Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na gaji da jiran ki a waje zan yi latti"

NUR dariya tayi tace"yanzu zaku tafi da anty zakiya "

Zakiya ko dariya ta keyi ganin TASLEEM bata gane su ba

Tace"baby ga mummy ki can ni anty zakiya ce"

Nur tace"baki gaya min plan din ba"

Zakiya tace"ni zan je office din sir Afan a madadin ki"

Nur ta zaro ido tace"kina ganin ba zai gane ba?kuma ya zaki yi da naki aikin?"

Zakiya tace"ba zai gane ba kin manta lokacin da muke remedial na taba yi miki test,kuma maganar aiki na kuma sir sameer yayi tafiya"

NUR tace"OK sai kin dawo karki damu da TASLEEM zan d'auko ta in an tashi daga makaranta yau 12:pm zasu tashi suna test,please zakiya karki yi fad'a dashi"

Zakiya tace"OK sai na dawo"

8:30am zakiya ta isa office direct office din sir Afan taje

Tana zuwa ta tarar da AFan zaune da sameer karasawa tayi ta gaishe su,sameer ne kadai ya amsa yana ta kallonta har ta je inda NUR ke zama ta zauna

Afan yace"ina jin ka bro"

Sameer yace"yau zani UK kwana uku zan yi kafin in dawo please ga amanan NUR da zakiya na barma ka kula da su har in dawo,komai ya faru ka jira ni sai na dawo"

Cikin mamaki Afan yace"meya had'a ka dasu kuma?"

Sameer yace"babu lokaci yanzu in nadawo zan ma bayani,amma dan Allah kayi min alkawari zaka kula dasu"

Afan yace"naji"

Sallama suka yi sameer ya fito gaban tebur da zakiya ta zauna yaje yace"ina zakiya ban ganta a office ba"

Zakiya tace"sir yau zakiya ba lafiya shiyasa bata zo ba"

Dariya ta so bashi amma ya dake yace"zo mu je mota ki ansowa zakiya sako"

Tace"toh"

Suna fita Afan ya tabe baki yace"aikin banza zubar da mutunci ba mamaki son su yake"

Suna kaiwa mota ya shiga,itama zakiya shiga tayi tace"bani sakon sauri nike"

Kallonta yayi sai yayi murmushi yace"zakiya meya haka ina NUR? "

Zakiya tace"na fad'a maka zakiya na gida"

Sameer yace"wai kina nufin ban gane ki bane?"

Murguda me baki tayi tace"toh miye dan ka gane ni?in tambaye ka yama akayi ka gane ni?"

Sameer yace"saboda NUR ta fiki natsuwa da hakuri,da a ce NUR ne da bazata shigo mota ba sai nace ta shigo,kuma bazata ce bani sakon sauri nike ba,kuma NUR bata d'aga hijabi ata baya"

Tace"toh sannu mutan da"

Yace"OK bani number ki airport zani"number ta bashi

Yace"zakiya please stay out of trouble "

Tace"I will try safe journey"

Yace"tanks"

Fita tayi,driver ya ja motar

Tana komawa office Afan yace"ta yi plan din wani building "ai zakiya na jin plan ta dauki jaka tayi gida tace"ba dani ba ni ba abinda na karanta ba kenan"

Labari ta baiwa NUR tace"gobe ma da TASLEEM zani office domin suna midterm break"

zakiya tace"sai kuje tare"

washe gari NUR ta shirya TASLEEM suka tafi office

suna kaiwa zakiya ta tafi department dinsu NUR ma ta tafi tasu

a receptionist ta tarar da sir Afan da file a hanun yace"ke zo nan"

tafiya NUR ta fara yi sai dai kafin ta karasa gaban shi Afan yasa mata kafa ta fadi kasa

dariya ya fara yi inda staff din suka taya shi TASLEEM ne kadai tace"sannu mummy tashi"hawaye ne ke zuba a idon NUR

Afan yace"kad'an kika gani tunda har kika mari ni gaban staff dina,wallahi na tsane ki,I hate you with passion kin yi min wasa da zuciyata"(me Afan ke nufi da NUR ta me wasa da zuciya?)yana gama magana ya shige office din shi

mikewa NUR ta yi ta kama hanun TASLEEM suka bi bayan shi

tana shiga office ta zauna ta fara aiki kamar babu abinda ya faru

bayan minti ashirin sai ga matan nan na rana nan Fatima ta shigo office din

Afan na ganin ta ya mike ya rungumeta yace" my only best friend in our family" murmushi tayi tace"bayan ka guje ni tunda kawata bata raye"

yace"ba haka bane dear aiki ne ya rike ni"

tace"alright ba komai na sami labarin kana minna shiyasa na nimi transfer zuwa news line tunga"

NUR dai kallon su take tana jin murya Fatima kamar ta taba jinshi a wani wuri

har TASLEEM ta sulale taje gun Afan ba tare da ta sani ba domin aiki take yi kuma tana lura da Fatima haka kawai ta ji bata yarda da Fatima ba

d'aukan TASLEEM Afan yayi ya azata a tebur sai surutu take zuba me

wani haushi ne ya kama Fatima ganin Afan ya manta da ita

tace"wai yar waye?"

kafin Afan yayi magana wani saurayi ya shigo

yace.....

gaskiya bana jin dadin wanan complain din nan da kukeyi na page yayi kadan ina so Ku sani takura kaina nike yi dan in faranta muku ga aikin gida ga hidimomi amma haka nike kokarin dan in faranta muku wasu har pc suke bina toh a daina in ba haka ba zan rage yawan page din kuma in maidashi page daya a rana

maman
noorul
hudah
luv u my fans
pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOURS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

LITTAFAI NA

1 EESHA
2IKLAS
3IMRANFAD
4MATAN GIDA
5RAYUWAR NUR

Dedicated to MAMAN NOORUL
HUDAH FANS CLUB

πŸ…Ώ4⃣9⃣&5⃣0⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Saurayi da baze wuce shekara 27 yace"oga an dawo da motar"

Afan yace"OK"

Kallon Fatima yayi yace"ya'ta ce"

Ba fatima ba har saurayi sanda ya juyo ya sake kallon TASLEEM

Wani murmushi saurayin yayi Wanda bansan na miye ba

Har ya kai kofa zai fita Afan yace"umar a kai d'ayan motan wanki"

Umar yace"OK sir"sanan ya fita"

Fatima tace"me kake nufi da yar ka ce?"

Dariya yayi yace"ban isa bane in haifeta?"

Tace"Afan please be serious "

Yace"yar wancan yariyar ne"

Ajiyar zuciya Fatima ta sauke a ranta tace"ashe ma matar aure ce bani da matsala da ita"

Afan yace"amma meyasa kika firgita dana ce miki ya'ta ce?"

Tace"babu na daiyi mamaki ne dan nasan tun rasuwar summaiya baka sake aure ba"ta karasa maganar cikin kuka

Yace"fatima ba kuka zamu yi ba addu'a zamu ta mata,nasan summaiya kawar ki ce amma dole zamu hakura tunda ta Riga mu gidan gaskiya,nidai addu'a ta shine Allah ya tona asirin duk Wanda yake da hanun a kisan ta Allah kar ya bashi abinda yake so,Allah ya......"toshe me baki tayi tace"ka barsu da Allah kawai"

bangaren umar ko yana barin office din kiran abokan shi yayi yace"na samo hanyar kudi"

abokin shi da suke harkan kidnapping yace"ina ka samo nama"

yace"a inda nike zuwa d'aukar mota in kai wanki ne nike so a sace yariyar oga domin suna da kudi sosai"

dariya abokin nashi yusufa yayi yace"yaushe zamu zarta?"

umar yace"ko gobe ne"

yusufa yace"shiyasa nike Sonka baka bari ta kwana"

nur ko d'agowa tayi ta gan babu TASLEEM a inda ta ajiye ta

mikewa tayi ta fara nimanta kamar ance kalli can sai ta hango TASLEEM zaune a tebur din sir afan

karasawa tayi tace"TASLEEM zo muje ki ci abinci"

TASLEEM tace"no mummy banji yunwa ina koyawa daddy karatu ne a suratul Al-ahgaf Haa-meem kenan "

NUR zata yi magana Afan yace"jeki in ta gama zata fito"domin shi yarasa dalilin dayasa yake jin son TASLEEM har cikin ranshi ba,ga ta da ilimin boko da na addini,wani lokaci har mamakin irin tarbiyar da akayiwa TASLEEM yakeyi

NUR babu inda ta iya ta fita fatima ko wani haushi ne ya dibeta tace"baby jeki wajen mummy ki"

Afan yace"no barta kawai ina jin dadin kira'a ta ne"

NUR dawowa tayi ta zauna ta cigaba da aiki,kallon kofar office din Afan tayi ta kalli fatima sai kuma tayi shiru kamar Wanda ya tuna wani Abu

muryar matan da ta kira bullet ta tuna inda take cewa"ka kashe min ita da abinda ke cikinta"sai kuma ta tuna da summaiya ta kira ta da fatima,

NUR tace"ko dai itace ta ba da kwangila kashe summaiya?"

jikin NUR ne ya fara rawa addu'a take Allah ya kare TASLEEM daga sharrin makiya

bangaren zakiya ko waya suke da sameer hankali kwance inda yace"mata yana asibiti ne ana gudanar da bincike"godiya ta mai suka yi sallama

4:pm nayi NUR ta kama hanun TASLEEM suka je office din zakiya daga nan suka yi gida

washe gari da safe suka zo office yau ma da TASLEEM aka zo kasancewar mid-term alhamis ne da juma'a kuma yau ta kasance juma'a sai Monday zasu koma school

yau ma gun Afan TASLEEM taje tana zuba surutu Wanda rabi kira'a ne

suna zaune Afan ya tashi yace"baby tashi muje shan ice cream"

tace"yeah"


yana fitowa ko ta kan NUR babi ba ya wuce ta rike da hanun TASLEEM

NUR taso tayi magana amma tsoro ya hanata

ostrich tunga ya kaita ta sha ice cream me sanyi gaske

sanda ya bari ta gama yace"muje office "

sai dai suna fitowa wani mota ya sha gaban shi kafin yayi wani kokari sun d'auke TASLEEM sun tafi da ita da gudun bala'i

tsayawa yayi yama rude ga mutane sun fara cika wurin

sanda ya kai awa d'aya sanan ya Shiga mota

office yaje direct ya tarar da NUR na aiki wuceta yayi ya je ya zauna

ganin ya dawo shi kadai yasa NUR bin bayan shi

tace"sir ina TASLEEM lokacin shan maganinta yayi"

kalllonta yayi yace"an tafi da ita"

cikin rashin fahimta NUR tace"ina?kuma waye?a ina aka kaita?"

yace"nima ban sani ba amma zan sa a nimo ta"labarin abinda ya faru ya bata ai sai NUR ta fadi summamiya"

tarota yayi ya fara kiran sunan ta

NUR ki tashi amma shiru

toilet yaje ya dibo ruwa ya yayayfq mata amma ba labari

ruwan roban ya juye mata gaba d'aya sai a sanan ta ja wani dogan ajiyar zuciya ta saki wani kuka tare da rike kola rigan Afan tana cewa,wallahi sai ka fitar min da ya'ta

police ya kira yayi filing complain har office suka zo d'aukan rohoton daga bakin Afan

a receptionist suka tsaya NUR da Afan suka fito

jin ihun NUR yasa zakiya fitowa NUR na ganin zakiya ta saki kuka da ya d'agawa zakiya hankali karasawa inda take zakiya tayi tace"my NUR meya faru? "

NUR ko ta kasa magana sai cewa take TASLEEM TASLEEM

zakiya tace"meya sameta eh"

NUR fashewa tayi da kuka cikin kuka zakiya ta yi mata ihu tace"ki fad'a min abinda ya faru please my NUR "

sai a lokacin NUR tace.......


fans please kuyi hakuri da halin da nur zata shiga nan gaba domin shine darasin littafin domin a zamanin nan da amana yayi karanci ba kowa zai iya fuskanta kalubale saboda d'an wani ba amma NUR ta daban ce kuma zata kare TASLEEM a kowani hali
Allah yasa mu dace

maman
noorul
hudah
luv u my fans
pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to MATAN GIDA fans group 1&2

πŸ…Ώ5⃣1⃣&5⃣2⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

NUR tace"zakiya an sace TASLEEM "

Zakiya tace"what?a ina"itama kukan take

Afan na cikin magana da police wayar shi tayi kara dubawa yayi ya gan bakuwar noba

Police yace"wanene?"

Yace"sabon Noba ne"

Police yace"d'aga mana kila kidnappers ne"

D'agawa yayi sai yaji wani murya kato na cewa"hello mune muka d'auke maka ya'in kana son ka ganta ka bamu kudi miliya ashirin"

Yace"what?miliyan ashirin"

Zakiya da NUR sanda suka mike police yayi me alama da hannu yasa a speaker

A speaker yasa NUR taje kusa dashi

Yusufa yace"in kana son ganin yar ka a raye ka bamu abinda muke so,kuma karka kuskura Ku sanan da yan sandw in ba haka ba,ka sinci gawan yar ka a bayan gari
Mun baka nan da awa ashirin da hudu ko mu kasheta"kwace wayar NUR tayi tace"dun Allah Ku rufa min asiri Ku bani ya'ta wallahi ba yar shi bane na roke Ku"kuka take kamar ranta zai fita

Ji tayi ance zamu kira Ku mu sanar daku inda za a ajiye kudin"diff an kashe wayar

NUR ta saki kuka tana surutai kamar zautaciya

Zakiya ma kukan take

Police yace"zasu sake kira,in suka kira ka ce sai ka ji muryarta kafin ka bada kudin dan mu tabbatar tana raye"

Yace"OK "nur ko rike kafar d'aya daga cikin polisawan tayi tace" dun Allah Ku rufa min asiri Ku ceton min ya'ta wallahi banda alaka dashi"

Suka ce"karki damu yar ki na lafiya"

Wayar afan ne yayi karan shigowar test dubawa yayi ya gan video ne

Ai sai ya gan TASLEEM a daure numfashinta na sama-sama

Kallon.police din yayi yace"video suka turo"da sauri NUR da zakiya suka kwace wayar suka fara kallon video

ganin Inda TASLEEM ke numfashi yasa NUR durgusawa ta saki kuka tace"TASLEEM karki min haka ke amana ce a guna " kallon d'an sanda NUR tayi tace"oga in baka yi wani abu ba zamu iya rasa ta domin tana da chronic asthma kuma da alamun ana shan taba ko wiwi agun"

kafin police yayi magana sai suka ji dariya a wayar yusufa yace"watoh baku ji gargadi na bako?nace karku sako yan sanda shine zaku sako su domin yanzu haka ku na tare da yan sanda"

NUR na jin haka ta mike ta fara koran yan sanda,amma sunki wucewa

gajiya tayi ta barsu,a haka Fatima ta zo ta same su d'aya daga cikin staff din ta tambaya ya bata labarin komai"

Afan yace"ina zuwa in kira manager banki na ya had'o kudin"

juyawa yayi ya shige office Fatima ta bishi tace"afan me kake shirin yi ne kana nufin zaka biya kudin ne?"

yace"eh Fatima in wani abu ya same yariyar nan bazan yafewa kaina ba Inda take numfashi nan za a iya rasa ta a cikin awa d'aya kacal in ba yi wani abu ba kin manta summaiya ma tayi fama da wanan ciwon?"

tace"karka fad'a min ka yarda da wanan yariyar ni fa ina zaton baki ta had'a da su dan su ansa kudi a gun ka,ka manta inda safeena ta taba yiwa sameer ne? su fa talakawan nan haka suke toh in ba ita ba ya akayi suka San ka fita da ita, nifa tun farko ba yarda da ita ba"

yace"kuma kina da point"fitowa yayi ya samu police din yace"shifa yana zargin da sa hanun NUR a sace TASLEEM dan haka shi ba zai ba da ko sisi ba"

wani irin kallo zakiya tayi me zata yi magana NUR ta hanata tace"Allah ya isa sakanina da kai amma ina guje maka ranan da zaka gane gaskiya domin a lokacin babu TASLEEM a kusa da kai,domin zaka rayu ne da nadamar ka kashe yar'ka da kanka akan abinda kafi karfin shi"tana kaiwa nan ta bar building din

a ranshi yace"me take nufi da zan kashe ya'ta da kai na?"

itama Fatima maganar ya tsaya mata a rai

zakiya ko office din su ta Shiga ta dauki Jakarta ta fita

haka NUR tayi ta yawo a titi tana kuka da niman taimako sai dai daga mai bata dari biyu sai ashirin har naira biyar ma

zakiya ko gida ta dawo ta d'au nan NUR ta dawo amma bata same ta ba

noban sameer take trying amma bai shiga

har sha biyu dare NUR bata dawo ba hakan ba karamin tashin hankali zakiya ta shiga fitowa tayi cikin Daren itama ta fara niman NUR tana surutai akan rashin dawowan sameer domin kwana shi hudu kuma a kwana uku yace zai dawo

tana cikin tafiya dai-dai wajen primary skol ta fara jin sheshekar kuka,dawowa tayi ta shiga ajin da kukan ke fita ta kunna wutan wayarta

NUR ta gani zaune a kujera tana kuka rike da dari shida da hamsi

da gudu zakiya taje ta rungumeta suka saki kuka mai cin rai

janta zakiya tayi zuwa gida sai dai babu Wanda ya runtsa sai kuka

NUR ko inhailer TASLEEM ta rike tana kuka

U S
[11/06, 16:50] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

dedicated to my LOVELY MOM
πŸ…Ώ5⃣3⃣&5⃣4⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

U S

A cikin kwana biyu aka tabbatarwa sameer zakiya da NUR yan biyu ne tun a asibiti ya kira ummi ya sanar da ita inda sukayi da zakiya da kuma sakamanko test din

Ba karamin dadi ummi taji ba

Tace"kenan sun tabbata yaran Hauwa ne? tace"amma sai sun gan abban su ya fad'a musu inda akayi zakiya ta b'ace"

Sameer yace "toh a ina za a samu abban nasu?"

Tace"jiya aka samo min number abokin kasuwanci shi wanda suke kasuwanci a Cameroon kafin ya auri hauwa, kuma ya bani number shi da adireshi asibiti da yake a Saudi"

Sameer yace"ki turo min gobe zani in ji ta ba kin shi"

Ummi tace"son baza ka huta ba?"

Yace"karki damu alkawari ne na d'aukawa zakiya zan taimaketa kuma dole in cika"

Tace"OK bari in turo Allah ya maka albarka"

Sameer yace"ameen ya jikin alhaji tsoho?"

Tace"da sauki"

Bayan ummi ta tura me address din da sunan asibiti"

Da safe sameer ya tafi saudi, bai sha wani wahala ba ya samu asibitin

Kiran wayar Abba yayi cikin ikon Allah bugu biyu ya d'auka

Bayan sun hadu sameer yayi me bayanin kanshi

Domin alhamdulillahi jikin da sauki

Sameer yace"Abba wai anty hauwa yan biyu ta Haifa ne?"

Abba yace"eh amma ban sani ba sai wata uku da suka wuce ta hanyar wani hira da naji maimuna tana yi da mahaifiyarta (anty amarya)watoh kishiyar ummana,basu San ina kusa ba sai maimuna tace "inda na sace yar da hauwa ta Haifa na wurgar a bula haka nasa alhajin korar NUR da ta girma domin nasan NUR baza ta yi zina ba har ta Haifa d'an shege,amma da yike na shanye alhaji sai ya Kore ta da hanun shi ni kuma na samu wuri ina wasa da dukiyar shi,sai dai abin takaici bani da haihuwa"

mahaifiyarta tace"yanzu ko yar na raye ko mace babu Wanda ya sani, kuma babu Wanda ya taba zargin NUR yan biyu ce"

tace"ai bayan na saci yar na koma nayiwa nurse barazana da Dr akan cewa in suka kuskura suka fad'a sai na hallaka su"tafawa suka yi inda mahaifiyarta ta dinga fad'i asiri da suka yiwa abbana dani

jin su suka kashe hauwa yasa nan take paralysed ya kama ni na daina magana dama ina fama da hawan jini,ba karamin wulakanci na gani gun maimuna ba dan bani da lafiya hakan yasa mahaifiyata zuwa kiran alhaji bashir Wanda ya baku addreshi na domin da taimakon shi aka kawo ni nan Saudi ko sau d'aya maimuna bata zo ta duba ni ba amma da na ji sauki zan nimo ya'ya na ko da kuwa NUR cikin shage tayi Wanda nasan baza ta aikata zina ba"

sameer yace"karka damu NUR da yar uwarta zakiya suna cikin koshin lafiya domin Allah ya dade da had'a su"

Abba yace"zan so in gansu in nimi yafiyar su ba da San raina nayi ta wulakanta NUR ba"

hajiya tace"ai sun ce zasu sallame mu nan da kwana uku nima ina so naga jikoki na"

Abba yace"sameer ka tsaya mu tafi tare mana"

babu inda ya iya yace"toh"domin yana so ya bawa zakiya mamaki hakan ma yasa be kirata ba

ummi kawai ya kira ya fad'a mata inda suka yi da Abba tuni ta Fara kiran dangi akan an gan ya'yan hauwa

zainab da ihsan suka ce suma zasu Nigeria Amina ma haka kanwar sameer itama zata

alhaji tsoho ma haka kowa zaije nan da kwana uku

Nigeria

washe gari da asuba NUR ta tashi ta fita domin bayan sunyi sallah asuba bacci ya d'auke zakiya bata masan NUR ta fita ba

sai karfe 7:am ta farka,amma bata gan NUR ba

tace"yau za a yi ta kare domin yau sir Afan zai San wacece TASLEEM a gun shi"

bayan tayi wanka hijabi tasa ta fita sai AFSAMAN builders

direct office din Afan taje inda ta tarar dashi da Fatima

a fusace zakiya ta karasa gaban shi tace"ka iya barci jiya?"

yace"wanan wani irin iskanci ne haka?"

zakiya tace" babu d'an isaka a duniya kamar ka wanda ya kasa ceto yar'sa agun kidnappers,tur da me hali irin naka"

mikewa yayi ya d'aga hannu zai mareta ai sai zakiya ta rike hanun tace"karka kuskura domin ni ba NUR bane da zata raini yar ka kuma ta dauki nonsense a gun ka,wallahi in ka taba ni zaka sha mamaki,toh ina son KA SANI YAR KA CE A GUN KIDNAPPERS.HAUWA UTHMAN ADAMS YAR DA KA HAIFI DA MARIGAYIYA SUMMAIYA wallahi in ka bari wani abu ya same ta zaka yi nadama har karshen rayuwar ka"

babu abinda ke amsa kuwa a kunne shi kamar kalmar YAR KA CE A GUN KIDNAPPERS HAUWA UTHMAN ADAMS

Fatima ne tace"ke ba musan karyar banza ai summaiya shekararta bakwai kenan da rasuwa"shiko ya kasa magana idonshi ya canja kala

zakiya tace"ai summaiya ce ta mutu ba yar ba ko kun gan gawan yar a gun da aka gan gawar summaiya?"

kalonshi Fatima tayi jikinta rawa yake domin ta d'au asirinta ne zai Tonu a ranta tace"bari in juya zancen inda babu Wanda zai zarge ni"

a fili tace"kenan kina nufin NUR ne ta kashe summaiya ta sace yar?"

zakiya zata yi magana fatima ta katseta da cewa"Afan shikenan NUR nada hanun a kashe summaiya"sai ta fashe da kuka

zakiya tace"baka da lokaci domin TASLEEM na da chronic asthma Wanda ta gada ne a gun uwata"

kallon zakiya yayi tace"kwarai kuwa"

NUR ne ta shigo ko takalmin babu ta gama yawo niman taimako amma babu Wanda ya taimaka mata ko dan kwalli babu ta kama kafar Afan tana cewa"ka dubi girman allah ka taimaka min ka ceto TASLEEM"

d'agata zakiya tayi tace"enough in ya gama dama ya barta ta mutu ai shine ubanta"

tureta yayi ya fita police ya kira cikin kankanin lokaci suka zo

manager banki cikin minti 30 ya kawo kudi a buhu,jikin Afan rawa yake"

kiran kidnappers din ne ya shigo wayar Afan ai kafin suyi magana yace"a ina zan same ku?"

suka ce ba kai zaka zo ba,ka ba wani

yace"OK"

suka ce kuma mace yace"angama"

NUR tace"ni zani"zakiya tace"ki bari ni in je"

NUR tace"ki yi hakuri ni ya dace inje

police yace"amma dole za a je da ambulance saboda yariyar ba lafiya muma zamu biko a baya"

Afan yace"no officer bana son nayi taking risk in suka San ka bita zasu kashe hauwa"

officer zaiyi maganan Afan ya katseshi

ambulance aka d'auko NUR ta Shiga sai inda suka kwatata musu sai dai kidnappers din na ganin Motan

ambulance suka


maman
noorul
hudah
luv u my fans
pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


Dedicated to IMRANFAD FANS GROUP

πŸ…Ώ5⃣5⃣&5⃣6⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Suna ganin motan ambulance Wanda suka tabbatar police na ciki domin ko NUR bata San akwai yan sanda ba a ciki ba

Ashe har da driver police ne kuma umar duk ya sanar dasu amma suka ce gwamma ayi ta takare domin baza su iya barin miliyan ashirin ya wuce su ba a banza

Parking driver yayi ya fito ya jigina da Motan

Fitowa NUR tayi da jakan kudi ta fara tafiya wajen drum din sharan da aka ce ta saka kudin

Binta driver yayi a baya sai kawai suka ji halbin bindiga daga baya

Jiki na rawa NUR ta fara waige-waige amma bata gan kowa ba amma driver ya fadi kasa da alamun shi aka halba

Karasawa tayi ta saka kudin cikin drum

Sai ga wani ya zo d'auka,amma kafin ya d'auka police sun halbe shi a baya

Sauran fitowa suka yi aka fara halbe-halbe,ran NUR b'ace wa yayi ganin yan sanda sun biyo su tsoronta kar a kashe TASLEEM dan haka ta fara gudu tana kiran sunanta amma shuru

ga yan sanda sai halbi suke kidnapers na mayar da martani

wani gidan kara NUR ta gani a dajin da gudu ta fara zuwa wurin

har ta fadi kanta ya bugi dutse,ba karamin ciwo ta ji ba amma ta cigaba da gudu ganin jinin yaki tsayawa yasa ta cire hijabin ta ta d'aura a gun ta cigaba da gudu har ta shiga dakin kara

a kwance ta tarar da TASLEEM babu alamun numfashi tartare da ita ai ihu tayi tana kiran sunanta

ganin kuka ba zai fishe ta ba yasa ta dauke TASLEEM ta aza a wuya ta fito

gudu take da TASLEEM a baya har suka iso wajen ambulance cikin motan ta saka ta

ta shiga mazaunin driver ta ja motan da gudu Wanda bata Masan tana yi ba

nan ta bar yan sanda suna shirmen su

AFSAMAN building company

Afan sai zurga-zurga yana up and down ya kasa tsaye ya kasa zaune zakiya ko zama tayi ta had'a kai da guiwa tana risgan kuka addu'ata Allah ya dawo da my NUR dinta lafiya

tuni yan jarida suka fara yad'a labari da gaskiya fa karya akan an sace yar UTHMAN C E O Afsaman builder Wanda wanan aikin Fatima ne ta sanar dasu

Fatima tace"gaskiya be kamata a bar NUR ba tare

Please Login or Register in order to submit comment