Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata da zuwan sa wajen sadian anjima, hakan akayi kuwa.
Mama ce takira sadiya tazo ta zauna kusa da ita a daki tace da ita, ki bude kunnuwan ki ki saura re ni toh mama, anjima zakiyi bako so nake ki nutsu ki saura re shi ki basa hadin kai game da abunda yazo dashi kina ji na ko, ahankali ta kada mata kai eh mama, yauwa 'yata tashi kije ki ci gaba da girkin Allah yayi maki Albarka. Tun da mama tace zatayi bako wani fargaba ya kamata wannan wani irin bako ne kuma da meye zaizo.
Daidai karfe 4:48pm suka ji door bell yayi ringing, mama na kitchen, sadiya zo ki bude kofa, da sauri tafito daga daki a gigice saka makon kwala mata kiran da mama ta mata kanta ko dan kwali bbu, gashin ta yasha man relaxer ta kama shi da katon ribbon ya kwanta mata luf luf a gadon bayan ta, rigar da ke jikin ta wani karamin top ne sai skin tight wando da ta saka, tayi kyau sosai mantawa tayi a yanayin dressing din da take tayi approching kofar taja ta bude, waza ta gani hada ido sukayi subhanallah Suleiman can't take his eyes off her nan take tagane yanayin da take ciki ta koma daki da gudu shi ma din sai yanxu hankalinsa ke zuwa jikin sa, Astagfirullah ya kada kansa yayi sallama ya shiga daga ciki babu kowa a falon, zaman sa yayi akan carpet din. Mama ta fito daga kitchen, au surkina ne ashe sannu da zuwa kunya kaman ya tona kasa ya birne kansa tana masa dariya suka gama gaisuwan su ta tashi, bari na turo maka ita.
Tunda ta shige daki da gudu kai da guiwa ta hada ta zauna akan gado ta rasa ina yake mata Ciwo, taji mama na cewa ina kike ne sadiya kifito, sauri tayi ta tashi gani nan mama, ta burma wani katon hijabin ta da ke ajiye kan gado.
Ha'a ba ke kika bude kofar ba eh ni ce to ya zaki shiga ki zauna baza ki kai masa ruwa ba ko kin manta na ce miki za kiyi bako a raza ne ta daga ido ta kalli mama, ya suleiman ne fa, eh shi din nake nufi je ki saura resa, mama tashige ta bar ta, kasa daga kafafun ta tayi daga wajen.
A hankali ta kira sunan, ya suleiman? Da kaman bata yarda da abun da ke shirin faruwa ba, da kyar ta iya jan kafanta zuwa kitchen ta dauko masa drink a fridge da glass cup a plate ta nufo sa.
Sallama tayi da muryan ta mai dadin gaske har a ransa ya ji sallamar, amsa mata yayi ta ajiye plate din a gaban sa tasa mu waje ta zauna ta gaishe sa, for the first time suke kunyan junan su. Tun kafin ya furta mata wani kalma a ranta take jin abunda take suspecting dinne zai faru. Erm sadiya kinyi mamakin gani na ko duk da nace miki zanzo, ita sai yanxu ma take tunawa ashe jiya yace da ita zaizo din, kada masa kai tayi a'a. Kyakkyawan ajiyan zuciya yayi sannan yayi gathering all confidence insa ya fara maganar a hankali, kar mu batawa kanmu locaci sadia nazo ne na sanar da ke damuwa ta abunda nake dauke dashi a zuciya ta tun da jimawa a kalla zai kai shekara bakwai yanxu. Ta daga kai ta kalle sa babu alamar walwala a tare da ita jira kawai take ya furta kalmar tasan abun yi dashi, ba komai bane daman illa soyayyar da nake miki kuma nake fatan mu kasance mata da miji na har abada.

