Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da baki harbeshi ba halin da yake ciki kawai yanzu ya ishe shi dan har rok'o yake a harbeshi dan yanzu shi ba mutum ba haka zalika shi ba Dabba ba shi ba rayayye ba shi ba matacce ba Soul mate addu'a kawai zamu ringa bin mommy dashi dan nasha mafarki da ita tana ce min na kula daku and I promise insha Allah zan zame muku tamkar yaya pls stop crying ki daina zubar min da wannan hawayen naki mai tsada"


Akram yace yana share mata hawaye da handkerchief d'in hannunsa mai kamshi


Samha janye fuskarta tayi tace "I want to see him Akram inaso naga Alhaji Bala da idanuna inaso naga halin da yake ciki ganinsa ne kawai zai kwantar min da hankali in daina jin rad'ad'in danake ji a zuciyata"

Murmushi Akram yayi yace "Anything for you my princess your wish is my command"


Samha murmushi itama ta sakar mishi Akram ya koma ya zauna yafara janta da hira sai data fara kyalkyale dariya hankalinsa ya kwanta


As promise bayan kwana biyu Akram yaje gidansu Samha Dan ya kaisu su gano Alhaji Bala dan su Suhaima ma sun dage sai sunje sun gano shi su Saiam da Safna ma ba a barsu a baya ba dan burinsu suma suga yanda Alhaji Bala ya koma su cigaba da la'antar shi


Har suka je inda aka ajiye Alhaji Balan dake kwance jikinsa na fitar tsutsosi basu gane shi ba sai toshe hanci suke suna waige waige dan su gano inda Alhaji Bala yake


Akram murmushi yayi dan yasan bama su San mutum bane a kwance Samha juyowa tayi tace "wai yana ina ne"?


Murmushi Akram ya k'ara yi yace " Gashi nan a kwance a gabanku"

Direction d'in hannunsa suka bi da kallo idonsu ya sauka akan Alhaji Bala da babu ko fata a jikinsa sai kasusuwa da tsutsosi dake fita a jikinsa in badan yana numfashi ba tunani zakayi wani dabbar ne Rabin fuskarsa a kwailiye


A razane suka ja da baya suna gwallo ido suka kurawa Alhaji Bala ido


Saiam ce tayi k'arfin halin magana cikin inina tace "kana so kace mana wannan abun dake kwance Alhaji Bala ne"?


Akram girgiza mata kai yayi yace " kwarai shine ya koma haka bamu San mai yake damunsa ba zakiga yana ta ihu yana cizge fatar jikinsa yana fad'ar abubuwan da ya aikata yana ya tuba ya daina kullum sai ya rok'i a harbeshi ya mutu akan azabar da yake ciki"


Girgiza Kansu kawai suke yi suna mamakin halin da suka ganshi a ciki dan ko iya manya manya tsutsosin dake crawling a jikinsa ya ishe shi azaba


Samha na k'ok'arin magana Na Maliya ya bayyana yana kyalkyale dariya babu Wanda yake ganinsa sai Alhaji Bala


Alhaji Bala da muryarsa bata fita yana daga kwance ya fara ihu yana Na Maliya ya kashe shi ya huta

Aikuwa na Maliya na watsa mishi ruwan kaikayi ya mik'e da skeleton d'in jikinsa ya fara cizge Sauran fatar dake jikinsa yana ihu har Dana fuskarsa


A tsorace su Suhaima suka ja da baya suna kallon ikon Allah Alhaji Bala kuwa sai cizge cizge yake yi


Yafi k'arfin minti Ashirin ahaka kafin ya zub'e a k'asa yana kuka yana rok'on mutuwa tazo ta d'aukeshi


Girgiza kai su Samha kawai suke suna Al ajabin halin da suka ga Alhaji Bala a ciki Saiam kuwa cewa take lallai Allah ba azzalumin bawa bane tun a gidan duniya yake Hisabi ko ahaka aka bar Alhaji Bala ya girbi abinda ya shuka

Ahaka Akram ya maidasu gida suna Al ajabin halin da suka ga Alhaji Bala


Dangin Alhaji Nazifi kuwa ganin suna tayiwa Alhaji Bala zancen Aure yak'i basu had'in kai ne yasa suka sa ranar da za'a d'aurawa su Suhaima Aure shima zasu d'aura mishi da Nazifa Cousin d'insa
[8:15PM, 4/22/2018] ‪+234 813 272 6929‬: 🌑 🌑 *B🅰K'IN D🅰RE*🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑


*Written by*
💅💅 *Sadnaf*💅💅


*A heart touching story*



® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




*Follow me on Wattpad@Sadnaf*











*END*



Shirye shirye ake tayi kowane b'angare babu kama hannun yaro inda kan amaren ya d'au zafi ga exams da suke yi ga gyaran jiki da ake musu kullum basu da lokacin Kansu ko kad'an Dan ana musu gyaran jiki suna karatun exams basa ma iya wani wayan kirki da angwayen nasu sai dai messages dama tuni suka daina zuwa zance



Alhaji Nazifi kuwa gyara yayi wa gidansa sosai Dan sai daya canza komai na gidan ya koma sabo hatta b'angaren Hajiya Nafeesa sai da aka saka sababin furniture's dangi kuwa sai murna suke suna yayi gyaran gida adaidai kamar yasan shima angwancewar zaiyi.


Ba k'aramin kud'i ya kashewa su Suhaima ba komai iri d'aya yayi musu sai dai bambamcin kala d'an k'aramin lefe ya k'ara musu bayan uban lefunan da aka kawowa kowace a cikinsu abinda ake cewa gata kam sun same shi Dan wasu kayan ma sai su shekara biyu basu yi amfani dashi ba


Akwana a tashi babu wuya duk abinda aka sawa rana sai yazo an shiga satin biki an fara shagulgula duk da Su Suhaima sun ce basa San wani party waleema kawai zasuyi a ranar da akayi d'aurin Aure amma sai da Angwayen suka tilasta musu zuwa dinner da suka had'a gabad'aya a wani katon hall Amare sun sha kyau sai walwali suke Akram ya k'asa d'auke idonsa daga kan Samha sai kallonta yake yi Dan tunda yake da ita idan ka d'auke wet lips ko kwalli bai tab'a ganinta dashi ba sai gashi ta sha Heavy make up ta canza mishi kamar ba ita ba Samha kuwa kamar ta nutse Dan kunyar irin kallon da Akram ke binta dashi dan ba normal kallo bane daya saba yi mata



Ahaka taro ya watse cike da farinciki da annashuwa



Samha a ranar Sam bata ganewa Akram dan sababin abubuwa ya b'ullo mata dashi da suka je sauke su a gida kamar ba Akram mai kunyar nan ba rikice mata yayi yana matse hannayenta ita kuwa jikinta ya hau rawa wani irin tsoronshi ya rufeta data ga yanda idonsa ya kad'a yayi jajur dak'yar ta fusge hannunta ta fito daga motar aguje har suna bangaje juna da Saheebar da itama ta fito jikinta na rawa dan kamar had'in baki Yazeed shima birkice mata yayi yana Neman maida ta cikinsa sabida rungumar da yayi mata


Jiki a sanyaye suka k'arasa part d'insu kowace da tunanin da take a zuciyarta take tsoron angwayen nasu ya rufesu


Su Saiam kuwa sai tambayarsu suke abinda yafaru suka gansu haka babu wacce ta iya magana acikinsu suka fara k'ok'arin rage kayan jikinsu


Suhaima ce karshen shigowa itama kana ganinta kasan a firgice take a k'asa ta zube tana sauke numfashi dan dak'yar ta iya kwatar kanta a hannun khaleed dan shi har dasu kiss ya mata


