Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dad'i bane da munzu tare", laa kardai kice mun laulayi tafara, "eh mana nad'auka kema hakan zanzo na tarar", ah haba Allah ya sauwake sai kace wata y'ar akuya yaushe ma akayi mun auren", "ke dai rufe bakin ki locaci bayyi bane, kin ga ni ba zama ne ya kawo ni ba tashi ki dauko mun posting letter d'inki inaso naje na mana submitting a TH Kafin rana yayi", toh shine baki fada mun ba kafin kizo koda jiya ne kika kirani ai sai nace mar zan fita yau, " toh ai nima da safen nan nayi shawarar zuwa yau kuma idan nace zanje daku kinsan ku matan auran nan sai ahankali sai kuce baku tambaya ba, shiya sa zan kai mana ni kadai dan ga na Aisha ma na karbo, kinga yau litinin idan nakai mana sai muyi reporting gobe dan zaman gidan nan ya ishe ni", "hmm niko ke, d'an wata biyun nan da nayi har gidan ya fita akai na, bari na dauko miki toh kisha ruwa mana kafin".
Ta dauko mata lettern ta bata, tayi mata rakiya zuwa kofar gate na gidan sukayi sallama. Ruky tace " toh gobe karfe takwas ya same mu awajen" sadia ta ansa mata da "in Allah ya yarda, kigai da gida".

[7/24, 2:49 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana Gani💝
Written by F k Ahmad
43 - 44
Da dare yayi bata shiga d'aki da wuri ba jiran sa take ya dawo ta fada masa zata fara fita clinical posting gobe. Around 8 o'clock ya dawo. Saboda kallon ta da yayi zaune a falon yasa yayi sallama zai shige sai yaji tace "sannu da zuwa" bayyi mamaki ba dan ya dauka tayi tunanin gyara halinta ne yace "yauwa" tana gani yayi wuce wansa daki batayi magana ba sai da ta kusan minti ashirin awajen sannan ta bisa zuwa dakin nasa.
Yana zaune gaban system dinsa yana danne danne ta zauna a bakin gadon kusa dashi kota kanta bayyi ba yaci gaba da aikin sa da taga shirun bayi da amfani yasa ta bude bakinta tace "daman nace gobe zan fara fita clinical posting ne", "okay awani asibitin zakiyi"? a teaching hospital, sati shida kuke yi ko? tace "eh", yaja wata drawer a gefen sa ya ciro bundle na hundred naira guda biyu ya ajiye mata yace "transport money dinki ne ki dauka". Duk maganan da sukeyi tunda ta shigo bai d'aga kai ya kalle ta ba. Godia tayi ta fice masa daga d'akin.
Washe gari da safe suka je suka yi reporting duk a department daya suka fara ita, Ruky da Aisha. Sai bayan azahar suka tashi.
Da suka rabu, sadia gidan su ta wuce, tana zuwa taci karo da asma'u a kofar gida zata fita, da tagan ta baki har kunne tana "ya sadiya oyoyo", sama ta d'aga ta suka shige ciki. Abba na zaune a harabar gidan yana shan iska a karkashin bishiya, ta isosa suka gaisa yayi murnar ganin y'arsa ta shige ciki.
Zara da Sadiq ne suka yo ta kanta da gudu oyoyo yayar mu sai yau, Sadiq yace "muna son zuwa gidan ki amma mama tace sai munyi hutun makaranta". "Ayya nima na kagu nazo na ganku sai yau na..." bata karasa maganar ta ba mama ta fito tana tafi tare da salati "ke kuma me ya kawo ki war haka, yaushe akakai ki gidan naki har kin fara yawo sadiya", "Allah sarki mama nayi kokari ai ban taba fita ba sai yau shima kinga sanadiyan yau nafara zuwa IT ne yasa da natashi shine na biya nan", "au ashe ma ba tare da suleiman din kike ba kina nufin bashi ya kawo ki ba", eh mama ni kadai na dawo, "kince masa zaki zo nan ne ko a'a, hade rai tayi ta kau da kanta tana a'a ni ban fada masa ba. A harzuke mama tace "me kike jira toh yanxu za ki fice mun daga gida ko sai na karya kafan ki", ayya mama ko gaisa wa fa ba muyi ba kike kori...kan ta ankara mama tayi kanta, da gudu ta fice daga falon tayi gun Abba tana ihu. "Maza ki wuce gidan ki nace kar na kara ganin ki cikin gidan nan idan bashi ne ya kawo ki ko da izinin sa kika dawo ba, tun ba'a jima ba kin fara yawo babu izinin mijin ki. Abba ya dakatar da ita "haba A'isha toh ya zaki mata koran Kare yi hakuri ta huta tukun". Abba ni zan tafi gida na tunda mama ko marmarin gani na ba tayi dama kai da kanne na nazo duba wa", yadda take maganar harda shagob'a aciki yaba wa mama dariya. Abba yace "uwata baza'ayi haka ba jeki huta, ki shiga ciki", ta biyo sawun mama ta shiga.
Da ta shigo Zara dariya take mata ita kuma ta harareta ta zauna kusa da Sadiq tace masa "ina Omar ne bangansa ba", abba ya aike sa bai Jima ba, tace "ni yazo shi mugaisa nayi tafiya ta ma. Asma'u tazo ta zauna kan cinyarta tana "ya sadia zan biki", tace mata "ma'u ga mama ki tambaye ta idan ta yadda muje", mama da tana nan zaune itama tace, "babu inda zata, mu a locacin mu haka aka mana ne, ku dai gyaran yanzu sai gyaran Allah o'o.
Sai da tayi la'asar a gidan sannan ta tashi tafiya mama ta ajiye ta tana jaa mata kunne, "sadia kinga ba wai zuwan ki nanne bana so ba nima nayi k'ewan y'ata kawai inason nuna miki abun da ya kamata da wanda bai dace ba, inaso ki nutsu kiyi zaman ki a gidan ki babu yaawon banza, tunda kin fara fita IT sai ki mai da ahankali kada kina sakacin nan. Ki dinga yiwa mijin ki girki akan locaci kada kice ke kinfita kin dawo da gajiyar ki sai kin huta koma ki k'iyi, ki guji duk wani b'acin ransa ki bisa sau da kafa ki guji fushin Allah ki masa duk abunda yake so. Yanzu ga turaren nan ki kai masa injini, Omar na jiran ki awaje kuje ya kaiki". "Toh nagode mama", ki gaishe sa shima yazo shi jiya bana nan naje jana'za ne Abban ku kadai ya samu, "toh mama zaiji".
Tana koma wa gida ta girka musu tuwo duk da kwana kinnan ba tayi dashi dan sai yaci yake zuwa gida wai shi yana fushi da ita. Bai dawo ba sai bayan isha'i. Sannu da zuwa ta masa ya ansata sama sama ya shigewarsa ciki. Abincin sa ta dauko zuwa dakin nasa tare da sakon mamar ta.
Sallama tayi ta shiga. Ya fito daga wanka kenan, ajiye tray din tayi a kan stool sannan ta kai turaren gaban mirror yana kallon ta tace "Mama ce ta baka wannan". Yace da ita "ayya ta dawo ne"? a'a ni natafi, juya wa yayi cikin tashin hankali ya tsaya kallon ta, "a yaushe din kika tafi? Yau ne da nata shi daga asibiti. shi sai yanxu ma ya tuna tace yau zata fara fita lallai ko akwai yawon kullum kenan. "Sadia tun baki fara fitan ba har kin fara tsaya wa awani wajen kan kizo gida"?. Idan zuwa gidan kike so basai ki fada mun zaki ba sai na kai ki da kaina ko during weekend ne ma kije ki wuni. "Toh naji ga abincin ka" tayi ficewar ta ko damuwa batayi ba shiko binta da kallo yayi ya kuma kallon food flask din shi akoshe yake amma bari ya taba koda kadan ne saboda kar ya shiga hakkin ta daya wa na rashin cin girkin ta tunda yau din ita ta kawo masa har daki.

[7/25, 3:12 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana Gani💝
Written by F k Ahmad
Pure Moment Of Life Writer's💝
Firstly, i'll like to dedicate this page to all members of PML and especially Maryam Muktar for making me being here, tnx a lot and my greeting goes to the leader who embraced me to the group though i don't know her name.😊
45 - 46
Babu laifi Sadiya ta d'au nasihar mama na kar ta barsa da yunwa, idan tayi breakfast zata kai masa d'aki haka ma dinner dan tunda take gidan bata tab'a ganin sa yazo da rana ba ko dan cin abinci. Haka suka ci gaba da rayuwan su. Suleiman yaa mata kokari sosai a matsayin sa na cikakken na miji kuma mai mata amma ace baya samun biyan bukatar sa wajen ta, ga sha'awar ta da yake damunsa barin ma da ya d'and'ani zuman ta yanzu fiye da wata kenan fa. Tashi yayi daga kwanciyar da yake zaune yace bari ya gwada zuwa lallamin ta ko zata yarda.
D'akin ta yaje ya samu a bud'e ya shiga. Takardun ta take duba wa, ko irin tasan mutun ya shigo d'innan bata kulasa ba, zama yayi gefen ta ya kamo hannun ta ya had'a da nasa tana kallon sa yace "nazo neman alfarma wurin matata ina fatan zata saura re ni", kau da kanta tayi gefe. Kallon ta yake har cikin ido yana ce mata "Inason matata, inaso na kasan ce da ita a kullum, Sadiya ni na miji ne mai bala'in sha'awa inaso ki dinga bani hakki na koda...", bai Kara sa ba ta warce hannun ta tana ''wai idan nace bana so bara ka k'yale ni bane ko dole ne sai ni, iye? "Kina nufin na karo mata, wacce zata na bani hakki na ko wani dare, wacce baza ta wulakan tani ba, ko so kike na zauna haka bakya tunanin kar ki je fani cikin halaka"? Budan bakin ta tace "Kayi duk abunda kaga dama bazai dame ni ba", yace "Haka kika ce?" tace eh. Ransa ne yayi matukar baci yace "Shi kenan zan karo mata tunda an halal tamun har ku hud'u ko dukka uku zan kawo su locaci daya tunda ba dumuwar ki bane" ya tashi yabar mata d'akin.
Wasa wasa suka share wata bakwai da aure amma sau d'aya shimfa d'a ta had'a su wannan ma ba da son ranta ba fin karfi yama ta. Gaba d'aya ya share al'amarinta ba dan yana so ba. Duk ranan da yayi yunkurin zuwa saduwa da ita sai ta b'ata masa rai shi kuma ya k'yaleta.
Duk tsawun watan nin nan babu abunda ya shafe ta dashi, gaisuwa da cin abinci ne kadai ke had'a su sai kuma idan aka kwan biyu ya kai ta gida ta wuni ya dauko ta.
Sun koma makaranta tsawun wata biyu yanzu. Cikin kawayen ta gaba d'aya babu wanda ta nuna wa da matsala a tsakanin ta da mijin ta banda Aisha da tasani ko Ruky bata gaya wa ba. Ita ma Aisha'n dan akwai ranan da ta je gidan ta tayi ta sallama taji shiru sai tayi yunkurin zuwa d'akinta taji Suleiman na mata nasiha akan rashin basa hakkin sa da take amma taki saura ransa tafi ta tabar masa d'akin nan taci karo da Aisha . Ajiye ta tayi ta dinga mata bala'i dan ta gyara halinta sai ta nuna mata akan zata gyara dan bata son masifar k'awar tata.
Haka a gidan su ma babu wanda ya tab'a sanin da matsala atsakanin su. Kwatsam Suleiman yaje wa da ummar sa zancan k'arin aure. Umma tayi ta fad'a ya za ayi wa sadia kishiya ita da ko shekara batayi ba a gidan. Saida ummar sa ta takura sa ya kawo mata Sadiya taji daga bakin ta da amince warta zai k'ara auren. Shiko babu musu yaje da Sadiya gidan ta saboda ita ta amince masa hakan, umma tace "Sadiya akwai wani abun da kuke boye mun ne ki fada mun a wani dalilin kika amince masa ya kara aure"?. "Umma munje ganin likitane saboda shiru da mukaji ko b'ari ban ta ba yiba yace dashi ya gwada kara wani auren dan wani locacin wata macen bata iya conceiving har sai mijin ta ya canja makwancin sa". Atake yajuya yana kallon ta baisan daga ina ta k'irk'iri wannan k'aryan ba ko kunya bata ji ba kuma yadda tayi maganar sam bata damu ba. Muryan umma ce tadawo da shi daga tunanin da yake. "Daman shine abunda kake boye mun yanzu na fahimci al'amarin, ka sanar da iyayen ta hakan kuwa?" Iyee! a'a, kadan ya rage bai kid'ime ba, saida yayi ajiyan zuciya sannan yace "Daga nan za mu wuce mu fada musu". Toh shi kenan Allah ya tabbatar mana da alkhairi", Ameen Umma.
Suna fita a gidan suka nufi gidan su Sadiya. Kafin su sauko a motar Suleiman ya kama hannun ta ya kalle ta yace " Sadiya kinga ni bazan iya fadan wannan kalmar da kika fada wa umma ba saide ke ki fada wa mama kinji", kada masa kai tayi ta sauko suka shige ciki.
Gidan babu kowa sai mama da suka tarar dan k'annen ta sun tafi islamiya, Abba ma ya fita. Sai da suka gama gaisawa Suleiman yace zai fita daga waje ya jira ta. Sadiya ta yayyafa wa mama k'ariyan ta. Jikin mama yayi sanyi bata ji dad'in saba amma ya ta iya tunda sai an kawo mata abokiyar zama kafin y'ar ta tasamu juna biyu. Tace da ita "Toh Allah ya kaddara mana alheri cikin ta", addu'a tayi musu, Sadiya tace za su tafi dan yamma yayi suka fice. Sai dare Abba ya dawo ta fad'a masa shima yayi musu fatan alkhairi gaba d'ayan su.

[7/26, 3:19 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana Gani💝
Written by F k Ahmad
Pure Moment Of Life Writer's
Sadiya k'awa a great fan, thanks for the love. Wannan shafin naki ne. Allah ya bawa Anty yaya lafia. Much luv.
47 - 48
Ba'afi kwana biyar ba Suleiman ya gama shirya kayan auran sa aka sa musu rana da Maryam wata yar uwarsa. Sati biyu aka yanke wa ranar aure, Suleiman dad'i kashe sa, ji yake kamar anyi an wuce wurin. Wannan auran shine kwanciyar hankalin sa zai samu kashe sha'awar sa kuma tunda zai had'a su gida d'aya k'ila Sadia tayi hankali idan tana ganin sa tare da ita ko za tayi kishi ta so shi.
Bayan auren Suleiman da Maryam, washe gari Sadiya da k'awayen ta na zaune a d'aki, Aisha ta kira ta gefe take tambayar ta, "Wai ni Sadiya meyasa bakya nuna wa mijin ki k'auna ko kad'an gashi sai da kika ja aka miki kishiya, munyi magana da ya Suleiman jiya shi ya kira ni yake fad'a mun zaiyi auren nan ne badan ya k'unta ta ta miki ba amma dan ki nuna kishin ki akan sa yana son ki sosai baya son rabuwa dake yace ya fada miki dalilin karin auran sa bakya biya masa buk'atar sa ko nima shaida ce kuma ya fada mun ne dan ni kadai nasan sirrin ku sannan bazai yu yasa ki agaba ya zauna haka ba gara ya kara auren. Shi azaton sa ma zaki basa hakuri ne ku zauna lafia ba sai ya kara aure ba tunda yana da ke amma kika nuna rashin kulawarki. Ni dai ina baki shawaran ki gyara tsakanin ki da mijin ki ko kuma kina kallo sabuwar Amaryar sa ta k'wace miki shi". "Hmmm lallai in dan wannan ya k'ara aure ba zai taba ganin nayi kishi akan sa ba tunda ba son sa nake ba". "Toh ke abu baya wuce wa ne a wajen ki me yasa baza kiso mijin ki ba"? Cikin zafi da b'acin rai tace "Saboda me yasa zai munafurce ni yaje sa neman aure na wajen su Abba ba da izini na ba? Dan ya nuna mun isan sa ko, shine nima nake nuna masa isata, ba'a siyan soyayyar mace a ko'ina saide wajen ta, bai fara zuwa waje na ba saida ya bita iyaye na dan yasan zai samu ko ta karfi ne toh bazan so shi d'in ba, in dole ne ai sai mu gani". "Kar ki manta fa, haka addinin musulunci ya koyar ba munafurtan ki yayi ba, izinin su yaje shi nema fa kawai kuma badan ASB ya gudu ba ya nuna bai shirya auran ki ba da kinsan Abba wanda kike so zai aura miki", "toh ya'isa hakan ni karki isheni da surutu", ta tashi ta bar wajen.
Tunda akayi auran, Sadiya bata samu ta zauna a gidan ba dan kullum tana makaranta tunda safe sai can yamma ta ke zuwa gida dan karatu suke sosai zasu fara tests sun kusan fara jarrabawa na first semester suna 400L yanxu.
Suleiman kam sai dare yake zuwa. Kullum yakan shiga wa uwar idan nasa su gaisa sannan ya wuce d'akin Amarya. Sakanin su babu laifi akwai shiri.
Maryam shiru shiru ce ita ba mai son haya niya ba. Tad'an girmi Sadiya kad'an tagama makarantar ta tun last year tana zaman gidan ta. Suleiman najin dad'in zama da Maryam sosai sam bata hana sa hakkin sa. dan ko ranan da aka kawo ta ma suka raya daren.
Satin Maryam biyu kenan a gidan. Sadiya ta fito d'ebo lunch din da zata ci a kitchen kawai sai taga Suleiman da Maryam wajen dining table, Maryam tana kan cinyar sa zai saka mata abinci a bakin ta dai dai locacin Maryam ta d'ago kanta suka had'a ido da Sadiya, kunya ya kamata ta sauke kanta ta ture hannun Suleiman ta maida shi baya, "Meya faru kuma Darling"? Suleiman ya tambaya, girgiza masa kai tayi, Sadiya tayi murmishi tazo ta wuce ta gaban su, nan ne Suleiman ke ganin ta. Shima din murmishi yayi wanda shi yasan dalilin sa amma ni nasan na jin dad'i ne dan idan taji haushi zata fara sonsa. Maryam taja jikin ta zata sauka daga cinyar Suleiman ya kamota "ina zaki je"? "Koma wa zanyi kan kujera", "a'a babu inda zaki nan ne kujerar ki yi zaman ki anan", a'a yaya ka kyaleni naje can jiya ma haka ta faru bana son na zama silar b'ata zaman mu da ita kaga zama na da ita muna nan lafia...", bata kara sa ba Sadiya ta kara zuwa ta wuce d'akin ta. Maryam ma tashi tayi tabarsa a wurin.

[7/27, 2:11 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana Gani💝
Written by F k Ahmad
Pure Moment Of Life Writer's
49 - 50
Da Sadiya ta shiga d'aki ta zauna duk da abun ba damunta yayi ba amma bai hana ta tambayan kanta ba, "Me ya kawo Ya Suleiman gida a tsakar ranan nan? Tabdi, kuttu ma abunda bai taba faruwa ba lallai kam yau wace rana, hmmm". Tayi murmishi takai abinci bakin ta.
Da daddare Maryam da Sadia na kallon film a falo sai shewa suke yi, ita Maryam akasa ta zauna while Sadiya na kan kujera. Suleiman ya fito shima zaiyi joining d'insu ya kallo inda Maryam take yazo ya zauna dab da ita takalle sa ta kad'a masa kai, ya mata signal sai ta hade rai ta masa magana kasa kasa, "ka tashi ka hau kan cushion d'in kar ka zauna kusa da ni please babu dad'i", sai ya d'aga muryan yadda Sadiya za taji sa yace "Ohk mata ta bari na kwanta", ya ja kafafun ta ya mik'ar dasu yayi placing kansa a cinyar ta yana facing fuskar ta ya kuma ce da ita "Thank you Darling", Maryam sai da ta k'ulu matuka dan ita kunyar Sadiya take yi. Tun shigowar sa tayi kaman bata gansa ba sai kallon ta take, shi kuma a ganin sa ko ta fara jin haushin sa ne. Da Maryam taga ba sarki sai Allah tunda yaki tashi sai ta k'yale sa amma she's not comfortable kawai dan ba yadda ta iya ne.
Saida d'akin yayi shiru na wasu minutes, hankalin su na kan TV, hannu Maryam takai kan suman kansa tana yawo dashi ya d'ago ido ya kalleta ta sake masa best smile ever, yace mata "you look more beautiful when smiling", tace "thank you for the lunch you came to eat, am greatful", "what for?, mata ta guda tagaiya ce ni naki zuwa, haba everything for you, duk wani aikin gabana kin fisa matsayi ai", dad'i taji har ranta. Zata kai masa kiss a forehead dinsa immediately wayan Sadiya yayi ringing, zuciyan Maryam ne ya tsinke Sadie ta tashi tabar wajen dan receiving call din, sam ta manta da sadiya na zaune a falon, suleiman yace mata "ya kika dakata ke nake jira ki sumbace ni fa", tace "yaya ashe ba mu kadai ne a falon ba na manta kai kuma baza ka hana ni ba". " na hanaki kuma dan meye, ke ba mata ta bace", "nasani amma bana son hakan yana faruwa agaban ta sai ta d'auka iya shige nake mata", sai ya nuna mata irin yayi fushin nan ya k'au da kansa yace "naji zan kiyaye gaba".
Sadia ko da tagama wayan ta a d'aki zaman ta tayi ta daura hannu a hab'an ta tace "no wonder! Ashe ita tayi inviting dinsa yazo shi, iyee soyayya manya"dariya tayi sannan tayi kwanciyar ta dan dama ta gaji da kallon bacci take ji.
Bayan Maryam ta karanci zaman da ke tsakanin sadiya da Suleiman sai ta dau alwashi zata gyara tsakanin su.
Wata rana Suleiman ya fita baya gida, Sadiya na zaune a backyard na gidan tana shan iska Maryam tazo ta same ta ta zauna kusa da ita. Crunches take ci sai ta mata tayi "Maryam gashi bismillah", ta dau biyu aciki tace "na gode". Duwatsu Sadiya ta d'iba tana wulli da su daya bayan daya cikin wani rami amma batayin sa'an saiti dan duk fad'uwa suke kasa, Maryam tayi darya tace "kawo na tayaki", ta miko mata sauran duwatsun suka kara sashi duk a kasa. A sannan ne Maryam ta dafa kafad'ar ta ta kira sunan ta "Sadiya", saida ta ansa ta sannan taci gaba da magana, " kinsan yanxu mun zama y'an uwa dake ko", tace "eh", " a gaskiya bana son yana yin zaman dake tsakanin ki da ya Suleiman ", wani bazan kallo ta juya ta mata, saide Maryam bata fasa maganar ba taci gaba "bai kamata kina masa abun da bai dace ba a matsayin matar sa, kinsan Allah yana fushi da matar da bata wa mijin ta biyayya ko?" Sadia tace, "Maryam ya ishe ki haka dan ina ganin girman ki saboda kin fini shekaru", "nasani kina bani girma ta kuma bana son ganin tab'e wan y'ar uwata wata rana shi yasa nake son maganta al'amarin, kiyi hak'uri ki gyara wasu halayen ki, wani locacin ya Suleiman kan yin wasu abubuwa masu haushi idan kina wajen, yana yin hakan ne dan ki shiryu amma bak'ya canza wa, meye amfanin zaman auren naki badan kiji dad'in rayuwar ki bane", wannan locacin Sadiya taje makura, ta tashi ta tsaya ta nuna Maryam da yatsa tace "daga yau ina so ki fita da ga harka ta kar kiga ina sake miki dayawa fitina ne bana so amma tunda kina mun sa'ido da shishigi muzu ba dake", ita ma Maryam ta tashi ta tsaya tace da ita "kiyi hakuri Sadiya ban zo da nufin in bata miki rai ba kawai dai abun da nake so ki gane shi ya Suleiman yana ara miki locaci ne kinsan d'an adam dole wata rana ya gaji da halayenki ni kuma ina gudu miki wannan ranan, yau d'in nan ya kamata ki basa hakuri idan yazo gida yanzu tactics na farko da zan baki shine ki je ki fara girka masa favorite dinsa kinji ni zan taya...", saukan mari lafiyayye taji fas a kuma tunta, Sadiya tace

Please Login or Register in order to submit comment