Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka ta bar dakin.

Da ganin ficewar Inna kuwa ya sake mun tattausan murmushi tare da matsowa inda nake kwance cikin takun shi na nutsuwa,tsaye yayi a kai na tare zuba mun idanu a hankali yace “Pretty laifin me kika yi wa Inna tayi miki irin wannan mugun dukan haka?” shiru nayi na ma kasa bashi amsa

Ganin haka ne ya sanya ya kamo hannu na yace “ ki fada mun mana”sai lokacin wasu hawaye masu zafi suka samu daman zubo min cikin kuka na fara fada masa abinda ya faru, tun bayan dawowar ta talla shiru yayi ya matse hannu na cikin kuka nace masa “don menene biyar maza da kuma maita?”

Kura mun ido yyi kamar bazai yi magana ba sai kuma ya numfasa yace “shekarun ki nawa?”dan shiru na dan yi sannan nace da shi “sha biyar (15)”dan jinjina kai yayi sanann
yace “ajin ki nawa a makaranta?”

Nan ma saida na dan yi shiru sanann nace da shi “Ai ni bana zuwa, Inna bata sanya ni ba”shiru ya dan yi sanann yace “islamiya fa?”inda wannan kan nace da shi “jiya nafara zuwa” ya girgiza kai yace “ ai ba mace kesa yaro makaranta ba, Mahaifi ke da wanann alhakin shi ke sanya yaro,ke Ina Baban ki?”wannan karan kuka na fashe da shi inda cikin kuka nace da shi “da mama na da Babana duk sun mutu,kuma Inna kullum tana cewa Mama na ce ta cinye babana wai mayyace”ta kare tana kuka me cin rai.

Jikin Usman yayi sanyi ba kadan ba yace “pretty fadamin tarihin ki,bana son ki boye mun komai game da tarihin rayuwar ki” nisawa nayi sanann nace “miye tarihi?”saida yayi murmushi sanann yace” labarin rayuwar ki”da jin haka kuwa na kwashe iya abunda na sani tun daga tasowa ta,da irin bakar azabar da Inna ta ganamun take kan ganamun har gobe har zuwa haduwar mu da shi na fada masa ban boye masa komai ba.


Ba karamin girgiza Usman yayi ba da Jin bakin zalunci irin na Inna yace “Aisha” nace da shi “na,am “ kamar daga sama na ji yace “kina son karatu?”jin tsantsan jin dadi nace da shi” Eh wlhh ina so sosai ma”saida ya dan murmusa sanann yace “zan saka ki a makarnta kin ji,hope za ki tsaya kiyi karatu?”

Da jin haka ai ban san lokacin da na mike zaune ba,na nemi duk wani ciwo da zafin da nake ji na rasa,da sauri nace “ da gsky zaka sani boko?Nima na zama yar gayu kamar kai?Na iya turanci nima ko?”

Kai ya daga mata ya daga mata almaun eh snanan ya dauko Pad (Always)guda daya ya bani sanann yace inje bandaki in saka, ido na zaro sanann nace “menene?Kuma a ina zan saka?”ido ya dan zaro sanann yace

“ Baki san shi ba?Kuma baki san yanda ake amfani da shi ba?” Nan da shi “ Eh” tashi yayi ya fita inda be jima ba ya dawo tare da wata ma'aikaciyar asibiti yanuna mata ni yace”help me out sister ina jin bata San komai
Ba please kiyi mata duk bayanin yadda zata kula da kanta da komai”inda tace da shi kar ya ji komai,kafin ya juya ya fita.

Matar ta zo ta zauna nan tayi min bayani akan Jinin Al ‘ada da komai inda take
na fahimta sosai har wanka ta koya min,sanna tace kar in yadda maza su zo kusa dani,don yanzu na girma Ina iya samun ciki, kuma yanzu azumi ya zamo dole a kina da sallah,in ko na sha Azumi to yanzu ya wajeba a kai na dole sai na biya,duk abinda ta fada mun na fahimta kuma na rike su a kaina,sanann kuma naji dadi sosai ,tare muka je bandaki ta nuna mun yadda zan yi amfani da pad tace idan banda ita ina iya amfani da kyali me kayau nace mata nagode sosai sannan ta juya ta fita,bata jima da fita ba yadawo da Leda a hannun sa,inda ya mika min na sa hannu na karba,kafin yace “natafi sai anjima,Allah ya kara sauki”murmushi nayi nace “tom na gode sosai” be ce komai ba ya fita daga dakin, yana fita na bude ledar pants ne sabbi da turare a ciki,inda naji dadi sosai saboda koh pant din kirki banda,guda daya nake dashi idan na wanke sai na jira ya bushe kafin na kuma sakawa.

Ina nan zaune Inna tadawo da kwano hannun ta ta zauna kusa dani tace “ tashi kici ki sha magani likita yazo ya sallame mu “tashi nayi na sauko kasa najawo kwanon na bude Dan wake ne da manja da kuli nasaka hannu na fara ci, sai dana cinye shi tas na sha ruwa ta daukoh magani ta bani, na sha sanann ta kira likita wai yazo ya sallame mu,inda yace mata ba yau ba sai zuwa gobe kafin nan jikina ya kara warware wa, nan fa ta shiga masifa be kula ta har ta gaji don kan ta tayi shiru.

Ban kuma ganin Usman ba har dare yayi Inna tace wlh bazata kwana ba sauro ya halakata haka ta bar ni, ni kadai asibitin gashi an dauke wutar nepa idan nagaji da kwanciya in tashi zaune har bacci ya dauke ni, fitsari ne ya farkar da ni,Ina bude idona naga haske fitila kusa da ni, da sauri na rufe idona na kuma budewa Usman ne zaune kan kujera Yana danna wayarsa be masan na farka ba kokarin tashi nafarayi saboda jikina duk ciyo yakemin,dagowa yyi muka hada ido gaba na ne yayi saurin faduwa,duk lokacin d muka hada ido har tsikar jikina ke tashi ban san dalili ba.

Tasowa yayi yakama ni nayi saurin ja da baya,tsayawa yyi chak yana kallo na kafin yace “ lpy dai?”cikin tsoro nace masa “matar nan ta dazu ta fada min kar na yarda na bari namiji yazo kusa dani,in ba haka ba ciki zanyi”na kare da iyakan Gaskiya ta.

murmushi ne ya subuce masa ganin yarinta tayimin yawa sanann yace “hkn gsky ta fada miki,amman ai banda Dan uwanki ko?Ni ba yayanki bane?”Ya kare yana tsare ni da ido.

Shiru nayi na kasa bashi amsa hakan ne ya sa yace “idan bakya son yayanki wazai tai maka miki?” kallon sa kawai nake yadda yake magana hankali kwance ga muryarsa me shegen dadi, kamar kar ya dena magana ganin irin kallon da nake masa yasa yayi shiru tare da miko min hannun sa yace “taso muje in raka ki” ba musu nabashi hannu na yadaga ni,yar naji tsikar jikina na tashi,abinda bantaba jiba wani da namiji be taba rike hannuna ba sai yau tafin hannun sa kamar auduga don laushi.

Inda bangaran Usman kuwa mamaki yake Ace irin wahalar da take sha, Amma hannu ta kamar auduga Ko da yake iya kyawun ta ma da yanayin skin color din ta ma abin mamaki ne saboda wusu matan duk kyan su indai suna cikin wahala bacewa yake yi,haka dai ya raka ni bandaki na shiga, na fitu muka dawo na kwanta, amman sam na kasa bacci sai juyi ni ke yi,da ya kula ne,cikin taushin murya yace “pretty lpy dai?”nan nace masa “na kasa bacci ne”nan ya ce “to tashi muyi fira” ba musu na tashi zaune yace “yawa yanzu bani labarin to”shiru nayi ganin haka ya sa yace “Ko ba ki da shi ne”da sauri nace masa “Eh banda labari”

Nan yace “Koh na qawayen ki?” Nan nace masa “ai ni kam bani da qawaye saboda Inna nace min mayya shine ko nafita wasa suke kora ta, wai kar na cinye su tausayi,babu ke wasa da ni,kuma babu me kawance da ni”ta kare tana hawaye, sosai ta bashi tausayi,ajiyar zuciya ya sauke sanann yace “shikenan kar ki damu yanzu ai kina da ni ko”da sauri nace “Ai kai yayana ne”murmushi yaye snanan yace “ba Yaya kadai ba ni Abokin ki ne kinji me kyau!!” murmushi nayi😊 Wanda yakara min kyau inda ya kafe ni da ido yace “pretty na wai Ina Kika samo wan nan kyau hk? Naga bakya Kama da Inna ko kadan."





💔SO💘


Love and romantic story
🌸🌸🌸writers by pinky darling
Ginbiyar jajirtattu 👸🌺🌺🌺


Bismillahi Ramanin
Raheem 💫


https://chat.whatsapp.com/L8T8LeP1z07HBcKiPOLs1P

_____________________________________________________________$
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


PAGE 6


Shiru nayi. saboda Nima bansan inda. Nasamo kyaun ba "yace "yadai pretty? ajiyar zuciya. nasauke. Nace Yaya na nima. Bansani ba. Wani qayata can Murmushi ya" sakar min me daukar hankali Nima. Murmushi nasakar masa. Saida yanisa Sannan "yace pretty. ki kwanta. Kiyi bacci Dr "yace gobe zai Baki, sallama. Gabana. Ne yayi mummunan faduwa. Lokaci. Daya hankalina. Yatashi shikenan zan dawo Shan wahala wurin Inna. Nan take idona yaciko da hawaye Kallo na yayi "yace lpy dai pretty?, Bakya son komawa gida ne? Da sauri Nadaga Masa Kai kamar bazai yi magana ba. Chan dai. "Yanisa pretty hakuri zakiyi. ki kwantar da hankalin ki. In Sha Allah. Ba. abinda zaifaru kinji. Koh qanwata, ahankali Nadaga Masa Kai yace yauwa go and sleep. Kamar naji abinda "yafada. na Kwanta tare da rufe idona har bacci yayi awon gaba. Dani ban farka ba sai asuba. Ina tash Banga Yaya Usman wata. Zuciyar tace yatafi masallaci bandaki nashiga nayi tsalki na gyara jikina. Nafitu na zauna gefen gado Ina tunanin. Rauwa nayi Nisa cikin. Tunani bam maji karar bude kufa ba. Sai jinayi andafa ni good morning my beautiful girl did you sleep well? Dagowa nayi ahankali Ina kallon sa "yana sanye cikin qananen Kaya. Bakin wando. Ne ajekin sa da blue din riga sumar kansa. Sai sheqi take. Takwanta. Ga sajen dake. Zagaye da kyakkyawar fuskar sa. Hannun sa. daure da agogo me shegen kyau Masha Allah na. fada cikin zuciyata. girgiza min. Kafada. Yayi "hankali nace barka. Da safiya yayana fatan katashi lpy?, Ajiyar zuciya yasauke "yace lpy Lau qanwata ykk?, Murmushi nayima sa nace lpy Lau Yaya nah, "yace Dr be shigo bane? Nace Eh ya daga Kai. "yace hope dai keci abinci? Yakara she maganar Yana Jan kujera. "Yazauna girgiza Masa Kai nayi. "Alamar banci ba. Sai da "yanisa Sannan "yace Inna bata zobane?, Eh nace Masa. "Yace okay Ina zuwa. Tashi yayi "yafita narakashi da ido bejima da. Fitaba Dr "yashigo dubani. Bayan mungaisa. Cikin sakin fuska. "Yace hope dai Babu Abinda. Kedamunki yanzu? Kai Nadaga Masa "yace okay Allah "yakara sauki "nace Ameen ngd, "yace shikenan idan me kula dake tazo zaku iyatafiya gida, nace tom. "Yajuya yafita nikuma gyara zamana saman gado turo kofar dakin akayi ba sallah akashigo Koh ba"afada min ba nasan Inna ce karasowa tayi kusa Dani. ke don uwarki bacci kikeyi haryanzu? Kallon tanikeyi sai faman masifa takeyi koh. Gajiya batayi. Usman ne yashigo da sallah ma riqe da Leda ahannun sa."yace Inna brk da spy kamar ba itace ke masifa ta"ce lpy Lau. Ygd "yace lpy, takowa yayi har kusa Dani yamika min ledar "yace tashi kici Kisha magani Dr yashigo? Nace Masa Eh har munyi magana. "Yace okay Ahankali na bude