Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

garin yayi me

sai dai fa gayun nan biyu sun hadu kuma farare ne Sol


wanan kenan

cigaban labari

maman
noorul
Hudah
luv u my fans
pls share
[08/06, 13:49] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GOUGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.
nagode fans Wanda suka bani kati jiya Allah ya kara budi ina son masoyana Allah ya bar mu tare

πŸ…Ώ2⃣7⃣&2⃣8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Sai missalin karfe 4:pm zakiya ta bar office bata damu ba da bata gan NUR ba domin tasan zata dauko TASLEEM a makaranta tana kai gida ta tarar da NUR kwance har TASLEEM ta tafi islamiyya

Tace"my NUR ya dai kamar kin yi kuka?"

NUR tace"wallahi bazan koma company nan ba"

Zaro ido zakiya tayi tace"meyasa zaki bar aikin?"

NUR tace"saboda sir Afan ya kira TASLEEM da shegiya"

zakiya tace"lallai ya taro match shi baisan baki da hakuri akan TASLEEM ba"

NUR tace"harda cewa kar na kara zuwa company shi"

zakiya tace"wanan ne kuma bai isa ba domin bashi ya dauke ki a aiki ba ummi ne kuma ai kina aiki a company nan tun kan su siya sai yanzu za a wani ce ki bar aiki"

NUR tace"ai dan ya gan ummi bata nan ne"

zakiya tace"ina taje ne ai jiya tana nan"

NUR tace"eh da yamma ta tafi Cameroon"

zakiya tace"gobe ki shirya tare zamu aiki"

NUR tace"ni dai bazan je a wulakanta ni da ya'ta ba"

bude waya zakiya tayi ta shiga video tana dariyar mugunta ita dai NUR kallonta take

washe gari da kyar zakiya tayi da NUR sanan ta yarda zata aiki

kamar inda suka saba ajiye TASLEEM suka yi a makaranta sanan suka tafi office

zakiya tace"jeki office dinki kiyi kamar babu abinda ya faru

NUR tace"toh"ta kama hanyar department dinsu itama zakiya ta shige nasu

NUR na shiga office dinsu ta tarar da Afan zaune a kujera zaune da sameer suna hira

karasawa tayi tace"good morning sir"

sameer ko kuri yayi mata da ido yana kallon sai kuma ya gan yau ta kara haske da rama

Afan ne yace"me ya dawo dake? bana ce karki kara dawowa company nan ba tunda bana ubanki bane"

dadi sameer ya ji a ranshi yace"ya samu mai yin maganin zakiya"

a fili kuma yace"ai korar ta zaka yi yariya sai shegen nacin siya"

Afan yace"get out"

kafin NUR ta yi magana Afan ya mike ya kama hanunta yana janta waje domin burin shi ya wulakanta ta

sai kokarin kwace kanta take yana fita daga office dinshi yayi wurgi da ita ta fadi kanta ya bugi desk ai sai ta saki kuka saboda irin zafin da taji ga jini na zuba

nuna ta yayi da yatsa yace"ke har kin isa na baki umurni ki ketare"

hayaniyar da zakiya ta ji ne yasa ta fitowa waje tana fita ta gan NUR kwance a kasa nan da nan idon zakiya ya canja

cikin b'acin rai zakiya ta karasa inda NUR Ke kwance ta taimaka mata ta tashi

boyewa NUR tayi bayan zakiya hakan da tayi ba karamin b'atawa zakiya rai yayi ba domin hakan na nuna tsoron Afan take kenan

Afan ne yace"ba mu San mazinaciya a company nan daga yau karki kara zuwa nan kazamiya kawai mazinaciya"

tuni idon zakiya ya fara canja kala sabar b'acin rai,kallon ko ina tayi ta gan duk jama'an office din sun taro suna kallon NUR dake bayan zakiya tana kuka

shiko sameer tsaye yayi yana kallon zakiya da NUR

wani tunani ya fadowa zakiya a ranta tace"bari in kara petrol a wutan nan"

a fili tace"da kake kiranta mazinaciya mai kake nufi?kana nufin TASLEEM shegiya ce!?"

Afan yace"in ba shegiya bace ita me za a kira ta?ai shegiya ce"

juyawa zakiya tayi ta kalli NUR ta gan idonta yayi ja alamun ranta ya b'aci"
a ranta tace"haka nike so"a fili ko
zakiya tace"yanzu kana nufin TASLEEM shegiya ce?"

yace"eh shegiya c....."

maganar makalewa yayi sakamako



maman
noorul
hudah
luv u my fans
pls share

[08/06, 18:18] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to Anty DALA


πŸ…Ώ2⃣9⃣&3⃣0⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Makalewa yayi sakamakon wanka me mari da NUR tayi

Mari da yayi sanadiyar firgitar da Afan da ma'aikatan dake tsaye a wajen

Shiko sameer rike kumatu yayi kamar shi aka Mara

Zakiya ko dariya ta kece dashi har da rike ciki da ma burinta NUR ta marda martani

Nuna Afan NUR tayi da yatsa tace"karka kara kiran ya'ta da shegiya,wallahi zan iya d'aukan komai amma banda cin mutunci ya'ta ta hanyar kiranta shegiya"

Afan ne ya d'ago ya kalleta da jajayen idonshi yace "ni kika Mara?"

Tace"eh an mare ka din wallahi zan iya yin fiye da haka in ka kara kiran ya'ta da shegiya domin ya'ta ba shegiya bane sai dai Kaine shege"

Sameer ne yace"manager kira security a fitar da ita an koreta a aiki"

NUR tace"ai ba sai an kira security ba zan fita da kaina domin bana bukatar aikin Ku"

Tana kaiwa nan ta bar building din ko ta kan zakiya bata bi ba ta wuce

Sameer ya kalle zakiya yace"ke kuma me kike jira?"

Tace"kai nike jira"

Kallo d'aya Afan yayi wa staff dinshi kowa ya bar wurin shikuma ya koma office cike da b'acin rai da tunanin hanyar d'aukan fansa

Sameer yace"ke ma an Kore ki"

Zakiya tace"toh"

Office ya wuce zakiya na binshi a baya yana shiga da minti biyu sai ga zakiya tana zuwa ta haye saman tebur din gaban shi

Sameer yace"miye haka"

Tace"wani abu zan nuna ma kafin in tafi"

yace"toh dan iskanci sai kin hau samar tebur"

tace"eh saboda mu fahimci juna In gan kwayar idon ka ka gan tawa"

rasa me zaice yayi yace"inaji"

wayarta ta Ciro a aljihun wandonta ta shiga vidio ta fara nuna me

zaro idon yayi ganin shi a video yana rawa cikin maye,kallonta yayi cikin ido ai sai ta tunsure da dariya tace"ina fatan ka gane wanda ke rawa a wanan video "

cikin in-ina yace"ina kika samu wanan video?"

tace"a inda kayi rawa harda amai"zufa ne ya fara zubo me ta ko ina"

tace"yanzu deal nake so muyi"

yace"na me?"

tace"so nike kasa sir Afan ya roki my NUR kuma a dawo mata da aikin ta gobe nan"

yace"za a dawo da ita amma wallahi Afan ba zai roke ta ba nasan halinshi ki yi hakuri"

zakiya tace"ashe so kake in turawa ummi video nan kuma zanyi playing a building kowa ya gani"

yace"yi hakuri wallahi a gida basan ina sha ba ki min rai kar abbana ya tsine min"

tace"komai na hanun ka kuma wallahi karka yi tunanin kwace wayan na da niyar deleting ko kuma yi min illa domin na Riga da na turawa mutane uku wanda in basu ganni ba zasu sake shi har internet dan na lura tun d'azun kake kallon hanun na nasan tunani kake ka kwace toh karka yi wanan kuskuren"

ai cikin tashin hankali yace"anty zakiya nifa kani ne a gun ki kike tunanin tozartawa"

zaro ido tayi kani kuma shekarar ka nawa?"

