Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Radio. Wahiba Malik Menk Jordan kuma sai ta kasance miskila mara son magana, ga dan banza reni da gani-gani. Sannan idan Ubanka ba wani ba ne, bata kula ka. Gashi tana da ilimi sosai, amma magana bai dame ta ba, bayan wannan halin Nadrah yarinyar tana da kirki sosai, domin ba kowa yake iya jure zama da Wahiba Malik Menk Jordan ba, domin kusan kullum sai ta mata rashin mutunci. Amma tana like da ita, tana hakuri hakan ne domin mahaifinta ya rarrasheta da tayi hakuri ta zauna da halin Yaran. Duk da babban damuwarta, shi ne ta samu kusanci da Malik kamar yadda uban ya ce, akwai wani abu daya da suke kokarin ganin sun cusawa yaransu, shi ne dole yaran su bayyana jikinsu ga Malik ta haka sha'awa zata saka ya ga ya bukaci yaran daga Khamis Shatima da Lalla Salmah wannan shine bu™atarsu da kuma kudirinsu.
Shirin su na rikito da Malik ba karami ba ne, sannan idan har akwai abin da suke hari tow dukiyar Malik ne, shi yasa duk abin da suke har kwanan gobe babu nasara, amma zasu cigaba da fafutukar ganin sun sami hakarsu ta cimma ruwa.
&
Amjad
Sintiti yake daga Office dinsa, zuwa bakin Office Win. Baki daya hankalinshi a tashe yake, kai yafi ma ganin hankalin shi zaune take da gindinta, wayar shi ce tayi kara ya Wauka tare da sakawa a kunnenshi.
"Chairman gata nan ta shigo kamfanin!" Hadiye yawu yayi, bai taSa kawowa a ranshi zata dawo yau ba, sai gashi ta dawo Win. Sai da ya sauya kaya sannan ta wuce office dinshi domin Mss Mary ta gaya mata yana son ganinta.
A hankali ta tura kofar, yana zauna a kujeranshi, zuba mata ido yayi. "Ke kuma haka ake rayuwa?" Dauke kai tayi tana kallon waje, "Nasan bai kyauta ba, amma a madadin haka sai ki tsaya ki ji me zance miki, ba wai kiyi gaban kanki ba. Gashi nan zaki hadu da Elbashir, duk abinda zai faru, ya faru amma ka da ki sake baku hadi da Malik ba, shine kawai zai yarda da bukatarmu"

Gyada kai tayi tana faWin. "Tow idan ban hadu da Malik din ba fa?" Murmushi yayi ya ce mata. "In sha Allah, zaku hadu ina jin hakan a jikina!" Gyada kai tayi a karo na biyu, sannan ta ce mishi. "A ina zan samu damar haduwa da shi?" Office dinsu yana kan titin sir Victor James black. Menk property management companies, ga wannan laptop din naki ne, mun tsara kome sannan na tura musu abin da zaki bukata, sannan sun amince da bukatar tattaunawa da ke, and ban sani ba ko zaki iya tafiyar da wasu abubuwan. Don Allah ku kula."
"Tow!" Ta fada tana me daukar laptop din, ta fita murmusawa yayi yana hango yadda yayi nasarar kome, ya barta a cikin ruwa tsundum. Juya kujeranshi yayi yana faWin. "Ina tausaya miki, domin kuwa nama na sakawa Zaki yadda zai fada yaci yana me shiga tarkona!"
Kamar yadda ya fada mata haka kuwa, ta isa kamfanin sai dai kuma tunda ta isa bata samu damar haduwa da kowa ba, asalima, kamar ba asan da zuwanta kamfanin ba, har yamma babu wani gamsashhen bayanin da zai bata kwarin gwiwa.
Haka ta tafi bayan an tashi gida ta nufa, tana isa wanka tayi ta kwanta domin tana hutun sallah. Don haka bata nemi abinci ba, sai dare. Washi gari da zata fita suka hadu da Abbas, nan yake tambayarta sun je gidan Hibba kuwa? Girgiza kai tayi tana faWin. "Kawu Nura zai zo daga Kamaru, idan yazo zasu tafi da abokin Abba in sha Allah da baban Chu-chu."

"Shi kenan. Ni dai ku tafi ku karbo min aure da Hibba!" "In sha Allah, kayi hakuri na makara." Ta fita da sauri, tana hada step, a kasa suka hadu da Hafsy! "Xnoo!" "Babu lokaci, idan na dawo zan har Wakinki!" Ta bude motar da sauri ta fada, tna sauke ajiyar zuciya. Da gudu ta sa kai zata fita Dundurosu ya tare mata hanya, sake glass tayi tana sako kanta. "kai mataccen nama, sai na bi ta kanka ne?" "A'a amma yau za a biya kudin wuta da na ruwa, kuma mun je har Wakinki jiya kina barci. " Bude jakarta tayi ta ciro katin banki ta cilla mishi. "kuyi kome kafin na dawo!"

"Har da sharholiya?" "Sai na kashe ka, idan kayi min wasa da kudi " ta fisgi motar a guje, ya ce. "Sai mun yi wallahi!" Dukan sitiyerin motar tayi tana faWin. "punk!" Ta kara wuta da gudun gaske, tafiyar da zai dauketa minti goma sha biyar, yar wutar ciki a cikin minti goma kacal ta isa harabar kamfanin, a hankali ta sauko kafarta wanda yake sanye da Hill na Vince brown sai jakar takalmin, sanye take da gown light brown, kanta sanye da yar dankwali ta daura shi baya, sai sunglass da ta saka shima brown. She look gorgeous and beautiful. Rufe motar tayi tana me takawa a hankali cikin nutsuwa, hannunta daya ri™e da jakarta da wayarta. Daya hannun ta soke shi a cikin aljuhun wandonta. Yau fuskar ba laifi hoda da kwali kawai ta dan goga, sai lipsglow.

Yadda take tafiya zaka iya cewa, wata macijiya ce, tsabar yauki da Yanga. Har ta shiga cikin kamfanin. Ma'aikatan kamfanin sake baki suka yi, suna kallonta domin ta share musu hadda, tana shiga ta nufi wurin matar jiya, ta tambaye ta shin Elbashir ya iso kuwa? Matar ta ce mata bai zo ba, kuma bata da sanin zai zo ko ba zai so ba. Shiru tayi tana sakawa da kuncewa.

A hankali ta d'ago idanu ta ce mata.
"Ko zan iya samun number shi!" "Kiyi hakuri Ma, tsarin aikin mu bai lamunci bawa Kowa number wani ba, domin akwai matsala idan aka fahimci haka!" Murmushi Zeenobia tayi tana faWin. "Babu wanda zai fahimci haka, idan kin bani" "amma Ma!"
"Shi kenan na fahimta!" Ta juya a hankali, jikinta a mace, Office dinsu ta tafi, tun da ta isa ta bata tsaya a ko ina ba, sai a wurin Mr Amjad. Tana shiga ta watsa mishi files din. "Kasan baka sama min appointment na zama da shi ba, ka bar ni sai yawo nake?" "Kinga ba wani abu bane, amma don zama da shi na nima, wallahi ki duba laptop din."

Shiru tayi kafin ta mike, "ina zaki?" "Gida!" Ta fada kai tsaye, tana me barin Office.
Wasa wasa tun daga lokacin, Zeenobia bata kuma gajiya da son ganin Malik ba, har sai da ta cika kwana talatin da bakwai, a ranar na bakwai tana isowa, Elbashir Jamal Arab, yana isowa a hankali ta bude motar dama, tana gabansu ne, dake an tura mishi sako akanta da kome da kome.

Har da number motarta, sai da tayi parking, ta fito a hankali yau sanye take da riga da skirt ta atamfar Super exclusive, wata yar karamar gyale ta rab'a a kafad'arta. Bakinta kuwa yaji lipstick alley, bakin kamar ba ita ba, gyara zaman glass dinta tayi, fari da shi. Sai da ta kwashe kome nata a motar, sannan ta wuce zuwa kamfanin duk da tasan shi ne amma duk kar a rena mata ajawali yasa baki daya ta tattara kome ta watsa a gefe, kamar bata san shi ba. Lokacin da ta isa cikin kamfanin dama sun santa suna ganinta suka tarbeta da hannu bibbiyu.

