Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"kallon mutumin yakeyi ji yakeyi kamar ya watsa masa mari kozai huce takaici, shi kanshi likitan ganin irin kallon da Ak yake masa shiya sa yawuce da sauri kada ya
huce a kanshi.
Aisha kuwa bakaramin wahala Tasha ba inda likitan dake dubata tayi masifa da fada sai kumfar baki takeyi bakaramin haushin Ak takeji ba wannan ai rashin hankali ne ko makaho ne bai kamata yasa miki karfi haka ba ko kinmai gardama ne? Ta tambayi Aishar da batada niyyar bata amsa, dakin hutu aka kaita tareda Kara mata ledan ruwa da alluran Bcci.

Kafun gari yawaye harya kirasu Mamie dasu bilki yan'uwa yaita kira Eeashar sana Asibiti priceless Jewel batada lafiya batareda tunanin dalilin dazai gaya musu ba, aikuwa nansu Mamie da brother Hakeem sukazo harda bilki wacce Hakeem yacema Mamie su biya su dauko ta Ramata kuwa cewa tayi basai taxo ba Adduar ta ya wadatar batareda bata lokaci ba Mamie ta tambayi abunda yasamu Aishar Ak kuwa da gaskiar shi yake shirin yima Mamie dalla dalla inda bilki ta farga tayi saurin katse shi,........" Wlh maleria ne yasata gaba jiya danaxo haka na barta jikin sai a hankali Ashe jikin nata yayi tsanani bayan tafiyata, "Adduar samun sauki sukai mata inda bilkin tayi hakan ne saboda surutun da mamakin da zaai shekara uku da Aure sai a lokacin ma'auratan suka San junansu it will look somehow, "Ammah bro duk ciwon sister neya rikitaka kazo asibiti babu ko riga? Sai a lokacin Ak ya kalla jikinshi inda kunya tagama kamashi yiyinda Mamie ta kalleshi tana girgiza kanta, " Allah ya shirya ka Ak dannaga alama kana gafda fara hauka, wucewa dakin da Aisha ke bccin hutu tayi bilki kuwa sanin Abunda yafaru da yayar tata bakaramin tausaya mata tayi ba inda suka koma gefe daya itada hakeem sai fira sukeyi kallo daya zakai musu ka faminci zallar soyyah a idonsu, "hmmmm wata sabuwa da Alama jinin buzaye yagama mallake gidan Alhaji MuktarπŸ‘―πŸΌβ€β™€

Mota Ak yakoma inda yakira PA dinshi tareda shaida masa yataho masa da sabuwar riga yana asibiti yazo kuma zai Aikeshi wani wuri.


Takarda ya zaro da biro a jikin motarshi inda yafara rubutu kamar haka.

*Ni Abdulkareem Muktar na saki Munafuka makira muguwa Shegiya macucuya Kuma Azzaluma Halima Mai fuska biyu, Saki uku nida ita har abada Kuma Allah ya isa tagama dani Bankuma yafe ba.*

Nade takardar yayi inda abubuwa suka dinga dawo masa dai'dai cikin lokaci kadan naga ya yaga takaddar tunowa dayayi da darajar malam liman a wurinsa nagartaccen dattijo Wanda baida kwadayin duniya da abunda ke cikinta idan banda haka saiyayi sha'ria da halima saboda tagama masa rami a rayuwa Amma ya dauki hakan a matsayin jarabawa tareda hakkin Aisha,
Wata takaddar ya dauko inda yakara rubutu kamar haka.

*N Abdulkariem na datse dukkan igiyar Auren dake tsakanina da halima na saketa saki uku a dalilin cin amanar Aurena datayi.*


