Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

MAI FARAR ƘAFA
(JAHILCI NE)


NA


MAMAN AFRAH


FCW


GAJERAN LABARI


FREE BOOK🥳



Page 1️⃣➡️2️⃣


Zaune take a kan kujera mai zaman mutum biyu, ta yi nisa a cikin tunanin da ita kanta bata san lokacin da ta dulmiya ba bare har ta san lokacin da za ta dawo daga nisan kiwon saƙa da warwarar da zuciyarta take mata a kan al'amuran rayuwar aurenta. Fara ce amma ba sosai ba tana da matsakaicin tsayi sai dai ba za a kira ta da gajera ba, shekarunta ba za su haura ashirin da biyar ba.




Safiyya kenan ƴa ga Malam Sadiq da Majida, abubuwan da suka taru suka cunkushe tare da cukurkuɗe tunaninta abu guda ɗaya ne wanda a kullum shi ne ginshiƙin da ya yi fice wajen daƙushewar duk wata walwala da farincikinta wannan abu ba komai bane fa ce jifanta da wasu mutanen suke da MAI FARAR ƘAFA. Wannan suna yana mata ɗaci a zuciyarta wanda wani s'in ta kan rasa a wane ma'auni za ta ajiye shi domin ita kanta bata san mafarin wannan al'amari ba bare har ta san ummul aba'isin samun sunan da har yau samuwarsa a gareta ba ƙaramin abu bane wanda take jin zai iya haifar da gagarumar matsala a rayuwarta matsawar dai mutane za su cigaba da mata kallon MAI FARAR ƘAFA.


"Ni yanzu ya zan yi da rayuwata, shin ina zan saka kaina me ya sa mutane basa gane cewar ni ma mutum ce kamar kowa ni ma ina da galihu kamar kowace mace mai ya sa mutane ba za su fahimci ni ma ina da ƴancin da zan rayu a gidan aurena kamar yadda kowace mace take rayuwa ba, amma a iya ƙarancin shekaruna a ce wannan shi ne gidan aurena na uku kuma a kowane gida sai da na haihu amma zargi irin na jahilci ba ya bari na cigaba da kasanceqa da ƴaƴana a gidan ubansu sai dai kowane na fito na bar shi ba dan raina yana so ba sai dai babu wata mafita da ta fi hakan.




" Safiyya ta kai ƙarshen zancen zucin nata da ɗan muskutawa ta gyara zamanta duk da har lokacin tana cikin kogin tunanin da ta dulmiya.


"Kowace mace taa rayuwa a gidanta hankalinta kwance sai dai ɗan abin da ba a rasa ba amma ni a nawa gidan saɓanin haka ne, ni kullum cikin fargaba da zulumin wanzuwata a gidan auren ko akasin haka, kullum kunnuwana suna tsoron sauraran furucin saki sabo da na san mutane jahilcinsu ba zai bari su bar ni na rayu cikin farinciki ba.




karkaceccen tunaninsu da ba shi da madogara ya hana su bar ni na rayu cikin kwanciyar hankali, tamkar dai ni ce kaɗai mace a doron ƙasa shikenan ni bani da kataɓus a gidan miji ko a unguwa, shin mutane mai ya sa ba za su gane komai Allah ne yake ƙaddarawa ba Allah kaɗai ne yake bayarwa kuma shi ke hanawa shi ke azurtawa kuma ya talauta, yana bayar da arziƙin ga wanda ya so a kuma lokacin da ya so sannan ya kan ƙwace a lokacin da ya so ba tare da sanin wani ɗan adam ba bate har a ce shi ne silar damuwa ko salwantar wani abu!" Ta kai ƙarshen maganar lokacin da hannunta ke kan tirtsetsan cikin da haihuwarsa ko yau ko gobe.


Ba komai yake saka ta a damuwa ba a halin yanzu sai ganin samun mijinta Rabi'u ya ragu kuma ta ji yana ta faɗar maganganu irin wanda mutane ke jifanta da su, maganganu irin wanda su ne silar fitowarta daga gidan mijinta Sani da kuma gidan mijinta na biyu Salisu. Wanda lokacin da shi Rabi'un zai aure ta ya yi watsi da maganganun yana ikirarin jahilcin mutane ne amma yanzu ana wayar gari ya fara hasashe tare da fara gaskata maganganun mutane, wanda hakan ba ƙaramar barazana bace ga aurenta domin kuwa ta san hakan yana dai dai da mutuwa, sutura tare da binne aurenta, ita yanzu a tsorace take da lamarin Rabi'u ta san a ko da yaushe zai iya sakinta shikenan ita kuma haka za ta ƙare rayuwarta kullum cikin aure-aure? Auren da ba ya ɗaukan wani dogon lokaci yake mutuwa, da yarintarta amma ake mata auri saki ba tare da wani laifin komai ba.




"Safiyya, Safiyya, Safiyya" Kiran da mijin nata Rabi'u kr faman zabga mata shi ya dawo da ita daga duniyar tunanin da bata san iya tsawon lokacin da ta ɗauka a ciki ba. A zabure ta fara ƙoƙarin tashi sabo da nauyi da jikinta ya mata, a gefe guda kuma zuciyarta na ata wani irin zillo wanda yake haɗe da faɗuwar gaban da ta ziyarce ta babu gaira babu dalili wani mugun tsoro yana yi wa gangar jikinta sallama a haka ta yunƙuro ta taso tana jin tsoron na ƙara kai mata ziyara dan daga jin kiran nan ta san akwai wata a ƙasa tabbas tana zargin akwai abin da ya faru ko kuma yake shirin faruwa.


Da sauri -sauri ta taso ta fito daga ɗakin dan har ta manta da tirtsetsen cikinta da ke cikin wata na tara, sabo da tsabar kiɗimar da take ciki. A dai dai bakin ƙofar shiga falonsa suka yi kiciɓis yana ƙoƙarin fitowa. Tun da suka ci karon jikinta ya fara mata wata irin ƙyarma wanda ganin biro da takardar da ke hannunsa su ne suka haddasa mata hakan.




Ko ta kanta bai bi tamkar ba shi ne ya ƙwala mata wannan kiran ba sai ma farar kujerar plastic da ya nufa ya fara.


ɗora takardar hannunsa wacce shigowarsa yanzu ya shiga falonsa ya ɗakko, a lokacin da yake ƙwalawa Safiyya kiran. A hankali Safiyya ta fara ja da baya har sai sa ta ji ta jingina bayanta sa bango sannan a saka hannayenta ta daddafe, a lokaci guda kuma wasu hawaye masu zafi suka shiga wanke mata fuska wanda ba komai ya kawo hakan ba sai sanin da ta yi cewa zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi.


"Oh ya Allah, ka zama gata kuma bangona abin jingina Allah ka bani ikon cinye duk jarabawar da ka jarabceni da ita da ma wacce za ka jarabce ni a nan gaba" Ta faɗa a zuciyarta idanunta kafe a kafin Rabi'u da ya sunkuya ya daddage yana rubutu a takarda.


"Ungo nan kije na sake ki saki uku!" Maganarsa ta katse mata tunaninta. Kallon takardar da yake miƙo mata kawai take amma ta rasa ƙarfin gwiwar da za ta saka hannu ta karɓa. Jikinta kuwa sai rawa yake tamkar mazari gabanta banda dukan uku-uku babu abin da take.


"Ki fice mini daga gida ga takardarki na sake ki saki biyu" Maganar sani ta faɗo mata a ranar da ya sake ta.


"Kar in dawo in tarar da ke a cikin gidana ki fice mini daga gida na yanke igiyoyin da ke tsakani na da ke" Ta ƙara tuno maganar da Salisu ya faɗa mata ranar da zai sake ta sannan yanzu ma ga Rabi'u yana furta mata kalma mafi muni da rashin daɗin sauraro.




"Babu yadda za a yi in cigaba da zama da matar da za ta kassara mini rayuwa, tun daga lokacin da na aure ki komai nawa ya tsaya cak, komai nawa ya canja daga fari zuwa baƙi ba na banbance duhu da haske ina dalili alheri sai ya zama mugunta na taimake ki na aureki amma kina neman ki daka na yi mutuwar tsaye komai nawa babu cigaba sai ci baya, a kullum al'amura daƙile mini suke kasuwa babu ciniki sai kwantan kaya, babu riba sai faɗuwa yanzu ina zuwa kasuwa na samu gobara ta kama shagon mu duk kaya sun ƙone mun yu mummunar asara duk da an kashe wutar amma ba ƙaramar asara muka yi ba, mai ya sa duk guntun shaguna basu kama da wuta ba sai nawa? Mai ya sa shagona da na maƙocina ne kawai giobarar ta yi wa dirar mikiya, sabo da shi ma ya raɓu da ni mijin MAI FARAR ƘAFA shi ya sa hakan ta same shi, kowane shago ana ciniki mutane suna ta tururuwar zuwa amma ni dai dai in gani daga nesa babu mai zuwa sai ƙalilan daga ƙarshe da aka ce kayana ne da tsada duk na karyar da su dan kawai na damu ciniki amma a banza shiru kake ji wai malam ya ci shirwa.To a yau na kai bango na kai maƙura na kai ƙarshe ya zama dole na jefar da ƙwallon mangwaro ko na huta da ƙuda kamar yadda sauran mazan da kika aura a baya suka jefar da ƙwallon mangwaron kuma suka huta da ƙudan ni ma yanzu na bi sahu sai a bi wani sarkin amma ba Rabi'u ba dan ni ko maƙiyina ne na ga zai auri mace MAI FARAR ƘAFA to wallahi zan ajiye ƙiyayyar da ke tsalaninmu in yada makaman yaƙina in yi ruww in yi tsaki dan ganin bai auri mace MAI FARAR ƘAFA ba" Rabi'u ya kai ƙarshen maganar yana mai ɗaga muryarsa tamkar wanda yake magana da wanda yake suke da muguwar razara a tsakaninsu bayan kuwa ga shi ga Safiyya wacce hawaye ke ta faman malala tamkar an buɗe famfo bakinta yana ta karkarwa tana ta so ta yi magana amma ta kasa tsabar kaɗuwa da maganganun Rabi'u duk da cewa ba wannan ne karo na farko da ta ji su ba , ta sha jin su daga bakuna mabanbanta, amma yau sai ta ji maganganun sun yi wa majiyar sautin ta shiga irin shigar karan tsaye wanda hakan ya ke ƙoƙarin yin barazana ga daƙushewar sauran jinta.


"Wai ba magana nake miki ba kin tsaya sai zubar hawaye kike tamkar dai an saar da ke mutuwar wani shaƙiƙin ki?"






"Dan Allah ka yi haƙuri wallahi duk abubuwan nan da kake faɗarsu ba laifina bane, ba ni ce ummul aba'isin faruwar hakan ba komai da kake gani muƙaddari ne daga ubangiji babu wani mahluƙi cikin bil adama da ya isa ya yi wa wani ɗan adam mummunan abu face komai yana faruwa ne da sanin da kuma izinin ubangiji komai sai Allah ya so yake faruwa duk abin da ya faru Allah ne ƙaddara kuma yana ji yana gani zai kawo maka mafita matsawar dai ka dogara da shi kuma ka yi imani da ƙaddara mai kyau da marar kyau ka ɗauki komai a matsayin jarabawarka idan ka yi hakan Allah zai baka damar cinye jarabawar k...


"Ke dalla malama dakata!!! Duk waɗannan abubuwan waye ya tambayeki? Shin kafirtani kike so ki yi? Ko an faɗa miki ban yi imani da Allah da ranar lahira ba hatta ƙaddarar na yi omani da ita dan kuwa yana daga cikin ƙaddarta aurenki tabbas ni na san auren MAI FARAR ƘAFA Allah ne ya ƙaddara mini amma babu yadda za a yi mutum yana ji yana gani ya je ya afka cikin wuta ya ƙone ƙurmus, dan haka ni yanzu babu komai a tsakanina da ke saki ne na sake ki gabaɗaya igiyar auren na yanke bare ki yi kwaɗayin in mayar da ke, ciki ne ki je gidanku ki haife zan masa yanka duk ranar da kika buƙaci bani ɗana to ƙofa a buɗe take za ki iya aiko mini da shi ko da kuwa a ranar da kika yaye shi ne kika cire shi a nono, yanzu ki karɓi takardar nan ki kama gabanki tun kan lokaci ya ƙure miki dan ni zamanki cikin gidan nan ma tamkar annoba haka na ɗauka"


Ta kasa furta komai hannunta da ke karkarwa ta miƙa masa ya dangwara mata takardar, wani yawu ta haɗiye mai ɗaci tana jin tamkar wanda ya damƙa mata garwashin wuta a tafin hannunta, ba kowa take tunawa ba sai mahaifiyarta tabbas sai ta fi kowa shiga damuwa.
MAI FARAR ƘAFA
(JAHILCI NE)


NA


MAMAN AFRAH


FCW


GAJERAN LABARI


FREE BOOK🥳

Page 3️⃣➡️4️⃣


A hankali ta fara jan ƙafafunta wanda suka mata ɗauyi hanyar ɗakita ta nufa duk da tana ganin wani dishi-dishi ga duhun ruwan hawayen da yake mata shamaki da ganin gabanta a haka ta tafi da tsohon cikin nan, bedroom ɗinta ta nufa ta ɗakko akwatinta ƴar tsakiya ta buɗe dama babu komai a ciki ta buɗe wardrobe ta shiga ɗaukan kayanta tana zubawa ita kanta bata san wane kaya babe take zuba wa shin hijabai ne ko mayafai ne ko less ko kuwa atamfofi abu ɗaya ta sani shi ne kayanta ne take zubawa. Bata ankara ba sai ganin ta yi idan ta zuba kayan suna zubewa a ƙasa sai a lokacin ta lura cewar akwatin ta daɗe da cika da kayan har ta kai matakin da murfin ma ba zai rufu ba bare a yi zancen zige zip.


Hannu ta kai ta kwashi wasu kayan ta mayar ba tare da ra lura da yawan wanɗan da suka rage a akwatin ba ta zige zip ɗin ta ɗauki hijabin da take sallah wanda yake linke haɗe da sallayarta ta saka ta ɗauki akwatin har ta fara tafiya ra tuna da takardar sakin da aka bata yanzu wacce tun shigowarta da za ta ɗakko akwati ta ajiye a kan gado. Hannu ta sanya ta ɗakko takardar ta haɗo fa ƙaramar jakarta pos, tare da janyo akwatin ta fito falo wayarta ta ɗauka ta saka a cikin jakar tare da takardar ta fito daga falon janye da akwatin.


Kallo ɗaya ta yi wa Rabi'u da ke tsaye a tsakar gidan ya kama tsantsa tamkar wanda yake jiran a ce masa kulle ya ce cass. Juyawa ta yi ta kama hanya za ta fice


"Idan an tashi zuwa ɗaukan kaya ki yi wa iyayenki karnki biyo masu ɗaukan kayan, dan ba na son ki ƙara tako ƙafarki cikin gidan nan" Ta ji amon muryarsa ya ratsa dodon kunnenta ba tare da ta juyo ba ra cigaba da tafiya dan bata da wasu kalamai da za ta iya furta masa su. Tana fitowa ta tare ɗan sahu ta shiga tare da faɗa masa inda zai kaita, shi ya karɓi akwatin ya taimaka mata wajen shigar da ita cikin adaidaita sahun sabo da ganin yadda take jan akwatin dakyar sannan ga kuka wanda bai san dalilin zubar da hawayen nata ba.




Haka ya shiga ya tada suka ɗau hanya. Safiyya kuwa tun da ya fara tafiya babu abin da take sai zubar da hawaye, ta wajen gidan Kakarta suka wuce gidan rufe yake da mukulli domin kuwa Kakar tata ta daɗe da rasuwa ta so a ce Kakar tata tana raye da a can za ta yi zamanta babu takura babu tsangwama saɓanin cikin gidan mahaifinta da ya zame mata kamar magarƙama sabo da rashin jin daɗin zama da kuma takurawa wanda take fuskanta a wajen kishiyar mahaifiyarta a duk lokacin da aurenta ya mutu tamkar a kanta aka fara mutuwar aure ta yi ta jifanta da mafanganu mararsa kai da ƙafa. Tana zancen zucin tana ta sharar hawaye bata ankara ba sai ta ji yo sautin muruar ɗan adaidaitan yana tambayarta.


"Baiwar Allah a dai dai ina zan ajiyeki" Ya tambaya ganin sun shigo unguwar da ta ce ya kaita. Sai da ta sauke wata nannnauyar ɓoyayyar ajiyar zuciya sannan ta buɗe baki dakyar kamar mai ciwon baki ta ce


"Wannan kwanar za ka shiga gida na biyu"


Karya kwanar layin ya yi yana zuwa ya tsaya a ƙofar gida na biyun kamar yadda ta faɗa. Jim ta yi kamar ba za ta fito ba sai kuma ta sako ƙafafunta ya fito cikin sanyin jiki.




Da kanta ta fito da akwatin nata ta buɗe pos ɗin ta bashi kuɗinsa kamar yadda ya faɗa yana karɓa ya ja ɗan sahunsa ya bar wajen. Yana ta tunanin kukan da Safiyyar ke ta yi bata ma tunanin ana kallonta tana kuka a titi sai dai tunawa da ya yi cewar akwai wasu damuwoyi da dama wanda mutum zai ji ya kasa riƙe zubar hawayensa ko da kuwa a ina yake kuma ko da a gaban waye.

A hankali ta ja akwarin idanunta da ke cike taf da hawaye suna kafe a kan ƙofar gidan mahaifin nata ba komai take tunawa ba sai yadda mahaifiyarta za ta ji idan ta ji cewar aurenta ya ƙara mutuwa a karo na uku kuma ba tare da ta yi wa gabaɗaya mazajen da suka saketan wani laifi ba.


Tafe yake a cikin motarsa, sanye yake da baƙin jeans da farar riga sai kuma baƙin takalmi da yake sanye cikin fararen ƙafafunsa. A hankali yake tuƙin idanunsa kafe a kan ƙofar gidan da yake hango wata a tsaye riƙe da akwati, amma shi wacce yake son yin tozali da ita ba ya tunanin a yau ma zai sake sakata a idanunsa domin kuwa ya ɗauki tsawon lokaci yana zuwa domin ya ganta ko da wulgawarta ne amma abin ya fassakara.


"Kina ina ne sarkin kuka, shin mene ne damuwarki? Mai kike so waye ya taɓa ki kin barni a damuwa ina ta tunanin damuwarki duk da cewar baki san da zamana ba bare har ki san na damu da damuwarki, sai dai abin da ya bani ƙarfin gwiwar ci gaba da jiranki sji ne na san ba matar aure bace tun da gidan ya mini kama da gidanku ne ba wai gidan aurenki ba zan cigaba da jiranki har ranar da Allah zai ƙara haɗa ni da ke wanda hakan zai sanya na rufe duka babin damuwar da ke cikin zuciyata" Cewar Annur da ke zancen zuci yana tuƙi. A dai dai lokacin da ya ƙaraso ƙofar gidan da yake son ganin wacce yake fata da burin sanyata a idaniyarsa a kullum.




Tun da yake a rayuwarsa sai biyu ya taɓa ganinta kuma a ƙofar gidan da take tsaye tana zubar da hawaye.


"Allah ka karɓi addu'ata ka ƙara haɗa ni da ita ba tare da na bi ta hanyar wani ba" Ya faɗa a dai dai lokacin da zuciyarsa ta buga da uban ƙarfi sanadin idanunsa da ya sauke a kan kyakkyawar fuskarta wacce take zubar da hawaye kamar yadda ya taɓa gani sau biyu yau ma hakan ce ta faru sai yanzu ya tuna cewar gabaɗaya ganin da ya mata sau biyu lokacin ma tana riƙe da akwati a hannunta sai dai gabaɗaya akwatinan mabanbanta ne kamar yadda ya lura domin kuwa babu wani abu duk ƙanƙantarsa da zai manta a game da ita. Da sauri ya take birki wanda ƙaran ya sanya Safiyya da ke tsaye har lokacin bata shiga gidan ba ta juyo da sauri domin ƙaran motar ya dawo da ita daga tunanin da take na yadda za ta shiga gidan nasu da kuma abin da zai faru. Hannu ya sanya ya shafe fuskarsa tare da murza idanunsa domin tabbatar da abin da idanunsa ke masa tozali da shi, domin yana son bambance tsakanin aya da tsakuwa yana son tabbatarwa cewar ba ƙarya idanunsa ke masa ba, kuma ba gizo bane sannan ba mafarki bane kamar yadda yake yi a kullum ita ɗin ce a zahiri, sabo da tsabar farincikin da ya samu kansa ciki ko lura bai yi da tirtsetsen cikin jikinta ba.






Safiyya kuwa dawowarta cikin hayyacinta daga tunani sai ta yanke shawarar shigewa cikin gidan. Annur kuwa da mugun sauri ya buɗe motarsa dan yana so ya cim mata amma yana sako ƙafarsa hakan ya yi dai dai da jan akwatin da Safiyya ta yi ta shige cikin gidan. Ko ƙofar bai tsaya rufewa ba dan so yake ya mata magana cikin gudu-gudu sauri-sauri ya tunkaro wurin sai dai cikin rashin sa'a Safiyya har ta shige dan ita bayan motar babu wani da ta gani dan gilashin motar yana da yalwar baƙi baka ganin na ciki bare ma tana cikin yanayin da ba za ta iya lura da ko waye a motar ba dan dama yana daga cikin halinta ƙin shiga sabgar mutane da shiga abin da babu ruwanta.


A dai dai ƙofar ya tsaya daga ɗan baya-baya idanunsa kafe a jikin ƙofar zuciyarsa tana ta zillo tana kaiwa da komowa dan ganin wacce duk bugun da zuciyar za ta yi tare da ita yake bugawa duk da bai san sunanta ba. Hannayensa duka biyu ya saka a cikin kwantacciyar sumar kansa yana murzawa tare da yamutsawa idanunsa na kawo ƙwallar da bai san dalili ba sai dai hakan ya san ba ya rasa nasaba da halin da ya ga wacce yake muradin gani cikin halin damuwa na zubar da hawaye. Ya fi minti uku tsaye a wurin yana kallon ƙofar daga bisani ya juya cikin rashin ƙarfin jiki ya nufi motar tasa.




Shiga motar ya yi ya zauna jiki babu ƙwari, goshinsa ya ɗora a kan sitiyarin motar yana jin wani abu na ratsa dukkanin ƙofofin jikinsa ya daɗe yana so ya ganta ko da daga nesa ne tsawon lokaci bai ganta ba amma kuma yau ya samu ganinta sai ya ji yana so ya mata magana, so yake ga ganshi tare da ita ya tambayeta damuwarta ta faɗa masa domin yana so duk runtsi ya yi maganin damuwar tata dan ba ya ƙaunar ganinta cikin ƙunci ya fi so ya ga murmushi shimfiɗe a kan fuskarta duk da bai taɓa ganin murmushin nata ba amma dai zai fi kyau a ce murmushin ne ya maye gurbin kukan dan ya san dai babu yadda za a yi kuka ya fi yi wa mutum kyau sama da dariya. Sai dai kash! Hakan bai samu ba. Ya jima zaune a cikin motar amma bai ga ta fito ba kuma bai ga wani ya shiga gidan ba duk da ya ɗaukawa kansa alƙwarin ba zai taɓa neman wani ya haɗa shi da ita ba ya fi so shi sa kansa ya samu wannan damar. Wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗagowa daga kan sitiyarin ya sanya hannu ya rufo ƙofar yana jin babu daɗi a ransa dan har wani ciwo-ciwo ya ji kansa yana yi masa. Motar ya kunna ya bar wajen yana rayawa a ransa cewar zai dawo ko Allah zai sa ya ƙara ganinta.




Safiyya kuwa shigarta cikin gidan muryarta har rawa take yi wajen yin sallama, Mama Majida da fitowarta daga kicin riƙe da kofi ta ji sautin yin sallama amma muryar mai sallamar ta mata kama da ta wacce ta sha kuka ta ƙoshi dan haka wajen hanyar ƙofar ta kalla aikuwa idanunta suka sauka a kan Safiyya da ke ƙara yin sallama a karo na biyu da ƙarfi gaban Mama Majida ya bada wani sautin rass sabo da tsabar kaɗuwar da ta ziyarce ta a lokacin da idanunta suka sauka a kan akwatin ƴar tata.




"Innalillahi wa inna ialaihir raji'un" Shi ne abin da take ra maimaitawa a zuciyarta. Duk da ta san aure rai ne da shi kuma babu wanda ya isa ya canja ƙaddarar ubangiji, sannan ba wai ta gaji da kasancewar ƴar tata ɗaya tilo bane da ba za ta so dawowarta gida ba duk da buri kowane iyaye a kan ƴaƴansu bai wuce su gansu zaune ɗakin mijinsu suna zaune lafiya da kuma kwanciyar hankali ba, babu wasu iyaye da za su so mutuwar auren ƴaƴansu sai dai idan haka Allah ya

Please Login or Register in order to submit comment