Su Saiam mai zasuyi idan ba dariya ba dan ko basu fad'a musu ba sun gano su


Suhaima ce tayi k'arfin halin magana tana "Aunty wai dan Allah wane irin turare kika fesa mana haka gaskiya kar ki k'ara fesa mana bama so fyad'e Khaleed ya kusa yimin a mota yana tambayata wane irin turare na fesa mai d'aga hankali"


Babu abinda su Saiam keyi sai dariya Safna kuwa tace " kinsan nawa muka kashe kuwa wajen had'a muku turaren nan ai sai ma gobe wlh wanka zamuyi muku dashi"


Samha da Saheeba kuwa tunda kowacensu ta zauna suke ta sake sake aranau suna ta ganin kiran angwayen nasu suka k'asa d'agawa


Suhaima ce kawai bakinta bai mutu ba sukayi ta magana dasu Saiam dan su basa jin wani nauyin juna tamkar kawaye haka suke

Safna ganin bakinsu Saheeba ya mutu basa magana yasa ta koma tana tsokanarsu dan tun yanzu su bari ma sai gobe Saiam ta karashe da 'wayaga idon Auta gobe a karshen gado tana dan Allah Akram kayi hakuri"


Samha kuka ta fashe dashi tana ta fasa Auren su Suhaima kuwa sukayi ta mata dariya


Washegari k'arfe 11 dubanin mutane suka shaida d'aurin Auren Suhaima da Khalid Saheeba da Yazeed Samha da Akram a karshe yayan Alhaji Nazifi ya matsa kusa da liman ya mik'a mishi bandir d'in dubu hamsin yace a d'aurawa Alhaji Nazifi Aure da 'yar uwarsa Nazifa

Alhaji Nazifi k'asa kwakwaran motsi yayi sabida mamaki har sai da aka d'aura Auren shi da Nazifa surukan nasu sai murna suke dan dama suna tunanin yanda zai yi rayuwa shi kad'ai idan y'ay'ansa suka tafi gidajen mazajensu



Ciki kuwa amadadin farinciki kuka amaren suka fara yi da suka tuna Hajiya Nafeesa kafin kace me kowace ta fara k'walla tana ina ma Hajiya Nafeesa tana rayye taga Auren 'ya'yanta gabad'aya tuni mutuwarta ya dawo musu sabo fill aka hau koke koke duk yanda anwagwayen suka so suyi hotuna da amaren nasu sai hakura sukayi


Alhaji Nazifi kuwa ana gama d'aurin Aure ya nufi b'angaren Hajiya Nafeesa ya tafi can kuryar d'akinta ya kwanta akan gadonta ya d'auko hotonsu dake taya shi kwana ya kife kansa akai yafara kuka yana mata addu'oin samun rahamar ubangiji dan bai tab'a tunanin zai auri wata ba bayan mutuwarta shi da yake tunanin bazai iya rayuwar Aure da wata ba sai gashi an d'aura mishi Aure da Nazifa


Kuka ya sha sosai har sai da yaji kansa na Neman darewa gida biyu dak'yar ya iya mik'ewa ya wanke fuskarsa yafito sabida kiran da ake ta damunshi dashi a waya.



Ciki kuwa Sai a lokacin su Saiam suka ji labarin Auren Alhaji Nazifi da Nazifa

Sunyi farinciki sosai da d'aurin Auren dan suna ta tunanin yanda Mahaifinsu zai yi rayuwa shi kad'ai idan sun tare.

Ahaka aka cigaba da shagulgula k'arfe biyu aka fara Walimar da Yayan Hajiya Nafeesa ya had'a musu a harabar gidansa


Nasiha da wa'azi akayi musu sosai mai ratsa jiki sai zubar da hawaye sukeyi


K'arfe hud'u da rabi dangin khaleed suka iso dan tafiya da amaryarsu dan Bauchi za'a kai Suhaima

Alhaji Nazifi kuwa dama guduwa yayi daga gidan yace yayansa ya wakilce shi wajen yi musu addu'a dan Sam bazai iya jure ganin kukansu ba dan sai arasa mai rarrashin wani



Rungume juna sukayi sosai suna kuka kamar zasu shide dak'yar aka bambare su daga jikin juna


Ahaka aka tafi kai Suhaima gidanta sai kuka take

K'arfe shidda dai-dai aka zo tafiya dasu Saheeba dan gidansu d'aya da Samha Katanga ne kawai ya raba su hakan kuwa ba k'aramin dadi yayi musu ba dan at least idan suna ganin juna zasu ringa rage kadaici


Suna rungume da juna har aka kaisu gidajensu sai kuka suke kamar zasu shidde kan Samha kuwa kamar ya rabe biyu sabida kuka


Ana fita dasu Samha aka shigo da amarya Nazifa b'angaren Hajiya Nafeesa aka kaita itama sai fargabar irin tarb'ar da angonta Alhaji Nazifi zai mata take dan tana da masaniyar bai San da Auren ba sai yau




Sai k'arfe goma sha d'aya su Akram suka shiga gidajensu Akram kamar ya zuba ruwa a k'asa ya sha dan cikar burinsa


A can karshen gado ya hango Samha nata kuka ta rik'e kanta


Nufarta yayi da sauri tare da watsar da kayan dake hannunsa birkitota yayi gabad'aya jikinsa hankalinsa a tashe ya fara tambayarta abinda ya sameta


Samha kuwa luf tayi a kirjinsa tana nuna mishi kanta


Hannu ya kai ya tab'a kanta aikuwa yaji da zafi rau da sauri ya duro daga kan gadon ya had'a mata ruwa mai dan dumi dan tayi wanka


Ganin tana ta wani nonok'ewa da dukan alamu a tsorace take yasa ya rok'eta data kwantar da hankalinta babu abinda zai mata ta dai bashi had'in ya bata abinci tasha magani stress ne ya mata yawa

Da haka hankalinta ya kwanta ta shiga band'akin tayi wanka tana fitowa ya tura mata gashashen kazar da ya shigo dashi gabanta ya rok'eta taci ta sha magani dak'yar taci cinya biyu tace ta koshi ta dai sha yoghurt d'in sosai


Paracetamol biyu ya bata ta sha daga nan ya umarceta data kwanta tayi bacci

Kan gadonta ta hau ko minti biyar batayi ba bacci yayi awon gaba da ita dan tana da tabbacin babu abinda Akram zai mata


Akram kuwa shima kintsawa yayi yayi nafilolinsa ya kwanta abayanta yana karewa surarta kallo sai hadiyar yawu yake yi


Su Suhaima da Saheeba kuwa angwayensu basu d'aga musu k'afa ba aranar suka baje amarensu

Alhaji Nazifi kuwa Palo ya dawo ya kwanta dan Sam baya jin zai iya kwanciya da wata macen idan ba Hajiya Nafeesa ba Nazifa kuwa ganin bai kulata ba yasa itama tayi kwanciyarta da kudurin sai ta karkato da hankalinsa gareta.


Akram time to time ya ringa tab'a jikin Samha yaji kanta ya rage zafi ahankali shima bacci yayi awon gaba dashi yana rungume da Samha kiran sallar asuba ne ya tashe shi daga daddan baccin da yake ahankali ya matsa kusa da Samha ya fara hura mata iska a kunne da zumar ya tasheta amma me kamshin turarenta ne ya fara rikita shi daga hura kunne yafara kai mata kiss ko ta ina


Samha jiki na rawa ta bud'e idonta ta fara k'ok'arin tureshi daga jikinta amma ina hankalin Akram ba a jikinsa yake ba romancing d'inta kawai yake yana rabata da kayan jikinta kai kana ganin yanda ya rikice kasan jjc ne his new to the club


Samha kuwa tuni ta b'are baki ta fara kuka tana had'ashi da Allah da annabi nikuwa nace sorry dear Akram yayi nisa


Sai da ya maida Samha cikakiyar 'ya mace ya dawo hankalinsa daga nan kuma fa ya fara bada hakuri yana rarrashi


Samha kuwa sai kuka take tana ta tsaneshi ita gidansu zata koma


Dak'yar Akram ya shawo kanta ya gyara barnar da yayi






Akram ko k'ofar gida bai lek'a ba yana ta aikin rarrashi Samha kuwa sai Langab'ewa take


Daddare kuwa tana idar da Sallar isha ta kulle k'ofar d'akinta babu yanda Akram bai yi da ita ba akan ta bud'e k'ofar tak'i akan dole ya hakura ya tafi d'akinsa ya kwanta yana ta juye juye





A Daren ranar Alhaji Bala ya amsa kiran Mahallici bayan uban wahalar daya sha haka aka tattara kasusuwansa aka binne shi


Tuni labarin rasuwarsa ya zagaye ko ina daidaiku mutane ne kawai ke mishi addu'ar Samun rahamar Allah


Mahaifiyarsa tayi kuka tayi nadama da bata binciki irin sana'ar da Alhaji Bala yaringa yi ba gashi duk kud'in daya Tara da dukiyoyin da ya ajiye bai amfanesu da komai ba bai hana Alhaji Bala mutuwa ba bai hanata b'uya ta k'asa fitowa Cikin bainar jama'a


*3months later*


Idan kaga su Samha baza ka gane su ba sabida tsabar kwanciyar hankalin da suka samu a gidajen mazajensu


Mazajensu basu da wani burin da ya wuce su faranta musu dan suna balain sansu

Quote

*get married to the person who loves and is ready to spend d rest of his life with you than for you to marry d person who you love d person u loved would take advantage of that love u have for him and misbehave cos u are going to tolerate him bcos of d love u have for him but wen you get married to the person dat loves you so much dear u would be treated like a queen cos there is no any woman on earth that can compare herself with you and steal your man from you be wise in choosing your life partner don't go for what your hrt loves so much*



Akram kamar ya had'iye Samha sabida so da kauna

Samha kullum tana tare da Saheeba suna hirar yanda zasu ringa farantawa mazajensu kowace na d'auke da juna biyu


Haka ma Suhaima tana jin dadin zaman gidan Aurenta abinda ya rage mata jin dadi shine nisan da tayi da 'yan uwanta amma duk da haka kullum tana mak'ale da waya a kunnenta suna waya dasu


Saiam da Safna kuwa duk sun haihu sun sanyawa 'yay'ansu Sunan Hajiya Nafeesa dan dukansu mata suka Haifa 'yar Saiam ana ce mata momy yar Safna ana ce mata Ammi


B'angaren Alhaji Nazifi kuwa tun yana d'auke kansa yana nisanta kansa da Nazifa har sai da yazo ya fara kulata sabida yanda ta jajirce wajen faranta mishi rai duk wani Abu data San zai faranta mishi rai yinshi kawai take tuni shima ya koma d'an yaro yafara soyewa dan Nazifa dama yarinya ce tunda mijinta ya mutu bata k'ara Aure ba duk wata yakan lek'a gidajen 'ya'yansa yaga lafiyarsu


Hajiya Lubna kuwa tuni ta samu d'an garinsu ta Aura duk da yana da mata ita taje ata biyu hankalinta a kwance yake dan tasan irin sana'ar da yake yi idan ta tuna Naila takan yi kuka ta bita da addu'a





*Alhamdulillahi rabbil alamin anan na kawo karshen Bak'in Dare kura kuran danayi a ciki Allah ya yafemin ina kaunarku tamkar yanda kuke kaunata masoyana da bazarku nake dancing thanks so very much for d love and support sai kunjini sooner or later*
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment