Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mum Aisha suka qara gudu tana rokon ASH da dukkanin zuciyarta da qarfinta.


Ganin halinda Husnah ta shigane kwata kwata kaman ta zauce gunjin kukanta kawai ke tashi a gurin ta saki Haydar ta kama Abdulhameed Shima tana rokonsa ya roki Dad dinta karya aura mata wannan mutumin kauyen.


Mum Aisha ma kuka takeyi sosai sbd tasan maganar ta gudu ma Bata taso ba Dan batada gurin zuwa har ita har Naufal gwara ta tsaya ta roko ASH ya sassauta ya dubi maraicinta ya janye hukuncinsa.


Yanayin Husnah tini ya karya zuciyar Haydar gabaki Daya harma da Abdulhameed Wanda yakejin radadin hukuncin da tausayinta sbd yasan ko kwana Daya bazata iya a rayuwar kauyen ba.


Haydar jajir idanuwansa sukai Yana kallan Dad dinsu cikin tsananin damuwa da qasqantar da Kai duk da yaji laifukan da su Husnah din suka aikata musamman ita din a bakin Mum Aisha gashinan tanata fada Amma duk girman lefin nata aure a kauye da Miji irin wannan qarasa zauncewa ma zatai.


Qarfin Husnah take ya fara qarewa ta rarrafo gurin Haydar ta qanqamesa tana sake kuka sosai da yake jinsa har cikin ransa ya rungumeta Yana kokarin rarrashinta Amma Sam taqi tsayawa kukanta tsananta kawai yakeyi tana cewa ta tuba ta Dena komai.


Abdulhameed ne ya zuba mata idanuwansa da sukai jajir yanajin Shima bazai iya barin akaita kauyen aure ba kaman yanda bazaiso Amatu tayi zaman aure a kauyen ba,
A Baya Amatu ta samu kanta a irin wannan halin ya tsaya Kuma ASH dinma ya tsaya suka qwatota Dan haka ko Husnah duk laifinta rayuwar kauyen da auren uzaifa kashe rayuwarta gaba Daya zatai.


Juyowa yayi ahankali tareda dago kansa daga duqen dayake ya kasa kallan ASH sbd nauyin da kirjinsa yayi ya Bude Baki cikin girmamawa da nutsuwa yafara rokonsa Shima tareda basa hakuri zuciyarsa ta sanyaya.


Husnah Da qarfinta ya fara qarewa rarrafowa tayi gurin Abdulhameed da sauri ta riqe hannunsa Daya da hannuwanta biyu a rude ta Kalli ASH tace


"Dad Dan Allah idan kayi alkawarin bazata barni ba ka auramun Abdulhameed na yarda zan zauna dashi shi akan wancan mutumin wlh tsoronsa nakeji,
Dad dan Allah ka auramun Abdulhameed wlh inaso zan zauna dashi zan masa biyayya zan shiryu,Dan Allah Dad."


Abdulhameed kusan mutuwar zaune yayi sbd mamaki me tsananin gaske da tashin hankali,
Dagowa yayi da sauri tareda kallanta cikin yanayi na rikicewa ma dayake Neman yi sedai kallan da ASH ke masa da yanda take kuka sosai har batada karfi ya sanyashi yin shiru.


Sake qanqame hannunsa tayi tana maimaitawa Dad dinta zata auri Abdul din zata zauna dashi ko inane.


ASH sai alokacin ya zuba mata idanuwansa da suka sake sauyawa sbd duk kukan datakeyi a cikin ransa yake jinsa sbd harga Allah Yana son 'yar tasa kawai hukuncine dole yayi mata idan yanaso ta dawo daidai.


Haydar Dora idanuwansa da sukai jajir yayi akan Abdul Yana masa kallan fatan hakan ta kasance Dan Shima zaiyi farin cikin Husnah ta auri Abdul sosai fiyeda uzaifa din.


Irin kallan da Haydar ke masa hakama da yanda Husnah ke zake kuka sosai a jikinsa ya sanyashi Jin zai iya auren nata Dan kubutar da ita daga auren da bazai taba son ai mata ba.


