Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kofa, anties na Suleiman ne suka zo tayi welcoming dinsu ba yabo ba fallasa. Sun zo mata da Karin ta suka koma falo suna ta shan hiran su amma banda ita da tayi jugum tayi shiru.
Can kamar karfe sha biyu suna fita sai ga kannan ta da kawayenta ta dadi kashe ta murna take kaman tayi shekara bata gansu ba. Daki suka shige ita da Aisha da Ruky suka bar su Zara a falon su na ta kallon tsarin gidan. Ruky zata zauna kan drawern da Suleiman ya ajiye letter akai sai taga papern, daga wa tayi zata bude Aisha ta warce, daga samun paper anan sai ki bude wa mutane sirrinsu, sirrin me kuma inji sadia gashi nan kuwa ko ba ke aka ajiye wa ba dan ni ma mijina haka yake mun. Ni ban kula da wani paper bama anan kuka ganshi ne, eh kar kice mun baki gani ba. Ruky ta karbi papern tare da ce wa bari na karanto miji. Sai da tagama kunya ne ya kama sadia ita me yasa bata gani ba tunda zu gashi za suyi making fun akan ta. Dariya suka yi ta mata taja tsuka ta bar musu dakin.
Bayan la asar suka waste ita kadai ta rage. Kitchen taje ta girka musu dinner jollof na spaghetti da yaji kayan hadi sosai ta hada da drinks da snacks wanda aka rako ta dasu ta jera akan dinning table.

[7/20, 3:25 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji bana gani💝
Written by F k Ahmad
35 - 36
Suleiman bai dawo gida ba sai kusan bakwai na dare bayan duk sun waste sun baro ta ita kadai a gidan locacin har dudun dare ya fara shigo wa tana tsoron ita kadai ce ga nepa sun dauke tun dazu gidan babu light ta du kunkune kanta cikin wata kujera a falo ta kwanta a kai har tafara gyangyadi.
Suleiman ya bude kofar ya sa kai, o'o ashe nabar ta babu wuta a gidan da sauri ya nufo kujerar da take badan yasan tana wajen ba dan dakin da duhu yaje shi laluban lantern din da ya ajiye akai jiya, shafa wurin yake ya ji ya taba abu mai laushi shiko yaci gaba da taba wa, ita da batasan shigowan sa ba arazane ta bude ido tasa wani wawan ihu shima baisan da ita awajen ba, tsalle tayi zata sauko ya kamota takara saka wani ihun sadia nine fa nan Suleiman ishiru kinji kiyi hakuri manta wa nayi na barki cikin duhu banzo na kunna miki generator ba lantern nazo dauka akan kujerar baki kula kingansa bako, raba jikin su tayi zata sauka kafan ta ya ci karo da nasa wani tsoron taji tayi ihu takoma ta kankamesa tana kyarma har kuka tasaka yayi saurin hade bakin su wani electric shocks taji tun daga tsakiyar kai har zuwa kafa, tana son kwace kanta amma ba zata iya ba suna cikin yanayin nan kawai aka kawo wuta falon ya gauraye da haske fisge jikin ta tayi da sauri dan taji kunya ya kamo hannun ta kallon cikin ido da ido suke yi wa juna, kauda kanta tayi ta nufi dinning area ta dauko plate biyu ta zuba nata shima ta zuba mai ta barsa awajen ita tashige daki dan taci nata. Jan plate din yayi gabansa yacinye harda kari sai jinjina mata yake matar sa ta iya girki shikam yaji dadi.
Bayan ya gama cika tumbin sa yaje yayi alwala ya sameta a daki kai da guiwa ta hada tana zaune, kusa da ita ya zauna ki tashi kiyi alwala muyi sallah locacin isha'i yayi, jeka masallaci kayi nima zanyi nawa, haba mata ta bakya son mijin ki ya ja ki sallah ki samu lada eh jeka ka mana ai ba sallah ne nace bazanyi ba ko, toh naji hakuri zakiyi tashi kiyi alwalan. Sai kuma ta tashi babu musu taje tayi alwalan ta dawo suka yi sallan.
Bayan sun iddar ne ta shiga bayi dan ta wasa ruwa, tagama ta fito har yanzu yana nan zaune ta dauka zai fita ta kulle dakin kaman na jiya tace masa kai baza ka je ka wasa ruwan bane a tsammanin ta fita zaiyi yaje nasa toilet din sai taga ya shige nata tsuka taja tayi shirin ta na bacci da wuri kan ya fito tagama shafe jikin ta da mayuyuka masu kamshi. Tana ganin fitowar sa daga shi sai gajeran wando ta rufe idonta ta dale kan gado tayi kwanciyar ta. Tun fitan sa kamshin ta ya dauke hankalin sa gaba daya ya rude sai ta kanta yayo, fuskarta na ta dayan side din idonta a rufe taji ana shafan jikin ta tabaya runtse idanun tayi da karfi tana jin sa sai ta shinshinata yake janyo ta yayi ya manne jikin su sosai kissing dinta yake romantically tana shure shure gaba daya ya fita hayyacin sa sai romancing dinta yake, hannun sa taji yana yawo kan kijinta sai wasa yake dasu karfin ta tattaro ta turesa daga jikin ta tashi ta zauna, da karfi yake mai da numfashin sa ya sake kamota tana fizge kanta ni ka kyaleni ka koma dakin ka mana me ya ajiye ka anan ha'a turesa tayi da karfin ta taja baya.
Saida shima ya tashi ya zauna yace sadia me kike nufi ni ba mijin ki bane da kike korina ina kike son naje bayan mata ta tana nan, kuka tafara yi masa tana ni kaje dakin ka, gaya mun inda yafi mun wannan dakin ke fa matata ta sunna ce ya za'a yi na barki na koma wani dakin, ni bana so ka tafi ka barni bana son kwanciya kusa da kai haka kika ce, eh ni sauka mun daga gado na, kin manta daga ke har gadon duk kun zama mallakina ko, ba wani ni karka sake zuwa kusa dani bana so, shikenan sadia ba zan tilas taki ba sai kinso zan taba ki amma barin dakin ki addini na bata yarda mun hakan ba zanyi shimfida ta a kasa ke kuma kiyi kwancigar ki kan gadon amma kar ki manta fa tun jiya yakamata mu raya sunna amma kika kulle ni awaje yanzu kuma kika hanani ba komai na kyaleki ne dan bana son mata ta tafada ga halaka ni na amince miki saida yardan ki zan kusan ce ki bana son tsinuwan mama'iku su tabbata akanki, yaja pillow daya ya sauka daga gadon. Jikinta yayi sanyi amma kuma taji dadi da ya kyaleta share sa tayi tai kwanciyar ta.

[7/21, 4:54 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji bana gani💝
Written by F k Ahmad
Dedicated to Sadiya, my khadija, baba Ruky😜 and Ummi takwarata ILYSM. Allah ya barmu tare.
37 - 38
Da asuba ya tashe ta sukayi sallah ta koma zata kwanta yace da ita bara kiyi azkar na safiya ba zaki koma bacci ki tashi muyi kinji sadiya ta, manna masa tayi asane take da yin azkar din dan ko agida ma tana yi kan ta kwanta yanzu ma bawai baza tayi bane akwancen take yi har bacci ya dauke ta sai da ya gama ya dubi time har shida yayi gashi yau Monday zai jesa sa aiki by 7:30 baya son tada ita don tamasa breakfast hakan yasa yaje shi kitchen din dan ya musu.
Potatoes yashiga peeling ya soya musu da kwai, ya dauko cat fish a fridge ya musu pepper soup dinsa ya gama tattara kitchen din ya kaisu su kan dinning table.
Dakin sa yaje yayi shirin sa na zuwa office ya fito yaje ya leka ta adakinta har yanzu baccin ta take. Kamar jiya ya dauko paper da biro ya rubuta mata "your breakfast is ready on the table, ina so ki girka mun tuwon shinkafa da miyan alaiyahu wa dinner luv u so much wifey". Same drawern jiyan ya ajiye akai yaje yaci chips din yayi tafiyar sa.
Bata farka ba sai almost 10 o'clock bude idonta ke da wuya taci karo da papern a gefen ta iskan fanka ne ya dawo dashi gaban ta kamar zata share sa sai kuma ta dauka ta karanta shi ta tabe bakinta ta tashi.
Bata fito ta karya ba sai kusan azahar saboda da chatting dinda ta zauna yi da frndz dinta tru WhatsApp. Babu laifi tayi enjoying na girkin sa ta gama tayi sallan ta na azahar.
Waya ta dauko zata kira mama su gaisa taci karo da numbern ASB tana ganin contact dinsa hawaye sukayi forming a idonta, sai last meeting dinsu ta tuna locacin da ya sauke ta a mota, yace da ita sai munyi waya yana mata smiling, Allah sarki Ahmad ko ina kake damuwa ta yazama kana nan lafia sai kuma ta tuno ai da wata wai ita salma agaban motan sanda ya sauke ta, tsuka taja dan sai yanzu abun ma ya bata haushi wa yasan ma ko eluding tayi dashi kai anya ta ma isa ni nasan Ahmad bazai biya mata ba sai abunda yaga dama yake yi, tayi dailing numban mama.
Sai can da yamma ta nufi kitchen zata musu girki sai ta tuna abunda yace ta dafa masa, hai damuwan sa ni abun da naga dama zan dafa dan ma yasamu ina masa girkin shine harda zaban na ra'ayin sa yaushe ma zan tsina alaiyahu na yanka ko a gidan mu abunda na tsana kenan yankar yakuwa,alaiyahu da kuma peeling dankali suna ban wuya. Ga kuma babu alaiyahu cikin kayan miyan da aka kawo. Tuwon shinkafan da miyan dayen kubewa tadafa shine best meal dinta tana son miyan sosai gashi tayi shi yayi dadi saboda tana sonsa yasa ta iya tsarrafasa mai kyau.
Kaman jiya har yanzu bai dawo ba anyi sallar magrib tana zaune sai kallon series film take dan tun a gida tana bi, har ta gama kallo bai dawo ba sai ta sake sake take azuciyan ta mutun shikenan akawo ta wani gidan abarta ita kadai tunda safe har na wuni dare yayi amma babu wanda zan gani an mun kulle sai kace ba'a sona a gidan mu ga mama taki tabar mun asma'u mu zauna tare tana dibar mun kewa, ni bansan wani irin aure bane hakan da haushinta ta tashi zata daki ta buge a kujera zata fadi yayi saurin kamata a tsorace ta saya kallon sa, yaushe ka shigo, tun dazu baki lura ba ko tunanin me kike yi har zaki fadi, raba jikin su tayi ta masa toh banji kayi sallama ba ai, ok toh am sorry bari na koma nakara yi tunda baki ji wancan ba.Hararan sa tayi ta wuce daki dan tariga taci abucin ta kuma dazu tafara fashin sallah. Shiko wuce wa yayi dan yaci abincin sa shima saida yayi sallah yazo gidan. Yana bude murfin flask na miyan kamshin sa ya doki hancin sa da wuri ya toshe hanshin dan baya son miyar kubewa baya cinsa rufewa yayi ya tashi dan ya sameta sai kuma ya fasa. Toh me yasa bata dafa mun miyan da nafada ba, shiga kitchen yayi dan ya daura ruwan indomie.
Sai da zai kwanta bacci ne ya jesa dakin ta bata kulle ba ya shige, ita ko ta jima da yin baccin shima yayi kwanciyan sa akasa.
Washe gari bayan ta dafa masa karinsa ya shirya ya fito ta gaishe sa ba yabo ba fallasa. Kujera yaja ya zauna shi yayi serving kansa tana kallon sa. Sadia ya jiya baki girka min miyan da nafada ba kika mun wani daban, gayen alaiyahun ne babu a gidan kuma ban san inda zan samu ba kaga ba fita nake ba balle nasan anguwan kuma ko dan aika bani dashi, OK! Sai yayi shiru na wasu seconds sannan yace da kin kira ni a waya kin gaya mun hakan ai koni sai na kawo amma kika tashi kika girka kubewa nasan dan baki sani bane bana cin miyan baki ganshi yadda kika barshi ban taba ba. Nagani, toh dan Allah karki sake kinji, uhumn. Yauwa duk wani abu da kika ga babu a gidan ki sanar dani.
Da ya gama breakfast din yace da ita ki dauko mun briefcase dina a daki, taje ta dauko masa yace toh ni natafi koh, juya wa tayi zata shige daki bata tanka saba yace sadia baki ce komi ba, to me zance maka, baza kiyi wa mijin ki addu'an fatan alhairi ba, toh adawo lafia tashige kayanta kansa kawai ya kada ya fita.

[7/22, 5:48 PM] Fannah k Ahmad: 💝BANAJI BANA GANI💝
Written by F k Ahmad
Dedicated to Maryam Muktar
Thanks for your support in making my work progressive.
39 - 40
Tunda ta tashi da safe tafara jin jikinta babu dad'i amma ta daure tayi aikin gidan, cikin tane yake mata murd'a sosai ga ciwon bayan da ke damun ta, dukunkune kanta tayi cikin bargo akan gado sanyi take ji, zazzab'i ne sosai ya kamata ga babu inda zata samu magani a cikin gidan haka tayi ta fama da jikin har yamma tayi.
Ba shine ya dawo gidan ba sai locacin sa da yasa ba zuwa ita ko sai tunani take ta gaji da zaman gidan, yau kwanan ta uku kacal fa yanzu haka za tayi ta fama ita kad'ai duk abunda zai sameta babu mai kawo mata agaji.
Da ya shigo bata falon d'akin sa yaje ya wasa ruwa ya nufi wajen abincin sa sai yaga wayam kan table d'in babu food flask ko daya. Kitchen ya shiga yad'au ko tana ciki ta makara da yin girkin ne nan ma yaga bata nan. Kwanuka ya duddu ba baiga abincin sa ba gashi ya kwaso gajiya da yunwa sai ya d'auka ko fushi tayi akan fad'an da yamata da safe dan bata girka masa abun da yake so ba shi yasa taki yi yanzu.
D'akinta yaje ya bude kofan, sheshekar kukan ta yaji, ganin ta yayi adunkule waje daya a gefen wardrobe tana karkar wa, yace "subhanallahi", dagudu ya karasa wajen yace, "sadia lafia me ke damunki", d'aga ta yayi zuwa kan gado sai yaji jikin ta da zafi sosai " me yasa meki, zazzab'i ne"? kad'a masa kai tayi da alamar eh, "tun yaushe hakan ya faru", muryan ta na rawa tace, "ka fita bai jima ba", "shine baki kira niba sadia me yasa kike son cutar da kanki, bana son kina irin haka, kinci abinci kuwa"? Kada masa kai tayi, " saboda meye baki ci ba kinsan rashin cin ma zai iya contributing rashin lafian ai, bari na kawo miki". Sai ya tuna bata dafa ba, ya kwantar da ita ahankali yaje ya hado mata tea mai k'auri yazo sa yana bata a baki, da k'yar tasha rabin kofi ya d'auko mata hijabin ta yasaka mata ya d'auko key din motar sa zai d'aga ta tace "ina zaka kaini", asibiti za muje sadia, k'ank'ame sa tayi tana "ni bana son asibiti allura za a mun ko, "a'a magani zamu k'arbo miki babu allura", sannan ta yadda tayi shiru.
Da suka iso asibitin zai d'aga ta yashigar da ita sai tak'i "ni idan har sai ka d'aga ni nafasa maganin ma shi kenan sai kowa yayi ta kallon mu ni bana so", "toh shi kenan ki fito idan zaki iya". Fito wa tayi da kanta ta tsaya shi kuma ya rufe gambun motar yana jira ta taka su tafi amma ta kasa da k'yar tayi steps biyu yana kallon ta suuu taje zata fadi saboda jiri da ya d'ebota, yayi saurin rike ta yace " kinga nace ba zaki iya ba", d'aga ta yayi bata musa masa ba suka je officin wani Dr. Abokin sa ne kuma sai da ya sanar dashi za suzo. Tambayo yi yamata akan yadda take ji sannan ya rubuta mata magun guna suka koma gida ya siyo musu abinci ahanya.
Da safiya tayi har yanxu jikin nata babu sauki duk da tasha magani sai zafi da take ji a cikin ta. Suleiman ba zai iya fita ya barta cikin halin nan ba, ya kira wurin aikin sa ya karb'i excuse na sati guda kuma sai yaci sa'a suka bashi dan last week ya nema saboda zirga zirgan auren sa suka hana sa.
A ranan shi yayi musu girki, wanke wanke, shara, moping kai duk wani aikin gidan shi yayi, ga kula da ita da yake yi saida ya jinji na wa mata dan yaji wuya.
Da k'yar ya rarrashe ta taci abincin kadan tasha magun gunan ta. Ki tashi kiyi wanka, tace "ni bazan iya ba", toh koh za muje na miki ne, zazzare idanunta tayi, ni bana so baza kamun ba, " toh haka zaki zauna ne muje in miki". D'aga ta ya shiga yi ta fashe masa da kuka, "ni kabar ni zanyi da kaina" tana kai masa duka duk da ba karfin jikin take dashi ba, kyaleta yayi yace "toh maza je kiyi" ya mika mata towel ta karba adaddafe tashige bayin tayi ta fito ta zauna shafa mai sai kallon ta yake, ta juya ta kalle sa tace "toh ka fita ni zan saka kaya na" murmishi yayi ya fice ya bata waje.
Sai da tayi kwana hudu kafin ta samu sauki sosai. Cikin kwana kinnan babu inda Suleiman yaje sa kullum yana gida tare da matar sa sai wahalan ayyukan gida da yake sha da kuma kula da jinyar ta da yake yi. Sosai tasha mamakin d'awainiyar ta da yake har da aikin da yake, tasan dai ya iya wanke wanke da shara dan duk locacin da yaje gidan su ya tari tana yi idan baba Hadixa bata zo ba ranar to yana taya ta. Ya sha gaya mata ya iya girki amma bata yarda ba sai yanzu da ya aureta ta tabbatar. Tasan ya mata kokari sosai amma dan bata da lafia ne shi yasa bata damu da nuna masa appreciation dinta ba dan aganin ta bayyi deserving ba mutumin da kullum in ya fita da safe sai dare yake zuwa gida. Amma yau har kwanan sa hudu babu inda yaje dan yayi jinyar ta saboda ya hana ta gayawa kowa bata da lafia a gidan su tun da zai iya kula da ita.

[7/23, 7:14 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana Gani💝
Written by F k Ahmad
Kuyi hakuri da posting din da nayi na fari ashe ba daidai na turo ba sai yanzu nagani, ga complete dinsa. Pls bear wit me masoyan Banaji bana gani.
41 - 42
Ranar lahadi da daddare tana cikin shirin ta na bacci ta fito d'aukan ruwa a fridge bata kula da yana zaune ba, rigar nata very silk ne yana mannuwa a jikin nata duk surar jikin ta ya bayyana. Tsura wa k'irjinta ido yayi acike suke pal suna yawo cikin rigar, bai San locacin da Sha'awar sa ya motsa ba ji yake kamar ya tashi ya rungumo ta, wuce sa tayi tashige d'aki bata gansa ba.
Gyaran bedsheet ta tsaya yi, d'an sunkuya wan nan da tayi yasa albarkatun k'irjin nata suka bayyana ta gaban wuyar rigar ta daidai locacin ya shigo d'akin sam bata lura da shigowan sa ba, cak ya tsaya yana kallon ta sha'awar ta ne ya kama sa sosai, ji kawai tayi an rungume ta tabaya, hannun sa ya kai kan k'irjinta ya fara shafa wa, turesa take da gasken ta amma inaa da karfin sa ya damkota suka fada kan gado yafara tura mata sakonni daban daban ta ko ina sai kokarin cimma burinsa yake, tun tana fizge wa har karfin ta ya kare. Jikin ta yayi likis ko magana bata iya yi sai sheshekar kukan ta yake fito wa kasa kasa shiko ya samu ya shige ta baisan wani duniyar ya tsinci kansa ba dan dad'i, wani ihu ta k'wala dan azaba numfashin ta kaman yad'au ke, ya tausaya mata amma baya jin zai iya katse jin dad'in sa haka ya ci gaba da pounding dinta har saida ya gaji dan kansa ya sauko daga kanta tana manta numfashi, asannan ya lura da halin da take ciki da sauri yaje ya had'a mata ruwan d'umi yazo ya dauko ta zuwa toilet. Wanna ya mata ya yasa mata jikinta sannan ya maida ta d'aki har yanzu jikin nata amace yake.
Tea mai zafi ya kawo mata tasha ya samu bacci mai nauyi ya dauke ta. Shima toilet ya koma yayi wankan sannan yazo ya kwanta kusa da ita, for the first time zasu kwana gado daya sai kallon k'yakkyawan fuskar matar sa yake yana dad'a godewa Allah da ya mallaka masa mace mai irin d'and'anon zuma da ni'ima lalle shi kam yayi dace. Matso da ita yayi kusa dashi ya manne ta jikin sa kaman zai cinye abunsa ko za a kwace masa ita. Bacci mai d'adin gaske yayi awun gaba dashi.
Asuban fadi ta farka jinta tayi ajikinsa da karfi ta tunkuda sa gefe shima ya bude ido yace "lafia sadia"? " meya daura ka nan", "wajen mata ta nazo ni mana, "daa anan kake kwana ne bana so kasauka mun daga kan gado na kuma wallahi Allah ya isa na da kamun mugun ta jiya, ko da wasa karka kara shiga tsabga ta bana sonka kuma bana bukatar sake ganinka ka fita daga rayuwa ta karka kara zuwa kusa dani sai ta fashe da kuka". Cikin fushi da bacin rai yace "idan ko haka ne ki kwantar da hankalin ki bana son tashin hankali na miki alkawari bazaki sake furta irin wannan kalamun akaina ba. Sadia ina kusantar ki ne saboda so amma tunda kika ki hakan ni na rabu dake", yatashi cikin zafin rai ya bankad'a mata kofar yaje d'akin sa.
Zama yayi kan kujera yana tunanin irin halin da yake ciki, dafa kansa yayi da hannun sa na dama yana "ban taba zatan irin wannan kalubale daga cikin rayuwar aurena ba amma tunda hakan kike bukata bazan sake zuwa koda kofar dakin ki ba".
Tun daga wannan ranar shike nan Suleiman yafi ta daga harkar sadia bai sake koma wa d'akin ta da sanin taba. Idan yayi sallar asuba sai ya shiga kitchen ya dafa abun da ba nauyi yaci ya tafi wajen aikin sa ba zai zo gida ba sai can dare idan yaci abincin sa a cafeteria yake zuwa dan ya daina cin tuwon ta.
Yau kusan sati uku baya barin ta gansa ko su hadu da juna a cikin gidan amma shi dan yasauke hakkin dake kansa kullum cikin dare sai ya tabbata tayi nisa da bacci yake shigo wa d'akin ta ya duba lafiar ta ya koma nasa d'akin.
Ita kuwa ko kad'an bata damu da rashin ganin sa ba dan hakan take bukata. Kullum sai ta wuni tana kallon wani series Indian film (silver linning) da ta sa Zara ta siyo mata tunda bata da wajen zuwa sai de kallon.
Sai da ta share wata biyu a gidan sannan Rukayya tazo mata ranan murna kasheta sai kace tayi shekaru bata ganta ba, locaci daya kuma tayi fushi ta zauna ruky tace "ha'a lafiar ki kuwa? Yanzu fa kike ta tsallen jin dad'i sai kuma ki hada rai sai kace mai aljanu". "Ai manta wa nayi nake jin dad'in amma fushi nake daku, ace tun ranar wuni da kuka zo mini ban kara ganin ko wannan ku ba sai ku share mutun dan rashin mutunci sai yau kika ga daman zuwa", "ohh dan ma kin samu gani na yau din koh? Toh bari natashi na tafi", "ah'a yi hakuri mana da wasa fa nake besty na kinsan yadda nake missing dinki kuwa? Aisha fa ya baku zo tare ba", "yanzu ma daga gidan ta nake wai bata ji

Please Login or Register in order to submit comment