Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiryen buki kawai suke yi ana saura sati ɗaya Alhaji Ahmad ya turo aka duba gidan Abubakar kana ya sa akayi mata other kayan ɗaki Dubai komai namore rauwa ansakawa Nimra hadda ƙatun inji, itama Maryam ya yi mata kayan ɗaki da komai na rauwa sai ma sha 'Allah, radda Inna Hajjo taji labarin dukiyar da a'ka narkama Nimra sai da taje ta gani ba ƙaramar kaɗuwa Inna tayi ba, saboda duk abinda ake batasan Nimra ƴar masu kuɗi bace ai da bazata tada hankalinta ba, nan dai Inna ta sauko tafa jan Abubakar a jiki har lokacin ɗaurin aure ya yi anyi hidima sosai ɓangaren su Nimra da na Abubakar ƙarfe biyar na yamma Alhaji Ahmad ya bada motocin kai Amarya Nimra ta sha kuka sosai zata rabu da ƴar uwarta gashi Alhaji Ahmad ya tura Usman ƙasar U S ya cigaba da karatu. Tare da Yayarta a'kazo kawota, sun iso lafiya nan suka kwana washegari suka shirya zasu koma Barno ai kuwa Nimra ta maƙale ma ƴar uwarta sun sha kuka sosai kana Hauwa'u ta ciro wani zobe na azurfa ta sakama Nimra anyima sa zane da manyan baƙi harfin sunayen su ne a'jikin zoben itama Hauwa'u tasaka ɗaya sai da aka ɓanɓare Nimra daga jikin Yayarta kana suka yima Inna sallama suka kama hanyar komawa Barno.

Sai da Inna tayi ta lallashin Nimra kana ta haƙura, daga gidan Abubakar dana IYayensa babu wata tazara haka shima Umar, Inna Hajjo da kanta ta raka Nimra gidanta kana ta dawo sai murna ta ke saboda kuɗin da Hajiya hauwa'u ta bata sunkai dubu dari4

rauwar Nimra keyi da mijinta cikin kwanciyar hankali tana kula da mahaifan Abubakar sosai ko girki tayi sai ta kaima Inna Hajjo shiyasa Inna ke kula da ita sosai ba laifi..


Page 18 and 19



___________Alhaji Ahmad ne zaune cikin ofishin sa ya na duba wasu files sai ga PA ta shigo ta ce" sir wata mata ce ta zo tana son ganin ka." "Ok ta shigo." juyawa ta yi ta fita ta ba matar damar shiga tura ƙofar ta yi ta shiga tare da sallama jin muraya wacce bazai taɓa mantawa ba ya sa shi ɗagowa da sauri kallon-kallon suka shiga yi ma juna cikin mamaki Alhaji Ahmad ya ce "Rabi da ma kina nan.?" Sai da ta zauna kana ta ce"ina nan mana ban jima da dawowa ba, na samu labarin kayi aure harda ɗa yanzu Ahmad dama kan iya auren wata ɗiya mace ba Ni ba.?" "Haba Rabi kema kesan ba laifina bane ke kika ce baki tashi aure ba karatu zaki ƙarshe ma ki ka bi tsohon Saurayin ki kuka bar ƙasar tu so kike inzauna jiranki.?" Shiru tayi "haba Rabi kema kesan da lafiyata bazan zauna banyi aure ba yanzu ƙaƙa kikeson a'yi.?"

"Aurena Ni keso kayi." A'razane ya ɗago ya na kallon zai yi mata musu suna haɗa ido ya ji wani abu ya dirar masa har tsakiyar kansa, ai da sauri ya ce "shikenan angama gimbiyar mata yaushe kike son a' daura auren.?" "Sati mai zuwa yanzu dai kafara tura min miliyan 30 zanyi shirye shiryen buki." Jikinsa na rawa ya ɗauke waya ya tura mata kuɗin ya ce "yanzu kuma sai me kike buƙata.?" "Bana buƙatar komai yanzu katashi ka maida ni gida." "To Ranki shidaɗe." Tashi ya yi ya ɗauki mukullan motarsa suka fitu har gida ya kaita kana ya wuce gidan sa saboda kansa ke masifar ciwo, Hawa na ganinsa ta taje ta tarɓesa kamar yadda ta saba hannu ya ɗaga mata tare da cewa "karki matso kusa gareni bana son ganinki." Yana gama faɗar haka ya shige ɗakinsa ya rufe, baki sake Hawa ke kallon mijinta har ya shige ɗakinsa ita abin mamaki ya bata saboda iya zamanta dashi ko gardama bata taɓa haɗasu ba tu miye matsalar me ke damunsa, haka ta yi ta zancen zuci da taga ba mafita taje tayi alwala ta tada salla bayan ta kammala ta fara karatun Alkur'ani mai girma

Inna Hajjo ce zaune ita ƙawarta Kanɗe ta na ɗura ta a'kan keken ɓera "yanzu Hajjo haka zaki sakama yarinyar nan ido sai abinda ta gadama shi ta keyi a'n barki nan zaune tunda shi Arɗo ta asirce shi to aike bazata iya komai dake ba." Nifa Kanɗe ban fahimci abinda kike nufi ba yarinyar nan duk abinda ta girka sai ta aiko min har kuɗi ta ke bani juya ma da suka zo ita da Garba sarƙar gorl da kawo min don haka babu wani asiri da ta ke ma malam kyau ta tawar da ta ke min ko Malam bai kaine cin arzikinta ba, bana son irin maganganun nan Kanɗe."
"Au daga faɗar gaskiya sai ki faɗa min baƙar magana shi kenan Hajjo idan ta yi tsami ma ji saboda yanzu idonki sunrufe a'kan kuɗi." Tana gama faɗar haka ta tashi ta fita
Inna Hajjo ta ce Allah raka taki gona haka kawai kisa na takura ma ɗiyar arziki da ƴarki ce Garba ya aura ai da bansamu arziki haka ba

Haka rauwa ta cigaba da tafiya Abubuwa da dama sun faru da masu daɗi da a'kasin haka ciki ko harda auren Alhaji Ahmad da Rabi wanda Rabi sai da ta shiga wurin Bokaye ta samu ta mallaki Alhaji Ahmad ta na juyasa yadda ranta keso saboda babu yadda batayi ba a'kan ta fitar da Hauwa'u cikin gidan amma abu ya gagara daga ƙarshe ta sa a'ka rufe mata bakin Hauwa'u ta zama kamar kurma duk abinda ke faruwa cikin gidan bata iya magana kuma bata iya faɗama kowa
sai da ga baya Rabi tasan Alhaji Ahmad ya haihu da Hauwa'u yaron na ƙasar US ya na karatu nanfa hankalin ta ya tashi tafara yawo wurin Bokaye saboda yanzu shekara8 da auren su ko ɓatan wata bata taɓa yiba taje asibiti Likita ya tabbatar mata da cewa bazata taɓa haihuwa ba, gashi dukiyar Alhaji Ahmad ta ke son mallaka
Duk wanna abin dake faruwa Nimra bata da masaniya idan ta kira Yayarta suyita fira hak zasuyi sallama ta kashe wayar tana don faɗa ma ƙanwarta halin da ta ke cika amma da tayi yunƙurin faɗa sai ƙanta ya fara sarawa sai na manta komai zata faɗa