"Yau kam kin zo a sa'a, domin Oga ma ya zo!" Murmushi tayi tana faWin. "Ayya ba damuwa!" Ta zauna tana kallon agogon hannunta, har suka shigo kamar bata ganshi ba, tana ganin yadda mutane suka mike domin girmama shi, amma ita tana zaune kamar wata sarauniya. Shi kanshi Elbashir sai da ya kalleta da wutsiyar ido, yarinya ce jagab, amma girman kan na meye? Koda ya shiga office dinsa, a hankali ya fara ganawa da bakinsa, kafin aka zo kanta. Tashi tayi ta nufi office Winsa. Ko da ta shiga ciki kallon juna suka yi, kafin ta ja kujera ta zauna. "Ina jinki me ke tafe dake?" Shiru tayi tana kallon office Win, kafin ta ce. "Malik Menk Jordan!" Kura mata ido yayi kafin ya ce mata, "Idan baki da abin yi zaki iya fita!"

Dariya tayi tana fad'in, "Ni wurin Malik Menk Jordan nazo!" "Baki da lafiya, tashi kije dama tunda na ganki na san za ayi haka fita na saka a fitar min da ke!" "Ai kuwa ba zan tab'a barin nan ba, sai na fara ganin Malik" "ke mahaukaciyar ina ce?" Murmusawa mishi tayi sannan ta ce mishi. "Mahaukaciyar garin nan"

Daukar wayar Office din yayi ya ce.
"Security kuzo ku fitar min da ita;" murmushi tayi, tana fad'in. "Ba zan fita ba, sai na samu ganin Malik Menk Jordan!" Kwankwasa kofar aka yi ya ce a shigo.

Wasu irin kartin maza, shiga suka yi sannan suka sara mishi. "Kuyi min waje da wannan yarinyar!" Mikewa tayi tana faWin. "Zan baka nan da kwana uku, ka haWa ni da Malik kafin na binciko waye shi! Daga lokacin da na fahimci waye shi, da zaman lafiya ko da bala'i sai ka haWa ni da shi. Ka ajiye kalmata." Ta juya ta fita ba tare da ta kuma cewa cikanka ba. Baki sake yake kallonta tabbas yana ganin tsagera amma ita wannan uwar tsagerancin ce.
Tun daga ta fita taa sauke ajiyar zuciya, bata tsaya ba asalin cikin gari ta nufa. Unguwar Kauraye, tasan ba zasu rasa wanda yasan Malik ba. Don haka ta nufi gidan Basiru Kaura.

Zama tayi tana kallon shi, ba zata manta Nasiru Kaura ba a rayuwarta. "Kaura! Waye Malik Menk Jordan!" Ware idanu yayi tare da rufe mata baki, "shiii!" Juyawa yayi ya riko hannunta suka shige cikin daya daga cikin dakunan gidan. "Baki da hankali ne? Kin waye kike son sanin waye shi?" Kallon shi tayi sannan ta zauna tana faWin. "Yau nake son sanin waye Malik ? Idan baka sani ba fine!" "Ba zan iya baki labarin Dodonmu ba, amma ki tafi unguwar kudu, wurin Boss me hannu daya, ya baki labarin artabon shi da Malik!"

"Tir!" Ta fada tana me mikewa, barin dakin. "Kaji da kyau sai na nimo, Malik Menk Jordan!" Daga haka ta bar gidan, gidan su ta wuce, tana me alkawarin shigar dare zata yiwa Unguwar kudu, tasan unguwar matattarar duk wani shaidanin marajin magana ne, don koda ta koma gida, ba wani damu ba, abincinta kawai ta ci ta nufi dakin da take ajiye wasu kayan fada. Tana ganin kiran Mr Amjad taki dauka, ai yasan abin da yasa shi hadata da Malik kuma yanzu zai addabeta da kira.

Sai da ta dauki kayanta, sannan ta koma dakin ta shirya cikin kwarewa, sannan ta saka bakakken kayanta, ta saka tare da nufar unguwar kudu, da mashin din Black ta nufi unguwar, da tambaya ta isa gidan Boss me hannu daya. Yana tsaye a wani shago wanda ake sayar da duk wani nau'in makami, amma babu bindiga.

