Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'in motarsu motar Alhaji Buba mai gwala gwalai na shawo kwana da wani mota a biye dashi abayansa da excort d'in motar 'yan sanda sabida kud'in da suka d'auko


A lokacin da Abdullahi yayi wa Alhaji buba mai gwala gwalai bayani jikinsa ne ya hau rawa zufa suka hau keto mishi


Kwantar mishi da hankali sukayi suka ce su dai bukatarsu ya d'ebi iyalinsa da dukiyarsa su bar gidan duk wani Abu da yasan mai Mahimmanci ne ya kwashe yabar komai a hanunsu



Jikin Alhaji Buba mai gwala gwalai na rawa yace musu ko dai su bar garin Abdullahi yace aaa ya dai samu wani wajen ba sai ya bar garin ba kar ya damu he is save


A takaice a Daren Alhaji Buba mai Gwala gwalai suka bar gidan da iyalinsa da dukiyoyinsa suka koma wani gidansa dake can wajen gari har da 'yan sanda biyu masu gadin shi


Babu komai a gidan daya wuce furnitures da kayan kallo


Alhaji Bala kuwa Allah Allah yake gari ya waye ya d'auki hanyar kano dan yasan account d'insa zai cika da kud'i kuma Alhaji Buba mai gwala gwalai yana da lafiyayyun abinci masu numfashi da zai ci ya koshi



Tunda Asuba Alhaji Bala ya d'au hanyar kano


A lokacin guda suka isa kano dasu Killer


Sai da suka ci suka sha suka huta ya kalli Akram fuska a d'aure yafara magana yana "Akram a yau kai zaka zama oga awajen operation d'in da zamuyi ayau sai kaci abinci dole duk Wanda yayi mana gardama inaso ka shek'a shi har lahira abaya nayi tolerating d'in ka not any more yanzu Dole ka ringa participating idan muka fita operation kaji ko baka ji ba"


Akram da sauri ya gyad'a masa kai yana "insha Allah"


Alhaji Bala kuwa yayi tsaki ya kwanta yana hararo yanda zai huta ajikin 'ya'yan Alhaji Buba mai gwala gwalai



K'arfe d'ayan dare dot suka dira cikin gidan kasancewar Alhaji Bala yasan description d'in gidan shine agaba yana leading d'insu Akram kuma yana biye dashi da wani dogon bindiga a a hanun shi sai zare ido yake alamar no mercy


Majestically Alhaji Bala ya zauna akan dirka dirkan kujerun dake girke a palon ya d'ora k'afa d'aya akan d'aya yana girgizawa tare da karewa palon kallo su lion kuwa tuni suka raba Kansu dan su taso mutanen gidan ciki kuwa har da Akram dake ta Abu azafafe kamar gaske......
[2:38PM, 4/7/2018] 鈥�+234 806 462 6766鈥�: 馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫


*Written by*
馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝


*A heart touching story*



庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




*Follow me on Wattpad@Sadnaf*


*Page 10*


Alhaji Bala wani irin murmushi ya ringa yi shi kad'ai a lokacin da yake bin ko ina da kallo yana hararo irin dukiyoyin da zai tafi dasu


Lion da Killer a tare suka dawo palon a gigice suna "oga babu kowa fa a gidanan babu inda bamu duba ba"


Adai dai lokacin da Akram da black suma suka fito daga d'aya d'akin dake cikin palon suma suna "Oga wlh mun duba ko ina babu alamar mutane a gidan ballantana kaya"


"What"!!!! Alhaji Bala yace yana mik'ewa hankalinsa a tashe a tsawace yace " spread yourself and check every where ina zasu je sai Dana samu information sosai akan Alhaji Buba mai gwala gwalai kafin mu taho"


Da Sauri suka k'ara raba Kansu suna duba ko ina Akram kuwa kamar gaske har da cilli da duk abinda ya gani



Alhaji Bala bin bayansu yayi hankali a tashe yana kuma following description d'in da Sharon ya tura masa na gidan sai gashi har a bedroom d'in Alhaji Buba mai gwala gwalai babu inda basu duba ba babu kowa kuma babu abun d'auka sune harda duba su drawer da karkashin gado


Jikin Alhaji Bala ne ya d'au rawa yana tunanin ko dai Sharon ne ya sanar dasu zasu zo shiyasa suka gudu suka bar gidan idan ba haka ba ya akayi suka San zasu zo



Rai a mutuk'ar b'ace yace cikin kakausar murya "Ku wuce mu tafi inaga ya Riga da yasan da zuwan mu"


Akram wani irin juyowa yayi in serious mode yana "waye zai gaya musu zamu zo yanzu haka zamu zo mu tafi bamu samu komai ba"



Alhaji Bala da zuciyarsa ke tafasa bai samu sararin bashi amsa ba sabida b'acin rai ya sa kai ya bar palon da sauri suka Mara mishi baya



Akram kuwa yayi ta godewa Allah aransa yana "soon zaka zo hannu dan iska kawai"




Indai zasu je operation black ne ke Jan motar amma Alhaji Bala da kansa yaja motar sai gudu yake falfalawa


Su Killer dai kallonsa kawai suke Dan sun San ransa a b'ace yake wani daji ya yanka da basu San dashi ba yana ta kutsawa ciki suna ta so su tambayeshi suna tsoro


Parking yayi awani k'ofar gida ya fito a fusace su killer suka Mara mishi baya da sauri


Alhaji Bala buga k'ofar yake kamar zai b'alla k'ofar


Sharon dake kwance shi da buduruwarsa suna bacci a firgice suka tashi jikinsu na rawa suka kankame juna suna Neman wajen b'uya




Alhaji Bala ganin babu alamar za'a bud'e gidan ne ya sa ya kalli Lion atake Lion ya gane mai yake nufi ya dalle katangar gidan tare da dira ciki ya bud'e musu k'ofar



Akram kuwa hankalinsa ne ya tashi yafara tunanin mai suka zo yi a gidan Allah yasa ba wani muguntar Alhaji Bala zai yi ba adai dai lokacin da suka shige suna bin Alhaji Bala a baya


Akram sai addu'oi yake aransa




Bugu d'aya Alhaji Bala yayi wa k'ofar d'akin Sharon ya Bud'e



Sharon da buduruwarsa har fitsari suka saki awando sabida tsorata da sukayi


Alhaji Bala ya tsaya daga bakin k'ofa yana bin Sharon da wani mugun kallo jijjiyoyin kansa a tatashe



Sharon kuwa ganin Alhaji Bala ne da yaransa yasa ya sauke ajiyar zuciya yana dafe k'irjinsa yana "Oga Ashe kai ne ai da ka kirani awaya wlh ka tsorata mu"



Wani mugun tsawa Alhaji Bala ya daka mishi yana "Ni zaka Yaudara Sani ni zaka ciwa amana nasaka ka aiki na biyaka kud'inka a karshe ka zagaye kaje ka fad'awa Alhaji Buba akan ya gudu yabar gidan za'a zo ayi mishi sata ko"




Sharon jikinsa ne ya hau rawa cikin in ina ya fara girgiza kai yana "wlh tallahi ban gaya mishi komai ba karka manta Oga ba yau na fara maka irin wanan aikin ba"


Alhaji Bala ransa a b'ace ya nufi wajen Sharon a tunzure ya shak'o vest d'in jikinsa ya had'a shi da bango yana "u would pay for all I loss babu Wanda ya isa yaci amanata na kyalle shi"



Akram Sallati kawai yake a cikin ransa dan yasan sai Alhaji Bala ya kashe Sharon



Alhaji Bala a tsawace ya kira sunan Akram yana "Shoot him"



