Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

isha'i."

Ya ce." To waye ya hana ki? da duk zaman da ki ke a gidan ba kiyi sallar ba?"

Ta ce." Duhu ko'ina babu haske."

Ya ce." Ki bud'e wannan ledojin da akwai fitila da batiri a ciki sai ki kunna."

Da sauri ta fara dubawa, ya kunna mata hasken wayarsa har ta saita fitilar ta kama, sannan ya kashe wayarsa, ya kama hanyar fita, ta bishi da wani irin kallo zuciyarta sai bugawa take.

Tana d'aura alwala a bandakin dake cikin falon ta dinga jin motsinsa kamar yana shigowa da abu, sai da ta fito ne ta fahimci cewa kayan abinci ne.

Nan falon ta gabatar da sallolinta, ta jingina jikin kujera tana kallon shiga da ficensa tsakanin kicin da dakinsa.

Gani tayi ya zo ya zauna a daya daga cikin kujerun dake falon, ido ya zuba mata, sai ta kasa jure hada ido dashi, domin yanzu gabadaya tsoro yake bata, ya sauya sosai! ya dawo Baban-baba na asali wanda ta san shi a lokacin da yake kwanciya a 'kasan mota!

Gyaran murya yayi kafin ya kira sunanta yanda za ta ji.''

Ta amsa ba tare da ta kalleshi ba.


Ya ce." Nan ne gurin da maigidana ya bani domin na zauna da iyalina. bayan haka kuma sa'i da lokaci za ki dinga zuwa kina gaisawa da kakarsa wacce take zaune a cikin gidan, za ki dinga taimaka mata da wasu abubuwa duk da cewa akwai masu aiki amma kema zaki shiga sahun su, akwai kayan abinci a kicin komai da komai na bukata maigidana ya bani kudi nayi miki sayayya! a cikin ledojin nan akwai kayan sawarki kala hud'u da mai na shafawa da sabulun wanka da wanki da sauran tarkacen ku na mata, abinda babu kada kiyi 'kwaron baki sai ki sanar dani, amma ina so ki zauna da masu gidan nan lafiya! mussaman maigidana domin shi ya mayar dani cikakken mutum kamar kowa, wannan dalilin yasa nake so kiyi masa biyayya kamar yanda za kiyi min, duk wani abu da yake bukata kiyi masa.''


A sanyaye ta ce." Insha Allahu zanyi iyakar bakin kokari na, ni dai buri na ka ri'ke ni amana kamar yanda kayi alkawari!

Tsaki ya ja kafin ya mi'ke tsaye ya ce." Wace amana kuma? ki daina wannan maganar, domin kada ki manta fa ke kamar siyan ki nayi a gurin mahaifinki, saboda haka ki daina wannan maganar."

Wani irin kallo take masa tana jin maganganunsa na amsa kuwwa! a kunnanta "Kada ki manta fa ke kamar siyan ki nayi a gurin mahaifinki, don haka ki daina maganar amana." Wannan magana ta jima tana yi mata yawo a k'wa'kwalwarta.



Jin yunwa na nema ta halaka ta yasa babu shiri ta dauki fitila ta nemi hanyar kicin ta je tana laluben abinci, aikuwa ta samu fulas cike da dambun shinkafa wanda yaji kayan had'i! ga ledojin ruwa nan pure water ta dauka ta fito da fulas din abincin a hannunta.
*BINTU*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb

*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE MANAZARTA WRITES ASSO..
_____


53&54
A ta'kaice dai Shahida ita kad'ai ta kwana, domin tun da yayi fitar nan, bai dawo ba, tun tana jin tsoro har ta hak'ura ta barwa Allah al'amarin, sai dai bakinta bai daina addu'a ba har san da bacci 'barawo ya sace ta.

Motsin shigowarsa da asubah ya tashe ta, sai ta mik'e zaune da sauri tana laluben fitilar da gurin bacci ta fad'i a gurin, batiran duk suka watse

Shigowarsa yayi daidai da lokacin da ta gama gyara fitilar haske ya mamaye falon.

