Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

[7/25, 10:39 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana gani💝

By F K Ahmad

Happy sallah to all my friends over the globe. Wishing you a very blessed eid celebration. Love you all.😘

Dedicated to each and every friend of mine.

01 - 02
Kwance take aranar wata asabar bisa kan gado cikin dakinta da kanwarta zara sai sharara baccin ta take hankali kwance.
Kamar karfe takwas na safiya sai taji ana knocking a kofar dakin tare dayin sallama.
Zara ce tsaye a kanta zata tashe ta,
ahankali tajuyo da kanta zuwa kallon kanwar tata suka yi ido hudu sannan take ce mata kin manta ne yau baba hadixa bazata samu zuwa ba tafada wa mama suna bikin 'yar kaninta toh gara kintashi kin warware gacen wanke wanke na jiranki mama tace kar rana yafito kije kiyi ta.
Daga hakan tayi juyawarta tafita.
Ita ko har yanxu baccin ba isarta tayiba batason tashi wa.
Da kyar tayi kokari ta tashi ta nufi toilet tana yar maganganun ta kasa kasa tana cewa ita batada hutu kenen yau bbu makarantar ma bazata samu barci ba dama kasancewar ta tsani yin wanke wanke a rayuwarta gara mata shara sau dubu.
Fitar ta falo ta tari mamar tasu,
ta gaisheta ta amsa mata cikin muryar zolaya take cewa yau su sadiya ansha bacci kenan cikin nata muryar shagoba take cewa bawani mama wai ita baba hadixa sai ranarda mutum yake bukatar hutawane sai tace bara tasamu zuwa ba.
Mama tace mata to ai mungama aikin gidan ma wanke wanke kadai ne yarage kije kiyita in yaso kizo ki wuni kina barcin naki daga haka tayi wuce warta kitchen nan taji kanshin breakfast da ake girkawa ya doki hancinta ta tattari kwanukan wanke wan tayi waje dasu.
Nan ta hada kayan tana wanke wa sauran kannenta da suka je islamiyan safe na 7-9am suka shigo gidan, nan ma'u ke sokanarta wai ya sadiya tazama baba hadixa yau su sadiq da umar ke mata dariya suka shige ciki bata kulasu ba.
Baifi minti uku ba kuma akayi wata sallamar.
Wani mata shine kyakkyawan gaske ya shigo gidan,
sukaga juna da fara'a afuskan su ta ansa masa sallamar tareda ce masa sannu da zuwa suleiman ina kwana,
cikin zazzakar muryansa ya ansamata yana cewa yau kece da wanke wanke,
eh wallahi yasu umma da inna ta?
Lafian su kalau masu inna, eh mana ba dole naji da takwarata ba,
yayi kyau to bari na gaida mama nazo nata yaki yayi shigewarsa ciki.

[7/25, 10:39 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana gani 💝
By F k Ahmad
03 - 04
Tana ganin shigowarsa da yayi sallama mikewa tayi a kishigidar da tayi tana washe baki tace a'a yau su suleiman ne a gidan nawa,
ya durkusa har kasa yana gaisheta tare da ajiye kulan abincin da yake hannunsa.
Wata sabon gani lalle yajima ban ganka ba ka buya,
shiko dan kunya kansa asunkuye yake cewa eh wallahi ayyukane suka min yawa a office.
Ayya toh yayi kyau Allah ya taimaka,
ya iyayenka suke da kuma inna?
Lafian su kalau mama ce ta aikoni na kawo wa yaran masa taga suna sonsa.
Allah sarki Hajiya Fatima harda wahala haka
na biya ta gidan inna ma nace mata nan zanzo dawo tace agaishe ku kwana biyu jikokin ta basuje mata ba.
Eh wallahi kasan yanxu sun kusa fara exams a makaranta da islamiya sun maida hankalin su ga karatu ne sai sunyi hutu.
Ayya toh yayi kyau,
bari nasa mu mutumiyar tawa a waje toh Suleiman. Da yafito wajen ta locacin har ta kusan gamawa saura tukunya uku matsowa yayi ya zauna tare da cewa kawo nataya ki tace a'a barshi nagama
sai da yayi da gaske sannan tabar sa ya wanke tukunyar nan take masa dariya wai ina yakoyi aikin mata ahaka suka gama tattara kayan zuwa ciki daga nan sukayi joining su mama a falo danyin breakfast.
Cikin annashuwa, wasa da dariya suka gama karya wansu gaba daya gidan.
Garin Maiduguri, anan mahaifin sadiya Alh. Muhd Omar Idris yake zaune da mamar sa da yan uwansa da iyalen sa, matarsa Hajiya Aisha(mama) sai kuma 'ya'yan sa Sadiya ce ta farko mai kimanin shekaru 21, mai biya mata Zara tana 19, Omar kuma 16 yake sai Sadiq 13 sannan auta Asma'u yar shekara 8.
Alh. Muhd Omar Idris shahararran dan kasuwa ne mai kudin gaske.
Yana son 'ya'yan sa musamman ma sadiya saboda takwarar mamar sa ce da kuma kasancewar ta yarsa ta farko.
Sadie na jami'ar Maiduguri tana karatun ta course na Radiography a level 300 take.
Sunanan a unguwar GRA anan jihar Maiduguri.
Mahaifiyar baban su na cikin gari wacce suke kiran ta Inna wato kakar su.
Yaran gaba dai naaji da inna kowani hutun su suna gidan ta
koda weekend ne ya zagayo sai sunje mata nakwana biyu tun suna kanana ahakan har suka saba da makotan inna wato gidan su suleiman saboda tana yawan aikan su can
sannan shi suleiman ma yana shigo wa inna a kullum ya gaisheta
haka ma mahaifiyar sa tana zuwa mata in ankon biyu.
saboda wannan sabo da shakuwa mai karfin gaske tashigo wa gida jen nan har ma da dangin su baki daya.

[7/25, 10:39 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana gani💝
By F k Ahmad
05 - 06
Mahaifin Suleiman Alh. Abubakar Ahmad yana tare da matarsa Fatima da kuma dansu tilo da Allah ya mallaka masu wato suleiman. Suleiman dan shekara 29 ne.
Ya kammala karatunsa a fannin computer engineering shekaru hudu da suka wuce, yanxu haka yana aiki ne a wata company.
Suleiman yaro ne mai hankali da nutsuwa ga kuma son addini,
sanin yakamata da kuma tsantsan tarbiyar da iyayensa suka yimar kasancewar sa shi kadai suke da baisa sun sangar ta shiba.
Haka ko acikin abokan sa lafiyyayen mutum ne ba mai son haya niyaba gashi kuma a rayuwar sa babu ruwanshi da 'yan mata har wasu abokan nasa ke zolayan sa da wai shi ustaz ne.
Su sadiya da iyayen ta ba karamar shakuwa sukayi ba dasu Suleiman da dangin su baki daya.
Suleiman da sadiya ne suka fi kowa shakuwa tun suna yara. Itace abokiyar wasarshi.
Hakan nan koda aiki akasata tare sukeyi.
Tana matukar sansa a matsayin babban yayanta sannan a matsayin kanwarsa
banda wannan alakar dake sakanin su bbu wani abu kuma.
Iyayensu na matukar jin dadin taraiyar su da shakuwar su.
Sadie yarinya ce mai takama da isa da jida kai ga kuma son girma sannan tana da ilimin ta iya gwar gwado fannin boko da islamiya gaba daya,
gashi kuma tana son tafiyar da rayuwar ta na en kariya.
Ita da kawayen ta na makaranta duk yaran masu shine Aisha da Rukayya,
kansu a hade yake ga kuma ilimin su da suke ji dashi a department din su.
Zaune suke abokai ne akarkashin wata bishiyar da suke shan iska cikin makaranta.
Na hango wani kyakkyawan saurayi da gani kasan yana ji da kai da kuma sangarta atattare dashi,
sai najiyo muryan abokan nasa a sama suna kirarin ASB, ASB wato Ahmad Sani Balarabe.
Daya daga cikin sune yake ce masa haba marurun zuciyar sadie gurl me yayi zafi haka yi hakuri kaji nan yadaga idanunsa ya harare sa abokan nasa suka kwashe mar da dariya.
Atake yahada rai yake ce musu haba haba da Allah enough ya isheku haka,
kunga tafiyata ma yunwa nake ji, yashige motar ya kama hanyar wata restaurant.

[7/25, 10:39 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana gani 💝
F k Ahmad
07 - 08
Tafiyar su suke a yanga ce suma restaurant din suka nufa sukaji ana musu horn,
mai abu da abunsa nan taake sadie tagane horn di motar tauraron natatun kafin ta juya.
Parking yayi ya sauko ya nufe su tare da cewa Hi bebes! mutuniyar tasa tace hi swthrt,
Rukaiya ma ta washe hakora tana ce masa Asb kwana biyu,
kalau wallahi ya weekend din, nayi missing dinka inji sadiya.
Da yaji shiru ta bangarar Aisha juya wanda zaiyi suka hada ido nan ta dauke kanta zuwa dayan side din yace Aisha as usual kenan ba magana, bata wani kulasa ba sai tabe bakin da tayi kurum ahankali tayi maganar ta yanda baza suji ba tana ce da wani shegen bakar glass din dake idonka.
Haka kawai take haushin sa saboda aganin ta wai bai dace da ya zama saurayin sadiya ba dan rashin halayen sa na gari.Nan yace dasu to emmata naga kuma eatery din kuka nufa muje muci abinci dan yun wa nakeji.
Ahmad Sani Balarabe yaron wani attajiri ne wanda uban sa naji dashi haka kuma ta bangaren dukiya ba wanda bai sakar masa ba.
Atakaice dai mahaifin sa shi yabata dan nasa da rashin tarbiya na gari.
Yana iya rashin kunyar sa acikin makaranta.
Idan akwai abunda zai burge ka gamida Ahmad to baifi ilimin saba don shi ke jan su a class da kuma son yin kyauta wa friends nasa da kowa ma.
Dan final year ne level 500 a department dinsu sadiya wato Radiography a university of Maiduguri (unimaid).
Bayan sun tashi daga school ne sadiya kecewa Aisha wai meyasa kike wa Ahmad hakane bayan kinsan saurayina ne, Rukaiya daman abun da take son tambaya itama, murmishi kadan tayi ta maida kallon ta garesu tace haba kawata sau nawa nake ce miki bana son taraiyar ki da wannan abun bakyaji, sanin kanki ne duk inda kika sa kafa a makarantar nan sai an nunaki da yatsa ga budurwar ASB, ko so kike bakin jinin mutane ya biki ne?
Amma lallai Aisha yanxu wanda nake so kike kira da wannan abun sannan bakin jinin mutane ya bini akan meye.

[7/25, 10:39 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana gani 💝
By fannahkahmad
©MWA
11 - 12
A can karshen bangaren class din suka zauna. Ahmad har mun kusan fara exams yanxu idan muka gama semestern nan kagama kenan bana son rabuwa da kai toh babu waya ne ko ce miki akai dan nagama mun rabu kenan, eh toh wai haka nake gani, zan rinka shigo wa skul din ai ko dan naga baby na, smiling take harda blushing tana sipping drink inta, amma zanyi missing dinka ba ko da yaushe zan samu ganin ka ba, eh da wannan ma kam.
Umma har yanxu na kasa sanar da sadiya son da nake mata ko zaki taya ni fadawa mamar ta a tambaye ta idan bata da wanda take so in ta amince dani sai a hadu mu aure koh. Toh Suleiman bari baban ka yazo kaga shi da kansa sai yaje maka tambayar mahaifinta kawai dan za'afi samun nasara tacan amma ka kokar ta ka fada mata ra'ayinka tukun. Toh Shikenan umma.
Abba, Abba kaga jiya mukayi test aka raba mana script din mu yau ni ce highest a class din mu. Wow 'yata kin yi kokari Allah ya bada sa'a. Ameen Abba. Nikam makarantar yaushe zata kare ne nxt year koh? A'a Abba 5 years course ne fa saura shekara biyu, ok nadauka hudu ne. Toh amma dai ina surkina zai fito kafinnan koh, sauke kanta tayi dan kunya datayi tana wasa da yatsun ta.
Mama ce tashigo da alama taji su tana ce wa aiko yafi ta ciro mijin nan dai nima na aurar da 'yata dan duk kawaye na suna aurar da emma tansu, kaji kawata da take anguwar su inna maman shafa ita ma wai babban danta suka saka wa rana,yara sun girma mazan ma basa barin su tsufa a kuruciyar su suke neman aure. Ai kinji sadiya zaki kawo mun surkina ko. Kada kanta tayi da alamar eh Abba. Toh yayi kyau Allah ya kawo nagari mai albarka. Amin tayi ficewar ta daga dakin, sukayi murmishi suna bin 'yar tasu da kallo.
Assalamu alaikum, wa alaikumu sallam a'a ummar suleiman ce sannu da zuwa 'yata karaso man bayan sun gaisa ne inna ke tambayar ta ya suleiman din ya kwan biyu bai shigo ba, yana nan kalau inna, danki na son ya shigo wajen ki amma yana kunyar tunkaran ki da zancan da zai zo miki dashi, ayyo wannan kuma wani zance ne haka yau Suleiman ke kunyar naji, shine nace toh bari ni nazo nafada wa inna ko za a samu gobayan bayanki, toh Allah yasa amin, inna daman akan jikar ki sadiya ce, tuni inna tayi murmishi dan kamar ta dago manufarta. Yace wai shi ita yake so da aure.

[7/25, 10:39 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana gani 💝
Written by Fkahmad
©Mikiya Writers Association(MWA).
09 - 10
Ke ma fa kinsan bibiyar emmatan da yake yi, akalla kinsan zaku kai hamsin awajen sa
sadiya taji dacin maganar ta dake, amma kinsan koyaya ma dai nice sama da su, nice wanda yake so, nice shugabar su. Ohon miki yarage naki inji Aisha. Duk zan can nan dasuke Ruky na gefe ta tabe baki sai kallon su take sai yanxu tayi magana, dallah ya isa haka mutafi driver na ya iso war haka sannan suka mara mata baya suka tafi.
Bayan kwana biyu ne su sadiya sai murna ake gobe Abban su zai dawo daga tafiyar da yayi kasancewar sa dan kasuwa ne baya zama agari.
Asuban fari, juyawa take akan gadon ta ahankali ta bude idanunta tana jin kiraye kirayen sallah sai tayi murmushi bisa tuna zuwan Abban nasu da tayi taje dauro arwala tazo tada zara dake baccin ta tsiyaye ruwan cup din da take rike dashi tayi zuwa hannunta sai fuskar zara a tsorace ta tashi ita kuma tana mata dariya da Allah kiyi addu'a mana sai wani sororo kike kallo na yau fa Abba zai dawo kinsan muna da aiki ko, ta wuce ta saya sallah ita kuma zara ta nufi toilet.
Yau shawarma Zamuyi wa baba inji zara lallai meat pie Zamuyi nishi nake ra ayi cewar sady toh kowa ma yayi abun ransa yauwa toh gara hakan, suka wuce kitchen, mama ce ta keyin girki mai dadi Ma'u da sadiq ne suka shigo, muma zamu taya ku aikin. Kaca kaca sukayi a kitchen din kowa na aikin gaban sa can kusan azahar suka gama aikin su suka jera na Abban su akan dinning table. Kowa yaje yin wanka.
Kamar karfe uku saura mama tafito daga daki kai ina kuke ne Abban ku ya kira suna airport dan Allah mama gaba dayan su suna hira ne a falo murna suka hauyi, mama muje mu dauko sa da wuri ai dama wanda bai shirya ba kam zamu tafi mubarsa duk suka yo hanhar mota. Suna isa kowa yafita yaje ya rungumo Abba da murnan su suka Koma gida.
Abba yayi wanka sukayi sallah umar ne yaja su. Ma'u tazo da gudu ta hau kansa, muje muci abinci Abba dama nikai nake jira kowa yaci nasa kin jiran ka suka yi saini, toh auta na nasan ke kadai ke sona dama. Sady ta turo baki bawani nan Abba muda muka girka maka abun da kake so fa nima ai nataya ku koh mama, daga mata kai tayi.
Yauwa Abba shawarma ko pie kafi so ka zaba zara duk dai ba kayan flour bane duka ina so,
tajuya sai kallon sadi take tana mata gwalo. Omar baba na kai da sadiq kunyi shiru fa, ni kallon shagwaban ya zara da ya sadiya nake sai kace nine yayansu ya daga musu gira sukai dariya. Sadiq ma yace nima yayan su ne.

[7/25, 10:39 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana gani 💝
By fkahmad
©Mikiya Writers Association
Dedicated to all members of Banaji Bana gani novel group and all other fans from other groups. Ni F k Ahmad ina muku godia da karfin guiwa da kuke bani. LYSM
13 - 14
Sai da tayi ajiyar zuciya tace toh alhamdulillah indan wannan maganar ne in Allah ya yarda kun samu goyan baya ta.
In ya dawo daga aiki ki turo min shi ya kaini gidan nasu a mota kinga sai nagaya wa mahaifin nata. Toh inna gaskia mun gode sosai Allah ya bar zumunci, eh toh ai wannan yiwa kai ne. Suleiman dan albarka takwara ta yake so,ai tasa mu yaro mai hankali da nutsuwa ga ilimi wa zai kisa saide mu gode wa Allah. Sallama tamata zata koma gida da farin ciki a ransu.
Bayan magariba suna zaune a gaban Tv sai kallon series film din da suke taji wayan ta na ringing a hannun sadiq yazo ya mika mata, tadaga wayar hello Aisha, sai murna take albishirinki, goro fadi naji sai ta zuba kike kamar ganyan shayi, ta dan yi dariya tace yanxu haka muna da manyan baki a gidan mu Mustapha ne ya turo ma gabatan sa sunzo neman aure na, ta turo idanunta sukayi waje dan Allah kawata, hmmm sa wasa kiga duk zanyi aure na barku da ruky, toh malama nidin ma bazanyi bane akace miki bari Asb ya gama makarantar sa kiga ikon Allah, wani dogon tsuka taji taja mata tana Allah zaba miki wanda yafi Ahmad dai ba shi ba ta katse wayarta. Oho dai kyaji dashi ta cigaba da kallon film din ta.

Washe gari.
Tana tafiya, class din su take approching da gudu Rukaiya ta rungume ta tabaya congrats Aisha na miki murna sosai kinji dadi zaki auri Mustapha inki, hmm bari kawai kuma Allah ya zaba muku nagari, Ameen kawata. Laaa time yayi fa kar lecturer ya riga mu shiga sadia fa tariga mu zuwa fa tana aji munyi waya da ita yanxu.
A seat nagaba suka zauna inda sadie takama masu su uku. Oyoyo amaryar mu, sadi gurl yane nan suka ga lecturer ya shigo suka nutsu.
Inna bata samu zuwa ba jiya sai yau da yamma Suleiman ya kaita gidan, suna isowa inna ta bude kofar motar zata sauka kenan saiga sadiya ma saukanta daga napep ta dawo daga makaranta taga inna na fitowa daga motar Suleiman da gudu tanufo su tafada kanta tana oyoyo inna yau da ya suleiman kikazo mana, inna ta washe baki eh tare muka zo. Toh bara kashigo bane kai ya suleiman sai taga ya sunkuyar da kansa ya kuma dagowa,
ina sauri ne sadiya kigai dasu mama natafi, yayi sauri yaja motor sa.


[7/25, 10:39 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana gani 💝
Written by Fkahmad

©MWA
15 - 16
Tabe bakin ta tayi a ranta take fadin toh Shikuma yau me ya same sa sai kace mai jin kunya na yana wani daddauke kai. Inna ce tayi nasarar dawo da ita daga tuna nin da tafara,
ke kuma me kike tunani haka, ta mata murmishi suka shige gidan. Baba yana tsaye a cikin harabar gidan, ah sannu da zuwa inna ya durkusa yana gaisheta bayan haka tace su shiga daga ciki.
Mama ta tarbi inna cikin fara'a da abun motsa baki. Tace dasu da akwai maganar da tazo dashi nan mama tace da yaran su shige dakinsu.Inna ta matso kusa da dan nata tace musu gamida takwara ta ce daman Allah ya sa ba'ayi mata miji ba, baba ya juya ya kalli mama suka hada ido,Kunyi shiru fa kodai kun zaba mata ne. A'a inna bamu zaba mata ba tukun jira muke ta fito da shi, Baba ma yace inna ni banaso nayi mata dole sai inhar naga wanda tazaba bayyi ba sannan na zaba mata wani.Toh ai Shikenan hakan na da kyau amma wannan yaro ne Suleiman ummar sa tazo ta sameni akan idan kun amince masa da neman auranta shi zai tunkare ta da soyayyarsa, tun da tafara magana suke jin dadin hiran ta. Baba yace masha Allah gaskia naji dadin shawarar da kikazo da ita, Suleiman dane mai albarka da addini ni dai na amince masa amma ya fara zuwa wajen sadian tukun muji daga bakinta,Haka ne kam Alh. nima na amince masa gaskiya hankali na ya kwanta da shi Allah yai masa albarka ya kuma sa shine mafi alkhairi cewar mama.Bayan inna ta koma gida ne ta nemi suleiman ta sanar dashi yadda sukayi da iyayayen ta, farin ciki fal a tattare da shi na an masa izinin zuwa wajenta.
A daren ranan around 9:30pm yake kwance sai tunanin ta yaya zai fara tun karan ta da maganan nan yake kodai zai kira ta awaya ne eh bari nafara kiranta tukunna kafin zuwa goben. Ya daga wayan sa yayi dailing numbern ta sai yaji call waiting yasan hakan mai faruwa ne amma baiji dadi ba a ransa Kamar ya katse amman baya ji zai iya.
Hiran ta take da Asb sai taji wani call ya shigo matada ta duba ko wanene to her surprise ya suleiman tagani akan screen din aranta tace ya suleiman kuma by this time, Allah ya sa lafia. Ta bangaran Asb kuma yana hlo bby bakya jina ne hankalin ta nakan screen din wayar ta amma inaa har yazama missed call kafin ta bashi ansa call din yakara shigo wa Baby ya wani abun kikeyi ne Na'am Asb sorry karya tamar mum na kira nane bari na tafi ta katse nasan sannan tayi receiving na suleiman Muryan ta na rawa tayi maganan hlo ya suleiman Na'am sadiya yakike, lafia kalau, yasu umma duk Lafian su Yadda taji muryan sa cikin kwanciyar hankali ya sa ita ma tayi ajiyar zuciya erm daam erm sadiya kina jina eh inaji, bai masan ta ina zai fara ba saboda abun da bai taba yi kenan a rayuwarsa wai yace wa mace yana sontatab lallai akwai aiki jaa agabans Sai kawai yayi concluding da daaman nace gobe idan kina gida zan zo miki da yamma Wani harbawa zuciyar ta taji yayi...

[7/25, 10:39 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana gani 💝
Written by Fkahmad
A big shout out to MARYAM MUKTAR the writer of 'Nida yah Fauzan' this page is proudly dedicated to you. Thank you for the love, care and support you gave me in developing this book. 😘
17 - 18
...ina gida insha Allah amma Allah ya sa lafia, A'a lafiya kalau babu komai Toh sai da safe koh, toh Allah ya kai mu. Ya katse wayar yana murmishi ita kuma bin wayar ta yi da kallo ta kasa gane meke faruwa kiran Asb tayi suka ci gaba da hiran su na masoya.
Washe gari zuwa yayi ya samu inna akan ta kira mamar sadiya ta sanar

Please Login or Register in order to submit comment