Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawo da wuri ba kana ya kashe wayar ya kira DSP akan ƙarfe 12 na dare yaransa su zagaye ko ina na cikin

haka kuwa akayi sai da wasu cikin banɗaki lungu da tsaƙu na gidan, da ƴan fashin nan shigo Rabi ta nuna musu ko ina na gidan, kana, ɗaya da ga cikinsu ya aza mata bindiga
wai ta kaisu inda Mijinta hadda su kukan munafunci ta haura sama da su, Alhaji Ahmad na jin duk abinda su ke yi amma ya yi kamar bacci ya ke, da shigowar su ka fara ta da shi wai ɗauko musu taƙardun da ya ɗauko Abuja, ba musu ya tashi ya ya nufe hanyar wadirof ɗinsa ya na buɗe wa ƴan sanda guda biyu su ka fito guda ya yi halbi nan da nan saura su ka fito su ka zagaye ƴan fashin su ma na wajen gida su ka shigo su ka ma na cikin gida haɗa su akayi har Rabi aka wuce da su state CID shikuma Alhaji ya koma sabon gidansa wurin matarsa,

nan ya shaida mata duk abinda ya faru
sosai abin ya ba Hajiya Hawa mamaki, kana tayi fatan Allah ya tsare gaba ya tuna ma masu irin halin rabu asiri, washegari, bayan sun kammala cin abinci ta shirya ya ce mata unguwa zasu fita, basu zame ko ina ba sai gidan da yakai Usman da A'isha da yarnsu, falo su ka tarar da Usman da yaransa su na wasa da kayan wargin da ya siyo musu, sallamar da Hajiya Hawa zatayi ne ya maƙale mata ganin Preety na fitowa da ga bedroom ta na kiran "Yaya man ni ma asyo min kyan wargi." Ta na dariya,
Idan har idanunta ba gizai su ke mata ba wannan yarinyar duk inda ta fito jininta ce saboda ga idanun ƙanwarta nan ta na gani da bakinta da komai sai wane gefe ta na kama da ita, Alhaji Ahmad ne ya ce "mushiga ciki mana." Sallama ya yi da Usman da Preety su ka amsa ta re da gaida sa cak idanun Preety ya sauka akan Hajiya Hawa, kasa ɗaure ta yi da gudu ta rungume Hajiya Hauwa, ita ma rungumeta ta yi su ka fashe da kuka sai da komai ya lafa kana, Alhaji ya warware ma matarsa komai, wani sabon kuka ta shiga yi yanzu tsawon shekaru ƙanwarta ta rasu, sai su ka yi ta lallashinta kana ta haƙora amma sai ta je ƙauyen Gagarawa,

jan jikokinta ta yi ajiki ta na jin ƙaunarsu na ratsata, fira su ka shiga yi sosai kana su ka tattara su ka koma sabon gidansu, wata ƙawarta Hajiya zainab mai gyaran jiki, nan ta biya kuɗaɗe aka fara gyaran jikin Preety, cikin ƴan kwanaki idan ka ganta baza ganeta ba, tayi masifar kyau na ɗaukar hankali Umma ta hana Usman ganinta ga kayan tsimi da sauransu su Arif kuwa anzama ƴan gida har an kaisu wata makarantar ƴaƴan masu kuɗi sun fara tafiya shi kuma Usman Abbansa ya gayara ma sa gindansa sosai ya kashe ma sa kuɗi idan ka shiga gidan bazaka so ka fito ba, don Umma ta ce sabon bikin aurensu za'ayi ana haka ne sai ga Ilham ta kira Preety sosai ta yi murna jin Preety na wurin dangin Mamanta koma Usman Yayanta ne, Ilham ta zo ita da mijinta sun samu tarba mai kyau da su akayi komai,


kana Preety aka kai Preety gidan mijinta, su Aryan ko wai bazasu koma ba wurin Umma za su zauna,
ranar Preety ta gurzu wurin Usman, soyayya su ke zubawa sosai wanda ko lokacin da su na Sokoto ba su yi ta ba,

sunje ƙauyen Gagarawa inda su ka iske Inna Hajjo ba ta da lafiya sosai ta zama abin tausayi ta na kuka ta na ba Hajiya Hawa labarin irin cutarwar da ta yi ma Nimra da ɗan cikinta Abubakar har Preety da zuwan Usman, ta na kuka ta na rokon su garafa, sosai su ka tausaya mata kuma su ka ce sun ya fe mata,


sai ga Kande ta shigo kamar mahaukaciya ta shiga ba su labarin wurin Bokan da ta tafi ya lalata tsakanin zaman Nimra da Inna Hajjo, ta na gama faɗa ta fita aguje ta na cire kayan jikinta yara su ka bita su na waƙar Kande mahaukaciya,

ga ƴarta cutar HIV ta kamata wurin yawon karuwanci,

su rabi kuwa anyike musu zaman gidan kurkuku na shekara ashirin, ta re da horo mai tsanani ko Alhaji Ahmad ya yi mata saki uku,


bayan wasu shekaru Preety ce na hango ta re da Usman da wata ƙaramar yarinya da bazata wuce shekara biyu ba, sun fito da ga mota sai fira suke gwanin burgewa,

Hajiya Umma da mijinta su na zaune falo su na fira da Aryan da Arif sai rigima su ke akan ba zasu je Dubai ba London zasu je, nan Preety da Usman su ka yi salma su ka shigo Hajiya Umma na faɗin "Yoyon Nimra zonan." Ta na jan hanun ƙaramar yarinyar "gaskiya Usman ko bar min Nimra anan yayeta zanyi kar tasha ciki saboda na ga alamar hankalinka bai kai nan, ba." Sosa kai ya yi kana ya ce "Da ma Umma yaye muka kawo ta kayanta na cikin mota, kai Aryan jeka ka ɗauko don da ga nan filin jirgi yi Torke zamu tafi sai Preety ta haihu zamu dawo."

Alhmdllah! Alhmdllah Alhmdllah

Anan na kawo ƙarshen wannan littafi
Allah kayafe muna kuskuren da ke ciki allah ya sa mu amfana da abinda ke ciki,

Sai mun haɗu cikin sabon liltafina mai Suna Riyann!!

Wanda na zo muko da sabon salo kala-kala soyayya cin amana da zalunci ƙiyayya romantic da s.... wa'zantarwa faɗakarwa da ni shaɗan tarwa

Ma'salam

Story & writes by
Zainab Abdullah pinky Darling 🌷
~Matar jay~






Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment