Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kwashe dukan abinda ya faru yafadama Dr afirgice Dr yaja baya yana girgizar kai yama kasa furta ko mai saida yanisa"yace yanzu man wannan yarinyar tazma matar ka? meyasa baka kirani ba wallahi da bazan yarda adaura ma aure da itaba yarinyar da yanzu ma take ƙirgan dangi mezaka yi da ita gaskiya sakinta kawai zakayi tunda ai da bakin ta tayi musu bayanin duk abinda yafaru kaga shikenan kahuta don idan kako ma gida mezaka fadama iyayen ka? shiru Usman yayi saboda maganar da Dr yake fada sama sama yake jinta don har zazzaɓi yake ji ajikinsa ƙarfin haline kawai na maza sallama akayi tare da turo kafar ma'aikaciyar nan ce tashigo tanace "ma Dr tayima Indo duk abinda yakamata yanzu haka ma bacci take bata farka ba

da hannu Dr yayi mata alamar ta tafi kawai tajuya tafita Dr yakalli Usman yace "man bakace komai ba yaza'ayi da yarinyar? dagowa Usman yayi ahankali yakalli Dr yace "ina sonta bazan iya rabuwa da itaba duk abinda zaifaru bazan taba bari wani abu yasame ta ba
da sauri Dr yakalli Usman yace"kana sonta fakace? wai man kanka daya kuwa mekagani ajikin yarinyar dazaka like mata?, daga masa hannu Usman yayi yace" koma dai yayi ne yanzu she is my wife karka koma ce mata yarinya don rainonta zanyi kuma ina sha Allah gobe zan bar ƙauyen nan saboda nasamu aiki garin
SOKOTO baki sake Dr ke kallon Usman don yanzu lamarin Usman tsoro yake basa shikuma Usman tashi yayi yakoma dakin danike inata bacci kusa dani yazauna yana shafa fuskata wani abu yake ji natsir garmasa har tskiyar kansa sai lokacin yakare min kallo banida tsayi sosai amma ƙirjina yataso alamar nafara ƙiragan dangi duk da kananen shekaru na amma inada babban kugu da shaf irin na manyan mata masha Allah komai najikina dai dai kamar ni natsara ma kaina gani kyakkyawa ajeni farko duk da ina cikin wahala amma besa narage kyau ba gafatar jikina da laushi kamar auduga sai sheki take ta kwanta tayi wane yalow kamar yar masu kuɗi ajiyar zuciya yasauke tare da kwanciya kusa dani yanata sake sake aransa har bacci yadauke sa bamu farka ba saida aka kira sallar asuba tashi mukayi ina kallon sa nace"yayana wai an daura muna aure ko mafarki nikeyi? cikeda damuwa yace "ko bakya sona ne preety? dasauri nagirgi za masa kai alamar a'a
murmushi yasakar min tare da miƙewa tsaye yashige ban daki sai lokacin nakula da bandejin dake daure akafata komawa nayi na kwanta don Baccin be ishe niba sabo da tashi ne lokacin salla shiyasa nafarka ko da yafitu nakoma bacci fita yayi masallacin dake cikin asibitin yayi salla bedawo ba saida gari yayi haske
yana shigowa ina farkawa daga bacci ahankali yatako har inda nike nayi sauri nace "brk da safiya yayana murmushi yasakar min tare da dura hannun sa akan fuskata yana cewa" lafiya lau esha yajikin naki? "dasauki nace zama yayi kusa dani yace" tashi ki wanke bakin ki muje gidan Inna kidauko kayanki SOKOTO zamu wuce yanzu ban s𝒐𝒏 𝒎𝒖 𝒎𝒂𝒌𝒂𝒓𝒂


PAGE 9
Idanu nazaro nace" SOKOTO fakace Yayana.?" daga min kai ya yi batare da yace komai ba, inason tambayar sa me zamuyi a' SOKOTO amma nakasa saboda Ya yi min kwarjini sosai bazan iya tambayar sa ba. haka nashiga banɗaki na wanke bakina da fuskanta nafitu ban tarar da shi a'dakin ba kamar bazan fita ba haka dai nadauki hijab ɗina nasaka nafitu waje inda nike tsamma nin ganin sa
ina fita nahango sa tsaye wurin motarsa ya harde hannayen sa a kirji ya lumshe idanunsa kamar me jin bacci karasa wa nayi wurin sa cikiy natsuwa nace "Yayana" ahankali yabude kyawawan idanunsa akan fuskata bece komai ba ya bude min gaban motar nashiga shima ya zauna gaban motar ya tada mukafara tafiya har muka iso gidan Inna babu wanda ya yima dan uwansa magana, ganin mun iso kofar gidan amma beyimin magana ba gashi ina tsoron masifar da zan tarar idan nashiga cikin gidan.

Ahankali ya bude motar ya fito ya zagayo ya bude min cikeda tsoro nafitu jikina har rawa yake nashige cikin gidan da sallama jikina sai faman bari yake ba'a amsa sallamar ba jikina ya kara yin sanyi haka nadaure nanufi kofar dikin inna tare da koma yin sallama ina daga kafa zan shiga dakin bazato batsam mani naji an bankado ni saida nafadi bakina ya fashi dajini, nafasa ihu ina daga kaina ina kallon Inna data karasa fituwa daga dakin tana fadin" wallahi INDO kadan kika gani karuwar banza maza kifita kibar min gida kafin natara miki jama'a banza ya'r iska." ai da sauri nakwasa aguje ina ɗingisa ƙafata dake ciyo karo mukayi da Yaya Usman yarike min hannu ya fara jana zai mayar dani cikin gidan ina turjewa saiga Inna ashe tabiyo bayana tana fadar "au ashe tare kuke iskancin naku har yakai kubiyo ni cikin gida tu wallahi duka zansa yaran unguwar nan suyimuku."
cikeda bacin rai Usman yace mata "ya isa haka bawani abu yakawo mu ba kayanta tazo dauka saboda zamubar garin nan yau." wata uwar guda inna tayi kana tace" yuni ina ruwana aini nayafe INDO har abada duk inda zakuje kutafi kaya kuma bata dasu maza kubar min gida."

har Yaya Usman yaja hannu na mun fita natuno da hoton da qanwar mama na maryam ta taɓa bani cikin wata karamar jaka bantaba buɗiwa ba, ai da gudu nayi cikin dakin inna na dauko ƙunshi kayana nafitu da gudu nayo waje gaba daya sai inda motar Usman take na tsaya, ina faman haki shima bayana yabiyo itama Inna ta biyo mu tana faman zagi da cin mutunci Usman be kulata ba mukashi ga mota muka kama hanyar barin garin. tafiya muke ahanya sai faman kalle-kalle nike tunda na taso cikin ƙauyen Gagarawa ban taɓa fita ko tashar ƙauyen ba iya kata cikin ƙauyen ban san dalili ba haka kawai na tsinci kaina cikin farin ciki, tafiya muke mai nisan gaske tun safe har rana tayi dana gaji da zama nayi kwanciya ta har bacci ya dauke ni. ɓangaren Usman kuwa hankalin sa naga tukin dayakeyi be tsaya ko ina ba sai ZAMFARA, lokacin an fara kiran sallar azahar gidan mai ya tsaya ya yi Salla ya siyo min abinci ya tashe ni naci abinci nasha ruwa muka cigaba da tafiya harmuka iso garin SOKOTO. i
lokacin da muka iso birnin SOKOTO ina falke banyi bacci ba nabaza idanu sai kallon abubuwan burgewa nike da manyan gidaje da makarantu zamani gwanin burgewa,

Usman betsaya ko'ina ba sai unguwar mana

inda tun kafin muzo ya turama wani


abokin sa kude ya siya mai karamin gida mai kyau da kayan da ake bukata, ba laifi unguwar nada kyau ta tsaru sosai dai dai wani madai daicin gida ya tsai da motar ya fito yazo yabude min nafitu sai lokacin ya yi min magana tun da muka baru ƙauyen bekula ni ba sai yanzu yace "dauko kayanki mushiga ciki." ya karasa maganar yana buɗe kofar gidan
ƙunshi kayana nadau ko nabi bayansa muka shiga cikin gidan Masha Allah gidan madai daici ne me shegen kyau daki uku ne agidan setroom da bedroom sai kuma wani bed room atsakiyar gida da banɗaki da wurin dafa abinci balaifi komai nagidan ya yi min kyau komai ansaka falo muka shiga na zauna shikuma ya shige banɗakin dake cikin bedroom ya yi alwala saboda lakacin sallan la'asar ya yi har yafitu ya tada salla ina nan inda ya bar ni zaune ina kallon falon yaji kujeru da kayan kallo da sauran kayan kawata falo.

yana idar da sallan ya jiyu yace "preety na tashi kije kiyi wanka kizo muci abinci." shiru nayi saida ya koma yimin magana san nan natashi ina raba idanu, miƙewa ya yi yaja hannu na har banɗaki ya nuna min yadda ake amfani da komai sannan yafitu yabar ni wankan sabulu nafara yi kana nayi na tsalki saboda naga jinin ya dauke nayo alwala nafitu zan dauke ƙunshi kayana insaka yana kwance saman 3setar yana waya na duka ina bude kayana duk tsumokara ne narasa wanne zan saka ashe Usman na kule dani be cemin komai ba yafita da makulan motarsa befi minti30 ba ya dawo dawata ƙatuwar leda ya a'jemin ya koma ya kwanta bude ladar nayi saboda nasan haka yake nufi ba magana zashi yimin ba, kayane ya'n kanti riga da siket da dogayen riguna sai riga da wando harda su pant da best duk kayan guntaye yene, babu me kai min guiwa sai abaya guda uku dogaye har kasa.
bakaramin daɗi naji ba ganin ya wan kayan duk nawa ne bakina yaki rufuwa najiyu na kalli Yaya Usman nace"nagode Yayana Allah ya kara budi na alkhairi." shiru ya yi yana kallon yadda nabata fuskata kamar zanyi kuka tom"sarkin kuka naji jeki kisa kayanki kiyi kwalliya kizo inyimiki photo." Murmushi nayi masa nadauke ledar kayan nashige bedroom salla nafara yi kana nashafa mai da pink din Jan baki da kwalli nasaka wasu riga da wando don sunfi tafiya dani cikin kayan wandon iya cinya baki sai riga pink iya kirjina nasaka mataji na gyara gashin kai na dana wanke nashafa masa mai ya sauko har gadon bayana nadauko wasu takalma bakake masu tsini nasaka, na fesa turare naje gaban madubi ina kallon kaina kamar wata aljana ni kaina na san nayi kyau
Yaya Usman yajini shiru kusan minti 20 ya tashi ya shigo dakin tsayawa ya yi bakin kofa yana kallo na nayi masa masifar kyau kamar asace ni agudu waya ya dauko yafara daukata video da hotuna
ni kuma ban masan ya nayi ba. nasha afa da kallon kaina ta madubi takowa ya yi har inda nike ya ka ma gashin kaina atsorace najuyo daniyar zan gudu.



❤️SO ❤

Love and romantic story

💋writes by pinky darling 💋

________________________________________________________________

https://whatsapp.com/channel/0029VaaRQxx65yDGceKYTI0r
________________________________________________________________________________________
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Bismillahi Rahamanin
Raheem 💫

PAGE 10

Rike ni ya yi ganin yadda na tsorata ni kuma da sauri na saka tafukan hannaye na na rufe fuskata, naji kunya yadda Yaya Usman ya tarar dani saboda rigar ta lafe ajikina har shatin breast ɗina ya fito, yana ta ƙoƙarin janye min hannu amma naki yarda.

Sakemin hannu ya yi ban ankara ba na ji ya ɗauke ni
chak kamar wata yar tsana bedire ni ko'ina ba sai kan kujerar palo, iduna na rufe na kasa buɗe wa saboda kunyarsa data dirar min gurfanawa ya yi gabana ya kamo hannaye na.

"preety kunayar mece haka,? shiru nayi saboda yatsunsa da ya saka yana wasa da tafin hannuna, wani abu nike ji yana yimin yawo cikin jiki tsikar jikina sai tashi take, ganin yanayin da na shiga yasa ya skar min hannu yaje ya dauko ledar abincin da ya siyo muna tare da filet da cokali. Kusa dani ya dawo ya zauna kasan kafet ɗin da ke shinfid'e a falon. Ya bude abincin ya zuba akan filat shinkafa ce da miya da kayan lambu da naman kaza, da lemon juice na kwali da ruwan gora, sai da ya gama hada komai kana ya ce "preety zo muci abinci" Ahankali na sauko na zauna kusa dashi ina faman kare jikina da hannu, shi kuma Usman ta gefen ido yake kallon duk abinda nike yi be kula ni ba ya fara cin abincinsa hankali sa kwance ganin banida niyar cin abincin yasa dakan sa yafara bani abaki nan ma nak'ici "Uhmm preety ko kici abincin nan ko nayi miki dure."kallon sa nayi ganin babu alamar wasa a fuskarsa dole na saka hannu na fara cin abinci a takure saboda ban saba cin abinci tare da kowaba.

Bawani abincin kirki ya ci ba ya tashi ya shige bedroom sai a'lokacin na samu damar sakin jiki naci abinci sosai nasha ruwa na tattara kayan wuri ɗaya nakai su kitchen. Nadawo na shiga bedroom da niyar chanza kayan dake jikina ban ganshi akan bed ba motsin ruwa naji a bathroom wanka yake da sauri nafara tubewa kafin ya fitu ya ganni riga nafara cirewa ina kukarin cire wando naji ya tura kofar banɗaki ya fitu ya daure kugunsa da tawul dayan hanunsa kuma rike da wani ya na guge gashin kansa. Kamar na fasa ihu haka naji yau wane irin abin kunya ne na aikata
Usman ko turus yaja ya tsaya kamar wani sakago yana kallon yadda kirjina ya ciko ya yi kyau yama kasa karasowa tsakiyar d'akin ni kuma sai lokacin na samu naja bargon dake kan gado na rufe jikina cike da kunya. Ganin da Usman yayi min haka bariga bangaren Usman kuwa wani feeling ne ya dirar masa dabe taɓa jiba duk daya san mutum ne shi me karfen sha'awa amma betaba jin irin ta yauba, juyawa ya yi ya koma banɗaki. Dafe da mararsa dake masa ciyo idan da sabo ya saba da ciyon mara saidai ya sha magani kawai saboda gujema aikata zina.

ganin ya kuma banɗaki dasauri na dauko abayar da yasiyo min na saka tare da mayafin ta na fice daga d'akin naje falo na kwanta tare da rufe idanuna ina tunanin abinda ya faru yanzu har bacci ya dauke ni.

Usman na komawa banɗaki ruwa ya kuma sakar ma kansa shidai iya ruyuwar da ya yi har kasar waje yaga mata kala-kala har masu kawo masa kansu amma be taɓa jin sha'awar su ba sai preety gata karamar yarinya da yanzu take girma gashi yana bukatar mace amma bazai iya kusantar taba. Saboda ganin yake tayi mai k'an k'anta wata zuciyar kece masa kayi romantic dinta ko zaka rage zafi wata zuciyar tace girman ka zai faɗi awurin ta haka dai ya yita sake sake har ya ya fito ya shirya cikin jallabiya baka da hula tayi matukar haska farar fatar sa ya feshe jikin sa da turaruka ya fitu saboda anfara kiran sallar magrib.

Tsayawa ya yi yana kallon yadda nike bacci da hannu cikin baki kamar wata baby me shan nono wayar sa ya d'auko ya fara d'aukata hoto sanan ya tashe ni yafice masallacin dake unguwar. Alwala nayi nima na tada salla bayan na idar nayi shiru ina tunanin ƙauyen mu da yanzu ina chan cikin duhu da sauro ko cikin ruwan sama wani lokaci idan mugun tar Inna ya motsa rufe dakin ta take ta turo ni waje inyita kuka ina rokon ta saboda inada tsoro sosai wani lokaci sai tayi bacci in lallaɓa inshiga ɗakin in kwanta, idan asuba tayi ta gani tayi min mugun duka ina nan zaune har akafara sallan isha nayi nakoma falo na zauna ina jiran Yaya Usman ya dawo na fara jin tsoro banjima da zama ba ya dawo dauke da wata leda ahanun sa da sallama yashigo na amsa tare da dukawa ina gaida sa "Yayana ka dawo lafiya,?" "lafiya" ya amsa atakaice yaje ya kunna kayan kallo saboda akwai wuta ya dauko rimout ya zauna kan kujera yana chanza channel. Boom TV ya saka Yana kallon waƙoƙin da suke sakawa matane da maza matan na sanye da irin kayan da Usman yasiyo min namijin da take rawa dashi sai taɓa mata jiki yake nikuma duk kunya ta kama ni nakawar da kaina, shi kuma ko ajikin sa hankali sa ma baya wurina mikewa nayi zanshiga bedroom naji ya ce"Zo nan Aysha" waigowa nayi amma naga har yanzu fuskarsa na kan tv ahankali na taka har wurin shi na tsaya jawo ni ya yi na faɗa jikinsa har fuskar mu na hadewa guri ɗaya.


PAGE 11



Ɗagowa na yi ina kallon sa bai kula ni ba sai hannu ya saka ya gyara min kwanciya ajikinsa. yayna shafa gadon baya na kamar wata yar baby, lafewa nayi ajikinsa ina shakar kamshin jikinsa, har bacci ya dauke ni. shi kuma Usman ganin ta yi bacci ya zare ta daga jikin sa.
Ya kaita bedroom ya kwantar ya dawo falo ya yi kwanciyarsa tare da kashe hasken falon, shima be jima da kwanciya ba bacci ya ɗauke sa saboda gajiyar tafiya INDO kuwa bacci ta ke sosai cikin kwanciyar hankali, zabura ta yi cikin magagin bacci ta fasa kara tare da fashewa da kuka jikin
ta har kar karwa yake saboda firgici. Ahankali ya ke jiyo sautin kukan ta, tashi ya yi tare da kunna hasken falon ya nufe bedroom din da take ya kunna mata haske zaune ya tarar da ita tsakiyar gado, gashin kanta duk ya hargitse ai tana ganin sa da gudu tayo jikinsa tana fashewa da sabon kuka. Bayan ta ya fara shafawa alamar tayi shiru ko magana ya kasa yi saboda har cikin kansa ya kejin kukanta. ahankali ya janye ta daga jikinsa saboda ya gaji da tsayowa amma ta rikesa gam kamar za'a kwace mata shi. "pretty bari mu zauna mana ba tafiya zanyi ba kinji." Da kyar ya samu ta bari ya jata bakin gado suka zauna tana kara makalewa jikin sa gaba da ya tabir kice masa ya rasa meke damunta "pretty faɗamin abinda ke damunki." shiri tayi masa shima be koma tambayar ta ba addu'a ya shiga yi mata ya na shafa kanta gumi ne ya jike mata fuska duk da AC dake aiki a dakin amma gumi take bayan ya'n mintuna bacci ya dauke ta amma tana makale ajikinsa. shima bacci ya dauke sa kiran sallar asuba ne ya tashe sa daga bacci zare ta ya yi daga jikin sa ya shege ban d'aki ya yi wanka tare da duro alwala ya zo ya tashe ta ya nufe masallaci be dawo ba sai da gari ya fara haske ya dawo kitchen ya shiga ya kuna gas ya soya musu wainar kwai da ruwan tea bayan ya kam mala kana ya shige cikin falo tsayawa ya yi cike da mamaki yadda anka gyara falon komai tsaf kamar ba shine suka har gitsa ba be ida shan mamaki ba saida ya shiga bedroom shima dai kamar falo komai net "Barka da safiya Yayana." ɗagowa ya yi suka hada ido Masha Allah ya furta bayan tayi Salla ta gyara gida wanka tayi ta saka wasu riga da siket masu lau nin ja da baki sai jan baki da ta saka red tayi masifar kyau da ma haka ta iya kwalliya da ma rashin gyara ne ya hana asalin kyaun ta ya fitu ashe ba komai ya gani ba lakacin da ya ganta ƙauye. sai da ta koma gaida sa kana ya dauwo duniyar tunanin da ya shiga "lafiya lau preety fatan keta shi lafiyar da kai ta amsa mai shikuma ya shige banɗaki ya yi wanka, ita kuma falo ta dawo ta zauna tana jiran 9fituwar sa bayan ya fitu wanka ya shirya cikin wani da kakkiyar shadda fara tasha aiki surfani sai hula baka me ratsin fari fari ya feshe jikin sa da turaruka masu masifar kamshi tun kafin ya fitu kamshin turaren sa ya yafara iso mata dagowar datayi ta na kallon kofa ya yi dai dai da fituwar wasa wow Allah ya yi halilta kyau iya kyau saboda duk kyaun INDO Usman ko kama kafar Usman ba tayi ba gaba dai yatafi da imanin kamar bata taɓa ganin sa ba sai da ya hura mata iska kana ta dawo haiyacin ta cikeda kunya ta saukar da kanta kasa ta na wasa da zoben hannun ta da har ya fara matse mata yatsa wani tsohon zobe ne k'anwar Mamanta maryam ta saka mata shi tace mata kar ta yarda ta cire sa na maman ta ne. kurama zoben idu Usman ya yi kamar ya taba ganin irin zoben ga hannun wata mata komai na zoben iri daya dana matar amma ina yasan ta yana son tuna wani abu amma ya kasa kansa ne ya fara sarawa nan da nan wani zazzaɓi me zafi ya taso masa ya saka hannu yadafe kansa tare da karantu addu'i kan kujera ya zauna ya lumshe shan yayyun idanunsa masu kama da me jin bacci a hankali ciyon kan yafara tafiya har ya dena Jin sa ga baki da ya ajiyar zuciya ya sauke kana ya ce "preety jeki kitchen ki d'auko kayan da na hada "tom tace kana ta tafi ta dauko tea ya hada musu mai kyauri suka sha da wainar kwai bayan sun kam mala yace ta dauko mayafin abayar ta tazo sufita cikin gari cike da farinciki taje ta dauko mayafin ta fitu sai da ya rufe ko ina kana suka shiga mota suka bar Unguwar

PAGE1️⃣2️⃣ to1️⃣3️⃣

BARNO
Wata babbar mace ce cikin shiga ta alfarma. daga wuyun ta zuwa hannayen ta duk gwala-gwalai ne zaune take cikin wani ƙatun falo na alfarma ta dura ƙafa daya kan daya ta zuba ma katun
talabijin ɗin da ke manne a falon ido fadar irin dukiyar da aka zuba ma falon bata
lokaci, ne nidai abinda nace duk wanda ya mallaki irin dukiyar dake cikin falon ya gama samun duniya sai fatan samun lahira mai kyau .
gaduk kan alama hankalin ta ba ya ga kallon tv tashi ga duniyar tunanin Hajiya hauwa'u kenan uwar gidan Alhaji Ahmed hamsha ƙen dan kasuwa wanda ke kasuwanci gwala-gwalai har kasa shen ketare. ba iya nan ya tsaya ba ya na harkar gine-gine kana ya nada Company kasar Birtaniya wanda ya saka sunan babban dan sa Usman wani ƙanan matarsa ta2 ke gudanar da harkokin Company Alhaji Ahmed Sani Yarima haifaffen dan BARNO ne asalin sa kanuri ne mahaifan sa duk Allah ya yi musu rasuwa. daga shi sai ƙanwar sa Sakint wadda take aure a kasar Turkiya inda a achan ne ya je kai mata ziyara ya hadu da uwar gidan sa hauwa'u nan suka kulla soyayya me karfe ya sha fama kafin ma haifin hauwa'u malam Yusuf ya amince da ƙyar ya yarda ya bashi auren ta, saboda subi2 kadai Allah ya bashi hauwa'u ce baban sai ƙanwarta Nimra mahaifiyar su tarasu wurin haihuwar Nimra malam Yusuf haifaffen dan Turkiya ne sheda matar sa da ya ransa ya na da tarin dukiya wanda shi kansa be san iyakar taba. haka dai mijin ƙanwar sa ya karbar mai auren hauwa'u bayan an kammala komai malam Yusuf yaraba dukiyarsa2 ya bama hauwa'u rabi ana gobe zasu bar kasar sudawo Nigeria cikin dare ciyon ciki ya kama malam Yusuf ya rasu. Sun shiga tashin hankali sosai bayan sati daya, da rasuwar malam Yusuf mijin sakinat ya tai maka musu suka hada dukiyar mahaifinsu suka dawo Nigeria. Nimra tasha kuka ganin ta bar kasar su ta asali bayan sun dawo Nigeria Nimra da hauwa'u suka yanke shawarar bama Alhaji Ahmed dukiyarsu ya juya musu kar ta lalace, da farko bau yarda ba sai daga baya ya nemo lauya aka yi komai arubuce dama Nimra ta kammala karatun ta zaune take kawai a gida. Alhaji Ahmed soyayya suke zubawa shida matar sa haka rauwa ta cigaba da tafiya har Allah ya bama hauwa'u juna2 murana wurin Alhaji Ahmed da yar uwar sa da Nimra ba a' magana kulawa take samu sosai wurin mijin ta da ƙanwar ta.har cikin ya isa haihuwa ta san talo ƙatun ɗanta namiji mai masifar kyau gashi kamar su ɗaya da Nimra babu
inda yabaro Nimra kamar Nimra ce ta haifesa. Murana wurin Alhaji Ahmed ba a'magana anan ya yi ma yaron sa huduba da Usman anyi taron suna lafiya sakinat da mijinta da yaran ta sun koma Turkiya. komai na Usman Nimra ce ke masa ko bacci tare suke gashi baya da rigima Alhaji Ahmed har mamaki yake irin shakuwar dake tsakanin Nimra da Usman ita hauwa'u tace ma Nimra tabar mata Usman duniya da lahira. Haka rauwa ta cigaba da tafiya har Usman yakai shekara 3 lokacin ya yi wayo sosai ga kiriniya ko ina zuwa yake ga magana ta zauna

Please Login or Register in order to submit comment