yace"talatin da takwas"

ihu tayi da cewa"eh shine zaka ce kai kanina ne?nifa shekara ashirin da biyar"

yace"ai Allah ne ya baki girman"

tace"hmmmm ashe kai tsoho ne toh shekara sir Afan nawa?"

yace"talatin da biyar"

tace"yayi mutan da,ni na tafi yau zan jira ka da yamma ka kawo wanan d'an iskan da yasa my NUR kuka ya bata hakuri"

yace"ai ban San gidan Ku ba"

tace"barkin sale muke wajen alakura primary school ka tambayi yaro ko babba gidan su zakiya duk sun sanni"

yace"toh anty"

tsalle tayi ta duro a tabur ta shafa kumatun shi tace"always be a good boy"

tana fita ta dauki jakanta ta yi tafiyarta gida cike da nishadi

yana ganin fitar ta yace......



maman
noorul
hudah
luv u my fans
pls share
[09/06, 00:25] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to MAMAN NOORUL HUDAH FANS GROUP's

πŸ…Ώ3⃣1⃣&3⃣2⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Sameer na ganin ta fita ya sa hanun a sumar kanshi ya hargisa

Yace"na Shiga uku wanan wani irin masifa ce?nasan wanan abun a maganar kudi zai kare

Tunawa yayi da lokacin da tsohuwar budurwar shi safeena ta hada baki da abokin shi da kidnaper suka amshi me kudi har miliyan biyar

A fili yace"I hate women za su iya komai akan kudi"

Tashi yayi ya tafi department din Afan a tsaye ya ganshi yana ta wurgi da kayan office dinshi

A ranshi yace"ya zanyi ya yarda ya bini gidan su yariyar nan"

Kallon shi yayi da alamu Afan bai Masan ya shigo ba

Sameer yace"bro"a fusace Afan ya juyo yace"wallahi sai na ci mutuncinta sai nayi sanadiyar hallaka rayuwarta"

Sameer yace"ka shirya samu je gidan su ka bata hakuri"

Afan yace"what?"

Sameer yace"yes!kai yaro ne baka da wayau ta yaya zaka rama abinda tayi maka?ai sai ta yarda da kai ba?"

Shiru Afan yayi na wasu sakonin kafin yace"me kake nufi?"

Zama sameer yayi kafin yace"abin da nike nufi shine ka je har gidan ka bata hakuri tare da nuna mata kayi nadama hakan zai sa ta saki jiki da kai ta sake maka daga baya ka rama"

Afan yace"wow bro ka kawo shawara amma a ina zan samu gidan su"

Sameer ko wani dadi yaji a ranshi yace"hmmm ni ina ruwana burina ka bata hakuri kafin mayya yariyar ta saki video na,sauran ka karata"

Ganin bai amsa me tambaya ba yasa Afan cewa"broh da kai nikeyi fa"

Sameer yace"Bari manager zai kai mu"

Afan yace"toh muje yanzu"

sameer yace"toh"

suna Shiga barkin sale suka fara karo da bola ga anguwan dirty kasancewar getto area ne

kallon juna suka yi Afan yace"manager wanan wani irin anguwa ne?"

manager yace ai barkin sale kenan nan gidan su yake a filin makaranta suka paka da kafa suka karasa gidan duk hacin su rufe da hanky

NUR dake zaune a sakar gida tare da TASLEEM tana koya mata karatu al-qurani mai girma

zakiya kuma na ciki tana sa kaya domin fitowarta kenan daga wanka

jin muryar manager yasa NUR d'agowa ta amsa jira yayi ta kai aya kafin yace"NUR tare fa nike da sir Afan da sameer

kafin tayi magana zakiya ta fito da gudu sanye da 3/qutr da armless kanta ko d'an kwali babu

tace"ce musu su shigo"

manager yace"cewa fa suka yi baza su iya shiga irin wanan gidan ba

zakiya tace"kai dai ka cewa sir sameer ya shigo"

yace"toh watoh yau na zama massenger kenan ko?"

