Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su tabbatar da abinda suke ji wayanda kuwa sukayi falling Victim kuwa tuni suka hau sujadda suna godewa Allah wasu kuwa suka ringa shirin zuwa ganin shi


Akram kuwa kansa ya d'au zafi 'yan jarida sun cika bakin office d'in shi suna jiran ya fito ya musu Karin bayani akan yanda yayi nassarar cafe Alhaji Bala da yanda akayi ya gano Alhaji Bala dan fashine



Sai da Akram yayi wanka ya shirya a toilet d'insa dake cikin office d'insa ya d'aura alwala yazo ya ringa jera nafilfili na godiya da Allah daya bashi nassara akan Alhaji Bala bai samu fitowa ya saurari 'yan jaridar ba sai wajen 10am na safe


Farin suit ne a jikinsa da bak'in nectie yayi masifar kyau ai yana fitowa camera ta hau haska shi 'yan jarida sukayi dafifi suka hau yi mishi tambayoyi har suna turereniya


Akram kuwa sai da ya gyara tsayuwarsa yayi godiya ga Allah tare da addu'a kafin ya fara magana cikin had'adden turancinsa inda gidan talabijin na AIT suke haskawa live tare da raba screen d'in gida biyu Akram a d'aya b'angaren yana kwarara jawabi d'aya b'angaren kuma hoton Alhaji Bala ne dan fashi da hoton Alhaji Bala da mutane suka sani a matsayin mai taimakon Talakawa



A dai-dai lokacin iyalan Alhaji Nazifi na zaune a palon gidan suna karyawa Samha mayar kallon Indian series tana aikin nata na kallo ganin sun tafi talla ne yasa ta fara k'ok'arin canza tasha inda kuwa ta kamo tashar AIT adai dai lokacin da aka hasko Akram yana kwarara bayani agefe ga hoton Alhaji Bala mik'ewa sukayi gabad'aya dan bazasu tab'a manta fuskar Alhaji Bala ba


K'ofin shayin dake hannun Samha ya subuce daga hannunta ya fad'i k'asa gabanta na mugun fad'uwa kurawa Akram ido kawai tayi


Adai dai lokacin da Saiam itama take kallon labaran ta latso lambar Alhaji Nazifi dan tace su kamo tashar AIT


Wayar na ringing amma Alhaji Nazifi ya k'asa d'agawa dan mutuwar zaunen da yayi.... ...

๐ŸŒ‘ ๐ŸŒ‘ *B๐Ÿ…ฐK'IN D๐Ÿ…ฐRE*๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘


*Written by*
๐Ÿ’…๐Ÿ’… *Sadnaf*๐Ÿ’…๐Ÿ’…


*A heart touching story*



ยฎ *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ษฏษ› ษ–ฦกล‹'ลง ฦกล‹ูณแƒง ษ›ล‹ลงษ›ล™ลงฤ…ฤฑล‹ ล‹ษ– ษ›ษ–ลณฤ†ฤ…ลงษ›, แƒชลณลง ษฏษ› ฤ…ูณลžฦก ลงฦกลณฤ†ษง ษ– ษงษ›ฤ…ล™ลง ฦกส„ ล™ษ›ฤ…ษ–ษ›'ลž_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




*Follow me on Wattpad@Sadnaf*


*Page 16*



Saheeba ce tayi k'arfin halin d'aga wayarta dan dukansu sun k'asa d'aga wayar TV kawai suka kurawa ido ko kifta idonsu basa yi


Cikin rawar Murya Saiam ta hau cewa su kunna TV su ga Tsinanne nan da ya kashe musu mommynsu dubunsa ta cika Allah ya tona mishi asiri


Saheeba ce mata tayi yanzu haka shi suke kallo bata Kara tsayawa taji mai Zata ce ba ta kashe wayar


Alhaji Nazifi kuwa ba ganin Alhaji Bala d'an fashine ya girgiza shi ba ganin Alhaji Bala mai taimakon talakawa da suke hirar shi shekaranjiya akan irin ayyukan alherin da yake yiwa Mara sa shi har suna cewa da za'a samu irin shi guda Ashirin da talakawa sun daina k'ok'awa har addu'oi suka runga mishi sai gashi wai Ashe shine wannan gagarumin d'an fashin Da ya addabi manyan masu kud'i


Samha kuwa tana nan a tsaye kamar an dasata waje d'aya Akram kawai ta zubawa ido dake kwarara bayani wani irin strange feelings da bata tab'a ji ba taji yana zagaye kowane sassa na jikinta


Suhaima ce tayi k'arfin halin magana tace "Allah mai Iko yanzu wanan Alhaji Balan mai taimakon talakawa dama shine tsinanne Dan fashin nan daya zo ya kashe mommy"


Saheeba da sauri tace "ni bashi yake bani mamaki ba yanzu dama wannan Dan iskan mutumin ba Dan fashi bane ya tsaya aka kashe Mommy agaban idonsa bai iya tab'uka komai ba duk da sunan bincike ake tafiya dashi Fashi ayi kissa agaban idonsa ayiwa mata fyad'e duk yana tsaye yana da ikon da zai hana shi aiwatar da mugun nufinsa akan yaran mutane yana da ikon da zai hana shi ya Harbe mana Mommynmu amma ya tsaya aka kashe Mommy a gaban idonsa na tsane shi wlh bai burgeni ba bai tashi sawa a kama shi ba sai da aka kashe Mommy"


Ta k'arasa maganar sirarran hawaye na bin kuncinta


Nanauyan ajiyan zuciya Alhaji Nazifi ya sauke ya juya ya kalli Suhaima yace "karki tsane shi Suhaima akan aikinsa yake ba kowane zai iya d'aukan risk d'in da ya d'auka ba mutane da yawa sun sha rasa rayyukansu agarin binciken mai laifi irin na Alhaji Bala masu fuska biyu ni kuma ji nayi ina kaunarsa araina ba dan shi ba mutane ba zasu tab'a sanin waye Alhaji Bala ba haka zai ta tafka zalunci a doron k'asa ba tare da ansan shi bane ki daina alak'anta mutuwar Mahaifiyarku dashi domin ko da ya hana ko bai hana ba lokacinta ya Riga da yayi gaskiya Akram S Adam yayi namijin k'ok'ari sosai sai dai ayi mishi addu'ar gamawa da duniya lafiya dan""""


Kiran mak'ocinsu daya shigo wayarsa ne ya katse mishi maganar da yake yi yana d'agawa shima yace ya kunna TV yaga ikon Allah murmushi kawai yayi yace yagani



Aranar duk Inda ka zagaya hirar Alhaji Bala kawai ake yi duk wani social net labarin Kawai zaka ji anayi na irin namijin k'ok'arin da Akram yayi har asirin Alhaji Bala ya tonu

Manyan masu kud'i da 'yan siyasa zirya kawai suke ringa yi suna zuwa ganin Akram tare jinjina mishi aranar Akram Sam bai samu zama ba kansa har wani ciwo yake


Alhaji Bala kuwa hannunsa da k'afa sanye yake da ankwa banda 'yan sanda biyu dake gadinsa Dan ba waje d'aya aka sa shi dasu killer ba for the first time da yaji wani irin kunya da nadama ya lullub'eshi wai shi da jama'an gari suka sani amatsayin mai taimakon talakawa sai gashi asirinsa ya tonu cikin kankanin lokaci Lallai Akram ya gama dashi yanzu Ashe dan yagano shi waye da irin sana'ar da yake yi yasa ya bishi har port Harcourt yaringa siyar da alewa ya San yanzu 'Yan garinsu sun ji labari har da Mahaifiyarsa da wane ido zai kallesu da wane ido zai kalli jama'an gari inama mutuwa ta d'auke shi yanzu ina ma k'asa ta tsage ya shige ciki

Ahaka ya ringa zancen zuci hawaye na kwarara a idonsa


Samha kuwa wunin ranar sukuku tayi shi ta kuma rasa mai yake damunta babu Wanda ya kai ta farincikin tonuwar asirin Alhaji Bala Dan kullum addu'arsu kenan to amma me wani Abu mai nauyi take ji game da Akram duk fitar lafazinsa na jawabai da yake yi akan Alhaji Bala da hanyoyin da yabi har yayi nassarar kama Alhaji Bala sai taji gabanta ya fad'i ta kuma rasa dalili haka kawai take ji aranta tsabar kiyayyan da take musu ne ya janyo haka amma me ta k'asa d'auke idonta daga kansa a hotunan sa da ake ta watsawa a shafukan face book dasu watsapp



A cikin kankanin lokaci aka mik'a Alhaji Bala kotu Dan a yanke mishi hukuncin sabida duk shaidun da ake bukata akwai su



Motocin 'yan sanda sunfi ashirin da suka yi layi kawai dan rakiyar Alhaji Bala zuwa kotu



Alhaji Bala kuwa kamar ya shide yayi kukan yayi nadamar har ya saba da ganin Na Maliya na zuwa yi mishi dariyar keta banda Hajiya Nafeesa da Mai gida dake yawan zuwan mishi daddare yayi ta ihu kenan har gari ya waye nan da nan ya zama siriri k'arfi da yaji banda kasumbar da ya ajiye


Ana fitowa dashi 'yan jarida sukayi dafifi suna shek'a mishi tambayoyi hasken flash kake gani ko ta ina



Babu ma hanyar da zaa wuce

Alhaji Bala kuwa sunkuyar da kansa yayi k'asa hawaye kamar an bud'e famfo jama'ar gari kuwa duk sun hau hau saman kwanun gidajen mutane Dan su hango Alhaji Bala mai fuska biyu


'Yan sanda ture jama'a kawai suke Dan su samu hanyar wucewa


Wani Dan jarida ne ya rok'i Alfarmar abasu minti goma kawai suyiwa Alhaji Bala tambayoyi

Dak'yar aka amince suyi mishi tambayoyin inda Alhaji Bala yaji kamar ya nutse dan kunya


Wata 'yar jarida ce ta fara jefo mishi tambaya "Alhaji Bala mai zaka iya cewa game da tuhumar da ake maka na fashi da makami kai da jama'an gari suka san mutumin kirki ne mai taimakon talakawa"?


Tana rufe baki wani ya jefo masa nashi tambayar " Alhaji Bala tsawon wane lokaci ka d'auka kana wanan mumunar aiki shin dama can ta silar fashi kayi kud'i kake taimakon mutane ko kuwa dama kana da kud'in daga baya ka koma kana farautar dukiyoyin jama'a?



Alhaji Bala kansa ya k'ara sunkuyarwa Dan bai San mai zai ce musu ba sai da wani ya k'ara jefo mishi nashi tambayar yayi k'arfin hali ya d'ago aikuwa tuni aka hau kashe mishi ido da flash 'yan jarida kuwa kamar zasu shige jikinsa sabida kawai suji ta bakinsa kowa mik'a recorder d'insa yake saitin bakinsa Dan ya ji mai zai ce Sosai


Alhaji Bala cewa yayi "bansan mai zance ba ayanzu banida bakin magana a yanzu ni ban ma San yanda zan muku bayani ba kuma yanda kuke mamakin tuhumar da ake min nima haka nake mamakin tuhumar da ake min"


Haka kawai Yaji kalaman na fita a bakinsa Dan gani yake idan yayi saurin mik'a wuya mutane sai sunfi yarda da shi Dan fashi ne amma idan ya ringa musanta zargin da ake mishi ahaka zai yi ta wahalar da shariar


Mamakine ya rufe Akram da ya ji mai yace

Alhaji Bala na k'ok'arin magana ya ji an jefo mishi dutse a goshi kafin kace mai jama'an gari sun hau cewa "karya kake azzalumi asirinka ya tonu dutse ake jefa mishi ko ta ina


'Yan sanda kuwa tuni suka hau sakin harbi sama dan su tsawatar musu da haka suka samu suka dan watse suka koma daga nesa suna jefo duwatsu


'Yan jarida kuwa tuni suka yi nasu wajen dan wasu a cikinsu sun samu nasu rabon dutsen

Ahaka aka tisa keyar Alhaji Bala da goshinsa Ke tsiyayar da jini da gefen kansa suka d'au hanyar high court



Cikar da kotun yayi b'ata bakine dan har waje mutane ne burin kowa yaga Alhaji Bala mai fuska biyu manyan masu kud'i ma da suka san shi sun samu zuwa ciki har da Alhaji Nazifi da Ghali
'Yan sanda sai da sukayi dagaske suka shige da Alhaji Bala ciki 'yan jarida kuwa suma sun cika kotun burin kowa ace shi yafi d'aukan rahoto


Alhaji Bala kuwa addu'a kawai ya ringa yi mutuwa ta d'aukeshi dan abinda ake cewa kunya kam jinshi kawai yake a hankali ya d'ago da kansa aikuwa suka had'a ido da Mahaifiyarsa idonta yayi jajir sabida kukan da ta sha yana k'ok'arin d'auke idonsa suka had'a ido da Hajiya lubna idonta kamar ya fad'o sabida harararsa da take yi da gani itama zuwa tayi ta tona mishi asiri


Wajen da masu laifi suke tsayawa ya tsaya ya sunkuyar da kansa a lokacin da aka ringa shigowa dasu lion Akram ne k'arshe daya shigo yana sanye da Uniform d'insa ya balain yi mishi kyau waje ya samu ya zauna


ba tare da b'ata lokaci ba Alkali ya fara gabatar da laifin da ake tuhumar Alhaji Bala dashi


Duk had'in kan da ake so su Lion su bayar sun bayar dan sun fad'i irin aika aikan da suka ringa yi Black ne ma yaso yayi karya ya ji an kwashe shi da wani mugun mari daya sa sai da ya jingina da bango murya kawai yaji ana ka fad'i iya gaskiyarka ko na canja ma kamanin

Da Sauri Black ya fara basu labarin duk abinda ya sani kamar an kunna radio ko ajiyar zuciya baya saukewa sai da suka gama amsa duk tambayoyin da aka musu aka koma kan Alhaji Bala daya sunkuyar da kai idonsa a runtse


Full name d'insa Alkali ya kira Alhaji Bala ya d'ago ahankali yana kallonsa


Alkali tambayarsa yayi akan ya basu labarin yanda akayi ya tsinci kansa a cikin wannan mugun sana'a mai kuma zai iya cewa game da tuhumar da ake mishi


Alhaji Bala sai da ya d'auki tsawon minti goma yana tunanin mai zai ce dan fa Sam ba zai iya mik'a wuya Cikin sauki ba


Kau da kansa yayi yace duk abinda ake tuhumarsa da shi karyane sharri aka mishi


Yana rufe baki yaga fatalwowin wayanda ya kashe sun fara bullowa ta jikin bango dukansu da dogwayen bulala a hannunsu


A razane yaja da baya ya wage baki zai yi ihu aikuwa yafara jin lafta ko ta ina.................๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚






I swear I don tire๐Ÿ˜ก๐Ÿ˜ก๐Ÿ˜ก

๐ŸŒ‘ ๐ŸŒ‘ *B๐Ÿ…ฐK'IN D๐Ÿ…ฐRE*๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘


*Written by*
๐Ÿ’…๐Ÿ’… *Sadnaf*๐Ÿ’…๐Ÿ’…


*A heart touching story*



ยฎ *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ษฏษ› ษ–ฦกล‹'ลง ฦกล‹ูณแƒง ษ›ล‹ลงษ›ล™ลงฤ…ฤฑล‹ ล‹ษ– ษ›ษ–ลณฤ†ฤ…ลงษ›, แƒชลณลง ษฏษ› ฤ…ูณลžฦก ลงฦกลณฤ†ษง ษ– ษงษ›ฤ…ล™ลง ฦกส„ ล™ษ›ฤ…ษ–ษ›'ลž_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




*Follow me on Wattpad@Sadnaf*





*AUNTY SIS*๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—
*Wherever you are just* *know that we are* *missing you so much*
*You will always stand as a legend* *in our world. We will forever Love and cherish you. Our heart warming prayers are always with you. Come back soon please*



*Page 17*


Tuni mutane suka k'aure da sallati sakamakon rawan alantar da Alhaji Bala ya ringa zubawa shi kad'ai yana ihu babu abinda kake ji sai sautun bulalai yana suyi hakuri zai fad'i gaskiya tuni ya fito daga inda masu laifi ke tsayawa ya nufi tsakiyar kotun ya ringa tsalla ihu yana shoshe shoshe

'Yan jarida kuwa tuni suka ja da baya suna d'aukarsa hotuna da video



Wasu 'yan sanda biyune sukayi k'arfin halin zuwa kusa dashi aikuwa suka ji saukan bulalai a gadon bayansu aguje suka bar wajen


Mutanen kotun kuwa hankalinsu a tashe suka zubawa Alhaji Bala ido dake Neman fita daga hayyacinsa sabida tsabar azaba

Alhaji Bala kuwa wani wawan ajiyar zuciya ya sauke a lokacin da suka b'ace take Na Maliya ya bayyana saman kansa yana kyakyata dariya sai yawo yake a saman ruwa babu Wanda ke ganinsa sai Alhaji Bala


Sai da na Maliya yayi dariya mai isarsa yace "Bala kad'an kagani sai na k'ara taso wayanda suka fi wanan yawa wlh sai ka rok'i mutuwa ta d'auke tsabar masifa da azabar da kake ciki"

Alhaji Bala kuka ya fashe dashi yana "Na maliya ka rufamin asiri na tuba wlh iya masifar da nake ciki ma ya isheni"


Dariya Na Maliya ya k'ara kyakyalewa dashi ya b'ace

Duk mutanen dake cikin kotun zubawa Alhaji Bala ido kawai sukayi suna mamakin surutun da yake yi shi kadai


Alhaji Bala bin jikinsa dake masifar rad'ad'i dan azaba ya ringa yi da kallo dan ji yake kamar an hura mishi wuta nan da nan wasu kuraje masu masifar kaikayi suka feso mishi wani razanan ihu ya saka ya fara Sosa ko ina kamar sabon mahaukaci


Tuni mutanen dake kotun suka k'aure da hayaniya suna Alhaji Bala ya haukace tun ba a je ko ina ba


Duk abinda akeyi Akram na daga gefe ya zubawa saurautar Allah ido dan ya d'an girgiza da lamarin Alhaji Bala tunda gashi dai sautukan bulalai kawai suka ringa ji basu ga kowa ba


Dak'yar aka samu mutanen kotun sukayi shiru sabida Alkali dake San magana

Alkali sai da ya gyara zaman glass d'in fuskarsa ya k'ara karewa Alhaji Bala dake Sosa jikinsa a haukace kallo yayi gyaran murya yana tunda Wanda ake case dashi ba'aji ta bakinsa ba sabida halin da yake ciki za'a d'age kara zuwa sati biyu masu zuwa aranar kuma za'a yanke mishi hukuncin daya dace da laifin da ya aikata su kuma su killer tunda sun amsa laifinsu batare da sun wahalar da sharia ba zasuyi life imprisonment with hard labour daga haka Alkali ya buga guduma tare da mik'ewa


'Yan sanda hud'u ne suka rik'e Alhaji Bala sakamakon fifizgewar da yake yana ihu dan tsabar Susa da yakeyi har jini jikinsa ke yi



Ahaka suka jashi sukayi mota dashi yana zunduma ihu


Ahankali mutanen kotun suka fara fitowa data kotun suna mai Al ajabin abunda ke faruwa


Hajiya Lubna kuwa ko ajikinta Dan Sam Alhaji Bala bai bata tausayi ba tunda lokacin daya ke tapka rashin Imaninsa shima babu digon tausayin wayanda yake zalunta aransa



Hajiya Saude Mahaifiya Alhaji Bala kuwa kuka ta ringa rizga hannunta aka dan ita kad'ai tasan irin masifar da take ciki bata jin zata iya komawa kauyensu dan tunda 'yan garinsu sukaji labarin Bala dan fashine sukayi zuga suka tafi gidajen kannensa suka ringa jifansu suna asirin yayansu ya tonu Ashe d'an fashi da makamine


Ita kuwa sai a makota ta b'uya Dan petur suka zazzagawa gidanta suka cinna mishi wuta suna munafika ce ita

tasan irin sana'ar da Alhaji Bala yake yi ita take d'aure mishi gindi


Magana take so tayiwa hajiya Lubna akan ko zata taimaka ta tafi da ita gidansu Dan bata da wurin zuwa Dan ko k'annen Alhaji Bala sun bar garin sabida tsabar tashin hankali amma ga mamakinta wani mugun harara Hajiya Lubna ta watsa mata tare da Jan tsaki tayi shigewarta mota Baki a sake Hajiya
Saude ta bita da kallo har sai data daina hangota


Akram kuwa sai da 'yan jarida suka kara tsayar dashi suna jera mishi tambayoyi dak'yar ya yak'ice ya gudu ya barsu dan ya gaji da wanan tambayoyin da suke mishi dan Sam shi ba gwanin magana bane yanzu nan zaiji kansa na ciwo



Alhaji Bala kuwa tukuru ya zama k'aramin Mahaukaci yana surutai tare da so she soshe cikin k'ank'anin lokaci hallitar jikinsa ya fara sauyawa yana komawa wani irin hallita cisge gashin kansa kawai yake yana buge buge jikinsa sai jini yake yana fad'ar abubuwan da ya aikata Lokaci lokaci Na Maliya ke bayyana ya ringa shek'a mishi dariya yana zuba mishi wani ruwa dake sa ya k'ara haukacewa wajen Sosa jikinsa





Bayan sati d'aya da zaman da akayi a kotu aka k'arawa Akram S Adam mukami ya zama babba banda uban kyaututukan da manyan masu kud'i suka ringa bashi gida ne mota kudi banda uban kyautar da Governor ya mishi har da su hutun wata uku Dan ya zagaya kasashen ketare yaje ya huta Akram kuwa godiya kawai yake yiwa Allah akan d'aukakar da ya mishi dan yasan duk abinda ya samu yin Allah ne ba nashi ba

Duk inda ka zagaya gidajen television gidan jaridu duk wata media hirar Akram s Adam kawai ake yi na irin namijin k'ok'arin da yayi na chapke Gagarumun dan fashi Alhaji Bala

'Yan mata kuwa tuni suka haukace burin kowace ace tazama buduruwar Akram s Adam ga kyau ga kud'i


Samha kuwa bak'on al amarin data tsinci kanta a ciki ne ya sa ta fara rama dan idan dare yayi Sam bata iya bacci Haka kawai take tunani na babu gaira babu dalili babu dama ta hau wani net sai taci karo da hoton Akram da labarinsa ita dai tasan babu Wanda ta tsana sama da shi amma ga mamakinta bata iya bacci sai ta bud'o hotonsa ta kalla bacci kuwa idan ya d'auketa sai tayi mafarkinsa ta kuma rasa Wanda zata samu ta gayawa halin da take ciki


Alhaji Bala kuwa lamarinsa yayi tsamari duk dare sai 'yan sanda sunji saukar bulalai amma sun rasa wayanda ke dukan Alhaji bala

Haka zai kwana yana ihu yana sosa jiki fatar jikinsa duk ta kwaye har wani wari yake yi sabida bayan ya sha bulala Sai Na Maliya ya watsa mishi ruwan da zai ringa cisgo fatar jikinsa


Rok'on 'yan sanda kawai yake akan su harbeshi da wanan azaba da yake ciki


Akram kuwa tunda aka bashi Hutu yafara shirye shiryen zuwa gidansu Samha duk da yasan by now ta riga da tasan ko shi waye amma still wani fargaba da rashin kwarin gwiwa yake ji dan yasan sun Riga da sun tsane shi tunda yana tsaye aka kashe mahaifiyarsu bai ma San ta ina zai fara tunkurar gidansu ba har ya kai shi da sanar da su abinda ke tafe dashi nasan Auren Samha dan ranaku daidayane bai yi mafarki da ita ba tunda yake bai tab'a jin San wata 'ya mace kamar yanda yake San Samha ba



Ahaka Akram ya ringa saka rana rashin kwarin gwiwa da fargaba na hana shi zuwa sai da ya samu sati d'aya ahaka kafin ya iya d'aure yaje tare da Amininsa Yazeed da yaringa karfafa mishi gwiwa.....


Wlh ba Jan aji bane ke hanani typing wlh abubuwa sun sha min kai amma insha Allah am almost there....kucigaba da hakuri Dani wayanda suka sani a da ai sun San ba haka nake yi ba๐Ÿคจ๐Ÿคจ๐Ÿคจ๐Ÿคจ๐Ÿคจ


๐ŸŒ‘ ๐ŸŒ‘ *B๐Ÿ…ฐK'IN D๐Ÿ…ฐRE*๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘


*Written by*
๐Ÿ’…๐Ÿ’… *Sadnaf*๐Ÿ’…๐Ÿ’…


*A heart touching story*



ยฎ *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ษฏษ› ษ–ฦกล‹'ลง ฦกล‹ูณแƒง ษ›ล‹ลงษ›ล™ลงฤ…ฤฑล‹ ล‹ษ– ษ›ษ–ลณฤ†ฤ…ลงษ›, แƒชลณลง ษฏษ› ฤ…ูณลžฦก ลงฦกลณฤ†ษง ษ– ษงษ›ฤ…ล™ลง ฦกส„ ล™ษ›ฤ…ษ–ษ›'ลž_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




*Follow me on Wattpad@Sadnaf*












๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚

*HAPPY BIRTHDAY IN ADVANCE MY BELOVED SON AFFAN U ARE ONE YEAR OLDER TOMORROW INSHA ALLAH*


*I hope you have a wonderful day and that the year ahead is filled with much love, many wonderful surprises and gives you lasting memories that you will cherish in all the days ahead. Happy Birthday*


*On this special day, i wish you all the very best, all the joy you can ever have and may you be blessed abundantly today, tomorrow and the days to come! May you have a fantastic birthday and many more to come... HAPPY BIRTHDAY*

*ALLAH YA ALBARKACI RAYUWARKA YA RAYAMIN KAI YA KAREKA DA KAREWARSA YASA KAZAMO MAI HIDIMANTAWA MUSULUNCI YA SAKA MAKA TSORANSA A DUK INDA KA TSINCI KANKA ALLAH YASA KAYI RAYUWA MAI AMFANI DA HAR BAYAN MUTUWA TA ZA'A RINGA FAD'AR KYAWAWAN HALINKA ALLAH YA NISANCEKA DA DUK WANI ABU NA ASSHA DA ABINDA ZAI SA KA SABA MISHI SHIRIYA TA ALLAH CE INA MAI ROK'ON ALLAH YA SHIRYAMIN KAI BISA TAFARKIN ADDININ MUSULUNCI ALLAH YASA YANDA MAHAIFIYATA TAGA AURENA TA GOYAKA NIMA ALLAH YA ARA MIN TSAWON RAI NAGA AURENKA NA GOYA ABINDA KA HAIFA AMEEN*๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™






*Page 18*




K'arfe hud'u na yamma suka isa gidansu Samha gaban Akram sai fad'uwa yake dan bai San wane irin tarb'a Alhaji Nazifi zai masa ba ballantana uwar gayyar Samha Yazeed ne ya ringa k'arfafa mishi gwiwa

Har suka aika mai gadi yayi musu sallama da Alhaji Nazifi gaban Akram bai daina fad'uwa ba

Mai gadin tare suka fito da Alhaji Nazifi Dan yaga Wanda yake Sallama dashi


Ganin Akram ne yasa mamaki ya rufe Alhaji Nazifi sakin murmushi yayi a lokacin da suka zube a k'asa suna gaishe shi Akram kuwa sai sunkuyar da kansa yake



Palon Saukar bak'i Alhaji Nazifi ya kai su yana ta tunanin mai ya kawo su wajensa


K'ara gaishe shi sukayi Alhaji Nazifi ya amsa tare da k'ara jinjina mishi irin k'ok'arin da yayi wajen kama Alhaji Bala ya k'ara da mishi addu'oin nassara a rayuwarsa



Akram shi dai kansa a sunkuye yake yana D'an samun relief na fad'uwar da gabansa yake yi dan yaga alamar Alhaji Nazifi bazai bashi matsala ba


Alhaji Nazifi wayarsa ya Ciro daga Aljihunsa ya kira Saheeba a waya akan ta kawowa bak'i ruwa da lemo yana katse wayar ya maida hankalinsa kan su Akram Dan yaji abinda ke tafe dasu



Ganin sun k'asa magana sai zungurar juna suke yasa Alhaji Nazifi yayi murmushi yana Allah yasa shima ba laifi yayi ba suka zo bincikarsa


Murmushi sukayi gabad'aya Yazeed yace ba Laifi yayi ba sun dai zo nema ne a gurin shi


Adai-dai lokacin Saheeba ta shigo da faranti a hannunta sanye take da doguwar Riga ta yane kanta da farin mayafi


Sallamar da tayi ne yasa suka d'ago gabad'aya suna amsawa

Saheeba a Razane ta ja da baya tana sallati a lokacin da suka had'a ido da Akram

Tuni ta saki farantin hannunta jikinta na rawa Dan take ta tuna bak'in daren da suka zo gidansu


Stammering ta fara yi tana nuna Akram da Hannu


Alhaji Nazifi kuwa yayi Sauri ya mik'e ya ruk'ota yana "Saheeba mai haka Akram d'in ne bakisani ba"


Akram kuwa shima jikinsa ne ya d'au rawa hankalinsa a tashe dayaga yanda Saheeba ta razana da ganinsa


Yazeed kuwa tunda tayi sallama ya k'afeta da ido baya ko kiftawa


Dak'yar Saheeba tace cikin inina tana nuna Akram

Please Login or Register in order to submit comment