake jikinta, dariya ma maganar tabama jama'ar wurin Abu saikace wasan yara taya mace da Auranta kuma ace tanada cikin wani? inda kassncewar babu kwakwaran shaida akan abunda ake zargin suda shi hakan yasa sanata yace a sakesu kai tsaye kotu za'akai karar saiyaji dalilin da zaisa a cirema danshi hakori, isarsu gida yayi daidai da kiran wayar Mama da aketayi inda dakyar ta iya amsawa Asibitin da leemah takene suka tasata gaba akan saita bada number wani nata an kira babu yanda batayi ba sukace indai zata biya kudin Asibitin ba matsala zata iya tafiya ganin batada kosisi kuma batada Wanda zata kira yabata gashi tabar wayarta a gidan AK tun daran 1st 9yt bareta kira samarinta hakan yasa badan taso ba tabada number Mamarta nan aka kira mama aka shaida mata tazo asibi ana nemanta cikin gaggawa tazoda kudin biyan AAsibiti cikin gaggawa itada sirikanta mata biyu suka shirya zuwa Asibitin shigowarsu malam yasa aka rankaya gaba daya inda kai tsaye aka nuna musu dakinda leemah ke ciki nan cikeda tashin hankali da tarin tambayoyi mama ke kallon leemah da halittar ta tagama chanzawa duk Wanda ya Santa ada bazai iya ganeta ba wasu dayawa musawa sukayi akan ba ita bace mama kuwa kallon ta takeyi batako kyafta ido sanadiyyan bayanin da likita yaimusu akan cikinda ke jikin leemah harna Wata Uku.





*Mr's Saddiq RumahπŸ’…πŸ»*


πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*




*Written by Anty Mamie*

*Alhamdullah Allah ya dawo dani kamar yanda naimuku Alkawari, gobe nasoyin posting amma messages dinku da yawan kiranda nake samu dole kujini yau saboda kada a kashe mun batir din waya, lol😜 masoyana Naga sakonin fatan Alkairi da Addu'a godiya nakeyi Allah ya barmu tare.*




*Dedicated to sister Husnah*



37





Kuka leemah keyi ganin yanda mamanta ke kallon ta babu ko kyafta ido, tun tana shirin jin saukan duka har'abun yafara bata tsoro, saida mama ta dauki minti biyar tana kallon ta inda akaita 'kallon kallo a dakin sautin kukan leemah kawai ke tashi sannan ta bude bakinta dayake mata nauyi, 'menene Laifin mu a matsayin muna iyayanki? Ilimi koko gatan da muka baki? Ciki kikayi kodai mafarki nakeyi? Diyata? Ni? Jinita dayin cikin Shege......Dan Allah mama kiyi hakuri kaddara ce,.....kaddara? Wace irin kaddara ce wannan data sauko tsakiyar gidan malamai? Durkushewa tayi kasa tareda ware duka muryarta tana kuka tana bugun kirjinta tareda Rokan Allah ya dauki Ranta akan ganin bakin ranan nan diyar cikinta hafiza wacce suka ginata akan ilimi da tarbiyya ita keda cikin Wata Uku ko sati daya batayi ba dayin Aure, kuka mama keyi inda Malam liman ke manne jikin bango sai kallon matar tasa yakeyi da diyarsa kamar TV babban dansa ne da jama'ar da sukazo tare ke shirin tabashi da niyyan lallashi yayinda ya dakatar dasu da hannun da Alamar su barshi kawai duk Wanda ke wurin saiya tausayama Malam da hawaye daya kebin daya a fuskarsa karona farko a tarihin rayuwar malamin da suka ganshi a yanayin nan wurin Mama yakarasa tareda tsugunnawa ya Tallabota jikinsa yayinda suka Mike domin shirin barin dakin suna gafda fita akaga idon mama ya kafe sama kumfa na fita ta bakinta jikinta na rawa kamar an jona mata wutan lantarki wani ihu leemah tasaka yayinda ta nufi wurin Maman tana kuka tana girgiza ta tuni likitoci suka dauketa da gaggawa inda babban wansu ya rufe leemah da duka tako'ina yana kuka harda majina yana mata Allah ya isa, kallon su Malam liman keyi yana durkushe kafun a Ankara shima ya zube bakinshi dauke da salati nan asibiti aka rikice da surutai yaran Malam liman ne duka Ukun suka taruma leemah da duka ta ko'ina Alkawari sukai saisun kashe ta tunda tayi sanadiyyan kashe musu iyaye bazasu barta ba, dakyar aka kwata leemah a hannun su wacce ko motsi batayi jini sai ambaliya yakeyi ta kasanta Asibiti ya cika makil kowa na ganin abun Al'ajabi kassncewar Malam liman sananne hakan yasa harda yan'jaridu da TV stations anata kokawan daukan labarai, cikin hanzari aka karayin gaba da leemah inda saida tarasa hakora Uku biyu a saman baki daya a kasa ta gefe duk yanda akaso ankasa daidaita numfashnta inda ake shirin sakata a coma.


