Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

city yake gabbatar ruwa. Mr prime idan har aka ce za a fito da abin da suke bukata, ai Malik bai yiwa mutanen da suka yi nominations dinsa izuwa matakin Mayor ba, taya zai yarda da muradunsu bayan shima yana da tasa muradun?" Mikewa Azagwaigwaidu yayi cikin fushi ya ce. "Prime minister a sake kidayan kuri'a Yallabai Khuldu Jahid Khan ya ci ba Malik Menk Jordan ba, mutumin banza kawai, dan luwadi waye bai sani ba, kaf gidansa babu Y'a Mace, wanda kowa yasan cewa Yallabai Khuldu Jahid Khan gidansa mata uku ne, Yara mata babu wanda yasan adadinsu, ka gayawa maigidanka kar yayi asarar kwayayyensa a ta baya, ya nimo ko karuwa ce, ta haifa mishi hana gori." Gyara zaman tie dinsa Elbashir yayi ya zuba masa idanu, kafin ya ce mishi. "Na maka uzuri ni tarbiyyar Malik Menk Jordan ne, ya haramta min cin zarafin kowa." Jin haka mutumin ya buWe baki zai magana, Mr Khuldu Jahid Khan ya ce mishi. "kul!" Shiru yayi sannan ya cigaba da cewa. "Me yasa Malik ba zai yi show up ba?" Gyara zama Elbashir yayi ya ce mishi. "Meye matsakarka da show up dinsa, kome yana tafiya yadda yake, Kasuwancinmu da siyasar mu, tow kai me kake bukata anan?" "Wadancan mutanen!" Ya nuna mishi mutanen kusan su goma a zaune. Tabbas sun zo kwanaki uku da suka wuce, akan Mayor Malik Menk Jordan ya saka hannun jari a kamfanoninsu, sannan zasu mishi biyayya. Wato da suka ki amsar buatarsu shi ne, bari su dawo nan. Dariya yayi ya ce mishi. "Khuldu Jahid Khan!" Rintsa idanun yayi. "Amma Elbashir baka da kunya shugaban mu kake kira kamar, abin wasan ka?" "Kai kare bada kai nake ba, da ubangidanka nake, idan ka sake na kuma jin tashin muryanka sai na datse harshenka" juyawa Elbashir yayi ya cigaba da cewa. "Saura kiris da kunyi kuskuren amsar, dukiyar Mayor Malik Menk Jordan, da sai kun yi danasani, a yanzu ma ba kyale ku zamu yi ba, zaku biya zunubanku. Sannan shi wanda kuka daura yarda akansa bai gaya muku karon battarsa da Mayor ba ne? Ya gaya muku sanadin da yake dogarawa da sanda, Mr prime minister na gama jawabi, babu wani dan kasuwan da zai bude wani kamfani matukar Mayor Malik Menk Jordan yana numfashi ba zai lamunci haka gasa ba." Yana mikewa, yan majalisunsa suka mike suma suna masu taka mishi baya, dayawan basu san Malik ba, kuma duk matsayin da suke da taimakon sunan Malik suka isa wurin, Idan aka ce maka Mayor Malik Menk Jordan tow, hantar sadaukan maza bari take. Domin tsaf dattijan Keivroto ba karamin tsoronsa suke ba, uwa uba ka tab'a mishi dukiyarsa sunanka shekakke.
Haka suka fito tare da raka Elbashir Jamal Arab airport, sai da ya haura jirgi sannan suka juya, wannan shi ke kira Powerful. Domin iya Elbashir yana taka muhimmiyar rawa koda Malik baya wuri.
Bayan fitar Elbashir. Jifa da kome na dakin taron Mr Khuldu Jahid Khan yayi, yana faWin. "Sai na kashe shi, shekaru arba'in da shida kenan ina niman hanyar da zan kashe dan shegiya bakon haure, Wan cirani!" "Yallabai wannan al'amarin, kasan cewa babu wanda ya isa karya Malik, kuma koda kuwa za a hada sama da kasa ne, babu wanda zai iya karya shi. Sannan idan kace zukatan al'umma zaka saya, ba zaka tab'a sayan tsoron da yake cikinsu ba, su ba zaban Malik suka yi ba, labarin abin da yayi kawai suke dubawa. Idan har akwai hanyar da zaka bi dole