Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"idan kika kara shiga gona ta sai na illataki", sakamakon zafin mari da Maryam taji ta daura hannun ta wajen marin tana kallon Sadiya dan ta kasa furta mata wani kalmar.
Sadiya ta juya za ta bar wajen kenan sukayi ido hudu da ummar Suleiman. Baki na karkar wa tace "umm umma sannu da zuwa kin dawo lafia?" Umma tace "da ba lafia ba zaki ganni anan ne, iyee mara kunya irin halin da kike acikin gidan kenan? kinyi abunda ba daidai ba baza'a gyara ki ba kuma ashe tun da kina cutar mun da d'a ban sani ba, toh wallahi na fada miki kiji kika sake daura hannun ki akan Maryam dan naji kalmar da kika yi amfani da ita na sai kin illata ta toh kisan zaman ki ne ya kare acikin gidan. Tunda Umma ta fara maganar kanta na sunkuye akasa. Maryam ne tazo ta kama ta tace "Yi hakuri Umma sannu da zuwa, yaushe kika shigo ne? muje daga ciki", "yo dama ina za kuji ni kuna wannan hayaniyar taku", suka wuce ciki.

[7/27, 9:56 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana Gani💝
Written by F k Ahmad
Pure Moment Of Life Writer's
Dedicated to sweet lovely but naughty sister Falmata k Ahmad. LYSM😜
51 - 52
Ko da Umma ta koma gida kiran Suleiman tayi a waya ta gaya masa abunda taje ta tarar a gidan sa kwata kwata bai ji dad'in sa ba. Zuwa d'akin ta yayi ya same ta tana nad'e kayan ta ya zauna a bakin gado yace "Sadiya, Umma ta gaya mun abunda kukayi da Maryama, baki kyauta ba Maryam na son ci gabar ki ne bawai dan jin dad'in ta bane ta miki magana, tana sonki da alkhairi ne nan gaba kar ki k'ara abun da kika yi dan Umma da kan ta bata ji dad'in hakan ba". Bud'ar bakin ta tace "ka taya ni bawa Umma hak'uri bazan k'ara ba", sosai ta basa mamaki dan baiyi expecting za tayi nadama ba, dad'i yaji ya taso yayi pecking goshinta yace " Allah yayi miki albarka", ya fita. Sai da ya fita taja wani dogon tsuka tace "aikin banza".
Washe gari Maryam na kitchen tana had'o musu breakfast Sadie ta shigo ta same ta tace da ita " ina kwana Maryam", murmishi ta mata sannan tace "mun tashi lafia?" "Lafia kalau, ya aiki?" "Gashi muna fama, Sadia ki yi hakuri da bata miki rai da nayi jiya", "a'a Maryam ni ya kamata na bak'i hak'uri ba ke ba", "a'a kar ki damu babu komai ai babu wanda yafi karfin kuskure a rayuwa", "nagode, bari na taya ki soye soyen" ta d'au masami ta saka a cikin mai.
Watan Maryam hudu kenan a gidan. Ranan ta tashi bata ji dad'in jikin ta ba suka je asibiti da Suleiman aka tabbatar musu da juna biyu take d'auke da shi na wata uku. Murna a wajen Suleiman kaman wanda aka yi wa wahayin shiga aljannah, a ka basu magungu na suka koma gida.
Da suka zo gida Sadia bata nan tana makaranta, yaso ya fara sanar da ita dan ta taya su murna, barin Maryam a gida yayi yaje sa sanarda da Umman sa.
Maryam na kwance kan three seater taji tana son shan tea ta tashi ta je ta dinning ta had'o zata je ta zauna kenan kofin ya sullub'e a hannun ta ya fadi ya zube gaba daya akan tiles, taci sa'a kofin roba ne bai fashe mata ba. Kitchen taje ta dauko bucket mai ruwan omo aciki dayan hannun ta kuma mop take rike dashi saida ta goge wajen zata juya ta mayar bata gani ba ta ture bucket din ruwan cikin ya zube tsantsi ya kwashe ta wata mahaukaciyar ihu ta zabga bata ankara ba tafad'i kan cikin ta ragajab da karfi bata sake motsa wa ba sai numfashin ta da yake fito wa kasa kasa.