AK kuwa gaba daya chanzawa yayi yayinda abun yafara ba Aisha tsoro ganin dama AK ya iya magana haka, kwana daya yayi a Asibitin dakyar Wanda daran jiya yadamu Aisha da roko da magiya akan tayafe mishi ganin duk abunda yake mata bai hanata jinyar shiba dukda babu yanda baiyi da ita akan ta kwanta akan gado ba amma kememe taki inda ta raya daran nata wurin Rokan Allah akan ya daidaita rayuwarta ko'itama zata samu jin dadi tun AK na kallonta Yayinda take burge shi har bcci yayi awon gaba dashi, washe gari Dagewa yayi akan bazaici abinci ba wai hannun shina ciwo a cewarsa mahuta ya bugan masa hannu sosai yanama tunanin har'yayi targade hannun yayi tsami inda Aisha baki bude take mamakin yanda Yaya AK ya kware a karya idan bata mance ba baima ba mahuta damar dukansa ba amma ji yanda yake gilma karya babu ko kunya, kiri kiri yakicin Abinci dukda yanajin yinwa a cewarsa indai Eesha bata bashi a baki ba tohfa saidai ya mutu da yinwa ko jiyama haka yayi inda madara kawai yasha Aisha kuwa ta murzama idonta toka dukda Tausayin shida takeji bataso yasamu weakness dinta, ana cikin haka ne kaninshi Abdulhakeem ya shigo inda AK yahade rai tareda kunkuni, "wai nayau ma kawai baza'a bar mutum ya sake da iyalinsa ba? Mtseww, Zama Hakeem yayi tareda murmushi, Daddy ne yace inzo in kwana dakai a Asibiti Anty ta koma gida itama ta huta.......ka kwana dawa? Badai niba? Wace Antyn? Badai my Eesha ba? Yafadi fuska a hade kamar zai mangare Hakeem, Allah ya kyauta in kwana da katon kato a daki daya bayan inada matata wacce zata kula dani, my Eesha ko bakyaso ki samu ladan jinyar mijinki ne? Ya fadi murmushi akan fuskarsa, mikewa Aisha tayi yayinda tajawo hijab dinta tareda shirin tafiya dukda tanaso ta kasance da Mijinta, kallon Hakeem tayi, 'yauwa ka bashi Abinci a baki yace bazai iya Amfani da hannunsa ba Nina tafi saida safe, 'wait Wait Hakeem ya furta cikeda dariya yana tafa hannu tareda nuna AK da yatsa, Badai Bros kike nufi zanba abinci a baki ba tsofai tsofai dashi? Nooooo it can't be possible kuna wasa ne wlh bazanba wani kato abinci a baki ba look ki ciyarda mijinki, 'nine katon? AK ya Tambaya sounding so serious fuska a harde, " am sorry bro but u and ur wife are very funny, 'Nina tafi Aisha ta furta tana shirin bude kofa inda AK yayi wani mugun tsalle daya tareda damko ta saikace bashi ke jinya ba, rungume ta yayi sosai da hannuwa duka biyu ta baya har'saida tasaki yar'kara sai kokarin kwace jikinta takeyi ina yaki barinta ihu tafarayi kasa kasa tana bubbuga kafarta cikin shagwaba, Kallon Hakeem yayi Wanda yasaki baki da hanci yana kallo da mamakin salon yayan nashi, toh magulmata sai abamu wuri koh jeka waje ka nemo mun lemun bawo mai zaki, 'Allah ya Baku hakuri ni ina zan iya kallon abun kunyar nan? Dama fita zanyi ko'bakace ba yafadi yayinda ya Mike, but Bros wannan uban lemun fa? Yafadi tareda nuna tarin lemun zakin dake jibge a gefe daya, 'look Malam basu nakeso ba kana bata mana lokaci, ko kunya baiji ba ya juyo da Aisha tana fuskantar Sa fuska sharkaf hawaye inda yake kokarin zame mata hijab ita kuma ta kunkume taki bari, Kofa Hakeem ya kulle tareda mamakin dama haka yayanshi yake baida kunya?
