Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da tasan dalili ba, da farkon da Babanta yace zata auri Malik da kwana biyu su shigar da shi kotu, karshe a raba dukiyarshi a basu, tayi farinciki ko babu kome zata shiga sawun matan da suka shahara, amma once lokacin da aka gama kome suka yi magana da Malik sau biyu akan ta amince zata aure shi, sai da magana tayi ™amari kowa ya sani, duniya ta dauki al'amarin bawan Allah nan ya kira Babanta ya gaya mishi ya fasa aurenta.
Kuma tsabar girman kai, mutumin naj bai gaya musu dalilin da yasa ya fasa auren ba,sai dai kawai ya ce ya fasa kuma har yau tunda ya ce ya fasa ko da wasa bai kuma nimanta ba, wani bin tana jin zai kira Yaranshi su yi ta waya, amma ba zai tab'a cewa a bata ba, wani abin tashin hankalin tun daga ranar Allah ya daura mata sonshi da kaunarshi.
Kai ko waya yake kamar ta gigice haka take ji, amma shi ko ta kanta baya bi. Wani abin burgewa ita ubanta yake kokarin shigar da ita, amma ita ta tsaya a ina nan bata son cusa kanta tunda dai baya yi da ita no way da zata ce sai yayi da ita, number wayarshi hotonshi da Yaranshi suna wayarta amma ko sau daya bata tab'a gwada kiranshi ba. Tana tsoron kada ta kira ya sake mata gwiwa.

Daki Jaddah ta koma, Maidah tana kallon kome, kamar bata san meke faruwa ba. Lokacin da Jaddah ta koma dakinta itama Maidah mikewa tayi ta koma dakin ta kira Lalla Salmah .
"Maamah! Dama Malik aure zai yi?" "Waye ya gaya miki.?"
"Yanzu naji Jaddah tana fadawa Nadrah da ta tambaye ta."
A nan ta shiga gayawa uwar abinda yake faruwa, sosai suka yi gulmarsu, har da zagin Nadrah Khamis Shatima, bata da kamun kai tunda gashi ta iya tambayar ashe wanda ya fasa auren har aure zai yi.
----
Jaddah kuwa kiran Malik tayi, ya kashe wayar cikin girmamawa ya kira ta.
"Babata me kike bukata?"
"Babu kome Malik, kawai ban ji dadin yadda Yarinyar nan Nadrah take ta jiran ka ba." Shiru yayi kafin ya ce mata.
"Anne! Kin san meye? Har ga Allah na so aurenta, amma kuma maganar gaskiya ba zan aure ta ba."
"Malik naga soyayyar gaskiya a tare da ita, idan bar kace ba za a bata damar haka ba, tow babu amfanin zamanta a nan, ka gayawa Mahaifinta ya turo ta koma domin ta haka ne kawai zata cire rai a tsammanin samunka."
"Zan mishi magana, in sha Allah idan kuma akwai abin da take bukata a tambaye ta sai na mata, domin ba zan barta da haushina ba."
"Duk da haka, yana da kyau ka gaya mata gaskiya ta haka zata kara ganin girmanka, ki babu soyayya kai Uba ne mata, balle kuma izuwa wannan lokacin na fahimci girman yadda take sonka. Duk da ban san me ya sauka maka ra'ayinka akanta ba, amma ina son ka sani ta hanyar rarrashi zaka iya wanke abin da ya janyo rashin aurenku, amma ka sani matukar ba wani babban dalili bane, ka juyawa auren Yarinyar nan ba, tow wallahi Allah sai ya kama ka, domin tayi matukar kokarin zaman jiranka, Malik da ace kai kake bin mutum gara shi yake binka kayi tunani sa kyau!"
"Anne, dalilina me karfi ne haka kawai ba zan ki aurenta ba, kawai zan lallabata ta fidda wani mijin tayi aure amma maganar gaskiya, bana son aurenta don Allah Anne ka da ki min dole!" Gyada kai tayi kamar tana gabanshi ta ce mishi. "Ba zan maka dole ba, kana da ikon auren abin da kake muradi, ko dan Yaran Nuratu. Sannan Jalilah mun hadu da ita!" Shiru yayi kafin ya ce mata. "Anne zan duba wasu takardun."
"Malik idan ba zaka auri Nadrah tayi maka wani abu, tow ita Jalilah fa." Kai tsaye ya ce mata. "Kawaliyan ce zan aura na kai gidana? Allah ya gani ba zan iya auren macen da ban isa da ita ba, sannan macen da ina ji ina gani sunanta zai taba Martaba ta da kimata!" "Malik kimar ce da kai?" Ta fada a fusace, dariya yayi ya ce mata. "Anne kima ne dani, da ba ni da kima wacece zata damu da tsoho me farin gashi. Kawai ana bina ne domin kudina da kimata, idan bani da su karen layi sai ya fini daraja. Anne matar da nake son aure wacce bata damu da abin hannuna ba, me tausayi da jin kai, wacce ta dandani irin rayuwar da nayi, ba wacce zata same ni daga sama ba, duk da..!"
"Malik a ina zaka samu irin macen da kaje bukata? A wacce duniya zata zo maka? Malik kayi hakuri da abin da yake hannunka, ka auri Jalilah tunda duk lalacewar masa tafi kashin shanu, Jalilah kaWai zata iya tsaya maka."
"Anne idan na auri Jalilah, shekarunta arba'in da wani abu, yaushe zata haifa min Yara? Idan na auri Nadrah burin da yake ranta sai ta idda a kaina, idan na auri wata mace daban daga wani waje, tunaninta daban nawa daban. Anne so nake na samu macen da duniya bai dame ta ba, shiru shiru wacce bata da dogon buri" gyad'a kai take fuskartar a murtuke ta ce mishi. "Shiru-shiru ka tafi makarantar Kurame, wacce bata damu da duniya ba, ka auro Aljana kawai, Malik rayuwarka ce ka da kayi auren idan kaso, shashashan wofi" ta kashe wayar dama an saba kwana biyu ba a yi ba.
&&&
A lokacin da Zeeno take wuce babban titin, South Craig. Khamis Shatima yana tsaye a bakin bankin Savanna. Suna tattaunawa da wani mutum kawai taga motar ta, ta wuce. A gurguje yayi sallama yana me bin bayan motar. Duk da tayi mishi nisa amma sai da ya bita, ganin tana shiga wurin wanke kai yasa shi rage karfin gudunshi ya bi bayanta.
Koda ta shiga shima cikin harabar SALOON WORLD din ya shiga, yayi parking, ya jima a zaune a motar kafin ya fito a nutse ba zaka tab'a yarda cewa ya ajiye kamar Nadrah ba, akan idanun Asp Zulfa da ta biyo bayan Zeeno. Tasan haka kawai K Shatima ba zai zo wurin ba, sai dai idan Zeeno wurin ko kuma akwai matar shi a wurin.
Lokacin da Zeeno ta shiga yan mata biyu ne, suka tare ta sannan suka nuna mata wuri ta zauna, suka shiga kawo mata kayan motsa baki, kafin suka ajiye mata menu, shigowar shi yasa suka d'ago kai, kasancewar wuri ne na mata zalla, kuma babu wata babbar mace balle ace matar shi ce, duk yan mata ne a wurin musamman da yake satin biki ne, akwai bukukuwa sosai a garin.
"Yallabai meke tafe da kai!" Murmushi yayi ya zubawa Zeenobia idanu kamar maye.
"Wurinta Princess Zeenobia nazo!" Juyawa tayi tana kallon Zeeno da vata san me suke ciki ba, sai da ta bashi hanya, ya wuce ya tare da zama a gabanta. Kallon shi tayi irin kai kuma daga ina? "Nazo wurinki ne!" Ganin yadda aka zuba mata idanu. "Ko zaka bani dan tazara, irin wannan zaman yayi kusanci da yawa!"
"Duk yadda kika ce Baby!" Sake baki tayi kafin ta kuma maimaita sunan Baby. Galala ta sake baki ta ce. "Baby! "
"Yes you are my baby girl!" Kallon kanta tayi kafin ta ce mishi. "Hala Yarka da ta b'ata me kama dani ce ko?" Girgiza kai yayi ya ce mata. "Ina sonki!" Daga haka ya mike ya nufi inda ake biyan kudi, ya bada katin bankin shi aka zari kudi masu yawan gaske. Sannan ya dawo wurinta. "Ki kula min da kanki, ina bibiye da ke." Daga haka ya juya ya fita, da farkon ganinta da yayi ya so, suyi rayuwar watsewa amma yanzi da ua ganta, ya kuma hango nutsuwar da ba kowa ya dace ya hango ba, ya shirya tsaf domin ya aure ta. Duk da yaji labarinta da kuma ™o™arinta, baya fatan ya rasa kuma yaji labarin dabanci ne a gabanta ba karuwanci ba. Shi yasa ya dan bata lokaci kafin ya bayyana kanshi.

Tun da ya fita take kallon kofar, "in sonki!" Dariya abin ya bata, har aka gama mata gyaran ta nufi wurin biya aka ce ya biya har da sauran canjinta, kallon matar da take wurin biyan tayi ta ce mata. "Ki dauki sauran canjin." Ware idanu tayi tana faWin. "Ma kudin yana dayawa kusan dubu saba'in ne" watsar da hannunta tayi tana faWin. "Babu abin da zan yi da shi, dauka kawai." Har gaban Zeeno ta fito kamar zata kwanta mata a kasa, ita kuwa ta wuce.
A hanyar komawa gida a ka turo mata text.
*Kina ta shirin ganin Malik bari na gaya miki, wadanda suka fiki basu samu ganin shi ba, balle ke karamar Yar iska karuwa irinki idan har kina ganin karya ce, bismillah, kamar yadda suke renawa amintattunsu hankali haka kema zasu rena miki hankali*
Wannan sakon ya fusata Zeeno, tabbas akwai renin hankali a cikin maganar amma yau, ko da muzuru ko da shawo sai ta ga Malik.... (LALLAI DUNIYA DA MUNAFUKAI! DON ALLAH WAYE YA TASHI SABON RIGIMA ANA ZAMAN LAFIYA SAURA PAGE BIYU NA GAMA FREE PAGES)
*Assalamu alaikum......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500¦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A'ishah. +227 84 50 64 76 500*
PLEASE IDAN KUN KARANTA KU MIN SHARE FISABILILLAHI
[31/08, 6:31 pm] usmanlauratu71: CINIKIN RAI....19
Beauty and the beast.
Mai_Dambu<Øß

<<<<<<<|=|>>>>>>>>
Wannan shafin na kune
@h Saudah Jaafari
@h Aysha Dashen Allahi @h Maman Zarai @h Mom Intyi @h Ummu Ihsani @h Z Autai
=ضÞ<Øýß
@&þ=ØDÞ in da ba kasa.......
<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>
Yadda take tukin yasa aka yi ta kauce mata a hanya. Har ta isa gida, wanka tayi tare da gabatar da sallah. Tana idar da Sallah hafsy ta shigo tana kallonta.
"Baby ina kika shiga ne?" Wani banzan kallo ta watsa mata, tunawa da tayi da Shatima. Ta sanshi sarai domin yana cikin files Win Malik, amma bata zata zai kawo kanshi cikin sauki haka ba.
Murmushi Hafsy tayi tana faWin. "Malama kwana biyu, bamu hadu ba?" "Eh abubuwa sun sha min kai!" "Kuma shi ne babu magana!" Gyada kai tayi tana faWin. "eh tow kuma da haka, idan ban miki magana ba, ke uwar me bakinki yake da ba zaki min magana ba?" Sake baki Hafsy tayi tana kallonta. Kafin ta juya zata fita ta ce mata. "Yawwa idan zaki fita, ki rufe min kofar domin na tsani sauro ya cije ni." Wato ita Zeeno bata da aiki sai kunsa maka bakincikin musamman idan ka damu da ita.
"Dan Uban sauron ya kashe ki" ta fada tana me barin dakin a wangale. "Kambu! Na rantse ban yafe ba. " Hafsy bata saurare ta ba, domin ta lura iya shege take ji, don haka bata damu da ita ba.
Sai da tayi sallah magariba da isha, sannan ta cancad'a wanka, tare da wankar kure adaka, musamman da ya kasance babban mutum ne, kuma tana son gani daya ya sara mata, ya san cewa ita ba irin kananun tsagerun nan ne ba.
Tsaki tayi kafin ta kira Hafsy a waya. "Dan Uban mutum me zan mishi?" Murmushi tayi ta ce mata.
"Ki zo ki min light make-up!" "Hala ajiye ni kika yi, ba ni zuwa." "Mtseeeeeew, kinyiwa Kanki dama biyanki zan yi!"
"Shegiya kamar kin san bani da kudi, gani nan tawowa!"
"Mayyar kudi! Ko kunya baki ji ba."
"Ki gaya min inda bolar kudi yake, na je na tsinta dan kaniyarki " ta kashe wayar, Hafsy kwalliya take yi, tana zuwa har gida tayiwa mutane, duk da kusan kayan kwalliyar Zeenobia take saya mata ko ta bata kudi, duk da jagaliyarcinta, tana kwalliya kawai bata damu da saka kaya ba ne, amma yarinyar ta san darajar ado da saka sutura.
Can Hafsy ta iso bakin kofar, ta buga kofar. Bude mata tayi, kallon wata hadaddiyar doguwar riga blue-black, har sa hat dinsa. "Wow ko nace sexy!" Zama tayi ta fara Ciro kayan, tana faWin. "Dinner zaki ne?" "Lunch za ni" d'ago kai tayi kafin ta ce mata. "Wai ke meye matsalarki da bakar magana." Dauke kai tayi tana latsa wayarta kamar bata san me take tambayar ba. "Kutumar Uba!" Ganin hotonta an manna a wani shafin yanar gizo an rubuta.
*BA IYA DABANCIN NE SANA'ARTA BA, HATTA KARUWANCI DA MANYAN MUTANE TANA YI DOMIN SAMUN DAMAR HADUWA DA MALIK MENK JORDAN!*
aka saka hotonta a gefen wani blank pic da babu hoton kowa sai alamar tambaya. Lekawa Hafsy tayi, ta amshe wayar. "Kiyi hakuri abin da nazo gaya miki kenan, amma da nasan baki san da zancen ba da." "Yi min kwalliyar, na rigada nayi al™awarin sai nayi aikin nan!" "Amma Zeenobia! Ki daina shiga duk wata kazamar harka, domin da ita za.."

"Ki min kwalliyar kawai!" Haka ta shiga mata kwalliyar, har aka gama cizon bakinta take, tana gamawa ta ce mata .
"Done!" Murmushi tayi ya ce mata. "Yayi kyau, bude wancan drower din akwai abin da kike so, ki sauka kawai!". Ta zauna tana kokarin zoge rigarta. "Zeenobia!" Bata juya ba ya cigaba da kokarin saka rigar. "Kiyi hakuri!" "Da aka yi me?" "Da abin da ya faru!" "Kai manta kawai!" Da taimakon Hafsy ta gama shirinta tsaf, sannan ta ciro Christian Dior bag and shoe, ta saka hill ne sosai. Sannan ta gyara zaman takalmin.

"Zeenobia ya baki saka turarenki ba!" Murmushi tayi ta ce . "Ban manta da shi ba, duba can akwai Tom Ford cafe rose." Ciro mata tayi ta fesa kadan, take dakin ya dauki wani sassanyar kamshi. Kama gashinta kanta tayi, ta daure shi. Sannan ta daura hat din kanta, "Don Allah zan iya daukarki hoto zan daukar a IG na ne, zan yi magana ne!"
"Yaushe kika koyo takife?" "Zaman da Yar kunama!" Gyada kai tayi tana fad'in. "You're welcome!" Daukarta hoto tayi sosai, a wurin ta daura a IG.
*SHI KARUWANCI IYA CE, DUK WANDA YA IYA YA KWASHE, DUK WACCE TA JI HAUSHI GOBE TA SHIRYA GANIN MAYOR MALIK MENK JORDAN...... UP-UP-UP SARAUNIYAR VOGUE MAGAZINE COVER*

Dama bata da wasu followers, amma tana sakawa ta yi amfani da Hashtag tare da gidan gwamnati dake Waterfall island, take aka fara bibiyar pagenta. A cikin abin da bai haura minti Talatin ba, sai ga Followers sama da dubu biyu sun bi ta, amsar wayar Zeenobia bata ta gyara pagen din tare da saka hotonta, ta kuma rubuta cewa.
*The dreams can be true!* Kafin ta saka yar ™aramar hoton <Ø9ß kallon Zeeno tayi ta ce mata. "Yar kunama ina zaki ne ma?" "Hmmm! Ina son zan kaiwa Malik wancan takardun ya saka hannun jari ne?"

"Bura Uba! Dama haduwa da Malik ne wannan adon? A tow dole mu gayawa duniya mu haWu da Malik!"
"A'a bana bu™atar haka, ina son sirri a rayuwata, domin sirri na da dadi, DABANCIN dai da aka sani a bar shi a haka, ban da personal life, wannan nawa ne ni daya na, koda kika ga na bude account ba yana nufin kowani shirme zan daura a kai ba, ina son rayuwata da take binne yafi armashi."

"Kin sa jikina ya mutu, me yasa kike boye kanki?" Murmushi tayi sannan ta ce mata.
"Hafsy a gare ku, ni ba kowa bace face wacce kuke tare kuke haya gida daya. Amma a gare ni, kune duniyata idan wani abu ya same ni, ba zaku yi kuka sosai ba. Amma idan wani abu ya same ku zan mutu ina kukan abin. Rayuwar mu ta zahiri tafi dadi sama da ta social media! Ina son kowa ya za sani a zahiri ba ta media badili ba, kin ga ajiye wannan Posting din saura minti goma kacal na isa inda zamu haWu."

"Ok ranki shi dade, a dawo lafiya!" Daga haka ta dauki key motarta da jakarta da files din, ko da ta sauka kasa, cillawa Dundurosu key tayi yana cewa. "Kai katon banza muje ka raka ni!" Haka ya cabe, sannan ya shiga gabar motar tana baya. "Uwar Wakina, ina zaki haka kika tashi kan gidan nan da kamshi?" "Meeting!" Ta fada tana kallon agogon chopard, tab'e baki tayi tana faWin. "Bakin Waterfall island zaka kai ni!" "What?" "Ka kalli titi ka da ka watsar da ni a rami" daga haka bata kuma magana ba, har suka isa bakin ruwan tara saura minti biyu.

Sai dai abin mamaki, tunda tazo babu alamar akwai me jiranta, ko za azo dauke ta, tun tara saura minti biyu har tara da rabi. Idan ranta yayi dubu sai da ya Saci, kallon agogon hannunta tayi tana kwafa. "Muje Man" tasar da motar yayi suka bar wurin.
Da Sacin rai ta isa gida, tana isa ko magana bata yiwu kowa ba, dama kuma haka take idan ranta ya b'aci bata magana. Har ta isa Wakinta ta kwanta bata cire kayan ba, sai fuskarta da ta gyara ta cire makeup din ta kwanta, wurin karfe biyu na dare, tana zaune akan abin sallah, wayarta tayi kara. Bakuwar number ce don haka ta dauka tana me sakawa a kunnenta. "Me ya hanaki barci?" Shiru tayi tana son tuno muryan. "baki gane ni ba ne? Ai na yi following din ki a IG!"
"Shatima rite?" " Yes Baby!" Murmushi tayi sannan ta ce mishi. "Ai ko a duniyar mafarki bana jin kalmar baby ta dace da bakinka. Ai kai Babana ne!"
"A'a naki wayon. Baby Ina sonki da aure!" Ajiyar zuciya tayi tana faWin. "Don Allah kayi hakuri ni bana son wanda bai kai ka ba ma, Ni har ga Allah ka min tsofa!"
"What! Shekaru na basu wuce hamsin da takwas ba fa!"
"Allah na tuba, ai ko talatin da tara ya tsufar min balle me arba'in! Ni bana son me shekaru irin naka, kada ya wuce talatin da biyar. Yawwa muci kuruciyarmu tare ba wanda xan aura ya cinye min kuruciyata ba."
"Zainabia kin san me kika faWa?" Ya tambaye ta, in serious tone. "Yes na! Ni bana son namiji da ya tsufa. Ba a san waye gawan fari ba, idan ka mutu ka bar ni kafin na samu daidai dani ya aure ni, zan sha wuya so kawai hang out!" Ta kashe wayar.
Sake kiranta yayi yana faWin. "Ni ba irin wadannan tsofin ba ne, ina da lafiyar da zan baki kulawa, ki amince da ni." Dariya tayi sannan ya ce mishi.
"Kaga kuwa bana son tsoho, har ga Allah idan nace maka ina sonka nayi karya, kawai zan ta bata maka lokaci ne, idan na samu wani nayi aure ba ni da dogon buri. Iya abinda ba samu ya ishe ni, na fahimci maganata."
"Young lady! Ina son na gaya miki wani abu daya, zan cigaba bibiyar lamarinki!"
"Hmmm! Ina baka shawaran ka da ka tsaya ka tafi akwai yan mata dayawa!"
"Ni ke idanuna ya gani, ki haifa kin Yara kyawawa irinki!"
"Sai da safe!" Ta kashe wayar baki daya, a wurin ta kwana, wurin karfe shida ta farka, ta shiga ban daki tayi alola ta gabatar da sallah asuba, karfe tara ta nufi wurin aikinsu, taso ta tafi ta titsye Elbashir, amma kada ya ce akwai wani abu da take nima yasa ta share shi.

Office din chairman ta shiga domin, tun a block one ta fahimci, akwai matsala musamman yadda ake kara kallonta ana kallon wayarsu. Fuska tayi tana me shiga Office din. "Wacce irin abin kunya kika aikata haka?" Ya cilla mata jaridar. Daga bangon shafin ta hango an rubuta.
*BAN SAN IYA MANYAN MUTANEN DA SUKE BINA ZAKU KWANTA DA NI BA!* bata kuma marmarin karanta sauran bayanin ba. "VOGUE MAGAZINE sun cire hotonki a jikin mujallarsu.
"Dama ai ban aike su, su saka hotona ba! Sannan da ake ihu kamar kare ni na bukace ka ko kai ne ka bukace Ni? Kamfaninka kake niman cigabanta, kai me yasa baka fuskanci Malik ba? Kasan hadarin da mutuwar da na fuskanta? Amma ka bude wawwaran bakinka kana min ihu. Kaci arzikin halaccin da kai min da sai na zane maka mazaunanka wallahi!"
Daga haka ya juya ta fita, bata tsaya ba sai a wurin motarta, tana shiga wayarta yana kara. Šauka tayi aka ce mata. "Ki tow daga kamfanin, akwai wata sharon ki ajiye motarki ki shiga."

"Waye kai?"
"Kiyi yadda nace!" Da farko ta dan rude, amma kuma daga baya sai tayi kamar yadda ya ce, har inda motar take ta ajiye. Sannan ta shiga sharon Win, sai da aka kaita gindin gada, aka bude mata bayan an zazzage jakarta da takalminta, sannan aka nuna mata wata Audi,. Shima suka fara tafiya sai da suka bar cikin gari, sannan suna isa wurin da aka ajiye wata mota Rr, ta fita sannan aka bude mata shi, ta shiga a hankali. "Wai ina zaku kai ni?"
Wayarta tayi kara tana dauka aka ce mata. "Saurin me kike?" Aka kashe wayar, ana fara tukin, aka saka mata wani abu tare da rufe mata fuskarta.
Sannan suka fara tafiya, sai da aka yi tafiyar minti Talatin kafin aka fito da ita, tana jin lokacin da aka tadda injin kamar jirgin ruwa. Haka aka yi ta gudu da ita, ba halin ta bude fuskartar. Suna isa ana fito da ita, jin ta taka kasa sosai yasata sauke ajiyar zuciya. A hankali suka shiga mata jagora har ta shiga motar da zai katai Mansion Win, duk wani abin da ake sai da aaka mata bayan ya cire bakin abin da aka rufe fuskarta.
Kallon kome tayi na gidan Black and whiter. A hankali take gyara zamap n hular kanta, da ya zame. "Ina ne nan?" Murmushi aka yi bayanta.
"Mayor Malik Menk Jordan Mansion!" Juyawa tayi ta ga Elbashir, "zamu iya shiga!" Kallon hanyar tayi tana takawa a kasaitacce, domin shi destroy all over record na kowa ta kuma kafa nata da kanta. Har cikin gidan ya rakata, aka bude kofar shiga gidan ya shiga tana bin bayanshi.
"Me yasa jiya kayi breaking promise dinka, bayan ba haka muka yi da kai ba?"
"Shiiiiiiii! Keep quiet ba a cika surutu anan ba!"
Gyada kai tai, har suka shiga cikin gidan a ranta ta ce. "ko makabarta ana magana balle nan!" A tsakiyar Main falo suka tsaya, karar inji yasa suka juya bayansu.
"Kan bura uban can.................
Hhhhhh kome ta gani ga Zeenobia ga Malik.....
*Assalamu alaikum......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500¦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan

Please Login or Register in order to submit comment