Dagowa yayi ya Kalli ASH cikin girmamawa da jarumta yace


"Eh inasonta zan aureta,Dan Allah a auramun ita zan kula da ita ta Dena dukkanin urin wannan lefin,ayi mata afuwa ta tuba"


Duk tashin hankalin da mum Aisha take ciki da kukan datakeyi Saida ta dago tana kallan Abdulhameed din da Husnah ta maqalalewa gaba Daya batama hayyacinta,
To tayaya ma zaa bari Husnah ta kaucewa hukuncin zuwa kauye bayan itace duk ta ja musu wannan masifar.


Haydar cikin damuwa me girman gaske ya fara rokon Dad din Daya tausaya ya sassauta Husnah abawa Abdul din Dan Allah tinda yace zai aureta din.


Maamah ma dagowa tayi ta Kalli Abdulhameed din da Husnah kafin ta dawo da kallanta gurin ASH batareda ta iya kallansa ba murya a shaqe sbd kukan datasha ta fara rokonsa akan karya aurawa Husnah uzaifa a aurawa Abdul din Dan Allah.


Mamakin tashin hankali mum Aisha tace Bata yarda ba sbd Husnah dince duk me girman lefi a duk abinda suka aikata din hakama itace ai ta Saka Naufal zuwa yiwa Fyade Dan haka itace tafi kowa cancantar zuwa kauye.


Babu Wanda ya kula mum Aisha din duk da daga ASH har maamah, Abdul da Haydar Babu Wanda zuciyarsa Bata quna da yanka akan maganar Husnah dince ta tura a yiwa Amatun fyade sedai Kuma duk da Hakan bazasu bari rayuwarta ta mutu gaba daya ba ta hanyar miqata hannun zuriar Sanda Fulde a kauye,zasu hukuntata ta wata hanyar Amma wannan din Kam bazasu iya bari ta tafi ba.


Abdulhameed ma da kansa ya qasqantar da Kai ya ringa rokon ASH din hakama Haydar,
Husnah dinma kanta a cikin kukan da qarfinta ya gama qarewa rokonsa takeyi tana maimaita ta tuba bazata sake tada hankali ba ko rigima da Amatun.


Numfashi ASH din ya sauke ahankali tareda Jin nauyin da kirjinsa ya tokale dashi ya Dan fada Dan haka ya Kalli Abdulhameed din a natse cikin kamewa yace


"Ka tabbatarda kana Sonta zaka aureta?


Gyada Kai Abdul din yayi kansa a qasa
kusan itama Husnah din gyada kan takeyi kaman ita aka tambaya jikinta duka rawa yakeyi sosai.


"Zaka iya tsayawa akan tarbiyanta?
Zaka iya tsayawa akan kulawa da ita da gyara halayenta?
Zaka iya tsayawa kayi hakuri da ciwonta?"


Sake qanqame Abdulhameed din Husnah tayi tana kallansa da jajayen idanuwanta dasuka gama shiga rauni tana fatan yace zai iya duka sbd ita gaba Daya shi din ma takeson aure a ayanzu ta yafe Faisal.


Numfashi Abdulhameed ya sauke ahankali tareda zubawa Husnah din idanuwansa ahankali Ya kalleta kafin ya Maida kallansa inda ASH yake zaune cikin nutsuwa da sanyi yace


"Eh inshallah duka zan iya."


Haydar Wani sanyi da ajiyan zuciya ne ya ringa saki cikin ransa Yana godewa Allah da Jin sabuwar kaunar Abdul din Dan kuwa ya ceto masa yar uwa daga abinda bazai iya qara rayuwa cikin dadi da farin ciki ba da anyi Husnah din auren kauyen.
##MAMUH#


*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at๐Ÿ‘‡
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070


Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#




AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar






76
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs๐Ÿ’ฏ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ‘
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku๐Ÿ’ฏ๐Ÿ‘*


MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER


08142800199
07068558096




*************
Mum Aisha na Jin ASH ya amince ya bawa Abdulhameed din Husnah ta fasa sabon kuka tana cewa Bata yardaba itama bazata iya auren kauyen ba.


Baice komaiba ya Bata kyakkyawan zabi akan ko tayi auren Daya zabar mata ko ta tattara tabar masa gidan harna Abuja harna Yola ta tafiyarta itada Naufal su tafi Babu ruwansa ko hadinsa da ita.