Suleiman na sanar da Umma farin ciki kal a fuskarta ta kasa b'oye wa, ta kusan yin jika tace da shi "zauna na kawo maka abinci kaci ko baka jin yunwa yau sai kaci girkina". Dariya yayi "Umma ni dama k'ewar girkin ki nake kuma banci bamnaugtyito a gida ina hanzarin nazo na fada miki", "dai dai ma kenan bari na zubo maka."
Baifi minti talatin da abun da ya sami Maryam ba Sadiya ta turo kofar falo ta shigo, jini ne taga ya malalo har zuwa kofar shigan, zuciyar tane yayi matukar tsinke wa tana bin jinin daga wajen zuwa ta inda yake fitowa sai salati take tana Allah yasa lafia dai, can kusa da kitchen tagan ta kwance cikin jini kaca kaca, wani razanan nan ihu ta saka ta karaso wajen ta taba ta, Maryam, shiru Maryam jijjiga ta tashiga yi babu alamar zata motsa, ta d'ago kan Maryam tagan sa afashe sai jini da yake zuba, kuka ta saka ta nemi wayan ta ta kira ya Suleiman, bai b'ata locaci ba ya d'aga, kukan ta kawai yake ji ba ya gane abunda take dad'i sai sunan Maryam daya ji ta ambato kuma tace yazo yanzu. Hankalin sa ne ya tashi ya bar abincin sa da yake ci, Umma na tambayar sa lafia yace "Maryam Umma, Maryam ce", "me yasa meta?" "Ban sani ba Umma muka rasa gidan". Da sauri ya d'auki mukullin motar sa suka nufi gidan.
Sadiya ta had'e kai da guiwa ta zauna kusa da ita sai kuka take, suka bude kofar suka shigo, da gudu tayo kan umma ta k'ank'ame ta dan atsorace take gaba daya, Umma kuka ta fara dan ganin abun tausayin nan, "shike nan cikin ya zube wayyo ni Fati", ta daura hannu akai. Suleiman ya k'inkimo ta da wuri ya kai ta motor suke je asibiti.
Emergency ward akayo da ita, likitoci suka shiga yi mata aiki da gaggawa, wani babban likitan da yake tsaye kusa da ita ne yaji tayi dogon numfashi yace da sauran "Ku daka ta", wasu gwaji ya mata result ya nuna ta riga da ta cika. Cire gloves na hannun sa yayi ya kad'a musu kai ya fita daga d'akin. Su Suleiman dake jira a kofar d'akin suka taso " Doctor ya jikin mata ta?" Ya dafa kafad'ar sa yace "am sorry, she's no more". Hawaye suka fara ambaliya a fuskar Suleiman yace " innalillahi wa innailaihi raji'un" ya shiga d'akin da gudu dan ya tabbatar wa kansa. Sauran likitocin suka fice suka basa wuri.
Sadiya da take tsaye kafafun ta suka kasa d'aukan ta ta sulale kasa tana rusa kuka. Umma sai salati zalla take tana hawaye. Addu'oi ya mata ya shafe fuskar ta sannan yaja farin k'yalle ya rufe ta dashi. Umma ta juya ta kalli Sadiya tana kuka tace "nasani, ai tun da kika furta mata wannan kalmar nasan zaki aiwata abunda kika fad'a yanzu burin ki ya cika da kika aika mun Maryama lahira". Suleiman ya tazo a rikice yana kallon ta yace " Umma! Me kike fad'i haka?" Tace ban fad'a maka bane wannan yarinyar tayi pointing Sadiya ta tab'a cewa za ta illata Maryam a gaba na ta fada". Sadiya da tayi suru suru da ido ta fara ja da baya tana girgiza kanta , Suleiman ya mai da kallon sa zuwa kanta, unbelievingly ya ke kallon ta yace "Sadia!"
*kuyi hakuri da wannan*

[7/28, 10:05 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana Gani💝
Written by F k Ahmad
Pure Moment Of Life Writer's (P.M.L)
_We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers._
Rukayya k'awa! Am sorry for the late wishes, never knew it was your day yesterday but can't keep moving without me saying Happy Birthday my dear. Wish you Allah's khair and blessing, this page is dedicated to you.
53 - 54
"Bani na kashe ta ba ya Suleiman, Umma ki yadda ba ni na kashe Maryam ba, ya Suleiman kasan bazan iya kinsan kai ba dan Allah ka fada mata wallahi zuwa nayi na tarar da ita acikin wannan yana yin sai na kira ka a waya, me yasa zan aikata hakan me Maryam tamun, tunda tazo gidan kasan muna zaman lafia", "da Allah rufawa mutane baki, ranar da naje na same ku shima cikin zaman lafian yake? Kawai dan kinji tana da juna biyu ke kin kasa d'aukan ciki shine kika ai kata hakan?" " Umma sab'ani aka samu ranar, ya Suleiman ai daga baya mun shirya ko? Kuma maganar ciki wallahi ban san tana da shi ba". Umma ta fita ta bar d'akin, Suleiman hannu ya d'aura a kansa ya zauna he's all confused ya rasa ya zaiyi, Sadiya tazo ta durkusa a gaban sa tana kuka ta kasa magana.
Umma ce ta bankad'o kofar ta shigo ta nuna Sadiya tace "gatanan ku shigo", a razane Suleiman da Sadiya suka tashi dan ganin abunda basuyi tsammani ba. Police biyu ne suka biyo bayan ta, d'ayan ya ciro handcuff ya ce ta saka hannun ta ciki, baki ta bud'e ta d'aura hannun ta akai ta shige bayan Suleiman da dugu", Suleiman yace "Umma me kike yi haka bai kamata ki...", "rufa mun baki, kayi shiru na ce, idan ni na haife ka kar kasa ke yin magana, babu abun da kasani, da ido na nagani kuma naji da kunne na dan haka ka matsa su tafi da ita", Sadia da ta gama tsorata gaba d'aya ta kid'i me sai kuka take ta kama rigar Suleiman tana "ban kashe ta ba Allah ku yarda da ni, ya Suleiman kar su tafi da ni zasu kashe ni", ta juya ta kalli Maryam tace "Maryam ki tashi ki fada musu bani na kashe ki ba, za su kashe ni nima", " wai me kuke jira ne ku fita da ita mana", "Umma kiyi hak'uri...", "k'ul na hana ka magana kar ka sake". Suka kamota har suka je kofar fita ya na kallon ta babu yadda ya iya sai hawaye da suke sauko masa, ta kama handle na kofar tana k'wala masa k'ira " ya Suleiman kazo ka karb'e ni dan Allah, nasan yadda abun yafaru zan gaya maka amma banyi kisan kai ba". Yadda tayi maganar kasan ta galabai ta da kuka sosai, Jan hannun ta da d'ayan police d'in yayi sai ta fad'i sumammiya a wajen. Da gudu Suleiman yaje ya d'aga ta arikice yake kiran sunan ta"Sadiya, Sadiya ki tashi kar ki mutu dan Allah kar ki tafi kibar ni ki tashi" ya fashe da kuka, dayan Police din ya kira wata nurse akayi rushing dinta zuwa emergency room. Within some minutes aka bata taimakan gaggawa amma bata farfad'o ba dan an mata allurar bacci dan ta samu hutu.
Suleiman da Umma suka je gida da gawar. Yamma tayi dan haka sukayi fixing jana'izar ta zuwa gobe da safe. Daga nan suka sanar da y'an uwa da abokan arziki sannan Suleiman ya fad'a wa Mamar Sadiya abun da ya same ta, Mama taje ta kwana da ita a asibiti.
Washe gari da sassafe kafin locacin jana'iza Suleiman yaje shi duba Sadiya a asibiti amma har locacin bata farfad'o ba, Mama ta bar Zara a kanta ta wuce jana'izar.
Sadiya bata farfad'o ba sai can yamma kuma likita yace baza a sallame su ba dan tana neman k'arin ruwa dan haka suka ci gaba da zama a asibitin.
Ummar Suleiman ta dage ita sai ankai Sadia Station dan bata yarda babu hannun ta cikin mutuwar Maryam ba. Iyayen Sadiya Sam basu ji dad'in yadda ummar Suleiman take acting ba sun san duk rashin hankalin y'arsu ba zata aikata kisan kai ba.
Da daddare Suleiman ya kwanta bacci amma ya gagara yinsa sai tunanin duniya da ta masa yawa. Maryam has gone and on the other side Sadiya na asibiti kuma ga rigimar Ummar sa, kab ya rasa ya zaiyi. Hak'ika ya zauna da Maryam na y'an wasu watanni ne amma yaji k'aunar ta tashige sa sosai badan komai ba saboda biyayyar ta agareshi. Tashi yayi ya zauna sakamakon tuno last word da Sadiya ta fad'a kan ta suma 'nasan yadda abun ya faru zan gaya maka', dafa goshin sa yayi yace "oh shit, me take nufi da tasan yadda abun ya faru, oh my Allah dole naje na same ta gobe da safe", addu'a yayi ya kwanta da k'yar bacci ta d'auke sa.
Washe gari da yaje shi gai da Umma kafin yaje shi asibitin yace da ita "Umma kiyi hak'uri ki ja da maganar kulle Sadia baya dan Allah", "ka bud'e kunnuwan ka kaji ni da kyau, idan har na k'yale Sadia to zaman ta agidan nan tabbas ya k'are", "me kike nufi da hakan umma?" "Ina nufin sallaman ta zakayi, eh sakan ta ya zamo wajibi Suleiman", zazzaro idanun sa yayi " Subhanallahi, Umma!" "Eh, dan haka kulle ta za ayi". Ta fice tabar sa a d'akin, ya bita da kallo.
Da yaje asibitin suka gaisa da mama ta fice ta basu gu. Sadiya na kwance da ta gansa ta tashi ta zauna da tai makon sa tace "nagode", ya zauna kusa da ita sannan yace da ita " ya jiki?" Tace "da sauki", "Sadiya nazo ni jin yadda incident na mutuwan Maryam ya faru, ki gaya mun gaskiya nasan abun da Umma ta fad'a ba haka bane", hawaye suna rolling kasa a fuskar ta ta zai yana masa abunda ta gani a locacin da ta je ta tarar da ita kuma ta masa baya nin fad'uwa tayi a bisa dalilin zube wan ruwan omo.

[7/30, 5:19 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana Gani💝
Written by F k Ahmad
Pure Moment Of Life Writer's(P.M.L)
_We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers._
Kuyi hakuri da rashing posting ina jiya.
Felt so much loved for the dedication, tnk u so much Aisha(_lady Fulani_). Allah ya d'au kaka book d'inki (HADEEYA).
55 - 56
Jin jina kansa yayi "nasan baza ki iya aikata hakan ba amma bansan ya zanyi nayi convincing Umma ba and you see she's my mother amma bari naje na same ta". Yatashi ya bar asibitin.
Da yamma ya koma wajen Umma bai same ta agida ba sai ya koma gidan sa nan ma bata nan ya d'aga waya zai k'ira ta sai yaga 6 missed call na Sadiya bai ga k'iran ta ba ne saboda ya bar wayan ya fita, da yayi trying nata bata d'aga wa, yayi ta k'ira amma shiru sai ya k'ira layin Mamar ta ko suna tare ita ma bata d'aga wa, hankalin sa ne ya tashi yayi gagga war zuwa asibitin.
Yana iso wa tun daga bakin gate din yaga ana shigar da ita cikin motar police tana rera kuka, ga Mamar ta ma kukan take Ummar sa kuma tare da police d'in suke. Da gudu ya fito daga motar sa yana approaching d'insu yana d'aga musu hannu su tsaya amma da yake tsakanin su da d'an rata har suka fice daga harabar asibitin basu gansa ba. Ya iso wajen Mama da ta durkushe tana kuka yace " Mama ki daina kukan ina tare dake, taso muje mu same su a station d'in", "Suleiman Ummar ka ta kasa tawakkali akan abun da ya faru, mun rasa ya za muyi", "kar ki damu Mama ina tare da Mata ta nasan baza ta aika ta abun da Umma ke zarginta akai ba, yanzu muje musa me su tukun" suka fice.
Suna isowa can, har Umma ta gama filling na case d'in an wurga ta cell na cikin station d'in. Abban Sadiya ma ya shigo wajen ya isosu dan Mama ta sanar dashi yazo ya same su.
Suleiman yaje wajen Ummar sa da dugu" Umma kiyi hakuri kibar wannan maganar ta wuce mana kin manta ni mata ta ce narasa amma ban damu kamar yadda kike yi ba", "ai dole ka fad'i hakan dole kace mun kar na damu, shi kenan tunda kai ka kasa bi mata hakkin ta a matsayin matar ka toh ni ta wuce hakan a waje na dole a bi mata hakkin ta, kai matar kace kawai amma ni y'ar yar uwata ce wacce iyyayen ta suka mutu suka bar mini ita amma kakar ku ta karb'e ta dan bata son zama ita kad'ai zata na d'eban mata k'ewa, idan nagan ta tana tuno mun da y'ar uwa ta kuma ka fa san da hakan amma kayi watsi dashi" ba haka bane Umma hak'uri zaki yi a fitar da Sadiya cikin wannan halin", toh naji zan hak'ura amma da sharad'i", eh Umma ki fad'a ko ma mene ne zan miki amma dan Allah mata ta ta fita acikin nan kuma ta samu kwanciyar hankali", "Suleiman idan ba manta wa kayi ba nagaya ma d'azu da safe akan idan na k'yale Sadia to ka bata takardar ta kenan". Dudum zuciyar sa da na Mama ya tsinke, ya juya ya kalli Mama sukayi ido hudu ta sauke nata idon. Abba kuma da yake kallon Umma yayi murmishin b'acin rai yace " kin kyau ta Hajiya Fatima", Abba ya dafa kafad'ar Suleiman yace dashi "Suleiman hakika na yaba da kai amma yanzu abunda ya ka mata shi ne ka aiwata abun da mahaifiyar ka ta fad'a dan koni nafison hakan akan wannan musibar". Mama ta d'ago ta kalle sa tace "Alhaji haka kuma za'ayi", ya daga mata hannu alamar ta dakata". Suleiman da har hawaye sun sauko masa yace "Abba kayi hakuri bana son rabuwa da mata ta ina son ta, na rabu da Maryam yanzu kuma kar ku raba ni da Sadiya itace farin cikina", ya juya ta b'angaran Umma "Umma ki tausaya mun dan Allah ki bar Sadiya ta zauna dani", Umma tace "toh lallai zata ci gaba da zama anan kenan". Dafa kan sa yayi ya zauna dambar a kasa. Abba yace dashi "Suleiman babu komai kayi biyayya ga mahaifiyar ka kar ka ba'ta mana locaci zamu tafi ina da uziri kafin magariba. Da k'yar ya iya bud'an bakin sa yace " toh shikenan" muryan sa na rawa ya furta kalmar "NA SAKETA". Mama ta lumshe idon ta ta furta " innalillahi wa innailaihi raji'un". Abba yace Alhamdulillah yaje yayi bailing y'ar sa Mama taje ta jata zuwa motar su ka tafi gida.
Suleiman ko kasa tashi yayi awajen Umma kam tafiya tayi tabar sa a cewar ta wai in ya gaji zai biyo bayan ta.
Akwana a tashi watan Sadiya guda kenan a gida, babu ruwan ta, taci gaba da rayuwar ta normal babu abunda ya dame ta da ta rabu da Suleiman dan acewar ta ma ta yar da k'wallon magwalo ta huta da kud'a, ko idan su Aisha suka mata maganan ta koma d'akin ta ba jin su take ba.
Suleiman ba karamin rama yayi ba cikin wata d'ayan nan, abun ya da mesa sosai ya za a masa 2 zero? Abinci ma sai Umma tayi da gaske yake ci. Yau Baban sa ya dawo da ga tafiya dama can baya gari kusan watan sa biyu kenan dan baya nan ma duk wannan haya gagar ta faru kuma babu wanda ya sanar dashi a cikin su kawai dai yasan rasuwar Maryam kad'ai ne.
Abba ya sha mamakin ganin sa a gida kuma me ya ramar dashi haka. Sai da ya huta tukunna ya tambaye sa, bai b'oye masa ba ya fad'a wa mahaifin sa duk abun da ya faru. Ya tausaya wa d'ansa sannan yace "tabbas Ummar ka tayi rashin hankalin su na mata kuma kaima da naka laifin da ka k'ira ni ka sanar dani things would not have been worst, dan yanzu sai da yardan iyayen ta zata koma amma kafara ji daga bakin ta ko tana son koma wa gidan ta sannan musan abun yi", "nagode Baba". Suleiman ya tashi yana jin dad'i.
Ta fito daga exam hall kenan zata je department d'insu ta sami friends d'in ta dan sun rigata gama wa. Sun fara exams d'in tun last week. A hanyar tafiyar ta sai taga abokan Asb suna tafiyan su da gudu ta ka rasa wajen su ta baya tana murnan ko zata ji wani information akan sa, su basu ganta ba kafin ta bud'e bakin ta ta musu magana kawai ta tsaya cak sakamakon jin hirar tasu da ya rikitar da ita, dayan su yace "nikam ka gane y'ammatan da muka gansu d'azu kuwa?" "Ehh toh, fuskokinsu dai looks familiar", " friend's na beb d'in ASB ne ai, ni yama sunan ta?" "Ka kyale zancan nan dai kawai", " Ahmad dan iskan yaro ba, ko kasan cewa har yanxu yarinyar batasan inda yake ba?" "Saboda me fa?" "Au baka san labarin ba kenan, ai yarinyar sashi a gaba tayi sai ya aure ta shi ko bai da niyyar aure baisan ya zaiyi da ita ba Allah ya kawo mafita akayi wa old man d'insa transfer zuwa Lagos, yanzu yana can kuma yaki sanar da ita kawai disappearing yayi daga life d'inta", " kai dan Allah, haka ya faru dama? Gaskiya bai k'yauta mata ba". "Hahaha, ai aganin sa wai ba tsarin shiba ce kawai dai yana tare da ita but ba auren ta zaiyi ba, ka duba duk shan wankan ta fa kuma y'ar masu shi amma yace ba tayi mar ba?" "Ai karshen dan iska ne yaron, tama yi sa'a da ya k'yale ta haka bai lalata ta taba", " ai inaga abun da ya raba sa da ita kenan dan bata basa daman hakan", "toh Allah ya tsirar da ita maa ai", " kai ka masan ya aka k'ara sa kuwa? Hana mu yayi mu fad'a mata any info. akan sa fa, chanja sim card d'insa yayi yace kar mu fada mata inda yake ko ba da numban sa, Allah ma ya so ta tayi aure yanxu", "yauwa barkanta da ta samu tayi auren".
Durkusa wa tayi awajen har kasa ta fara rera kuka mai tsuma zuciya da tsantsar nadama cikin ta, kukan take tayi tana kallon su suna tafiya har suka b'ace da ganin ta. Ta zama abun tausaya awajen duk masu wuce wa suna kallon ta. Sai da tayi kukan mai isan ta sannan ta tashi ta nufi wajen Ruky da Aisha.
Suna ganin ta cikin yanayi da take suka gane tana cikin damuwa da rashin hankali. Kan Aisha ta fad'a tana kukan da k'yar suka rarrashe ta tayi shiru sannan ta labar ta musu abun da ya faru kuma ta fashe musu da wani kukan. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" kawai Aisha ta iya fad'a, Ruky tace "Sadia karki manta idan musiba tazo miki innalillahi wa innailaihi raji'un zaki na mai mai tawa", " nasani Ruky abunda yafi bani haushi me yasa tunda banji labarin nan ba tun kafin miji na ya auro Maryam ya kamata nasani gashi yanzu nayi sanadin rabuwa da miji na da ba'a auro Maryam ba Umma baza tamun sharrin ni na kashe ta ba har yayi silan rabuwa na da ya Suleiman, Asb ya cuce ni, Allah ya isa tsakani na dashi". Aisha tace "ya isa haka, ai naga tun abun bai b'aci ba ina miki maganar gyara sai kice ke bakya ji bakya gani ko, toh kin ga abun da ya haifar saide Allah ya tsare gaba". "Wallahi nayi nadamar sanin ASB a rayuwa na, na tuba yanzu idan har miji na yane ma

Please Login or Register in order to submit comment