Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

radau abakin sa. dole Alhaji Ahmed yakai sa makaranta. Akwai wata makociyar su Nimra me suna Fateema tana son Nimra sosai har Nimra na shiga gidan ta kamar yadda Nimra tasaba bayan ta gama taya yayar ta aiki tayi wanka taje gidan Fatimah suyi ta fira har tana koya ma fateema yaren Turkiya tana zuwa bakin kofa suka hadu ita da Fatima zata fita kasuwa, Nimra tace zataje itama, haka fateema taja su a motarta suka nufe kasuwa.




Bayan sun isa kasuwa sun gama siyayya sun fitu riƙe da kaya zasu shiga motar su sallama suka ji a ba yan su tare suka waiga suna amsa sallamar wani mutum ne babba baza a kirasa da matashi ba saboda yadda nau'in jikinsa yake, ba laifi kaykkyawa ne bafulata ni cike da karfin gyuwa ya gaida su suka amsa kana yace "idan badamuwa ina son magana da wannan ya nuna Nimra." Fateema "ta ce badamuwa amma karka daɗi sauri muke." Godiya ya yi mata kana ya gabatar ma Nimra kansa "suna na Abubakar m Ardo ni ina zaune cikin ƙauyen jigawa ina zuwa nan ne kasuwanci fatan zaki karɓe ni.?" shiru tayi tunda ya fara magana take kallon sa yadda ya ke magana cikin kwanciyar hankali da natsuwa tsin tar kanta tayi da yi masa murmushi ta juya zata shiga mota ya biyo ta ya na fadar " baki ce komai ba." tsayawa tayi tare da saka hannu cikin jaka ta dauko katin address ɗin gidan su ta bashi tare da shegewa mota. kallon ta kawai fateema tayi ta na mamakin sa'ar da wanan mutumen ya samu wurin Nimra saboda sun sha fita tare maza da ya wa suna haukar son Nimra manyan yan kasuwa da masu kuɗi da ya'n siyasa amma babu wanda ta taɓa kulawa sai wannan da ga duk kan alama talaka ne. Tana wanan tunani ne har suka iso gida Nimra ta yi mata sallama ta shige gidansu saboda tasan Usman ya kusa da wowa makaranta. Tana shiga daken ta ta shige saboda taga motar Abban Usman tasan yayar ta na wurin sa wanka ta koma yi tare da kwanciya akan gado tana tunanin mutumen da suka hadu da shi da zu, tashi ta yi kamar wacce aka tsikar tafitu falo tana jiran Yayarta. Bata jima da zama ba Usman ya dawo daga school da gudu yazo ya rungume ta ita rungume sa tayi sosai ajikin ta kana suka sake juna Usman ne "yace Ummiena yakike.?" "lafiya lau yaron kirki fatan kayi karatu Sosai.?" daga mata kai ya yi
kana taja hannun sa suka haura sama tayi masa wanka yace abinci a' kaishi islamiyya. har ta kammala shirya Usman Yayarta bata fitu ba shima yaron beda muba saboda yafi shakuwa da Nimra fiye da Umman sa abinci ta bashi sai da ya ƙushe kana taje ta kai sa islamiyya ta dawo dawowar ta ya yi dai-dai da zawan Abubakar kofar gidan su me gadi ya hana masa shiga sallama tayi masa ya amsa kana tayi mai jagora zawa cikin gida falon baki ta aje sa kana tayi cikin gida ta kawo mai abin motsa baki juice ta kawo masa da ruwan gora masu sanyi gaisawa suka kara yi kana ya fara magana " da