Inna Kaɗe tunda taji Inna Hajjo ta samu sarƙar gorl ta fara neman hanyoyin da zata bi ta kwance ta sanan ta shiga tsakananta da Nimra ta na saka da tunani wata dubara ta faɗu mata ai kuwa ta zabura ta ɗauki hijab ta fita saida ta kusa fita ƙauyen kana ta yanke wani daji tafiya mai nisa kana ta isa wurin wata bokka, ta na isa taji an ɓarki da mahaukaciyar dariya saida ta tsorata sanan wani ƙaton mutum ya baiyana gabanta da sauri ta durƙusa ta kai gaisuwa gurin Boka ta buɗe baki zatayi magana ya dakatar da ita ya ce "nasan duk abinda ke faruwa yanzu mekikeson a'yi musu.?" "Tace Boka mai gobe so nike duk dukiyar da surukar Hajjo ta mallaka da mijinta Garba da ita Hajjon su dawo gareni su shiga cikin baƙin talauci da sai Hajjo ta tsani Surukarta sanan duk abinda na faɗa ma Hajjo bazata yi min musu."
Ɓarkewa ya komayi da dariya sanan ya ce " ai wannan mai sauƙi ne kije a'ngama ladar aikinki ƴarki zaki kawomin na kwanta da ita."
Shiru Kanɗe tayi tana tunanin can dai ta ce "shikenan angama zan kawo ta anjima." Ta kamo hanya ta dawo hankalinta kwance saboda ta san ƴar tata bataji ta san maza
haka kuwa a'kayi bayan magrib ta saka Larai gaba sai wurin Boka ta na kallo ya shige bukka da Larai ya gama lalata da ita ta fitu suka dawo gida.

Asubar fari Abubakar da Nimra sun tashi sallah suka ga gida wayam komai a'n kwashe ba'abar musu komai ba cikin tashin hankali suka fito zuwa gidansu Abubakar da shigarsu suka tarar da Baffa da Inna Hajjo tsakar gida hankali tashe har shanon Baffa a'n sace Baffa ya ce " Garba lafiya na ganku da asuba nan suka faɗa ma Baffa suma abinda suka ta shi suka tarar aiko hankalin Inna Hajjo ya ƙara tashi tayi kukan kura tayi kan Nimra ta shaƙo wuyanta ta na "wallahi sai naga bayanki annuba kawai mai farar ƙafa wallahi Garba sai ka saki wannan tsinanniya munafuka maiya." Baffa ne ya kife Inna Hajjo da mari har saubi2 kana ta saki wuyan Nimra ya ce "wallahi Hajjo Garba na sakin wannan buyar Allah kema aurena da ke ya ƙare."
"Garba ja matarka ku tafi gida Allah ya rufamuna asiri duniya da lahira." "Amin Baffa ya ja hannun Nimra suka fito daga gidan banda kuka babu abinda ta keyi wannan masifa da me tayi kama, ga mari ga tsinka jaka suna isa gida masallaci ya wuce sai da ya dawo ya shiga lallashin matarsa har ta haƙura ta daina kuka, haka rauwa tafara yima su Baffa tsanani abinci da zasuci ma wataran gagarar su yake ga shi Nimra ta samu ciki mai masifar laulayi, ga rashin kwanciyar hankali ita babbar matsalarta bata samun wayar Yayarta takira Abban Usman ya ce mata baya ƙasar amma Yayarta na lafiya nan dai hankalinta ya fara kwanciya cikinta har yafara girma Maryam ce ke taimaka musu da abinci ita da mijinta Umar don bata san abinda ke faruwa ba sai da tazo gidan Nimra tana nan zaune Inna Hajjo ta shigo ta zage Nimra tas kana ta fita, tun daga lokacin ne ta fara kawo ma Nimra Abinci na safe da rana da dare, Abubakar ya rasa inda zai sa kansa saboda Inna Hajjo harshi zagi ta ke Baffa ne ke bashi ƙarfin guywa, cikin dare rashin lafiya ta taso ma Baffa mai tsanani hankalin Inna tashe takira Abubakar ya zo a kai Baffa asibiti amma koda suka isa rai ya yi halinsa
Washegari a'kayi zana,izar Baffa a'ka kaisa ma kwancensa tunda ga lokacin Inna ta ƙara uzzura ma Nimra zagi da hantara ba'a magana gashi cikinta ya shiga watan haihuwa yau ko gobe tun cikin dare Nimra ke nuƙuda har garin Allah ya waye amma fir Inna ta hana a'kaita asibiti waisu ai ba asibiti suka haihuba a'na haka Maryam ta zo ta tarr da Nimra kwance cikin jini idanunuta har sunfara kafewa da gude taje ta faɗama Umar yazu suka kai Nimra asibiti ko da suka isa bata masan inda kanta yake ba sai da suka sha masifa gurin likita kana suka karɓe ta suka yi mata allurai da ƙarin ruwa sai da tashi leda huɗu na ruwa kana ta farfaɗo bayan sallar juma'a na ƙuda ta koma taso mata da kyar kulata ya samu suka ceto abinda ke cikinta saboda ga kan Baby ya fara fituwa amma ƙarfinta ya ƙare idan suka barta Babayn na iya mutuwa, likita ya sa hannu ya ida fitar da Babayn sai dai a'nyi rashin sa'a sun ceto abinda ke cikinta ita kuma Allah ya karɓe kayansa
Innalillahi wa,inna ilaihi rajiun! rauwa kenan Abubakar kowa ya na kasuwa wurin niman abinda zasu ci saboda Inna ta hana mai zama wai sai ya fita dawowarsa kenan ta ce masa Maryam ta ɗauki Nimar suna asibiti ya na isa ana fituwa da Babyn da Nimra ta haifa kyakkyawa ce sosai ma'aikatan asibiti sai magana suke na kyaun da yarinyar ta ke da shi da zuwansa Umar ya miƙa masa Babyn ya ƙafe ta da ido saboda gaba ɗaya bata kama dashi da Nimra da Aunty Hawa ta ke kama bakinta ne kawai irin na Nimra sai ya tsun ƙafarta irin nasa, kiran sallah ya fara yi mata kana ya yi mata huɗu ba da Nana A'isha
yana gamwa ya miƙama Maryam ita ya shiga ɗakin da Nimra ta ke gabansa ne ya yi mummunar faɗuwa ganin a'nrufeta da farin mayafi jikinsa har rawa yake ya jane mayafin wata ƙara ya saki wadda duk wanda ya jita sai hankalinsa ya tashi zubewa ƙasa ya yi sumamme koda Umar da Likita suka shigo ko numfashi ba ya yi nan 'aka fara bashi taimako cikin ikon Allah ya farfaɗo kana a'ka basu gawar Nimra suka nufe gida banda kuka babu Abinda Maryam keyi gashi sai kiran number Aunty Hawa ta ke akashe.





