Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dalilin yasa na hak'ura har na haifeta, amma na shiga damuwa sosai, saboda ina fargaba kada na kawo maka yarinyar kace ba kai ne ubanta ba, sai dai nayi farin ciki sosai da Allah yasa yarinyar tayi kama da kai, don Allah Hajiya ku yafe min."

Hajiya ta dinga kuka tana fadin" Fatima kinga ikon Allah ko? yanzu kin tabbatar da cewa, ba a yiwa Allah wayo tunda ya saukar da ishara a kanki, ya kamata kiyi hankali kuma"

Ta ce"Wallahi Hajiya nayi nadama sosai, na san kuma abinda na aikata ba dai-dai bane don Allah ki bashi hakuri ya mayar dani d'akina"

Na kalleta zuciyata cike da b'akin ciki abinda ta aikata Na ce"Har abada aure ya haramta a tsakaninmu, idan kin manta to bari na tuna miki, saki d'aya sau uku nayi miki, ba kuma a lokaci guda ba, ballanatana ki kawo min wani k'auli da ba'adi! saki uku ya halarta a kanki, ni dake har abada mun gama zaman aure, wannan yarinya kuma na 'karba Allah yayi mata albarka"


Sosai take kuka tana bani hakuri wai idan aka tambayi malamai za su iya gyara lamarin, kallon mahaukaciya kawai nake mata, ina ji Hajiya na tambayarta sunan yarinyar ta ce" Sunan mahaifiyarsa nasa mata wato Aisha, amma sai nake kiranta da Shukura"

Ta ce"Aikuwa kin kyauta da ki ka sanya mata sunan Aisha, Allah yasa ta gaji halinta.

Tashi nayi na basu guri domin zamana a gurin ina kallon fuskarta yana tuna min da munanan abubuwan da suka faru a baya.

Wannan shine mafarin dawowar Shukura hannuna, domin hana ta tafiya nayi da ita, Hajiya ta cigaba da rainonta, ita kuma tunda ta tabbatar da cewa ba zan mayar da ita ba, sai ta fara biye-biyen malamai, daga 'karshe dai ta je tayi auran kisan wuta wanda ko wata uku ba tayi ba ta fito, ta zo ta matsanta min cewa lallai sai na mayar da ita gidana, sai da nayi mata jan ido sosai! ta saurara min, na nuna mata cewa ko babu mata a duniya sai ita wallahi ba zan 'kara zaman aure da ita ba.

"Wannan shine tarihin rayuwata da Fatima matata ta farko, kuma Uwar Shukura, kasancewar asubah ta gabato zan tsaya miki a nan kafin na cigaba da baki labarin abinda ya wuce..



*Duk wacce ta fita da littafin nan ba da yawu na ba, ki biya kafin ki karanta. #500 ne ga hanyar da za a biya kudin..0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel.*
*BINTA UMAR ABBALE*


*ABACHE POULTRY FARM*=ØÜ=ØÜ=ØÜ
*Shahararran kamfanin da suka 'kware gurin kiwon kaji k'ossasu! masu rai da lafiya. a kamfanin ABACHE POULTRY FARM ne kad'ai za ka samu irin lafiyayyun kajin da kake bukata, domin kamfani ne da babu irinsa a SOKOTO. Suna kiwon kaji irinsu (buluras da maja)* *domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu! ga masu gidajen abinci (restaurant) k'ofa a bude take ku garzaya ABACHE POULTRY FARM. domin yin oder lafiyayyan kajin da za ku 'kawatar da mutananku sannan kuma suna bada sari na k'ananun kaji a ko'ina a fad'in Najeria! ABACHE POULTRY FARM. ba a nan kawai suka tsaya ba suna da gurin sayar da kayan ma'kulashe wato ABACHE SNACKS AND MORE 'Kayattacen guri ne na mussaman da suka tanadar muku da kayan dad'i masu kyau da tsabta kamar irinsu MEAT-PIE- DOUGHNUT- CAK-SAMOSA- Domin shagalin biki ko suna ko nad'in sarautu murnar Birthday da dai sauransu. ABACHE POULTRY FARM AND ABACHE SNACKS MORE. suna nan a KWASAI wato SOKOTO BAFARAWA ESTATE domin neman 'karin bayani sai a tuntu'bi wannan numbers.*
*08069459550*
*08039451082*


*VIP GROUP SAU UKU A RANA MAI BUKATA YA YI MINI MAGANA*
77&78
Saukar ajiyar zuciyarta yake ji tare da sheshshekar kukanta, wanda yake masa tsananin zafi a cikin ransa, shima kukan zucci yake, sakamakon tuna abunda ya wuce na daga rayuwarsa, hannu yasa ya dinga goge mata hawaye yana rarrashinta da kalamai masu sanyi, har ya samu tayi shiru ta daina kukan, ya matse ta tsam! a kirjinsa yana jijjigata kamar 'yar goye.

Kiran sallar asubahi ne ya raba tsakaninsu, a hankali ya cire ta daga jikinsa ya tashi ya shiga toilet domin d'aura alwala.

Sai da yayi wanka tukkuna sannan ya d'aura alwala a gurguje ya fito daga band'akin, nan ya sameta a zaune gefen gado. kallon juna sukayi, yayi mata murmushi na mussaman kafin ya bud'e k'ofa ya fita, sai ta bishi da kallo tana mamakin al'amarin, gabad'aya jikinta ne ya mutu sakamakon jin labarinsa, ta rasa wane tunani za tayi domin gani take kamar ita d'in ba ta dace dashi ba, duba da matsayi da mu'kamin sa, ya kere mata nesa ba kusa ba, ya za'ayi ta saki jiki dashi ta kwantar da hankali har tayi rayuwar aure dashi.

***
Tunanin da na jima a cikinsa shine rayuwar aure da talaka dai-dai da ni, don wallahi ban ta'ba sanyawa raina auran mai kudi ba, duba da lalura ta, bayan haka kuma bani da wani kyau na kuzo a gani, sai kuma gani a matsayin matar babban mutum! wanda jama'a suke alfahari dashi, wannan kad'ai ya isa na godewa Allah a bisa ni'imar da yayi min. to amma a raina nake jin kamar auran namu akwai matsala ta kowane 'bangare.


Wanka nayi na shirya jikina cikin riga da siket na atamfa, mai kawai na shafa a jikina na gyara gashin kaina, ban d'aura dankwalin ba, sai kawai na yafa a kaina na fito falo na zauna, tunani yayi min katutu! domin kwata-kwata na kasa shiga kicin ballantana nayi tunanin abinda zan ci, da damuwa gami da fargaba sun taru sun cushe min ciki bana sha'awar komai .

Haka ya shigo ya same ni cikin wannan halin. kallo d'aya nayi masa nayi saurin kawar da kaina, yayi bala'in kyau cikin 'kananun kayan da yake sanye a jikinsa, mutum ne shi mai wani irin kwarjini da haiba wanda da yawa mutane basa iya had'a ido dashi, sosai k:ananun kayan su kayi masa kyau, ya dawo matashin saurayi, farin gilashin da yake tu'ammali dashi a koda yaushe, yana 'kara masa kyau mutu'ka!


Kusa dani ya zauna jikinmu har yana had'uwa 'kamshin turaransa duk ya dabaibaye gurin.

Gefe na d'an matsa ina wasa da yatsun hannuna.

Ya kama hannun da fad'in." Yaushe za a yi min lalle ('kunshi) irin na amare ina bukata" yana maganar ne lokacin da ya had'a yatsunmu guri daya.

Jikina ya d'an mutu sakamakon jinsa a kusa dani, namijin 'kokari nayi gurin gaishe shi.

Ya amsa tare da sa bakinsa daidai kunne na ya ce." Ya gajiyar kuka?"

Murmushi nayi na ce" Labarinka ya bani tausayi sosai! amma kayi hakuri jarrabawa kowa da irin tashi, sannan ka godewa Allah da ni'imar da yayi maka."