Ya kalle ta babu walwala a tattare dashi ya ce." A nan ki ka kwanta ne?"

Kanta ta daga masa alamar ."Eh." ya kama hanyar d'akinsa ba tare da ya sake wata magana ba, wannan ya sake tabbatar mata da cewa ba a gidan ya kwana ba.

Jiki a sanyaye tayi alwala ta fito anan falon dai ta gabatar da sallah, ta jima tana addu'a tana kuka sosai take neman sassauci a gurin mai duka domin ba ta ta'ba tunanin cewa zata fuskanci irin wannan matsala ba.

Sai da gari ya waye sosai ya fito cikin shiri ya d'ora rigar sanyi babbah da sabuwar hula irin ta sanyi ya rufe kunnuwansa sannan ya rufe idonsa da gilashi b'aki, tsira masa ido tayi domin gani tayi kamar yayi haske ba kamar can baya ba sai dai har yanzu wannan k'asumbar tana nan duguzaza! tare da tsalli-tsallin furfura.

Ganin yanda take kallonsa sai ya sha kunu! ya ce." Na zama tibi ne?"

Ba ta ji abinda ya fad'a ba amma yanayin yanda ya yi maganar yana tsatstare ta da ido ta fahimci cewa ransa a 'bace! sai ta d'auke kanta tana mamakinsa a cikin zuciyarta.

Gyaran murya yayi sosai ya bud'e ta domin ta ji abinda zai fad'a mata.

"Zan tafi can kudu wani aiki kamar yanda maigidana ya umarce ni, don haka za ki cigaba da zama anan babu wata matsala tunda akwai ci dasha saboda haka ki kwantar da hankalinki, amma ban amince ki je ko'ina na ba, abinda na aminta dashi zuwa gaishe da kakar maigidan kamar yanda na fad'a miki da farko.

Tsoro ta cire a ranta ta kalle shi sosai kafin ta ce." Shi maigidan naka bai san cewa kai ango bane zai tura ka wata uwa duniya, kada fa ka manta amana ka d'auko ni a gaban iyaye na mai yasa tun kafin tafiya tayi nisa ka sauya hali, wallahi ban yi tunanin haka daga gare ka ba."


Hannu ya d'aga mata da fad'in." Za kiyi min rashin kunya ne?" ta girgiza kanta. ya cigaba da cewa; idan na zauna a gidan me zanyi miki da har ki ke wannan maganar."

Sunkuyar da kanta tayi tana mamakinsa.

Ya cigaba da cewa'' Ai ban ta'ba ganin makwad'aicin uba irin naki ba, wanda bai san k'ima da mutumcin 'ya'yansa ba. domin ya ba ni auranki ne a matsayin fansa a gare shi, ke da bakinki kuma ki kayi al'kawarin girmama maigidana saboda alherin da yayi miki keda mahaifinki, amma har kina da bakin fad'in wata magana a kansa, to ki iya bakinki idan ba haka ba ranki zai yi mummunan 'baci!

Kuka take sosai! ta ce." Yanzu mai ya kawo wannan maganar? wato ka naso ka nuna min cewa maigidan ka ya fi ni kenan, kada fa kamanta bani da kowa a wannan gari sai kai, ban san ko'ina ba, sannan akwai rashin sabo wannan shine dalilina na fad'in wannan maganar amma bada cin mutunci ba.

Tsaye ya mi'ke tare da fad'in" Ni dai na fad'a miki ki kiyaye! kuma ki iya bakin ki, maigidana ya fi kowa daraja a guri na ciki kuwa har dake, mutukar kina so na shirya dake to ki girmama shi kuma ki san irin maganar da zaki dinga fad'a a kansa.


Cikin shashshe'kar kuka ta ce." Kayi hakuri zan kiyaye insha Allah, yanzu kwana nawa za kayi?"

Ya ce."Sati biyu zanyi." a sanyaye ta ce." To Allah ya kiyaye hanya ya bada abinda aka je nema."

