Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Gina wani katon shago ya zuba kaya kanensa suke kula da shagon
Saude Albarka kawai take sa mishi


Watarana kuwa sun fita fashi da yamma a lokacin basu fiye zuwa gidajen jama'a ba sai dai su tare matafiya akan hanya su k'wace musu dukiyoyinsu da kudinsu


A hanyar Abuja suka yi fashin inda ogansu Chris ke tsaye yana basu umarnin chaje matafiyan suga ko akwai inda suka b'oye kud'i cikin zafin nama Ukasha da Alhaji Bala suka ringa chaje matafiyan



Matan da suka sunkuyar dakansu akwance suna rawar jiki ahankali wata dattijuwa ta d'ago sakamakon jin kamar muryar tilon danta



Arazane ta mik'e tana nuna Ukasha tana "Ukasha dama kai Dan fashi ne"



Ukasha wani irin fitsari ne ya kubce mishi ya gwallo ido yana kallon mahaifiyarsa da ke mishi wa'azi kusan kullum akan ya guji haram ya kusanci Halal yaji tsoron Allah a duk inda yake


Hannu ya d'ora akai ya zube akan gwiwarsa yana kallon mahaifiyarsa da hawaye ke gudu akan fuskarta


A take ogansu Chris ya gane mai ke faruwa wani mugun tsawa ya daka wa Ukasha yana "Who is she to you"?



Cikin rawar jiki Ukasha yace mishi " she's my mother am dead she never knew am armrobber"


Wani irin dariya ogansu Chris ya kwashe dashi yace "who ever knows our secret must die before counting of 3 shoot her she must die"





Wani mugun ihu Ukasha ya fasa yace " no boss don't do this to me all am doing is because of her I can't kill her she's my mother how can I kill her"


Wani Dariyar ya kwashe dashi yace " UK I Said shoot her if not am going to shoot d both of you"


Ukasha girgiza kansa yayi yace "I can't kill my mother pls kill me and leave her am begging you boss don't kill her pls"


Ogansu Chris counting ya fara yi take ukasha ya juya ya kalli Mahaifiyarsa data kura mishi ido hawaye kamar an bud'e famfo da sauri yafara cewa "Ummina Dan Allah ki yafemin nayi miki ba daidai ba bana so na ringa ganin irin wahalar da kike sha akanmu bana San aikatau dinan da kike yi shiyasa na zabi wanan sana'ar Dan babu hanyar da zan samu kud'i sai shi Ummi ki yafemin kasheni zasu yi Dan Allah ki yafemin"


Adai dai lokacin da ogansu Chris ya kusa gama counting 10 a guje mahaifiyarsa taje ta tsaya agabansa ta hade hannayenta tana mugun kuka tafara magana tana "Dan Allah kar ka harbe Min d'a ka harbeni na rokeka da girman Allah karka harbeshi agabana kayi hakuri"


Maganar da bata k'arasa ba kenan Oga Chris ya sakar mata bullet akai ya sakarwa Ukasha sau biyu



Wani irin ihu Alhaji bala yayi yaje wajen Ukasha yana jijjiga shi ogansu bakin bindiga ya buga mishi aka ya ja shi kamar tsumma ya jefa shi a cikin mota Alhaji Bala sai kuka yake yana kallon gawan Ukasha da mahaifiyarsa ahaka suka tafi suka bar wajen



Mutuwar Ukasha ba k'aramin girgiza Bala yayi ba atake yaji shima idan ba kashe Oga Chris dinan yayi ba hankalinsa bazai tab'a kwanciya ba


Aikuwa daddare bayan sun kasafta kud'in Ogansu Chris ya aika a siyo mishi giya Dan idan dai suka fita operation suka dawo sai yasha giya ta kusa kwalba goma



Sai da yasha yayi mankas ko hannunsa baya iya d'agawa Alhaji Bala ya d'auki bindigarsa ya bud'e mishi wuta kafin sauran suyi wani yunkurin d'auko bindigarsu ya harbe su duka sai huci yake Dan shima yanda yake jin zuciyarsa babu Wanda bazai iya kashewa ba



Had'e kan kudadden yayi yayi nashi gurin tunda daga lokacin ya zama ogan kansa inda ya samo wasu sababin yaran sune su lion dasu killer........


Insha Allah zan k'arasa tarihin Alhaji Bala ko gobe ko jibi Dan naso nayi shi yau na gama amma ina da dan tsayi
[2:34PM, 4/7/2018] 鈥�+234 806 462 6766鈥�: 馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫


*Written by*
馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝


*A heart touching story*



庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





*WANAN SHAFIN NAKU NE MASOYANA NA ASALI MASU KAUNATA TUN KAFIN SU SAMU CONTACT D'INA MASU K'AUNATA BADAN RUBUTUNA BA*


*FRESH KHADY*
*HALEEMA LEEMA*
*AISHA YAR ALJANA KAUNARKU HAR ARAINA WLH ALLAH YA BARMU TARE*馃挏馃挏馃挍馃挋馃挏馃挍馃挋馃挌鉂ゐ煉旔煉旔煉旔煉�




*My Salmab rigimamiya ina gaisuwa*




*Page 6*



Batare da b'ata lokaci ba yaje ya nemo wani boka dayake cewa kansa Mallami akan ya ringa musu aiki kafin su fita operation sabida yanayin aikin nasu akwai Hatsari


Mai gida ake cewa Mallamin inda yayi fice sosai akan tsubuce tsubuce ba iya b'arayi yake yiwa aiki ba harda matsafa da kidnappers


Kafin su fita operation sai sun fara zuwa wajensa ya duba musu akwai sa'a afitar tasu ko babu kamar kuwa mai gani amadubi dan duka yanda operation d'in nasu zai kasance Mai gida sai ya gaya musu har wani zobe ya bawa Alhaji Bala akan yasa A tsakiyar yatsan shi na hagu indai da akwai danger a duk inda suke ko kuma ana nemansu zaiji zoben hannunsa na mishi zafi



Da wanan d'aurin gindin da Alhaji Bala ya samu awajen Maigida yasa ya rufe ido yake farautar dukiyoyin jama'a da rayakansu babu d'igon imani ko kad'an a zuciyarsa tamkar yanda zaka kashe Sauro kana daga cikin d'aki haka yake kashe mutumin da ya nemi ya mishi gardama ko kuma ya hana shi kud'i ga fyad'e da bai d'auke shi a bakin komai ba dan in dai zai fita operation indai yayi tozali da mace wala mai Aure ko buduruwa to fa sai ya mata fyad'e dan yana cikin sharad'un mai gida ya ringa yiwa mata fyad'e




Tuni Alhaji Bala ya zama kungurmin dan fashi Dan yanzu ba iya matafiya yake tarewa ba har manyan gidaje yake zuwa fashi idan kuwa yaje fashi tsautsayi yasa babu kud'i a gidan to fa aranar sunanku gawa Dan bazai fito batare da ya d'auki rai ba


Ad'aya b'angaren kuwa Mahaukatan kud'i kawai yake Samu Dan bai fiye sakarwa su lion kudi ba sosai he is very selfish ga wayon masifa duk abinda su lion zasuyi idonsa na Kansu dan bayaso suyi betraying d'inshi kamar yanda yayi betraying d'in Oganshi Chris




Acikin kanensa babu Wanda bai Mallakawa gida ba banda Mahaifiyarsa da ya tamfatsawa wani katon gida da masu aiki



Albarka Saude kawai ke sa mishi Dan duk a tunaninta aikin da Alhaji Bala keyi ne Allah yasa mishi Albarka


Yan cikin garin kuwa irin kud'in da suka ga Alhaji Bala na samu ne cikin kankanin lokaci yasa suka fara tunanin ko dai yana yankan kai ne




Abinka da Kauye tuni kananan maganganun da yan garin ke yi ya koma kunen Mahaifiyar Alhaji Bala data tashi daga mai dan wanke zuwa Hajiya Saude sabida duk shekara Sai Alhaji Bala ya biya mata Umara da Hajji


Hankalinta ne ya tashi data ji abinda yan kauyen ke cewa inda ta nemi Alhaji Bala da yazo da gaggawa tana so taganshi aikuwa babu b'ata lokaci yaje ya sameta




Murmushi yayi a lokacin da Hajiya Saude ta gaya mishi zargin da ake mishi agari inda ya musanta zargin da ake mishi yace aikin mai yake yi kuma kowa yasan aikin mai na kawo kud'i



A take Hajiya Saude ta samu relief a zuciyarta ta shawarce shi akan ya ringa taimakawa 'yan garin nasu tunda yana da kud'i kuma ba laifi akwai Mabuk'ata da yawa agarin Alhaji Bala shawararta ya nema akan ta fad'a mishi wane irin Abu suka fi bukata a Kauyen


Anan Hajiya Saude ta zayyano mishi abubuwan da suke bukata



Aikuwa kafin shekara d'aya da Maganar Alhaji Bala ya tamfatsa wani k'aton makaranta asibiti da wani katon massallaci tuni ya siye zuciyar mutanen Kauyen duk Inda ka zaga kyawawan halayenshi ake Fad'i Dan kowani dan siyasan bai isa yayi kwatan abinda Alhaji Bala ke yi ba a cikin kankanin lokaci mutane suna fara Sanin Alhaji Bala da irin taimakon da yake yi dan indai kaje ka samu mahaifiyarsa ka fad'a mata matsalarka to kamar angama yi maka ne Dan tana bashi list
D'in masu Neman taimako zai bata



Tuni kowa yasan da labarin Alhaji bala ba iya 'yan garin ba dan har daga wasu jihohin ake zuwa garinsu Alhaji Bala Neman Taimako ahaka manya Manyan mutane suka San shi amma basu San ainihin Sana'ar da yake ba



Alhaji Bala ganin mutane sun sanshi da yawa ciki kuwa har da manyan mutane yasa ya fara tunanin bad'a kama sabida kar wayanda yake yiwa fashi su gane shi



Anan ya fita can k'asar waje yaje ya samu Mask mai irin fatar mutum sak aka mishi bak'in fenti ya koma yake Sawa idan zai fita fashi acikin irin wanan yanayin ya had'u da wata lubna 'yar Ethiopia suka kula soyayya acikin kankanin lokaci ya Aureta abunka da akwai masu gidan rana





Shekararsu biyu da Aure ta haifo mishi wata tsalleliyar 'ya mai mugun kama da ita dan ta ma fi Mahaifiyarta kyau nesa ba kusa ba kai kana ganinta tunani zakayi ta had'a jinsi da larabawa ga gashi



Alhajj Bala tunda yake bai tab'a San wani Abu arayuwarsa ba sama da 'yarsa Naila yana bala'in ji da ita Wanda yake ganin ko ruhinsa zai iya cirewa ya bata gatan da yakewa Naila ya wuce tunanin mai tunani Dan dai dai da makaranta daya saka ta sai da yaja wa masu makarantar warning sosai akan ta ko kud'a baya so ya tab'ata ballantana akai ga duka musamman ya samu Nanny da bata da aikin da ya wuce ta ringa kula da ita har su taso


Kowane lungu da sak'o na gidan shi mak'ale yake da hoton Naila sai data shekara bakwai ya daina kwana da ita burinsa bai wuce yaga duk abinda yagani ya siyo mata ba abunda dai ake cewa gata Naila ta same shi



Mahaifiyarta kuwa tunda ta haifi Naila bata k'ara b'atan wata ba hakan kuwa ba k'aramin damunta yake ba Alhaji Bala ke kwantar mata da hankali akan karta damu Naila kawai ma ta ishesu rayuwa

A haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Alhaji Bala yake k'ara samun dabaru da k'warewa na fashi sosai Dan har 'yan siyasa yake robbing abun shi abun yana ciwa mutane tuwo a kwarya amma an rasa Wanda yake wanan aika aikan


Watarana Alhaji Bala yaje gidan wani attajiri shi da yaransa Dan suyi fashi bayan sun gama kwashe uban kudade da gwala gwalai anan yace zai keta had'in matar Attajirin ai fa nan gizo ke sak'ar dan Attajirin fir yak'i yarda a tab'a mishi mata yace sai dai idan bayan ranshi



Da yake doka Mai gida ya basu akan idan zasuyi wa mace fyad'e kar su sake su kashe mutum sai sun gama biyan bukatarsu agaban kowa sanan idan zasu kashe mutum sai su kashe

Aifa nan Alhaji Bala yafara k'ok'awa da Attajirin da yak'i bari yaje kusa da matarshi duk gindin bindigar da ya ringa buga mishi akai jini na wanke masa fuska hakan bai sa ya hakura ya bashi hanya ba k'okawa suke sosai inda Attajirin ya kai hannunsa fuskar Alhaji Bala dan ya yak'uso mishi fuska aikuwa sai gashi ya Ciro mask d'in fuskarshi anan yayi tozali da fuskar Alhaji Bala


Ya gwallo ido cikin kinkina yana nuna shi da hannu dan shima kansa Yasan Alhaji Bala awajen taimakon talakawa


Alhaji Bala kuwa k'arasa cire Mask d'in fuskarshi yayi ya ce ya daina mamaki shine nan anan ya hau gaya mishi mugayen halayenshi da Sana'arsa inda a k'arshe ya sa su Lion suka rik'e mishi Attajirin ya ketawa matarsa haddi agabanshi


Ya harbe matarsa ya harbe mutumin sau biyu daga nan suka saka kai suka fice


Suna fita mak'ota suka shiga gidan dan duk abunda ke faruwa suna ji har 'yan sanda sun kira amma shiru basu k'araso ba har b'arayin suka tafi

Abunka da babban mutum tuni aka kaisu asibiti acikin daren duk da basu da tabbacin suna rayye


Suna zuwa aka k'arbesu Matarsa kuwa dama ta Dade da rasuwa Mijin ne dai ake ganin da alamar yana numfashi



A lokacin da likitoci suka dukufa akan shi dan ceto ransa bud'e idonsa yayi a cikin mayuwacin hali ya yafito d'aya daga cikinsu


Yana isa inda yake yayi Sauri yace ya k'ira mishi d'aya daga cikin 'yan sanda dake waje


Da sauri suka kira d'aya daga cikin 'yan sandan yana zuwa Attajirin yace da k'arfi "ba kowane ke robbering mutane ba sama da " ALHAJI BALA MAI KUD'I WANDA KE TAIMAKON TALAKAWAN NAN SHINE YAZO YAMIN FASHI YAYI WA MATATA FYAD'E YA HARBETA YA HARBENI"


Cikin sauri sauri Attajirin ya gaya musu yanda sukayi da Alhaji Bala inda mamaki ya hana d'an sandan motsawa yana k'ok'arin ya tambayeshi ko dai mai kama dashi ne rai yayi halinsa



Tofa anan yan sanda suka fara bincike a b'oye dan su San sana'ar da Alhaji Bala keyi inda suka saka mishi ido sosai a lokacin suna zaune a garin kano


Mai gida ne yafara gaya mishi yayi taka tsantsan an fara sa mishi ido asirinsa ya kusa tonuwa idan da hali ya bar garin kano


Aikuwa a cikin kankanin lokaci Alhaji Bala ya koma port Harcourt da zama shi da iyalansa


Inda 'yan sandan suka tabbatar da zargin da suke mishi anan suka samo Akram dan ya k'ware a binciko sirrin mutum dan har pretending ya tab'a yi akan shi mahaukacine sabida kawai su kamo wani dan yankan kai


Tuni Akram shima ya koma portharcourt da zama ya samu wani dan benci ya baza sweet alewa har dasu sigari yafara siyarwa a opposite gidan Alhaji Bala yana ganin duk wani shige da ficen Alhaji Bala da iyalinshi har da 'yar tilon 'yarsa dayake bala'in ji da ita kamar ransa


Sai da ya samu wata shidda yana lura da duk wani movement d'in Alhaji Bala inda watarana da yamma Bayan akram ya gama had'a wani plan


Alhaji Bala na dawowa gida tunda ga nesa Alhaji Bala yaga antaru a opposite d'in gidansa ana alamar akwai abunda ke faruwa


Parking yayi ya nufi wajen da saurinsa dak'yar ya kukutsa cikin mutane anan yaga Akram na dambe da wani akan sai ya biyashi kud'insa daya siyi sigari da sweet Akram har dasu kuka yasaka yagaggun kaya



Tsawa ya daka musu suka rabu da juna suna sauke ajiyar zuciya Akram kuwa har da guntun hawayensa da majina


Anan Alhaji Bala ya tambayesu mai ke faruwa suka fad'a mishi yayi wani tsaki ya Ciro sabbabin Dari bibiyu masu yawa ya mik'awa Akram


Akram kuwa ya tsuguna har k'asa ya fara yiwa Alhaji Bala godiya

Ko tsayawa bai yi ba ya nufi wajen motarsa


Daddare bayan su Alhaji Bala sun gama cin abinci haka kawai Akram ya ringa fad'o mishi a zuciya haka kawai yaji yaron ya kwanta mishi bai tsaya wani dogon tunani ba ya mik'e yayi waje


Direct wajen Akram ya nufa daya buga tagumi yana kallon waje d'aya har ya zauna agefenshi Akram bai sani ba sai da ya dafashi


Ya juyo a firgice suna had'a ido yayi sauri ya sauka daga kan bencin zai tsuguna Alhaji Bala yayi sauri ya maidashi ya zauna


Alhaji Bala sai da ya gama kare mishi kallo yace "kabani takaitaccen tarihinka"



Wani irin farinciki ne ya rufe Akram amma a zahiri kuwa k'walla suka hau zubo mishi

Anan Akram ya karkata kai ya fara zuba mishi mugun karyar irin talaucin da suke ciki shi da iyayensa shine babba a familynsu su wajen goma sha biyu babansa makaho ne haka ma mamansa sanadiyar accident da sukayi yanzu shine komai nasu


Wani irin tausayin Akram ne ya rufe Alhaji Bala ya tambayeshi yana so yayi bankwana da talauci da sauri Akram ya zube a k'asa yace mishi ee
Alhaji Bala k'ara tambayarshi yayi kowane irin aikine zai iya?


Bud'ar bakin Akram sai yace koda yankan kai ne zai iya


Wani irin murmushi Alhaji Bala yayi yace kar ya damu zasu had'u gobe ya shirya zasuje wani wajen



Aranar Akram kwanan farinciki yayi ya kira manyansa akan su taya shi da add'ua su kuma sa ayi mishi sauk'ar Qurani akan Allah ya kareshi daga wani mugun Abu



Washegari da sassafe Alhaji Bala ya d'auki Akram suka d'auki hanyar Maiduguri inda Mai gida yake sai daddare suka isa wajen Mai gida idan banda adduoi babu abunda Akram keyi a zuciyarsa




Abun mamaki mai gida shima yana ganin Akram yaji San shi har a zuciyarsa


Anan Alhaji Bala ya gabatar mishi da Akram akan yanaso ya zama yaronsa shima ya duba akwai alheri atattare da Akram ko dai babu



Abun mamaki Har Mai gida ya gama dube dubensa haske da alheri kawai yake hangowa attatare da Akram


Cikin farinciki mai gida ya fara gayawa Alhaji Bala irin Al khairan dake tattare da Akram akan zai ringa samun mahaukatan kud'i dan haka ya ringa lallab'a Akram ya ringa binshi a hankali kar ya ringa matsa mishi akan yayi Abu



Take Alhaji Bala ya amince bakinsa har kunne anan suka kwana mai gida ya ringa musu tsubuce tsubuce Akram kuwa ya ringa zuba addu'a a zuciyarsa



Washegari suka koma port Harcourt da Akram da shirin shima next operation dashi zasu tafi




Duk abunda ke faruwa Akram na sanar da manyansa halin da ake ciki


Ahaka suka fara fita first operation inda suka nufi garin bauchi sukayi wa wani hamshakin mai kud'i sata sukayi wa yaransa biyu fyad' duk abunda ake yi Akram na mak'ale da secret camera d'inshi a lokacin babu yanda Alhaji Bala bai yi da akram akan shima yayi wa d'aya daga cikin 'yan matan fyad'e yak'i next operation ma ya kuma yiwa Alhaji Bala gardama akan shi zai ringa rakasu amma bazai iya kashe mutum ba bakuma zai iya yiwa kowa fyad'e ba tun a lokacin Alhaji Bala yaso ya fasa kwakwalwar Akram amma mai gida na hana shi ........

Wanan shine takaitaccen tarihin Alhaji Bala


Cigaban labarin


Alhaji Bala sai da yayi wa Naila yar shekara goma sha hud'u uban siyayya na wajen dubu d'ari hud'u sanan ya k'arasa gida



Inda yana isa gida Naila ta fara tsalle tana mishi oyoyo


Duk girmanta kuwa sai daya d'aga ta sama ya yi juyi da ita kafin ya sauketa k'asa yana tambayarta ya gida Hajiya Lubna kuwa tana daga gefe tana ta murmushi tana jinjina irin soyayyar da Alhaji Bala ke nunawa Naila




3hrs ltr

Bayan Alhaji Bala yaci abincin dare ya huta suna ta hira da Naila tana bashi labarin School shi kuwa sai biye mata yake yana k'yalk'yala dariya Hajiya Lubna kuwa ganin alamun gajiya a tattare da Alhaji Bala amma yak'i zuwa ya kwanta yasa tacewa Naila ta hakura gobe sai ta cigaba da bashi labari amma a yanzu Daddynta ya gaji


Alhaji Bala da sauri da ya mik'e dan dama ya gaji hanya yake nema


D'akinsa ya nufa direct ya shiga wanka yana fitowa ya fad'a kan gado ko towel d'in jikinsa bai cire ba dan wani mugun bacci yake ji ga gajiya ko minti biyu bai yi da kwanciya ba bacci yayi awon gaba dashi


Kafin Hajiya lubna tayi shafe shafenta tazo wajen shi har yayi nisa a bacci


Girgiza kanta tayi ta gyara mishi kwanciya ta kashe fitilar d'akin ta bar d'akin ta koma Palo dan akwai film d'in da takeso ta kalla


12:30 am dai dai


Alhaji Bala yayi wani irin juyi dan ya gyara kwanciyarsa kamar cewa akayi ya bud'e idonsa ya kalli bakin k'ofa aikuwa ya hango Hajiya Nafeesa a tsaye rigarta gabad'aya a jike da jini har d'iga jinin ke yi ta zuba mishi ido tana kallonshi hawaye sai zuba suke a idonta



Wani irin razananan Ihu Alhaji Bala yayi take fitsari mai zafin gaske ya kubce mishi ihu yake sosai da iya k'arfinsa


Hajiya Lubna da Naila ta Dade da bacci a cinyarta a guje ta mik'e Naila tabi bayanta



Suna shiga d'akin sukaga Alhaji Bala ya rufe idonsa da k'arfi yana "dan Allah kiyi hakuri ki rabu dani"



Karar bud'e k'ofar d'akin ne yasa ya bud'e idonsa da sauri ya duro daga kan gadon jikinsa na wani irin k'yarma yabi ya jike da gumi sai sauke nannauyan ajiyar zuciya yake kamar Wanda yayi gudu.....



B'angaren su Saiam kuwa a lokacin da suka isa asibiti tana had'a ido da Alhaji Nazifi Hawaye ya hau zubo mata dan yabi yafita daga hayyacinsa kamar ba shi ba hawaye kuwa sai zubo wa suke a fuskarshi


A hankali ta kalli gefen gadonshi ta hango Samha itama a kwance idonta a rufe itama hawaye nata zubo mata ahankali ta k'arasa gadon da Samha ke kwance ta rik'o hannayenta adai dai lokacin da Samha ta bud'e jajayen idonta babu ko digon fari ahankali ta fara magana cikin rawar murya tana " Aunty Saiam yanzu Mummy ta tafi ta barmu kenan muma yanzu mun zama marayu bazata sake dawo wa ba"?


Saiam kuka ta fashe dashi ta jawo Samha ta rungumeta tana rarrashinta


Alhaji Nazifi dake kwance a gefe kuwa ya fashe da wani irin kuka.........
[2:35PM, 4/7/2018] 鈥�+234 806 462 6766鈥�: 馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫


*Written by*
馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝


*A heart touching story*



庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com







*ALHAMDULILLAHI ALHAMDULILLAHI MASOYA NA SAMU SAUKI BANSAN TA INA ZAN FARA DA YI MUKU GODIYAR IRIN KAUNAR DA KUKA NUNA MIN BA HAKIKA BAKA SANIN MASOYANKA SAI ABU YA SAMEKA NI KAM SAI DAI NA GODEWA ALLAH DAN MASOYANA BAZASU KIRGU BA NASHA ADDU'OI BANDA KIRA DA TEXT MESSAGES NIDAI BAZAN IYA LISSAFAKU BA SAI DAI KAWAI NAYI MUKU GODIYA A DUNKULLE NGD ALLAH YA BAKU LADA YA SAKA MUKU DA ALHERI DA ZAN IYA LISSAFOKU WLH DANA LISSAFOKU AMMA INA BAZAN IYA BA MARYAM I GITAL BARSMARH YAR LELE MAMAN MANAL HADIZA KADUNA YAR BAIWA PHAUZA NAFEESA I SHEHU BANIDA ABINDA ZAN CE MUKU SAI ADDU'A KAWAI*


*KUNGIYATA REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS NGD DA KAUNA DA KULAWA DA KU KA NUNA MIN ALLAH YA BIYA MUKU BUKATUNKU NA ALHERI*


*INA GODIYA AUNTYNA AUNTY SIS ALLAH YA RAYA MIKI ZURIA*


*INA MIK'A GODIYATA GA GRPS GRPS DA SUKA RINGA MIN ADD'UA ALLAH YA SAKA MUKU DA ALHERI*



*WANAN SHAFIN NAKU NE YAN GIDAN MIEMIE B DA ZAUREN BIEBIE ISAH THANKS FOR D LOVE AND SUPPORT*馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹





*Page 7*



Saiam da Sauri ta Saki Samha dake sheshek'ar kuka ta nufi wajen Alhaji Nazifi dake kuka kamar k'aramin yaro

A gefen gadon ta zauna tare da Ruk'o hannun Alhaji Nazifi ta saka d'aya hannun nata ta goge hawayen dake ta zubo mata tace muryarta na rawa


"Daddy dan Allah kayi hakuri ka daina kuka haka Allahn da ya bamu ita shi ya k'arbeta Dan yafi mu San ta hakuri ,zamuyi mu ringa mata addu'a Mummy tace kar mu sake zubar mata da hawaye addu'ar mu kawai take bukata Daddy a matsayinka na Mijinta addu'a kawai ya kamata ka ringa binta dashi idan kai kana kuka mu mai zamuyi Daddy Dan Allah Daddy kayi hakuri ka share hawayenka kukanka na k'ara tunzura Samha kukanka na k'ara karya mata zuciya kai ya kamata ace ka rarrasheta"


Alhaji Nazifi kamar k'aramin yaro ya ringa gyad'a kai da sauri yana goge hawayen da suke k'ara tultulowa



A hankali yafara magana cikin rawar murya

"ALLAH YA JIKANKI NAFEESA ALLAH YA KAI HASKE KABARINKI TUNDA NA AUREKI BAKI TAB'A YARDA NA KWANA DA FUSHINKI BA BAKIDA BURIN DA WUCE KI FARANTA MIN RAI KINYI MIN BIYAYYA NAFEESA KIN BINI SAU DA K'AFA KIN BAWA YARANA TARBIYYA INGANTACIYA KO DAN WANAN INSHA ALLAHU ALJANA CE MAKOMARKI BAZAN TAB'A SAMUN MACE IRIN KI BA NAFEESA NAYI RASHIN DA HAR NA KOMA GA MAHALLICINA BAZAN SAMU WACCE ZATA MAYE GURBINKI BA ALLAH SARKI NAFEESA INA MA ACE NASAN DAREN JIYA ZAKI TAFI KI BARNI INA MA ACE NASAN GANIN K'ARSHE NAKE MIKI DA WLH BAN KWANTA BA DA NA ZAUNA NA NEMI YAFIYARKI NAFEESA ALLAH YA JIKANKI NAFEESA"


Duk inda Alhaji Nazifi yakai Dan ya danne kukan daya taho mishi kasawa yayi sai daya k'wace mishi


Saiam da Samha kuwa mutuwarta ya dawo musu sabo fil aransu suka hau kuka


Kamar Wanda aka mitsina suka ga Alhaji Nazifi ya mik'e yana "Saiam

Please Login or Register in order to submit comment