farko dai na gabatar miki da kaina tom maganar gaskiya Nimra sonki nikeyi kuma auren ki nikeson yi idan ke amince amma fa ni talaka ne ba mai kuɗi ba ina dai da rufin asiri ban sa ya zaki dauke ni ba saboda nasan ke fi karfina sone kawai da baya duban yana yi da matsayi amma fa ko baki amince ba nagode da karmawar da kika yimin ba tare da ke wulaƙanta ni ba." murmushi Nimra tayi kana "tace naji baya nin ka kaba ni kwana2 in Sha'Allah zan nemeka." shiru ya yi kana ya mike zai fita tare da yimata sallama akan bayan kwana2 zai dawo, yaji shawarar da ta yanke." Ya tafiyar sa itama ta kuma cikin gida falo ta tarr da Yayar ta zaune tana karatun Alƙur'ani wuri ta samu kusa da Yayarta ta zauna ta na jiran ta kammala karatun suyi magana.


ɓangaren Abubakar kuma cike da fargaba ya koma ma saukin sa anya Nimra zata yarda ta aure sa,? da wannan tunani ya ida wuni har dare


Nimra kuwa ba yan Yayarta ta kammala karatu mai do hankalin ta tayi gun ƙanwar ta tace"Ummien Usman lafiya dai.?" "na ganki cikin farinciki me ke faruwa.?" Nimra tace" Aunty wani ba wan Allah ne na hadu da shi da muka fita kasuwa nida Fateema ya na da hankali sosai wallahi, kuma ya kwanta min a rai nan dai ta kwa she duk yadda suka yi ta gaya mata kana ta dura da cewa har ya zo dazun kina tare da Abban Usman shi yasa ban kira ki ba, amma nace masa bayan 2days ya dawo zan fada masa shawarar da na yanke."


shiru hauwa'u tayi chan dai tace "yanzu dai zan gaya ma Abban Usman idan ya dawo a fara yin cikakken bincike a kan sa kafin alaƙar ku tayi nisa." "badamuwa Aunty."

fira suka shiga yi sosai kafin akira sallar mag riba ko wanensu ya tafi wurin sallah.


PAGE 1️⃣4️⃣


________Bayan Nimra ta idar da salla ta kira yar ai kin su mai suna Maryam ya rinyar tana da hankali da natsuwa ba laifi suna shiri da Nimra sosai idan kaga suna wasa bazaka taɓa cewa ya'r aiki ce ba, Nimra ta shaƙu da Maryam sosai kamar ya'n uwa komai tare suke yi bacci ne kawai ke raba su,
bayan Abban Usman ya dawo Hauwa'u ke bashi labarin a'binda Nimra ta gaya mata ya ce" tu shikenan zai sa ayi masa bin cike kafin Abubakar ɗin ya dawo in'sha Allah".
Haka kuwa akayi ya saka an yi masa bincike sosai a kan Abubakar anan ya samu cikakken bayani game da shi, Mahaifin Abubakar Malam Ardo bafulata ni ne da a' TARABA suke zaune daga baya suka dawo garin JIGAWA, tare da matarsa Inna Hajjo sai d'an su guda Abubakar lokacin baifi 6years ba suna nan zaune da yake malam Ardo ya na da wayewa ya saka Abubakar makarantar Firamare har zuwa Sakandire, lakacin girma yafara taso ma Abubakar shine malam ardo ya fara fita da shi kasuwar cikin gari in da ya ke sana'ar sayar da shadda da ya duka da takalma, ba laifi Abubakar na tai maka ma Mahaifinsa sosai ahankali har Malam Ardo ya bar ma Abubakar ragamar kasuwanci ya dawo ya koma har kar noma da kiyo da Abubakar ya so cigaba da karatu amma ganin Mahaifinsa na bukatar sa akusa dole ya hakura haka rauwa ke tafiya har Abubakar ya hadu da wani mata shi kamar sa mai suna Umar shima
cikin ƙauyen Gagarawa yake da ke cikin garin JIGAWA suna mutunce sosai har suka zama abokai har iyayensu sun san da alakar su Umar ya fi Abubakar gogewa a harkar kasuwanci ya fi shi zurfin ilimin boko saboda har NCE ya na da aiki ne bai samu ba, kamar kulum suna zaune suna fira Umar ke cema Abubakar dan uwa"Ya kamata murinka fita garu ruwa muna saro kaya fa." Abubakar ya ce" gaskiya fa ka kawo shawara zan fada ma baffa duk abinda ya ce zan ga ya ma."
Umar yace" shikenan sai na jika." bayan Abubakar ya koma gida suna zaune shida baffansa da Inna Hajjo ya ke shaida ma baffansa yadda suka yi da Umar baffa"ya ce badamuwa ai in dai ana samun cigaba ba matsala Allah ya taimaka yan zu yau she zaku tafi ne.?" "Da yake bamu yanke shawarar in da zamu fara tafiya ba sai na ga ya ma idan ka amince kai da Inna." baffa ya ce"Hajjo keji abinda Garba ya fada ko.?" "Eh naji Allah ya bada Sa'a ya tsare." Amin."baffa ya ce kana ya jiyo gun Abubakar yace" kaje ka gaya masa na amince sai afara shirin tafiya amma fa ba yan kadawo aure zaka yi saboda shekaru sun fara ja." cikin jin kunya Abubakar "yace in Sha' Allah baffa." Inna Hajjo ta ce" wanda ko mata ba ya kulawa ta ya za'ayi maganar aure, dama ina so ahada shi aure da ya'r gidan ƙawata kande."
baffa ya "ce ba ruwana idan ya na sonta ba matsala."
Tashi Abubakar ya yi ya fice daga cikin gidan bai tsaya ko ina ba sai gidan su Umar ya shaida masa cewa baffa ya amince Umar yaji daɗi sosai yace"gobe zamu fara shirin tafiya jibi zamu wuce." Abubakar ya "ce ina zamu fara.?" Umar ya "ce BARNO zamu fara tafiya ko ya kace.?" "ba laifi Umar Allah ya kaimu lafiya." Umar ya ce"Amin." suka yi sallama Abubakar ya dawo gida,