"Kuka Aisha keyi maidan sauti tunowa da irin wulakancin da azabar da AK yake gana mata a ganinta rainin hankali ne kwana daya rak yadawo wai yana Santa yana Santa kodai yana Sha'awar ta? Kuka takeyi sosai.....'nooo my Eeasha please please not again banaso in Zama sanadiyyar zubowar hawayanki insha Allah daga yau har'abada please my wife karki horani ki tausaya mun.......'daka rasa swt 18 dinka koh? Daka rasa matar so? Ni banza yar'tasha Mara tarbiyya kazar kowa yar'duniya wacce batada gata wacce tagama rabarda duk wani mutincinta a titi wacce batada Amfani a gidanka face taci takuma cika maka Masai da kashi mai wari a gida....." Nooo Eeasha please please karkice haka ki fahimce AK dinki nasan naso kaina dayawa na cutar dake Wanda bazaki iya yafemunba wlh kiyimun duk hukuncin daya Dace I deserve please wife but ki kasance tareda ni karki gujeni wlh dakin San wanene ni da kinsan halinda nashiga a kanki da kinsan mahaukacin Soyyar da nake miki saikin tausaya mun.....'oh yes, tafadi tana shirin kwace jikinta daga nashi amma yaki sakinta, Soyyar da babu komai sai azaba da bauta? Soyyar tozarci da duka? Soyyar bauta? Mara yan'ci? Ko zamanin jahiliyyah bantaba jin labarin irin soyyar nanba, 'girgiza mata kai AK keyi kamar zaiyi kuka kwalla tafara cika masa ido cikeda nadama tareda tsanar kanshi akan abunda ya aikata, Aisha kuwa kuka takeyi tuno da azabar daya gana mata eye? Gayamun gayamun haka ake soyya a duniyar ka? Inko haka soyyar ka take tun wuri kaje ka nema wacce zakayi irinshi da ita badaini ba not again nagama wlh nagama kokuma idan matar so tadawo....rufe bakinta yayi danashi jin zuciyarshi tana shirin fashewa tumomai da abunda leemah tayi Wanda bazai iya sauraran taba tun ana na hankali tana kokarin kwacewa dakai masa bugu ina dorata yayi akan gadon Asibitin inda yayi Mata rumfa da jikinsa sunkai minti goma a haka har'karfin Aisha yakare inda ya sake bakinta yafara lashe hawayan dayayi Alkawarin bazasu Kara zuba a sanadiyyar saba saidai tayi hawayan dadi insha Allah, runtse ido Aisha tayi jikinta na rawa tana wasiwasi Anya ba mafarki nakeyi ba? Yaya AK kecewa yana Santa? Ashe dama zataga ranan nan a zahiri ba'a mafarki ba? 'Likita dake tsaye a kansu Wanda baiyi minti daya da shigowa ba shine yayi gyaran murya tareda kauda kansa gefe yana murmushi duba jikin AK yazoyi inda yake shirin aiko masa dawasu maganin, 'Ranka shi Dade da Alamar sallama kawai kake bukata Dan naga jiki yayi kyau Alhmdlh da Allah bai kawoni ba kila da'a dakin nan za'a sama mana tsarabar dan'baba, Hakeem neya shigo jin maganar da doctor keyi aikuwa ya tuntsure da dariya inda AK ke zaune a gefe sai kame kame yakeyi tareda gyarama Aisha dankwalinta daya cire mata, fusge dan'kwalin tayi ta cusa kanta ciki cikeda kunya shikuwa sai hade rai yakeyi a dole bayasan Raini, "bari in rubuta muku takardar sallama mu ai haka mukeso Lallai uwargida Maganinki yafi asibiti tasiri wannan aiki haka hmmm, likita yafadi cikin barkwanci tareda barin dakin aikuwa mikewa AK yayi yafara hada kaya, 'Bros ya haka? Ina kuma zaka? Inji Hakeem dayake faman dariya, 'ban saniba koba a gabanka aka sallame niba look bansan munafunci uban maiya dawo dakai bayan na sallame ka? zo kayi gida Malam, yafadi har yana hankade Hakeem waje harda Danna sakata a dakin inda Hakeem keta sheka dariya, wooooo soyyah masu gari dole inba su Mamie da Daddy labarin nan hahahaa love on point Gskia nima dady ne zai nemo mun matarda zan Aura naga alaman baya zabin banza, 'Allah ya isa indai akayi gulmata Dana matata, Ak yafadi da karfi sounding so serious Aisha kuwa Yanzu abun yadaina bata mamaki sai tsoro.








