Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*Written by*
馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝


*A heart touching story*



庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





*HEA MASOYANA FANS D'INA INA FARINCIKIN SANAR DAKU INA UPDATING NOVEL D'IN BAK'IN DARE A WATTPAD ACAN ZAN RINGA POSTING KAFIN WATSAPP SO PLS IF U ARE REALLY I DIE FAN DONT FORGET TO SEARCH FOR SADNAF FOLLOW AND VOTE ME THERE I WOULD B GREATFUL WEN I START COUNTING YOUR VOTES*馃檹馃檹馃檹





*Page 8*



Wasa wasa sati biyu kenan da Alhaji Bala yaje wajen Mai gida abunda ake cewa kwanciyar hankali Sam Alhaji Bala bashi dashi dan Duk abinda Mai gida yace yayi ya yi amma Kullum sai Hajiya Nafeesa tazo mishi a cikin mafarki ko a zahiri yabi ya zama kamar mai k'aramin tab'in hankali Dan ko yaya yaji motsi sai ya firgita ya zunduma Ihu



Hajiya Lubna da Naila kuwa hankalinsu yayi masifar tashi da halin da suka ga Alhaji Bala a ciki Dan tunda ya fara shafa wani magani mai Warin kashi a jiki ga jajayen candles da yake kunawa duk dare suka fara tsorata da lamarin Alhaji Bala Naila b'uya ma take a d'aki dan ta fara zargin Daddynta yafara samun tab'in hankali kowane lokaci zai iya rufesu da duka dan abun nashi ya kai yanzu har da rana Ihu yake shi kad'ai idan yana zaune a cikin Palo ya kuma k'i gayawa Hajiya Lubna abinda ke faruwa idan ta matsa mishi da tambayoyi sai ya rufeta da fad'a tamkar zai daketa


A haka suka zuba mishi ido suna mishi addu'a samun sauki



B'angaren su Saiam kuwa Addu'a suke babu dare babu rana akan Allah yayi wa Hajiya Nafeesa Rahama ya kuma toni asirin Alhaji Bala har akayi sadakan bakwai bakinsu na d'auke da azumi idan kagansu sai sun masifar baka tausayi dan kowacensu kalar idonta ya koma ja sunyi shak'uwa da mahaifiyarsu fiye da tunanin mai tunani ko abinci basa iya ci ballantana akai ga cikakken bacci ahaka nasu nafila ne akan Alhaji Nazifi tunda danginsu dake tayasu zaman makoki suna dan kwantar musu da hankali sabanin Alhaji Nazifi da ke wuni a d'aki baya fitowa ba um bare uhum uhum haka zai yi tagumi yana kallon Hoton Hajiya Nafeesa lokaci lokaci yana share hawayen dake zubo mishi duk Wanda yazo mishi gaisuwa sai dai ya hakura ya tafi dan Alhaji Nazifi baya ko motsawa daga inda yake kiran Sallah kawai ke sa ya tashi Sallar ma a d'aki yake yinta a k'arshen sujadarsa kuwa kuka yake fashewa dashi yayi ta yiwa Hajiya Nafeesa Addu'ar Rahamar Allah



Sai da akayi Sati biyu da Rasuwar Hajiya Nafeesa Alhaji Nazifi ya d'an fara dawo wa dai-dai a inda ya nemo wani babban Mallami mai tarin ilimi yace ya taya shi da addu'ar Allah ya tonawa azzalumin da ya kashe Hajiya Nafeesa Asiri shi da zaman lafiya har Abada


Mallamin kuwa yace ya kawo kud'in Sadaka ya had'a kan Almajirai ya raba musu ayoyi da addu'oi insha Allahu asirinsa na dab da tonuwa


Makud'an kud'i Alhaji Nazifi ya bashi tare da yi mishi godiya


A Daren ranar suna zaune a Palo gabad'aya kowanensu hannunsa d'auke da carbi yayan Hajiya Nafeesa Alhaji Musa da tun magriba yana gidan kallon Alhaji Nazifi yayi dayake Jan counter kansa a sunkuye yayi yace mishi yanzu sai dai a d'aga Auren Safna da Saiam idan Hajiya Nafeesa tayi Arba'in sai a d'aura musu Auren dan ba dan rasuwarta ba da gobene d'aurin Auren



Saiam juyar da kanta tayi dan ita yanzu Sam Auren bama ya gabanta bata jin zata iya Aure ta rabu dasu Sahiba gwara ta zauna ta kula da kanenta tunda itace Babba



Alhaji Nazifi sai da yafara Sauke ajiyar zuciya kafin ya d'ago yace " A goben za'a d'aura musu Aure insha Allahu babu abinda za'a fasa dan Nafeesa ta rasu bashi zai sa a d'aga daurin Auren ba dan ko an d'aga ba dawowa zatayi ba ni nasan burinta bai wuce taga ranar d'aurin Auren Su ba kuma insha Allahu zan cika mata wanan burin nata dazu na yiwa iyayen mazajen waya akan su zo da shirinsu gobe k'arfe goma sha d'aya za'ayi D'aurin Auren in yaso sa tare idan an kwana biyu"


Tunda Ya fara magana Saiam da Safna suka d'ago arazane suna kallon shi kuka suka fashe dashi kamar had'in baki Saiam tace"Daddy dan Allah kar a d'aura mana Aure gobe mummy satinta biyu da rasuwa yau ya za'ayi a d'aura mana Aure gobe ni wlh na hakura da Auren zan zauna na kula da kanena idan mukayi Aure waye zai kula dasu Daddy Dan Allah mun fasa bama San Auren" Saiam ta karashe maganarta cikin matsanacin kuka



Alhaji Nazifi Da ji yake kamar shima ya fashe da kuka girgiza kai yayi ya mik'e daga kan kujera ya nufi inda suke a zaune

Zama yayi agabansu ya tank'washe k'afafunsa ya kira sunan Saiam da Safna yace "Karku manta ni ina rayye ban mutu ba ni zan kula dasu har zuwa lokacin da suma zan Aurar dasu burin Mahaifiyarku Kullum bai wuce taga ranar Aurenku ba kuma ni nasan a yanzu idan aka d'aga d'aurin Auren nan sabida ita bazata ji dadi ba gwara in cika mata burinta duk da bata Raye idan ta kanenku ne insha Allahu ni zan kula dasu ba wai ana d'aura Auren gobe a goben zaku tare ba sai an d'an kwana biyu haka mun d'an k'ara samun nutsuwa mun k'arasa sauran shirin namu sai Ku tare"



A takaice da k'yar Alhaji Nazifi da Alhaji Musa suka shawo kansu Saiam suka yarda za'a d'aura musu Aure a gobe Su Suhaima kuwa tausayin Kansu ne ya k'ara lullub'esu dan ahaka da suke d'an ganin juna hankalinsu ke kwanciya ayanzu kuma idan Saiam da Safna suka yi Aure gidan girma zai k'ara yi musu



B'angaren Akram kuwa suna nan suna shirye shiryen yanda zasu kama Alhaji Bala cikin Sauki shi da yaransa inda Akram ke kiran su Lion da suka Dade da komawa gidansu dake Daji dan cika Umarnin Alhaji Bala

Akram kuwa karya ya ringa musu da Mahaifiyarshi ce ba lafiya shi yasa bai dawo ba amma kafin ogansu ya dawo zai dawo


Akram ganin anyi sati Biyu Alhaji Bala bai kira shi ba yasa yafara shan jinin jikinsa yana tunanin ko dai Alhaji Bala ya gano cewa shi Ss ne



Lambar Alhaji Bala ya gwada kira bai d'aga ba sai da ya mishi miss call biyar bai d'aga ba take hankalin Akram ya tashi oganshi ya kwantar masa da hankali yace ya kira su Killer ya bugi cikinsu yaji idan kuwa suma basu d'aga ba to tabbas sun gano shi


Yana kiran Killer ya d'aga wayar Akram yace mishi a cikinsu akwai Wanda sukayi waya da oga kuwa dan yana ta kira bai d'auka ba


Mamaki ne ya rufe Killer yace mishi suma tun jiya suke kiranshi baya d'auka yanzu nan ma fire ya gama kiranshi bai d'auka ba


Hankalin Akram ne ya kwanta da yaji abinda yace sai yace mishi to bari zai cigaba da kiran shi watak'ila yana hutawa ne da haka suka yi Sallama



Oganshi yace ya kwantar da hankalinsa tamkar Alhaji Bala ya gama zuwa hannu ne









B'angaren Alhaji Bala kuwa ayau yafi kowace rana shiga tashin hankali dan Hajiya Nafeesa bata b'acewa idan ta zo mishi a yanayi na ban tsoro take zuwar mishi sosai Hajiya Lubna sallati kawai take yi dan ita bata ganin abinda yake firgita shi yake ihu yana zagaye d'akin abinda Alhaji Bala ya kwana yana yi kenan


Naila kuwa kuka kawai take tana tunanin ko aljanu ne suka sako Alhaji bala agaba


Sai da aka fara kiraye kirayen Salla Alhaji Bala ya daina ganin Hajiya Nafeesa


A guje ya fito daga d'akinsa duk yabi ya firgice kamar bashi ba daga shi sai dogon bak'in jallabiya babu ko dogon wando a ciki yaje ya hau motarsa ya bar gidan




Rabonsa da yaji shi cikin kwanciyar hankali tun kafin yaje gidansu Hajiya Nafeesa a 360 ya ringa fisgar motarsa ikon Allah kawai ne ya kai shi mai duguri wajen mai gida




Yana parking yasa hannu abayan seat d'in motarsa ya zaro k'aramar bindigarsa yasaka a Aljihunsu fuskar nan tashi a turb'une




Sai da mai gida ya gama uzurinsa kafin ya fito daga cikin gidansa



Ya zauna akan buzunsa yana kallon Alhaji Bala daya k'afe shi da ido ya tsaya tamkar wani soja


Murmushi mai gida yayi yace "kura ya dai ko dai fatalwar ce duk ta firgita ka haka dama na gaya maka wanan zabin farkon shi zaka bi ka ta rabu dakai idan ba haka ba wlh sai ta zarar dakai"


Alhaji Bala wani irin kallo yayi wa mai gida yace "mai Mara bata da zararren ai babu dan ta zarrar Dani duk inda nayi sai na ganta yanzu mai gida kana so kace min babu abinda zaka iya yi wanan matar ta rabu dani"?

Mai gida wani kallo ya watsa mishi yace "idan da akwai zan tsaya b'ata wa kaina lokacine babu abinda zan iya yi akai zabin nan dai nafarko shi zaka bi ta rabu dakai"



Dariyar mugunta Alhaji Bala ya kwashe dashi yace " yanzu dai kana so kace min Fatalwa ta fi k'arfinka kana so kace min duk abubuwan nan da ka rataya da aljanun da suke maka aiki bazasu iya min maganin matar nan ba"?


Mai gida zuba mishi ido yayi yana kallonsa a dai dai lokacin da zoben daya saka a hannun shi ya fara mishi zafi


Take Mai gida ya mik'e hankalinsa a tashe yana kallon Alhaji Bala dan yasan ba alheri ne ya kawo shi wajensa ba kafin ya kai ga wani tunani


Alhaji Bala ya zaro bindigarsa daga Alhajinsu ya nuna shi dashi yana "Mai gida banga amfaninka a doron k'asa ba tunda bazaka iya magance min matsala ta ba idan dai k'asar da kake bugawa ta gaske ce bai kamata ace da ka buga bai gaya maka gidan matar nan da zamuje zai zame min masifa ba dan haka gwara na kasheka tunda yanzu ba amfani kake min ba kafin mai gida yayi wani yunkuri


Alhaji Bala ya sakar mishi bullet hud'u


Mai gida take ya zube a k'asa jini na ambaliya wajen yafara dan girgiza


Alhaji Bala dake huci yayi tsaki yajuya ya nufi wajen motarsa



Alhaji Bala sai da ya bar wajen mai gida yafara tunanin wajen wa zai nemi taimako wane mallami zai samu ya iya mishi aiki Hajiya Nafeesa ta rabu dashi yana cikin wanan tunanin wani tsohon Mallaminsa Mallam na maliya ya fad'o masa arai shima wani hatsabibin Mallami ne dan shi akan ruwa yake zama a dalilin Mai gida ya watsar dashi



Bai tsaya wani dogon tunani ba ya d'auki hanyar Sokoto bashi ya isa kungurmin dajin ba sai Tara na dare


Sai daya sha bak'ar wahala ya iya gane wajen


Tunda ga nesa ya faro jiyo muryar Mallam na Maliya na mishi maraba tun bai k'arasa ba ya hau fad'a mishi abubuwan dake tafe dashi



Alhaji Bala kuwa da hanzarinsa ya k'arasa wajen da yaji muryarsa na fitowa


Sai da yayi kamar zai yi mishi sujadda kafin ya d'ago ya kalli Mallam Na Maliya dake ta juyi asaman ruwa a zaune shi ba a k'asa ba shi ba a sama ba


Sai da ya fara kwashewa da wani mahaukacin dariya yace "Kura matar nan da ka kashe tana da k'arfi rabaku sai an sha wahala amma awajena Abu mai sauki ne zan baka wani ruwa ayanzu kayi wanka da shi zaka daina ganinta na 'yan kwanaki kafin ta cigaba da zuwar maka kafin lokacin kasan yanda zaka je kabarinta ka haka rami agefen kabarin nata kasa wanan wuk'a da layan ka binne idan dai kayi haka ta rabu dakai kenan har abada"



Jikin Alhaji Bala ne ya hau rawa yace "Na Maliya ai bansan a inda aka binneta ba"



"Wanan yafi komai Sauki kaje unguwarsu idan kaje ka samu wani Mara k'arfi kace ya raka ka makabarta zaka je kayiwa mammata addu'a daga nan zaka iya bugar cikinsa kaji a inda aka binneta tunda sunan mijinta ba b'oyayye bane kana cewa Ashe matar Alhaji wane ta rasu ni kuwa ina kabarinta yake da haka zaka bugi cikinsa bayan kayi mishi alheri ni nasan zai nuna maka daga nan sai ka aiwatar da kudurinka indai ka samu ka binne ni nasan zata rabu dakai har Abada"



Wani nanauyan ajiyar zuciya Alhaji Bala ya sauke Dan gani yake abin da kamar wuya kansa ya k'ara sadawa k'asa kamar zai mishi sujadda kafin yace "Godiya nake Na Maliya menene ladan aikina"



Wani Mahaukacin dariya Na Maliya ya kwashe dashi kafin yace " kai ma kasan bana fad'a sai komai ya kammalla kuma duk abinda nace ayimin idan ba'ayi min ba kasan mai zai biyo baya dan ba iya fatalwar matar zan sa ya ringa bibiyarka ba har da sauran mutanen daka kashe"


Alhaji Bala girgiza kansa yayi yace angama indai Hajiya Nafeesa zata daina bibiyarsa da haka yayi mishi sallama da zumar sai ya dawo ya mik'e a gajiye yaje ya hau motarsa ya kuma d'aukar hanya.......
[2:37PM, 4/7/2018] 鈥�+234 806 462 6766鈥�: 馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫


*Written by*
馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝


*A heart touching story*



庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




*Follow me on Wattpad@Sadnaf*


*Page 9*


Alhaji Bala ba k'aramin farinciki yayi ba a lokacin da yaga ya kwana biyu Hajiya Nafeesa bata zo mishi a amafarki ko a zahiri ba


Tuni yafara dawowa dai-dai hankalinsa ya fara kwanciya sai a lokacin yaje ya samu Naila har cikin d'akinta sabida ta daina fitowa gabad'aya sabida tsoronsa da take ji


Hajiya Lubna kuwa ido kawai ta zuba mishi bata k'ara bi ta Kansa ba tunda taga alamar baya so ya fad'a mata abinda yake damun shi



Naila da sauri ta mik'e a lokacin da taga ya shigo

Alhaji Bala ya sakar mata murmushi yana "zo nan babyna kar dai kice gudun daddynki kike"?


Naila itama murmushin ta sakar masa da ta Gan shi a nutse ta tafi da gudu ta rungume shi tana "Daddy what happened to you"



Murmushi Alhaji Bala yayi a lokacin dayake kwantar mata da dogon gashinta San tilon 'yarsa na ratsa mishi zuciya yanda yake jin San Naila he can do anything bcos of her

Zame ta yayi daga jikinsa ya rik'e hannyenta ya nufi dogon kujerar dake d'akin ya zaunar da ita ya zauna a gefen ta tare da kuma rik'e hannayenta yace " am so sorry dear Some thing came up that Daddy could not handle but now am fine u should not be scared again"


Naila murmushin farinciki ta saki tace "Daddy yanzu ka warke babu abinda yake damunka"


Alhaji Bala cikin farinciki ya gyad'a mata kai


Naila kuwa ta tashi ta fara tsallen murna kamar wata yarinya dama yarinyar ce ma tunda she is 14yrs



Alhaji Bala mik'ewa yayi yace ta shirya anjima zasu tafi shopping ta zabi duk abinda take so



Naila wani tsallen murnar ta k'arayi tare da rungumeshi tana " I love u daddy you are d best dad eva "


"I love you to Darling"

Alhaji Bala yace adai dai lokacin da yake barin d'akin fuskarsa d'auke da tsantsar farincikin yayewar matsalarsa



D'akin hajiya Lubna ya nufa dan ya rarrasota dan yasan fushi take dashi



Bai sha wahala wajen rarrashinta ba abunka da mata da miji sai gashi sun bige da soyayya dan dama tunda ya dawo basu had'u ba sabida rashin kwanciyar hankali sai da komai ya wakana Hajiya Lubna ta hau bashi shawarwari akan ya daina wasa da Sallah dan ita tasan aljanu ne suka ringa tsorata shi sabida babu wani kariya a jikinshi



Murmushi kawai Alhaji Bala yayi yace mata to zai gyara daga haka ya mik'e ya fad'a band'aki




Siyayya yayi wa Naila na fitar hankali Hajiya Lubna sakin baki kawai tayi tana kallon shi dan siyayyar ma har Dana banza bata kuma isa ta hana shi ba idan ma tayi magana cewa zai yi ita kad'ai ce dashi gwara ya kashe mata



Sai da magriba suka dawo gida bayan ya kaisu wajen shakatawa aka ringa jido musu siyayyar da sukayi ana shiga dashi cikin gida



Alhaji Bala yana tsaye aka gama shiga da kayayyakin Hajiya Lubna da Naila kuwa dama sun Dade da shiga ciki



Wajen motarsa ya koma ya shige ciki tare dasa lock


Wayarsa dayake communicating dasu killer ya d'auko daga bayan seat d'in motarsa dan baya shiga da wayar cikin gida sabida tsaro


Bai yi mamakin ganin miss call d'insu ba dan yasan Dole dama su neme shi



Layin Killer ya fara kira bugu d'aya ya d'auka

Yana amsa gaisuwar da Killer ya mishi yace "karku damu oll is fine na d'an shiga rububi ne hope duk kuna villa( sunan da yake cewa gidansu dake daji)


Killer ce mishi yayi " eee oga duka muna nan AKram ne kawai har yanzu bai zo ba sakamakon mom d'insa bata da lafiya yama ce zai kiraka ya fad'a maka"


"Zancen banza zancen wofi ina ruwanmu da wani Mom d'insa bata da lafiya who even cares ko mutuwa tayi dole ya dawo bakin aikinsa bansan mai yasa yake so ya ringa take umarnina ba amma babu komai zanyi wa tufkar hanci tunda mai hanani is gone let me call the fool"


Bai bari Killer yayi magana ba ya kashe wayar yana huci tare da dialling number Akram


Adai-dai lokacin da Akram ke kan Sallaya yana Jan carbi idonsa a lumshe fuskar Samha nata mishi yawo a ido dan kwanaki nan shi kad'ai yasan mai yake ji akan Samha duk fitar numfashinsa sai ya tuna ta bai tab'a jin San 'ya mace a zuciyarsa kamar yanda yake jin San Samha duk da Sau d'aya ya tab'a ganinta


Ringing d'in wayarsa ne yasa ya bud'e idonsa tare da d'aukar wayar ganin mai Kiran ne yasa ya mik'e da sauri tare da gyara zamansa ya d'aga wayar





Alhaji Bala fad'a ya rufeshi dashi yana "wai meyesa kake so kaga kana bijirewa umarni na ne?

Yanzu kawai Dan uwarka bata da lafiya shiyasa Baka koma Villa ba tuntuni yo ko mutuwa tayi na baka umarni kak'i bi Akram abubuwan da kake min ya isa haka not any more yanzu ba zanyi tolerating wanan nonsense d'in naka ba idan muka fita operation dole ka ringa participating idan na saka doka dole kuma ka bi baka isa kuma ka bar cikin mu ba Dan idan kayi joining d'inmu ba fita idan kuwa ka dage zaka fita sai na kasheka na kashe family d'inka gudun tonuwar asirinmu yanzu ba anjima ba ka shirya ka tafi Villa jibi muna da operation and kai zakayi leading d'inmu ranar kaji mai nace ko baka ji"



Da k'yar Akram ya iya cewa naji sabida tsananin mamakin Yanda Alhaji Bala ya canza take ya fara tunanin ko dai Mai gida ya fara ganowa shi d'an lek'an asiri ne


Jikinsa na rawa yafara Neman oganshi Abdullahi dan ya gaya mishi halin da ake ciki





Shima mamaki ne ya rufe shi daya gama jin abinda Akram yace ajiyar zuciya ya sauke yacewa Akram "tabbas Alhaji Bala is up to some thing tunda kaji yace yanzu kai ma dole ka ringa participating idan ya fita operation"


Akram hankali a tashe yace "oga yanzu ya za'ayi nifa bazan tab'a iya wani Abu ba idan ya fita rashin imaninsa har fyad'e fa yake sawa ayiwa yaran mutane da matan su ni aganina kawai tunda mun Riga da mun samu evidences kawai gobe aje har gida ayi arresting d'in shi"


Da Sauri Ogan shi yace "aa Akram ai inaga yanzu ya fara gano ka ne so shi yasa yake so ya tabbatar ko kai d'an lek'an asirine yanzu abinda za'ayi idan yasan wata ai bai San wata ba ka shirya kaje ayau d'in kamar yanda ya bukata inyaso kafin Ku fita operation d'in ka ringa k'ok'ari kana sanin wanda za'aje ayiwa operation d'in idan yaso sai ka sanar damu ko ta text message ne mu kuma zamuyi sauri mu sanar dasu akan su bar gidan da dukiyarsu kar su kwana a gidan kai kuma u would pretend ka jagorance su aranar kai ma irin no mercy d'inan kaga idan kuka je ka babu Wanda zaku samu mun Riga da mun ruguje mishi plan bai Sani ba haka zamu ringa mishi a duk lokacin da zaku fita ka dai kawai ka ringa sanar damu gidan da za'aje kaga ahaka zamu kama shi red handed dan inaso aranar da za'a kama shi a har video covering da yan jarida zamu tafi inaso kafin muyi arresting d'in shi yafara samun failure a duk fitar da zakuyi"


Wani irin murmushi Akram ya saki yace "hakan yayi oga dama fargabana ace nima zan aikata wani Abu da hanuna da sunan investigation amma tunda zaa ringa rushe mishi plan fine ni kuma zan ringa updating d'inku inda za'aje operation Dan yana fad'a mana so I have to get going Dan yanzu yace na tashi na tafi wanan dajin"


Girgiza kai Ogan shi yayi game da jinjina k'ok'arin Akram akan aikinsa yace "Allah ya tsareka ya kare ka da karewarsa addu'ar mu na tare dakai"


Murmushin jin dadi Akram yayi yace "Ameen oga ngd bari na kira Mahaifiyata itama tayi min addu'a" ahaka sukayi Sallama


Akram ya kira mahaifiyar shi itama ta raka shi da addu'a




Alhaji Bala kuwa yana gama waya da Akram ya fito daga motar ransa a b'ace yana tunanin bai San mai Akram ya d'auki kansa ba dama mai gida ke hana shi yaci ubansa yanzu kuwa Tunda Mai gida ya ware dole ya bud'ewa Akram wuta operation da zasu fita next sai Akram yayi kisa ya kuma yi fyad'e wanan ya zama dole idan yak'i kuwa ya harbeshi


A Daren ranar Alhaji Bala Sam bai yi bacci ba yana ta bincike akan Alhaji Buba mai gwala gwalai hamshakin mai kud'in dake zaune a garin kano duk wani information da yake so ya samu akan shi ya samu Abu d'aya kawai ya rage mishi yasan yanayin gidan wayarsa ya d'auka ya kira wani sharon da bashi da aikin da ya wuce ya ringa mishi bincike akan yanayin gidan daza su je operation


Dan Sharon ya k'ware ta wanan fanin yana gama gaya mishi Sharon yace an gama shi dai yaji alert gobe zai ji cikakken bayani akan description d'in gidan


Washegari kuwa ya turawa Sharon kud'i


K'arfe Hud'u na yamma Sharon ya mishi sending description na gidan Alhaji Buba mai gwala gwalai


Murmushin nassara Alhaji Bala yayi ya d'auki wayarsa ya kira Killer


A lokacin duk suna zaune awanan k'aton palon har da Akram dake zaune acan gefe yana Dane Dane akan k'aramar wayarsa amma duk abinda su Killer suke yana kallonsu jin da Alhaji Bala suke waya yasa ya nutsu tare da baza kunnunwansa dan yaji mai yake cewa dan kaf a cikinsu da Killer kawai Alhaji Bala yafi yin waya


Bayan minti Biyar Killer ya katse wayar yana murmushi ya kalli su lion da hankalinsu gabad'aya yake kanshi ciki kuwa har da Akram yace musu


"Oga ne ya kirani yace gobe mu shirya da sassafe mu tafi kano mu sauka a gidansa na can dan k'arfe d'ayan dare zamu tafi operation gidan Alhaji Buba mai gwalagwalai yace akwai shegun idan ba'ayi wasa ba dukan mu sai mun samu one one million dan a gobe yake kai kud'in cinkinsa gida kafin ya kai banki"


Wani ihu su Lion suka saka Akram shima ya wayance yana ihun murna

Nan da nan kowa ya hau lissafin abinda zai yi idan million d'aya ta shigo hannunsa ciki kuwa har da Akram dake lissafi awayar shi na karya nan kuwa text message ya turawa Ogan shi akan gidan da zasu je operation gobe


Ogan shi kuwa yana recieving d'in text message d'in Akram ya tashi ya had'a kan yaransa guda biyu suka d'auki hanyar gidan Alhaji Buba mai gwala gwalai dan sananne ne


Suna parking

Please Login or Register in order to submit comment