Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

breakfast dan idan ya farka zai tashi ne da yunwa ke kuma sai kiyi surprising d'insa da abincin.

Breakfast mai rai da lafia ta had'o musu tayi arranging akan table taje tayi wanka ta zauna tana cancare k'walliya agaban mirror taji yayi hugging d'in ta ta baya, ya sunkuyar da kansa yadda zai zama visible via the mirror ya sake mata k'yakkyawan smile ita ma smile din ta masa sending back, yace "mata ta kyakkyawa ce shiya sa duk shigar da kika yi tana karb'an ki tana miki kyau", ita kuma tace " kodai sai idan nayi kwalliyar nake kyau ba", girgiza kansa yayi ya d'an b'ata rai "ko kad'an kada ki kara fadan hakan, mata ta tana da kyau ba kwalliyar ce take da kyau ba", " toh meye na b'ata rai nima da wasa nake ya zanyi downgrading kaina nasan inada kyau, amma kasan me", yace "uhumum" duk wani abu me kyau da kagani a tare dani toh gadan sa nayi kuma kasan a ina nagada?" "A'a sai kin fad'a". All these maganar da suke yi through mirror suke kallon juna shi kuma yana jingine a bayan ta, ta juyo ta mai da kallon ta garesa ta d'aura hannu a k'irjin sa "komai gadan sa nayi a wajen ka", murmishi yayi "dama ana gadan wani wanda ba jini bane?" "Oh baka sani ba, toh mata tana gadan mijinta ta kyau da sauran abubuwa". Jan ta yayi ya manne jikin su sannan yace " thank you for the love you make me last night, I really enjoyed it Allah ya miki albarka". Kunya taji ta sauke kanta tace "oya go and take your bath, your breakfast is ready", " toh ai sai na shirya mata ta kafin naje ni koh", a sannan ta tuna towel ne ajikin ta babu kaya, wardrobe d'in ta bude ya ciro mata wani rubber fitted gown ya mika mata "wannan nake so kisa ka", " wannan kuma ya Suleiman ya matse ni sosai fa bana saka shi", " ungo toh yau zaki saka sa dan ni shi nake so, ko sai na saka miki da kaina", "ayya kayi hak'uri ya Su...", ji tayi har ya kamota yana kokarin saka mata dan dolen ta tayi shiru ya saka mata. "Haba kiga yadda kyanki ya k'ara fito wa amma kike mun bakin cikin kar na gani, matso gaban mirror mana ki gani". Janyo ta yayi wajen kasa d'ago kanta tayi su had'a ido, "oh! wai kunya kike ji toh bari nashige wanka ta ko zaki zo kimin ne?" Ya lakaci kumatun ta ya shige toilet din yana mata dariya dan yasan tayi fushi dashi kenan.

Ta kalli kanta da kyau ta mirror, ta ga yadda rigar ta fito da surar jikin ta kaf, ga wuyar rigar ya sauko sosai dan har rabin k'irjin ta duk suna waje. Tsaki taja sannan tace "Allah ya Suleiman ina maka ganin babu abunda ka iya baka waye ba ashe dai kai ba haka bane dan ko wani dan iskan ma sai ya baka waje, a suna wai kai ustaz hmm" ta fita taje falo.
Da ya fito yana expecting yaga ta d'auko masa kayan da zai saka sai yaga ma bata d'akin. Fita yayi yaje d'akin sa ya shirya ya fito ya zauna tayi serving d'insa ita ma zata zuba nata a wani plate yace "a'a me za kiyi haka?" "Nawa zan zuba", " no plate d'aya za muci da ke dan Annabi yace mutum biyu suci abinci atare yafi wanda zai ci shi kadai albarka, kuma idan mutum uku ne toh yafi biyu, haka zalika cin abinci mutum hudu yafi uku albarka dan haka ki taso muci tare", tace "toh Hubby na bari na k'aro mana dan nasan kafiye ci dayawa wannan bazai ishe mu ba", ta kashe masa ido sai taga duk hankalin sa kuma ya koma kan k'irjin ta da suke girgizuwa wajen zuba abincin da take. Sai ta tuno babu ruwa a wajen. "Oh! ina zuwa ban d'auko mana ruwa a fridge ba", ta tashi dan ta d'auko, yanzu kuma hankalin nasa sai ya koma kan tudun mazaunin ta yadda yake juya wa gefe da gefe ahankali yace " Allah na gode maka da baiwar nan, yau ni da Sadia muke cikin wannan irin salon so haka, lallai mahakurci mawadaci ne".
Ranan through out tare suka wuni manne a jikin junan su suna shan soyayyar su har dare yayi.
Suleiman ya shigo d'akin ta daga shi sai boxer ya kwanta akan gadon ita da take zauna tace "wai ya Suleiman kai kullum sai da boxer kake kwanciya ne?" Saida ya jawo tafad'o kansa sannan ya ansa ta "idan na kwanta da riga ajiki na yana damu na ne kuma tun ina karami na saba kwanciya da boxer kad'ai", ya kwantar da ita a k'irjin sa, tayi dariya tace "toh ai idan kwanciya da riga zai dame ka inaga boxer'n ma haka ne ko?" Shima yayi dariya yana ce "Haka ne fa dan babu yadda na iya ne kinsan bazaiyu na kwanta hakan ba. Oh! Ko so kike na cire sa na kwanta haka?" "A'a ni bance ba", " kin fad'a mana, nasan ko zaki fi jin dad'in ki kwanta haka ajikin nawa?" "uhn uhn", "bari na cire", hannun sa yakai da wasa zai sauke wandon ta runtse idanun ta da karfi zata tashi ya kankame ta. " ina zaki je? Da wasa nake miki fa matsoraciya kawai". Aranta tace kwantar dani da kayi a bare skin d'in k'irjin ka ma ya nake ji balle kuma ka tub'e gaba d'aya.

*_Follow me on Whattpad @ fkahmad for comments and also your votes cos they really mean a lot._*


[8/4, 10:46 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana Gani💝
Written by F k Ahmad
Pure Moment Of Life Writer's
_we don't just entertain and educate, we touch the heart of readers._

Dedicated to each and every Fan of Banaji Bana Gani, P.M.L writer's and my whattpad readers. Thank you so much for the love, Allah ya had'a mu a next littafi na.
_END_
63 - 65

Washe gari, Suleiman ya shirya zuwa aiki Sadia ta masa rakiya har zuwa wajen motar sa da suit case nasa a hannun ta bayan ya shiga ya zauna ya miko mata hannu zai karb'i jakar sa sai tayi dragging d'insa baya kuma da fushin ta, ya d'ago ya kalle ta yace "ha'a meya faru kuma?" Ta turo baki tana "Ba kai bane", " ni kuma me nayi", "nasan idan kafita a gidan nan baka zuwa sai dare shikenan nayi ta wuni ni kad'ai kullum", yadda tayi maganar da shagob'a yasa abun ya basa dariya amma sai ya sassau ta dariyar, " oh har ma dariya nake baka ko, shi kenan ga jakar ka ka tafi dama na saba zaman kad'ai ci ai", ta ajiye masa a cinyar sa zata bar wajen ya kamo hannun ta ya zaunar da ita a cinyar sa yana "kiyi hak'uri mata ta, ai ke kika bani dariyan, toh amma dama zama na awaje har zuwa daren yana damun ki ne?" "Yana damu na mana", "shine baki tab'a fad'a mun ba", " ai yanzu na gayama sai ka daina", "toh in nazo gidan da wuri me zaki ban?" Ta marairai ce kanta tace "Ya Suleiman kawai so nake ina ganin ka kusa dani mana kuma zan dafa maka abu mai dad'i sannan ai ko babu komai zanji dad'i idan nasa wannan handsome face naka a gaba nayi ta kallo". Kallon ta yayi da kyau sannan yace "yanzu nasan mata ta tana sona tunda har kika damu dani na miki alkawarin daga yau bazan sake zama dare ba idan nafita" tace "tnk u my Hubby", " you just deserve it mata ta" sai yayi pecking goshin ta. "Ya Suleiman idan naji ka ambaci matar ka sai inji kana hura mini kai, dan nasan duk duniya ni kad'ai ce", "OK yanzu ki shiga ciki ni zan tafi kar nayi late", "OK Allah ya kiyaye ka ya dawo mun da kai lafia", har cikin ransa yaji dad'in addu'ar dan yau ne farkon addu'an da ta masa yace "Ameen dear, me kike so na ka kawo miki?" Washe hakora tayi "ice cream nake so, bye" "ohk bye" yaja motar ya tafi.

Wayan ta ne yake ringing da ta duba Aisha ce da murna ta d'aga "k'awa ta, wlhy kina raina ban samu na k'ira ki ba har kika riga ni", " ai baki da tace wa mara kirki kawai, ace kin koma gidan mijin ki amma baza ki fad'a mana mu taya ki murna ba sai Zara da suka had'u da Ruky a kasuwa take gaya mata" "ayya yi hak'uri Aisha ba haka bane yau fa kwana biyu kacal da nakomo, kinsan ya akayi Abba na ya k'yale ni na koma ne? Ai da labari kaca kaca amma kar ki damu zan zo miki a weekend muyi gist d'in", " hmm toh sai naganki", "insha Allah zaki ganni tare da Ruky ma zamu je dan ta kira ni jiya ita ma taci mun mutun ci" "yanzu kinyi hankali ko har yanzu kina ba ya Suleiman though time", " ah na daina mana, da d'inma dan akan ASB nake hakan amma yanzu ya Suleiman ne agaba na *banaji bana gani* akan sa zan iya yin komai", dariya Aisha ta k'yalk'yale da "iyee su Sadie manya, kai amma kin iya soyayya fa", "lalala ai bakisan wani abu ba duk iya wata ina bayan ya Suleiman ke kinga yadda ya iya soyayya kuwa ashe da nice bana basa chance na hakan, yanzu ma da zai fita na masa complain ya mun alkawarin zuwa gida early kullum, inaga zan bawa Ruky advice na auren ustazu dan gaskiya akwai dad'i sun iya soyyaya" "hahaha lallai kam abu yayi kyau, toh Allah bada zaman lafia bari naje na ci gaba da aiki na" "toh ki gaida Mustapha da unborn babyn mu".

Bayan sati uku.
Hadari ne ya had'o da alama damuna ta fara kenan a wannan lokacin. Da safe ne Sadie tayi wankin towels na kitchen bayan tagama aiki dasu ta fita waje ta shanya. After kaman 30 minutes ruwa ya sauko kuma da karfin sa, suna zaune da Suleiman ta tashi da sauri zata fita, ya ke tambayan ta "ina zaki je haka da sauri", " ina zuwa yanzu", shanyan nata taje kwashe wa amma saida ta jike sharaf, da ta dawo ya ganta haka karkarwa take sosai ya tazo yazo kusa da ita "kardai cikin ruwan kika fita?" Tace "eh, na d'auko towels da na shanya ne". Rigar jikin ta ba mai nauyi bane shi yasa ta manne mata ajiki kana iya ganin duk halittan ta ta ciki dan ko inner wear bata sa ba. D'an dariya Suleiman yayi yace kinga yadda kika yi kyau kuwa?" Ita kam har yanzun bata dai na kar kar wan ba, "ya Suleiman sanyi nake ji", ya d'auko mata towel ta tub'e rigar kuma ya had'o mata tea mai zafi tasha.
Zuwa yamma jikin ta yayi zafi sosai zazzab'i take ji, ya Suleiman yayi rushing d'in ta asibiti aka tabbatar musu da ciki ne da ita na wata uku sannan aka basu magunguna, murna a wajen su da iyayen su kam babu magana. Suleiman ya sa Umma ta nemo wa Sadia y'ar aiki dan haka babu abunda yake barin ta tayi agidan, idan yana gida ma shiya ke mata.
Bayan wata shida, Sadia ta haifi bouncing baby girl wacce taci sunan margayiya Maryam, Sadie ta mata ikirari da Farhan.

A year later
Farhan na kan gadon ta, daga bacci ta tashi tafara kuka ya Suleiman yayi saurin d'au kan ta ya fara wasa da ita, Sadiya kuma ta gama shirin ta dan za su je Super market, Suleiman yace "ina madarar ta ki had'o mata tasha", "madarar ta ya k'are jiya, yanzu ma shine main abunda nake son siya" "ok kiyi sauri mu tafi", ta d'au ko gyallen ta a wardrobe suka fita.

Sun gama shopping d'insu ya Suleiman yaje settling bill d'in, Sadia da take rike da Farhan tana jiran sa sai taji wasu maza biyu a bayan su suna hira tana sauraran su saboda muryan d'ayan su seems familiar " Abokina wai yaushe za kayi aure ne?" Dariya yayi yace "kai an gayama shi auren sauki ne dashi ko da yake yanzu ma abunda ya kawo ni garin nan kenan", " haba! Duk matan da suke Lagos kabar su ka gangaro Maiduguri?" "Ai da biyu nazo nan, kaf y'an matan da nake sharholi dasu sai da na tashi aure yanzu duk suka gudu sunki aure na shine nazo neman wata budurwata na da dan nasan ita kam tana mutuwar so na nasan zata aure ni". "Tab, ina zaka same ta yanzu? Kuma aganin ka zata aure ka d'in ne?" "Sosai ma kuwa, kai! Dan baka San yadda Sadia take so na bane". Sadia da tagama sanin da ita yake ta tara hawaye ta juwo immediately suka had'a ido. Ahmad yayi exclaiming "Sadia! Dama kina nan kusa dani", " ya juya ya nawa abokin nasa magana "kaga ikon Allah ko, itace yarinyar da nake fad'a maka ai", sai kuma ya juya kanta " Baby I hope you ain't upset with me dan yanzu ma ke nazo nema, zan aure ki Sadia". Wani wawan mari ta sake masa da yatsun ta biyar tas kake ji, kowa awajen sai da ya juya dan ganin meke faruwa nan ne Suleiman ma ya juya kallon su, sauri yayi ya karaso dan ya ga alamar fitinar harda matar sa aciki. Sadia ta fara balbale sa da maganganu "idan irin wannan tunanin kake a kaina toh kasani nariga da na manta da kai arayuwa ta da jima wa kuma wannan y'ar da kake kallo y'ata ce sannan ga mijina masoyi na wanda nake al fahari dashi", shi sai yanzu ne ma hankalin sa ya kai ga kallon Farhan da ke hannun ta. Taci gaba da maganar " Banza macuci mayaudari azzalimi, na gode wa Allah da ya hanani auren ka". Ta juya kan ya Suleiman ta kamo hannun sa tayi mar smiling tace "sweetheart mu tafi", ya Suleiman just can't take his eyes off matar sa, yaji dad'in the way she is proud of him suka taka zuwa motar su.
Sai daga baya ne Suleiman yake tambayar ta akan wane ne shi take gaya masa ASB ne kuma ta basa labarin komai tun lokacin da suke tare har rabuwan su da kuma zancan da taji sukeyi da abokin sa a wajen.