ita dai NUR ido tasa musu tana kallo manager na fita

NUR ta kalli zakiya tace"Allah yasa ba wani fad'a kika tono ba,meya had'a ki dasu?"

kafin zakiya ta bata amsa su sameer sun shigo dan haka tayi shiru

TASLEEM na ganin su ta ruga a guje tana dariya daddy oyoyo dan a ganin ta babanta ne ya dawo daga umura

da sauri NUR ta mike amma kafin ta rike ta har ta rungume Afan

shiko shiru yayi ya tsaya kamar soja can anjima shima ya rungumeta wanda bai San sanda yayi hakan ba"

NUR na ganin haka ta karasa a fusace ta janye TASLEEM cikin matuka b'aci rai tace"ubanwa yace miki daddy kin ne eh?ashe ba na hana ki zancen wani daddy ba?wallahi in kika kara gani wani kika je wurin shi a matsayin dadin ki wallahi sai na zane ki kuma in kulle ki a daki"

maza je ciki ki zauna kuma ban yarda ki fito ba sai na baki izini ko fisari zaki yi ki yi shi a ciki

fashewa da kuka TASLEEM tayi ta ruga a guje

shiko Afan haka kawai bai ji dadin inda NUR tayi da TASLEEM ba domin ya ji son yariya har zuciya shi

sameer ko kallon su yake in ya kalli zakiya ya kalli NUR a ranshi yace"kenan wanan ne na fara gani a office din Afan ashe yan biyu ne shiyasa na ta rudewa"

zakiya ko kallon Afan take daga sama har kasa wani mugun kama yayi mata da TASLEEM

wani tunani ne ya fado mata ai da sauri ta dafe kirji

sameer ne ya katse su da cewa"mun zo ganin ki ne NUR"

d'agowa ta yi da jajjayen idonta ta harari Afan sanan tace"meya faru?"

yace"mun zo ne aka....."

zakiya ta katse shi da cewa"bari in kawo mu ku wajen zama da ruwan sha"

jin ruwan sha yasa suka ce"what a nan gidan zamu sha ruwa? ki barshi kawai"kallon sameer ta yi tace"za Ku sha ne ai"tuni ya gane mai take nufi yace"toh je ki kawo dama kishin ruwa Nike ji"

murmushin mugunta ta yi tace"good"

ruwa ta kawo musu a kofi sameer ya fara sha ya bawa Afan

Afan yace"ni banzan iya shan ruwa nan ba"

kallon zakiya yayi tayi me alama da ido ai sai ya je dai-dai kunni Afan yace "ta ya zata yarda da kai in kana nuna kema a gidan su"

ruwan ya amsa ya sha kad'an duk abinda ke faruwa NUR na lura dasu

a ranta tace"kome zakiya ke kullawa oho Allah dai yasa kar ta jefa mu halaka

sameer ne yayi gyran murya kafin yace"NUR mu zo ganin ki ne akan abinda ya faru d'azun wallahi d'an uwa na yayi nadama sosai"

zakiya tace"ai sai ka bari yayi magana da kanshi tun da yana da baki ba kurma bane"

taba Afan yayi,Afan yace"NUR dan allah kiyi hakuri nayi nadama ki dawo aikin ki"

NUR zata yi magana zakiya ta amshe da cewa"babu damuwa gobe zata dawo amma sai ka mata alkawarin hakan ba zata kara faruwa ba"

ba tare da wani tunani ba yace".....


maman
noorul
hudah
luv u my fans
pls share
[09/06, 12:47] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers we are the best among the rest

Dedicated to Anty shamsiya maman fati)

πŸ…Ώ3⃣3⃣&3⃣4⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Ba tare da tunani komai ba Afan yace"nayi alkawari"

NUR tace"zan dawo akan sharadin baza ka kara magana ya'ta ba"

(wai meyasa NUR take nisanta TASLEEM da Afan ne?hmmm)

Yace"OK babu komai"

Amma ki fito da ita mu gaisa tunda an zama d'aya

Tace"yanzu ka yi alkawarin babu abinda zai shiga tsakanin ka da ita"

Zakiya zata yi magana NUR ta katseta da cewa"zakiya please"

Shiru tayi,sameer yace"ina su mama mu gaisa"

Kallon juna suka yi da NUR kafin zakiya ta harare shi tace"mu kadai ne a nan gidan"

A ranshi yace "ashe karuwai ne zaman Kansu suke yi"

Afan yace"toh mu zamu wuce mun gode"

Zakiya tace"toh a gaida gida"

Suna shiga mota suka sauke ajiyar zuciya

Afan yace"wanan wani irin gida ne?"

Sameer yace"kai dai bari yanzu ma ji nike kamar in yi amai amma ba laifi sun share ai"

Afan yace"hmmm gaskiya bazan iya rayuwa a gidan ba"

Sameer yace"kai dai bari "

Bangaren NUR ko suna fita ta kalli zakiya tace"me kike had'awa ne?"

Zakiya tace"me nayi kuma?"

NUR tace"zakiya nasan ki ciki da waje nasan akwai wanda kike blackmailing cikin su biyu"

Zakiya tace"my NUR ki yarda dani ba abinda nayi"

NUR tace"nasan baza ki fad'a min ba yanzu amma intayi wari zan ji amma ki yi a hankali kar ki jefa mu a halin da ya fi wanda mu ke ciki yanzu"

Kallon kofa NUR tayi ta hango TASLEEM na leke

Tace ba na ce kar ki fito ba sai na baki izini ba?toh me kike a kofa"

Cikin kuka TASLEEM tace"mummy ki yi hakuri please"

Da k'yar NUR ta yarda TASLEEM ta fito sanda zakiya tasa baki

Sanan ta yafewa TASLEEM tare da gargadi

Zakiya tunani take akan fushin da NUR tayi domin bata taba yin fushi da TASLEEM irin na yau ba tambayar kanta take toh meyasa?kuma ta lura tun shigowan Afan fuskarta ya canja

Ga kamar da Afan keyi da TASLEEM kai akwai wata a kasa,kuma sai ta binciko koma menene"

Maganar NUR ne ya dawo da ita daga duniyar tunani

NUR tace"zani pharmacy na karbowa TASLEEM magani daga nan zan siyo kubewa muyi tuwo"

Zakiya tace"toh sai kin dawo"

Daki NUR ta shiga sai ga ta ta fito sanye da hijabi

Tace"toh na tafi ki kula da TASLEEM dun Allah Zakiya karki yi wanan barci taki"

Tace"toh umma"

Wucewa tayi zakiya ta bita da kallo

Sai gata ta dawo tace"TASLEEM saka hijabi muje"

Zakiya dai shiru tayi har TASLEEM ta saka hijab ta fito suka tafi

Ajiyar zuciya zakiya ta sauke da gudu ta shige d'aki

Wani katon akwati ta d'auko ta bude karamin zip hoton wata kyakyawar mata ta gani d'aukawa tayi ta ijiye gefe

Cigaba tayi da dubawa sai ga hoton Afan ya bayyana a bayan shi an rubuta the love of my life and the father to my unborn dauther hauwa'u

Rufe baki tayi tace"kar dai shine mahaifin TASLEEM "

Cigaba tayi da dubawa har ta gan wani diary

Budewa tayi a farko page an rubuta summaiya nasir and uthman Suleiman Adam

Karantawa ta fara yi har ta kai karshe inda ya tsaya ne a ranan da summaya zata baro Cameroon

A lokacin da Afan kecewa summaiya please ki kula min da ya'ta hauwa'u uthman Adams

Rike baki zakiya tayi tace"babu shakka shine mahaifinta kuma da dukan alamu NUR ta sani"

Wani handbag ta bude sai ta gan


Maman
Noorul✍✍
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[09/06, 16:13] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers we are the best among the rest.

dedicated to HUBBEY AND SMASHER GROUPS
πŸ…Ώ3⃣5⃣&3⃣6⃣

Bismillahir Rahmani Rahim

Ta gan wasu hotuna na summaiya da wata mata

Tace"dole yau NUR ta amsa min tambayoyi na"

Bayan wasu lokota sai ga NUR ta shigo da Leda a hanunta ga TASLEEM a gefenta da biscuit

NUR ko sai cewa take zakiya ina kike ne?mun dawo jin shiru yasa ta shiga ciki d'akin tarar da ita tayi zaune ga akwatin summaya gabanta da hotuna a baze

Wani fad'iwan gaba taji karasawa tayi ta fara had'a kayan tace"zakiya menene haka ashe ba munyi dake babu wanda zai bude akwatin nan ba"

Zakiya tace"bana son wani magana bayani nike so akan wanan hotunan"

NUR tace"wani bayani kike so bayan kin San komai"

Zakiya tace"a da na d'auka na sani amma yau na tabbata baki dauke ni a matsayi yar uwa ba tunda har kika iya boye min sirrin ki,a yau na tabbata bani da kowa a duniya NUR ko kin manta alkawarin da mukawa juna akan babu abinda zamu boyewa juna sai ga shi kin boye min.sirrin ki"

Jikin NUR ne tsanyi cikin tsanyi jiki tace"ki yi hakuri zakiya wallahi tsoro ne ya hana ni fad'a miki"

A fusace zakiya tace"kina nufin baki yarda dani ba kenan ko toh nagode yau zan bar gidan nan in shiga duniya atleast nasan banda kowa"

Zubewa NUR tayi ta fashe da kuka tace"yi hakuri wallahi na tuba kuka take kamar an mata mutuwa hakan yasa zakiya tausaya mata

Ta sugunna ta d'aga ta,ta rungume tace"na yafe miki ni basan meyasa nike jin zafi a zuciyata ba in kina kuka ko cikin b'acin rai,babu damuwa in baki son fad'amin"

NUR tace"yanzu zan Sanar dake komai ke ce farin ciki na"

Fitowa tayi ta duba TASLEEM sai ta gan wasanta take a sakar gida bata Masan meke faruwa ba

Ganin haka yasa nur komawa d'akin ta rike hanun zakiya ta zaunar da ita itama zama tayi

Sanan tace"tabbas sir Afan shine mahaifin TASLEEM "

Zakiya tace "amma meyasa baki had'a su ba tunda kin San TASLEEM na bukatar tasan mahaifinta,kuma tana da lalurar dake bukatar kulawa sosai miye amfanin ajiye ta a nan tana wahala kudin makaranta da magani ma da k'yar bayan ga mahaifinta da kudi" dafa hanunta tayi tace"my NUR karki min mumunan fahimta amma ya ka mata TASLEEM ta San waye mahaifinta domin ni kadai zan iya fad'a miki zafin rashin Sanin mahaifa,bana son abinda ya same ni ya same TASLEEM "

Ajiyar zuciya NUR ta sauke sanan tace"zakiya ba wai naki maganar ki bane duk dama bana son rabuwa da TASLEEM amma ina bin maganar mahaifiyarta ne da tace"NUR ki rike hauwa da amana kuma kar ki yi gaggawar niman mahaifinta domin a halin yanzu ban yarda da kowa ba,wanda tasa a sato ni tana kusa da mahaifinta kuma zata iya yiwa ya'ta illa amma kar ki damu in lokaci yayi kaddara zata had'a su domin shi zai zo har Inda take ba sai kin nime shi ba,ki yi hakuri nasan zaki fuskanci kalubale ko a gun iyayen ki ne amma ki jure ki dauka wanan shine kaddararki,ki sakawa ya'ta suna hauwa uthman Adams"fashewa ta yi da kuka tace"zakiya a lokacin da take maganar tana yi ne tana shafa fuskarta har ta koma ga ubangijinta"