Mikama PA dinshi yayi tareda bashi izinin kaiwa gidansu leemah inda saida Aisha tayi kusan sati daya a asibiti gatan duniyar nan ta ganshi a wurin Ak makale mata soyyah kuwa hmmm kamar ya kashe kanshi bakaramin soyyah suke sha'ba hakuri kuwa ta sha'shi inda yaita mamakin yanda yasameta a vargin nanta warware masa komai Addua sukaita ma ya'u inda ya kudiri aniyar duk Wanda yakara jin yakira matarshi da makamancin sunan Ustaziya ko Yar'duniya kowaye kuwa saiyayi sha'ria dashi kuma zai fito ya nunama duniya shikadai ne namijin dayasan ta sai inda karfin shi yakare akan hakan, koda aka sallami Aisha Kyautar 1st 9yt dinta na musamman na jiranta inda yasai musu dankareriyar motoci guda biyu hadaddu shida ita na Aisha fara tas a cewarsa saboda rayuwar shida ta haska shiyasa yaimata kyautar farin mota, tashi kuma milk color inda ya biya musu kujerar hajji itada family ta gaba daya su garbati Mai rake za'a zama Alhaji a cewarsa it is the little he can do ganin baida wata hanyar faranta mata zai cigaba da wanke mata bakincikin daya dasa mata da karfin shi dakuma dukiyar shi koda zai zauna baida ko'sisi a duniya zai kararda komai akan Priceless Jewel dinshi tattali na musamman yake bata kamar zai maidata cikin shi.

Halima saida takusan kwasan wata daya sannan aka sallameta tayi baki tarame ta kode saikace Mai ciwon kanja'mau inda tun kafun akai ko'ina tayi nadama matuka iyayanta gaba daya basa bin ta kanta inda mamarta bata amsa koda gaisuwar ta ko kallon inda take batayi malam liman kuwa kullum cikin wa'azi yake mata a cewarsa hannunka bazai rube ba ka yanke dukda abun namasa ciwo Amma bazai bar sanrai yasa yayi aikin jahilci ba, gaba daya aikin gidan ita keyi babu yanda malam bai lallashi mama akan ta dinga sassauta mata ba hakan yasa Maman ta tattara halima da malam din dukansu ta watsar a cewarta da tanada wurin zuwa babu abunda zaisa ta zauna gida daya da halima taga Alamar malam dinne ke daure mata gindi Inda kullum halima na kunshe a daki kamar daddawa duniya tamata zafi danma Allah ya taimake ta cikin baya bata wahala ko kofar gida tayi Alkawarin bata Kara fita koda malam yabata takardar sakinda Ak ya aiko mata ranan tawuni kuka kamar ranta zai fita ganin yanda tacuci kanta da rayuwarta Allah yamata gata babu abunda tarasa San zuciya yasa tama Allah butulci Ina ranar bariki? Duk ribar da mutum zai samu a bariki na lokaci kadan ne yayinda zai karasa sauran Rayuwarsa cikeda nadama wacce batada amfani tanaji tana gani tayi asarar nagartaccen miji har abada, mahuta kuwa bishasha kawai yake zubawa inda neman mantan shiya ninku saikace Wanda akaima baki kowace kareda doki binta yakeyi abun yazama mishi jaraba saidai muce Allah ya kyauta yakuma hanemu da aikin danasani Mara amfani.

Aisha fa tama rasa bakin godiya saidai hawayen farinciki ganin yanda mijinta ke rurutata takara godema Allah daya tsare mata budurcin ta tabbas duk macen datayi asarar budurcinta a titi wlh wlh tayi asarar babban farinciki da kwanciyar hankali a gidan auranta bawata daraja da zatayi matukar Mijin yagane duk sanda yake miki babu inda auranku zekai koma Auran yayi tasiri wlh sai an samu zargi tareda wasi wasi a zaman.

"Misalin karfe goma na dare Ana sati daya daidai da daran 1st 9yt dinsu bayan tagama kimtsawa tadau wanka sai kamshi takeyi kamar koda yaushe wayarta ce tayi Kara *King of hrt* shine sunanda yafito baro baro akan fuskar wayar tata batareda bata lokaci ba ta amsa tana faman zuba mishi kirari tana wasa Mijin nata kamar yanda ta saba, sanar mata yayi ta sameshi dakin shi Wanda anan ne akayi sha'galin😜 batareda bata lokaci ba dama a shirye take tunda yamma ta hada hadaddan hadi na musamman, danyan zogale ta gyara da madarar pick na ruwa ta markada tareda zuba masa Zuma Mai kyau akai shita wuni sha dukda baida dadi a baki Amma biyan bukata yafi dogon buri, Alkawari tayi koda duk kwanan duniya Ak zai dinga karata Ana dinketa Bazata taba guje ma shinfidar shiba, duk halinda take ciki Alkawari tayi bazata taba hanashi kanta ba zata juri komai saboda king of hrt, she is Ever Ready, yes a shirye take da faranta mishi koda hakan na nufin Ajalin ta, tana bude kofar dakin sanye da hadaddun kayan Bcci red cikin takun kasaita yayinda take mamakin abunda ya boye Mijin nata tun dazu bai makale mataba kamar yanda yasaba, batasan sanda tasaki ihun dadi ba tsalle tayi tareda rungume mijin nata tarasa awace duniya zata sakashi ganin yanda.............😜
Saimun hadu a next page Wanda zai zama second to the last insha AllahπŸ‘―πŸΌβ€β™€