"Boss me hannu daya, Nazo sanin waye Malik Menk Jordan?!" A mamakance kowa ya juya.yana kallonta.......
Kuncanki wacce drama zata fashe next page.....
*Assalamu alaikum......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500¦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A'ishah. +227 84 50 64 76 500*
*Idan na samu lokaci zan karo page 1 zuwa dare! In sha Allah*
[8/28, 2:44 AM] Maman Sadiq Da Khadijah: CINIKIN RAI....15
Beauty and the beast.
Mai_Dambu<Øß
Maniyyata sun fara payment! Jiran me kike?
<<<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>>>>>>>
Baki daya suka juya suna kallonta, idan ka gansu, karti ne na bugawa a mujalla, Murd'ad'an Giants. "Waye Malik Menk Jordan?" "Timmmmmm!" Aka bugata da kasa, sai da taji kamar kashin bayanta ya rugurguje. Domin buguwar irinta a kai ka lahira ne babu notice. Ganin yadda suka bugata da kasa, bata tashi ba suka juya abin su suna cigaba da aikinsu. "Boss me hannu daya,waye Malik Menk Jordan?" Sake surarta aka yi aka maka da tsohuwar motar da take wurin, "wash Allah na!" Ta furta dakyar domin ta bugu asalin buguwa, tashi tayi tana nishi dakyar.
"Last warning ka gaya min waye Malik Menk Jordan!" Da wani irin gudu, mutumin yayi kanta, kafin ya isa ta gyara tsayuwarta, kafin ya idda nufinshi akanta, ta saita shi tare da dukan wuyar shi sai, ya cilla kafin ya fadi sosai a kasa, juya wuyarta tayi ya bada wani irin sauti. Sannan ta ce. "waye Malik Menk Jordan!" Da gudu kartin mazan nan suka nufeta, karfe ta dauka a kasa kafin su isa wurinta, ta isa, gare su ta shiga musu wani irin jahilin duka, idan baka tsayar da tunaninka ba, zata zaka yi ganga ake bugawa cikin wani irin zafin na'ma. Duk abin da yake faruwa Idanunta a rufe. Sai da suka zube baki daya. Sannan ta bude idanunta hancinta yana zubda jini. D'aga kai tayi sama, sautin takunshi taji kawai ta kara rike karfen hannunta, kafin ya yi tunanin kai hannunshi jikinta tuni ta kai mishi wani irin bugu a gefen kanshi. Sannan ta kalle shi ya fadi a sume.

"Waye Malik Menk Jordan?"
"Hmmm yaushe aka haife ki? Yaushe aka reni ki da zaki gwada kwanji da Malik Menk Jordan, kin san waye shi? Shi din Mayor ne birnin nan bakidaya, a shekara sau uku ake ganin Malik Menk Jordan, sunan shi kad'a hantar fusatattun maza yake, balle kuma muryan shi firgita mace me juna biyu yake. Shi karfin da shi daya daidai yake da na kartin maza Wari, kasuwancin sa yana sama da Ibadar shi da ki tab'a Mishi Kasuwancin sa gara ki kona garin nan ba zai tab'a kula ki ba, Yarinya Malik Menk Jordan ba kanwar lasa bane koma gida kiyi hakuri, idan wani abu ne a tsakaninku tabbas ba zaki iya ba!" Wani irin duka ta kaiwa kofar da yake tsaye, sai da kofar ta karye.
"Farautar shi na fito a daren nan babu makawa sai na sami abinda ya kawo ni, idan kuma aka ki bani, zan ta karya maka mutanenka ne!" Ta fada tana goge jinin da yake gefen bakinta.

"Zan gaya miki, amma ki sani sanin Malik ba abu me sauki ba ne, kinyi yi yarinya da son sanin wani waye shi. Zauns na baki labarin Malik Menk Jordan! Dan kazar da Uwarsa ta kasa, Allah keci da abinsa. Giwa babbar dabba, Zaki baka cin bakin wasu sai dai kaci ka rage."
------------
Kasancewar Hausawa sun yad'u ta hanyar fatauci da kasuwanci, yasa duk inda suka samu matukar wurin akwai kasuwanci basu tab'a barin wurin.
Mahaifin Malik ya taso tun daga Birnin Kano, ya sauka a garin Keivroto, mutum ne da yake da nasibi da Kasuwancin, sannan yana da matukar wadata. Domin daga yadda yake shiga ta Alfarma, gashi yana da gogewa a kasuwanci. Izuwa lokacin da ya iso garin babu wani bakin fata da yake da damar yin kasuwanci, domin turawa mulkin mallaka sun mamaye ™asar da kasuwanci. Kuma wani abin damuwa anan yadda baki daya aka hana wasu yan kasuwan sai fararren fata da larabawa.
Masu mulkin garin babu abin da suka sani sai cin hanci, idan ka sakar musu kudi, zasu baka garin kayi yadda kake so, shi kuma kasuwanci yazo yi. Don haka ya sake musu bakin aljuhun. Suka yi yadda suke so, a lokacin akwai wani tantirin dan kasuwa Mr Jahid Khan kaf Keivroto kowa yasan halinshi.

Sonkai, son zuciya, bakinciki da keta,
mugun da zalunci, mutum ne da baya bukatar kishiya, duk abin da za a gani daga gare shi ake gani, shi yasa ya k'amk'ame sauran jahohin baki daya. Menk Jordan yana da mata da Yaronsu, baturiya ce tana Demark, asalin ™asar ce mahaifinta babban malamin katolika ne, tunda ta ga Menk Jordan tace bata da miji sai shi, Menk Malik Jordan, Jordan ya samu asali ne daga kakanshi wanda suka yi tafiyar kasuwanci har aka haifi Menk, lokaci kakan da Uban basu nan, Malam Abdul Malik yana zuwa, ya saka mishi Menk domin mahaifinshi ya rasu a jordan. Shi yasa da ya girma yaji tarihin mahaifinshi a inda ya rasu ya kara Jordan a sunansu, domin Jordan yake kiran Kakanshi, sai ya zama mana Jordan ya fito as family din su.

Menk Malik Jordan ya fara bin kakanshi fatauci har zuwa lokacin da ya fara zuwa da kanshi. A wani tafiyar da yayi ya dawo ya samu labarin mutuwar kakanshi, haka yasa shi bazama, duniya niman kudi, sai yar Uwar.

Bayan tafiyar da yayi ya kai karo har Demark anan ya hadu da Diana, wacce tayi ruwa tayi tsaki, tace sai Menk Malik Jordan. Ubanta da yake yana sonta, ya barta ta aure shi, da cewa ba zata yi musulunci ba, baki daya sun gina rayuwarsu ne a Demark, har suka samu cikin Malik, haka suka yi ta tarerayar cikin har aka haife shi lafiya kalau. Kafin ya tafi Kano ya dauko yar uwar shi. Suka zauna da matar shi, duk wani kulawa Qudussiyah ta musu,

Wani abokinshi ya bashi shawaran su tafi, Keivroto kasuwanci, babu karya Malik da danginshi kasuwanci a jininsu take, domin duk abinda suka tab'a tana yad'o da yabanyayya.
A bangaren Keivroto kuwa, tunda Jahid Khan ya ga Menk ya fara samun jama'a sai kishi da bakin ciki ya fara kama shi, haka yasa shi fara turawa ana lalata duniyar Menk, wanda har ta kai an mishi wani irin taron dangi, amma mutumin bai yarda yayi give up ba, haka shi da matar shi suka kara hada karfi da karfe suka kara habbaka Kasuwancinsu. Abin mamaki sai gashi kasuwancin yafi nada albarka.

Bayan shekaru goma, lokacin Malik yana da shekaru goma sha bakwai, wannan iftila'in ya faru da su, shine na farko konewar Kamfanin Menk Jordan house, kamfanin yin takalmi da jaka, abin tausayi wannan itace mafi girman asarar da yayi a lokacin. Domin Diana tsabar kuka sai da ta daina gani, ana cikin wannan yanayin wasu daga cikin abokanshi suka saka shi zuwa amsar bashin duk da baya so, haka suka tilasta shi amsa, yana amso kudin barayi na biyo bayanshi, suka amshe kudin tare da mishi shegen duka.

Ko kwana Waya baa yi ba masu kudi, suka shiga mishi sallama, last dai abin da ya faru shine wasu sun zo gidan sun mishi kashedi. Daga haka sai tsintar gawar shi aka yi ya rataye kanshi, duk da masu binciken gawa sun tabbatar da ba kashe kai bane, kisan kai ne. Haka ya d'aga hankalin Diana wacce bata kawo haka Aranta ba, sai da ta kusan zarewa, kafin Allah ya nufeta da dawowa dai-dai, karshe bayan rasuwar shi ta musulunta, ta koma Salsabilah,. Abin haushi suna wannan rayuwar aka kwace musu kome nasu, hatta passport da zai fitar dasu kasar an kwace haka yasa Malik ya shiga tashin hankali, ga Mamanshi da bata da lafiya. Haka wata rana ana ruwan sama, ta fara rawan dari yaron nan ya rasa yadda zai da ita, dole ya shiga niman wanda zai taya shi su kai Mamar asibiti be samu ba. Dole haka ya dawo, sai a wani tsohon wheelbarrow ya dauka ya sakata suka tafi asibitin, yadda zaka san an shirya kashe su domin da ya kaita babu wanda ya damu ya duba ta, sai ya ajiye kudi haka suka barta a dandaryar kasa, ya fita yana yawo kwararo-kwararo. Kafin a hanya motar Jahid Khan ya buge shi, bai damu da buguwar ba, ya tashi.....duk da ba yawa managing.....
*Assalamu alaikum......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500¦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A'ishah. +227 84 50 64 76 500*
[28/08, 7:47 pm] usmanlauratu71: CINIKIN RAI....16
Beauty and the beast.
Mai_Dambu<Øß
Ai dama kome a shirye yake, don haka Jihad Khan ya fito, yana faWin. "Yarona! Ina zaka a cikin wannan daren? Ina iyayenka?" Girgiza kai Malik yayi yana faWin. "Babana ya rasu, Ummata tana asibiti, zata mutu don Allah baba ka bani kudi a duba ta!" Ya fada yana me rike kafar Jahid Khan.
"Ai kai Yarona ne, dole a kula da mahaifiyarka, muje na ganta." Riko hannun shi yayi suka shiga motarshi, suka nufi asibitin, kallonta yayi in pitiful kafin ya ce. "Ina Director na asibitin nan?" Baki daya asibitin aka taru musamman Drs da nurses, "ku duba lafiyarta kafin na dawo!" "Ok Sir!" Suka fada, sannan ya rika hannun Malik suka fita. "Yarona zan baka wani aiki, kafin ka dawo za a kula da ita kaji." Gyada kai yayi. Daukar shi yayi har wani kofar gida, ya mika mishi ™aramar bindiga. "Ka shiga gidan nan, akwai Hashim Zubair, ka harbe shi. Shine wanda ya kashe maka Babanka ya dauke maka dukiyarka. Ka tattara fushinka a zuciyarka, ka dauki fansarka!" Gyada kai yayi, sannan ya fita daga motar, ya nufi gidan ba tare da wani abu ba, ya buga ai kuwa lauyan babanshi ya bude mishi kofar, "A'a Malik kai....!" Sake mishi harbin yayi har sau uku. Faduwa Hashim Zubair yayi, a wurin bai shura ba. Shima kuma Malik ko da ya gudu, ya sami Jahid Khan yana jiranshi, don haka yana Isa wurin shi, Yan sanda suna cafke shi. "Shine ya kashe babban Lauyan nan ta fafutukar kwato hakkin talakawa, a tafi ea shi." Sake baki yayi yana kallon Jahid Khan. Har aka saka shi a motar yan sanda. Haka suka tafi da shi, a hanya yayi ta dambe da su har suka yi hatsari. Ya fita dakyar, daga nan bai tsaya ko ina ba sai asibiti, koda ya isa ya samu Mahaifiyarshi ta rasu, tsayawa yayi akan gawar har aka zo aka tafi da shi, ba a taba kai mutum gidan yari babu shara'a ba, sai akan Malik, tunda aka kai shi, ake dukanshi da azabtar da shi, sai yayi wata shida a dakin da babu haske ko kaWan, sannan aka fito da shi. A lokacin Jahid Khan yazo yake bashi labarin shi ya kashe iyayenshi, shima anan aka kawo shi, tow makabarta shi ce, Malik bai ce mishi kome ba, domin a zaman da yayi cikin gidan ya koya mishi shiru ko nace mutuwar Iyayenshi ya saka ya koyi hakuri da shiru, wasa wasa sai da Malik ya kwashe shekaru sama da goma sha biyar a gidan Yari, an manta da tarihinshi a lokacin muka hadu da shi, amma kafin mu haWu Malik ya gawurta a cikin gidan Yari, domin sai da ya kwace duk wani matsayi da masu fada a ji a cikin gidan. Malik ya samu karfi tun a cikin gidan yarin, domin Yaran da yake dashi a cikin gidan suka fito tow kasuwanci suka fara mishi, misali fasa kori, sayar da kayan maye, shiga harkan siyasa, Yaranshi sun yi karfin suna..
A lokacin sai da ya kai babu wani ne tarin matasa irinsa, gashi a cikin gidan ya

Please Login or Register in order to submit comment