Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saba dashi ba kinga bazai baki wahala ba ki daure, ba yana sonki ba in kika ci sa'a ma bazai takura miki ba. Kai inji wa bari kawai nidai Allah yayi zan zama matar mallan Sai ahankali dan zumuncin da muke yi ma nasan zai hanani zuwa gida janku amma ko wlhy ba zaiyu ya bani wahala ba. Ke gara Kuma fa kin bi mijin ki sau da kafa fa, hmm nidai kyaleni amma inhar na tabbata da zancan mama gaskiya ne na ASB wai yaudara ta yayi bai kyauta min ba dan nikam naso shi sakani da Allah Kuma ni BANAJI a jikina ko kadan akan yaudara ne dan nasan bazai tafi yabar ni haka kurum ba Ji nake kaman wani abu ne ya same sa amma I'm ever ready to be with him in ya dawo, ta goge hawayen ta dake shirin saukowa. Kinsan Sai yanzu nake tabbatar da zancan Aisha na cewa bai dace da ke ba, dan nima gani nake kamar guduwa yayi ya kyale ki, ruky ba haka bane ki daina fadan hakan akansa danni BANAJI BANA GANIn akwai dalilin da zai sa yamun hakan ba banga dalilin da yasa kuke ai batashi haka ba ta rushe mata da kuka.
Sadie ta daina receiving calls na Suleiman tun daga ranar da aka saka musu rana har gashi anfara bikin Aisha, jiya suka sha dinner party yau kuma suna wajen kamu.
Da yamma Amarya da kawayenta na zaune suna hira Sadie taga wani sabon number na kiran ta Sai da zuciyarta ta buga ta ware ido tana kallon numbern tana ya Allah kasa ASB ne da sauri ta daga hello, shiru yayi yana sauraran muryan ta, Sai ta sauke wayan akunnan ta tana kallon numbern da taji shiru azatan ta ma yankewa yayi ta sake daura a kunnan wake magana, da gangan yayi gyaran murya dan tasan na miji ne. Ahhh Asb kaine? Kamun magana kayi shiru, ASB? Sadia kina ina ne haka nake jin surutai, bisa jin muryan sa da tayi taja tsuka ta katse wayar tayi zaman ta kusa da ruky tana gunguni ina ruwan ka da inda nake tun ban shigo ba har ka fara mun shishigi, lafia malama ke da waye haka, da wannan munafikin mana tun yanzu yana tambaya ta wai ina nake yana jin hayaniyar mutane. Jin muryan Aisha sukayi ta gefensu, karde dama baki tambaye sa ba kika fito, wai ke aisha ce miki akayi da igiyar auran sa akai na ne ku jira sai an daura mana, toh me yarage an riga da an basa ke, ya kamata ace kina neman izinin sa kan ki fita kinga zaiji dadin hakan, iyee jin dadinsa akace miki nake nema ne ni ba musguna mun yayi ba da auran nasa ko ce masa akayi ni na nema dan haka ya bini ahankali. Hmm Allah ya shirye ki, tabe bakin ta tayi tace ameen.
Washe gari aka daura aure aka kai Aisha dakin ta. Ran wuni kawayenta suka je mata sai da yamma Sadiya ta koma gida.
Tana bude kofar gate dinsu taci karo da shi tuntube tayi zata fadi yayi saurin taro ta, rike ta yayi gagam, kanshin turaran sa da taji yasa ta dago arikice dan taga wanene sai ido hudu da sukayi da Suleiman kallon ta yake har cikin ido, tana kokarin fusgan hannun ta yayi saurin sake ta, daga ina kike Sadie kwana biyun nan duk ina zuwa bana samun ki, shekaran jiya nakira kika kashe mun waya ga kuma ina jin wajen da hayaniya, yadda yake magana yasa ya bata tausayi da dariya locaci daya kuma sai ta dake, batayi niyan ansa shi ba amma sai taji ba dadi tayi ignoring dinsa yasa tace daga bikin Aisha kawata nake, all this days kullum sai kin tafi, toh Ina ruwan ka dan ma ban tattare kaya na naje ni na zauna ba. Da izini wa kike fita , lallai ma iyayena mana sai jikin sa yayi sanyi toh amma kinsan yana da kyau nima kina tambaya ta koh, hmm ka jira sai na koma karka shinka tukun bari ma na fada maka kaji kar kadauka auran nan sabi da ina so ne zanyi umurnin iyaye na nake bi dan haka kada kasa a ranka za ka takura mun da sunan wai kai ustaz dan ko a gidan mu ba a takura mun ba. Bai taba tsammanin hakan daga gare ta ba Iya tsawun zaman su tare bai taba ganin tana rashin kunya ba sai yau shi yasa yayi shiru sai binta da kallo yake tajuya har tashige gida yayi ficewar sa.
Tundaga hakan bai sake neman ta awaya ba dan yasan ba dagawa za tayi ba hakan yasa ya fita daga har karta gaba daya badan yana so ba.
Akwana a gashi ba wuya har locacin biki yadawo gobe jumma'a za a daura aure. Sadie da frnds dinta na zaune a daki tasha gyaran jiki da kitso yanzu lalle akayi mata ahannu saura kafa aka aiko mata da yaro abban ta na neman magana da ita ta tashi taje samunsa a falo ta tari dakin ba kowa sai wani da ta gani ta baya kuma tasan ba abban ta bane sallama tayi ya juya yana ansa ta sai ta hada rai kamar wacce aka turo wa sakon mutuwa kauda kanta tayi. Kiyi hakuri da na biyo ta wannan hanyar nacewa abban ki ne ya kira ki idan ba hakan nayi ba nasan bazan samu daman magana da ke ba dan kina rejecting calls dina, sadiya ya kamata ki bawa kanki hakuri ki danne zuciyarki tawassali za kiyi da abunda Allah ya daura miki, da kinyi istihara kinga alkhairun da ke cikin zaman mu tare. Ki bani daman na nuna miki soyayya ta kinga a gobe kin zama mata ta. Ya Suleiman kafadi abunda ya kawo ka ni zan koma ciki, OK dama nazo tambayar ko kina da wata bukatar ne ke da kawayen ki dan nasan ba kira na za kiyi ki fada mun ba. Babu abunda muke bukata zata juya tafita ya da katar da ita, Sadie! ta tsaya daga Inda take yataka yazo shi kusa da ita, masha Allah lalle kike mun gashi yayi kyau, asannan ta tuna hannayen ta masu lalle da take rike dasu dan ta kaici yasa bata kula sa ba tayi ficewarta ta barsa.
Tashigo dakin hawaye na gangarowa daga idonta ta sauna kusa da Aisha, ni wallahi ba haka naso nayi bikin aure na ba sabi da Allah ki dubi rashin adalci da mutumin nan yayi mun, last week na aika Zara tace masa za muyi dinner da kamu, ce mata yayi fa tazo ta fada mun shi babu wani event da zaiyi a auran sa Kuma nima bai yadda inyi ba, su mama suka yarje masa akan eh babu kyau yana rage albarkar aure akayi canceling wai saide ayi walima yanzu Kuma yazo yana tambayata ko ina da wata bukatar toh me Kuma zan nema na samu tunda ya hana ni wancan ma.

[7/25, 10:39 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana Gani💝
Written by F k Ahmad
29 - 30
Haba Sadie meyasa ranki zai baci akan wannan mai makon ki gode wa Allah da ya baki miji mai tsoran sa kinga bazai yadda da yaga kina wani abunda ba shiba cikin addinin ki, in ki na da irin sa akusa da ke babu wani sabon Allahn da yara ge miki kiji dadi kinsamu irin Suleiman a matsaya yin mijin ki dan ko wace mace burinta ta su kamar shi. Ke daman kullum maganan ki kenan idan akace Suleiman to sai kinyi supporting dinsa kina ko wace mace zata soshi to ke me ya hana ki auran sa, subhanallah sadiya kina da hankali kuwa ki daina sabon Allah mana ina da kawa mijin fa kawai daga fada miki gaskiya tunda abun naki zai koma kaina ne bari nayi shiru.