*Mr's Saddiq RumahπŸ’…πŸ»*



πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*



*Written by Anty Mamie.*



*Dedicated to Sister Husna*


42



Aka kawata dakin da rose flowers masu ban sha'awa na masoya saman gadon yasha red bedsheet masu matukar kyau an zuba flowers jajaye gwanin ban sha'awa yayinda aka watsa multicolors balam balam Mai hrt shape ta'koina har zuwa kasan dakin Wanda ke dauke da karamin table dauke da madaidaicin Hadaddan red cake da rubutun, *"Happy One week Anvasary"* tareda hotonsu a jiki Wanda ya matsa mata suka dauka sanda take jinya a asibiti dukda babu Kwalliya fuskarta hoton yayi kyau sosai kanta nakan kafadar shi yayinda shikuma yake kallon fuskarta daya tallabo da dayan hannun sa gefe daya kuma Kwalbar Hadaddan champagne ne tareda red glass cups dogaye guda biyu, wani cool music ke tashi a hankali cikin wakan sanannan mawakin nan black American "Akon a wakarshi Mai taken " Am so lonely " cikin sauti Mai natsuwa da ratsa jiki "bin dakin tayi da kallo inda lokaci daya ya sunkuce ta tareda direta tsakiyar gadon dayasha gyara sai dariya sukeyi yana mata chakulkuli saida suka dauki minti biyar sannan ya dakata yayinda ta kalleshi cikeda mamaki, "king of hrt wai yaushe kayi duk wadannan abun? And na menene? Bakinsu ya hada wuri daya yana bata wani irin sako Mai wuyar fassara saida suka dawo hankalin su sannan ya rike hannun ta har zuwa wurin cake din tareda mika mata yar'karamar wuka red, " bismillah nakosa inci cake dinnan dear feed ur hubby please, "but cake din mainene? Na Anvasary din sati daya da first 9yt dinmu ne idan zaki tuna tundaga ranan bamu Kara kwana a dakin nan ba saidai inbiki dakinki saboda jinyar da kikeyi, " tugunnawa yayi a gabanta kamar karamin yaro sanye yakeda wando 3quater fari tareda red armless riga Mai daukeda rubutun, *Give me Another special place in ur hrt* a gaban rigar Wanda rubutun ya kasance fari, "shiyasa a karona biyu nakara gayyatarki dakina Wanda banaso ki dinga tunowa da komai sai ire iren abubuwannan just our happy moments, Mr's Abdulkareem congratulations because am All urs sai yanda kikai dani babu boka ba malam kin gama mallakeni yanzu dai ki ciyarda mijinki, yafadi yana chuno mata baki, Cikin wata sabuwar duniyar farinciki ta Lula yayinda ta yanka cake din Wanda ya kasance chocolate and red velvet cake sai hadiye miyau takeyi tareda gutsoro madaidaici tana shirin dorawa akan karamin Tea plate ta hango wani Jan Abu namata kyalli tacikin cake din, hannu tasa tareda turawa tsakiyar cake din dauko Hadaddan karamin case ne Mai kamada gidan dan'kunne tana budewa tayi ido biyu da kyawawan zobuna guda biyu sai kyalli sukeyi tareda daukar ido na mace Dana miji cikeda mamaki ta maida kallon ta ga AK Wanda ya kashe mata ido daya yana zuba murmushi, Rike hannunta na dama yayi tareda Amsar zoben ya zaro na macen Dan siriri Mara hayaniya saika saka ido sosai a zoben zakaga Harafin A&A Wanda aka rubuta da ruwan gold, yatsar hannunta na biyu ya rike inda ya kalleta with a serious look, " My Eeasha I know I made a mistake a baya banyi Alkawarin bazan Kara bata miki raiba Amma nayi miki Alkawarin hawayan idonki bazai Kara zuba ba a dalilina namiki Alkawarin duk hawayan dazai fito idonki a gidana insha Allah zanyi iyakan kokarina Inga ya kasance na farinciki sannan zanyi iyakan kokarina wurin faranta miki da dukkan Abunda nake dashi, kasancewar bikin mu baayi wani shagalin da zamu dinga tunowa dashi ba kasancewar abubuwan da suka faru ada cikin rashin Sani shiyasa na hada miki yar'karamar dinner nidake a dakinmu Mai tarin tarihi da farinciki inaso ki manta da abunda yafaru a baya ki rike ranar yau a zuciyarki wacce Ranar yaune zai zama Ranar da zamu dinga Celebration akai, My wife, please kikara bani dama a karona biyu insake taka rawa a rayuwar ki, zura mata zoben yayi a tsintsiyar hannun ta Wanda ba karamin kyau yayi mata ba yayinda ya rike hannun tareda sumbatar shi, a daran masoyan sun Kara lulawa sabuwar duniyar ma'aurata Mai tarin natuwa tareda tsayawa a'rai saidai muce Asuba tagari Eeashar AKπŸ’ƒπŸ½.



*Bayan wata Shida.*


Leemah ce keta mutsu mutsu gwanin ban tausayi dukta bushe ta jeme tayi baki tarame ga uban ciki, tun tana daurewa tana nishi da kuka kasa kasa harta galabaita ita kadai a daki da Alama nakuda takeyi bakaramin wahala tasha ba taci kuka harta gode Allah yayinda mama batasan Abunda ke faruwa ba kasancewar bata shiga harkarta gaba daya, Addua takeyi Allah ya dauki ranta kozata huta da azabar da take ciki inda takasa jurewa ta kwallama Maman kira cikin kukan azaba tana rokon yafiyar iyayan nata tareda nadamar abunda ta aikata, cikin hanzari mamar ta karasa dakin saida ta tausayama halinda taga diyar tata bakaramin azaba take sha'ba, wurin malam ta garzaya tareda amso rubutun nakuda Wanda yadade a ajiye, dakyar tasamu halima yasha kadan saboda tanasha tana dawoda rubutun ne ganin anata Abu daya har yanzu babu Alamar haihuwa hakan yasa malam ya dauko shatan keke napep aka sakata a ciki batasan inda kanta yakeba Allah ya taimaka unguwar babu mutane a lokacin babu Wanda ya farga da abunda ke faruwa, cikin ikon Allah Ana gafda isa asibitin halima tasaki wani uban ihu Wanda harta Mai napep din saida ya tsorata batareda bata lokaci ba Ashe yaron ne yayi mugun karata inda jariri ya sumbulo kasa salati mama tasaki ganin kashi jaga jaga a wurin da gudu likitoci suka karasa tareda gadon daukan Mara lafiya duk mai imanin dake wurin saida ya zubar mata da hawaye sakamakon karantan da jaririn yayi harya shafan mata wurin kashi,kai tsaye dakin tiyata akayi hanzarin shiga da ita inda mama keta kukan tausayin diyar tata bata taba ganin Abu irin wannan ba, katotuwar baby gal ta Haifa kyakyawan gaske Mai kamada ubanta sak kamar mahuta yayi kaki saidai bbyn farace tas, anyi ankin cikeda nasara saidai Halima tasamu larurar yoyan fitsari inda sai a hankali A hankali zata warke tareda shawarwari masu kyau daga likitoci hakan yasa suke zaune a asibitin tana jinya inda Malam yace tana samun sauki zataje Kano ta karasa jinyar gidan babban wanta saboda gudun surutun jama'a wadanda basuda gadonka Amma sunada gadon maganarka, Allah sarki halima bakaramin nadama tayi ba kullum batada aiki sai neman yafiyar iyayanta da Ubangiji a cewarta sakamakon zinar datayi ne take girba tun ba'aje ko'ina ba.



Mahuta uban duniya shida yammatan shi su meenah da finah kuwa kowa shagalinsa yakeyi suna holewa inda baa iyakar junansu kawai suka tsaya ba duk Wanda ya taya saisun bashi yammatan biyu kuwa meenah da feenah likafa ta cigaba domin yanzu har lesbianism sukeyi "Subhanallah" hakan yasa lokaci daya kuraje masu matukar wari da uban kaikayi suka Addabe suda wari da kaikayi tun abun nayi kadan kadan harya fara wuce hankali idan suka fara Susan jikinsu har saisun jima kansu ciwo ko'a gaban waye kuwa idan yafara musu saisun Sosa hakan yasa abokan iskancin nasu suka fara guduwa ganin yanda warin ke damunsu ga kurajan sun fara rashewa saboda uban Susan da sukesha hakan yasa meenah da feenah zuwa asibiti domin ganin wani kwararan likita ganin yanda ki Bcci sun daina samu saboda azabar susa su kansu warin jikinsu damunsu yakeyi, gwajin farko aka shaida musu dukansu su biyun suna daukeda cutar ciwon sanyi tareda hepatitis wacce tayi mugun tasiri a jikinsu bugu da Kari ga Infection daya mamaye su, fadin irin tashin hankalin da suka shiga bata baki ne atake akaba kowacce Gado inda suka fara Amsar kulawar da batada amfani sai uban kudi da suke kashewa, ganin abun bana karewa bane yasa suka sanarda mahuta saboda kudin hannunsu kaf yakare a magani da kudin asibiti inda batareda bata lokaci ba yazo ganin halinda suke ciki yama fisu shiga tashin hankali baiyi kasa a guiwa ba a lokacin yaje domin tantance jininsa cikeda tashin hankali da Adduar Allah ya kubutar dashi, "hmm su mahuta kenan Ashe ka Iya Add'ua, ya manta da Ubangijin sa na lokaci Mai tsawo ganin yana cikin tsanani shiyasa ya tuna Allah Wanda shi Allah ba'a masa wayau da dabara gwajin farko aka sanar dashi ya kira iyayansa domin bazaa Iya nuna masa sakamakon gwajin nashi ba saida wani babban jigon shi,babu yanda baiyi ba Kiri Kiri likitan yace saiya kira wani na jikinsa Babba, ganin babu mafita yasa yakira sanata da mommy inda cikeda tashin hankali suka karaso asibitin tareda uban bodyguard sai jiniya ke tashi a asibitin saikace shugaban kasa ne yazo, ganin result din kai tsaye sanata ya yanke jiki ya fadi Wanda hakan yayi sanadiyyar shanyewar barin dama na jikinsa gaba daya mommy ma baa barta a baya ba saida ta suma inda mahuta ke tsaye kamar mutum mutumi yakasa ko motsi sai hawayan dake bin idonshi.


Awani madaidaicin gida na Hango Hajiya Ramata da Alhaji Garbati Wanda ake shirin Auransa nanda wata biyu masu zuwa inda Ak yajashi jikinshi sosai tareda dorashi a wani sashi na kasuwancin shi, Alhmdlh kuma Garbati ya shiga da kafar dama kasancewar samai rikon gskia da amana inda AK ya siyan musu karamin gida Mai matukar kyau tareda daki hudu da sunan Aisha anan gaban unguwansu kadan inda dakyar suka koma saida Aishar tasa baki sannan dakyar Ramata ta yarda inda AK ya biyama Mai'unguwa kujerar umara adalilin Adalcin sa uwa uba shine Wanda yafara masu Eeashar sa sutura a garin Kaduna Wanda yabaka muhallin zama fiyeda shekaru masu yawa bakaramin masoyin ka bane kuma uwa uba mutumin bai taba goranta maka ba, Murna wurin mai'unguwa baa magana ganin shima yanzu za'a fara kiransa da Alhaji mai'unguwa matsayi akan matsayi inda Aisha bataje hajji ba sakamakon yanayin da take ciki a yanzu Mamie ce taje a madadin Aishar.
Aisha nagani zaune a kujerar parlor tareda katotan ciki a gabanta ta kumbura hancin nan yayi double fuskarta ya ciko sosai kafanta nakan cinyar AK Wanda keta tsokanarta yana kiranta da sabon sunanta " Orobo Maman iyabo"kukan sha'gwaba take masa tareda Alkawarin zata gayama mamien ta



*Mr's Saddiq Rumah*πŸ’…πŸ»



πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*


*Written by Anty Mamie.*

*His Smile😌OMG, paradiseπŸ’ž Alhmdlh for having u in my life, u are a great blessing from Allah SWA. I want you in my arm's, in my drmz, in Reality and in fantasy, U have Always been supportive My dearest hubby may Allah protect,πŸ‘πŸ» Bless,πŸ‘πŸ» GuideπŸ‘πŸ» and prolong ur life for usπŸ‘πŸ»MAI'NI.*


*Dedicated to sister Husna.*


43


*END*


Shirye shiryen bikin Auta bilki akeyi babu sassauci tareda Angonta Abdulhakeem inda babu Wanda yakai Alhaji Muktar farinciki Mamie kuwa bakinta yaki rufuwa da murnar samun Nagartttun sirikai mata daga gidan mutunci marasa San abun duniya inda Hajiya Aisha tafi kowa murnar ganin yar'uwarta kuma kanwarta Kawarta sannan Aminiyar ta wacce batada kamarta zata Aura kanin mijinta inda taita godema Allah hidima akeyi bana wasa ba, Lefen leemah da Ak yayi Shiya kai aka chanza masa wasu daga cikin kayan tareda Kara masa da sababbin yayi inda aka chanza duka setin Akwatin kasancewar a wurin Abokin kasuwancin shi dama ya siya kayan ba'a wani sha wahalar gyara Lefen ba, Kaninshi yaba gaba daya kayan a cewarsa shine gudunmawar sa na bikin Hmm zokaga murna da gulma a unguwa masu kishi nayi masu bakin ciki nayi wasu har'cewa sukeyi asiri su Ramata sukayi saboda mallake iyalan Gidan Alhaji Muktar inda munafukai suka fara kananan maganganu irinsu Virus harda tunoda rayuwar Aisha nabaya, Ak baiyi kasa a guiwa ba inda aka tasa keyar virus magarkama a dalilin batancin sunan daya dade yanama su Aisha wasa wasa maganar saida taje kotu inda dama burin Ak kenan yanaso ya wanke Matarshi da marigayi sirikinshi daga karshe da wuya yayi wuya Virus ya warware duk kullin dayayi ma Aishar harda sharrin dayayi akan yaga ya'u da diyarsa na zina harda niyyan fyaden da sukaso yima Aisha Allah bai basu nasara ba, nan Ak ya bude Babban murya tareda shedama Duniya Matarshi Tsarkakkiya ce shine namiji na farko kuma na karshe a rayuwar ta nan kotu ta wanke Aisha tsaf daga zargin da ake mata, murna wurin Aisha kuwa baa magana Virus kuwa Tara aka cishi tareda horo Mai tsanani na tsawon shekara uku a gidan yari saboda samun shida laifuka masu yawa da akayi.



*A'gurguje*
*Bayan shekara Goma.*


Shekara hudu kenan da Rasuwar mahuta inda ciwo Mai karya garkuwan jiki yayi Ajalinsa wato *HIV* Wanda yasha jinya Mai tsawo cikeda nadama tun kafun ya rasu ya nema Alfarmar Amso mishi yarinyar sa a hannun leemah wacce Malam Babba ke rikewa yayinda leemah ta auri wani magidanci Mai mata uku itace cikon ta hudu ba laifi yanada rufin asiri suna zaune a garin Kano tareda yaronta daya wanda yaci sunan malam liman, Bakaramin soyyah iyayan mahuta kema Zainab ba diyar mahuta, saboda tausayi da soyyar da sukema mahuta ganin yanda suka hanashi tarbiyyah harda sakacin sune yakara jefa shi a rayuwar dayayi nadama ce sukayi Mara amfani domin mahuta tuni ya rigamu gidan gskia saidai muce Allah ya gafarta masa mukuma ya kyautata karshan muπŸ‘πŸ».

"Yammata ne guda biyu kyawawa babbar fara tas wacce bata Gaza shekara Goma ba Mai suna Husna, sai Mai bimata chocolate color hartafi Babban kyau, Mai suna Rahma suna cemata "Ummita" sai karamin namiji Wanda shine karamin su Wanda bazai Gaza shekara hudu ba inda sunan Alhaji Muktar yaci suke cemasa "Calipha" babu Abunda ya bari na ubansa kama yakeyi sak da Ak babu abunda ya bambanta su, Hajiya Aisha wacce tagama zama babbar mace ceta fito daki sanye da doguwar riga baka yayinda take turo Dan karamin bakinta hayaniyar yaran dukta isheta inda kai tsaye kitchen ta dosa a dalilin kaurin dataji, sanye yakeda Apron ya zake sai game yakeyi da yaran a wata katotuwar wayar shi yana biye musu sunata ihu duksun makalkale shi yayinda yake zaune a doguwar kujerar kitchen din basa kojin kaurin da dake tash kai tsaye ta kashe gas din Wanda tafashen nama ya Dora zai musu abincin dare kasancewar Aishar bata iyayin girki saboda uban laulayin daya tasata a gaba inda Ak keyi duk sanda yake gida kokuma ya dibesu suje restaurant kokuma gidan Mamie kona "second Grandma" wato Ramata kamar yanda yaran kece mata, kwata kwata bai yarda da abincin yan aiki ba dukda sunada su"Haba Haba 1st love duk kuncika gida da ihu bakwa kojin kaurin naman da yake konewa katasa yaranka kun hanani Bcci, Shiru sukayi mata kamar basusan da ita a wurin ba, " dear magana fa nakeyi ko baku ganni bane? "Sorry wife mun jiki muna zuwa please bari mudan gama wurin nan, " Husna, ta kira sunan babbar diyarta, "Yes mommy ta amsa batareda ta kalli mamar tata ba sai ihu sukeyi da daddyn su ganin basuda lokacin tane kamar yanda suka saba mata hakan yasa itama taimusu abunda tasaba, kwace wayar tayi dadan gudu gudu ta fita tsakar gida inda gaba daya suka biyota suna ihu harda Daddyn su, Please mommy please mommy ki bamu wyyooo mommy za'a cinyemu, Ak neya fadi cikin muryar magiya kamar yanda yaran keyi, Damkarta sukayi suna ihu A'daidai lokacinda Mai gadi ya wangale gate din gidan wata bakar hadaddiyar mota tashigo nan yaran suka fara tsallen murnar ganin motan kai tsaye suka rungume bilki wacce takeda yara biyu a lokacin duk maza Mai aikinta ce tafara fitoda manya mantan kulolin shake da abinci kala kala Wanda bilki ta tsara domin yin dinner a gidan yayyin nasu itada iyalan gidanta gaba daya dama sunayin haka jefi jefi saboda karuwar zumuncin nasu kai tsaye suka rankaya katafaran parlon dake gidan inda Ak ke tsokanar Eeashar sa, " Maman yan hudu taka a hankali, harara ta wurga masa, 'dayan ma yana kare? Gskia daga wannan zan huta....wlh baki isa ba, duk shekara saikin sullubo mun kyawawa masu kamada ke idan har Allah ya bamu saikin haifo mun yara Ashirin insha Allah, "Yeeeeaaaaahhh mommy zata Haifa yara ashirin inji Calipha Wanda keta faman tsallan murna A tunanin shi cikin jikin Mommyn nasa ne dauke da yara Ashirin, dariya akai tamasa inda " Aisha taketa faman hade rai sanin yanda Ak ke kaunar yara ita kuma tana bukatar hutu, 'Gskia ni wlh hutawa zanyi Yara ishirin inyi Yaya dasu? "Wlh koki haifo mun kokuma in nemo Mai haifo mun, yafadi cikeda zolaya " Aiko baka isa ba indai akan haihuwa zakai mun kishiya duk

Please Login or Register in order to submit comment