Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zasu Dan haka yanzu dazai tafi wata qasa duniyar Jin takeyi kaman bazai iyaba sedai tinowa da Haydar na can Kuma zasu kula da juna sosai yake sata Jin hankalinta ya kwanta,


Husnah Kuma exams ne a gabanta shiyasa ta kasa gane kanta sosai ta dage sbd kusan Amatu sosai take kawo wuta a nata karatun Dan haka yanzu da Bata kaunar abinda ma zaisa Dad dinta ya duba cigaban Amatu akan nata Sam Bata kaunarsa.




*****Ta bangaren ASH TALBA kuwa kusan kullum da Amatu ta gane Yana shan tea da dare koyaushe kafin ta shige saita dafa ta Kai dining a flask ta ajiye ta shigewarta,
Shima Daya fahimci yanzu kullum ana aje masa sai ya rage fitowa cin abinci tareda su Sai ya gama komai zai fito yasha ya koma ya kwanta.


Mum Aisha tayi tafiyar dole wadda take Jin idan batai ba zata iya fashewa a cikin gidan sedai a Tararda gawarta Dan haka tayi tafiya kanta ya fara warwarewa kafin ta dawo tasan yanda zatayi da yar cin Amana maamah wadda taci amanar aminta da zumunci.


Tafiyar Abdul tazo daidai da tafiyar Husnah porthcrt mahaifiyar Faisal ta rasu Dan haka sosai hankalinta ya tashi haka itama Maamah sosai ta shiga damuwa ga exams sunayi a lokacin,


Ranar da Abdulhameed ya wuce AmatulMaleek Tasha kuka a jikinsa kaman shine yayan itace kanwar
haka ya ringa rarrashinta Yana Bata qwarin gwiwan fuskantar rayuwarta batareda tsayawa kebe kanta ko takura kanta akan aurenda ASH Kila ya manta dashi.


Maamah ma taji dadin shawarar Daya bawa Amatun sbd so take Amatun itama ta manta da Wani maganar auren harsu samu Abeeda ta tashi Dan Tana tashi tasan ASH TALBA bazai qara ko kwana da auren Amatun ba zai sallameta asiri rufe batareda Abeeda ma tasan anyi auren an warwareba.


Abdulhameed ya tafi yabarsu da kewansa Dan haka maamah dole cikin kwanakin ta Maida kulawanta da tattalinta ga Amatu wadda ta shiga damuwa sosai na tafiyan Abdul sbd shine abokinta Kuma abokin shawararta.


Farha da maamah ne suka dage harta sake batareda ta Dade cikin damuwarba sbd exams dinta.


ASH TALBA tin washe garin rasuwar umman Faisal yaje yayi gaisuwa ya dawo,
Husnah ma itace ta riga Amatu gama exams dinta Dan haka babu Bata lokaci tayi Shirin tafiya porthcrt Kuma tareda maamah zasu itama tayi gaisuwa.,
A bangaren husnah da gangan ta da tafiyar maamah din sbd idan suka tafi gidan ze Kona ba kowa sai Amatu da masu aiki wainda suke bangarensu daban,cikin mansion dai ze kasance Amatu ce kawai Dan haka tsoro da firgici bazai taba barinta yin karatun da zatai exam me kyau ba sbd itama Bata karatun exam din ya lalace ne kwata kwata daga ranar da umman Faisal ta rasu.


Ita kanta Amatun da zasu tafi hankalinta tashi yayi sosai da barinta da zaayi ita kadai a gidan sosai ta shiga damuwa Amma batai magana ba sbd tasan ma ba lallai atafi da ita ba Kuma ko taje Yan uwan Faisal din da yawa basa Sonta ganin itace ta Hana ya auri Husnah ko gaisuwar rasuwar txt tai masa har so uku duk bayan awanni saita masa ta tura masa sbd bazata iya kiransa ba tin ranarda aka daura aurenta masu sake magana ba baice mata komaiba ko a waya haka itama batasan me zata ce masa ba,
A makarantar ma sosai suke wasan boyo da juna kaucewa juna sosai sukeyi basa son su Hadu.
##MAMUH#


Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#


AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar


31
Su Husnah na hanyar zuwa airport ta Ciro wayarta daga handbag dinta shedan na ingizata ta Dan shakka Amma Kuma zuciyarta na sake turata ta Nemo numbern Naufal ta tura masa txt din idan Yana son Neman gafarar AmatulMaleek ita kadaice a Mansion ko Babu kowa Se masu aiki hakama Dad dinta baya gari.


Tana tura sakon ta mayar da wayarta handbag dinta ta rufe tareda kallan maamah da itama itan ta kalla cikin kulawa ta saki murmushi tana Dan kwantawa jikin Maamah ahankali tace


"Maamah Allah yasa mum dina ta samu lafiya ta dawo cikinmu Ina kewanta sosai."


Numfashi me dumi maamah ta sake tana amsawa da "Amin ya Allah" zuciyarta na Dan nauyi sbd duk lokacinda ta Tina da Abeeda da auren mijin Abeedan Dake kan tata 'yar Jin takeyi hankalinta da duniyarta na jijjiga sosai cikin tashin hankali da damuwa.


Suna Isa airport Basu Wani jimaba suka hau jirginsu ya tashi Husnah na sauke ajiyar zuciya me sanyi.


Ranar da suka tafi din a school Amatu ta wuni Se magrib ta dawo gida cikin sanyin jiki tayi wanka ta fito taci abinci Takoma daki ta kwanta zazzabi na Neman rufeta sbd kadaici da rashin nutsuwar zuciya.


Bacci Rabi da Rabi tayi har tasamu asuba tayi ta tashi tayi sallah sai alokacin ta koma baccin kirki.


Bacci tayi cikin nutsuwa da Kwanciyar hankali har qarfe Tara kafin ta tashi tayi wanka ta fito daure da towel ta zauna gaban mirror ta shirya ta Saka undies kafin ta Saka doguwar rigar army green ta fito qamshinta na tashi ahankali cikin sanyi ta nufi kitchen Bata nufi dining ba Dan batajin zaa jera abinci tinda ita kadaice sedai ga mamakinta tini aka jera abincin breakfast dinta komai da komai Yana kan dining din dole can ta koma taci abincin tana gamawa ta miqe Takoma daki ta sake Dan gyarawa ta fito.


Dayake ko Farha kwana biyu Bata Nan ita kadai ta shiga mota driver ya jata zuwa school.


Acan ta wuni yauma sai yamma ta dawo tana gama komai ta shige ta rufe daki ta kwanta.


Kwana hudu da tafiyarsu maamah ta gama exams dinta ita Dan haka yau din data gama da wuri ta dawo tana shigowa mansion din ana Kiran laasar.


Wanka tafara yi Tayi sallah tana Jin nauyin dayake kanta kaman ya sauka tinda ta gama jarabawanta.


Abincin yau dinma baa dining taci ba a plate da trey aka kawo mata ta zauna Palo tana ci tana Dan kallo Sama sama.


Ko data gama da kanta takai kayan kitchen ta gyare gurin ta zauna tana Dan duba wayarta har magrib ta tashi ta shige daki tayi sallah
Tana idarwa Bata fitoba ta zauna a sofa tana waya da maamah suka jima suna wayar har Akai sallan ishai ta tashi tayi ta gama ta fito taci abinci kadan tareda Dan dakatar dasu Farida suka tayata fira a palon har 9 kafin suka tafi itama ta tashi ta shige bedroom dinta.


Tubewa tayi ta daura towel tareda shigewa wanka.


Tana cikin toilet taji kaman tashi Bude kofan dakin da rufewa
Gabanta yayi mummunan faduwa ta kashe ruwan wankan tana saurarawa.


Shiru Babu motsin komai Dan haka ta sake kunna ruwan tana qarasa wankan cikin faduwan gaba da mamaki.


Tana gamawa towel ta janyo ta daura tareda riqesa gamgam ta fito toilet din gabanta na tsananta faduwa.


Tana Bude kofar toilet din ga mamakinta sai Taga wutan dakin a kashe bayan tasan a kunne tabarta.


Hakan data Gani ya Sanyata sake qanqame towel dinta tana Neman juyawa toilet da sauri Dan ta rife kanta Amma taji mutum na kokarin fitowa daga gefen wardrobe na kayanta cikin matsanancin firgici da tashin hankalinta Dake barin jikinta ta qwalla Wani irin ihu me qarfin gaske da Gidan gabaki daya ya dauka.


Cikin sauri Yayi saurin sakinta jikinsa na rawa tareda nufar kofa ko Gani bayayi ya buge goshinsa da qarfi a kofa take ya saki Dan qaramin ihu Shima Amma Bai tsayaba ya fice da Wani irin sauri yabi ta kofan kitchen ya fita ya zagaya zuwa bayan sashen mum Aisha da akwai fence a gurin me tsayi da wire na wuta Amma dayake yasan inda ake zuwa ayi disconnecting Saida yayi disconnecting bayan shigowansa.


ASH TALBA after 9 na dare ya dawo gidan daga tafiyana Dan haka Yana shiga Shima wankan yafara shiga sbd rage nauyin tafiyar da yayo.


Fitowansa wanka kenan yaji ihun Daya ratsa kunnuwansa Bai fara kawo tinanin komaiba saida ya Tina da cewan akwai 'yar mutane a gidan Kuma Sam ya manta da Hakan Dan haka da sauri ya janyo bathrobe blue ya Saka kan towel Dake qugunsa ya fito dagashi sai slippers dinsa masu taushi ya nufi hanyar palonsu da sauri Yana jefa idanuwansa kan agogon Dake palon yaga karfe goma sha Daya Dan haka da sauri ya qarasa Yana sake jiyo ihunta Wanda take ya sake shiga mamaki da qara sauri.




Yana isowa dakin Bai tsaye komaiba ya Bude tareda shiga Yana nufan inda take jikin kofan shiga toilet tanata ihu dukkanin jikinta na Wani irin rawar tashin hankali Tama fice hayyacinta gaba Daya.


Wutan dakin yafara kunnawa Kai tsaye tareda nufarta Yana kokarin kamota daga jikin bangon tana sake qanqamewa tana jikinta na jijjiga,


Kafin ma ya sake wata motsin zuwa gareta tini jikinta ya saki zata zube a gurin ya tarota da hannu Daya Yana Saka Dayan kan kirjinta ya dafe towel dinta dayake warware Yana Shirin sauka daga kirjin.




Numfashi ya sauke ahankali Yana kallan dakin ahankali Yana duba Menene matsalar,


A bayan jikin wardrobe yaga shatin takalmin babba a gurin sbd tsaftar gurin yasa shatin qurar qasa Dake jikin takalmin ya maqale.


Wani sarawa kansa yayi batareda ya gasgata abinda ya ganin ba bare tantancewa Dan bama zai yiyu ace Wani ya iya shigowa Nan dinba.


Kan fuskarta da take tayi ja ya dawo da idanuwansa ya sauke ya kalleta dakyau ahankali tareda dauke idanuwansa Yana daukanta gaba data Dan kuwa tabbas idan abinda yagani Kuma yake tinani mutum tagani Kokuma aljan.


Fitowa yayi da ita daga dakin ya nufi hanyar palonsa da ita har lokacin batasan ko matsi Batayi.




Kofar bedroom dinsa ya tsaya cak da ita sbd bayajin zai iya shiga da ita dakinsa Bai Dan haka ya juyo palonsa ya kwantar da ita kan kujera ahankali Yana dagowa towel dinta na fara zamewa da sauri yakai hannunsa ya dafesa Yana juyar da fuskarsa tareda miqewa gaba Daya ya bar gurin.


Bedroom dinsa ya shiga Kai tsaye ya Bai tsaya shafa komaiba ya Saka pyjamsa dinsa na bacci masu Dan kauri sbd bayason sanyi sosai ya dauki wayarsa ya fita Yana Kiran Jameel akan gaba Daya a bincike Mansion din ciki da wajensa.




Jameel na Jin Hakan ya sanar da securities Dan haka tini suka kunna shegun fitilinsu masu shegen haske duk da akwai haske koina gidan.


ASH din Bai fada musu abinda yake faruwaba Kuma baida niyar fadan Amma ya basu Daman duk abinda suka Gani su harbesa ko menene Dan haka suka hau dubawa a shiryensu ba sauki ba Imani suna gani zasu Ma koma Menene ko waye ruwan bullet dinsu.


Sosai suke bincike gidan ciki da waje Amma Basu ga kowa ba ko komaiba sedai sunga anyi disconnecting security electronic wire din gidan an kashe gaba Daya.




Ganin haka suka Ankara da dai Wani ne ya shiga gidan cikeda mamaki da bacin ran Wanda yakeda wannan qarfin halin suka sake bazama suna sakawa ransu koma waye wlh saisun kamasa.




AmatulMaleek cikin firgici ta Farka tasake Bude Baki zatai ihu sbd batasan inda ma take ba ga ba haske sosai a palon,
Tana Bude Baki yakai hannunsa na dama Dake kusa da ita ya Dora a bakin tareda sauke mata idanuwansa a karo na biyu Yana mata kallan da bana fizge ba,


Rawa jikinta keyi sosai ta Dora tafin hannuwanta akan nasa dayake kan bakinta zata janye hannun nasa tayi ihun sbd Bata ganesa ba a firgice take har lokacin,


Saukan hannuwanta akan nasa yasaka shi janye nasa hannun Yana kallanta zeyi magana ta fasa kuka me qarfi sbd gane waye a tareda itan tana Kiran sunan maamah da Abdul harma da Haydar.


Shiru yayi duk kuka da ambatar sunanyen datakeyi Bai motsaba kaman yanda Bai waiwayo ya kalletaba sbd dole tana buqatan kukan ta fita shock data shiga,


Ta bangare daya kuwa tinani be barkatai a ransa gameda lamarin,
Sedai Kuma anyi na karshe Dan kuwa Shima Saiya kama ko waye da hannunsa idan kuwa Wanda yake zargi ne tabbas zai Basu mamaki me girman gaske.




Kuka da tashin hankalin data shiga ya Sakar mata zafin jiki tana ji tana Gani yabarta a palon ya wuce ciki bayan ya rufe kofan palon duk da yasan koma waye ko wace giyar yasha kaddara bazata kawosa har palonsa ba.


yanda Amatu Taga Rana haka Taga Daren a firgice ta kwana,
A tsorace ta kwana,cikin rawar jiki da damuwa tareda tsananin buqatan mahaifiyarta ta kwana,
Sai guraren asuba baccin wahala ya dauketa me Dan karfi Dan haka Koda ya fito da asuba ganin tana bacci qyaleta kawai yayi ya koma ciki a cikin gida yayi sallan asubar ranar sbd bayajin zai iya fita yabarta bayan baa samu kama koma waye ba akwai yiyuwar Yana cikin gidan har lokacin Kokuma ya gudu.




Sai guraren 9 ta Farka gaba Daya jikinta ba qwari hakama kanta ciwo yakeyi sosai,


Jikinta ta kalla har lokacin towel ne a jikinta Dan haka Bata tsaya ko kallan kofar bedroom dinsa ba ta miqe daqyar Dan jiri na dibanta ta nufi kofa takai hannunta kenan zata Bude ta fice shikuma Yana Bude ta bedroom dinsa Wani sanyin AC tareda qamshinsa ya huro Bata juyo ba Bata Kuma tsaya ba ta Bude kofar ahankali ta fice cikeda kunya da baqin cikin yanda rayuwar ta take Neman komawa.


Sai data fice Shima ya fito Kuma meeting ne dashi Amma Yana Dan shakkan barinta gidan ita Daya duk da yasan da rana ne Babu abinda zai iya faruwa.


Saukowa yayi shirye cikin navy blue yadin cashmere haskensa da haibansa ya fito sosai hakama kamewa da nutsuwansa,
Qamshinsa Kawa bayar musu a palon Bai tsaya yayi breakfast ba ya fice.


Yana fitowa harabar gidan Tini aka Bude masa mota ya shige suke tada motacin suka fice bayan Jameel ya bawa securities tabbacin su Saka ido sosai kome suka Gani su kawai dashi.
#MAMUH#




Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#




YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#




AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar






32
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs๐Ÿ’ฏ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ‘
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku๐Ÿ’ฏ๐Ÿ‘*


MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER


08142800199
07068558096




*************
AmatulMaleek na fitowa bullowa palonsu su Farida na palon suna aiki shiyasa ta Jin Dan qarfin halin iya shiga dakinta har lokacin zuciyarta a Bata bugawa daidai ta Bude dakin ta shige.


Farida da karima Satan kallanta sukai ganin kofar data fito Kuma daga ita Se towel Amma ko dagowa su kalla Basu Isa ba sun sani.


Tana shiga dakin toilet ta nufa da sauri ya shige tareda rufewa Yana sakarwa kanta ruwa.


Ajiyar zuciya ta ringa saukewa tana Jan numfashinta Dake Neman shidewa cikin ruwan dayake saukar mata,
Ta jima a Hakan kafin Wani irin kuka me sanyi ya zuwar mata tana Jin kaman batada kowa,
Jin takeyi ko Husnah da Bata tareda mahaifiyarta Bata kaita maraicin uwa ba,
Bata taba Jin damuwan yanda maamah take fifita kulawan Husnah akanta ba sai yanzu,
Ina zata Saka rayuwart gameda wannan kaddarar Dake farautarta?
Batada tabbacin zata ringa tsira daga wannan mummunan kaddarar koyaushe,
Dan uwanta da Haydar dinta dasuke ture damuwar kowa su tsayu a tata basa tareda ita,
Mahaifiyarta Bata tareda ita Yaya zatai da wannan mugun abun dayake bibiyanta?
Da ASH TALBA Baya gidan a Daren zata iya mutuwa sbd tashin hankali da firgicin data samu kanta.




Kuka tayi sosai a toilet din idanuwanta suka kumbura sukai jajir kafin ta bawa kanta hakuri ta fito jiki ba qwari.


Dayake su Farida sun gyare dakin sunyi komai kafin ta fito sai Babu alaman komai na abinda ya faru jiyan
Sanyin AC da qamshin me dadi ne kawai yake tashi cikin dakin.


Batada karfin tsayawa shirywa gaban mirror Dan haka ko Mai Bata iya shafawa ba body mist kawai ta iya shafawa ta Saka Riga da wando masu Dan kauri ta koma kan gadonta ta Haye ta kwanta Dan ko apatite na cin abinci batada shi.


Daki karima ta kawo mata abincin ganin bata fitoba,
Yanda karima ta ajiye abincin har Azahar tayi Yana gurin ajiye Bata iya saukowa taci ba.


Sallan Azahar tai tayi addua sosai tana hawaye tana fadawa Allah damuwarta sbd batasan ma Yaya zatayiba.


Shiru shiru Bata fitoba duk ayyuka da abincin dasu karima sukaita kawowa suna jerawa Bata Ciba,
Kowacce daqiqa Daya idan ta wuce yammaci na kusantowa tareda dare tsoro ne yake cika zuciyarta.


Ana yin laasar ASH ya dawo gidan sbd hankalinsa Daya rabu biyu,Rabi akan aiki da tafiyan Dake gabansa a gobe Rabi Kuma akan Amatun Dake gida ba kowa hakama Yana tinanin tinda su Husnah Basu dawoba Kuma gashi kusan sati biyu koma fiye zasuyi yanason turata ta bisu Amman Kuma case da Akai na Faisal da familyn yasaka Bayajin zuwan nata acan yanada amfani,
Farha Kuma baijin tanada karfi ko iKon da zata iya tare Amatun idanma akace ta dawo gidan kafin dawowansu.




Jin shigowan motocinsa gidan ya Sakata Dan Jin sauki Sauki a tareda ita harta iya Dan daurewa taci abincin kadan Amma har lokacin ta kasa kunna wayarta sbd Batasan me zata fadawa maamah ba bayan tasan koma yayane itama tana buqatanta,


Ana yin magrib ta tashi jiki ba qwari Tayo alwala ta fito jikinta na tsananta sanyi hakama Kwanciyar hankalin zuciyarta na lalacewa sbd ganin duhu Dake Sako kai.


Kafin sallan ishai sbd ragewa Kai firgici da tashin hankalin datake ciki ta fita zuwa kitchen din dayake palon Dan dafa masa tea din data Saba dafawa a kwanakin.


Tinda ya dawo Bai fito ba sai da Akai kiran sallan magrib ya fito sanyeda dark ash jallabiya me tsananin santsi da taushi qamshinsa na Dan tashi ahankali ya nufi masallacin gidansa
kana ganinsa kasan hutawa yayi yanda ya kamata shigarsa gidan sbd bacci yayi bayan ta tashi wanka yayi ya shirya ya fito sallan.


Ma'aikatan gidan nasa suna ganinsa duk suka miqe suna tasowa ya daga musu hannu Yana Dan girgiza Kai a natse Yana cewa


"No,muyi sallah tukuna shine a gaba"


Gaba sukai zuwa cikin masallacin suka bi sahu Dan tada sallah.


Naufal Dake dakin mum Aisha cikin azababben duhu da zafi sbd komai a kashe yake hakama baida iKon ko motsawa bare kunna Wani abu a dakin asan akwai mutum ciki,
Azababbiyar yunwa da tsoro ne fal cikeda zuciyarta sbd Bai tsaya tinanin komaiba ya shigo gidan gashi fita ta gagaresa hakama a kunnuwansa yaji umarnin ASH na a harbe duk abinda aka Gani mutum ko Dabba ko aljan,
Daqyar yake iya motsawa sbd wahala da yunwa da tashin hankalin yanda zai fita yabar gidan.


Kaman Wanda baida kafafu a iska yake tafiya haka ya fito dakin Dan Daman dakon su shiga sallan magrib yakeyi duk da yasan akwai christians a ciki securities din da basa sallah suna tsare da Gidan amman dai ficewan bazata masa wuya ba tinda sunsan shi Dan gidan ne Kuma basusan shine ya shigo jiyanba da aketa nemansa.


Yana fitowa ya fara Sanda zufa na jiqasa koina idanuwansa kaman zasu fado ya fito Yana nufo hanyar kitchen da zata basa Daman ficewa da sauri.


Adaidai lokacin ne ita Kuma AmatulMaleek tana kitchen din ruwan zafin dayake Kan gas din yakusa tafasa Dan haka ta juya ta dauko flask kenan sukai arba da juna ya shigo baisan da itaba itakuma ta juyo Bata San da Shiba.


Sakin flask din hannunta tayi gabaki daya jikinta na daukan rawa ta Bude Baki da karfi zata Saki ihu
A rikice ya fizgo butan ruwan zafin Dake kan gas din Yana watsa mata ruwan tayi saurin yin Baya tana juyawa ruwan ya sauka a bayanta cikin matsananciyar azaba ta saki ihu me karfi shi kuwa ganin komai na Neman lalace masa ya tafi lahira ba shiri ya sanyashi cikin rudewa da tashin hankali Yanke shawarar bankawa kitchen din wuta yanda kafin a biyosa sai an tsaya cetan Amatun ya samu ya gudu.


Qananun towels da aprons dake Jere a kitchen din ya fizgosu duka ya jefa kan wutar gas din Dake ci Yana sake kwaso wasu kayan duk ya zuba
Yayo kanta tana zube qasa bayanta da gefen wuyanta da ruwan zafin ya taba suna Wani irin azababben azaba baiyi wata wata ba ya daga hannu zai mareta karima data shigo kitchen din ta qwalla qara me karfin gaske tana ambatar wuta.


Hayaqi da duhu tini ya cike kitchen din hakama wutan sosai ta kama duk da ruwan Dake kokarin kashe wutar Amma Sam abin ya gagara ga gas.


Ihun karima ya Saka Naufal bangajeta Yana fitowa da gudu yayi Baya,
Daidai isowan ASH su Jameel da securities na bayansa Kai karima Dake rawar jiki tana kuka ya kalla yace


"Abeeda fa??


Shiru tayi tana zare ido a rikice sbd batasan waye Abeedan ba Dan haka Bai tsaya sake Batawa kansa lokaci ba ya fada cikin kitchen din da wutarsa ta fara yawa sosai.


Cikin saa a kofa yayi tintibe da ita ya sunkuya ya daukota gabaki dayanta Yana fitowa


Muryansa a Bude abinda kowa baitaba jiba yace


"Kota yaya karya fita gidan Nan ku harbesa idan yaqi tsayawa"


Aikuwa tini suka bi bayan Naufal a tsiyace kan kace me Yana Neman guduwa ASH da Amatu ke jikinsa har lokacin cikin sautinsa Daya sake gigitasu yace


"Ku harbi duka qafafun bastard din,duka biyun ku harbesu"


Aikuwa take suka sakarwa kafafun Naufal din wuta kowacce harbi daddaya sukai mata take ya zube a gurin bayan Wani mahaukacin ihun Daya saki Yana cewa ya mutu.


Jameel ne ya Bada umarnin a kira ambulance ta daukesa zuwa asibiti hakama a kira Police suyi handing case dinsa su sungama dashi.


ASH juyawa yake Neman yi zuwa cikin gidan da ita Amma tini wutar tayi qarfi Ashe Dan haka da sauri akai Baya ana kokarin zare cylinder na gas da wainda suke Jere a bayan kitchen din ana ficewa dasu.


Gobara dai sosai da sosai ta kama gidan Dan haka dole aka fitarda mota aka dauke ASH daga gidan tareda Amatun kafin asamu kashe wutar before ta kama koina gidan.


Kai tsaye gidansa Hilton aka wuce dasu sbd duka gidajensa Dake garin akwai mutane a cikinsu haya ne da dai sauransu,
Ko kafin su Isa Jameel yayi making reservation Dan haka suna Isa Kai tsaye batareda sunbi ta main hall ba suka hau lift zuwa suite da aka kama.


Kwantar da ita yayi Yana taba jikinsa wayarsa Bata tareda shi Dan haka dole da landline yayi amfani ya buqaci likita ko nurses.


Babu Bata lokaci nurse biyu suka iso dakin tareda Neman izinin shigowa.


Suna shigowa da hannu Daya ya nuna musu inda Amatun ke kwance tana motsawa a hankali ta farfado sedai radadin datake ji abayanta da wuyanta.


Dubata sukai cikin kulawa sosai sukaga konuwar bata Riga ta taso ba Dan haka cream na qonuwa kawai suka bayar tareda Dan maganin zazzabin dayake Neman rufeta jikinta na rawa.


Bayan ficewarsu daga shi har ita Babu Wanda ya motsa bare magana,
Bacin Rai da fushi me tsananin gaske ne a cikin ransa Amma a Fili Babu me iya gane Hakan.


Ita kanta rawar da jikinta keyi da azaban datake ji yasa ta kasa ko dogon motsi Se hawaye masu dumin dasuke bin fuskarta.




A haka lokaci me tsayi ya tafi kafin ya miqe ya shige toilet sbd alwalan sallar ishai da Akai tin kafin isowansu.


Yana idar da sallah Jameel na zuwa ya kawo masa wayoyinsa da duk abubuwan buqatansa tareda sanar dashi an kashe wutan hakama masu aikin suna Nan Babu abinda ya samu bangarensu.


Maganar tafiyarsu gobe da safe yakeson yayiwa ASH din Amma baiga fuska ba sbd ran Maza a bace yake shine kadai yake iya gane tsananin bacin ran ASH din.


Shiru yayi tareda yimasa saida safe ya wuce Yana fidda wayarsa Dan siyawa Amatun ticket itama tinda dai Babu yanda zaayi Takoma gidan a wannan halin din da Naufal angama da matsalarsa bayajin har abada zai sake tafiya da duka qafafun biyu sedai Daya idan anyi dace ma kenan.


Mansion din ya sake komawa ya Saka karima dubo masa handbag din Amatun me daukesa wallet nata na Id cards da komai Yana Karba ya fito Saida yafara siyan ticket nata na tafiyan nasu kafin ya wuce gida Dan tafiyar safe zasuyi zuwa Lagos kafin daga can su zasu wuce Ghana.
#MAMUH#




*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at๐Ÿ‘‡
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070




Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#




AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar




33
*_REALTASTE 247 CATERING SERVICES_*


*_ASLM ALAIKM_*
*_Yan uwa abokan arziki yan gayu masu bikin alfarma na manyan mutane da

Please Login or Register in order to submit comment