Ya amsa da amen kafin ya d'ora da fadin." Akwai komai na bukata, idan wani abu ya 'kare to kiyi wa Sule magana wanda ya kawo ki nan, abokina ne zai yi miki komai kafin na dawo"

Ta ce." To shikkenan.'' hanyar fita ya nufa, sai ta mi'ke domin yi masa rakiya ya dakatar da ita da fadin." Koma ki zauna bana bukata."

Ta koma ta zauna tana kallo ya bud'e kofa ya fita tayi saurin zuwa ta bud'e labule tana le'kansa, juyo wa yayi suka had'a ido, sai tayi saurin sauke labulan gabanta na cigaba bugawa.


Kamar yanda ya sanar mata da cewa akwai komai na bu'kata hakane. koda ta duba kicin din komai da komai da akwai, sai ta kunna karamin gas din da ta gani a ajiye. ta d'ora ruwan shayi, sannan ta feraye dankalin hausa ta soya dai-dai cikinta, a kicin d'in ta had'a shayin ta zauna tana sha tare da had'awa da dankalin da ta soya.

Tunani ne yayi mata yawa, gabad'aya ta rasa a ina zata ajiye wannan al'amari! ashe Baban-baba mayaudari ne ba ta sani ba? ita dai har ga Allah ta ke k'aunarsa take kuma yi masa kallon mutum mai mutunci da amana, ashe kallon kitse takewa rogo, tun ba aje ko'ina ba ya fara gwada mata wasu dabi'u marasa kyau! hawaye ta share! tana tunanin Baba Asabe, watakila dama abinda take ta guje mata kenan shiyasa hankalinta bai kwanta da al'amarin ba, tabbas duk abinda ya fad'a akan mahaifinta gaskiya ne, beyi masa sharri ba, domin ita kanta ta san ba suyi sa'ar uba ba, sai yanzu take sake gazgata maganarsa, domin duk uban arziki mai kishin 'ya'yansa ba zai dauki aure ya baiwa irinsu Baban-baba wad'anda basu da asali ma'ana ba a san daga inda suke ba.

Sosai ta ci kuka ta koshi a kicin din, ta ajiye al'amarin a matsayin kaddararta, domin a yanzu duk abinda za ta fito ta fad'a a banza babu wanda zai saurare ta.


Wanka tayi ta shirya cikin atamfah riga da siket daga cikin kayan da ya kawo mata jiya, tasa hijabi a jikinta ta kama hanyar fita, tana so ne ta je ta gaisa da masu gidan kamar yanda ya umarce ta kafin ya tafi.


Sai da tayi tafiya sosai sannan ta fito harabar gidan, nan taga mutane rukuni-rukuni a wata rumfa yawanci maza ne matan basu da yawa, suna zazzaune, daga can bakin gate kuma ma'aikata ne masu tsaro sun kai bakwai harda masu bindigu a hannu.

Da sauri ta d'auke kanta. tana jin fad'uwar gaba, lallai duk yadda akayi wani abu ne zai faru a gurin, da alamar suna jiran fitowar maigidan ne.

Wata hanya ta bi duk da cewa bata san ina za ta shiga ba kawai dai tayi hasashen nan ne hanyar da zata shiga cikin gidan.

Wani lafiyayyan k'amshin turare ya daki hancinta. da sauri ta d'ago kanta tana kallon hanyar lokacin da suka fito tare da escorts dinshi guda biyu. ido suka had'a da saurin gaske tayi kasa da kanta jikinta yayi bala'in mutuwa! "Wannan ai shahararran attajirin nan ne da ake nuna fuskarsa a tibi." sake kallonsa tayi a karo na biyu cikakken mutum kamili mai halin dattako! yana sanye da farar shadda kal dinkin tazarce da jar dara ya nad'a farin rawani a saman hular. as'usul kamar koda yaushe idonsa sakaye da farin gilashi, yayi kyau sosai ba'a magana domin gabad'aya shekarunsa sun 'buya sakamakon gyaran fuskar da akayi masa wanda ya sake k'ayata fuskarsa, gemu kad'an ya bari wanda ya kwanta luf da furfura kad'an-kad'an.