Wata kawar su Deejah ce tasa baki, Sadie ki rungumi mijin ki hannu bibbiyu zaki ji dadin sa wataran, kiyi kokari ki masa biyayya zaki kara dankon soyayyar ki awajen sa kinji kawata, harara ta juya ta danka mata, Ruky kam dariya tayi ta tashi ta bar dakin, muguwa kawai tabita da kallo. Ha'a sadiya lafiar ki cewar Hajara sai Kuma ta basu dariya dukka suka fashe dashi.
Yau aka daura auran Suleiman Abubakar Ahmad da Sadiya Muhammad Umar bayan sallar jumma'ah. Daurin auran da yasamu hallarar dumbun jama'a ta ko wani bangaran dangi. Duk da babu wata shagali da akayi amma ansha biki yayi dadi. Mama nata murna itama yau zata kai yar ta dakin miji.
Amarya Sadie cikin kawayenta babu laifi ta sake sosai akayi murnan biki. Sai bayan sallar isha'i akazo daukan Amarya. Ruky da Deejah ne aka bari cikin kawayenta su suraka amarya sai anties dinta kanwar mama da step sistern Abba.
Sai da akazo fita da ita daga gidan takama sabon kuka ita baza ta bar gidan ba ta ruga aguje zuwa dakin ta sai bata musu locaci take gashi dare yayi karfe tara saura abokan ango har sun gaji da jira, mama ta shigo dakin ta fara balbale ta da fada, ke wace irin yarinya ce da bata jin rarrashi an miki fada an miki nasiha an baki hakuri duk kinji ji, ya kike so ayi da ke, sai ga abba ya shigo shima dama Anty Hadiza ce kanwarsa take ta kiran sa akan sadiya taki tafia gidan ta yayi gyaran murya suka suna kallon sa yace dasu duk ku fice ku bar ni da ita.
Cikin minti kalilan shida Sadiya kadai suka rage a dakin. Takowa yayi yazo ya zauna kusa da ita a bakin gadon yayi shiru na en wasu seconds sannan ya kama hannun ta na dama ahankali yace da ita mama ta kiyi hakuri da abunda Allah yayi ni mahaifinki ne, ni nayi miki zabi sannan kinsan ba zan zaba miki abunda zai cutar dake ba, ke da ko yaushe ina alfahari dake akan biyayyar ki sai Kuma yanzu ki gaza yin hakan, da za kiyi hakuri ki daure kiyi zaman lafia da mijin ki zaki ji dadin rayuwar auren ki, tunda ya fara magana kanta akasa yake tana kuka, amma idan kince ba kya son auran Suleiman ne shike nan ni zanje na karbo miki takardar ki yanzun nan Kuma na hada sa da Zara a daren yau din nan Dan nasan ita zatayi abunda nake so dasa haka ya tashi zai fita daga dakin tayi saurin shan gaban sa ta durkusa tana zubda hawaye a'a abba kayi hakuri na tuba zanje ni gidan Suleiman Abba dan Allah ka yafe ni, har a ransa yaji dadin sauya wanda tayi a taake, tashin ta yayi ya dago kanta yana mata smilling yace kin tabbatar da hakan tace eh abba, haka nake so da ke magana kinsan bazan taba son abunda bakya so ba shi wancan saurayin da kike so da yazo shi neman auran ki zan basa ke amma sai akayi rashin sa'a ba mutunin kirki bane. Ga Suleiman yanzu shine mijin ki, ki rike sa da kyau ki bisa sau da kafa kinsan biyayya na saka shakuwa sakanin mata da miji barin ma ace kun riga kun san juna da jimawa, kun shaku kun zama data kada kiyi abunda bayaso, Suleiman na sonki kiyi zauna dashi lafia kinji uwata kiyi anfani da kalamai na za su miki anfani. Kada kanta tayi, toh abba na gode yauwa yata muje na rakaki, to his suprise sai yaga ta make kafada takoma baya, has me ya faru Kuma Abba ni bazani ba bana son barin gidan nan abba ni kadai fa zanyi rayuwa acan babu kai babu mama da su Zara ma fa duk suna nan ni bazanje ba. Haba sadiya ya za ayi kiyi rayuwa ke kadai shi mijin naki fa ba tare kuke ba, yanzu gashi muje inkai ki da kaina gidan ki dan ko musulunci ma haka ya koyar idan kuka aurar da yarku to kuyi mata rakiya zuwa gidan ta. Kinga tashi muje mu. Da kyar ta yadda ta bisa suka fito zuwa falo.
Kawayenta, anties dinta da mama duk sun gaji da jiran ta suna zaune suka ga Abba ya fito yace da mama ki dauko min key din mota na. Alh ina Kuma zakuyi kar kace mun kai ta zakayi Dan naji made da abokan sa suyi tafiyan su, eh kaita zanyi sai akayi ya fada mun inda aka ce hakan haramun ne Kuma da ke ma ya kamata mukai ta ai, a'a ni rufa min asiri ba dai ni ba Kuma kai din ma gaskiya da kunya haka Kasai mutane su samu abun magana a gari baza ka kaita ba ai gara ace ma mijin nata ne ya zo shi daukan ta zaifi.

[7/18, 4:09 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji Bana Gani💝
Written by F k Ahmad
Kuyi hakuri jiya ban samu nayi posting ba yau kuma nayi shi very late. kinji sadiya nasan kece mai da muna dan haka nayi riga kafin bada hakuri.😛
31 - 32
Su Anty Hadiza ma suka taya ta gaskiya bai kamata ba, ka kira Suleiman din ya tafi da ita kaga mu sai mu zauna kawai. Sadiya da take labe a bayan sa tana kuka duk haushin su take ji, Abba ya juya da ita zuwa dakin sa ya daga wayan sa ya kira Suleiman akan neman sa yake da ya sauke wayan ya dubi time har tara da rabi ya kusa. Within 15min. ya isoshi gidan yayi sallama ya shiga falon Abba da mama ne suka sa yar su a gaba suka sauna sai nasiha suke mata shima din Suleiman ya shigo wa ya samu waje ya zauna akasa kusa da Abba. Abba ya dafa kafadan sa kaga 'dana abun da nake so dakai ga matar ka Ku tashi Ku tafi gida yanzu Allah yayi muku albarka, ya baku zuri'a dayyiba. Ameen abba mungode. Babu wani bata locaci ya mike zai fita sai kuma ya juya yana kallonta. Sam babu alaman zata tashi, mama da ta lura da taurin kan yar nata ta mike ta dago ta suka yi waje.
Inda yayi parking motarsa suka dosa Abba ma ya biyosu. Suleiman yayi sauri ya bude mata front door seat sai da tazo zata shiga kuma ta juya da gudu tayo kan mama tana kuka, itama mama sai da zuciyarta ya karaya tana tausayin yar nata Abba ya zo ya jata zuwa motar ya shigar da ita rike rigarsa tayi wai bazai tafi ba. Yayi kokari ya kwace rigar sa ya tura mata kofar ya kulle ta kai hannu zata bude Suleiman yayi saurin danna central lock takasa bude shi sai ta kukan ta take. Abba ya daga musu hannu Suleiman ya ja motar suka fita daga harabar gidan. Haka ta hakura da kukan dan kanta tayi shiru. A bakin titi yasamu ya sauka ya siya musu kaji da drinks masu sanyi suka nufi hanyar gidan su.
Suna isa gate man ya bude musu suka shiga yayi parking ya sauko itama ya bude mata kofar ya na jiran ta fito amma taki ya mikar da hannun sa ya kamo nata, warce hannun ta tayi daga rikon da yayi mata ta dauke kanta daga direction dinsa. Durkusa wa yayi a gabanta yana kallon ta, Sadiya ban dauka zaki kini a matsayin mijin ki ba. Zaman da mukayi da shakuwan mu a baya kina nufin ba komai bane a wajen ki, kisani fa ni masoyin kine, bazan so miki abunda babu alkhairi a cikin ta ba ni nadace da ke. Yanzu ki tashi muje daga ciki. Kallon sa tayi ta danka masa harara murmishi yayi ya kada kansa ya mike ya tsaya kallon ta yana jiran ta fito yayi gefe yana mata nuni da hannu alamar ta fito still tana zaunan ta da ya lura fa bata locacin sa za tayi ya sun kuya yakai hannunsa zai dagota ta ture shi. Sai da yayi dabara yasamu ya dankota ya rike ta mai kyau ya dagata cak ya nufi cikin gidan da ita, shure shure ta ke tayi ni ka sauke ni bana son iskanci shi dariya ma ta basa tana tayin masifar ta har suka ido cikin dakin ta direct kan gadon ta ya duro ta tana huci sai kace ita tayi wahalan dauko sa.
Ajiye ledojin hannun sa yayi akan chess of drawer ya sunkuya ya kama kafanta jikinta ya fara rawa atake ta rikice tana jan kafan baya ya dago yana kallon ta da mama ki kamar yayi dariya sai kuma ya danne, tana ganin sa ya fara yaye mata kasan skirt runtse idanunta tayi da karfi zata fizge kafan ya rike ta ki tasya mana, ya danko kafafun dukka biyu ahankali ya cire mata half shoe dinta ya ajiye a gefe ya yatsura ido wa tafin kafan da ya sha zanan lalle yashafa su da hannun sa yace tabarakalla nagode wa ma halicci da ya mallaka mun mai wannan halittun kafa masu kyau sai gashi an masa ado da lalle ya kara masa kyau da haske, wannan adon duk ni akayi wa. Bude idanunta tayi ta sauke su cikin nasa, ni dai kafafu na ba naka bane ta fizgo su. Toh ai nima ba wai nace nawa bane cewa nayi mallakamun su Allah yayi ko ba mallakina bane ke, dauke kanta tayi ta matsa gefe daya. Wai da kin dauka mezan miki ne takalmi nazo cire miki fa dariya ya mata ya tashi ya cire hulan sa ya mika mata, kin karba tayi ta tsaya kallon sa, karba ki ajiye ki samu lada man kauda kanta tayi. Murmishi kawai yayi ya ajiye hulan gefen gado ya nufi toilet dan ya dauro alwala. Da yafito haka ya sameta inda take kamar yadda ya barta. Je kiyi alwala muyi sallah, ni nayi sallah na a gida, eh nasani nafila zamuyi, toh bana sallan baki ya sake yana kallon ta sai kuma taji kunya, ba don sallar ibada bane da har ga Allah ba tayi niyar yi ba ta miki ta shiga bayin. Kafin ta fito har ya shimfida musu sallaya ya zauna jiran ta.
Nade laffaya a jikinta tayi ta tsaya abayansa ya jasu sukayi raka'a biyu ya musu adduo'i yace da ita zo na shafa miki addu'an kin kula sa tayi kaman bata ji sa ba. Tashi yayi ya fice daga dakin dan dauko musu cups da plate a kitchen. Da ya dauko yazo shi zai bude kofar dakin ya jita gagam akulle ha'a sadia kwankwasa wa yayi sadia kina jina bude kofar mana knocking ya kuma yi nan ma shiru. Fitarsa tayi locking kofar, ta dauko night gown dinta daga akwati ta saka ba a jera kayanta cikin wardrobe ba tukunna. Kan gado ta haye tayi kwanciyar ta. Sadia bude kofar mana wai lafiar ki, daga muryanta tayi yanda zaiji lafia ta kalau barci zanyi sai da safe. Daskarewa yayi dan bai zaci za tayi hakan ba, toh haka zaki kwanta da yunwa baki ci komai ba plate fa naje ni dauko mana a kitchen, bude ki karba idan kika ci sai ki kwanta. Manna masa tayi haka ya gaji ya bar kofan ta ya wuce dakin sa.
Bayi ya shiga ya wasa ruwa ya jeshi ya kwanta kan gadon sa. Boxer ne kadai ajikin sa danshi baya iya kwanciya da kaya ajiki, jujjuyawa yake bacci yaki daukan sa mikewa yayi ya je falo ya kunna wutan ya wuce kitchen yana dube dube ko zaiga abunda zai saka a cikin sa dan yunwa ne ya hana sa baccin baici komai ba tun abincin da yaci da safe sai ta kai kawo yake cikin abokan sa yakasa zama yaci, haka ya bar kitchen din bai samu komai ba, fridge yaje ya bude ya ciro goran ruwa daya ya kwan kwade shi tas zai koma daki sai wani abu yace dashi yayi checking kofar ta in ta bude ko zai samu yaci namar kazan. Yakai hannunsa handle din ya jishi a kulle. Akufule ya koma kan three seater ya kwanta da kyar yasamu baccin ya sace sa.