Sharon kuwa ya zube a k'asa ya rik'e k'afar Alhaji Bala yana rok'on shi



Akram kuwa jikinsa ne ya d'auki mugun rawa Dan bazai iya kissan kai ba shima yasan rashin Harbin zai sa asirinsa ya tonu Dan Alhaji Bala yace indai suka k'ara fita operation sai yayi kisan kai idan yak'i kuma Alhaji Bala zai d'ago shi


Wani tsawan Alhaji Bala ya k'ara buga mishi yana "ka Harbeshi nace kana b'ata min lokacin "



Akram d'aga bindigar yayi duk da yasan ba iya Harbin zai yi ba Hannunsa sai masifar rawa yake adai-dai lokacin da buduruwar Sharon ta tafi da gudu ta fad'a jikin Sharon tana "please don't kill him he is the only one i have pls I beg of you sir"


Da yake buduruwarsa Yoruba ce kuka take sosai tana rungume da Sharon da jikinsa ke rawa gumi na keto mishi ko ta ina


Wani irin bak'in ciki ne ya rufe Alhaji Bala yace a tsawace "Akram shoot the both of them before counting of two"


Akram jikinsa ne ya cigaba da Rawa shima take ya jike da Gumi


Alhaji Bala kuwa ya nufi wajen Akram yana "zan harbeka wlh ka Harbesu Nace"


Alhaji Bala yace yana buga k'afarsa da k'asa



Buduruwar Sharon kuwa sai ihu take


Tsabar rawar da jikin Akram keyi bindigar sub'alewa yayi daga hannunsa


Alhaji Bala ya d'auki bindigar hannunsa ya bugawa Akram akai sau biyu


Akram ya saki wani gigitacen k'ara a lokacin da jini ya wanke mishi fuska tare da fad'uwa k'asa




Alhaji Bala ya juya a fusace ya sakarwa Sharon bullet akai sau biyu ya sakarwa buduruwarsa a kirji



Wurgar da bindigar yayi ya cakumo Akram da hannu biyu yafara jijjigashi yana "mai kake nufi Kana cikinmu bazaka iya kashe mutum ba sau nawa zan gaya maka aikinmu babu imani babu imani sau nawa kake so na gaya maka this would be the first and last da zan saka ka kayi Abu ka k'i yi wlh if u try it again I would kill you".


Yace yana wurgar dashi tare da yin waje



Lion yayi sauri ya taro shi Akram ya rik'eshi sukayi waje kansa kamar ya fad'o





A ranar Sam Alhaji Bala bai yi bacci ba bak'in cikin kud'in da bai samu ba da abincin da bai ci ba kawai yake acan k'asan ransa kuma yana mugun jin haushin Akram


A daren ya fara tunanin gidan Wanda zai kuma zuwa acikin garin kano a gobe da zai samu makud'an kud'i



B'angaren su Saiam kuwa tunda aka d'aura Auren Saiam da Fawazz da Safna da Faisal suke iya k'ok'arinsu wajen kwantar musu da hankali da faranta musu rai ta hanyar zuwa gidan su had'u gabad'aya a Palon gidan suyi ta jansu da hira har dasu Samha



Hakan kuwa ba laifi ya taimaka wajen kwantar musu da hankali Dan su Samha gani suke tamkar 'ya'yyensu ne su Fawazz


Hakan kuwa ba k'aramin dadi yayi wa Alhaji Nazifi ba dan yaran nashi sun d'an fara farfadowa ba kamar da ba duk da kullum cikin dare in suka zo kwanciya a cikinsu sai wata ta zubar da hawaye sabida Hajiya Nafeesa lokacin da take raye kafin su yi bacci sai tazo ta tayasu hira idan sunyi bacci ta tofesu da addu'oi takan lekosu sau d'aya biyu kafin gari ya waye basu tunaninta ma su zubar da hawaye sai sun zo kwanciya kullum cikin tsinewa Alhaji Bala suke suna tashin dare akan Allah ya tona mishi asiri


Duk da Nazifa wata cousin d'in Alhaji Nazifi da mijinta ya rasu shekara uku da suka wuce itama tana bakin k'ok'arinta wajen ganin tana d'ebe musu wanan kewa daddare hakan bai sa sun kasa tuna mahaifiyarsu ba


A ranar da akayi sadakar Arbain tamkar aranar akayi rasuwar sabida yanda aka cika gidan Alhaji Nazifi inda mutuwarta ya k'ara dawo musu sabo fil addu'oi kawai ake bin hajiya Nafeesa dashi ana fad'ar kyawawan halayenta Alhaji Nazifi kuwa aranar har da d'an zazzabinsa


Bayan kwana uku da akayi Arbain d'in Hajiya Nafeesa aka fara shirye shiryen tariyar Saiam Safna inda hankalinsu ya tashi gabad'aya in banda kuka babu abinda suke yi Dan basa so su rabu da juna ko kad'an ganin junan da suke yi ya na d'an rage musu kad'aice



Da kuka da k'yar aka banbare su Samha daga Jikinsu Saiam a lokacin da aka zo tafiya dasu gidan mazajensu Alhaji Nazifi ma sai da ya koka sosai aka rasa wanda zai rarrashi wani a cikinsu



Aranar babu Wanda ya runtsa a cikinsu dan gidan wani irin girma da fad'i ya kara yi musu



Inda b'angaren amaren amadadin amarci angwayen kwana sukayi suna aikin rarrashi dan Saiam har da zazzabi


Wasa wasa sau Hud'u Alhaji Bala ya na fita operation inda suka je babu abinda suke samu gidan empty suke samun shi nan kuwa aikin Akram ne dan yana fad'a musu inda zasu je operation zai yiwa Ogansa Abdullahi text message duk da Alhaji Bala ya sa mishi ido sosai dan haka kawai yafara d'orawa Akram karan tsana


Aranar da Alhaji Bala yaje gidan wani Alhaji Tahir Hamshakin mai kud'i da ya tada kai Alhaji Bala baije gidan ba sai daya tabbatar da akwai kud'i a gidan kuma iyalansa na nan da confidence d'insa ya had'a Kansu Killer suka je suna zuwa suka tarar da gidan wayam babu kowa ballantana a samu abun d'auka


Jikin Alhaji Bala ne ya hau rawa hankalinsa a matuk'ar tashe yana mamakin abinda ke faruwa dashi ji yake kamar ya zauce


Su Killer kuwa tuni hankalinsu ya tashi suka fara zargin duk yanda akayi an fara ganosu idan ba haka ba ya akayi duk inda suka je basa samun kowa



Zaman dirshan Alhaji Bala yayi a k'asa ya d'ora hannu aka yana tunanin abinda ke faruwa dashi take mai gida ya fad'o mishi arai da a lokacin da yake raye ne da yanzu ya fad'a mishi abinda ke faruwa dashi yanzu wa zaije ya samu baya San zuwa wajen Na maliya dan bai San mai zai ce ya bashi ba a ladan aikin da ya mishi Hajiya Nafeesa ta daina zuwar mishi to ya zai yi dolensa dai yaje wajen nasa dan shi kad'ai zai iya gaya mishi abinda ke faruwa dashi da duk inda yaje baya samun abinda yake so



Da wanan tunanin ya shirya da sassafe bayan ya sallami su Killer yace zai musu waya ya d'auki hanyar sokoto


Yana isa wajen Na Maliya yafara arba da ruwa mai yawa yana ambaliya kamar zai yo kansa a tsorace yaja ya tsaya yana ganin yanda ruwan ke yowa kansa baya ya fara yi da sauri adai dai lokacin da ruwan ya b'ace bat sai ga Namaliya agabansa sai yawo yake a saman ruwa fuskar nan tashi a murtuk'e


Gaban Alhaji Bala na fad'uw ya zube a k'asa kamar zai mishi sujadda bai d'ago ba Na maliya ya fara magana cikins wanan irin murya yana "Kura kana wasa dani ya mukayi dakai"


Jikin Alhaji Bala na rawa yace "Kayi hakuri nayi maka laifi Allah ya huci zuciyarka yanzu ka fad'amin ladan aikina ko menene ko nawane zan bayar akwai kuma wani gagarumin matsala dake tafe dani"


Wani Mahaukacin Dariya Na Maliya ya fashe dashi sai da yayi dariyar na wajen minti goma kafin ya tsagaita yace "ya zama dolenka ne ka bayar da ladan aikin da nayi maka idan ba haka ba sai ka gwammaci ace mutuwa kayi da ace kana rayye bazan kuma saurarka ba har sai ka biya ladan aikin Dana maka da farko kafin na Saurareka"



Alhaji Bala jiki na rawa a tsorace yace "menene Ladan aikinka"?


Na Maliya dariya ya k'ara fashewa dashi yace " ladan aikina shine ka kawo min Naila in ba Aljanina dan Saurayi ya huta da ita na wata uku bayan wata uku kazo ka d'auketa"



Alhaji Bala bai San lokacin da ya mik'e tsaye ba yaji kamar guduma ake kwada masa akai kirjinsa kuwa kamar ya fad'o cikin inina yace "Na Maliya bazan tab'a iya baka Naila ba Dana baka ita gwara ni ka kasheni banida sama da ita arayuwata zan iya sadaukar da komai nawa sabida ita Haba Na Maliya ya za kayi min haka dan Allah ka fad'i wani abun na baka ni ko Mahaifiyata ce ma dan Allah banda Naila"



Murya a k'aushashe Na Maliya yace "baka isa ba dan Dana maka aikin sai Dana baka sharad'i ka kuma yarda dan haka dole ka kawo min ita nan da sati d'aya ko kuma duk abinda ya biyo baya kai ka siya da kud'inka dan sai ka nemi mutuwa ma ya d'aukeka sabida tashin hankalin da zan jefaka a ciki



Alhaji Bala zubewa yayi a k'asa take hawaye ya hau wanke mishi fuska yace " Na Maliya ka rufa min asiri karka min haka dan Allah zan kawo maka Mahaifiyarta zan kawo maka Mahaifiyata amma dan Allah banda Naila dan Allah ka taimaka min wlh Naila yarinya ce shekararta goma sha biyar"



Na Maliya Wani Mahaukacin dariya ya k'ara kwashe wa dashi yace "ko matan duniyan nan zaka bani bana so Naila nakeso ka kawo min idan ba haka ba duk abinda ya biyo baya kai ka siya da kud'inka na baka nan da Sati d'aya ka kawo min ita"


Bat Na Maliya ya b'ace Alhaji Bala ya saki wani gigitaccen k'ara yana "wlh bazan iya ba Na Maliya bazan iya baka tilon 'yata ba gwara ka kasheni Dana baka ita"



A haka Alhaji Bala ya kwanta a k'asa yana ihu da kururuwa akan bazai iya bawa Na Maliya 'yarsa ba sai da yaga wajen ya fara duhu sosai ya mik'e ya bar wajen sai kuka yake kamar wani k'aramin yaro.....馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀



Alhaji Bala yaga ta kansa ooo ni 馃槀馃槀馃槀
[2:38PM, 4/7/2018] 鈥�+234 806 462 6766鈥�: 馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫


*Written by*
馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝


*A heart touching story*



庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




*Follow me on Wattpad@Sadnaf*


*Page 11*





Hajiya Lubna da Naila dake zaune a Palo suna kallo wajen k'arfe goma sha d'aya na dare a firgice suka mik'e a lokacin da suka ga Alhaji Bala ya shigo k'afa babu takalmi yabi ya fita daga hayyacinsa idon nan nasa yayi jazur



Hajiya Lubna sallati kawai ta ringayi har Alhaji Bala ya zube akan kujera yana dafe da kansa


Naila da Sauri ta matsa kusa dashi tana "Daddy mai ya sameka"



Alhaji Bala d'agowa yayi tare da cire hannunsa daga kansa a lokacin da ya k'urawa Naila ido hawaye masu zafi suka hau zubo mishi wai princess d'insa daya ke jinta tamkar ruhinsa ita zai kaiwa Na Maliya a lalata ta har na tsawon wata uku da ace yasan abinda Na Maliya zai nema kenan gwara ace Fatalwar Hajiya Nafeesa tayi ta bibiyarsa har ya mutu bazai tab'a iya kai Nailarsa wajen Na Maliya ba yayi duk abinda zai yi



Naila hankali a tashe ta hau sharewa Alhaji Bala hawaye itama hawayen ya hau zubo mata tana "Daddy mai yasa kake kuka mai ya faru"


Hajiya Lubna sakin baki tayi tana kallon ikon Allah Dan zata iya cewa this is the first time data ga hawaye a fuskar Alhaji Bala ko a lokutan baya da yake cikin tashin hankalin da bata San abinda ya haddasa ma sa shi ba bata ga yana zubar da hawaye ba kamar yanzu




Alhaji Bala hannayen Naila ya ruk'o yana "Angel insha Allahu indai ina rayye babu Wanda ya isa ya cutar dake I would protect you with all I have banida sama dake a rayuwata zan iya yin komai akanki babu wanda ya isa ya keta miki haddi sai dai idan bana numfashi


Hajiya Lubna da sauri ta mik'e jikinta na rawa ta nufi wajen Alhaji Bala tana " Alhaji wai mai yake faruwa ne waye zai tab'a Nailan"?


Alhaji Bala mik'ewa yayi ba tare da ya kalli Hajiya Lubna ba ya nufi b'angarensa



Hajiya Lubna tayi sauri ta sha gabansa tana "Bala magana nake maka kayi min bayani waye zai cutar da Naila"?



Alhaji Bala matsawar da Hajiya Lubna yayi ya nufi d'akinsa Dan a halin da yake ciki baya jin zai iya wani dogon magana



Hajiya Lubna bin bayansa tayi da kallo har ya shige d'akinsa


Juyawa tayi ta kalli inda Naila ke zaune ta had'a tagumi da hannu biyu hawaye na ta zubo mata Dan Sam bata gane mai Alhaji Bala yake nufi ba



Aranar Alhaji Bala ko runtsuwa bai yi ba yana saman gado a zaune yana ta tunanin yanda zai biyowa Na Maliya Dan Sam ba zai iya kai tilon 'yarsa ba



A takaice sai da Alhaji Bala ya zama tamkar wani zararre sabida fargaba da tsoro dan gani yake Tamkar Na Maliya zai iya zuwa ya d'auke Naila



Hajiya Lubna ta k'asa gane kansa tambayar duniya tayi mishi akan ya gaya mata abinda ke faruwa yak'i ya gaya mata


Aranar da aka samu kwana uku da dawowarsa daga wajen Na Maliya yana zaune a d'akinsa ya buga tagumi yana tunanin yanda rayuwa take juyawa dashi sai ayanzu yake daya sani bai kashe Mai gida ba Dan yasan mai Gida bazai tab'a masa haka ba yana ganin shima Kashe Na Maliya kawai zai yi ya huta inya so idan ya gama dashi sai ya San abun yi akan operation da yake fita babu Nassara


Da wanan tunanin ya samu hankalinsa ya d'an kwanta washegari ya d'auki Hanyar sokoto da sassafe da zumar zuwa ya kashe Na Maliya




B'angarensu Akram kuwa sun gama shirya yanda zasu damke Alhaji Bala Dan sunga alamar ya fara d'ago Akram sabida mugun sa mishi ido da Alhaji Bala yayi Dan a ranar da zai tafi sai da yace mishi idan suka kuma fita wani operation d'in Akram bai tab'uka abin arziki ba babu abinda zai hana ya kashe Akram




Kwana biyu da tafiyar Alhaji Bala ogan Akram Abdullahi yayi arranging d'in motocin 'yan sanda aka je akayi arresting d'insu Lion gabad'aya

Akram dake cikinsu a hankali ya fita daga tsakiyarsu yayi joining d'in yan sandan ya zaro I D card d'inshi ya nuna musu yana Murmushi



Mamaki ne ya hana su motsawa sakin baki kawai suka yi suna kallon Akram kamar wani sabon hallita


Akram d'aya bayan d'aya ya bisu ya kwace wayoyin hannunsu da bindigogi aka tasa keyarsu aka yi waje dasu



Killer k'asa hakuri yayi sai da yace "Ak meyesa ka yi mana haka Ashe shigowa kayi cikinmu Dan ka San sirrinmu you are not part of us y Akram y"?



Akram murmushi yayi yace " am Neva part of you guys nayi pretending Na zauna a cikinku Dan nasamu enough evidence akan Ku da Mai gidanku Alhaji Bala Alhamdulillah Na samu more than enough evidences"


"Yaro take them away"

Da sauri d'an Sandan da aka kira da Yaro ya tasa keyarsu Killer suka shige motar



Su Akram suka bisu a baya



Alhaji Bala kuwa b'oye bindigarsa yayi a wandonsa gabansa Na fad'uwa ya nufi inda Na Maliya ke zama Dan ya yanke a ransa zai yaudari Na Maliya ne akan ya amince idan ya sakankance sai ya zuba mishi Harbi


Tun kafin ya k'arasa Ya fara jiyo dariyar Na Maliya mai barazanar toshewa mutum kunne
jiki na d'an rawa Alhaji Bala ya k'arasa yana nan a zaune a saman ruwa sai yawo yake yi


Zubewa yayi agabansa kamar zai yi mishi Sujadda Na Maliya kuwa ya cigaba da kyalkyala dariya


Alhaji Bala ganin yak'i ya mishi umarni daya d'ago ne ya sa ya d'ago Dan Ya Kalleshi ga mamakinsa sai ganin bindigarsa daya b'oye a wandonsa yayi akan ruwa a gefen Na Maliya



Da Sauri ya mik'e tare da kai hannunsa wajen daya b'oye bindigar yaga babu komai


Na maliya kuwa ya cigaba da kyalkyala dariya


Wani irin tsoro ne ya rufe Alhaji Bala Na maliya kuwa ya tsayar da dariyar da yake yi yace "ka bani tausayi ka d'auka k'arfina dana mai gidanka daka kashe d'aya ne to idan kana tunanin zaka iya kasheni karyar ka ta sha karya domin a tafin hanuna kake duk wani motsin ka da shirin da kake yi ina kallonka ba zaka iya kasheni ba dan haka ka juya ka tafi ranakun Dana d'ibar ma idan sun cika baka kawo ta ba zan zo na d'auketa da kaina idan kuma ka d'auka da wasa nake karka kawo ta kagani karbi bindigar ka ka b'ace min da gani"



Alhaji Bala ja da baya yayi da sauri jikinsa na mugun rawa a lokacin dayaji bindigar a wandonsa


Zube wa yayi a k'asa yana "ka rufa min asiri karka min haka ka fadi duk abinda kake so zan kawo maka cikakkun 'yan mata guda goma zan kawo maka kud'i amma Dan Allah ka rabu da 'yata ba zan iya kawo maka ita ba



Na Maliya Dariya ya kwashe dashi ruwan da yake kai yafara iyowa kan Alhaji Bala


Alhaji Bala kuwa ya fara falfala gudu wuf yaga anyi sama dashi an Nana shi da k'asa sai gashi agaban motarsa



Aguje ya mik'e ya hau motarsa yabar wajen


Ikon Allah ne kawai ya kawo shi gida Dan Sam ba'a hayyacinsa yake ba Na maliya ya masifar tsorata shi



Yana isa gida b'angaren Naila yayi a guje dan yaga ko tana nan Dan gani yake kamar Har Na Maliya ya d'auketa








Naila dake kwance da wayarta a hannu

Please Login or Register in order to submit comment