Ya ce" Kullum a cikin godiyar Allah nake, gashi yanzu ya amsa min addu'a ta, ya azurtani da mar'atussaliha"


"Nayi mamakin sosai da wannan al'amarin, amma ya akai kake sauya hallitarka? don wallahi ban ta'ba tsammanin kaine kake kasancewa mutum biyu.

Dariya yayi ya ce" Zan baki labari anan gaba, ni dai burina ki saki jiki da ni, ki ri'ke ni amana, domin nasha wahala a hannunku, shiyasa nake tsoronku, amma dai ina da tabbacin ke ba zaki wahalar dani ba ko?" Yanda ya fad'i maganar ne ya bani dariya da tausayi. Na ce" Auranka nawa?"


"Wannan shine na uku kuma ina rokon Allah yasa nayi dace." Ya fada tare da rintse hannuna da nasa.

Shuru kawai nayi ban ce komai ba.

"Kinyi shuru ko baki amince dani a matsayin miji ba"

Na ce" Ni dai gaskiya sai nayi tunani tukkuna, domin naga kamar kana da dabi'ar auri saki, ita mace tana da rauni me yasa ba za kayi hakuri da hallayar mata ba.

"Bangane abinda ki ke nufi ba" yafada da alamun rashin dadi a tare dashi.

Na ce" Ni ina tunanin wani abu ne"

Hannuna ya ri'ke jikinsa na rawa ya ce" Ki daina tunani a kaina matata kuma kada ki dauki abinda nayi miki da wata manufa! nayi hakan ne domin na gwada ki kuma alhamdulillhi, kin yi d'ari bisa d'ari! ni yanzu na ga matar aure."


Ido kawai na zuba masa ina auna maganganunsa, yayin da shi kuma ya zage! sai kalaman soyayya yake zuba min tare da rarrashi da daukar alkawari.


Na ce" Ni dai gaskiya zan fad'a maka abinda yake zuciyata shine, ba zan iya rayuwar aure da kai ba"

Cikin rashin jin dadin furucina ya ce." Saboda me ki ke wannan maganar menene dani da ba zaki amince mu raya sunnar ma'aiki ba"

Kasa magana nayi saboda yanda ya bani tausayi, nasan har cikin zuciyata nake tausaya masa, amma kwata-kwata bana jin sonsa a cikin raina.

Cikin rashin jin dadi, ya tashi ya fita, sai na bishi da kallo, ina tunanin abubuwa da yawa a cikin raina.

Minti ashirin da fitarsa, ya dawo amma tare da Hajiya suke, gabana ya fad'i, dama cikin tunanin yanda zata kar'bi al'amarin nake, duba da cewa; yayi abun a rufe bai bayyana gaskiya ba, fuskarta a sake ta nemi kujera ta zauna tana kallona.

Saukowa 'kasa nayi na gaisheta, cikin sakin fuska ta amsa gaisuwata sai kallona take wanda ya sanya na tsargu, na shiga wasa da yatsun hannuna tare da k'ok'arin mayar da hawayen dake kokarin zuba.

Sai da ta bud'e muryarta sosai sannan ta ce" To ke Shahida idan ban da abunki menene abin damuwa a cikin wannan al'amarin, ai komai na Allahu ne , ni wallahi nayi murna sosai da jin wannan abu, kuma nayi muku fatan alheri, dama buri na kenan yayi aure, to Alhamdulillhi, bukatata ta biya, saboda haka ki kwantar da hankalinki, duk abinda ya same ki, na alheri to halinki ne ya ja miki, domin mijinki yayi min bayanin dukkanin abinda ya faru, don haka ki saki jikinki damu, sannan kuma kiyi hakuri ki 'karbi wannan aure hannu biyu, domin hakan alheri ne.

Ajiyar zuciya na sauke na ce" Hajiya al'amarin ne na rasa ina zan ajiye shi a raina, amma cikin zuciyata sai nake tunanin kamar ni ba tsaran auransa bace, bayan haka kuma ina tunanin wani abu."

Shi ya rigata magana da fadin" Wannan ba hujja bace Shahida, na san abinda kike tunani, amma bari kiji wani abu, ko kin fi haka rauni ko nakasu! wallahi zan aureki, domin ni bana bukatar kyau! ko wata d'aukaka! tarbiya nake buk'ata da amana, kuma na samu da yardar Allah, saboda haka kisa a ranki cewa; ni naki ne har abada kuma uban 'ya'yanki."

Kallonshi nayi, tare da girgiza kaina, domin ni abinda nake dubawa daban da tunaninsa.

Ta ce" Nima hankalina ya kwanta da yarinyar nan Alhaji Habu, saboda haka kayi k'ok'arin rarrashinta domin ta samu nutsuwa."

Ya ce." Insha Allahu Hajiya."

Ta kalleni tare da cewa" Shahida ni zan tafi amma don Allah kada ki bijirewa auranan, kiyi hakuri ki zauna tare damu kinji ko"

Tausayi ta bani sosai! na ce" To shikkenan Hajiya nima na gode sosai"


To tunda ya fita bai sake shigowa ba sai bayan isha'i, ya shigo ya same ni kan dadduma na idar da sallah, ina addu'a.

Zama yayi kusa dani tare da d'aga hannunsa sama yana fadin" Allah ka mallaka min zuciyar matata ka bamu zuria masu albarka.

Ina jinsa yana ta addu'oi, nima ina yin nawa, na shafa a fuskata, shima shima ya shafa, ya kalle ni da murmushi na mussaman a fuskarsa, babu yabo babu fallasa na gaishe shi, ya amsa a lokacin da yake 'kok'arin rike hannuna. da sauri na janye, na tashi na bar shi a gurin.

Beyi zuciya ba, ya sake zuwa kusa dani ya zauna tare da rungumo ni jikinsa, kawai sai na fashe da kuka! ina ture shi! " Ka matsa daga kusa dani"

Ya ce" Me yasa zan matsa bayan ke din halalina ce''

"Ni ban san ya za'ayi nayi rayuwar aure da kai ba, domin baka cikin tsari na" Na fad'a tare da cire hannunsa da d'ora a saman cinyata.

Ido ya zuba min da alamun damuwa a tare dashi ya ce" Menene abinda ba kya so a tare dani?"

Shuru nayi masa, ya ce" Kada fa ki butulcewa Allah Shahida."

Ajiyar zuciya na sauke da fad'in" Nafiso na auri daidai da ni, mai rauni da rangwamin gata.

Ya ce"Sai kuma Allah ya baki Saddiku a matsayin miji shin ya za kiyi kenan? da yanayi na 'bacin rai yayi maganar.


Tashi nayi na shiga d'aki na kwanta tare da tsirawa rufin d'akin ido! hawaye masu zafi suke zuba, shin ya zanyi ne? na san Ubangiji ya gama yi min komai da ya mallaka min babban mutumin mai daraja irin wannan, amma a jikina nake jin kamar akwai abinda zai faru mara dad'i dangane da auransa.


Shigowarsa d'akin yasa nayi saurin goge hawayena, ya ce" Kina yi min asarar hawayenki wanda ya fi gold tsada a gurina, bari kiji wallahi duk abinda za kiyi ba zan rabu dake ba, domin ni naga matar aure.

Kallonsa nayi a lokacin da yake maganar, nan naga tsagwaron sona a cikin k'wayoyin idanuwansa.

Ya ce" Yini guda duk kin rasa sukuni! kinyi rama ta ba gaira ba dalili, kowane bawa fa, da kaddararsa, ke taki k'addarar auran dattijo wato Saddiku, kuma kin shigo hannunsa kenan, domin ba zan iya rayuwa babu ke ba.

Na ce" Aikuwa ba zaka samu nutsuwar da kake bukata ba, tunda dai ni bana 'kaunarka, tausayinka kawai nake ji, kuma ban san ya za'ayi nayi rayuwar aure da kai ba.

Murmushi yayi kafin ya ce" To tunda akwai tausayi ni na tabbata da akwai k'auna, amma mu je zuwa dai tunda kin fad'i haka.