Wani irin kukan baqin cikin rayuwa ta sake fasawa tana barin palon ko Gani batayi jininta na hayewa gaba Daya.


Maamah ya kalla da alaman kema kinada magana ne?
Ta miqe a silale ta fice zuciyarta a nauyaye itama Dan kuwa yau tagama ganin qasqancin rayuwa ga baqin cikin auren kawu bello,
Idan suka ce Basu yarda ba a sake tada Wani rigimar Azo ayita tashin hankali a gabansa sauran mutuncin ya qarasa zubewa.


Tana ficewa Husnah jikinta da qafafunta na rawa ta miqe sedai bama zata iya Kai kanta cikin gida ba sbd barin da jikin keyi sosai Kuma har lokacin hawayenta Basu tsaya ba.


Abdulhameed dinne ya miqe ya kama hannuwanta ta sake qanqamesa tana tsiyayar hawaye suna fice palon aka bar Haydar Se Dad din Mr Jameel ma ficewa yayi ya Basu guri Dan suyi magana sosai.


Suna fita Husnah ta fasa kuka mara sauti tana Neman zubewa qasa Abdul ya riqota da kyau jikinsa tareda tsayawa cak Yana kallanta a natse kafin ya Bude Baki yace


"Kukan Kuma yanzu na Menene tinda bazaki auri uzaifa din ba?


Sake fasa Wani kukan tayi tana fadawa jikinsa ta qanqamesa cikin kuka take cewa


"Nidai kace gobe a daura damu kar abari saika dawo Dad zai iya sake fushi ya auramun mutumin, Dan Allah a daura mana auren muma tareda su mum Aisha gobe
ku tafi dani bazan iya zama anan ba Nima zan Biku"


Numfashi me sanyi ya sauke ahankali tareda Dan dagota daga jikinsa sbd gaba Daya a rude take shiyasa takeda maqalqalesa din.


Cireta daga jikinsa yayi gaban Daya tareda kama hannunta suka qarasa cikin gida sbd ta huta ta nutsu.


Sama yahau da ita har bedroom dinta ya zaunar da ita bakin gadonta tareda daukan tissue Dake gefen gadonta ya share mata hawayenta cikin kulawa yace ta Dena kukan ya Isa haka.


Daqyar ya samu ta dan dawo hayyacinta ya sake kwantar mata da hankali da kalmomin rarrashi da kulawa kafin ya fice ya barta kwance.


Daga dakinta Kai tsaye dakinsa ya wuce sbd nauyi da kansa da zuciyarsa sukai sbd baitaba tinanin yin aure a yanzu ba hakama yanada budurwarsa dayake tinanin aure bayan sun dawo gaba Daya itama acan take karatu tareda su.


Yana Isa daki toilet ya shige da kayan jikinsa ya sakarwa kansa ruwan sanyi sbd harga Allah lissafinsa ya kunce da lamarin duk da Baya Dana sani ko baqin cikin Hakan sbd da gaskiyarsa kaman yanda bazai iya kalla ya bari rayuwar Amatu ta lalace ba zai iya bari rayuwar Husnah ta lalace ba sbd 'dan uwanta Haydar dayake kaunar Amatu da zuciya Daya bakuma zai iya barin AmatulMaleek ta shiga irin wannan halin ba kota halin yaya,
dakuma Dad dinta ASH dayake yiwa Amatu son da har zai iya hukunta 'yarsa irin haka akanta Badan zuciyarsa bazata quntata da hukuncin nasa ba shi kansa,
Saikuma mahaifiyarta mum Abeeda datake tsananin kaunar tasu mahaifiyar da zuciya Daya kauna Kuma me tsanani batareda sun hada jini ba tin yarinta,,
Wannan dalilan ne yasa Bazai iya barin rayuwar Husnah ta lalaceba zai aureta Kuma zai kula da ita sbd tana Neman me kulawa da ita ne ya dorata a hanyar dangana da tawakkali bawai so qarara ba da rashin kwaba kaman yanda maamah tayi mata shiyasa duk ta koma batada lissafi ko tinanin daukan abu da sauki.


Gidan tsit ya dauka kusan kowa tasa ta ishesa ta tashin hankali da masifa,
Haydar ko Daya dawo daga gurin Dad dinsa ciwon Kai ne da toshewan zuciya gabaki daya a tareda shi sbd Kai tsaye Dad dinsa ya sanar masa AmatulMaleek shine me aurenta Kuma uban cikin dayake jikinta sbd toshe wata sabuwar hanyar fitinar ko tashin hankalin.


Abdulhameed na fitowa toilet shima ya shiga ya sakarwa kansa ruwan sanyin da kaya a jikinsa Dan samun sanyi da sassaucin zafin Daya rufe jikinsa duk da kusan ba auren ne yafi masa ciwo ba kaman yanda aka boye masa Kuma Amatun yafi Jin zafin boye masan datai Dan kusancinsu kusan yayi karfin da basa fa boyewa juna komai.


Yana fitowa kaya ya Saka na bacci ya hau gado ya kwanta gefen Abdulhameed Wanda Shima ba bacci ko alamansa a idanuwansa sbd daki Daya suke amfani dashi tin zuwansu tinda ba wani dadewa zasuyiba su koma.




Bangaren su kawu bello kuwa farin ciki ne fal a zukatansu sun kasa zaune sun kasa tsaye musamman kawu ashiru da uzaifa sbd shi kawu bello kome ne zaayi duk da komen ne Yana farin cikin Shima Dan maamah din Hutu da Jin dadi ya sauyata hakama ASH TALBA bazai barsu hakanan ba aike da kayan arzuka Akai Akai Sunday auren sirikarsa,da qanwarsa da 'yarsa tilo a gida Daya,Aiko kayan arzuka sai sun ture duniya sabuwa.


Kawu yusufa da Sam shi aure auren be damesa ba kudi dai kudi dai kawai kallansu yakeyi bakinsa a washe yace


"Kai ashiru sai farin cikin sabon auren jar fata kakeyi kana mantawa da laraba da zafin kishinta da tashin hankalinta kana Kai matar mutane kauye laraba zata iya fasa mata hanci da langa fa,ko sati aurenka bazaiyiba Kila zai mutu Dan wlh Babu me iyawa da haukar laraba sai Kai Saka aurota,
Ga sauran matan ka Nan duk ta Maidasu bayinta Yan wahala ya zakai da matar binnin idan ka Kai??"


Dariya kawu bello ya saki Yana cewa


"Tin anan idan kasan bazaka iya karya laraba akan matar binnin ba wlh kace ka hakura bazakaiba Dan Babu ruwana a lamarin laraba ba mutunci ne da ita ba"


Uzaifa dayaji ana ambatar uwarsa shiru yayi Yana Jin ba dadi wa babansa idan har ya rasa wannan matar binnin datai jajir ta nuna kaman mangwaro.


Kawu ashiru shiru yayi Dan kuwa Shima yasan balain laraba Amma Kuma bayajin zai fasa amsar auren Aishan binnin akan laraba suna Isa zai saketa tabar gidan ya Saka Aishan wajenta tinda Daman baida gurin Saka Aishan binnin.


Kayan jikinsu kawai suka zo dasu gashi akwai daurin auren da safe basuda wasu kayan Dan haka suka cire kayan suka nade suka ajiye da niyar sakawa da safen karsu kwana dasu su yamutsasu,
Sanyin AC Dana garin duk a cikin qashinsu ya shige a Daren sbd kwanan da sukai ba kaya ajikinsu.




*******
Cikin dare sosai Amatu ta Farka daga baccinta jikinta duk yayi mata nauyi Amma dai Bata Jin ciwon komai bayan na nauyin.


Anty Farha Dake waya har lokacin da Mr Jameel ya gama fada mata duk abinda ya faru Dan kawai ta Dan sassauto masa sbd ya lura da ba lafiya ba yanda take masa a kwanakin.


Gama jinsa tayi batareda ta sauko din ba yanata lallabata tana amsa masa a taqaice saiga Amatun ta tashi kashe wayarta kawai tayi ta ajiye gefe tareda miqewa ta nufo Amatun.


Tashi zaune Amatun tayi anty Farha na mata sannu tana cewa


"Kina buqatan wanka dan jikinki ya sake na hada Miki ruwan zafi sosai ko?"


Gyada Kai Amatun tayi tana Bude Baki a ahankali tace


"Amma Ina Jin yunwa sosai anty Farha abinci nakeso"


Murmushi anty Farha tayi tana cewa


"To Abar wankan sai kinci abinci kenan."


Tea ta hada mata me kauri mara sugar kafin ta zubo mata macaroni da aka dafa tareda potatoes da nama kadan Se carrot a ciki Wanda karima ce Mr Jameel da kansa ya kawota ta kawo musu da magrib.


Sosai Amatu taci abincin tasha tea taji jikinta ya sake samun karfi ta sauko gadon ta nufi toilet Kai tsaya tana tafiya a hankali.


Ruwan zafi sosai ta gasa jikinta dasu kafin ta fito kayan sanyi ta Sanya tayi duk Yan abubuwan da zatai ta koma ta kwanta anty Farha ta rufeta take bacci ya dauketa me dadi.




Qarfe 6 na safe tana bacci Akai knocking kadan tareda budewa Kai tsaye Mr Jameel ne ya budewa ASH din lokacin anty Farha na sallame sallarta ta dago ahankali tareda yiwa ASH din barka da asuba tana miqewa suka shigo.


Amsawa yayi a natse idanuwansa akan L.A dinsa Dake bacci kaman baby kafin ya tambayi jikin nata
Anty Farha ta tabbatar masa da lafiya kalau ne yanzu.


Anty Farha ce tafara ficewa daga dakin Mr Jameel ya bi bayanta Yana Jin kaman ya rungumeta har sai ta sauko daga fushinta gabaki daya.


Suna ficewa ya qaraso bakin gadon ya tsaya Yana sake zuba mata idanuwansa masu kyau tsawon mintina kafin ya Maida idanuwansa kan cikinta duk da Yana rufe da abin rufa Amma tinda yasan da abinsa Yana iya ganin tudinsa.


Hannunsa Daya ya Dora a cikin cikin kulawa kafin ya ranqwafo ahankali ya Dora bakinsa kan lips dinta yayi kissing dinsu Yana Jin Sonta kaman zai faso kirjinsa ya fito.


Tasowa yayi Yana kama hannunta da nasa hannun ya sarkesu tafin hannuwansu na haduwa cikin dumi da sanyi.


Cikin baccinta ahankali taji qamshinsa na shiga hancinta har cikin kanta,
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali cikin baccin lokacinda qamshin yaketa sake shigarta sai gashi ta motsa ahankali tana kokarin farkawa.


Numfashi me sanyi ta sake tareda Bude idanuwanta ahankali sbd Jin mutum kusa da ita.


Akan kyakkyawar fuskarsa Dake kallanta nata idanuwan suka sauka ta Dan sake lumshe idanuwanta ta Bude akansa.


Numfashi mara sauti ta sauke a zuciyarta kafin ta dauke idanuwanta daga kansa ahankali batareda ta motsa ba tukuna ta zare hannunta Dayake cikin nasa ahankali tana Dan gyara Kwanciyarta.


Jin yayi jikinsa na Neman mutuwa da yanayin nata Dan haka ya sake kamo hannunta ahankali zaiyi magana ta rigasa da Bude Baki ahankali cikin sanyi da rashin kuzari tace


"Ina kwana"


Mamaki ne ya Dan kamasa sbd gaisuwar kaman daga sama ya jita bayan shi ba gaisuwan yake buqata ba a lokaci Jin lafiyanta Dana babynsa yake buqata.


Amsa gaisuwar yayi a tsanake Yana son yin magana ta lumshe fararen idanuwanta alaman bacci takeson komawa Dan haka dole yayi shiru Dan kada ya hanata baccin Kila tana buqatansa.


Tinda ta Maida idanuwanta ta rufe bacci Bai zo mata na hakama Bata motsa ba bare Bude idanuwan har tsawon lokaci kafin ta Bude ahankali tareda tashi zaune tana kokarin sauka gadon ya kalleta tareda miqa hannu zai riqo hannunta ta Dan dago ta kallesa da idanuwanta a sanyi tace zata iya ta gode.
Toilet ta wuce ahankali ta shige tareda rufo kofar.
##MAMUH#




*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at๐Ÿ‘‡
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070




Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#




AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar






77
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs๐Ÿ’ฏ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ‘
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku๐Ÿ’ฏ๐Ÿ‘*


MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER


08142800199
07068558096




*************
Tana shigewa toilet ta jima Bata fito ba sai ga dr beeba ta shigo dakin tareda wata nurse da anty Farha.


Gaidasa sukai cikeda girmamawa suna Dan mamakin ganinsa a wannan lokacin danma itama Dr beeba ta kwana asibiti ne yasa tashigo dakin a lokacin.


Fitowa tayi daga toilet din a natse cikin sanyinta batareda ta dago ta Kalli kowa ba bayan Dr beeba Dake mata yaya jikin ta amsa a cikin sanyi tana zaunawa a hankali bakin gadon.


Tambayoyi Dr beeba din Tai mata tareda fada mata ta kula sosai ta cire damuwa sai Kuma kiyayewa da yanayinta tace ta sallamesu su koma gida.


Rubutawa tai a folder din Amatun kafin ta miqawa nurse din dake tareda ita tana fadawa ASH din dole sai ankula sosai sbd samun BP ga me juna biyu baa cika so ba Gaskia.


Dr beeba na ficewa Amatu Dake zaune ta Kalli anty Farha tace ta Bata hijab ta Saka tana Dan Jin sanyi.


Doguwar hijab anty Farha din ta miqawa Amatun ta Saka a natse har qasa kusan ma cikin idan ba Wanda yasan dashi ba Baya ganinsa.


Basuda Wani kaya Dan haka Yan abubuwansu Mr Jameel ne da kansa ya dauko ya fito dasu suka fito.


ASH dinne a gaba batareda yace komaiba sbd ko kallansa ma LA din taqi yi bare ya samu Daman yin magana.


Suna isowa mota dayake akwai mota Daya a asibitin a tareda dasu kafin wadda ASH da Mr Jameel din suka zo da ita yanzu.


Kai tsaye dayar motar Amatu ta nufa tana cewa anty Farha gidanta takeson su tafi Batason koina.


Shiru anty Farha tayi tareda tsayawa tana kallan Amatun cikin Dan mamaki kafin ta juya ta Kalli Mr Jameel Dayake tsaye Shima yaji abinda ta fada.


ASH Daya Bude mata mota Yana jiran qarasowarta kafin ya juyo da sauri mr Jameel ya qaraso cikin girmamawa da kare zancen ya sanar masa LA din tace a motan Farha zasu koma gidan.


Juyowa yayi ahankali ya kalleta yaga harta Isa motan Farha din batareda ta waiwayo ba ko alaman ma zata waiwayon.


Baici komaiba ya barta suje a motan Farha din sbd kada ya takurata ko kadan.


Mr Jameel da duk yake Neman rikicewa shiga motarsu yayi bayan ya rufewa ASH din kofa bayn shigarsa motar ya tada Basu fice ba Saida sukaga motar su Farha din ta fara ficewa.


Mr Jameel dayake yasan ba mansion sukaiba sai ya bari suka bace musu Dan kada ASH ya lura da hanyar da zasu bi daban.


Anty Farha Kai tsaye hanyar gidanta ta kama su Kuma Mr Jameel ya dauki hanyar mansion Yana shiga tinanin wannan sabuwar lamarin Kuma.


Ko da suka Isa mansion su kawu sunyi breakfast sun shirya tsaf abinsu sai kyallin Mai sukeyi da suka Saka aka kawo musu suka shafa sbd yanda duka fuskokinsu suka bushe kaman anyi hayaqin yashi suna zaune.


ASH na dawowa suka fito suka qaraso gurinsa suna gaidasa cike da girmamawa suna tambayar jikin Amatu.


Amsawa yayi Yana sake Basu tabbacin karfe goma sha Daya zaa dauka auren Amma Banda na uzaifa zai masa kudi ya samu mata acan kauye ya aura Husnah zai daura mata auren da Abdulhameed idan sun amince da Hakan.


Matse fuska uzaifa yayi sedai su kawu Basu bari ya nuna ba suka hau washe Baki suna cewa ai da Abdulhameed din da uzaifa duka Daya ne duk Wanda aka nawa nasu ai.


Ciki ya shige yabarsu suka koma masaukinsu suna tausar uzaifa Dayake Jin baqin ciki a karo na biyu ana masa ta leqo ta koma haka Akai masa lokacin Amatu yanzu Kuma Yana murna ya samu zuqeqiyar lafiyayyar yar Madara anzo an Hana masa zaa bawa Abdulhameed Dan anga ya fisa jikin girma da cika ido.


Dayake su kawun Basu rasa nasu ba Kuma sun San kudine dai zasu ta shigosu Dan haka suka taru suka danne uzaifa suka hanasa magantuwa akan maganar har su koma.




Husnah gari na wayewa ta fito Kai tsaye dakin maamah Dake daki itama tin jiyan ta kasa fitowa abin duniya ya isheta ya sha mata Kai,
Ga wannan auren na kaddada baqa da zaa daura mata,ga rashin sanin halinda Amatu take ciki ga ASH din Babu Wanda ya sake ganinsa ko Jin idan ya janye hukuncin nasa ko ansamu sassauci ga Abdul Rana tsaka da zaa daurawa aure ba shiri.


Husnah na shigowa ta zube gaban maamah din tana fasa kuka sosai tana rokonta ta yafe mata tace a daura aurenta da Abdul ayau din itama kada daga baya Dad ya sake fushi da ita ya aura mata uzaifa ko Wani daban Wanda bataso.


Shiru maamah tayi mata sbd itama cikin tsaka me wuyan take Amma kukan Husnah da yanda take rokonta har cikin ranta take jinsa dan son datake wa Husnah din Allah ya Gani har qasan ranta take kaunarta kaman itace ta haifeta.


Karyewa zuciyarta tayi ta rarrasheta akan suyi addua kawai Allah ya musu zabi Mafi Alkhairi Amma ita yanzu ko fitama daga dakin batajin zata iya bare zuwa rokon ASH.


Kasa fitowa daga dakin Husnah tayi ta rakube gefen maamah din tana Jin zazzabin tashin hankali na rufeta Dan duk ta sake shiga firgici idan ba ganin tayi Yan kauyen sun kwasa sun tattara sun tafi ba hankalinta bazai taba dawowa jikinta ba.


Tana zaune zuru Abdulhameed yayi sallama dakin ya shigo cikin nutsuwa sanye da Ralph Lauren sweatsets black da suka fito da haskensa sosai slippers ne a qafarsa masu tsada.


Baisan Husnah na dakin ba Saida ya shigo ya ganta zaune gefen maamah din duk a firgice gwanin tausayi.


Tana ganinsa taji sanyi da nutsuwa na San shigarta ta taso ta nufosa tana kokarin shige masa ya riqe hannuwanta tareda tareda Yana kallanta cikin nutsuwa yana cewa ta nutsu.


Nutsuwar take kokarin yi Amma bazata iyaba ta kasa.


Janta yayi suka dawo Palo ya zaunar da ita tareda sakin hannuwanta Yana kallan fuskanta data kumbura gaba Daya ta sauya kamanni.


Magana zaiyi Haydar Shima ya shigo palon Yana ganinsu ya qaraso a natse ya zauna gefen Husnah din tareda zuba mata idanuwansa baice komaiba itama kasa cewa komai din tayi ta fada jikinsa tana fashewa da kuka sosai Wani irin maraicin rashin uwa da Uba takeji Yana daibaiyeta Haydar ne kadai sanyin datake samu a rayuwarta sai Abdulhameed idan ta samesa to Kila ta samu me rarrashinta.


Shi kansa Haydar hawayen tausayinta da kaunarta yake ji na Neman cika idanuwansa Amma Yana buqatan nuna jarumtarsa ya tsayawa yar uwarsa sbd Shima a yanzu auren yakeso a daura mata da Abdul su tafi da ita ya Bata kulawan datake buqata hakama yasan Abdul din zai Bata kulawan da zata buqata ta dawo daidai kaman yanda itama takeson binsu din can.


Abdulhameed

Please Login or Register in order to submit comment