Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokaci mu tafi wurinsa, idan yaso sai mu shirya ba. murmushi Alhaji Nasr Hadejia yayi ya ce mishi.
 Idan Allah ya kai mu gobe, sai mu tafi. Ina son na kira iyalina ne su zo da Yarana.
Dariya suka saka ya ce mishi.
 ai ku yan Nigeria kuna da hakuri da juriya, ina zan iya wannan hakurin? Kawai malam ja sa Madam ta dawo nan, kafin nan karatunsu da kome nasu zai dai-daita.

 Hmmmmm! Tow ya zamu yi? Kasan idan baka yi hakuri ba, ya zaka yi da hakkin Allah, shi Allah ya sauke hakkin mu da yake kansa, saura mu mu sauke wanda yake kanmu. Ina da Yara mata biyu, ina jin kunyar na bude idanu na kalle su bayan na sabawa Allah, sannan Allah ba zai kare mu ba. Sannan ba zai kare bayan mu ba, amma idan muka are kanmu da iyalinmu Allah zai kare bayanmu bayan mutuwar mu. jinjina kai Yamini yayi yana faWin.  Na gamsu da bayaninka. Allah ya kare zuriarmu bayan mutuwarmu  Allahumma Amin da wannan suka ajiye zancen zasu tafi wurin Mayor Fahad Albagwi.

Washi gari kuwa Yamini shi da kansa ya taso ya dauki Alhaji Nasr Hadejia, izuwa farfajiyar gidan gwamnati. Sun taras da mutane, musamman manyan bai don haka suka tsaya su jira. Bayan kamar minti Talatin sai ga sakataren Fahad ya fito dake an isar mishi da yayi bain. Duk da kasancewar sun same mutane a wurin bai hana sakataren isowa wurinsu ba, ya ce musu.
 Ku iso ana kiranku. mikewa suka yi, tare da bin bayanshi, a cikin ofishin Mayor. Cikin girmamawa da mutuntawa Mayor ya mike tare da tarbansu yana faWin.
 Malik sune mutanen da suka zo da nufin raya garin Fiston, amma Shu'iba da Dulma sun hana su, har nan suka zo suka min kashedi. Malik na kira ka ne, domin ka taimakawa bayin Allah nan, suna san cigaban jahar nan ta fuskar Kasuwancinmu. duk da basu ga fuskarshi ba, amma baki daya basu wani gamsu da shi ba, domin kuwa ba a niman taimakon dan daba akan yan daba yan uwanshi. Hadin kai ne dasu, d'ago hannunshi me dauke da zobban ya yi musu wani alama.
 Wai ku gabatar da sunanku?
"Aswad Yamini, wannan abokina Alhaji Muhammad Nasr Hadejia. a hankali ya juyar da k 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ujeran ya zuba musu idanu, mutum ne mai tsannanin kwarjini da cikar halitta. Mutane da matukar ka kalle shi sau daya sai ka sunkuyar da kanka asa. Domin yanayin zubinsa kamar zubin zaki ne, rintsa idanun Yamini yayi yana jin wani irin yanayi. Domin kallo daya yayiwa Malik ya hautsina mishi tunani, banbancin shi da Nasr Hadejia da ya kuma kallonsa ido ciki ido har sau biyu. Duk da wannan yanayin bai hana shi jin kamar ya zuru da gudu ba.

 Had'ejiya ta Jigawar Nigeria? da sauri Alhaji Nasr ya d'ago suka kara kallon juna a karo na uku. Mikewa yayi yana me fashewa da dariya, Fahad Albagwi ka had'e ni da dan uwana dan kasar kakana. Ai ni na samu aboki waye ya isa ya ce ba zasu gina wurin shakatawa ba. A shelantawa duniya na tsaya musu. Ai ko don albarkacin dan kasata na tsaya musu. Yamini kai ma Wan uwana ne, domin Mahaifiyata yar yankin jaziratul arab ne. lallai sun taki sa'a kuma sun dace. Sai dai basu san cewa akwai ragon azanci a amincewa Malik. Musamman yadda tambarin shahararsa tasa ya fantsama yayi wanka da munanan ayyuka ba, mutum ne ya yayi wanka da zunubai babu iyaka.
Don haka suka bada yardansu tare da yarjejeniyar habbaka Kasuwancinsu. Amma ya boye musu makasudin amsar alaarsu.
 Batun ma'aikatanku da suke hannunsu, zan amso su kafin rana tayi tsakiya. ya duba agogon hannunshi. Sannan ya juya yana kallon Fahad.  Albagwi alkawari. gyada kai yayi, sannan ya fita. Bin bayanshi suka yi da idanu.  Mayor hankalina bai kwanta da Mutumin nan ba, idan abun nan ba zai yiwu ba, mu hakura ko Yamini? murmushi yayi sannan ya ce mishi.
 Ni kuwa naji kamar alkhairi, koda kuwa akwai matsala ba zai gaggare mu ba. Kwantar da hankalinka. haka suka amince da Malik domin kiri-kiri Alhaji Nasr Hadejia yaki karban Malik, ba don kome ba. Sai don sanin duk inda aka samu dan daba zai yiwu ya ki taimakawa yan uwansa.