PAGE 20 to 21
Number Alhaji Ahmad ta kira amma har ta katse bai ɗaya ba suna isa gida a'ka fito da gawar Nimra suka shiga da ita cikin gida duk Nimra ta rasu amma hakan bai sa Inna ta sauko da mugun halinta ba Mahaifiyar Umar ce ta yi ma Nimra wanka ta shirya ta 'aka fito da ita domin a'kaita ma kwancinta amma Inna Hajjo na ɗaki ita da ƙawarta Kanɗe sai mutanen Unguwa ne kawai a waje ankira Inna Hajjo ta zo ta ga Nimra za'a fita da ita amma fir ta ce ita ko gawar Nimra bata son gani, Abubakar kuwa ganin a'nfito da gawar Nimra ya ga da gaske Nimra ta rasu kusa ga gawar Nimra ya je ya zauna ya na jijjiga ta "haba Nimra ya zaki min haka wai da ma da gaske tafiya zakiyi kibarni Nimra karki yimin haka Please ki tashi kiga ƴar da kika haifa muna." Haka ya rinƙa sabbatu ga ba ɗaya ya fita haiyacinsa sai kuka yake kamar mace duk wanda ke wurin sai da ya zubar da hawaye saboda tausayin Abubakar gashi mutanen Unguwa sai ya bun Nimra suke ba ta da wani mugun hali ga kyauta abinta bai haɗa ta da mutane iya zaman da suka yi da ita bata taɓa ko da musayar magana da kowa ba, Umar ne ya yi ƙarfin halin zuwa kusa ga Abubakar ya na bashi haƙuri har ya tashi a'n ɗauko gawar Nimra za'a fita a'yi mata salla Abubakar ya yanke jiki ya faɗi hannunsa dafe da zuciya nan jama'a suka yi kansa amma ina rai ya yi halinsa salati jama'a suka ɗauka wasu na kuka saboda tashin hankali, Umar ne ya ke ta Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!!
"Abubakar ka tashi kata shi kar kai muna haka da wanne ƴar ku zata ji da rashin Uwa ko da rashin Uba." Haukace Inna Hajjo ta fito ta yo tsakiyar gida ganin Abubakar kwance babu a'lamar rai a'tare da shi ya sa ta fasa ƙara ta na kuka da ta na Allah ya isa Nimra ta cuce ta ta kashe ma ta ɗa haka ta yi ta ai bata Nimra wai mayya ce abinka da ƙauye wasu sun yarda wasu kuma da ke da ilimi ba su yarda jahilci ne kawai irin na Inna Hajjo, Haka Liman yazo ya shirya Abubakar a'kayi musu sallah shida matarsa a'ka kaisu gidansu na gaskiya, rauwa kenan ba a'bakin komai ta ke ba amma mun ɗauke ta da zafi Allah ya sa muyi kyakkyawan ƙarshe,


bayan a'ngama addu'ar uku satin suna ya zagayo yarinya ta ci sunan ta A'isha kowa ya kama gabansa Maryam ta so Inna Hajjo ta bar mata A'isha amma fir ta ƙi yarda gashi har lokacin bata samun wayar Aunty Hawa Alhaji Ahmad kuma ba ya ɗauka har text message ta tora masa amma bai kira ta ba dole ta haƙura lokaci ba yan lokaci ta na zuwa duba A'isha , Inna Hajjo ta kwashe kayan ɗakin Nimra gaba ɗaya ta siyar bata barma A'isha komai ba Maryam ta so ta yi magana amma Umar ya hana mata ya ce ta rabuda ita saboda kafin Nimra ta rasu tun cikin na ƙaramin ta ba Maryam wasu sarƙoƙin ta na gorl da wasu hotona da zoben da Aunty Hawa ta saka mata ta ce duk abinda ta haifa idan ya girma Maryam ta bashi saboda jikinta na bata kamar mutuwa zatayi.



Ɓangaren Alhaji Ahmad kuwa Rabi na nan sai yadda tayi da shi ta sa ya maida Usman Nigeria nan ya cigaba da karatun jami'ar Maiduguri tunda ya dawo ya ke tambayar Ummansa ina Ummie nai amma ta kasa ba shi amma shima daga baya ya dai na tambayar ta, Rabi kuwa taji ɗaukar ta kardun kadarorin Alhaji Ahmad nan ta ga ta kardun kadarorin su Nimra ita da Yayarta hankalinta ya tashi sosai ba ta zame ko ina ba sai wurin Boka nan ya tabbatar ma ta da rabin dukiyar Alhaji Ahmad ta su Nimra ce shine ta ce ma Boka ya yi duk yadda zai yi kar Nimra ta wai wayo dukiyarsu sannan ya ya ƙara rufe ma Hauwa'u baki kar ta ne mi ƴar uwarta asa ta manta da ita gaba ɗaya hak shima Usman kar ya koma tambayar ta sanan duk abinda ke faruwa gidan kar ya yi magana haka kwa a'kayi wannan shine dalilin da ya sa Usman ya bar maganar Nimra ya maida hankali wurin karatu Mahaifiyarsa kuwa babu ruwanta da shi shine ma ke shige mata har ya fara sabawa da ita wata rana suna fira yaga tayi shiru sai murza zoben hannunta ta ke ya yi ta tambayar ta me ke da munta sai dai ta ce masa ba komai, Alhaji Ahmad kuwa ya sa account ɗin Usman a Company sa da ke ƙara Birtaniya duk kuɗaɗen Company cikin account ɗin Usman zasu rinƙa shiga ba tare da Rabi ta san da haka ba,


a'na haka ne Usman ya kammala karatun sa shine 'aka turasa aikin NYSC ƙauyen Jigawa ganin Usman ya bar gari ya sa Rabi taje wurin Bokanta a'yima Usam asiri da bazai dawo gida ba har'abada koma ya manta da IYayensa ko maganar su wani ya yi masa sai ya shiga ciki wani mugun hali da zai sa ba zai iya tunawa da kowa ba, wannan shine dalilin zuwan Usman Jigawa har ya haɗu da Indo


_____________________ Dawowa labari
cikin gari Usman ya tafi da Preety ya kaita wurare daban-daban kana suka je book shop ya siya ma ta liltafin koyon karatu da rubutu kana suka dawo gida, masallaci ya wuce ita kuma ta shiga gida ta yi salla ta kuma yin wanka ta sauya kaya bai dawo ba sai bayan sallar isha ya na shigowa cikin ladabi da gaida sa ya amsa kana ya ce "Preety tashi mu shiga kitchen muyi girki ba musu ta bi bayansa suka shiga kitchen ya nuna mata yadda zata kunna gas da kashe wa haka dai ya yi ta koya ma ta abubuwa ba laifi ta na ganewa sosai taliya da kifi suka dafa da zoɓo kana suka koma farlo, banɗaki ya shiga ya yi wanka ya shirya cikin wasu ƙananun kaya farar riga da yallown wando ya taje sumar kansa ya sha fama ma ta mai sai sheƙi ta ke Wow! Masha Allah ba ƙaramin kyau kayan suka yi masa ba ya fitu sak kamar wani ɗan Indai sau zuba ƙamshi ya ke fitowa ya yi kamshin turaren sa ne ya ya shaida ma ta fitowarsa ahankali ta ɗago ta na kallonsa Masha Allah abinda ta faɗa kenan cikin ranta ashe ya fito fili,
"Preetyna ta shi kiyi wanka kizo muci abinci." "To." Kawai ta faɗa kana ta wuce ta yi wanka ta shirya wata arniyar riga ta saka iya cinya pink color hannu ɗaya keda rigar ta baje gashin kanta ta rabasa biyu wani baya wani kuma ta gaba ta sako shi ta saka jan baki pink color ta shafa kwalli ta feshe jikinta da mayukan turarukan da ya siyo ma ta,

kana ta fito kwance ya ke kan doguwar sofa ai bai san lokacin da ya tashi ba "Wow! Preetyna com on." kamar ta ji abinda ya faɗa tazo wurin sa hannuwa ya ware ma ta alamar ta shigo cikin jikinsa tafiya ta yi

ya yi hugen ɗinta sai da tsikar jikinsu ya tashi saurin sakinta ya yi ita kuma ta maƙale masa.


PAGE 22 23




_______ƙoƙarin cireta da ga jikinsa ya yi "Preety sake ni mana na gaji da tsayuwar."
"Yayana bangaji da jin ƙamahin turaren ka ba." Ajiyar zuciya ya sauke kana ya ce "haba Preety yanzu saboda ƙamshin turare baza ki bari in zauna ba.?" Sake shi tayi kana ya ja hannunta suka zauna saman sofa "Pretty je ki ɗauko liltafin da na siyo miki zamu fara darasi." Wani tsalle tayi kana cikin farin ciki ta shige bedroom ta ɗauko liltafin ta dawo,
"Yayana gasu." "To zaune kuma ki maida hankali sosai bana son inkoya miki karatu amma ki ƙi maida hankali." "Zan maida hankali sosai Yayana." "Yauwa ƙanwar Yayanta." ABCD ya fara koya mata amma ga mamakinsa sai ya ga tana karantawa har zuwa Z bai gama shan mamaki ba sai da ya zo ɓangaren 1234 suma har (100) shanye mamakinsa ya yi suka koma ɓangaren su one Letar word to Letar word duk ta harda ce raɗau akanta'



"Preetyna waye ya koya miki duk wannan.?"
cikin farin ciki ta fara gaya masa "Ai lokacin da Inna ke ɗora min tallan goro makaranta nike zuwa in laɓe bayan taga nima ina sauraron abinda ake koyawa ƴan makaranta."

"Kai masha Allah Preety yanzu abinda zan koya miki NOUN da PORONOUN

*NOUN/SUNA*
What is a Noun?
Menene Noun?

A Noun is a name of persons, animals, places or things.
A Noun is a name of anything.

A nou always begins with a Capital Letter.

Noun suna ne na mutum, dabba, wurare ko abubuwa.
Ko wane iri suna Noun ne.
Shi noun suna ne na komai fa komai. Yawanci koda yaushe ana fara rubuta noun ne da capital letter.

Examples of Noun
Misalan Noun.

Persons/Mutane

Maryam
Aisha
Zainab
Aliyu
Musa

Animals/Dabbobi

Lion/Zaki
Cat/Mage
Rat/Bera
Cow/Saniya
Goat/Akuya

Places/Wurara

Sokoto
Zaria
Lagos
Katsina
Niger
Jigawa

Things/Abubuwa
Plate/Faranti

Key/Mukulli
Car/Mota
Spoon/Cokali
Chair/Kujera
Bed/Gado


Examples of Noun in Sentence
Misalan Nouns a cikin sentence wato jimla
This is my new *Shoe*
Wannan sabon takalmi nane

I want to buy a *Goat*
Ina so na siyo *Akuya*

*Zainab* has traveled to *kano*
*Zainab* tayi tafiya zuwa *kano*

PRONOUN/WAKILIN SUNA

A pronoun is a word use instead of a noun.

A pronoun is a word that you use to refer to someone or something when you do not need to use a noun, often because the person or thing has been mentioned earlier.

A pronoun is a word that stands in for a noun, often to avoid the need to repeat the same noun over and over. Like nouns, pronouns can refer to people, things, concepts, and places.

Translations.
Fassara.

Pronoun/Wakilin suna shine amfani da kalma maimakon suna. Pronoun/wakilin suna kalma ce da kake amfani da ita don yin nuni ga wani ko wani abu lokacin da ba ka buƙatar amfani da suna, sau da yawa saboda an ambaci mutum ko abu a baya.
Pronoun/wakilin suna kalma ce da ke tsaye ga suna, sau da yawa don guje wa buƙatar maimaita suna iri ɗaya akai-akai. Kamar sunaye, pronoun/wakilin suna na iya nufin mutane, abubuwa, ra'ayoyi, da wurare.

Examples of pronoun
Misalan pronouns

I - ni
you - kai
he - shi
she - ita
we - mu
they - su
him - shi wanda Ke nesa
her - ita wadda take nesa
he - shi
she,
us - mu

Examples of pronoun in sentence
Misalan pronoun/wakilin suna a cikin jimla

*He* is our English teacher
Shi Malamin turancin mune

Did you see *her*?
Kin gan ta?

*We* are happy today.
Yau muna Farin ciki.

*I* am a nurse.
Ni nurse ce

This is *our* house
Wannan gidan mune.

*They* going to school.
Suna tafiya zuwa makaranta.

Did you tell *her*?
Kin fada mata?

haka ya yi ta koya ma ta da yake Aisha akwai ƙwaƙwalwa nan da nan da hardace;

bayan ya gama koya mata karatu ya zuba musu abinci suka ci kana ya kuna musu tv suka fara kallo har bacci ya yi awon gaba da su,


washegari bayan sun kammala duk abinda ya kamata ya ɗauketa suka fita bai zame da ita ko ina ba sai Unguwar Mabera wata makarantar hardar Al'Kur'ani ta Dahiru Usman Bauchi nan ya siya mata fom ya cika ya yi mata duk abinda ya kamata sannan ya yi ma Malaman bayani matarsa ce saboda yaga akwai maza amma ajinsu da ban nan Malaman suka shaida mai babu wata matsala akwai ajin matan aure wata ma tashiya ce Malaman suka kira mai suna Ilham Malam Yusuf ya ce ma ta ga sabuwar ɗaliba nan ta kula da ita saboda itama matar aure ce ta ce ba laifi hannun Aisha ta ja suka shiga ciki sannan Usman ya yi ma Malam Yusuf godiya ya wuce wurin aiki;

Ilham kuwa sai kula ta ke da A'isha kamar sun san juna haka rauwa ta cigaba da tafiya saboda har boko Aisha ta fara zuwa

Please Login or Register in order to submit comment