[7/25, 10:39 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana gani 💝
Written by F k Ahmad
19 - 20
Kallon sa kawai take hawaye sun ciko mata ido sai kada masa kai da take yi, sai yaji babu dadi ganin hawaye na sauko mata har yanxu kallon sa take, kinyi shiruvbakice komai ba. Tashi tayi ta koma daki da gudu ta kwanta ruf da ciki akan gado tana rera kuka, Shikenan ka gama dani ya suleiman, zaka raba ni da Asb zaka raba ni da farin ciki na, tunda har mama tace na saurare ka nasan sai da kasamu amince warsu kafin kazo waje na amma ni bani da ra'ayin auran ka ni Ahmad nake so. Tunda ta tashi ya ke bin wajen da kallo jikin sa yayi sanyi zai tafi ko sallama bai jira yayi da mama ba yaji an bude kofa.
Abba da umar ne suka shigo, zai durkusa har kasa Abba ya tallafo kafadar sa haba suleiman kai da kake shirin zama surkina ai mun zama daya basai ka durkusa ba ya mika masa hannu sukayi musabaha haka omar ma.
Abba surkifa naji ka fada wazaka basa au omar bakasani bako uwata nake shirin basa fa, laa babban yaya zai zama uncle, murmishi yamasa. Inaa kun gaana da ita sadian ko, eh abba zan wuce gida ma yanzu, toh kagai da iyayen ka suleiman angode ko.
Da daddare ne bayan sun gama dinnern su Abba ne ya kira sadia, tazo ta zauna kusa da shi, mama ta dazu suleiman yazo yasameki kunyi magana ko Allah ya sa an dace, sai yaga hawaye ne kawai ke bin kuncinta, a hankali ya kai hannun sa zuwa fuskar ta ya shafi hawayen yaji sa da dumi sai yaji babu dadi da ya tuna cewa Annabi yace 'idan kazaba wa yarka miji kaga tana zubda hawaye toh taba kaji in hawayen na da dumi toh lallai yarka bata son mijin da kazaba mata dan haka kada ayi mata auran dole yayi kyakkyawan ajiyan zuciya sannan yace da ita mama ta bakya son auran suleiman ko, kada masa kai tayi da alamar eh, meyasa ko kina da wani ne, kanta a sunkuye yake ta kara ce dashi eh. Toh Shikenan tashi kishiga ciki. Ta barsa a dakin yana ta sake sake a ransa har mama ta shigo ta samesa, Alh. kayi magana da sadian ta amince ko, uhmm a'a, kaman ya bata amince ba saboda meye, ki kyaleta bataso bazan mata dole ba tun da tana da wani amma zan binciki yaron nagani tukun in yadace sai a aura mata koh. Toh Shikenan Alh. Allah sa adace. Tana komawa daki waya ta daga ta kira Ahmad. Hello Asb, bby yane, kalau kaga sai da na fada maka dazu Abba sai ra'ayi na zaibi, ya tambaye ni ko ina da wanda nake so nace masa eh, ok yanzu boss yaja da zancen baya kenan, ni ba nace maka ka daina cewa boss dinnan ba its indecent bakaji, alright zanyi barci, ha'a swthrt ya baka fada min komai ba, idan Abba ya sake tunkara ta da maganan ya zance masa, kawai ce masa kin fadamun mana, kana nufin in yace yana neman ganinka ko katuro ma kana shirye da hakan, of course yes. Tnk u kayi baccin ka sai da safe, kwanciyanta tayi tana mai jin dadi.
Lallai yarinyar nan fa, tana ganin aure zanyi ne a yanzu, waima tunda ni take expecting Zan aure ta ne, ashe ko takama iska. Shima yayi kwanciyar sa.
Can cikin dare suleiman ne ya tashi yayi arwala yayi raka'a biyu yai istihara yana rokon Allah yasa sadiya rabonsa ce kuma shima bayya son takura ta, in har taki yarda da auran toh a kyaleta amma shi har ga Allah yana so ta kasan ce matar sa. A haka ya idda addu'an sa yana neman zabi mafi alkhairi ya kama baccin sa. Sai da aka kwan biyu Abba yasa mama ta kira ummar suleiman ta fada mata abun da sukayi da sadia kuma ta bata hakuri sosai. Suleiman na zuwa gida ummar sa ta sanar dashi sad news dinnan duk da haka bai fitar da tsamma ni a kanta ba zai ci gaba dayin addu'a in rabonsa ne zai samu. A ranan Abba yace da sadia tafada wanda take tare da shin yana son ganin sa. Dadi take ji itama zatayi aure saura Rukaiya da sauran kawayen su.

[7/25, 10:39 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana gani 💝
Written by F K Ahmad
Follow me on wattpad @fkahmad
21 - 22
Suna zauna kan wata benchi a makaranta sadiya na basu labarin abun da ya faru da ita kwanakin nan, Aisha na mata bakin cikin rejecting din suleiman da tayi haka ma Ruky duk tana supporting Asb amma tasan ba kalan na aure bane shi. Hmm baku san wani abu bama ai yanzu haka na kagu naje Asb Abba na yace in fada ma sa yana neman ganin sa. Tashi tayi arikice tana baki da hankali ne sadiya yanxu Ahmad dinnan zakiyi introducing wa Abba itama tashi tayi wai ke Aisha meye ruwan ki aciki ne ke zaki aure sa ne ko ni, bani nazaba zama da shi ba, kuke ganin illar sa amma ni banga wani abun rashin so atattare dashi ba. Toh Allah ya shirye ki kigani wa kanki. Amin ni kun ga tafiyata wajen sa.
Ta iso class dinsu ta tarar suna hira ne da abokansa tagaisa dasu ta samu waje ta zauna, ya tashi yaje ya zauna kusa da ita, ya dai yammata kaman kina da magana koh, eh Ahmad abba ne yace in fada maka yanason ganin ka cikin kwana biyun nan kaga sai ka hada sa da manyan ka ko, zuciyan sa ne ya buga, haba sadia wai ce masa kika yine yanzu kike son yin auren, a'a kawai shi ya fada mun in sanarda da kai, toh nifa gaskiya bantashi yi ba tukun ko kin manta ko makaranta na bai kare ba jarrabawa fa muka sa agaba, nasani amma shi ban fada masa hakan ba, ai sai ki sanar dashi kice van gama makaranta ba sai naje nayi service ma tukun zanyi aure, kai anya kuwa abba na fa idan ya fara abu sai yaga karshen sa ya fiso ayi a gama locaci dadi amma har kake zancan service why not ince masa bayan ka gama final exams dinka zaka turo. Shikenan toh hakan ma yayi, yauwa gara hakan ni zan tafi sai anjima ok bye.
Kai kuna jin yarinyar nan kuwa zancen aure fa take mun wai ubanta ne ya turo ta, gaba daya suka kwashe da dariya, lallai babban yaro zai zama ango za musha biki kenan, ah lallai kam sai de fa angon basai ta kara jinaa ba nagama skul din ai tun a ranan zan sauke ta, ah haba bad guy daka ka mata haka kasata hauka, ai ita tasani wa yace tayi haukan sona. Hahahah.
Har aka kwan biyu Abba baiji komai daga wajen sadiyaba hakan yasa yakira ta yake ce da ita ya naji shiru fa baki fadamin komai gamida yaron da nace Kituro ba, eh abba nafada masa daman yana makaranta ne shiyasa, hade giran sa yayi uwata daman karamin saurayi dan ajinku kika janjabo mana, a'a abba ya girme nifa yana final year su zasu gama fa yanxu, hmmm yayi kyau kina nufin sai yagama zai turo iyayensa eh abba, toh Allah ya kai mu baifi wata biyu ku gama exams dinku ba ai.
Tun daga locacin suleiman bai damu ba babu ruwan sa yana zuwa gaida iyayen sadiya bayan kwana biyu haka ma inna yana shigo mata aka ci gaba da sada zumunci babu laifi.
Bayan sati biyar
Yaune last paper din su Ahmad, har yagama project dinsa an masa signing ya gama komai.
Last three weeks akayi relocating baban sa wajen aiki suka koma Lagos, shima jira yake yagama jarrabawan sa zaibbar maid a yau. Flight na dare yayi booking, duk wannan bai sanar da sadiya ba.
Sadie tun shekaran jiya suka gama nasu papern gashi sai kaudi take yau zata je taya asb murnan gama bokon sa, ta shirya masa graduation gift nasa. Ta daga waya zata kira Rukaiya ta raka ta skul zuwa dinner din su Asb sai kuma ta fasa dan tasan zata fadawa Aisha sumata shishigi.
Around 3pm tagama shirinta tsaf tana gaban mirror sai juye juye take ta yafa gellen ta tadau hand bag nata da waya sai dakin mama. Toh mama sai nadawo su ruky na jira na awaje toh sai kun dawo. Dama can karya ta mata akan zasu je gaida wata kawar su ba lafia.
Tana isa skul din ta kira sa awaya, ya fito ya sameta, tun kafin tadawo suke ta haukan celebrating gama makarantar su dan da safe suka gama papern su. Congratulations swthrt, tnk u dia here is ur gift ta ciro wani karamin box daga jakarta ta mika masa. Wrist watch ne aciki, wow! Beautiful tnk u. Mention not ta ciro waya ta kashe musu selfie's sunyi kyau abun su.
Bakin kofar hall din suka je su, group na yammata kala kala na tsaye a wajen sai gulman su sadie ake ana pointing dinsu. Wata hadaddiyar beb ce tazo ta gaban su oh congrats dia zata kai masa hug shima yakai hannun sa tadaka musu tsawa tare da ture yarinyar meye haka, wanke ta da mari tayi gaba daya aka yo takan su, suka taru wa sadie dama haushin ta suke ji sai fada suke, shiko ya jaa tsaki ya bar wajen su. Da su kaga babu wacce ya tankawa acikin su dan kansu suka daina.
Itama binsa tayi zuwa hall din alocacin har an fara wasu events din ma, ganin sa tayi zaune da wata a gefensa hira suke har yana mata dariya kokarin kama hannunta yake kan tace meye yakai bakin sa yayi kissing bayan hannun ta, da sauri tayo kansu, tazo dab dasu taji yace love you dear, bata san sanda hawaye suka ciko mata ido ba.
Tunda take tare dashi bata taba jin haushin sa ko ganin munin halinsa ba sai yau, duk da ana fada mata halayensa, kuma ita kanta tasan da yawan yamma tan sa da yake hulda da su harma agaban idonta yake kula su amma babu wanda ya kona mata rai kaman na yau. Sai ta tuna locacin da Aisha ke ce mata you don't deserve to be with ASB take share ta sai kuma ta girgiza kanta no way, i trust u asb kawai dai hakan yaza me maka habit ne but nayi alkawari zan canja ka Ahmad, zaka zo hannu na, ta goge guntun hawayen ta da yake rolling a fuskar ta, taje kusa dashi.

[7/25, 10:39 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana gani 💝
Written by F K Ahmad
©Mikiya Writer's Association
Follow me on Wattpad @fkahmad
23 - 24
Ahmad! A dan razane ya juya yana kallonta, lafia? Kada masa kai tayi, ki zauna mana ko baki ga an fara programs bane, yaja mata kujeran kusa da shi ta zauna suka sashi tsakiya, ita wancan ta dayan side din, haka take satan kallon dayan hannun sa da yake rike da na yarinyar ita ko yasan bata barin sa ya taba ta shiya sa baiyi karan banin hakan ba.
Bayan an tashi ne suka fito tare harda yarinyar ko uffan batace da ita ba har zuwa locacin. Sai yammata ke zuwa wishing dinsa da comments daban daban yana jin kansa on top. Yagama ban kwanan sa da abokan sa da duk kowa na wajen yace da su sadiya su tafi kar dare ya musu zaiyi dropping dinsu, tana kallo taji yace Salma u can get to d front seat, haka ta bude kofar gaba yashige, aranta ta nana sunan salma koh zanyi maganin ki, tashige bayan motar su katafi. Babu wanda ya kula juna ahanya har suka iso kofar gidan su sadiya ya sauke ta tace tnk u Asb sai munjitu, ok zan kira ki bye ta daga masa hannu yana kashe mata wani mugun smile ya ja motar sa da salmar sa a gaba suka wuce.
Sai da aka share sati biyu sannan mama ke ce wa abba ni yanzu sadia ba yaka mata tace da saurayin nan ya turo magabatan saba dan naga sun gama exams din sannan tace shi ya ma ga makarantar wannan karan, abba yace nima din haka naga ni, toh bari ko anjima na fada mata kace kace ya turo ziwa jibi, eh hakan nada kyau dan dai bata ji dadi ba kwana biyu, tagama shan magungu nan ta taji sauki ai bari na sameta.
Karatun Qur'ani take a dakin ta, kallo daya zaka mata kasan ta rame sosai sanadiyar zazzabin da tayi. Mama tayi sallama ta shigo. Sai da takai karshen ayya ta ansata, zama tayi kusa da ita ta kira sunan ta, sadiya ina Ahmad haka naji kike kiran sa ko, da mama ki ta kalli mamarta yaushe tasan sunan sa sai kuma ta fashe mata da kuka, lafia me ya same ki kuma, ta rungume ta tana rarrashin ta, ba wani abunne yasa natam bayesa bafa sai albishirin da nazo miki dashi, Abban ki ne yace ki fada masa ya turo iyayensa ayi maganar auran ku. Amma inaa sai kukan da taci gaba dashi tana batasan inda ahmad yake ba cikin satin biyun nan, mama ma saida ta rikice, bakisan inda yake ba kaman ya, ta kasa fada mata komai haka tayi ta rarrashin ta har tayi shiru sai ta kyaleta ta huta tukun tafada mata abun da ke faruwa. Tafita tabarta adakin jiki sanyaye.
A hankali ta kwanta ta lumshe idanunta ta fara tuna a bubuwan da suka faru tun ranar dinnern su asb da ya sauke ta a mota yatafi toh bata kara ganin sa ko jin muryan sa ba numbern wayar sa bata shiga tun a daren ranan, haka take ta faman dailing numbern akai akai amma shiru gashi kuma batasan gidan su ba balle taje ko tasan abunyi. Ita kadai ke cikin yanayin nan tarasa me zatayi tana son sanarda friends dinta amma sanin kaman Aisha ba kula ta zatayi ba akansa yasa bata fada mata ba, da kyar ta iya fadawa Rukaiya, ta taya ta jimami sannan tazo mata da wata shawaran kiran abokan sa tace batada numbern ko wannan su. Tabdi bari na duba call log dina inaga zan samu numbern hamza abokin sane ya kira ni kwana kinnan kuma banyi saving ba. Suna samun digits dinsa suka kira sa yace dasu tun rabuwan su daga dinner kaf cikin abokan su babu wanda yasa ke ganin sa ko jin sa a waya. Haka taci gaba da damuwa har ya haddasa mata zazzabin nan amma yanxu da sauki.
Zara ce tashigo ta katse mata tunanin da ta tsun duma aciki, ya sadiya kisha maganin ki locacin sa yayi inji mama, tadauko sa kan drawer ta balla mata biyu ta mika mata da ruwa ta karba tasha.
Bayan wasu mintuna mama ta kara zagayo ta, lallaban ta tayi tasamu tafada mata duk abun da ya faru har sai da ta tausaya wa yarta. Taje tasamu abban su ta labarta masa komai. Abba yace toh bata baci ba tunda tana da wani ma nemin, ni dama ga suleiman dinnan hankalina yafi kwanciya da shi, ai nima din Alh. yanzu kam zata amince masa ai ko bata yarda ba sai anyi auren dan ni ma shidin nake so, ta tashi ta barsa a dakin.

[7/25, 10:39 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji bana gani💝
Written by F k Ahmad
25 - 26
Saida washe gari bayan abba da mama sun gama shawara, mama ta daga waya ta kira umman Suleiman, sukayi gaisa as usual, ya surkin nawa Allah Sa dai bai canja ra ayi ba, Saida umma ta danyi dariya tace shi da akullum addu'an sa Allah yasa rabonsa ne dan bai fitar da tsamma in ba, toh alhamdulillah, itama sadian Wanda take ce sai shi din ma babu labarin sa tun ranar da suka gama bokon sa taji sa shiru da alamun dai yaudaran ta yayi. Allah sarki bakomai Allah sa hakan shine mafi alheri, in Allah ya yarda ma. Wannan kice yau dana zai kwana cikin farin ciki, dariya tayi sukayi sallama.
A bangaren Suleiman ko da umman sa ta sanar dashi farin ciki babu iyaka har Saida yayi sujjada Ya gode wa Allah, Ji yake kamar ma an daura musu auren ta zama matar sa sabar murna, har ya daga waya zai kira ta Kuma sai ya fasa dan ya rasa ta ina zai fara nuna mata farin cikin sa. Shi soyayyar da kansa ma baisan ta ina zai fara nuna mata ba dan ji yake tana masa kwarjini yanzu, ya zauna shi kadai yana murmishi yana imagining tazo masa da nata kalamun soyayyar tana mai jin kunyar sa Kuma.
Sadiya na zaune zai chatting take taji saukin jikin ta sosai. Abba da mama ne suka same ta. Abba sannu da zuwa yauwa uwata ya jikin naki da sauki, Sadiya inaso ki saura re mu da kunnan basira kina Ji na, eh mama. Maganar Suleiman muka zo miki dashi, batayi tsammanin mummunar labarin nan daga wajen su ba badan iyayenta bane su da bazata saura re suba , haka ta sunkuyar da kanta tana jin su, mai zai hana kiyi hakuri ki aure sa ina laifin dan nan kinfi kowa sanin halayen sa na kirki fa babu Wanda ya kaiki shakuwa dashi, abokin kine fa amma kwastam sai ki kisa dan za'a hada Ku aure ban zaci hakan daga gare ki ba kiyi tunani mana kinsan za kuyi zaman lafia tare, wanda yasan darajar ki da kiman ki baza ki yarje masa ba, kar ki manta mu kanmu ya dauke mu iyayensa, kiyi la'akari da wannan ki dubi yadda yake kulawa dake anan kinsan zaki samu fiye da haka a gidan sa, ki amince masa kinga yanzu abban ki ya yarje masa, iyayensa za suzo saka ranar auren jibi. Dudum zuciyarta ta har ba. Kinji dai abunda mamar ki ta fada ko, eh abba nagode yauwa Sadie ta mama ta shafa kanta suka barta a dakin.
Tsuman zaune tayi hawaye na ambaliya a fuskar ta, taya zan sosa, da wani idon zan kalle sa, Wanda nayi zaman yaya da kanwa dashi Kuma zanyi zaman mata da miji. Kai wato tundaa fa kallon munafirci yake mun ba kanwar sa ba, dan kauye ma irinsa wai shi ustaz mtsw. Nikam nawa ta kare Idan nashiga gidan sa takura no zaiyi babu fita kullum Sai hijabi da manyan kaya babu kwalliya na zama matar mallam kenan sai wa'azi zai dinga mun kullum, Kuma zai raba ni da kawaye na. Wayyo Allah na auran ustaz ko takura na shiga uku sai ta fashe da Kuka.
Shi ko Suleiman kasa zuwa wajan ta yayi a ranan har washe gari ma aiki ne ya masa yawa a office bai samu zuwa ba.
A yau ne aka kawo kayar tambayar auran sadiya Kuma akasa rana wata biyu daidai. Kaya kam masha Allah yayi niki niki, ga jama'a sai shigo dashi suke. Lekan su take ta window ita kam dan ta kaici ko sanar da su Aisha bata yi ba sai mama ce ta fada musu, ruky ce ta samu zuwa Aisha kam ita ma ta kusan zama Amarya nan da sati shi yasa bata samu zuwa ba.
Baban Suleiman da yan uwa da abokan arziki sun samu tarbuwa mai kyau daga wajen jama'an Abban Sadia duk sun jinjina wa kansu sunji dadin sa. Ahaka suka gama komai lafia kalau suka watse.

[7/25, 10:39 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji bana gani💝
Written by F k Ahmad
27 - 28
Ruky yanzu na rasa Asb kenan ake nufi, wannan malamin zan aura kinsan ka'idan su kuwa, Sadie hakuri zakiyi ba duk suka taru suka lalace ba ke da kikayi zaman tare dashi ma ai baza arasa halayensa da kika

Please Login or Register in order to submit comment