Itama zakiya kuka take NUR tace"a ranan da na fara ganin sir Afan kallo d'aya nayi mishi na shaida shi domin da muke makaranta na bude jakar summaiya ranan kin je lecture na gan hoton shi wanda tun ranan ban kara budewa ba hakan ma yasa na hana ki budewa,zakiya ina tsoro kar wani Abu ya sami TASLEEM domin bazan iya rayuwa babu ita ba,kuma ina gudun karya gano yar shi ce zai raba ni da ita"

Shiyasa ma yanzu nike son barin aiki a company amma duk inda naso bari company sai wani abu ya maida ni ga shi yau har gida ya biyo ni"

Zakiya tace"kila lokaci ne yayi,dole ne ma kiyi aiki a wanan company kuma a office din dan gane waye mugu cikin su,wanda ke da hanun akan sace summaiya ni ma ana wa bangaren zan sa miki ido akan sa sameer duk da dai kin ce mace ce amma a halin yanzu kowa suspect ne har da hajiya hafsat mahaifiyar Afan din kar ki damu ina tare dake"

Rungumeta NUR ta yi tace"nagode zakiya"

Bangaren sameer da Afan ko suna kaiwa gida kowa yayi part dinshi kowa da tunanin da yake sameer na tunanin hanyar da zaibi ya goge video shi kuma Afan hanyar da zaibi ya hukunta NUR gefe d'aya kuma ga tunanin TASLEEM a zuciyarshi

Bayan sati daya


Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[10/06, 01:25] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
RAYUWAR NUR
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS, WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to NANA KHADIJA KANO

πŸ…Ώ3⃣7⃣&3⃣8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Bayan sati d'aya zakiya ne zaune a office tana aiki shiko sameer na ciki,shima yana nashi aikin

Bangaren NUR ko tana shirin zuwa meeting da sir Afan a flims investment plan din da tayi ta dauka ta ba messager ya kai mota office din sir Afan ta shiga domin shi baya rufe office dinshi shiyasa yake hango NUR in tana aiki

Karasawa tayi tace"sir na gama zamu iya tafiya

Ba tare da ya kalleta ba yace"OK jira ni a waje "

Tace"toh"sanda ya share fiye da minti talatin sanan ya fito

Zakiya ko gajiya tayi da aiki ta tsaya tana hutawa a haka sameer ya fito ya ganta

Wani haushi ne ya kama shi ganin inda ta aza kafafu a sama tebur kamar wanda ke falon gidan ubanshi ga a/c ta kunna

A ranshi yace"yariyar nan na niman raina ni sai na tashi tsaye
Zamu shirya dole in nuna mata bana tsoronta"

Hade rai yayi yace"ke zo nan"

Tace"ina?"

Yace"biyo ni"

Bin shi tayi a baya suka shiga office,zama yayi

Yace"yariyar nan na fara ganin alaman kin raina ni"

Hayewa tayi saman tebur ta zauna suna fuskartan juna

Tace"sannu mutan da,me nayi kuma ne?"karashe maganar da d'aga me gira"

Yace"sauka kafin raina ya b'aci"

Tace"me ran naka yake jira da har yanzu bai b'aci ba"

yatsa shi ya nuna mata yace"ke"

Lankwasa yasar tayi tace"kai ba a nuna ni da yatsa sauke shi"

Yace"in kina so ki zauna a office din nan ki yi gaggawar goge wanan video ko in...."

Katse shi tayi cewa"me zakayi in naki gogewa?wallahi ka bi a hankali ko in nunawa ummi inta dawo in fact zan tura mata ta watsaap"

Yace"kina turawa ke ma zan tona miki asiri"

Tace"na me?

Yace"nima gayawa ummi zanyi ku karuwai ne kuma zaman kanku kuke yi"

Murmushi tayi tace"ka kira ta yanzu dan Allah wallahi ka ci darajar abu d'aya da sai na nuna maka kuskurenka na kirana da my NUR karuwai ko yanzu ba kyalle ka nayi ba sai na hukunta ka mashayi kawai"tana kaiwa nan ta bar office din

har zata fita ta

Please Login or Register in order to submit comment