Shu'iba da Dulma.
Malik ya jima yana nimansu, ba don kome ba sai don akwai tsohuwar gaba, wanda suka jima da shi a ransu, sai dai bai samu damar ramuwa ba, domin kuwa basu tab'a zama wuri guda. Asalima wasan boya suke da shi, shi kuma yayi alawarin duk wanda ya gaya mishi inda suke zai mishi kome, ana haka Fahad Albagwi ya tura mishi sakon ganinsu. Ana gab da zaben kasa.
Dulma dan uwan Shu'iba ne, kaninshi cikin su daya, a duniya babu abun da Shu'iba yake so sama da Dulma, domin ta kai, hatta matar da ya aura tunda Dulma ya ganta ya ce, yana sonta. Babu musu Shu'iba ya bar mishi ita. Karshe azaba da wahala ya kashe Yarinyar, tun daga lokacin Shu'iba ya samu damar auro mata Dulma ya shiga abin da yake so da su.

Hill and Tim town.
Ana kiran wurin nan haka ne, sakamakon duwatsun da suka kewaye wurin, kuma akwai ma'adinai irinsu kuza, ana hakarsa na fitar hankali. Ba aramin samu suke ba. Sannan sun kwashe maza matasa da yan matasa,. Suke musu wannan aikin cikin azaba da wahala, dalilin wannan dukiyar da yake kasa yasa suka watsar da duk wani cigaba da ya dace su samu. Musamman a fuskar garin, domin idan suka gyara garin su waye zasu musu wannan aikin? Duk matasa zasu samu abin yi. Shi yasa wurin suka kawata shi da nauyin azaba kala-kala. Babu wanda ya isa ya gudu, akwai zakuna masu gadin mutanen, domin kuwa idan mutane suka ne gudu bude zakunan ake suyi fata-fata.
Koda Malik ya bar ofishin gwamnati, bude motarshi yayi, masu kula da lafiyar shi suka fito suna me niman take mishi baya, d'aga musu hannu yayi. Ya dauki wata local gun, sannan ya shiga motar bayan ya dauki wata glass na Prado ya saka a fuskarshi, fuskar shi a kame, na zaka Wauka yana dariya ba.

Haka ya juya ya fita, a duk lokacin da yayi irin su wannan shirin, tabbas ba aramin al'amari ba ne, jinjina kai Elbashir Jamal Arab yake, yana faWin. "Allah ka jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya, amma tabbas maza sun fita farauta." Haka ya koma cikin motar ya zauna, tare da kunna wakar rosta.
Tafiyar kilomita bakwai ya kai shi, Hill and Tim town.
Tun kafin a bude mishi kofar shiga town din ya fara musu barna, har ya isa cikin sansanin, koda yake fushin sa ba a kan kowa yake saukewa ba, akan wadanda suka tab'a shi ne.

*present*
Koda yake kusan rabin ayyukan da tayi, bata jin akwai wanda ya kai na yau, shi yasa tayi kokarin ganin ta nime haduwa wani dan kasuwan da zai zuba jarinsa. Sai dai batayi nasarar haduwa da shi ba. A gajiye ta fito daga ginin ta fito inda Black yake jiranta, wurga jakarta tayi tana faWin. "Wash Allah na!" Ta zauna a cikin motar tana mika. "Ina zamu?" Idanunta a lumshe ta ce. "Akwai inda yafi gida ne?" "Babu" ya bata amsa, sannan ya ja motar suka bar wurin.
"Chairman! Yarinyar nan ta kawo abin da bamu zata ba, mu kyaleta haka!" Murmushi Mr Amjad yayi ya ce mishi. "Ban gama gamsuwa ba, sai tayi min abin da3 zan barta. Amma ka sani duk kudaden da take samo mana, na hannun jari bai kai na babban kifi ba." Shiru MD yayi ya ce mishi.
"Akwai matsala, idan har aka sake kifin ya sake ya zama me k'aya za a wahala."

"Bana kwai na, sai da zakara don haka da ita zan amfana!"
--
A kan hanyarsu ta dawowa gida ne, suka tsaya a traffic jam. Yan sanda ne suke bincike, "Kai Xno ga mutuniyar!" Juya kanta tayi zuwa ga inda yake nuna mata, kafin ta tabe baki ta ce. "sun fito cin na goro!" Ta fada tana dauke kai, domin ta gama gajiya likis. Dama da gayya ita kanta Asp ta fito kan titin. Sake mutanen da suka tare take, kafin su Zeeno su iso ta saka an tare hanyar, dauke kai Zeeno tayi.
"Ina driving license din ku?" Banza suka mata. Ba aramin kunya ta ji ba, domin ana ta wucewa da kafa, kuma ana kallonsu.
"Ina magana kin min banza!" Babu wanda ya d'ago kai ya kalleta, hannu ta kai da niyyar zata cire key din motar. Zeeno ya kai mata wani irin duka da bayan hannu, faduwa can tayi, kamar an cillata. Sauka daga motar Zeeno tayi tana me cire top din suit din jikinta, a hankali ta shiga nad'e hannun white shirt din jikinta tana faWin.
"Kul ki ce zaki tab'a min mota ta, zan kyale ki ne domin kakin jikinki idan ba haka, kul ki kuma shiga harkata!" Mikewa Asp Zulfa tayi tana faWin. "Kika saka hannunki a jikin Yar sanda." Wani juyar da kai tayi tana faWin. "Idan ta kama na zane ki zan yi ki tsaya a bakin aikin ki."
"Da shi haka yana nufin duk wanda ya nime saita miki hanya, sai kin kashe shi dalilin da yasa kika kashe Asp Ayuba kenan?" Rintsa idanunta tayi, ta nufi Zulfa da wani irin sassarfa ta cukume ta. "Idan kika kara kiran sunan tsinannen can, sai ja tura ki idan na tura shi, ki bincike idan kin samu labarin wanda ya ga lokacin da na kashe shi, ki zo nan a gaban jama'a ki saka handcuffs." Daga haka ta koma cikin motar ta zauna. Wani irin kallon banza Zeeno ta aikata mata, tana mata gargadi.
*Past*
"Kai ku sake mishi zakunan nan!" Haka suka sakar mishi dabobbin. Yarda bindigar yayi ya nufi zakunan da mugun gudu, kamar yadda suka nufe shi. Oho faduwar gaba asarar maza, a fusace Mayuntan zakunan nan suka nufe shi, aikuwa aka rungutsume akayi wata kazamar arangama, a duk inda aka raya fansa, tow zaka samu tsoro da fargaba bai cika samun matsuguni a wurin ba. Haka ce ta faru da Malik, domin a duk lokacin da ya dunfaru wani abun da ya shafi fansarsa. Haka suka hautsine da wani irin fada, me tashin hankali. Kafin wani lokaci,ya watsar da gawarsu, ya mike yana karkad'e jikinshi yana kallon inda Dulma yae. Hannu ga saka a cikin aljuhun wandon shi ya dauko cigarette, ya kunna tare da zukar hayakin ya hura a sama.......
*Hi......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500 normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A'ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: CINIKIN RAI....
Beauty and the beasta&
Mai_Dambu
005
 Kai Shu'iba ka rufawa kanka asiri, ko a tashe ka da nakiya. Ko kuma a turo yan bindiga dad'i su alburushe ka. har ga Allah maganar tayiwa Lalla Salmah zafi.  Shi yasa baku rabuwa da abin kunya a kowacce magazine ba. Ai gara Malik ya tsare kansa da dukiyarsa ce,ba mutumin banza ba ne." Tana gama fadar haka ta mike zata bar kwaryar Majalisar.  Ya tabbata dai yan PKO party basu da abin faWa, tunda karen farautar da suke karewa ta kusan kare mishi. Shugaban majalisa a tsige Malik Menk Jordan kawai.

Shiru tayi sannan ta cewa shugaban majalisar koli.  Yallabai kafin ka yankep hukunci ka fara nazari, idan kace zaka biyewa yan amshin shata zasu kaika su baro ka, su basu da nasu sai na wasu. Kullum ra'ayin wasu ke yawo a kansu banbancin uban nan gidansu da Ubangidan mu kenan. daga haka ta fita ta bar kwaryan majalisar koli da hayagaga.

Tana fita ana mika mata wayarta, amsa tayi tana faWin.  Elbashir ina ka shiga ka bar ni sa tashin hankali? Kasan abin da ya faru kowa? amsa maganar yayi da cewa. _Ina sane, sai dai Malik ya hana ni dawowa ne, ya ce nayi fucus din matsalar gaba na, amma please ki tuntubi Mr Shatima, a madadina ya je ofishin jam'iyyar PKO yayi magana akwai lauya malik._

 Shi kenan, zan tabbatar haka ya faru. ta fada tana me kashe wayar. Tasan dole yau ta isa Keivroto city kome dare tunda har Malik ya iya hana Elbashir Jamal Arab dawowa tow wannan shi ne lokacin da ya dace tayi kokarin ganin ta shigar da bukatarta. Sai dai izuwa yanzu take da damar shiga ga Malik ko dan Maidah tunda an soke zancen Nadra Shatima. Dama tun can ta tsani yarinyar sai kuma aka yi rashin dace Malik yayi rejected Win bukatar Shatima. Domin bata mantawa a lokacin yan mata dayawa sunso shi. Haka ko Wahiba da Wahida, basu amshi Nadrah ba. Shi kuma Malik yana tafiyar da rayuwarsa ne daidai da fahimtar Yaran. Bayan abin da zai tab'a ran su, shi yasa ya dauke su a garin Keivroto ya mai da su demark su yi karatu. Da wannan damar itama take amfani idan zata taso Gista ta tura mishi Maidah. Sai dai wani lokaci bata jin wani gamsashhen bayanin sun hadu ko basu hadu ba, ba kamar duk lokacin da Nadrah taje ba, tana samun ganinsa. Ko last year kafin Mr Shatima ya mai da Maidah Demark wurin su Wahiba da Wahida, Malik da kansa ya bashi Shawaran ya mai da ita wurinsu, sannan ya dauka rashin aurensu daga Allah ne, don baya son haka ya tab'a relationship Winsu. Koda yake taji a bakin Mr Khamis Shatima ne da bai da sirri, bai san itama burinta ta tura yarta ga Malik din ba ne. Murmushi tayi, izuwa yanzu ta koyarwa Yarta duk abin da zata kama zuciyar namiji, imma ta koya mata yadda zata iya daukar kowanni abu daga namiji, imma ya kama da affairs ne da namiji ta yarda, amma bata son yarta tayi mu'amala da wani namijin domin tana bukatar yadda yarinyar zata kama Malik. Tow amma me yasa Malik yaki auren Nadrah Khamis Shatima? Domin tasan kuma yarinyar tafi yarta kyau, nagarta da son jama'a. Banbancin ta da Maidah koda yake ai Barewa bata gudu danta yayi rarrafe, halinta halin Yarta. Koma mene ne ohon musu kanta ta sani, ba wasu ba yarta ta samu shiga ga Malik ko nawa zata barar zata san yadda zata cusa yarta ga Malik. Koda kuwa zata kama da bin malamai da bokaye ne sai sun mallake shi.
**
A cikin abun da bai wuce sati daya ba, aka d'aga curfew inda aka bar kowa, dakin Ammyn Abbas ta nufa, tana me shiru. D'ago kai Ammyn Abbas tayi tana murmushi.  Zainaba a hankali ta iso gabanta tare da riko hannunta.  Gaya min akwai da wani abu ne? kansa a sunkuye ta ce mata.  Ammyn aikin da na samu, sun ce min lallai dole sai dai na zama me gayyato musu mutanen da zasu saka hannun jari a kamfaninsu. Kaina ya kunce ban saba ba, ban iya mu'amala da. murmushi tayi tana me zaunar da ita ta ce mata.  Inji waye ya ce ba zaki iya ba? Zaki iya mana, kika iya daukar na wasu ma balle naki, Allah ya sa'a.  Ina son tsoro ne kar a samu matsala, na ga sun addabe ni da lallai na fara aikin ne, shi yasa na fara jin kamar akwai wata manufa a kasa.
 Ki yarda a ranki zaki iya, sannan ki saka nutsuwa a ajiye jagaliyancin nan, ki fuskanci reality dinki, da yau Alhaji Badaru Daniyal yana raye kina nufin zai barki ne a haka? Shi ya so ya inganta Miki rayuwar ne, bai da burin ki rike wuka ko gatari.

D'ago kai tayi Idanunta sun yi jajjur, har wani kyali suke, alamar ta tuna wani abin da ya shafe ta, kasa tayi da kanta tana faWin.  Ba laifina ba ne, ayayinda ake tunanin mika ni ga gidan Marayu, shi yayi adopt dina a matsayin second child dinsa, ya tafi ya bar min abu biyu masu daraja. Ammyn don Allah bani da wani abin da ya shafi past dina ne, ina son sani wace ce ni?
Girgiza kai tayi, sannan ta ce mata.  Bayan takardun da na baki, babu wani abu da na sani game dake, shima Alhaji bai san kome ba, sai abin da aka baki.
 Shi kenan na gode ma haka, ba mamaki Allah ya turo ni rayuwarku ne, shi yasa na kare nan. Amma ina ji a raina kamar ina da wata rayuwar.
 Allah ya sa. Ammyn Abbas ta fada, tana me dauke kanta daga Zeenobia din, har tafi daga dakin.
Bin tayi da idanu, tabbas bata yi hankali da zata gaya mata kome ba, bata samu nutsuwar da zata gaya mata daga wacce duniyar take ba, amma bari tayi digging kad'an daga cikin rayuwarta da abin da suka sani.
***
Zeenobia
_Past_
Alhaji Muhammad Nasr Hadejia, Dan asalin garin Hadeja ne na Jigawar Nigeria, bahaushe ne, da kasuwanci ta shigo da shi garin Fisto kasancewar garin da yake tsubirin lord island, kasancewar gari me dauke da manya manyan duwatsu, halo dai hade yake da ruwa me kyau. Garin Fisto yana daga cikin jahohin Gista da ake yawon shakatawa da bude idanu, sai dai wani abu daya da yake maida garin baya shine kabilanci. Kabilanci yayi tasiri da garin, musamman yadda har turawa suna zuwa yawon buWe ido.

Kasancewar kasuwanci ya kawo Muhammad Nasr Hadejia, kuma abin burgewa yana da ilimin addini da na boko, wanda yasa shi kallon garin a matsayin garin da za a cigaba sosai. Sai dai wani abu biyu da ya dakushe garin. Kabilanci da zalunci, haka yasa shi fara binciken da bibiyar hukumomin haraji na garin Fisto, Allah ya bashi sa'a zuwan farko ya hadu da Aswad Yamini. Shima dan kasuwa ne, a'a Balarabe daga kasar Yemen. Shima mutum ne mai matukar son kasuwanci da cigaba. Don haka a tare suka yi decided yadda zasu gini bakin tsibirin. Yadda zai bada abin da ake bukata, domin ginin zai kasance a cikin ruwa ne, kamar yadda bora-bora island yake. Wannan shine kudirinsu. A lokacin Alhaji Muhammad Nasr Hadejia yana da matar shi har da Yaransa biyu mata, a garin su Hadeja. Sai dai bai yarda ya kawo su. Aswad Yamini yana da matarsa da dansa daya a garin domin a tare suka zo Fisto.

*Present*
Police headquarters.
 Har yau babu wani shaidan dan da za a iya kama Malik shi, abin da na sani mu jami'an tsaro, zamu yi tafiya kafada da kafada, da hukumar binciken farin kaya. A duk lokacin da sahihan shaidu suka samu a cikin tabbatar an kama Malik tare da gurfanar da shi a gaban kuliya. Na gama magana.
 Ok sir! bakidaya an sandan suka amsa, sannan kowa ya mike tare da shugaban yan sanda bakiWaya. Suna fita yan jarida suka nufe su.  AIG wai da gaske ne kuna yiwa Malik aiki.? inji wani dan jarida. Shiru yayi kafin ya bada amsa wani gidan jaridar ta kuma wurga mishi tambayar.  shin yau babu tabbacin Malik zai fuskanci kotu kenan? Shin Malik yana da ikon juya kowanni bangare na siyasa kenan? duk da ba a bashi izinin yayi magana ba, amma dole ya gayawa duniya cewa hukumar yan sanda basu yiwa Malik aiki.
"Yaku yan jarida ina son na sanar muku cewa, hukumar yan sanda basu bin bayan kowanni bangare fecce aiki da gaskiya da Amana, sannan da ace yau hukuma ta kama Malik da laifin kashe Prime minister, da ba a rufe awa ashirin da hudu ba, ba tare an kama shi ba. Duk wani hujjojin da ake bukata mun tanada shi, sannan duk wani binciken da ya dace, anyi bai da masaniya a kan kashe Prime minister."

"Sai dai har yau muna da labarin cewa, Malik Menk Jordan shi ne yaron da ya kashe Manyan yan siyasa da jami'an tsaro uku, shekaru kusan arba'in da suka gabata, shin wannan ba hujja ba ne da zai iya rufe shi har abada ba?" Kallon dan Jaridar AIG Yasir Aswad Yamini yayi, kafin ya ce mata.
"Har yau muna kan bincike.
 Yallabai"
Suka shiga kiranshi, amma ina yan sanda sun kare shi. Har ya isa cikin motarsa. Kallonta yayi ta zuba mishi idanu.
"Omooooo! Me yasa kika zauna a nan zafi ba zai dame ki ba?"
"Taya ba zan zauna ba? Wallahi kaji tsoro Allah, akwai cases sun kai ashirin akan Malik Menk Jordan, me yasa kake tsoron bayanan laifinsa ko kai ma kana tsoron mutuwan ne?"
"Mutane irinku, kullum tunanin su hango laifin wasu baku tab'a zama ku fahimci me yasa wane ya zama haka." Bata bari ya kawo karshen zancen ba, ta bude motar zata fita, riko hannunta yayi ya ce mata.
"Me yasa kike fushi?" Idanunta cike da takaici ta ce mishi. "Ok ya batun binciken ki?"
"Sake ni!" Bakinsa a dai-dai kunnenta, "let me kiss you." Ture shi tayi, tana faWin.
"Ni ba yar iska ba ne....." Sumbatar ba zata ya kai mata, ta wani ware idanu ta. Hura mata isa yayi. "Asp zaki iya tafiya!" A hankali ta bude kofar ta fita, kallonta yayi yana murmushi. "Ki kula min da kayan alatuna. Zan gayawa Auntynki!" Bata saurare shi ba, tayi gaba. How comes? Taya zata dauki wannan al'amarin.

Haka ya tafi ya barta da Faduwar gaba, tasan Aunty Fannah, da Bala'in kishi. Musamman akan Mijinta bata hada shi da kome ba.
-----
Kamar yadda suka bukata yau ta fara zuwa aikin, sai dai tunda ta isa bata zauna ba. A tarihin rayuwarta wannan lokacin shi yafi kome bata wahala. Sai yawo suke manyan ofisoshin gwamnati, da gidajen masu kudi,babu karya wanka iya wanka yau tayi shi. Shi yasa duk inda suka je cikin ruwan sanyi suke samun ganawa da Mutanen da ta je gani.
Past.
Daga cikin abubuwan da Nasr Hadejia da Aswad Yamini, yasa suka samu ganin Mayor na wannan lokacin, domin a basu damar Fahad Albagwi, a lokacin ya basu full attention dinsa, sannan ya basu damar gini a bakin tsubirin, tare da dauko masu gine-ginen zama daga kasar Canada.
Duk wanda ya saka gaskiya a cikin al'amarinsa, zai ga gaskiya domin a kasa da wata uku suka gama ginin, tare da fara kokarin bude shi, a lokacin manyan attajiran Fisto da Keivroto suka yi ta zuwa......
*Hi......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500 normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A'ishah. +227 84

Please Login or Register in order to submit comment