ranar tafiya ta zo bayan sun kammala shirin tafiya suka yi sallama da iyayensu har tasha baffa ya raka su ya na yi musu addu'a,
kana motar su ta kama hanyar BARNO sun isa lafiya kwanan su daya suka fara shiga kasuwa suna sarin kayan da zasu tafi dasu suna cikin kasuwar ne Abubakar ya hango Nimra tunda ya ke baj taɓa kula mace ba sai Nimra kushi sai da Umar ya bashi ƙarfin gyuwa kana ya je gurinta
Wannan shine asalin Abubakar Alhaji Ahmad ya shaida ma matar sa komai game da Abubakar kuma tayi farinciki sosai ta san inda yar Uwar ta zata zauna.

PAGE 15


Bayan sallar magrib hauwa'u ta haura sama ɗakin ƴar uwarta da sallama ta shiga

kwance ta same ta kan bed amsa sallamar tayi tare da tashi zaune ta na fadin "Auntyna."
"na'am ummien Usman magana nazo muyi." "to ina jinki Aunty." "dama akan Abubakar ne Abban Usman ya sa anyi masa bincike sosai a'kan sa Alhamdulillah bashi da wata matsala ko mugun hali yanzu sai ki kirasa ki gaya masa Abban Usman na son ganin sa." "Aunty bani da number sa sai dai gobe idan ya zo zan ga ya masa". "to ba laifi Allah ya kaimu gobe lafiya." Nimra ta ce"Amin." nan dai suka cigaba da fira kafin Maryam ta shigo ta bar musu ɗakin ta koma ɗakinta Maryam ta ce "Aunty Nimra ya akayi ne Abban Usman ya amince.?" "Eh ya amince har an gama bincike akan sa." "Masha' Allah gaskiya naji daɗi Aunty Nimra zakiyi aure Allah ya sanya alkhairi." "Amin Maryam nagode sosai amma fa zanyi kewarku keda yarona."
Maryam tace "ai ƙafar ki ƙafata bazan iya bari kitafi kibar mu ba biyar ki zamu yi." dariya ce ta kama Nimra sai da tayi mau isar ta kana tace"yan zu Maryam zaki iya biyata mu zauna tare.?" tace"sosai ko saboda jinki nike kamar jinina.
Nimra tace "fatana Allah ya baki miji kema kiyi aure Maryam." "Aunty Nimra wa zai aure ni ba uwa ba uba bani da kowa sai kakata, kega ba zaiyu in samu miji ba." ta karshe maganar cike da damuwa dafa kafa darta Nimra tayi kana tace "haba Maryam bawa baya taɓa yanke ƙwauna a' wurin Ubangiji saboda haka ke cigaba da addu'a in sha 'Allah zakiyi aure maybe ma ki riga ni aure ."
"Aunty Nimra kenan in Sha'Allah zan cigaba da addu'a nagode sosai."

fira suka shiga yi ita da maryam har bacci ya dauke Nimra kana Maryam tayi gidansu da ke ba yan layi.


Washe gari yau ne Abubakar zai dawo wurin Nimra ya ji Shawarar da ta yanke ƙarfe hudu ba yan an gama salla ya ce ma Umar ya shirya ya raka sa gidan su Nimra
ɓangaren Nimra kuwa da kanta ta shiga kitchen ta haɗa masa girki da lemon juice kana taje tayi wanka ta shirya cikin wane arnen leshe pink color dikin duguwar riga ce irin me baje war nan ƙasa rigar ta karɓe jikinta matuƙa ta kafa daurin kallabi msi kamar gwargwaro wani karamin maya fi ta ɗura a'kan kafaɗar ta fari sai takalma plete suma farare sai sarƙar azurfa da ta saka da agogo wow!! masha 'Allah ko makiyin ta ya kalle ta ya san ta hadu tayi kyau sosai abin ba'a magana, sai da ta feshe jikinta da turaruka masu mayen kamshi kana ta sauko falon ƙasa sau kowar ta kenan Maryam na shigowa tana faɗin "Aunty Nimra ai kasa ƙarasawa tayi saboda kyaun da taga Nirma ta yi kamar aljana, Nimra tace "ya a'kayi ne Maryam.?" sai lokacin tadawo haiyacinta "dama Yaya Abubakar ne ya zo shida Abokin sa na kai su falon baƙi. "Ok kishiga kitchen ki dauko kayan da na haɗa masa ki kaimu su ina zuwa." "tom tace kana ta wuce

ita kuma Nirma ɗakin Aunty Hauwa tashi ga tare da sallama amsawa tayi tana faɗin "ummien Usman ina zuwa haka masha 'Allah kamar wacce zata je gasar kyau.?" dariya Nimra tayi kana "tace Auntyna Abubakar ne ya zo shida Abokin sa, zanje muyi magana ki faɗa ma Abban Usman ya zo." "ok idan na kammala saka kaya zan je in gaya masa." "ok."


kana ta fice daga ɗakin ta nufe falon baƙi da sallama ta shiga kana ta zauna suka gai sa da Umar shikuma Abubakar ya sake baki sai kallon Nimra ya ke ko keftawa baya yi gyaran muyar da Umar ya yi ne ya dawo da shi haiyacinsa ya ce"Abubakar ka faɗa ma Madam tayi min jagora wurin ƙanwarta.
dariya Abubakar ya yi kana ya ce "ba gata nan ba kafaɗa mata da bakin ka ai yafi sauƙ.

Nimra tace "wai akan wa yake magana.?" Umar yace"akan ƙanwarki da ta kawo muna kayan abinci."

