Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawo kuma tace"ni zan iya d'auka komai amma in aka tabo mai NUR ban San meyasa ba sai inji jinina ya fara gudu a 360 kuma in haka ta faru zan iya cin mutuncin koma waye.so beware"tana gamawa ta bar office din

Toilet ta shiga ta kunna famfo ta wasawa kanta ruwa sanan ta saki kuka mai karfi

Domin ta ji zafin Kiran su da yayi da karuwai amma bata son ya gane shiyasa bata yi kuka a gaban shi ba dan kar ya gane weakness dinta

Tafi minti ashirin tana kuka sanan ta wanke fuska ta fito ta cigaba da aiki kamar babu abinda ya faru

bangaren NUR ko cikin kwarewa tayi bayanin plan din ginin da tayi planing a meeting inda kowa ya gamsu har da tafa mata daga karshe akayi signing contract din wa Afsaman building company

Afan yace"ke bani files di nan inyi sighing in turawa audit department na flims suyi treating in sun gama su turawa sameer yaduba"

tace"toh"

Jakarta ta fara dubawa bata gani ba tace"sir yi hakuri na manta da shi a mota"

ai a fusace yace"ke meyasa baki San komai ba sai bin maza eh"kowa a wajen sanda ya juya ya kalleta

Afan yace"yes gaskiya ne maza ta ke bi domin zaman kanta take karama da ita tasan dadin namiji"

hawaye tab a idon nur,wani dattijo ya kalleta yace"ya'ta zo nan"

da k'yar ta ja kafafunta da yayi mata nauyi ta karasa gaban shi

yace"ki daina bin maza kin ji ba abu ne me kyau ba,me kike nima gaki da kyau ga ilimi"

bata iya magana ba sai ma fashewa da kuka da tayi

shiko manager din flims sai signal yake mata

Afan a ranshi yace "sai kin yi da na sanin mari na da kika yi a gaban staff dina bazan kawai"

a haka meeting ya tashi jiki sayaye NUR ta bar building din taje ta shiga mota tana shiga Afan yace"get out"

fita tayi ta karasa bakin titi ta tari napep ta shiga bata koma office ba makaranta su TASLEEM taje ta d'auketa suka tafi gida

sameer ko bayan sun gama magana da zakiya tunani ya fara inda zai kwace wayarta sai dai damuwarshi tace ba wayar ta kadai yake ba

amma ya dau alwashin goge shi ko ta halin kaka koda kuwa na wayar ta ce kadai

4:pm zakiya ta koma gida ganin NUR tayi fuska a kumbure alamun ta sha kuka,ganin haka yasa ta boye nata damuwa tace"my NUR meya faru ne na gan fuskarki haka"

NUR ta fashe da kuka cikin kuka ta bata labarin abinda ya faru

abin ya matukar taba zakiya amma sai ta daure tace"daga yau karki kara yi me kuka,kuma ki cigaba da aikin ki saboda TASLEEM zamu jure cin fuskar shi da mun gano Wanda ya bawa su bullet aiki zamu mika me yar'shi mu kara gaba domin nima ina son in fara niman iyaye na da taimako wanan abin wuyar

Ciro shi tayi ta nunawa NUR

NUR tace"kullum in na gan wanan abin wuyar sai yayi kamar na taba ganin shi a wani wuri"

zakiya tace"kullum haka kike cewa amma har yau baki tuna ba,ki shirya TASLEEM mu ajiyeta a islmiyya DJ ya kaimu bye-pass koyon mota"

tace"toh"

a islamillaya suka ajiye TASLEEM sanan DJ ya kaisu bye-pass inda NUR zata koya mota domin zakiya ta iya kuma tayi haka ne dan kar su zauna cikin damuwa"

Cameroon

ummi ne zaune gaban alhaji tsoho watoh mahaifinsu

yace"hafsat wai har yazun baki koma Nigeria ba"

tace"inashaallah zan koma sati nan dama kasuwanci ne ya rike ni a nan"

yace"



maman
noorul
hudah
luv u my fans
pls share
[10/06, 02:26] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we the best among the rest.

Dedicated to AYSHMAN 4real (indo)

πŸ…Ώ3⃣9⃣&4⃣0⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace"amma ya maganar yaran da kika ce suna kama da hauwa"

Ummi tace"suna aiki a company mu a Nigeria abinda ke d'aure min kai shine sun ce su ba yan uwa bane domin d'ayan sunanta NURUL HUDAH ABUBAKAR MUSA

D'ayan kuma AISHA IDRIS amma ana ce mata zakiya abba wallahi kamar su d'aya babu ko babanci

Amma da na tambaye su ko su yan biyu ne sai suka ce ah'ah kawance ne kawai NUR tafi kama da hauwa harda murya kuma nafi kyautata zaton itace yar hauwa domin daga sunan mahaifinta za a gane,sai dai ita kuma zakiya kamarta d'aya da yaya Mohammed (Abban sameer)daman kasan hauwa tafi kama da shi"

Yace"amma baki tambayi sunan mahaifiyarta ba"

Ummi tace"na tambayesu ita zakiyar tace balkisu ita kuma NUR tace hauwa ka gan alamu sun nuna NUR ce yariyar hauwa,har kano naje gidan alhaji abubakar amma aka tabbatar min yana asibitin Saudi ba lafiya wata na tarar da alamun matar shi ne sunanta maimuna abun mamaki ina tambayarta hauwa ta hau ni da fad'a ta Kore ni,washe gari na dawo na tambayi mai gadi nan yake sanar min hauwa ta dade da rasuwa wajen haihuwar yar'ta NUR nace me ina NUR din take nan yake sanar min NUR ta bar gidan sanadiyar dawowa gida da tayi da jaririya mahaifinta ya koreta wanda tun lokacin ya kwanta ciwo,nace toh ya nuna min gidan mahaifan alhaji"

Yace"ko naje babu Wanda zai kula ni domin duk an asirce su mahaifiyar shi ce zata saurare ni kuma tana Saudi tana jinyar d'an ta"

Dana tambaye shi inda zan samu NUR shine yace"bai sani ba amma yana zaton zan same ta a minna ne domin nan take makaranta a da"

Shiyasa dana buge ta a titi na bita har gida na gan yar Wanda yanzu zata kai shekara bakwai itama yar kamar su d'aya da Afan shiyasa na yarda yar NUR ne kuma ina kyautata zaton bata hanyar aure aka same ta ba jinin ne kawai yasa yar tayi kama da Afan
Dana tambaye su mahaifinta sai suka fara kame-kame a lokacin bana son in matsa musu saboda ina tsoron kar su gudu

amma tabbas zakiya yar hauwa ce sai dai wani ikon Allah jira nike abubukar ya dawo in tambaye shi ko yan biyu ne domin shi kadai ke da hanyar ansa wanan tambaya

alhaji tsoho yace"yanzu da gaske hauwa ta rasu kenan?"yana magana ne yana hawaye

ummi tace"Abba ya kamata a bar kukan nan haka addu'a take bukata tun ina Nigeria ake kukan nan babu ma kamar sameer domin shi kadai yayi mata farin sani da yake yana da shekara sha biyar tayi aure"ta karashe maganar cikin kuka

alhaji tsoho yace"Allah jikan ki hauwa yasa kin huta kuma aljana shine makoman ki na yafe miki duniya da lahira nima na gane kuskurena,na rashin yi miki gata a baya Allah yasa kin hadu da mahaifiyar ki"

ummi tace"amin abba sai dai har yanzu ban sanar dasu afan ba ina jira a tabbatar tukuna"

alhaji yace"hakan yayi domin na San ba hankali ne dasu ba"

ummi tace "ai na gargade su kan na taho kar su sake su wulakanta su"

bayan wata d'aya sameer ne zaune yana tunanin haryar da zai bi dan goge video wayar zakiya domin ta fara kaishi bango

yace"amma ai tace akwai a wayar wasu,dole ne ma in goge shi ko ta halin kaka"

ai be gama tunani ba ta shigo tsalle tayi ta haye tebur tana fuskantar shi tace"ya dai"hade da d'aga me gira

yace"ke miye haka wanan wani irin iskanci ne da rainin wayau eh zaki wani haye min tebur"

tace"ni ba surutu ya kawo ni ba zuwa nayi in fad'a ma duk randa sir Afan ya kara hantarar my NUR wallahi zan saki video nan"

a ranshi yace"dole in yi wani abu ayau domin yariyar nan ta gama raina ni"a fili kuma yace"me yayi kuma?"

tace"jiya zuba mata drinks a jiki yayi a public harda wani kiranta yar iska"

sameer yace"toh kije zan yi wani Abu akai"

tace"da yafi maka"

tana fita ta kira messager tace"ya je restaurant ya siyo mata abinci da cock me sanyi"

yace"toh"har zai tafi sameer ya kira shi yace"ya shigo"

yana shiga ciki sameer ya kulle kofa ya ciro wani magani a drawer yace"in ka siyi cock ka bude ka saka mata guda ukun nan"

messenger yace"an gama oga"kudi ya Ciro mai yawa ya bashi

sanan yace".......


are you ready guys?let have fun

maman
noorul
hudah
luv u my fans
pls share
[10/06, 13:40] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Ddecated to mom noorul hudah fans group

πŸ…Ώ4⃣1⃣&4⃣2⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Sanan yace"ina fatan cock din gora ta aike ka?"

Yace"eh shine"

Yace"good da dabara zaka bude inda baza ta gane an bude ba"

Yace"inshaallahu sir zanyi shi cikin natsuwa"

NUR ko tana cikin aiki wayarta tayi kara tana d'agawa

Tace"hello anty"

Anty su TASLEEM ne tace"ki yi sauri ki zo ki d'auki hauwa ta samu attack amma da sauki mun bata inhailer sai dai mun tashi domin 3:39 ne yanzu kuma mun ji shiru Baki zo ba"

Jiki na rawa NUR tace"gani nan zuwa yanzu nan"

Ko kallon Afan bata yi ba ta d'auki jaka ta tafiyar ta tafiya take tana hada wa da gudu a hanyarta na barin department dinsu har zata shiga elevator tayi karo da wata mata kyakyawa da gani zata ja shekaru har wayarta ya fadi,daukowa NUR tayi ta mika mata

Tace "dan Allah ki yi hakuri baiwar Allah wallahi ban kula bane"

Matan tace"babu komai"cikin fara'a tayi magana suna had'a ido NUR ta ji wani mumunan fad'iwar gaba

Matar ko kwarjini NUR ta mata

NUR bata yi magana ba ta shige elevator tana tunanin kamar ta taba jin muryar matan a wani wuri

Matar na shiga ta tsaya a receptionist tace"tana nima C E O na company "

Receptionist tace"ba ya nan ya je meeting "

Matar tace"OK in ya dawo ki ce mai FATIMA cousin din shi ta zo daga kano"

Tace"OK ma"bayan Fatima ta tafi

Manager yace"meyasa kika ce mata baya nan bayan yana ciki"

Tace"shi yace duk Wanda ya zo in ce ya fita yana son ya huta"

Yace"alright "

Zakiya ko messenger ya kawo mata abinci amma bata ci ba domin wani aiki aka kawo mata daga admin tayi treating

Ga aikin na da yawa har 4:30 yayi bata wuce ba kowa ya tafi ita kadai ta rage da sameer

Tsaki tayi tace"tun d'azun ina nan bana komai ba bani aiki ba sai yanzu a ce gobe da safe ake so"

Sai misallin 5:39 ta gama wani yunwa ne ya kamata,abincin ta bude ta ji shi da sanyi ai sai ta bude cock ta kurbe duka ko digo bata rage

Tace"bari in d'an huta kafin in tafi gida

Bayan Minti biyar sai kanta ya fara juyawa

Can anjima ta mike ta fara rawa dai-dai nan sai ga sameer ya fito ganinta a wanan halin ya sashi yin murmushi yace"yau za a yi ta ta kare karasawa yayi ya jata zuwa office din shi ya kunna waka a waya tana rawa

Can anjima ta kwanta a kasa ta fashe da kuka cikin maye tace"ni bani da kowa a duniya sai my NUR sun toni akayi ban San iyaye na ba,tashi tayi ta kama me riga tace"kasan Inda mu ke ji ni da my NUR na rashin yan'uwa?"

jin surutan da take yi yasa ya ajiye karamin cameran dake hanunshi a table yace"ai in mutum baya hayyacin shi yafi fadin gaskiya bari in ji maza nawa ta bi ko wanan ma ya isheni

ta kara cewa my NUR na da uba amma bata dace da uba na gari ba shiyasa

kecewa tayi da dariya tace"kasan waye abbana?alhaji idris mai gwal shine abbana mai kudi ne in fada ma a lokacin da nike tare dasu rayuwar sarauta nike yi,domin abinda nike so shi ake yi kawai rana d'aya ummina tace"ni ba yar'ta bane,shafa kumatun shi tayi tace sai ta Kore ni wai itama ta samu nata cikin
hakan yasa muke rayuwa nida my NUR amma sai mutane suke mana kallon karuwai"

kuka mai hade da dariya tayi sanan tace"ni narasa ta inda zan fara niman iyaye na ina son in ji dalilin su na yardani da suka yi a bola tun ina jinjira"

jikin sameer ne yayi sanyi yace"toh ai ke da NUR yan biyu ne"

dariya tayi har da rike ciki tace"ina ganin ka mai hankali Ashe kai sha-shasha ne ni da NUR ba yan biyu bane kama mu kayi ita tasan asalinta"

yace"how comes?wanan ba gaskiya bane akwai magana a kasa"

zakiya tace"ko blackmailing dinka da nike yi ina yi ne dan farin cikin NUR ban San meyasa ba in na ganta cikin b'aci rai nike jin zafi ba shiyasa nike boye damuwata dan kar in ta mata da hankali ina matukar kaunar NUR,dana tambayi abbana ta wani hanya zan nimi iyaye na sai yace"da abin wuyar nan zan nimi su domin dashi suka since ni"zaro abin wuyar tayi ta nuna me

ganin abin wuyar yasa shi mikewa tsaye a yace"........"

toh fans ga Fatima ta zo minna ko mai zai faru? nima ban sani ba




maman
noorul
hudah
luv u my fans
pls share

[10/06, 16:00] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

Home of gorgeous,interllingent and exper writer we are the best among the rest.

Dedicated to imranfad fans group

πŸ…Ώ4⃣3⃣&4⃣4⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

mikewa yayi yace"a ina kika sami wanan abin wuyar?"

Cikin maye tace"kai baka da hankali ne baka ji nace ma dashi aka since ni ba?"

Yace"no wonder kike min kama da yan gidan mu ashe ke yar anty hauwa ce,amma ya za ayi a ce baki da alaka da NUR kai ban yarda ba,ba a irin wanan kamar a banza,sai na binciko gaskiya"

Tace"kawo kunni ka in fad'a ma wani sirri"dariya ta kece dashi kafin tace"ai TASLEEM ba yar!yar!yar!"bata karasa ba wani barci ya sace ta"

Waya ya Ciro yana son ya kira ummi ko tunanin me yayi sai kuma ya maida wayar

Yace"bari in bari tukunna sai na binciko tsakanin su da NUR,toh amma tayaya?"

Tunani yake can kuma kamar Wanda ya tono wani abu yace"yes D N A"

Waya ya Ciro a aljihun shi ya kira wani abokin shi Dr SUDEX (domin jin labarin wanan Dr Ku biyoni a littafi na mai fitowa mai suna NI DA YAYA SUDES) yace"Dr SUDES pls me ake bukata in za a yi D N A"

Dr SUDES yace"lafiya ko dai wata ta laka maka ne tunda kaki aure ?"

Dariya sameer yayi yace"kaifa d'an iska ne in Allah ya yarda bazan gani ba,please be serious "

Dr SUDES Yace"ta jini ne sai kuma gashin kai amma bazan boye maka ba babu equipment nayi na gashi a nan sai kasa shen waje kuma shi yafi nuna komai"

Sameer yace"nagode"

Yana yankewa ya kira abokinshi Dr dake aiki a us bayani yayi me

Dr Philip yace"ya zo da sumar su"godiya yayi me sanan ya yanke wayar

Cire hulan kan zakiya yayi domin zakiya bata sa hijab ko atampa ma bata sawa kullum cikin wando take sanan ya sinke dogon gashin ya samu leda ya saka

Yace"sauran NUR amma tayaya zan samu sumar ta ita da kullum take cikin hijabi?dole in nimi hanya"

Zama yayi kusa da zakiya yana kallon fuskanta,tsaki yayi yace"women are all the same"

Takawa yayi zuwa wajen fridge budewa yayi ya ciro giya ya bude kwalban ya fara sha domin ya tuna abinda safeena tayi me

Iska ne a ka fara yi ga gari yayi duhu yayi baki alamun hadari

Zakiya bata farka ba sai 7:30 na yamma tuni an fara ruwa irin me hade da iska nan

NUR ko jin zakiya shiru-shiru yasa hankalinta mugun tashi gashi nobanta bai Shiga

Rungume TASLEEM tayi wanda tuni barci wahala ya dauketa

Ita ko NUR bata yi barci ba sai addu'a take Allah yasa zakiya lafiya

Zakiya na farkawa ta fara kallon wuri ganinta a office din salim yasa ta firgita

Hango shi tayi kwace a kushin din office din jikinta ne ya fara rawa dan ta dau yayi mata wani abu ne kokari take ta tuna abinda ya faru amma ta kasa sai ma wani mugun ciwon kai da take ji

Tace"shikenan ya cuce ni,ya raba ni da martaba na,ashe gaskiyar NUR ne da ta gargade ni akan na fita harkan su basu da imani amma naki,ya zan fuskanci NUR da wanan mumunan labari"

Ihu ta kurma a firgice sameer ya tashi yace"ke lafiya?"

Tace"Allah ya isa sakani na da kai,ashe dama kai macuci ne ban sani ba,me nayi maka ka b'ata min rayuwa?"

Sai a sanan ya gane me take nufi tashi yayi ya fara takawa zuwa gunta tana masawa baya har ta kai karshen bango,matseta yayi a bango

itako ta runtse ido yayi da bugun zuciyar ta ya karo

kallonta ya tsaya yi sun fi mimti biyu a haka kafin yace"me kika d'auke ni?mazinaci toh a sarin rayuwata babu zina

bude ido tayi suka hada idanu kallon juna suka tsaya kafin sameer ya d'auke nashi

a ranshi yace"babu komai a idanun mace sai yaudara na tsani mace"amma a fili yace"ki je cikin toilet ki duba jikin ki in baki yarda da ni ba,in akwai abin da nayi miki zaki gane sai dai in kin saba bin maza ne baza ki gane ba"

hararar shi tayi ta murguda me baki tace"eh din ka manta ni karuwa ce?"

yace"yariyar nan ni kika yi ma kallon banza da murguda baki?"

tace"eh anyi mutan da"

binta yayi ai da gudu ta shige toilet din office din shi ta rufe

murmushi yayi yace"zan kama ki ne yariya"

lekowa ta kuma yi tace"kalli"kallonta yayi sai ta me gwalo ta koma ciki

shi ko yace"yariyar akwai raini wai ni take kira mutan da"

zakiya ko sanda ta tube kayar jikinta duka ta fara kallon jikin ta tace"ta ya zan gane?"matsa nono ta tayi ta ji ba zafi

kasanta ta duba ta gan babu alaman wani Abu kawai sai ta mayar da kayan ta fito

yace"ya dai? "

tace"kamar ya"

agogo ta duba ta gan 8:pm tace"oh my god zan tafi gida dare yayi"

yace"ke kina hauka ne baki gan ana ruwa ba?"

tace"wallahi tafiya ta zanyi my NUR na nan hankalin ta a tashe kuma nasan yanzu tayi fushi ni bana son fushin ta nasan yanzu tayi kuka sosai"

yace"toh wa zai kaiki gida?"

tace"motan ka zan d'auka"

yace"nifa da wanne zani gida?

tace"kai ka sani mai yasa da nike barci baka tasheni ba?"

yace"muje in kaiki"

tace"toh"

misallin karfe 8:37 ya kaita gida har zata fita yace"


maman
noorul
hudah
luv u my fans
pls share
[10/06, 16:00] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to MAMAN IHSAN GORGEOUS WRITERS FORUM

πŸ…Ώ4⃣5⃣&4⃣6⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Har zata fita a motar yace"ke ji mana"

Dawowa tayi tace"kai ina ji"

Yace"wata magana nike so muyi please ki ajiye duk wani wasa a gefe tambayar ki zanyi kuma ina son ki fad'a min gaskiya"

Tace"toh"

Yace"abun wuyar dake wuyar ki a ina kika samu?"

Hawaye ta fara yi tace"nima ban sani ba"

Yace "d'azun cikin maye kin fad'a min wata magana shiyasa nike son Karin bayani,kin ce baki San iyayen ki ba kuma sintar ki akayi"

Zaro ido tayi tace"ni din ni ban fad'a maka haka ba"

Jawota yayi ta fad'a kirjin shi sanda suka ji wani yanayi yace"kalli idona zakiya"babu musu ta kalleshi yace"you can trust me I want to help you"

Haka kawai taji zata iya yarda dashi,nan ta kwashe komai ta fad'a me

Yace"miye sunan mahaifiyar NUR?"

Tace"hauwa da abubakar musa"

A ranshi yace"kenan NUR ce yar anty hauwa amma ita zakiya fa?domin babu shakka wanan abin wuya gidan mu ce,ummi na dashi,zainab da ihsan (kanne Afan)na dashi kuma akwai a wuyar Amina kanwata Wanda duk alhaji tsoho ke bawa yara mata,toh in zakiya ba yar anty hauwa ba ina ta samu?
a fili kuma
Yace"ko zaki iya fad'a min dalilin da yasa NUR barin gida?"

Tace"gaskiya bazan iya ba"

Yace"babu matsala amma baki tunanin ke da ita yan biyu ne?"

tace"ban sani ba gaskiya amma NUR ta tabbatar min ita kadai iyayen ta suka haifa kuma a wajen haihuwarta ne ummita ta rasu sai dai akwai ranan da NUR ta fad'a min abin wuyata na mata kamar ta taba ganin shi a wani wuri

toh sai shekarar jiya da wasa nace mata kodai a wuyar mahaifiyarki ce? "

sai tace"eh na tuna a wani hoton ummina na taba gani,toh a lokacin sai nayi zargin duk inda akayi ina da alaka da NUR domin muna mugun kama da juna,amma matsala d'aya ce NUR bata San dangin mahaifiyarta ba,a ranan nasu yi mata tambayoyi sai na lura tana cikin damuwa"

sameer yace"nima ina zargin Ku yan biyu ne,kuma nasan dangin ki amma bazan gaya miki ba sai na tabbatar yanzu abinda zamu fara yi shine asan alakar ki da NUR daga nan sai mu nimi dangin mahaifiyar NUR Wanda na tabbatar suma suna niman ku kuma suna kusa da Ku"

tace"nagode sir sameer Allah ya saka da alkhari"

murmushi yayi yace"sir sameer?yau ba mutan da kenan?yanzu ya zamu samu sumar kan NUR ?"

tace"jira ni yanzu kuwa"

yace "please karki sanar da ita komai sai an tabbatar"

tace"na gane"

takawa tayi har ta isa gida tura kofa tayi tarar da NUR zaune a sakiyar d'aki ta hade kai da guiwa tana kuka
da sallama ta shiga dakin

NUR najin muryar ta d'ago ta kalleta tace"zakiya meyasa kika dade ne?kin San irin damuwar dana shiga da baki dawo ba?"

zakiya ta karasa tace "ki yi hakuri my NUR wallahi aiki ne ya rike ni dana gama barci ya dauke ni"

zuwa zakiya tayi zata rungumeta sai NUR ta tureta,zakiya tace"NUR ki yi hakuri nace please kin ji"still NUR bata yi magana ba ai sai zakiya ta saki kuka

NUR na jin kukanta ta taso ta rungumeta tace"yi shiru na daina fushin"

zakiya na ganin NUR ta rungumeta dama babu hula kanta sai kawai ta fara shafa kanta tana kokarin sinke sumar

tana sinkawa tace "my NUR ina zuwa ban biya mai keke ba"

NUR tace"Allah yasa ba club zaki ba"

tace "ai na daina"

da sauri ta fita ta je ta shige motar sameer yace"kin samu?"

tace"eh gashi nan"

yace"a you show nata ne?"

tace"eh yanzu ma na sinko shi shiyasa ma ban Ciro na cumb ba Dan za a iya samun matsala domin duk cumb d'aya muke amfani dashi"

yace "good gobe zan tafi UK by 10am kwana uku zanyi please kula da kanku kanne na"

zakiya tace"kanen ka?taya muka zama kannen ka?kodai dan ka gan muyi kama da larabawa kake kalen dangi?"ta karashe maganar da d'aga me gira"

hanun yasa a goshi yace"oh god me hali baya dainawa amma ai nima ba baya bane a kyau"

hanci ta d'aga me,tace"nifa baza a d'auki nawa sumar ba?Allah dai yasa ba safi za a dashi ba "

yace"me kika ce?"

tace"cewa nayi nagode da taimakon ka"girgiza kai yayi yace"ai na d'au naki dazun lokacin da kika bugu,kiyi hakuri nasa miki Abu a drinks "

tace"ba komai nima ai na maka laifi,bari in tafi kar ma NUR ta tada drama yanzu ma sanda nayi kukan karya ta hakura"

yace"OK gobe zan tafi ki kula da my NUR da TASLEEM in na dawo ina son ki sanar dani komai akan TASLEEM da NUR"

tace"inshaallah" har zata fita a motan yace"ji mana"juyowa tayi ta kalleshi ai sai ya mata kiss a goshi yace"zakiya stay away from trouble"

murgud'a mashi baki tayi ta fita tana shan kwanan gidan ta taba dai-dai inda yayi kissing dinta tayi murmushi tace"safe journey sir meer"

washe gari
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to MAMAN NOORUL HUDAH FANS CHAMBER

πŸ…Ώ4⃣7⃣&4⃣8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Washe gari NUR ta tashi ne da zazzabi

Zakiya tace"hanya kuwa zaki iya zuwa aiki my NUR? "

NUR tace"wallahi bana jin dadin jikina amma zan kokarta domin bana son abinda zai had'a ni da sir Afan kin San niman dalili yake"

Zakiya tayi murmushi tace"karki damu na samo mana mafita ki yi barcin ki kawai"

NUR tace"ina jin mafita"

Zakiya tace"OK bari ki gani"

Akwati ta bude ta ciro atampa da hijabi tasa

Sanan tasa hijabi tace"ya kika gani ne"

NUR tayi murmushi tace"kamar ni kin gan inda kika yi kyau kuwa toh meyasa baki sa atampa ne sai ki ta shiri kamar wata ngozi ko Galle babu,yanzu ko ba me gane mu"

TASLEEM ne ta shigo d'ankin taje gaban zakiya tace"mummy

Please Login or Register in order to submit comment