ledar dankali ne da. wainar kwai. "Ahankali na Fara cin dankalin da kwai Inna na. Gefe Tana. Kallo na idan nadago muka hada ido. Taharare ni. Nikuma inyi kamar ban ganta ba. "Tana son tayi magana "Amma saboda Usman tayi shiru. Kuma gaba Daya hankalinsa baya kanmu. Kansa na kasa "Yana Dan nar wayarsa bayan nagama cine na. Cema Yaya na Kammala sai lokacin yadago muka hada ido. Nayi saurin kawar da kaina. Okay ledar magani "yadau Koh "yahada min nasha. sannan "yace ma Inna zamu iya tafiya Dr "yabata sallama Inna "tace tom idan kega dama. Tashi mutafi, miqewa nayi tare da daukoh rangan hijab Dina ita Koh Inna harta Kai kofa hk nabi bayan ta.har mun fitu natuna da ledar magani da takayan da Usman yakawo min. Najuya da sauri naje nadauko "abakin get nasame Inna. Da Yaya Usman tsaye nayi inajiran Inna "tawuce mutafi Usman ne "yace pretty mutafi ga mota Nan waje in ajiye ku gida, da sauri Inna "tace mota fa kace? Dan Nan daga Kai "yayi alamar What jikin Inna har rawa yake wurin sauri taga mota bayan inna. Muka bi nida shi WATA hadaddiyar motace nagani baka sai sheki take gabanta an rubutu CMC key "yayi ma motar ta bude sannan "yace ma Inna tashiga mutafi. Ai Koh Inna taki shiga sai raba idano take jikin ta narawa "tace wlh nayafe bazan shiga ba kayanka ni dariyace ta Kama usman😂 "yace haba Inna Taya zan "yanke Miki Kai wlh ni ba Dan "yankan Kai bane kayarda Dani, shiru Inna tayi "Tana mazurai da ido Chan dai "tace Indo kifara shiga ingani idan har Baki Bata ba nima. Zanshigo. 🤣Dariya Usman yakuma yi sannan "yabude motar yace pretty shiga ba. Musu nashiga nazauna. "Yace Inna saura ke tace saura ni dame? "Ai wlh idan kagan nin lahira. Kaini akayi, takarshe maganar "tafara tafiya akafa. Usman "yabi bayani ta. "Yana Mata magiya da. Kyar Inna tayarda zata shiga motar. Amma fa "sai yasauke gilas din motar "yace nayarda mutafi sannna "tabiyo shi dazata. Shiga motar bakalar addu'ar da batayi ba harda tashiga bandaki tana shiga motar ai saida Inna "takusa sumewa saboda waning sanye da. Yaratsa Mata qasusuwa ga wani. Kamshi me masifir Dadi duk yacika Mata hanci. Usman "yarufe marfin motar "yaja suka tafi. Inna dai tunda "tashiga motar bakinta ."yamutu nikuma sai kallon hanya Nike wai yau nice 'acikin mota irin ta Yan gayu. bangaren Usman Kuma tuke "yakeyi hankali kwance "Yana biyar karatun 'al kur'ani me girma da. "Ya kuna cike da burgewa. Koh da. Muka. Isa. Inna tayi bacci tashin ta nafarayi "aiko tazabura da.karfi "tanace wa yasiyar da mu Koh Indo? Dariyace ta kwace min. Usman "yakura min ido "yadda Nike dariya gwanin burgewa. Duka Inna "tanada min abaya. Shegiyar yarinya ni sa'ar kice shiru nayi. Usman "yabude muna motar muka fitu Amma Inna Bata. Dena masifa ba. Tarigamu shigewa cikin gida nikuma natsaya muyi sallama da. Yayana Usman ne "yafara cewa tom pretty kikula da kanki Kisha maganin ki in Sha Allah zuwa gobe zandawo, nace tom yayana Allah "yatsare yakai ka lpy "yace Ameen bye kasa tafiya nayi Shima hk Chan dai "yanisa Sannan "yace pretty lpy? Koh akwai Abinda kike bukata ne?, Girgiza Masa Kai nayi 'Alamar a'a Murmushi "yasakar min. me yaye min damuwa. "San Nan "yashiga mota Ina daga Masa hannu har wuce. Kamar karyatafi "yadawo inyita kallon sa. Nadade tsayi har na hakura nashiga cikin gida inata tunanin yayana Sam na manta banyi sallama ba aikoh Inna Tayo kaina dayake gidan ubanki ne dole kifadu. Min gida. ba sallama. Mayya kawai, wasu hawaye ne masu zafi suka cika min idanu. Narasa me natare. Ma Inna gidan duniya take min. Wannan cin kashin.


💖SO💔

Love and Romantic story





writes by Elharm pinky darling🌺🌺

Ginbiyar jajirtattu 👸


Bismillahi Ramanin
Raheem💫


https://chat.whatsapp.com/L8T8LeP1z07HBcKiPOLs1P
________________________________________________________________

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️




Page7








Anya rayuwata zatayi mindad'i ban kulata ba nashigewa tadaki nakwanta ina tunanin rauwar danikeyi har bacci yadauke ni saukar ruwan sanyi ajikina ne yafarkar dani mikewa nayi ina kallon Inna dake tsaye daroba ahannu sai faman huci takeyi banyi magana ba ke "dun ubanki nisa'arki ce da zakizo ki kwanta min adaki shara da wanke wanke duk nizanyi miki sune ko uwarki zatazo tayimin wallahi indo dukan tsiya zanyi miki inga ubanda zai ramamiki munafukar banza mayya maza kifitu zuwa aiki.






haka nafitu jiki ba karfi nafara shara bayan nagama nafara wanke wanke ina gamawa naje dakin inna nace"Inna in hura wuta in dura girki.? banza tayimin saida nakuma tambayar ta sannan tace" aikesan inda kayan abincin suke amma tsabar iskanci kikazo kina tambayata tu gasu nan akaina zoki dauka me idon mage kawai.
ban kulata ba nafitu saboda nakula duk lokacin danike bata hakuri kamar nakara mata karfi haka zatayi tazagina haka naje nahura wuta nadura tuwan masara da miyar kuka sai bayan isha nagama girkin jikina duk yayi kaurin hayaki sallah nafara yi sannan naje naja ruwa arijya nawuce bandaki nayi wanka na gyara jikina bayan nagama shiryawa nafitu waje insha iska saboda anfara zafi wata guntuwar tabar ma naja nazauna narafka uban tagumi kamar wacce akacema gobe zata mutu nafara tunanin makaranta araina nike fadar anya inna zatayar da yaya usman yasaka ni boko haka dai nayita saka da warwara har akayi sallar isha nayi naje nadauke abincina inaci inna nadaki ko sallan magarib batayi ba ta fitu rike da mayafi ahannu "kinafita zanje gidan lami idan Dije tazo nemana tajira ni ba dade wa zanyi ba. bata majira amsata ba tafita
nikuma naciga da cin abincina inna bata jima dafita ba yaro yashigo wai wani na sallama dani awaje shiruwa nayi har yaron zaifita nace







"kace inazo daki mashiga cike da mamakin wake sallama dani saboda babu me zuwa wurina zance haka dai na saka hijab harda fesa turaren da yaya usman yasiyo min tare da pant natafi cike da fargaba.
kamar wata mara gaskiya haka narinka leken bakin kufar gida kuda ba haske amma nagane ko waye dasauri nafitu ina sakin wani murmushi ko magana nakasa sai raba ido nikeyi shima dai kallo na yake becemin komai ba dayaga banda alamar magana yayi gyaran murya yace "eshana baki iya gaisuwa bane.? kunyace takama ni na sunkuyar dakaina kasa ina wasa da yatsuna sannan nace"brk da dare yayana juyar da kansa yayi be amsaba saida nakuma gaidasa yajuyo "kireki gaisuwar ki banaso tunda saida naroka" yana wani bata fuska wai yayi fushi. gabana ne yabuga dakarfi idan yaya usman yayi fushi shikenan banida me sakani bako haka.






zanyi tazama ina tallan awara nace "kayi hakuri yayana bazan sake ba nakarashe maganar kamar zanyi kuka kallo nayayi kafin yamatso kusada ni yakama hannu wana yace "pretty badai kuka ne zakiyi ba? kesan banason ganin hawaye akan kyakkyawar fuskar nan taki. Dagowa nayi ahankali muka hada ido dasauri na saukar da idona kasa kirjina na buguwa da sauri ban San dalili ba ban iya hada ido dashi idan ko muka hada ido har wani yar nikeji ajikina matse min hannu yayi "bazakiyi magana ba pretty na? Cikin sanyin murya da yazame min jiki nace "bakuka zanyiba yayana ban ankara naji wani abu mesanyi kamar yabi saman kafata dasauri naja baya Ina zare idona arazane duk da babu wada tacce hasken farinwata ne amma kana iya ganin abinda akasa bakomai ne yarazana naniba face maciji gudan katu baki tsabar firgita ko magana nakasayi sai nuni nikewa yaya usman da hannu tanbaya ta yake amma nakasa furta komai "pretty wai menene hannu na yake bida kallo wayar sa yadauko yahaska ai dasauri naga yayo kaina Yana esha "kimatsa daga nan da sauri nikuma kamar wacce aka daure ko motsawa banyi wani abu naji yashige min akafa kamar tsinin alura atake jikina yafara tsuma ko da yaya usman iso wurina danike har nayanke jiki nafadi sumammiya arazane yafara jijjigani yana fadan" aisha pretty na kitashi karkiymin haka gabadaya yarikice komai yakasa yimin shikama macijin yana sarata akafa yayi tafiyar sa


inna tadawo daga gidan kawarta ta hango mota kofar gida aiko da sauri takara so ganin Usman rungemi dani kamar wani zararre sai faman jijjigani yake ai ko Inna takurma ihu tana fadin "nashiga uku jama'a kukawo min dauki yakashe minjika dama ban yarda da Kai shikenan ka lalata min jika aiko abinka da kauye nan danan jama'a sukayo kofar gidan Inna wani matashi ne yayo kan usman zai dake shi Usman yadaga masa hannu yana fadin"kar wanda ya kuskura yatabani Ina tace iyye "kalalata min jika Sannan kace zakayi muna rai ninwayo wallahi bazan yarda dolema adaura muku aure da ita yau basai gobe ba don bazan zauna da karuwa ba nan dai wasu suka marama Inna baya akan adaura muna aure wasuku ma nafadar afara dubani idan tashi inyi bayanin abinda yafaru wane dattijo ne yace ma usman "Kai yaro kayi muna bayanin abinda yafaru kayi shiru ka rungeme yarinya kaki magana rashin maganar kafa yana nuni da ka aikata abinda ake zargin ka

kan Usman ne yayi mugun sarawa Jin mugun abinda akejifar shi da shi girgiza Kai kawai yayi yanajin jina jahilce irin na kyauye

Inna tace"ai bazaiyi magana ba saboda yasan abinda ya aikata adaura musu aure kawai nan danan akakira liman yazo yace ma usman "yabada sadaki ko motsi yakasayi don ko alabaran almara betaba Jin inda aka tabayin haka ba ahankali liman yazo kusa dashi yacire agogon azurfar dake daure a hannun usman yakuma cikin mutane "yace ma Inna ko tasan sunan sa da sauri tace eh "nasani Usman naji likita Yana kiransa yace tom jama'a kushai da zan daura auren Indo da Usman akan sadakin agogon azurfa nan dai aka daura aurena da Usman kamar amafarki naji shelar da liman keyi a hankali nafara bude idona aiko naga zahiri ba mafarki bane da gaske ne arazane natashi Ina son inyi magana amma azabar danike ji cikin ƙafata ya 𝒉𝒂𝒏𝒂 𝒎𝒊𝒏.𝒎𝒂𝒈𝒂𝒏𝒂



PAGE8


Ahankali mutane suka fara wa tsewa, ina kwance ajikin Usman nakasa ko da mutsin kirki kawai nafashe da kuka be yimin magana ba miƙewa tsaye yayi tare dani ya bude motarsa ya sakani ya ja motar be tsaya ko inaba sai hospital fituwa ya yi tare da bude bayan motar yabdauko ni ya shiga da ni ciki, ofis din Dr ya wuce dani ina rungume ajikinsa da shigar mu Dr ya taso ya zo inda Usman ya tsaya dani man"lafiya wacece meyasa meta,? haka Dr ya jero masa tambayoyi amma yaga Usman baya da niyar amsa masa ne ya sa shi saka hannu daniyar ya karbe ni da sauri Usman yajaba yana yimai alamar karyataba ni
Dr yamatsa gefe yana kallon ikon Allah don shi beyi tsammanin miskilancin Usman yakai haka ba dayaga dai bashida niyar ajeni yayi masa bayanin abinda ke damuna sai kawai yafita yadawo tare da wata ma'aikaciya yana nuna mata Usman dake rungume dani yaki ajeni ko gajiya baya yi
matar ce tazo kusa damu tana cewa"oga lafiya me yasame ta,? sai lokacin yayi magana "maciji ne yasare ta aƙafa Please kiduba min ita sosai kiyi mata duk abinda yadace" tom yallabai muje daga ciki matar tafada ba musa yabi bayan ta muka shiga wani daki ya'ajiye ni kan gado yajuya yafita ita kuma matar tadauko kayan aiki allura tafara yimin daga nan bacci yayi gaba dani
yaya Usman nafita ofis ɗin Dr yakoma yayi zaune kan kuje yadafe kansa dake masa wani masifaffin ciyo tunanin yakeson yi amma gabadaya yakasa ga zuciyarsa sai zafi take ganin halin dayake ciki Dr yadauko ruwa masu sanyi yabashi ba musu yakarba yabude yafara sha saida yashinye ruwan gorar tas sannan ya"aje Dr yadafa kafadar sa yace "meyake faruwane man naga ko natsuwa bakada sai lokacin yadago kansa ya kalli Dr kamar bazaiyi magana Dr kuma yayi shiru yana kallon sa don har yacire ran Usman zaiyi magana sai kwai Dr yaji yana cewa" Ali ina cikin damuwa sosai ban san meke shirin faruwa dani ba nan dai

Please Login or Register in order to submit comment