Nimra tace"ok wai Maryam kake nufi.?" Umar yace"ita wallahi yarinyar ta burgeni sosai shine nace ko zaki bani auren ta.?" Nimra tace"me zai hana idan kayi mata, bara na kira ma ita." fita tayi cikin farinciki tana fatar Allah yasa Maryam ta yarda da Umar ko ba komai Umar ya nada kirki sosai ba laifi kaykkyawa ne, kitchen ta same ta tsaye Nimra tace"Maryam jike shirya kizo keyi baƙo ya na falon baƙi. haba Aunty Nimra kima kefara zolaya ta ko? "ke Maryam na taɓa yimiki irin wannan wasa ne.?" ta gir giza kai "tom maza kije ki duba cikin kayana akwai wata jar atamfa da farin mayafi da takalma kisaka kidu ba cikin sarƙo ƙina akwai wata farar sarƙa da ya'n kunne kisaka kizo ya na jiran ki." ta juya tayi tafiyarta ta bar Maryam cike da ma maki waye yazo wurin ta, sanin halin Nimra zata iya dawowa ya sa taje ta shirya kamar yadda ta umarce ta ba laifi atamfar tayi mata kyau sosai saboda Maryam farace sosai tana da kyau dai- dai nata falon baƙi ta shiga gabanta sai dukan uku -uku ya ke sallama tayi kana ta shiga Umar ne ya amsa sallamar saboda Alhaji Ahmad ya kira Nimra ita da Abubakar suna falonsa suna magana
gai da Umar ta sake yi kana ta nemi guri ta zauna Umar ne ya yi gyaran muyar kana ya gabatar mata da kansa da kuma abinda ya ke nema agurinta idan ta amince ya na son azo nema masa auren ta tare da na Abubakar
sai da Umar ya kammala magana kana "tace zatayi shawara da Aunty Nimra." dariya ya yi kana ya ce" ai Nimra tace tabani ke, sai dai idan kece ba kya sona." gir giza masa kai tayi kana "tace ba haka bane kawai zanyi shawara da ita." Umar ya ce"to ba damuwa Allah yasa naji alkhairi." ta ce "Amin."

ɓangaren Nimra kuwa da Abubakar sun gama magana da Alhaji Ahmad a'n tsai da magana akan ya turo maga batan sa asa rana nan ya yi ma Alhaji Ahmad godiya kana yaje suka gaisa da Aunty Hauwa kana suka koma falon baƙi suyi sallama saboda gobe zasu koma JIGAWA nan sukayi musayar number ita da Abubakar shima Umar haka sukayi da Maryam kana suka yi ma juna sallama suka tafi ceki da kewar juna kamar sun daɗe tare



PAGE 1️⃣6️⃣⏩1️⃣7️⃣


Bayan su Abubakar sun wuce Nimra ke tambayar Maryam "wai ya kuka yi keda Umar.?" nan Maryam ta sanar mata duk yadda sukayi
sauke nunfashi Nimra tayi kana tace"tom ke Maryam kina son shi ne ko ya ya.?" "Ina son shi amma ya zanyi da kaka.?" Nimra tace"ai kaka ba matsala bace gidan nan zata dawo da zama kega baza'abar Aunty ita kadai ba.?"
Sai lokacin Maryam ta sauke ajiyar zuciya tace"tom shikenan Aunty Nimra nagode sosai Allah ya jiƙan magabata." "Ameeen anjima idan ya kira ki sai ki gaya masa ke amince.?" tace"tom in'sha Allah Aunty Nimra."
Kana ta fitu ta shige kitchen ta dura girki ita kuma Nimra kwanciya tayi Usman ne ya shigo da gudu ya fada jikin ta yana fadin "Ummiena am back." murmushi ta sakar mai kana ta shafa sumar kansa da ta kwanta kamar balarabe tana jin ƙaunar yaron na ratsa ta sosai tashi zaune tayi kana tace "habibi fatan kayi karatu sosai.?" daga mata kai ya yi kana tace tom" jeka kayi wanka kaci abinci bayan sallar magrib kazo muyi karatu." "tom Ummiena bye." ya fice daga dakin ya nufe dakin sa
bayan sallar magrib ya zo ta koya masa karatu kamar yadda suka saba ba laifi yana da ƙuƙari sosai shike na daya a school ɗin su ta boko da islamiyya gashi ɗan shekara 7 haka zakaji yana zuba larabci kamar balaraben asali, bayan sun kammala ne ya ce "Ummiena wai aure zakiyi kibar ni.?" gir giza masa kai tayi kana ta ce" ai bazan tafi na bar kaba my son da kai zan tafi." murmushi ya yi kana ya ce" da gaske Ummiena.?" "sosai ko yarona lokacin sallar isha ya yi Abbanka na jiranka kufita masjid." ya ce"tom Ummiena bye." "bye my love."
washegari Abubakar ya kira ta ya shaida mata sun kama hanya komawa gida tayi masa addu'a sosai kana sukayi sallama akan insun isa zai kirata.

Basu isa ba sai bayan sallar la'asar bayan sun isa kasuwa suka wace da kayan su saboda iyayensu na cikin kasuwar suna isa kowa ya yi ɓangaren sha gonsu zaune Abubakar ya tarar da baffa bayan ya gaida baffa nan suka shiga fira sosai ya na ba baffa labarin yadda kasuwar garin take wayar sa ce tafara ƙara ya na ɗauko wa yaga sunan Nimra gabadaya ya manta da ya ce zai kirata idan sun isa, kasa ɗagawa ya yi saboda kunyar baffa yake ji gashi bai masan ya fara kula mace ba, wani kiran ne ya koma shigowa har ya kusa tsinkewa kana ya ɗaga sallama tayi masa cikin zazzakar muryarta mai daɗin sauraro kasa amsawa ya yi saboda ganin yadda baffa ya kafe sa da ido ganin yadda duk ya diriri ce baffa ya fice daga shigon ya barsa.

ita kuma Nimra jin shiru ya sa ta katse kiran ganin baffa ya fita ya sa Abubakar kiran ta da sauri ta ɗaga saboda hankalinta bai kwanta ba ganin har karfe5 bai kirata ba shiyasa takira sa,
sallama ya yi mata ta amsa kana tace "najika shiru ne hankalina bai kwanta ba shiyasa na kira ka fatan kun sauka gida lafiya.?" ajiyar zuciya ya sauke kana ya ce "lafiya lau Alhmdulillah fatan kuna cikin ƙushin lafiya.?" "lafiya ƙalau ya su baffa fatan kasa me su lafiya.?" "Alhamdulilh Nimra ina kasuwa tare da baffa idan na koma gida zan kira ki." "Nimra tace"Allah ya kaimu ka gaida su baffa." yace "in Sha'Allah bye."
Bayan sun kammala wayar ya fitu wajen shagon zaune ya tarar da baffa guri ya nema ya zauna baffa ya ce masa "Garba ka hada kayan shago mu tafi gida yamma tayi." "tom baffa." tashi ya yi
ya fara hada kayan dake wajen shagon ya na sakawa ciki yana kammala wa Abubakar ya ja su akan babur ɗin baffa suka nufe gida ba yan sun isa inna ta tarbe su tana fadin "a'a mutan BARNO saukar yau she.?" dariya Abubakar ya yi kana yace "bayan sallar la'asar inna kasuwa na sauka wurin baffa na'aje kayan da muka saro." "tom Masha Allah Allah ya yi albarka." ya ce "ameen." abinci ta kawo musu da fura saboda baffa tare da Abubakar yake cin abinci, bayyan sun kammala cin abinci suka nufe masallaci bayan sun dawo wurin sallah suna zaune suna fira kamar yadda suka saba gyaran muraya Abubakar ya yi kana ya ce "baffa magana nikeso muyi," baffan ya ce "tom Ina jinka habu." kana "ya ce dama da muka je BARNO ne na hadu da wata yarinya nan dai ya gayama baffa komai a'kan Nimra har binciken da Alhaji Ahmad ya sa akayi a'kan sa bayan ya gama yima baffa bayani ya yi shiru don tunda ya fara magana inna keson tsoma bakin ta baffa ya hanata, gyara zama baffa ya yi sosai kana ya ce "naji bayanin ka habu nima zan tura ƴan uwana suyi bincike a'kan ta insha'Allah kana aje a nemar ma auren ta kamar yadda mijin yayar ta ya bukata." inna tace "ina da magana indai ni na haife Abubakar ban yarda ya aure ƴa'r kowa ba se ƴar ƙawata kande." baffa"ya ce wallahi hajjo idan kika koma magana ke san abinda zai biyo baya, yarinyar da ya ke so ita zai aura bazan yi masa auren dole ba kamar yadda aka hada nu dake banda masifa da rashin kunya babu abinda kika iya hakuri kawai nike dake, saboda haka ki kama kanki kesan halina idan na juyo kanki abin bazai miki kyau ba." "Abubakar tashi katafi Allah ya yima albarka sai na nemeka, karka damu da maganar mahaifiyarka." "nagode baffa sai da safe inna sai da safe." Akufule ta ce "idan ubanka ke da gobe kace kar inga safiya." tashige ɗaki baffa ya gir-giza kai kana ya ce "habu tafiyar ka Allah ya bamu alkhairi." "Amin." ya fice ya nufe gidan da baffa ya gina masa anan ya ke kwana shida Umar.
__________Yana shiga cikin gidan kwantawa ya yi tare da ɗauko wayarsa ya kira Nimra bugu ɗaya ta ɗaga tare da yin sallama amsawa ya yi suka gaisa, kana suka shiga firar soyayya nan ya ke shaida mata ya yi magana da baffansa kuma ya amince idan ya gama shawara da ƴan uwansa zai turo anemar masa aurenta, sosai Nimra taji daɗin labarin fira suka cigaba da yi sai da Umar ya shigo kana suka yi sallama. Umar ya ce" Abubakar wai kuka yi da baffa a'kan aurenka da Nimra.?" "Ai baffa ya amince sai dai Inna ta ce bata yarda ba wai ƴar gidan ƙawarta kande ta ke so na aura." Umar ya ce "Ya salam yanzu Inna ta rasa yarinyar da zata haɗaka sai wannan mara kunya, ga rashin tarbiya tu me baffa ya ce.?" Abubakar ya ce" ai kasan halin baffa bazai yarda ba ya ce duk yarinyar da nikeso ita zan aura indai tanada tarbiyya da ilimin addini da hankali." Dariya Umar ya yi kana ya ce "ai da sauƙin tunda baffa ya baka goyon baya Ubangiji Allah ya shige muna gaba." "Amin Umar kaifa.?" "Ai kasan Mahaifina bashida matsala ya amince, ya ce zai je ya samu baffanka a tsaida lokacin da zasu je ane marmuna aure.?" "Kai masha 'Allah Abubakar ya fada kana ya ce" Allah ya tabbatar muna da alkhairi."-------------------------------
Baffa ya sa anyi masa bincike sosai Alhmdllah komai sai masha 'Allah, yau ta kama Assabr zasuje Barno nemawa ƴaƴansu
aure Alhmdllah sun isa lafiya an tarbe su hannu biyu kana suka gabatar da abinda ya kawo su, Alhaji Ahmad ya yaba da halayensu baffa, an bama Abubakar auren Nimra a'kan sadaki dubu100 shima Umar an bashi auren Maryam a'kan sadaki dubu500, an tsaida ranar aure nan da wata2 masu zuwa.
Kana su baffa suka dawo gida cike da farinciki, babu kalar zagin da Inna batayi
ma Abubakar ba ko gaisuwar sa bata amsawa, ɓangaren su Nimra kowa shirye

Please Login or Register in order to submit comment