Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hotel din, muje na muku iso cikin dakin taron. gyada kai tayi, suka shiga cikin hotel Win, sannan suka fara zaga cikin dakin taron.  lokacin da aka gama taron baki daya suka fito ko daya bayan daya suka fita? girgiza kai yayi ya ce mata.
 Mr Elbashir Jamal Arab ta fara fita, tare da yan majalisunsa, sai Prime minister. kallon shi tayi tana kallon agogon hannunta.  an samu minti nawa a tsakaninsu? shiru yayi yana kallon sama kafin ya ce mata.  Za a kai minti Talatin zuwa arba'in! gyada kai tayi tana cewa.  Ok ina son zan duba dakin da Cctv din ku yake.  Ok Ma da ya fada, tare da yiwa Wan sanda da suke tare jagoranci har dakin. Ita kuma ta cigaba da zaga dakin taron tana kallon wurin.

Har yamma suna zaune a wurin, kafin karfe uku garin yayi tsit, a hotel Win tayi salla, sannan suka koma office dinsu. Anan ta ga an kama mutane dayawa, wasu yan jagaliya ne, kallonsu tana faWin.  waWanan sune aka kama ko?  Yes ma! wucewa Office dinta, ta nufa tana me zama a kujerenta.  Ma ya zamu yi da su?
 A rufe su, kada a ba da belinsu, a tura su ga kotu. shiru yayi kafin ya ce mata.  Ma akwai mutanen Xno kuma ba a kama su da laifin tadda zaune tsaye ba, kawai dai sun fito ne zasu kai Yara asibiti aka kama su  Umarni aka ba ni, idan shima Xno din ya taka doka a karya shi, don haka kayi yadda nace. shiru yayi sannan ya ce mata.  Mace ba namijin ba ce. d'ago gajiyayyun idanunta tayi tana faWin.  Mace ce kuma yar daba? ta tambaye shi, gyada mata kai yayi.  Ku tattaro min files na masu laifi bakidaya, don haka babu zancen sake su.

Shiru yayi yana kallonta, bata san inda take tura kanta ba ne hala.  Hala baki san wace ce ita ba? Gaskiya ba zan iya wannan aikin ba, kawai a sallame mutanen. sake baki tayi tana kallon shi,.kafin ta ce mishi.  Nawa take biyanka? murmushi yayi mata sannan ya ce mata.  Ai ko daya bata biyana amma kuma ina gaya miiki gaskiya ne domin su yan jagaliyar nan sun fi mu, yanci don haka ki kyale mata Mutanenta, domin kowani lokaci zata iya zuwa kuma zata dauke su.
Murmushi tayi sannan ta ce mishi.  Ok ina jiran zuwanta. Ina jiran abin da zata yi.
-------
Bubuga kofar dakinta ake, domin tun bayan da tayi sallah hafsy ta fita. ˜wanciyarta tayi abin, bata san wainar da ake toyawa ba, abun da ya faru kuwa tighgas da ake wurgawa ne ya haifarwa Chu-chu numfashinta ya fara sarkewa wanda yasa dole Black da Dundurosu suka fita da ita zuwa asibiti basu gaya mata, bayan sun kai ta asibitin ne, shi ne Black ya ce bari ya zo ya sanar halin da ake ciki, ai kuwa yana barin asibitin yan sanda suka kama shi, duk yadda ya musu bayani amma fir suka ki yarda suka saka shi cikin yan kame. A gidan kuwa kiran Dundurosu suka yi ya gaya musu, ai ya turo Black an kwantar da Chu-chu. Ai ko ba gaya musu ba, an kama Black. Jin bugub ba na kare bane, yasa ta bude kofar  Zeeno an kama Black  barcin da bai gama wartsakewa bane ya neme shi ta rasa.  Garin yaya? nan suka gaya mata.......
#Mmmj
#Zeeno
#Beauty
#Beast
#RomanceS
#Tycoon
#WeatherMan
#Rumors
#Jelousy
#Cursed
#Mai_Dambu
*08130269641 for more info*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: *CINIKIN RAI......*
Beauty and the beasta&

Mai_Dambu
BOOK ONE

004
 Meeeee? ta kuma tambayarsu a hargitsassen murya. Diriricewa suka yi bakiWaya tai musu ba wani irin kwarjinin da suka kasa samun damar bata amsa.  Nace, garin ™a™a hakan ya faru? sake shiga rudani suka yi, juyawa tayi cikin dakin ta tsaya cak, tama ruWe baki Waya tana me kallonta a madubi. Juyawa tayi ta kalle su.  Kuna nufin an kama Black?"  Eh Zeenobia! suka bata amsa. Doguwar rigar da tayi sallah la'asar da shi ta saka, sannan ta dauki key din motorcircly tare da hilmet, kallon shigar jikinta tayi sannan ta koma wurin kayanta ta sauya riga da wando sai top da ta saka. Sai wasu chain da tasaka a wuyarta.

Kana ganin shigarta kasan sai a hankali kawai, domin daga sama har kasa zaka gane abin ya motsa ne.  Zeeno ko zamu raka ki ne? da ta watsa musu harara tilas suka janye kudirinsu nason lallai sai sun bita.  Paul fito min da bike dina. jikinsa na rawa ya fitar, ya shiga karkad'e mata. Tana isa wurin ta saka key ta tashi machine din, wangale mata kofar gidan yayi. Ta cilla kan babban titi a guje. Ta ina zata fara ma? Ta ina zata shiga? Babban asibiti ta fara nufa, inda ta shiga bin lunguna da yake cikin garin. Har ta isa asibitin, shima da kyar aka bude mata kofar, tana shiga cikin asibitin ta wuce emergency room.
Mikewa Dundurosu yayi yana faWin.  Xnoo! takawa tayi har wurinsa ta kalli Chu-chu da take barci.  Ya jikinta? numfashi ya sauke sannan ya ce mata.  Sunce zuwa dare zasu sallame ta, sai dai kuma ina ga an kama Black. cizon leSenta na kasa tayi sannan ta ce.  Ba gani ba ne, sun yi ram da shi ne, amma ai sun san mutane na, wani shafaffe da mai ne zai kama min iyalai na? saka hannu tayi a cikin aljuhun wandonta, ta ciro katin banki ta mika mishi.  zan tafi ka tabbatar idan an sallame ku, ka isa lafiya ko kuma ku kwana a nan, bayan nan kada ka saka rayuwarka cikin kasada. ta dunkule hannunta, shima ya dunkule na shi, suka dan naushi juna, alamar Goodluck.

Yadda ta fita bata tsaya ba, nufar shingen yan sanda tayi, tana zuwa kafe machine din tayi, ta nufe su.  Xnoo! Da fatan lafiya dai? murmusa musu tayi sannan ta ce musu.  Ina dan gidana da kuka kama? shiru suka yi, kafin suka yi kasa da murya.  Xno yana can babban office din mu, nasan Ammar yana can yana ™o™arin ganin an sake shi, ai ba zamu iya rike miki shi." Murmushi tayi sannan ta bar wurin. Kai tsaye babban office din yan sanda ta nufa, duk inda ta wuce babu wanda yayi yunkurin dakatar da ita, tana isa office din ta kafe machine din. Ta cire hilmet Winta nufi cikin office Win. Tana shiga ciki ta hadu da dan sanda da ya su a sake black. "Ranki shi dade, da Kanki?  Eh ina mutumina? shiru yayi sannan ya ce mata.  Kiyi hakuri amma. gyara tsayuwarta tayi, sannan ta ce mishi.  baka ji me nace ba ne?

Numfashi ya sauke, sannan ya ce mata.  ina jinki sai dai matsalar sabuwar ASP muka samu tana da zafin kai sosai. dariya tayi sannan ta ce mishi.  Zafin kai fa? Ok ina take? shiga cikin sosai suka yi don dama suna ba™in kofar shiga ne. Fitowar Asp Zulfa daga office Winta yasa suka tsaya cak.  Xno gata nan! ™o™arin danne fushinta Xno tayi tana me saukar da murya.  Ranki shi dade, nazo niman belin Yarona ne. kallonta tayi na wani lokaci. Kafin ta ce mata.  Kallonta a wulakance Asp tayi tana dandana wayarta.  Waye d'anki anan? nuna shi Xnoo tayi.
 Ok wancan dan ta'addan masu tadda zaune tsaye? Ko ba shi ba ne?

 Ina ga ke bakuwa ce a wannan yankin, muna tarban bakinmu da karammawa ce, sai gashi ke a rashin dace kinzo lokacin rashin sa'a. Please sake min shi, domin ya kai mara lafiya asibiti ne aka kama shi. Zeeno ta gaya mata.  Meye shaidarku?" Ciro wayarta tayi ta mika mata, tana faWin.  Asibitin da ya kai mara lafiyar ne suka zari kudina, sannan bayan nan idan baki gamsu ba zamu iya zuwa ki gani da idanunki! mika mata wayar tayi tana tab'e baki ta ce.  wannan hujjar bai gamsar da ni ba, domin naji labarin kina cikin yan daban da suka yi kaurin suna?

Cizon leSenta tayi, tare da matse hannunta. "Yar sanda, ba bincike nazo ki min ba, belin Yarona na zo beli. yadda Zeeno tayi magana ne ya bawa Zulfa haushi, ya Zeeno tana yar daba, mara yanci zata mata magana kamar wata me yanci, bayan ita kaki ne a jikinta.  Kai bude wancan cell din ka watsa min wannan mara kunyar a cikinsa na ga waye ya tsaya mata a faWin garin nan. dariya Zeeno tayi tana faWin.  Ni ba fada nake nima ba, amma tabbas zaki yi kuskuren da zai janyo hankalin waWanda suka tsaya min ba ni mutumina! hannu ta kai da nufin hankad'a Zeeno. Cikin wani irin zafin nama,. Zeeno ta juyar da ita daga nufin hankad'ata, karshe ita ta fadi warwas.  Kinga yar sanda ba fada na zo ba, don Allah ki bani mutmina!

 Kika kifar da Yar sanda a bakin aikinta? Lallai yau zaki sani! Ciro waya Zeeno tayi ta shiga latsa wasu number, can kuwa aka dauka.  Yallabai gamu a Office din yan sanda, ta kama min Black kuma tana son lallai sai ta keta min jikimata." Kashe wayar tayi tana kallon Zulfa da ta kallo wasu irin kwagirin domin dukkan masu laifi wasu tika-tikan dasu.

Nufar Zeeno tayi, amma kafin ta iso an kira layin.  Hello yallabai? shiru tayi.  Yallabai yan jagaliya ne masu tadda zaune tsaye fa, idan aka sake ta ai. shiru tayi tana kallon Zeeno da ta koma daya daga cikin kujerun cikin office din ta zauna tare da fara fyeduwa.  Ok Sir! ta fada ranta a matukar had'e.  Ke yar sanda! Ba gaba da gaba, ko ta baya irinki goma sai sun shirya, kinga da kira daya. Me zai faru idan kika kara aikata makamancin irin wannan kuskuren. Takawa tayi har gabanta.  Tube jami'ai irinki nake a bainar nasi na zane mazaunan su, sannan na saka su, su lashe ™asar takalmina. ta wani d'ago mata takalmin kafarta, ta nuna mata tana murmushi. A fusace Zulfa zata nufeta.  Madam gaskiya kibi umarnin na sama dake, idan ba haka ba. shiru tayi, tana gani aka bude Black. Zeeno ta riko hannunshi suka bar Office. Har harabar office suka nufa, ranta na soya tabbas yar sanda nan, taci albarkacin Mr Amjad, haushin da bata sauke a kan Zulfa ba, shi ta sauke a kan Black. Domin tsinka mishi mari tayi. Sunkuyar da kai yayi,  Kasan yadda ka zubda min da mutuncina? Har ni yar sandan can zata rufe? Me yasa baka kira ni farkon al'amarin? Kasan waye na kira ya musu magana? Kada ka kuma min wannan gangancin." Daga haka ta cilla mishi key din machine din, ta nufi wurin motarta. Daukar hilmet yayi ya saka, sannan ta shiga motar tana me tadda shi. Horn tayi me karfi da tashin hankali. Fitowa Asp Zulfa tayi ta zuba mata idanu. Sannan ta wani juya tare da d'aga musu kura. Fyaduwa sajan Barau yayi yana me dariya. Kallonshi Zulfa tayi ya daina,  Waye ya tsayawa wannan yarinyar da commissioner ya kira ni da na kyaleta?
 Yar kunama kenan, yar karamar mace sai babbar kasada, tayi nata tayi na me karamin karfi. Yar jagaliyar da babu irinta. juyawa tayi tana faWin.  Akwai files Winta ne a Office din nan? gyad'a kai yayi yana kallonta.  Muje ka bani. dariya yayi yana faWin.  Madam me zaki duba a cikin files Win? Ki rufe shi kamar yadda aka rufe domin babu wanda ya isa ya bude har ya kamata, kada ki manta halin da ake ciki na case din Prime minister.

Wuce shi tai tana faWin.  Ba ni file Winta." Haka ta wuce, duk yadda ya so ya mata bayanin wacce Zeenobia amma fir taki saurarenshi. Haka ya wuce ya shiga duba tsofin kundi har ya ciro mata, ya fita ta kai mata. Office Winta ya kai mata, tana zaune ya ajiye mata. Tana waya, da alama da babba take wayar sannan ta ce mishi.  Ok Sir Allah ya kawo ku lafiya, amma an samu zaman lafiya domin an dakatar da zanga-zangar babu wani abu, sai case din Prime minister. Naji kace Arshad Abdul Qayyum, zai zo don haka na ajiye kome cikin kulawa, babu abin da na tab'a tunda zaku wuce da shi. Capital Crud shiru tayi kafin ta ce.  In sha Allah sir, amma a dan bani damar wani ayyukan please Sir akwai aikin da nake bukatar farawa." Murmushi tayi tana sosa goshinta.

 Ok Sir!" Ta fada a kunyance, domin idan na an gaya maka tana sa matukar kunya ba, ba zaka yarda ba don irin manta nan ne masu yanayi biyu kunya da mutunci, haWe da zafi me yaji. Ajiye wayar tayi.  Sajan Barau ka kawo? gyada kai tayi. Mika mata yayi a hankali ta amsa. Ta karkad'e shi tana kallonshi.  Jami'a na musamman zasu zo daga Capital Crud City, sune zasu amshi case din Prime minister.  Ayya kice dama kwantar da tarzoma kika zo yi? . Gyada kai tayi tana buWe file Win. Hoton Zeenobia ne, me dauke da manyan rubutun sunanta. Zeenobia Nasr Hadejia. Kura mata idanu tayi kafin ta fara buWe shafi na biyu.

A ranar talata ga watan march, an kama yar shekaru goma sha biyar, da laifin duka Mr Martha's vineyard, a tsohuwar unguwar tabkin. Shiru tayi tana kallon hotonta a lokacin tana karama ne ba. Ajiyar zuciya tayi. Sake bude wani page tayi tana kallon. A hankali ta gama bude file Win, kusan duk laifuffukan da ta samu, laifi daya ne taga an saka babu hujja.  Sajan Barau! ta kwala mishi kira. Shigowa yayi ya sara mata.
 Naga wani laifi amma an ce babu hujja, an rufe case din. Sannan wacce ita? ajiyar zuciya ya sauke yana me cewa.
 shekaru goma sha uku, baya da suka wuce an tsinci gawar yan ta'addan Eagle bandit sakamakon ambaliyar da aka yi na kwacewar da Dam yayi, a cikin mutanen da suka tsira har da yarinya yar shekara bakwai a duniya, wacce ta manta da wasu abubuwan da suka shafi rayuwarta na baya. Lokacin ban jima da fara aiki ba, wannan al'amarin ya faru. Alhaji Badaru Daniyal shi yazo har Office din yan sanda tayi cike-ciken takardu, sannan ya amshe ta.
Matsalar da aka samu, shi ne tayi fama da matsanancin ciwon mantau, wanda ya sa ta koma kamar ba mutum ba, domin ba a san lokacin da ta dauka a hannun yan garkuwa da mutanen ba. Amma laifinta ba farko kamar yadda kika gani, Laifin duka tayiwa Martha's vineyard, domin a lokacin yayi kokarin wulakanta uban rikonta ne, ita kuma ta hana faruwan haka. A lokacin da aka kawo korafin DSP Ayuba, shi ya saka aka kamota aka rufeta, tun daga lokacin da aka sake ta, ba a kuma samun kyakkyawan alaka da ita ba, domin sai ta fand'are, Madam garin nan yayi shura akan zalinci, wannan zalincin shi ya samar da Xno, domin kare mutumin da ya™e dawainiya da ita, Madam ban san zahirin gaskiyar abin da ya faru ba. Amma sakamakon sauya-sauyan wuraren aikin da nake samu, ban san dalilin da ya mai da ita cikakkar yar daba ba, sai dai dawowa na garin nan na fahimci tana ™are gidan al'umma charity House. shiru tayi tana kallonshi.
 Ko tana karuwanci ne? ta tambaye shi, kafin ya ce mata.  Subhanalillahi, idan aka ce daba da jagaliyanci, tow kuwa babu sama da ita, domin da kankantar shekarunta, take dakawa maza gunba a hannu, tunanin tana hulWa da maza duk ban sani ba. mikewa tayi tana faWin.  Dole mu dawo da case din da aka ce babu hujja, sannan ina da ayar tambaya akanta, domin ban yarda da ita ba. She acting over confidence.  Ok Madam .  Dole nayi digging a rayuwarta single mistake na samu a rayuwarta sai na bude mata wuta ita da dabar ta.

****
Zeeno.
Koda suka isa gidan, jama'ar gidan kamar su goya su suke, sauka tayi a motartana faWin.  Daga yau duk abin da ya faru, kafin a aiwatar da kome, a tabbatar da an sanar da ni kafin ayi wani aiki. Wannan mutuwar Prime minister, ya sauya mana kome don haka kada wani ya sake ya fada hannun wancar yar sandar domin ba zai mana kyau ba. Idan wani abu ya faru daku rayuwata ce zata cutu, wannan al™awari ne da na dauka muku, don Allah ku dinga nazarin kome kafin ku aiwatar!
 Ayya Zainobia kina da naki rayuwar ki kyalesu mana, kema kiji da naki rayuwar mana. inji Hafsy. Domin tana masifar jin haushin ganin yadda Zeenobia take bada rayuwarta akan mutanen nan.
 Hafsat ba zaki gane ba ne, su din sune ni idan babu su, tow kuwa babu ni.

TaSe baki tayi, tana me wucewar ta domin tasan yanzu dai sai su raba hali akan mutanen da take mutuwa akan su, basu sumarta.
Tunda ta zube a saman gadonta take, sauke ajiyar zuciya. Exactly 3 year sanyi ne da ciwon kai yake bibiyarta tun safen yau amma baki daya ba ta ce ba. Don rabonta da wannan yanayin.
****
Green House.
House of representatives. Crud City Hall.
Yan majalisar kolin ne suka hadu. Shiru hall din ya dauka, domin tattaunawa akan abin da ya faru. Fitowa Assamblywoman, Mss Lalla Salmah ta zuba musu idanu kafin ta ce.  Izuwa yau duniya da sauran ™asashen nahiyar Afirka, sun daura idanunsu akan Mayor Malik Menk Jordan, Ni dai ban laifin shi ba, kuma har abada ban zan ga laifinsa ba, domin kare kai da dukiyarsa baya nufin ya kare kansa a matsayin lusari ba.

 Keee Lalla Salmah, babu me sauraren wannan zancen naki. Dole majalisar koli ta sauke Mayor Malik Menk Jordan, ko kuma mu Wauki mataki akan dan ta'adda." Inji wani dan gajeren mutum me katon ciki. Dariya tayi tana faWin. "Same scandalous wai suna da bakin magana, mutanen da basu gudun abin kunya.

Kura mata idanu yayi har ga Allah, maganar ta bata mishi rai. Bai san lokacin da ya fara kokarin tsalleke wurin zamansa ya tsallako wurinta ba.  Idan ban miki shegen duka ba, Alqur'an uwata shege ta haifan!"
 Mr Abid ka kiyaye bakinka, Mayor Malik Menk Jordan ba kanwar lasa ba ne, don haka muje ga tattaunawar mu. Kowa yasan waye Malik, sannan izuwa yanzu abin da ya faru ya dace mu nazarci meke yake faru.
 Yallabai, harkan Kasuwancin garin Keivroto city harka ce ta ban mamaki. Sai dai a bangaren ilimin rayuwa dole a fuskanci matsala, ba laifi ba ne idan Malik ya k'amk'ame kome, ai na shi ne. Kuma iyawarsa ya kai shi wannan matakin. Ko mutuwar Prime minister bana da ja tabbas bai da cikakken masaniya akan mutuwarsa.
 Wai Lalla Salmah me kike son fada? Me kike son gaya mana? Waye bai san cewa kaf duniya Malik bai daukin ran kowa da daraja ba, har kwanan gobe Malik ubangijinsa shine kudi, matansa kuwa kartin maza ne kin isa ki kare shi da abin da ya faru, shekarun talatin da wani abu baya, tun yana daura igiya a matsayin zariyar wandonsa muka san Malik shi kare ne, wild dog ne da muka watsa mishi kashi ya bi yana haushi, duba kaina Lalla Salmah. Kin fito daga babban gida kada ki sake goyan bayan da Malik ya baki, ki tab'a nasabar gidan ku. Ka da ki zama me bawa kasungurmin dan luwaWi goyan bayan. Ba zamu lamunci haka ba, don haka dakatar da Malik ya zama dole.
 Shu'iba kada kayi wasa da rayuwarka,Malik ba abin wasan yara ba ne ka iya kalamanka domin duk tsohon da bai
Kunyar hawa jaki, jaki ba zai ji kunyar kadda shi ba........"
*Hi......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500¦ normal 1k VIP for information 08130269641*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: https://chat.whatsapp.com/KZbdBOduk2c2nLpNQp7Qh3
CINIKIN RAI....!
Beauty and the Beasta&
006
_Past_
A lokacin da suka zo ganin wurin dayawan su, sun yi fatan da sune suka kawata wurin domin ai sune yan kasa ba Nasr Hadejia da Aswad Yamini ba. Taya ba™in haure zasu zo su fi yan gari kawo cigaba har haka, wani abin ya tsaya a ransu. Matukar tsaya musu. Kuma ba iya shi ba, asalin su mutane ne masu matukar Kyashi da Hassada da wannan dalilin yasa suka buWe iyakokin duk wani tubalin bakincikinsu, inda aka fara turo musu yan jagaliya suna yiwa mutanensu daukar amarya. Koda Alhaji Nasr Hadejia ya ga haka sai ya shigar da bukatar jami'an tsaro su shiga cikin al'amarin amma abin haushi sai aka yi rashin dace. Domin yan sanda bakinsu daya. Haka yasa jikinsu yayi wani zai ce me yasa suka nace da son suyi wurin shakatawa? Abin da mutum be gane ba, shi ne fisto yana cikin garuruwan da suke bu™atar a inganta su. Na farko zai samawa birnin cigaba, na biyu matasan garin da suke sana'ar daba da jagaliyanci zasu samu aikin yi, dattawan da suke sana'ar kamun kifi, zasu samu damar baje kolin sayar sa kifinsu. Sannan gari ne masu al'adar gargajiya. Wannan dalilin yasa baki daya mutane biyun nan saka zuciyarsu, akan lallai su kawo cigaba da garin.
A hankali kome ya fara kwace musu, domin a zahirin gaskiya yan daban sun dame su. Abubuwa biyu ya dame su, ga asarar dukiyarsu ga wasu daga cikin mutanensu a hannun yan garkuwa. Akwai wata rana da Alhaji Nasr Hadejia da Aswad Yamini suka hadu a gabbar tsibirin. Kowanen su, yana da damuwa amma dan samu kwarin gwiwa a tsakaninsu yasa suka sauke ajiyar zuciya a lokaci guda.  Hadejia ina ga ya kamata mu sake budar wurin Mayor Fahad Albagwi da wannan al'amarin, idan har muka yi haka tow ba makawa zamu samu adalci, kaf garin nan kansu a haWe yake ba zasu sake mana mutanen mu ba. kallon shi yayi sannan ya ce mishi.  Ni ma nayi tunanin haka, amma nasan Allah yana sane da al'amarin mu, Allah zai tsaya mana.
 Ka saka mana

Please Login or Register in order to submit comment