ka bi. Sannan rigimarka da Malik kar ya shafi Kasuwancin wadannan bayin Allah domin basu ji ba, basu gani ba." Tsamo tsamo Mr Amjad yayi kutumar Uba, wato labarin Malik da yake ji, ba kome bane sai da Elbashir yazo yasan waye Malik shi baya tare su, amma anyi mishi abin da yake bukata. "kuma da ace Malik ne yazo da kansa, kana tsammanin ba wanka zai yi da jinin Daylam Yunis ba, kai ya dace ka koyawa mutanenka girmama kai, su daina zakewa. Bani manta shige asirin baya idan Malik yazo da yaron nan, baya tab'a yin tari matukar ba Malik ne ya bashi iznin yin haka ba, kai kuma saboda dalilinka kasa kowa ya zama me damar magana, kai idan har baka yi a hankali ba, sai ka Waure kanka. Kayi kokarin niman hanyar da zaka kadda Malik ni kuma zan tsaya maka har sai ka kadda shi. " "Shi kenan." Ya fada yana kurban ruwan zafi. Fita prime minister yayi, kiran wayarshi aka yi, p.a dinsa ya mika mishi. Jikinsa ne ya dauki mugun rawa, ya kasa dauka ji yake kamar zai fadi. Har suka kusan isa motarsa sai da ya shiga cikin motar ya dauki kiran. "Ranka ya dade." _Kayi kuskure Prime minister, sauka lafiya_ kashe kiran aka yi, wasu mutane da ba asan daga ina suke ba, suna zuwa suka budewa janye p.a da driven, suka budewa motar prime minister wuta, sai da suka tabbatar da ya kama da wuta, sannan suka wuce a babur dinsu.
Lokacin dasu Mr Amjad suka fito, ganin motar prime minister duk da jami'an tsarosa bai hana a kashe shi, an tashi motar da wuta ba, take duk suka juya kowa ya cikawa bujensa iska, wannan tashin hankalin ba karamin firgita Mr Amjad yayi ba dole tasa ya koma kamfanin S digital art. Yana shiga bai tsaya parking me kyau ba, ya nufi cikin kamfanin, a firgice yana ji kamar ya tsula fitsari a jikinsa. Kai tsaye elevator ya shiga, sai da ta ganshi cikin ya tabbatarwa ya tsira, ya sake ajiyar zuciya. "Wannan wacce irin masifa ce, taron dangi akan Mayor Malik Menk Jordan ba shi ne mafita ba, tabbas." Wayarshi ce ta yi gunji, sai da ya zabura, kamar zai gudu kafin ya tuna ai wayar shi ce take tsiwa domin da zasu shiga taron ya sakata a gunji. Dauka yayi yana faWin. "Hello!" _Kada ka karya da abin da ya faru, ai dama ba iya nan ne shirin ba. Ka fahimta ko_ "Ni wallahi da zaka cire ni a cikin wannan lamarin da naji dad'i, Tunda aka iya kashe babban minista akan idanunmu, bamu iya me kake tunanin zai faru? Ku shafa min lafiya" ya kashe wayar, yana isa floor 9 ya bude kofar, jikinsa yana rawa ya nufi office din MD, kamar wanda aka koro shi ya isa office din, "ku bani ruwa ina jin ishirwa ne" mika mishi ruwan Salim yayi, sai da ya shanye ruwan tass, ya nime kari. "Sir lafiya?" Ajiye goran yayi ya ja kujera ya zauna, duk suka zuba masa idanu. "Zeeno baki tafi ba ne?" Mikewa tayi tana faWin. "Eh Yallabai Amjad. " Sauke numfashi yayi ya ce. "Hussain wani matsayi take bukata ma?" "Security service!" "Ya miki haka?" "Eh yallabai!" Kallonta yayi ya ce mata. "Zeeno naso na baki matsayin da zaki na, nimo mana manyan mutane suna saka hannun jira ni a kamfaninmu, na sha gaya miki ke kyanki shine jarinkie, akwai mata dayawa da suke niman matsayin da kika taka, Zeenobia idan har kika amshi security service, harajin da gwamnatin jahar Keivroto take amsa a hannunku duk wata ba zai kai ba, zaki cigaba da bangar siyasa ne? Shekarunki nawa?" Sunkuyar da kai tayi kasa ta ce mishi. "Ashirin nake!" "You see! Kiyi amfani da damarki, akwai Mss Mary zata hadaki da Dauduwa, ta kware a fannin sauya salon mutum da fasalinsa, albashinki dala dubu dari uku, kudin US. A cikinsa zaki samu dala dubu hamsin ki biya kudin haraji, me ya fi miki." Juya idanu ta yi, ta ce mishi. "I,m satifai, idan har zaku bani dis moni, I kan do anitin!" "Yes good gurl yanzu ya yarda zaki iya, tunda kika yi magana da turanci, Hussain bani list na sunayen nan!" Ciro mishi kundin yayi ya mika mishi, a hankali ya bude yana kallon shi. "Ikon Allah kace har ka tura baki daua saura daya ne kawai ya rage?" "Yes Chairman na tura baki daya, wanda ya rage na Mayor Malik Menk Jordan ne!" Sarawa kanta yayi, ta dafe da karfi. "Lafiya!" Suka tambaye ta, "lafiya lau! Zan tafi." Mai da kundin yayi ya ce mishi. "Ajiye akwai dayan fa na baka, bani na bata!" Bude drower din yayi ya dauko mishi wani kundin. "yawwa Dauduwa zata gayyace ki, ga wannan su zaki fara jaraba sa'arki akansu." Juya Idanunta tayi ta ce mishi. "Wancan na farkon fa da ka mayar da shi?" A razane ya ce mata. "Wancan ai konawa zamu yi, kai Salim dauka ka je ka kona, kunna mana tv ta ji abin da yake faruwa, sunan da yake jikin wannan kundin bala'in duniya ne da tashin hankali ke yarinya ce, da babu ruwanki. Kada ki tsoma ranki da zuciyarki cikin wannan lamarin. " Murmushi ta yi ta ce mishi. "Tow amma kada ka kona, bari na ga yadda zan ji da wadannan zan dawo kansa." "Anya zaki iya?" Kunna tv aka yi ta juya tana jin labarin. _A yau garin Keivroto city ya tashi da mummunan al'amari da rabon a fuskanci haka tun shekaru talatin da suka wuce, lokacin kashe Mr Jahid Khan mahaifi ga Mr Khuldu Jahid Khan, me manyan kamfanonin hakkar ma'adinai, kuma Uba ga jami'iyyar adawa ta CDL civilian democrats labor, bayan nan ba a kuma samun tashin bom haka ba, sai dai shaidun gani da idanu sun ce wasu matasa hudu suka gani da babura, inda suka sauka suka idda mugun nufinsu, tare da kashe Mai girma Prime minister, a halin yanzu ana danganta mutuwar da Shahararren attajirin Wan kasuwa, mai girma Mayor Malik Menk Jordan, wanda aka tabbatar da cewa anyi taron nan ne domin a kawo karshen mulkinsa inji wata majiya. Idan baku manta ba, Mayor Malik Menk Jordan shine mutum na farko da yake da kashi casa'in a na kamfanonin a garin Keivroto city, sannan yana da sahalewan shuwagabannin Kananan Hukumomin Wari da shida, bayan nan dan kasuwa ne da ake zarginsa da hamdama da babakere, ga abin da wani ganau yake fada_ sako wani murya suka yi. _Gaskiya idan ka cigaba da barin Mayor Malik Menk Jordan yana abin da ya gadama, wata rana Keivroto city zata zama makabartan binne mutane amma ace babu wanda ya isa taka mishi burki sai abin da yaso, fisabilillahi taya za a rayu?"_
Kashe tv Salim yayi ya ce. "Da ina jin labarin Mayor daga nesa ne amma yau da naji ya kashe prime minister na yarda mutumin nan shaidani ne, Zeenobia Kinji ko?" Kallonsu tayi tana faWin. "Ya naga kun razana, shi ne ya baku tsoro? Ni kuma gani nake ba kome ba ne." "Ke ki raba kanki da masifa Mayor Malik Menk Jordan ba kanwar lasa ba ne......
Zeeno
#Beauty
#Beast
#RomanceS
#Tycoon
#WeatherMan
#Top-notch
#Rumors
#Jelousy
#Cursed
#Mai_Dambu
[8/28, 2:22 AM] Maman Sadiq Da Khadijah: *CINIKIN RAI......*
Beauty and the beasta&

Mai_Dambu
BOOK ONE
003
"Mr Amjad!"  Kiyi abin da na saka ki, babu ruwanki da Malik Menk Jordan, idan da kin ga abin da ya faru, ba zaki fara shiga wannan lamari ba. Kowani mutum yana da iyakarsa don haka ki tsaya iyakarki kallon shi tayi na wani lokaci, kafin ta ficce daga office Win, lallai tana son sanin waye shi? Me ya taka har haka da kowa yake jin shakkarsa haka. Tana fita Mr Amjad ya kalli MD da Salim.  a firgice nake, ina ga zan zauna a kamfani na tsawon kwanaki, domin Malik ya manta da ni, idan ba haka ina fita qur'ani kashe ni zai yi."

Shiru sukayi kowannen su, da abin da yake yawo a ransa, kafin Salim ya ce masa.  Yallabai me yasa ka razana haka ne? Ni fa bana tunanin Malik ya kai yadda kuke fada, kawai kashe prime minister yayi haka ne domin ya cusa muku tsoro da firgici. Kuma yayi nasarar haka" juyar da kai Mr Amjad yayi yana kallon window waje. Kafin ya mike kana ganin yadda fuskarsa ta nuna zaka fahimci yana cikin damuwa soka hannunsa yayi cikin aljuhun wandon ya ce.
 Tabbas rayuwar tana tafiya da yadda mutane suka tsarawa kansu, amma rayuwar da Malik ya tsarawa kansa, yafi kowacce rayuwa bala'i. Kallon juna MD da Salim suka yi kafin suka mai da hankali kan Mr Amjad.
Kuma aka rasa waye zai magana, wayar Amjad ne yayi gunji. Kamar ba zai dauka ba, ya dauka. Amjad Lamid ne? kamar wanda aka watsa mishi ruwa haka ya amsa da cewa.  Eh ni ne, waye  Na kira ne, na baka shawara kada ka sake shiga abin da babu ruwanka tsakanin Malik Menk Jordan da Mr Khuldu Jahid Khan

 Amma waye kai? Mr Amjad ya tambaye shi, murmushi me sauti na wayan yayi sannan ya ce mishi.  Sani na bai da wani amfani, amma zan baka shawara ka nisanta kanka, daga wannan hatsaniyar Malik ya fi ku hauka, a duk lokacin da ya fahimci kana cikin masu niman shi sabga shi. ya fada mishi yana kashe wayar.


Wani azzababen tsoro ne ya mamaye zuciyar Mr Amjad, ilahirin jikinsa rawa yake, yadda zaka fahimci, yana cikin tashin hankali. "Sir akwai matsala ne?" Kallon MD yayi da ya tambaye shi, sannan ya ce mishi.

 Na jima ina Kasuwancina, ban tab'a shiga tashin hankali irin na yau ba, amma qaddara sai da ta haWa ni hanya da Malik Menk Jordan, a da wai-wai nake shi a yau da na gani da idanuna na tabbatar shi din ba kanwar lasa ba ne.

 Sir wai mene ne matsalar ne? MD da shima yake razane, domin daga yadda Mr Amjad yake firgice zai tabbatar maka da cewa yana razane.  Ban san kaddaran da ta hada ni da Malik ba? Amma nasan mutuwa ta ce ta kusa bayan haka kura mishi idanu suka yi. Sannan ya cigaba da cewa.  Idan har kuka ji labarin na mutu don Allah ku saka idanu akan iyalina.
Su kansu a rude suke, domin kuwa labarin mutuwar Prime minister ya ratsa lungu da sao na cikin garin Keivroto city.

^^^^
A lokacin da Zeenobia ta bar S..... Digital art, ta nufi hanyar gida da mutanenta, a nan ne ta fahimci garin ba lafiya domin duk inda suka wuce zanga-zanga ake wanda zai nuna maka, alamar kowa a fusace yake, ko da yake ai ba kowa bane domin wannan rigimar ba don talaka aka yi ba, suna yi ne domin kare muradunsu da aljuhunsu. Duk wanda zaka gani tow ba yana yi don talaka ba ne, yanayi ne domin cikawa aljuhunsa yan canji.

Ajiyar zuciya Zeenobia tayi tana kallon yadda ake fashe-fashe, babban burinta su isa Al'umma charity House, domin kare wannan gidan hakkine da ya rataya akanta, ba iya ita ba, ga duk wanda yake numfashi a cikin gidan. Domin ganin yadda yan zanga-zanga suke barnan dukiyar gwamnati, yasa ta kalli black ta ce mishi.
 Ka taka motar, mu isa akan lokaci domin za a iya saka curfew nan da wani lokaci.
 An gama Yar kunama! Ya kuwa karawa mutanen gudu, cikin ikon Allah suka isa gidan cincirindon jama'ar gidan a bakin get din gidan yasa ta sauke ajiyar zuciya. "Yar kunama!" Sauka tayi daga motar tana kallonsu.  lafiya kuka yi cirko-cirko? ta tambaye su, tana cire glass din idanunta.  ina zamu iya nutsuwa mun ji labarin gari babu lafiya, ke kuma da su Dundurosu kuna waje. murmushi tayi ta wuce bakin get ta ja kofar tare da rufe kofar gidan bakidaya.  ina son nayi magana da murya daya, kowani lokaci za a iya saka dokar tab'aci, ban lamunci wani ya ketare gidan nan ba, idan na fahimci haka ya faru hmm. ta fada tana haurawa sama.

 Didih wai da gaske Malik Menk Jordan, shaidani ne? juyawa tayi ta dauki yarinyar da bata wuce shekara uku ta shiga tafiya da ita.  Sweetheart ban sani ba, Shaidani ne ko mutumin kirki ne, abin da na sani ya kashe Babban mutum me daraja. ta fada tana shafa kanta.

 Didih Abbana ya ce wai shaidani ne, shine Iya tace kar a bari kiji labarin kome. juyawa tayi ta kalli Iyar da ta mata yake.  Iyah sun fadi wani abu ko Sweetheart?" Gyada kai tai, sannan ta wuce kofar dakinsu yarinyar ta ajiye ta, sannan ta wuce Wakinta, kafin ta bude ta samu Hafsy tana dakin.  Alhamdulillahi kin dawo lafiya kallon juna suka yi, sannan ta wuce ban daki. Sai da sauya kayanta, sannan ta dawo falon dakin. Bude karamin firji tayi ta dauki abin sha, ta zauna tana me kunna TV.  Ni tsorona daya kada wani abu ya same ku, sai gashi kin dawo akan lokaci. kurban fanta tayi tana kallon tv.
_Izuwa yanzu hukumar sun saka dokar curfew na tsawon awanin kafin a gama binciken mutuwar mai girma Prime minister._ gidan tv suka fada, rage arar tayi tana faWin.  Ban san wacce duniya muke ba, amma kuma. saukowa daga gadon Hafsy tayi, ta rike hannunta.  Meke faruwa? gyara zama tayi sannan ta ce mata.  Aikin da aka ba ni, wai zan na gayyatar mutane su saka hannun jari a kamfanin na zata security service zasu bani. ta fada tana sauke ajiyar zuciya.

 Tir security service? Allah ya sauqaqe miki. Ai wuce wannan level din, matsayinki ne. Zaki kara zama yar gayu eyee! ware idanu tayi, tana gyada kai kafin ta ce mata.  Hafsy ina son aikin amma kuma. sai da ta sauke ajiyar zuciya me nauyi, wanda zai tabbatar maka tana cikin damuwa. Kafin ta cigaba da cewa.  ina son aikin amma kuma, gani nake kamar akwai kasada. Domin ban saba harka da mutane ba, taya zan iya bibiyar mutane don su saka hannun jarinsu. Ala misali wani abu ys faru nice a ciki fa. rike hannunta hafsy tayi tana faWin.  ina ji a jikina zaki yi nasara, matuar aka samu matsala tow dauke shi a matsayin jarabta, bayan nan kuwa labarin zai sauya.

Kurawa Hafsy idanu tayi tana, ta kasa kiftawa. Kafin ta ce mata,  ni kuwa gani nake kamar wani abu zai tafi ya dawo. Bana son abin da zai d'aga min hankali! Dariya Hafsy tayi tana fad'in.  Ni kuwa gani nake ba wani abin da zai faru, domin kuwa khair in sha Allah." Ajiye tin din fanta din tayi tana cewa. "Allah yasa." Daga nan suka bude hirarsu.

A cikin Keivroto city kuwa, rikici ake wanda ya haifar da kona-kone, wanda yasa dole jami'an tsaro suka shiga kame mutane, don kuwa barnan tayiwa. Kuma take-taken mutane shi ne nufar manyan masana'antun Menk Jordan manufacturer's, don haka aka zuba matakan tsaron ko ta kwana. Sannan aka bada umarnin duk wanda ya isa wurin a tashe shi.
-------
Public Officer For Legal Investigation and Criminal Emergencies stations Keivroto city (Police stations) fitowa jami'an yan sandan suke da sauri.  Ya ku jami'an tsaro, ku sani a yau garin Keivroto yana fuskantar tashin hankali da barazanar barkewar rikicin siyasa da kabilanci, sakamakon mutuwar Prime minister, Zubair Fatihu Sayyad! Don haka a cikin sanarwar da muke samu ya tabbatar da cewa manyan kamfanonin Mayor Malik Menk Jordan, yana fuskarta barazana don haka dole zamu kwantar da tarzoman da ake yi, sannan mu tabbatar mun kare takalawa da dukiyar al'umma da gwamnati.
 Yes Sir suka fada lokaci guda, kafin su rufe baki sai ga wasu manyan motocin Hilux 44 bakake wuluk har guda shida. Hankalinsu ne ya tsaya akan motar. Suna yan sanda ne suka fara fitowa a motar da bayan motar. Kafin suka budewa bakar audin da take tsakiyarsu. A hankali aka sauko kafa, sannan ta fito sanye da bakar madubi. Sara mata aka shiga yi, ta fito rike da sandarta, tana me zare glass din daga idanunta.  Barka da zuwa Asp Zulfa!" Nufar cikin Office din yan sandan tayi tana faWin.  Ku tattaro min baki daya yan sanda office din nan, da na sauran yankuna baki daya, ina son ganawar gaggawa.   Yes Ma suka fada mata, kafin minti Talatin, bakidaya sun haWu.  Barkanku jami'an tsaronmu. Duk da a kurarren lokaci na iso, ayi kokarin rubayyan tsaro da kwantar da hankulan al'umma, sannan a tabbatar an saka shinge ga wasu wuraren kafin zuwa gobe, kafin nan a tabbatar an kama duk wani me tadda hankalin al'umma, umarni ne daga sama ba umarni na wa ba ne. ta fada tana kallon kayan sadarwan.  Akwai dakin tsaro?  Eh ma! Gyada kai tayi tana faWin.
 Ku kai ni dakin na ga yadda kulawar garin take, za a turo jami'an tsaro daga Gista nan da awa ashirin da huWu, sannan ina
son na je inda gawar Mai girma Prime minister yake!  Yes ma, gawar Prime minister tana, trust palace hotel. Anan suka gabatar da taron. dakin tsaron suka kaita, kai tsaye ta umarci a fara aikin binciken wucin gadi.
Daga nan, hotel inda aka yi zaman suka wuce. Cikin gari aka kara baza jami'an tsaro, inda gawar Prime minister suka inda aka saka zaren criminal scenes. A hankali suka tsallaka wurin, leda suka bata a ta saka a cikin takalmin, sannan ta amshi handglove, kafin ta wuce.  Ma baki saka facemask ba!"  Ok officer a hankali ta shiga zaga motar, tana gefenta wani dan sanda ne, yana rubuce rubuce. Sai da suka gama zaga motar kafin ta bude motar inda prime minister yake zaune.  ina masu binciken gawar me suke samu?
 Gasu nan mikawa juna hannu suka yi, sannan ta ce mata.  Khairat Hadi, nice na jagoranci binciken gawar prime minister, sai dai rashin wanciyar hankali yasa ban gama ba, na koma gefe domin kuwa akwai abubuwan da ya faru. Bayan zuwanmu. gyada kai tayi tana faWin.  Ok gba damuwa, yanzu sauran binciken dole sai kun wuce da shi office din ku ko?

 Eh haka nake son na gaya miki! kallon hotel Win take, tana me gyada kai kafin ta ce.  Akwai Cctv a cikin hotel din nan, daga shigowa zuwa nan harabar guda shida ne, don haka a nad'e mun duk wani bayani da aka shigar na wata shida baya, har zuwa yau. Sannan a kai ni dakin da aka yi taron.  Tow muje ma" haka ta shige har cikin hotel. Ganin yadda ma'aikatan hotel suke cikin damuwa. Murmusawa musu tayi tana faWin.  kada ku damu, aikin mu zai yi shi ne bisa goyan bayanku. Sannan idan muka gama, zamu tafi." Inji dan sandan da yake bin bayan. Shiru tayi tana kallon fuskar mutanen wurin. Kafin ta ce musu.  A wani daki aka yi taron?
Fitowa Manager din hotel din yayi, yana fadin.  Sunana Nuhu Kasim, ni ne manager na

Please Login or Register in order to submit comment