Juya masa baya nayi tare da rintse idona! sai kawai na jishi a kusa dani, yana k'okarin rungume ni! na ture shi da karfi! na tashi zaune tare da matsawa 'kuryar gado!

Kallo na yayi na minti biyu kafin ya ce" Kin san dai hukuncin matar da take 'kauracewa mijinta ko?"

Gabana ya fad'i! da jin maganarsa.

Cikin rawar murya na ce" To me kake nufi?"

Murmushi yayi wanda ya tsaya iya fatar bakinsa ya ce." Bana nufin komai sai alheri, ko zan kar'bi hakkina ba yanzu ba sai zuciyarki ta aminta dani, amma yanzu ina so ki bani hankali domin cigaba da warware miki abinda ya faru da rayuwata wanda baki sani ba, ina so na baki labarin d'aukakata da kuma cigaban labarin zaman aure na da matata ta biyu.

Jin haka yasa na kalle shi da fad'in" Ya sunanta?"

"Zinaru" yafad'a yana kallon fuskata. baki na ta'be da fad'in" Yunwa nake ji yanzu" sauka yayi daga gadon, ya kama hanyar fita ba tare da yace min komai ba, nima na bishi da kallo tare da nazari da tunanin abubuwa da yawa a tare da ni, da shi.


*Duk wacce ta fita da littafin nan ba da yawu na ba, ki biya kafin ki karanta. #500 ne ga hanyar da za a biya kudin..0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel.*
*BINTA UMAR ABBALE*




78&79
Hannunsa ri'ke da fulas mai d'an girma ya shigo dakin, ido na tsira masa har ya 'karaso gurin da nake zaune, cikin taushin murya ya ce" Tashi ga abincin na samo miki gurin Hajiya." Shuru nayi ban ce komai ba, kuma bani da niyyar tashi.


Ya ajiye fulas din kan dirowa, ya hayo gadon yana k'okarin janyo ni, Na cire hannunsa da fad'in" Don Allah ka daina ta'ba ni."

A sakarce ya kalle ni, kafin ya girgiza kansa, yanayinsa ya nuna kamar ya fara gajiya da abinda nake masa, ni kuwa duk abinda nake yi, baya damuna, domin har yanzu ban yi na'am dashi a cikin zuciyata ba, amma kuma ina mamakin yanda yake min rawar jiki, kuma ina kallon tsagwaron sona a cikin 'kwayoyin idanuwansa.

Kansa ya sunkyar k'asa yayi shuru tare da tsirawa k'asa ido! wannan ya sake tabbatar min da cewa; ransa a 'bace yake da abubuwan da nake masa.

Jiki a sanyaye na sauko daga gadon, na shiga band'akin dake cikin dakin, na wanko hannuna na fito, na same shi a yanda yake, kusa da kafafunsa na zauna tare da janyo abincin na bud'e, abinci ne mai rai da lafiya, sai 'kamshi yake, lokaci 'kank'ani yunwar da nake ji ta dawo sabuwa, hannu nasa da bissimillah a bakina na fara cin abincin.

Tashi yayi ya fita, minti uku ya shigo da ruwa da lemo ya ajiye a gabana, kunya duk ta rufe ni ganin irin hidimar da yake min, ni kaina na san abinda nake masa bana kyautawa. a hankali na ce" Sannu" bai amsa ba, kawai ya nemi gefen gado ya zauna tare da kunna wayarsa yana dubawa.

Har na kammala cin abincin, hankalinsa yana kan wayarsa, na je na wanke hannuna, na zaune can 'karshen gado.


A nutse ya kalle ni tare da fad'in" Kin 'koshi?" shuru nayi ina kallonsa don ban ji abinda ya fad'a ba.

Murya ya bud'e kafin ya sake maimaita maganarsa. kai na d'aga masa alamar "Eh na ko'shi.

Ya ce" Kin shirya saurarata yanzu?"

Cikin jin nauyi na ce"Eh" sai ya ajiye wayar hannunsa a kusa dashi, wannan karon beyi yun'kurin rungume ni ba, sai dai ya mayar da hankalinsa kaina sosai kafin ya cigaba da bani labarin rayuwarsa.


"Zinaru, 'kanwar maigida na ce, ina nufin mutumin da nake aiki a 'kar'kashinsa, ni dai da bakina da nasa ban ta'ba fad'a masa cewar bani da aure ba, sai kawai ya same ni da wata magana wacce na kasa yin jayyaya dashi.

"Saddiku na yaba da hankali da nutsuwarka, wananan dalilin yasa nake neman wata alfarma a gurinka, ina fatan zan samu.

Na ce" Alhaji wace irin alfarma ce wannan?" domin ni a gani na mai nake dashi da har zai nemi alfarma a guri na.

Ya ce" 'Kanwata nake so ka aura" gabana ne ya fad'i! na kalle shi tare da fad'in" Alhaji ai ina da aure"

Murmushi yayi kafin ya ce" Allah ta'alah hud'u ya ce mu aura mutukar muna da iko! to ballanatana kuma na san da cewa; baka da aure, na samu labari a bakin abokinka Faruk, wannan dalilin yasa na nemi wannan alfarmar a gurinka.

Wato Faruk ne ya fad'a masa cewa; bani da aure, amma gaskiya ban ji dad'in abinda yayi min ba domin kwata-kwata babu maganar aure a tare dani, amma tunda al'amarin ya kasance haka, dole nayi hakuri, domin ba zan iya jayayya da wanda ya rufa min asiri ba.


Na ce" Alhaji Na gode da wannan kyauta da kayi min, tabbas hakane, bani da aure a yanzu, amma shekarun baya na auri 'yar uwata har da rabo a tsakaninmu."

Ya ce" Ma sha Allah. ai duk Faruk ya fad'a min komai. amma idan kana ganin da akwai matsala sai na janye.

Na ce" Haba Alhaji ai kafi 'karfin komai a guri na wallahi, zan auri 'kanwarka kamar yanda ka bu'kata"


Ya ce" Na gode sosai Saddiku da wannan rufin asirin da kayi min, sai dai kuma hanzari ba gudu ba"

Shuru yayi fuskarsa da alamun damuwa.

Na ce" Alhaji da akwai matsala kenan?"

Ya gyad'a kansa da fad'in" 'Kwarai kuwa Saddiku ba zan munafurce ka ba, yarinyar nan ta d'an yi yawo gaskiyar magana kenan, bana tsammanin za a samu budurci a tare da ita, bayan haka kuma tana da aljanu, wanda muke tunanin sune suke sanyata aikata munanan ayyuka"

Gabad'aya jikina ya mutu! cikin zuciyata nake tasbihi ga Ubangiji duba da irin kaddarar da take wanzuwa a tattare dani, ba zan ta'ba bijirewa umarnin Alhaji Harazimi ba, domin yayi min abinda ba zan manta ba.


Na ce" Alhaji kada ka damu. auran Zinaru a gare ni, kamar jahadi ne, mutukar tayi istibura'i zan aureta na kuma zauna da ita da zuciya d'aya, maganar aljanu kuma, ba su fi k'arfin Allah ba, insha Allahu zanyi iyakar bakin kokarina akan hakan.

Nan da nan, ya saki fuskarsa cikin jin dadin lafazi na, ya ce" Na gode sosai Saddiku Allah ya saka maka da alheri, hakika ka rufa min asiri a lokacin da nake bukatar hakan, a duniya bani da matsalar komai, sai ta Zinaru, 'kanwata ce, mu biyu iyayenmu suka haifa, asali mutumin Nijar ne, cikin zinder aka haife ni, neman kudi ya kawo ni Najeria, har nayi aure na tara iyali na, bayan rasuwar iyayenmu, Zinaru ta dawo hannuna, wallahi tunda ta zama cikakkiyar budurwa ta gagare ni, babu irin dukan da ban yi mata ba, amma k'arshe sai ta tattara kayanta ta gudu, sai tayi wata uku hud'u sannan zata dawo gida, wannan dalilin yasa na daina dukanta, sai na tsananta da addu'a tare da sanya matakan tsaro a gidana, amma duk da hakan, sai ta fita yawo, maza na d'aukarta a mota su tafi uwa duniya, wannan shine dalilin da yasa na yanke shawarar yi mata aure, ko Allah zai sanya ta shiryu.

Cikin damuwa na ce" Ranka ya dad'e ka kwantar da hankalinka, duk abinda yayi farko, yana da 'karshe! ni nayi maka al'kawarin ri'ke yarinyar nan amana, zanyi iyakar bakin 'kok'ari na insha Allahu.

Sosai ya dinga yi min godiya har sai da ya bani tausayi.

Wallahi Shahida idan kin ga Zinaru, sai ki dauka ita tayi kanta saboda tsananin kyau! domin ta ko'ina tayi, cikakkiyar mace kyakykyawa, tana da duk abinda namiji yake bukata, dama na fad'a miki asalinsu, 'yan nijar ne, buzaye ne gashinta har baya gata da kyau! sai dai rashin kyawun hali.

Amma kin san wani abu, wallahi kwata-kwata ni ba ta kwanta min a raina ba, kawai dai na aureta ne saboda d'an uwanta, dama can a tsari na bana son auran kyakykyawar mace, saboda wasu dalilai nawa.

Zuwa na gurinta sau d'aya aka d'aura aure ta tare a gidana, washe garin ranar d'aurin auran Alhaji Harazimi yayi min kyautar d'aya daga cikin kamfaninsa na shinkafa! sosai al'amarin ya bani tsoro mutu'ka! na kalle shi a lokacin da yake bani takardun kamfanin, na ce"Alhaji kada muyi haka da kai, don Allah ka janye wannan kyautar, wallahi ban auri yarinyar nan don abun hannunka ba, na aureta ne tsakani da Allah, da kuma darajarka, amma ban aureta don ka bani wani abu ba.

Murmushi yayi tare da cewa" Saddiku ba ka ji bahaushe yana fad'in" Yaba kyauta tukwici ba, wallahi zan iya mallaka maka duk kadarorina, saboda rufamin asiri da kayi, ka auri 'yar uwata ba tare da ka 'kyamace ta ba, a wannan zamanin da kowane uba yake kokarin samawa 'ya'yansa uwa ta gari, sannan ba kowa ne zai yarda ya auri mace irin Zinaru ba, ai ni ka gama yi min komai, saboda haka kyauta nayi maka, kuma babu mai canza ta, ina bukatar ka tsaya da k'afafunka saboda nauyin iyali, tunda akwai yaran da su kayi iya aiki ta dalilinka, to za su cigaba da zama a 'kar'kashina, amma kai na 'yantaka insha Allahu.


Gabadaya sai jikina yayi sanyi da kalamansa, hannu biyu nasa na 'karbi takardun ina godiya. Ya ce" Zaka cigaba da gudanar da komai na kamfanin, domin ya riga ya bar hannuna, kuma na tara duk ma'aikatan dake karkashin kamfanin na sheda mu su komai, saboda haka kanka tsaye, zaka cigaba da gabatar da komai."

Na ce" Na gode sosai Alhaji Ubangiji Allah ya 'kara suttura duniya da lahira, Allah ya amfani zuria" ya amsa da "amen ya Allah tare da mi'ko min hannu mu kayi sallama.


Abota ta da Alhaji Faruk babu ganin 'kyashi, ya taya ni murna sosai, kuma ya taimaka min ta hanyoyi da dama, har kawowa yanzu muna tare muna gudanar da harkokinmu.

Hajiya tayi farin cikin alherin da ya same ni tare da duk wani mai k'aunata, amma a zahiri ina ganin masu yi min hassada! sai dai tsakani na dasu addu'a ce.

Zama na da Zinaru da farkon fari, yayi dad'i sosai, don har na dinga k'ok'arin sanyata cikin zuciyata domin a lokacin ina ganin kamar tayi hankali ta nutsu ta shiryu kamar yanda muke bu'kata, don tun da na fahimci cewa; tana cikin jerin jarababbun mata nake

Please Login or Register in order to submit comment