Duk sai ta dabarbace! domin wani irin kwarjini yayi mata, tun kafin ya k'araso gurin da take ta zube 'kasa tana gaida shi da yanayin maganarta.

Bai amsa ba sai dai ya yi mata alama da hannunsa ma'ana ta tashi, kasa mi'kewa tayi kanta yana 'kasa tana kallon kyakykyawar kafarsa cikin ba'kin takalmi maigidan yatsa.

Ganin ta kasa tashi yasa ya wuce ya bar ta a gurin, yaransa suka rufa masa baya.

Tashi tayi tana buge jikinta zaninta duk ya kwashi ciyayi! a sanyaye ta juya tana kallon bayansu har suka 'kurewa ganinta, ta sauke ajiyar zuciya mai zafin gaske.

A hankali ta tura kofar falon wacce ta kasance ta gilas. sallama tayi a nutse da yanayin maganarta.

Hajiya Saude tayi saurin kallon bakin k'ofar tare da amsa sallamar. kallon rashin sani take mata, ita kuma duk sai ta daburce! ganin kallon da matar take mata.

A sanyaye ta isa har gurin da take ta zube 'kasa tana gaishe ta,

Cikin wani irin yanayi ta amsa gaisuwar tana mamakin daga ina yarinyar take, domin ita duk a tunaninta irin nakasassun da suke zuwa gidan neman taimako ne, da jin yanayin maganarta ta kurame ba sosai take fita ba.

Ta sauke ajiyar zuciya cike da d'an tausayin yarinyar a tare da ita ta ce." Ai yanzu maigidan ya fita idan taimako ki ka zo nema yana waje can zaki tsaya."

Ganin tayi shuru ba ta amsa ba, yasa ta bud'e muryarta ta sake maimaita maganarta .

Cikin jin nauyi ta ce." Sunana Shahida ni ce matar Baban-baba."

Jim tayi kafin ta ce." Ayyo! amaryar Sule ce ashe. sai tasa dariya da fad'in ai jiya nan yake sheda min cewa ya k'ara aure har maigidan ya bashi gurin zama a cikin gidanan Allah ya sanya alheri ai mu nan da Sule muke kiransa."

Murmushi tayi ba tace komai ba, sai dai cikin zuciyarta take ta auna maganganun matar ashe dama sunansa Sule na gaskiya.

Hajiyan ta cigaba da cewa." Ai Sule mutumin kirki ne sosai ki ri'ke shi da kyau sosai! kuma ki zauna da kishiyarki lafiya."

Gabanta ya fad'i jin maganar kishiya, ta dinga kallonta lokacin da take jaddada mata nagarta da kyawun halinsa, sai ta ji wasu zafafan! hawaye suna nema su kufce mata.

Da k'yar! ta iya danne damuwarta, ta ce." Hajiya ko da akwai wani abu da zanyi miki?"

Girgiza kanta tayi ta ce." A'a babu komai, sai dai ki zauna ki d'ebe min kewa ai na ji dad'in zuwanki gidan nan saboda zaman kad'aici yana damuna, Shukura kuma ba gwanar zaman falo ba kullum tana daki da waya a hannu."

Sunkuyar da kanta tayi tana nazarin maganganunta, to shin maigidan bashi da aure ne? ko kuma ba a gidan yake zaune ba? bata da mai bata amsa sai kawai tayi shuru, tare da tsirawa tv ido kallon kawai take amma ba sosai take jin abinda ake fad'a ba.

Cikin riga da wando na bacci ta fito daga d'akinta. ganinta a zaune yasa tayi turus! tana kallonta babu annuri a fuskarta ta kalleta da fadin." Hajiya wannan wacece kuma?" ta fada tana nuna ta da yatsa.

Tana shirin bata amsa ya shigo, duk sai su kayi shiru suna kallonsa, a nutse ya zauna kan kujera yana kallon Shukuran dake tsaya da alamun rashin gaskiya a tattare da ita.

"Kin yi sallah?" tambayar da ya yi mata kenan.

Sai ta hau diri-diri kafin ta ce." Daddy bani da tsarki ai."

Shuru yayi be ce komai ba, da shagwaba ta ce" Daddy don Allah ka bari na je gidan bikin nan, kamar hakan bai dace ba tunda Aunty Samira 'kanwar mommy ce kuma kai ma 'kanwarka ce ka taimaka Daddy don Allah." ta 'karasa maganar tana karyar da kai.

Shuru yayi bai ce uffan ba, ta kalleta da fadin." Hajiya kisa baki don Allah"

Kallonsa tayi da fad'in.'' Alhaji Habu ina nema mata alfarma." Yanda ta fad'i maganar cikin 'kaskantar da kai ya bashi dariya!

Ya ce" Na amince amma ba don halinta ba, kuma ban yarda da kwana ba, aje a dawo."

Tsalle ta buga da fad'in." Daddy na gode Allah ya 'kara girma."


Duk abinda suke tana takure a gurin tana kallonsu, sai dai ba sosai take jin abinda suke tattaunawa ba. ita gabad'aya zaman sa a gurin shi ya 'kara firgitata! ta kasa gane wane yanayi take ciki, haka kawai mutumin yake cika mata ido.

Hajiya ta nuna ta da yatsa da fadin." Yallabai wannan ita ce amaryar Sule fa, wallahi da farko na dauka irin masu zuwa neman taimako ne, sai da ta gabatar min da kanta tukkuna na tuna amma ga dukkan alamu tana da matsalar rashin ji kurma ce"

Kallon da yake mata ne yasa duk ta tsargu! ta kasa 'kwakwkwaran motsi.

A hankali ya kalli Hajiyan da fadin." Ya sunanta?"

"Shahida sunanta, ai na ce na samu abokiyar hira duk da cewa ba ta ji sosai hakan bai zai hana ta d'ebe min kewa ba."


Ya ce." 'Kwarai kuwa nima wannan ne dalilin da yasa na bashi guri a gidan nan, na ce ya zauna saboda ki samu walwala.

Ta ce." Maganar auranka dai shuru Alhaji kullum sai kace kana kan hanya.'' Shukura da sauri ta ce." Hajiya ai daddy ba sabon aure zai yi ba, Mommyna zai dawo da ita.''

Wani irin kallo yayi mata kafin ya mi'ke ba tare da ya ce musu komai ba ya haura samansa.

Hajiya ta ce." Shukura mahaifinki ya tsani ayi masa maganar Fatima mutukar kina so ki ga b'acin ransa to ki ambaci sunanta, wannan k'iyayyar tayi yawa."

A sanyaye ta ce."Wai Hajiya me ya faru ne? na lura daddy ya tsane ta sosai kuma yana da ri'ko! kome tayi masa ai sai yayi hakuri tunda na shiga tsakani, sannan da dangantaka a tsakaninsu."

Ta ce." Shukura labarin yana da tsayi sosai! amma babu shakka Fatima ta yi abubuwa da yawa marasa kyau a can baya! wanda ba su da amfani, saboda haka tayar da al'amarin yana nufin 'bacin ran mu gabad'aya.

A sanyaye ta ce." Shikkenan to Allah ya kyauta." ta amsa da "Ameen ya rabbi."

Shahida na zaune tana satar kallonsu, yanayin fuskokinsu da yanda suke magana a hankali cikin rashin walwala yasa ta gane cewa lallai abinda suke tattaunawa ba mai dad'i bane.

****
To kwana d'aya biyu har ta saba! kullum idan ta tashi za ta gyara gurinta, kafin tayi wanka ta shirya jikinta tsaf! sai ta karya kummalo ta nufi cikin gidan a can take yini tare da hajiya, idan lokacin shiga kicin yayi ta je ta taimakawa masu aiki, sosai Hajiya take jin dadin zama da ita, wannan dalilin yasa ta umarce ta cewa duk abinda take bukata kada tayi 'kwauron baki ta tambaye ta, anan take cin abinci rana da dare. sai tayi sallar isha'i take tafiya gurinta, sai dai abinda yake damunta yanda Shukura ke 'kyamarta! hantara! kyara! wataran harda zagi! kuma kullum ita ke zuwa ta gyara mata d'akinta ta wanke mata bandaki da sauransu, amma bata ta'ba godiya ba, wannan abu yana damunta sosai!


Kasancewar ta samu caji a wayarta yasa ta tura masa text na gaisuwa da kalaman soyayya! tana jiran amsarsa, shuru bai bata amsa ba, jikinta ya 'kara yin sanyi gabad'aya bata da wani kuzari, yau kwanansa tara da tafiya babu wata magana da ta ta'ba shiga tsakaninsu ta hanyar sadarwa.


Cikin kwana goma da tayi a gidan ta sauya fatarta tayi luff! tayi kyau daidai gwargwado kuruciyarta ta sake bayyana, Shahida bata da wani kyau na ku zo a gani, sai dai tana da dirin jiki mai kyau akwai cikar kirji tare da kyakykyawan k'ugu ko'ina a jikinta a cike yake bata da rama kuma tana tsakatsaki ita ba doguwa ba sannan ba gajeriya ba, tana da yawan gashi cikkake irin na asalin hausawa, bakikirin! haka take d'aure shi da ribbon ya taru sosai a kanta, tana yanayi da Nafisa Abdullahi jarumar finafinan hausa, sai dai har taso tafi Nafisa cika da kwarjini. ba ta da makusa bayan matsalar kunne (rashin ji) da Allah ya hallice ta.


Yau kwana goma sha biyu kenan da tafiyarsa, tana lissafi saura kwana biyu ya dawo,sai murna da farin ciki take, domin ita kad'ai ta san irin halin da take shiga a duk lokacin da za tayi bacci! tsoro take ji ita kad'ai a wannan gurin, koda wani abu ba zai shiga tsakaninsu ba, idan tana jin motsinsa a gidan rahama ne.


Shuru lokacin da ta shiga falon, sai sallama take babu wanda ya amsa, cikin zuciyarta take tunanin ko Hajiyan na d'aki bata fito ba, sai ta yanke shawarar shiga dakin. a lokacin ne yake saukowa daga sama cikin pyjamas (kayan bacci) irin masu falmaran amma babu ta ciki kirjinsa wanda ya ke cike da kwantaccen gashi 'baki duk a waje!

Da saurin gaske ta kawar da kanta! tana jin wani irin fad'uwar gaba, 'kafafunta ne suka shiga kyarma! ta zube a k'asa tun kafin ya 'karaso gurin da take.

"Alhaji Ina kwana?" tafad'a cikin sar'kewar murya.

Bai amsa ba da hannu yayi mata alamar ta tashi.

Tashi tayi amma ta gagara kallonsa, gabad'aya ma tsigar jikinta ce take tashi ganinsa haka.

Gurin cin abinci ya nufa ya zauna domin karya kummalo.

Ita kuma jiki a mace ta kama hanyar fita, ya tsirawa bayanta ido, duk da cewa a cikin hijabi take hakan bai hana shi ganin 'kirar jikinta ba, ya sauke ajiyar zuciya mai zafi! yana danne abinda ke taso masa. muryarsa ya bud'e sosai kafin ya kira sunanta.

Juyowa tayi tana kallonsa, yayi mata alama da hannu ta je gurinsa.

Gabanta ya tsananta da fad'uwa, shin idan ta je me za tayi masa? abinda take rayawa kenan a zuciyarta. amma tuno gargadin mijinta yasa a sanyaye ta nufi gurin nasa kamar yanda ya umarce ta.
*Littafi na daya yana daf da k'arewa ku yi hanzari ku biya kudin littafin na biyu domin cigaba da karanta labarin.>p Yanzu ne fa za a fara wasan. ina fata za ku yi mini kara gurin sayan littafi na biyu. Allah ya yassare.*

*Normal group posting sau daya a rana #500... Vip group posting sau biyu a rana 1k. 0502382124...Binta umar gtbank. idan kati za a turo sai ayi mini mgn ta WhatsApp 07084653262.. Mutan nan Nijar dala dari Vip jakka daya katin airtel za ku tura mini ta WhatsApp*


*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE MANAZARTA WRITES ASSO..
_____

*Ga hanyar da za a biya kudin littafin....Normal group #500 posting sau daya a rana, Vip group 1k posting sau biyu a rana. account number.... 0542382124...Binta umar gtbank. idan kati za a tura sai ayi mini magana ta WhatsApp da wannan lambar.07084653262....Mutanan Nijar za ku tura dala dari. Vip jakka daya, za a turo mini ta WhatsApp. Allah ya yassare.*

55&56
A nutse ta d'an tsaya a jikin daya daga cikin kujerun cin abincin, amma bata yarda ta kalleshi ba, kanta yana 'kasa, sai dai a jikinta ta ji yana kallonta. gabanta ya dinga fad'uwa tana kiran innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! 'kadaicewarsu, a falon su biyu yana nufin abubuwa da yawa, saboda haka sai tayi ta maza! ta d'ago kanta ilai kuwa sai ta ritsa shi ya zuba mata ido wanda har ya fara sanja kala, ya 'kan'kance ya kuma yi ja! ta sake shiga rud'ani mara misaltuwa! cikin yanayin maganarta ta ce." Yalla'bai ko kana bukatar wani abu ne?"

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya nuna mata tarin abincin dake shirye a teburin alama yayi mata wai ta had'a masa abin kari.

Cikin rashin kuzari ta fara abinda ya umarce ta, gurin tsiyaya shayi (tea) ya zubo mata a hannu saboda gabad'aya ta kasa nutsuwa sakamakon kallon kurillan da yake mata.

Yarfe hannun tayi, tana d'an ya mutse fuska! babu zato babu tsammami ta ji ya kama hannun yana dubawa! da saurin gaske ta k'wace hannunta tana d'an harararsa, gefe guda kuma k'afafunta sai rawa suke domin ba 'karamin tsorata tayi da abinda yayi ba.

"Sannu.'' a hankali ya furta duk da ya san ba lallai ne ta ji ba.

Ba tare da tace masa komai ba, ta juya da sauri ta bar gurin. kallo ya bita dashi yana ayyana abubuwa da yawa a tare da ita.


Cikin mutuwar jiki da faduwar gaba ta isa sashenta, ta zube kan kujera tare da dafe goshinta.

Sam 'kunar dake hannunta bata dameta ba akan abinda ya faru a tsakaninsu, shin wai mai yake shirin faruwa ne? gabad'aya mutumin bai kwanta mata a rai ba, duba da irin mugun kallon 'kurrila da yake mata, bayan haka kuma menene hujjarsa na ri'ke mata hannu a matsayinsa na babba mai hankali ai ya san hakan ba daidai bane, tunda yafi kowa sanin matsayinta a gidan, matar aure ce kuma matar yaronsa.

Gaskiya al'amarin ya sanya ta cikin rud'ani haka ta yini tana tunane-tunane!

Wajajen tara na dare text ya shigo wayarta, da yake tana samun chaji a can cikin gidan, tunda gurinta babu wuta haka take zama cikin duhu sai hasken wannan fitilar da ya kawo mata ranar da suka zo gidan.

Farin ciki ya cika mata zuciya ganin mijin nata ne ya turo mata sa'kon, cikin rawar hannu ta bud'e domin karantawa!

Hawaye ne suke 'kwace mata ganin abinda yake rubuce.

_"Ba zan dawo jibi ba, saboda maigidana ya umarce ni na zauna tsayin sati uku na kula masa da wasu harkokinsa ."_

Tana kuka ta rubuta masa amsa kamar haka.

_Don Allah ka dawo wallahi ina cikin matsala da kewarka akwai abubuwan da suke shirin faruwa."_


Ya dawo

Please Login or Register in order to submit comment