[7/19, 9:14 PM] Fannah k Ahmad: 💝Banaji bana gani💝
Written by F k Ahmad
33 - 34
Around 1am na dare sadia ta bude idanunta sai taji cikin ta yayi kara alamun ita ma yunwar ce ya tada ita toilet taje ta wanke bakinta tazo ta zauna ta bude ledar ta fara cin naman ta hango dayan ledan ta ja ta bude ga drinks ne har sunyi dumi daga sanyin da suke. Cup tafara duba wa a cikin dakin bata samu ba taje ta bude kofar tana dube dube ina za taga kitchen.
Can ta hango wani kofar banda na fita waje dan tagane ta wanda suka shigo gidan. Zuwa yayi ta bude ta leka duhu ne dilim a dakin ga bata san inda switch din yake ba, takoma daki dan dauko wayanta ta kunna torch light dinsa ta nemi switch din haske ya gauraye kitchen din tasaki hamdala sai ga cups dinma kusa da ita da ta dauka zata kashe wutan sai ta tsaya kallon tsarin cikin kitchen dinta color na drawer din da komai na kan da na cikin sa black and white ne yayi kyau sosai har da su cups,plates,dishes,plastic spoons,forks da duk wani electric gadgets din cikin kitchen din ta black and white wow! tayi exclaiming dariya ta tsaya yi tayi mamakin ganin favorite color dinta dadi sosai taji dama yana daga cikin burin ta tsarin gida mai kyau more especially kitchen gashi tasamu. Dauraye cup din tayi a sink ta fice daga ciki tana murna, tsaya wa tayi cak da ta gansa akwance kan sofa kallon sa take how comes bangan sa ba da zan wuce kuma taba wa kanta ansa kila ban lura ba no wonder wutan falon a kunne yake maybe bacci ne ya dauke sa bai kashe ba, mtsw dube shi ko kunya baya ji daga shi sai boxer ajiki. Wuce wa daki tayi taci gaba da cin abun ta.
Asuban fari ya farka yaje yayi alwala yaje sa masallaci sai kaman karfe shida ya dawo. Dakin ta ya nufa yaji abude take ya shiga. Baccin ta take ya zauna kan drawer zai tada ita sai yaga sallayar ta a shimfide da hijabin ta akai alamar tayi sallah kenan, ahankali yace ok bari na kyale ki tunda kinyi sallar ciga ba da baccin ki. Ragowar naman da taci ya gani dauka wa yayi yaje kitchen ya dumama a microwave ya ci awajen ma sannan ya fara tunanin ko ya dafa musu breakfast sai kuma ya fasa da ya tuna ummar sa zata aiko musu daga gida. Koma wa yayi daki yayi wankan sa ya shirya zai fita yaje shi dakin ta dan ya duba ta, har yanxu bata farka ba daki sa ya koma ya dauko paper da biro ya rubuta mata kaman haka "idan kika tashi umma zata aiko abinci yanxu sai kici kar ki jirani dan zanje nayi agida saboda zamu hadu da abokai na daga can sai mu wuce gaisuwan iyaye ki kula mun da kanki mata ta". Nadewa yayi ya kai kan side drawern ta ya ajiye ya zauna gefen gadon yana kallon cute face nata murmishi ya samu kansa dayi ya daura hannun sa kan wajen fuskanta yana shafawa, pink lips dinta ya tsurawa ido ya kai hannun sa zai shafa sai tayi motsi ta gyara kwanciyarya ta daga nan yatashi kawai yayi tafiyan sa.
kamar karfe tara da Rabi ta farka ta nufi toilet tayi wanka ta fito tayi shirinta cikin rigar atampa da skirt mai kyau tayi daurin ta na zamani ta zauna gaban mirror tana chancare kwalliya taji an bude

Please Login or Register in order to submit comment