*Mrs Saddiq RumahπŸ’…*


πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*




*Written by Anty Mamie*


*Afuwan jiya nayi mistake a wurin page number, 36 zansa nasa 37 yanzu zan cigaba da 38 kawai gudun rikicewa.*



38




Dole hakeem sukabi yakaisu gida yayinda ko takardar sallama bai jira ankawo ba suna isa gida mai'gadi ya bude gate tareda gaishe shida jiki yanaso ya gaya musu zuwan yan'sanda neman AK amma ganin rashin dacewar hakan Ga Wanda yadawo daga Asibiti yasashi tsuke bakin shi inda Aisha ta kira bilki batareda bata lokaci ba tazo yayinda suka Kara kimtsa gidan tas ko'ina sai kamshi yakeyi Mamie ceta kira Aisha tareda shaida mata kada tayi girki za'a kawo musu daga gida tahuta na kwana biyu hakan yasa suka koma daki itada bilki inda take bata labarin sabon salon AK dariya bilki ta dinga yi inda ko kadan bataji tausayin Shiba saima cewa datayi kadan yagani, "idan ankawo abincin ki daure kibashi a baki kada ki sakar masa fuska, a haka suka tsaida maganar, aikuwa ana kawo abincin AK ya shigo dakin da sallama "hmmm maza kenan ji yanda yayi ladabi cikin kwana biyu" yayinda yayi wanka ya chanza cikin farin jallabiya kallan bilki yayi yana murmushi, " kanwar mu sannu da zuwa yasu mama? 'Lafiya kalau suke sunce a gaida ka, tafadi dukda ada ta tsani AK amma koba komai zaici darajar Auran yayarta da yakeyi kuma tsakanin miji da mata sai Allah, my Eeasha am hungry please Dan Allah Kibani Abinci Eesha yafadi a dole so yakeyi Aisha taji tausayin shi, 'Bata Musa masa ba suka fito gaba daya harda bilki inda jalof rice ce tasha hadi sai kamshi takeyi ga hadaddan Pepe chicken awani kula hakan yasa Aisha ta zuba abincin yayinda ya zauna akan dining bilki na tsakiyar parlor tana kallo kusada kujerar shi Aisha ta zauna yayinda ganin baida niyyar ci yasa ta juyo da kujerarta sosai tana fuskantar sa tafara ciyar dashi batareda tabari sun hada ido ba inda yakecin abincin cikin natsuwa so yakeyi ta dinga sakewa dashi amma taya? Taya zai fara? Maiya kamata yayi domin gyara kuskuran daya tafka? Yah rabbi ka kawomun mafita a gidana, ya furta a zuciyar Sa inda saida yaci ya koshi sannan ta diba nata awani plate din tareda dauka tabar wurin parlor takoma inda bilki take nan suka zauna sunaci suna fira harga Allah baiso ta tashi ba dukda baida abunda zaice mata amma yanaso taita Zama kodan ya dinga kallon ta, waito taya ake lallashin mace ne? Ooh gskia lamarin mata sai a hankali dukda kukan dayayi mata a gabansu daddy Yanzu maiya rage? Oooh GOD wazai gayamai abunda zaima matarsa ta huce? Ba ance mata nasan goyo ba toh kodai tsugunawa zaiyi yace tahau bayansa yaita zagayawa da ita? Nooo nooo Goya wannan katuwar saita karyani ai, murmushi yayi tunowa dayayi da jikin Aishar, ita kuwa Aisha Rashin sabo yasata barin wurin ganin yanda ya kafeta da ido bazata iyacin abinci a gabanshi ba hakan yasa ta tashi.



A' Asibiti kuwa Ansamu Malam liman da mama sun farfado amma an rikesu a cewar likitoci sai sunyi kwana biyu saboda tabbatar da lafiyar su Wanda Malam din bai damu ba ko kadan baisan dawani ido zai kalla jama'a ba, taya zaifara? Taya? Tabbas yasan hakan na cikin jarabawar shi dukda ganganci da sakaci irin nashi dasai yanzu yake ganin gudunmawar da suka bada wurin bata tarbiyyan diyarsu nan yaita kuka yana neman gafarar ubangiji Wanda ya jarabceshi ya nuna masa duk tarin ilimin shi ba shine zai Hana Allah jarabtar bawansa ta inda bai zato ba, nan ya kudiri Aniyar idan komai ya daidaita zai karbi halima da hannu biyu baya cikin iyayan dake gudun kuskuran su zai Amsa kuskuransa da hannu biyu tareda kulada cikin jikinta har Allah ya sauke ta lfy koda kuwa jama'ar gari zasu koreshi akan yana rainon cikin shege duk zaginda za'ai mishi zai toshe kunnan Sa barna ce anriga an tafka hannun ka baya rubewa ka yanke, inda labari yagama bin gari duk inda ka waiga maganar diyar Malam akeyi karya da Gskia haka mutane keta ruruta lamarin har kasashan ya'da labarai saida akasa domin yazama iznah ga iyaye Wanda wasu da biyu sukeyin hakan domin tozarta malamin masu zagi da takaicin leemah nayi, masu ganin ganganci da Laifin su Malam nayi, harda masu Allah Kara, nidai nace kanku akeji.




Ta fannin mahuta kuwa Lauyoyin Dadyn shine suka bashi shawarar janye karar da yake shirin makawa kotu ganin duk yanda ake daukan lamarin tohfa ya wuce nan, Ranka shi Dade wannan ba maganar kudi akeyi ko matsayi ba duk abunda akace akwai idon mutane a ciki gaba daya Al'ummah sun karkata akan case dinnan kasancewar ta diyar babban Malami a ganina fa barin sha'riar nan itace hanya mafi sauki kada Allura ta tono garma babu abunda mutane ke jira illah iyaka Susan Wanda yaima halima ciki ya kake ganin za'ai idan muka fito da kanmu tareda tona kanmu har a'kasan Dan gidan babban dan'siyasan da yayi suna shine ya banka ma diyar babban Malami ciki ya kake ganin makomar siyasar ka? Goge zufa daddy yayi dukda baiso hakan ba amma Yaji dadin Sha'awar nan Allah yaso shi dayayi tabargaza garin neman gira arasa ido hakanan yanaji yana gani aka rufe case din Inda sukayi luf sukayi shiru suna kallon yanda Abun zai kasance.

Mahuta kuwa tuni aka saka mishi hakorin Roba a wawulan bakin shi inda ya kudiri aniyar nanda wani lokaci zaibar kasar domin haduwa da manya manyan likitoci asan yanda za'ai dashi bazai yiwu babban guy kamarshi ba Dan kudi yakarasa Kuruciya babu hakori a bakinsa ba, yawa ne indai kudi na aiki tohfa komai yazo da sauki tuni yakoma kan network inda ya hada duka kawayan leemah meenah da feenah ya ajiyesu gida na musamman babu ko kunya aka dasa daga inda aka tsaya a cewarsa Gari dayawa maye bazai taba cin kansa Sa Ga mata jaga jaga wasu ma koda kudinka saida rabon ka, sukuwa ko kishin kansu basayi tunda rufin asiri suke nema kuma mahuta ya sake musu kudi wani Kishin namijin bariki zasuyi Wanda baida tabbas?

AK ne zaune a parlor sai safa da marwa yakeyi misalin karfe goma na Dare Wanda tuni Aisha tadade da Danna ma dakinta sakata, sai sake sake yakeyi yarasa abunyi, dakin limah yashiga nan yafara jido akwatinan lefenta daya hada mata kaf saida ya hadasu akwati dozin da manyan jaka guda biyu, dukda ta dinka wasu bai damu ba, akwatin dankunne yabude tareda Addu'ar Allah yasa gold dinda yasa mata a lefe yananan, aikuwa yana dubawa saiga dankunne da sarka da zoben gold nan yaita kinkimar kayan yana jerasu tsakiyar parlon dakyar ya karasa dukya gaji, kai tsaye dakin Aisha ya nufa yaita buga mata kofa sanin bazai taba dainawa ba harsai ta fito yasata bude kofar fuska a hade sanye da Riga da wando masu taushi blue color sunyi kyau sosai sai kamshi takeyi tana yamutsa fuska, "yadai? Bcci nakeyi lafiya ka tasoni cikin daran nan? My Aeesha magana zamuyi ki sameni a parlor, yafadi tareda Kare mata kallo yakoma parlon, kai tsaye ta bishi kanta babu Dan kwali tsayawa tayi trus tana mamakin uban hadaddun sababbin akwatin da suka cika parlon nasu kallonta yayi, " zauna mana sarautar mata,

Please Login or Register in order to submit comment