Three weeks later, su Sadiya sun gama makaranta yau ne Attestation d'insu.
Tayi shirin ta cikin white Arabian gown tayi rolling d'inta in red, haka baby Farhan ma ta mata dressing white top da red skirt, head band d'in ta ma red da farin cover shoe akafarta. Ta d'auko graduation gown dinta ta rike a hannu. Suleiman ne ya shigo shima cikin shirin sa in white trousers da red suit akai. "Wow! Abu Farhan kaga yadda kayi kyau kuwa?" "Haka Ummu Farhan ma zata haska kowa wajen wannan taron". Murmishi tayi " OK what's the surprise gift you've got me? Tun jiya kake cewa sai za mu fita zaka ban". Hannu ya sa acikin inner aljihun sa na suit ya ciro wani k'aramin box ya bud'e, zobe ya fitar mai harafin S&S"wow!" Kad'ai ta iya furta wa dan ya bata mamaki matuka, "you like it?" Bakinta a bud'e suke tayi saurin fad'an "oh yes, my Hubby i love it not even like", murmishi yayi ya kama right finger'n ta d'aya ya saka mata tace "Beautiful, S&S and what does it mean?" "SADIYA & SULEIMAN". Hug ta kai masa tace "Thank you sweetheart, i love you so very much, Allah ya k'ara maka bud'i". "Ok mu tafi kada muyi late almost 10 d'in ma yayi", ya juya ya d'au ki Farhan ya ciro waya ya musu selfie, Sadiya sai k'arar snapping d'in da taji ta juyo "oh hoto kuke banda ni, nima sai nashiga", sauke wayan sa yayi yace " baza muyi da ke ba dan gaskia memory'n wayar nan ta cika da pic's d'inki", "ah toh ko wani outfit ai da hoton da za'a masa koh", " a'a gaskiya banda yanzu dan waya na zaiyi hooking", "haka kace? Wato dan sabagen muni na ne zai saka wayar ka hooking ko? Ya maka kyau", ta had'e rai da gasken ta tayi fushi ta juya masa baya. "O'o ba haka na fad'a ba na isa nace mata ta mummuna ce, ko naki d'au kan ta a hoto ai da wasa nake", ya kai hannun sa zai juyar da ita ya musu hoton kawai k'walla yaga sun ciko mata idanu. " Haba Sadia me ya same ki kuma?" Baki ta turo "ba kai bane kak'i d'auka ta a hoton", " yanzu dan wannan shine zaki min kuka zo mu d'auka toh, am sorry". Mak'e kafad'a tayi, kunnan sa ya kama da d'ayan hannun sa ya k'ara ce da ita "kiyi hak'uri mata ta, ko sai naje har kasa ne?" Har yanzu bata kula sa ba d'in, ajiye Farhan yayi kan gado ya sake kama kunnen zai durkusa sannan ta juyo a rikice tayi maganar "a'a ya Suleiman me zakayi?" "Durkusa wa zanyi na bawa princess ina hak'uri mana", nan ne tayi dariya ta kai masa kiss a forehead, " ni ma da wasa nake maka ya zansa miji na yin hakan?" "Ai kece gaba dani dole na sauke kai", duka kad'an ta kai masa a k'irji tayi hugging d'insa tare da cewa " World's best husband". Idon sa ne yaci karo da wall clock yace shikenan ai mun gama yin late d'in, oya mu tafi", ya d'au Farhan ya mika mata.
Suna isa wajen taga kaf family'n ta suna zaune ne akan kujeru Abba, Mama, Zara, Omar, Sadiq da Asma'u har Ummar Suleiman ma tana wajen. Saban mamaki baki ta sake ta saya kallon su sai kuma ta juya kan Suleiman ta kalle sa yace mata "Surprise!" Tace "you did it?" Ya kad'a mata kai "Wow ya Suleiman, you are way awesome, thank you sweetheart", " everything for you", kamar tayi hugging d'insa take ji but tana kunyar jama'ar wajen. Ruky da Aisha ne suka shigo wajen da gown d'insu ajiki. Ruky tace "ke me kike jira baza ki saka ba kina rike dashi a hannu?" Nan ne tasa ka, Aisha ta tambaye ta ina daughter Farhan?" Ta nuna mata ita "gata can wajen dadyy'n ta, Yusrah fa? (Y'ar Aisha), "ita ma tana wajen uban ta". Wani Photographer ne Suleiman yagani ya masa magana yazo. Yace da kowa ya taso dan family picture za suyi, haka duk dangin nasu suka taso mai hoto yayi arranging d'insu amma saide ya raba wajen tsayuwan Sadie da Suleiman. Atake Suleiman yace " kai wa ya gaya maka ana raba mata da miji?" Ya janyo ta wajen sa. Su Abba da su Umma duk suka fashe da dariya, Ruky tace "wa annan ai love birds ne", Aisha ta juya ta mak'e bakin ta " bakya ganin su Mama ne ko kunya bakya ji". Mai hoto yace cheese, Sadie da Suleiman suka kalli juna da smile a fuskar su sannan suka kai wa Farhan kiss lokaci d'aya kuma hakan sukayi appearing a hoton.
_"AND FOREVER THEY LIVE HAPPIER"_



*_Follow me on whattpad @ fkahmad for your votes and also comments._*
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment