Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fatan kasancewa har iya ƙarshen numfashinsa.


"Ranka ya daɗe wata wuta na hango tana shirin kama wa a gidan nan wacce idan ta kama za ta haifar da gobara wacce ba ƙaramar ɓarna za ta yi ba don...


"Ibra ka dai san ban cika son gutsiri tsoma ba, kuma ka san wannan doguwar Hausar da kake jerowa ba wai ina fahimta bane sanin kn ka ne ban zauna na yi rayuwa a ƙasar Hausa ba na tsawon lokacin da zan ke iya fahimtar wannan murɗaɗɗiyar Hausar gwara ka mini gwari-gwari yadda zan fahimta"




"Ranka ya daɗe wata ƴar unguwarmu na gani a gidan nan mai suna Safiyya to cikin ikon Allah sai ma na ji ka ce ita ce za ta maka ɗanwaken"


"To sai aka yi yaya? Mene ne matsalarka da hakan ni fa ba na son shishshigi in ma wa na ce ya girka mini kai mene ne naka a ciki"


"Ranka ya daɗe ka gane mana, yarinyar nan aurenta uku, aurenta na farko ta auri wani Sani haihuwarta ɗaya suka rabu saboda gabaɗaya samunsa ya ragu sai uban talauci ya baibaye shi aikuwa suna gano FARAR ƘAFA gareta ya rattaba mata saki, ɗan ma mahaifiyarsa ya baiwa dan ba ya so FARAR ƘAFARTA ta shafe shi. Bayan ta fito ta auri wani Salisu shi ma dai hakan ce ta faru ɗan nasu yana wajensa ya ba wa sabuwar matar da ya aura. Ta zo ta auri wani Rabi'u shi ma dai auren bai je ko ina ba ya sako ta da tsohon ciki saboda karayar arziƙin da ya same shi talauci ko ta ina ya masa katutu ba komai bane sila kuma sai FARAR ƘAFAR Safiyya.




Yanzu maganar da nake maka a ranar da ya sake ta ubanta mahaifi ya saki mahaifiyarta ya musu korar kare kuma ba a kan komai ba sai a kan FARAR ƘAFAR Safiyyar dan ba ya son komai nasa ta kassara masa shibya sa ya jefar da ƙallon mangwaro ya huta da ƙuda. Tun daga ranar ba a ƙara jin ɗuriyarsu ba aka rasa ma ta inda suka bar unguwar dan kowa sai ya ce bai gansu ba wannan ya sa mutanen unguwa suka yi ta murnar cewar annoba ta bar wajen su. To fa yanzu ina shiga gidan na yi arangama da tauraruwa mai wutsiya wacce ganinta ba alkairi bane wato Safiyya MAI FARAR ƘAFA. Shi ne na ce ba zan yi ƙasa a gwiwa ba dole in garzayo in faɗa maka domin a ɗauki mataki dan kar a sakankance sai dai ka ga komai na arziƙi yana ja baya komai yana lalacewa ya ɓalɓalce dan da zarar ta ɗauki kwanaki uku a gidan nan to kuwa abin ba zai yi kyan gani ba" Ibra ya kai ƙarshen magana yana kallon Annur da tun da ya fara magana yake kallonsa da baki a sake.




"Allah mai hikima da baiwa, Allah mafi ji da gani Allah mai yadda ya so da bawansa. Wato ka ce ashe ƴar baiwa ce Safiyyar bamu sani ba"


"Baiwa kuma Ranka ya daɗe, ana ga yaƙi kana ga ƙura, kaska raɓi mai jini ce fa ba wai baiwa gareta ba zama da ita jafa'i ne d...


"Dakata Ibra!!! Ka san mai kake faɗa kuwa, Safiyyar kake jifa da munanan kalamai haka? Shin in banda JAHILCI da rashin imani da cewa Allah ke bayarwa kuma shi ke ƙwacewa a ce wai har ɗan adam yana iya hana alkairi ya samu mutum, ko kuma a ce yana sanya alkairin da mutum yake da shi ya rasa. Shin ina ilimin jama'a yake? Kenan idan har ɗan adam zai iya talauta wa to ina tauhidi yake? Shin ina imani da ƙaddara mai kyau da marar kyau? Shin bayan faɗin ma'aikin Allah ne cewa mutum ya yi imani da Allah da mala'ikunsa da litattafansa da ranar lahira da kuma imani da ƙadddara, alkairinta da kuma sharrinta.




To in har mutum ya yi imani da waɗannan abubuwan kenan ba zai zargi kowa a kan wani abu da ya same shi ba, duk abinda ya same shi zai fawwala shi ga Allah ne domin duk abinda Allah ya ba wa mutum to ko duniya za ta taru babu mai ƙwace masa haka idan Allah bai bashi ba ko duka duniya za ta taru ba za su bashi ba, saboda haka duk abinda Allah ya bayar shi ya ga dama ya bayar kuma a ko wane lokaci zai iya karɓa. Kuma da kke maganar idan ta yi kwana uku to a wata huɗu kaɗan ne babu a kwanakin da suka yi a gidan nan suna gidan nan daga ita har mahaifiyar tata kuma Alhamdulillahi arziƙinmu na ta haɓaka babu asara ko ta ƙwandala da ta same mu dan ko yanzu bayan shigarka cikin gidan nan an mini waya motocina da na yi odarsu suna nan zuwa na biliyoyi ma kuwa kuma sanin kan ka ne akwai kwangiloli da nake yi wanda kullum sai dai alkairi da samun nasara a cikinsu ba wai faɗuwa ba da a ce JAHILCIN da kuke jifan Safiyyar da shi na FARAR ƘAFA haka ne da tuni ai wata maganar ake ba wannan ba kuma ina so ka sani ko da a ce yau zamu wayi gari a gidan ƙasa da langa-langa wato mun talauce babu cin yau sai an nemo to wannan ba zai sa mu zargi Safiyya ko wani ɗan adam da haka ba dama Allah ne ya bamu kuma shi ya karɓa , dan ya bamu bai mana alkawarin za mu dawwama da arziƙin ba dan haka ka kiyaye idan ka ƙara wani furuci marar kyau a kan Safiyya wallahi!!! Sai ka gwammace kiɗa da karatu idan ku JAHILCI ya muku katutu to ni fa ilimina kuma Alhamdulillahi ina aiki da shi bar wurin nan" Annur ya kai ƙarshen maganar yana aika wa Ibra wata muguwar harara.


"Haka ne, haka ne, haka ne" Shi ne kawai abinda Ibra ke maimaita wa yana tafiya cikin sanyin jiki kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki.


MAMAN AFRAH😍








MAI FARAR ƘAFA
(JAHILCI NE)


NA


MAMAN AFRAH


FCW
GAJERAN LABARI
FREE BOOK


🔚🔚🔚


Page 1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣


Tun daga wannan dana Ibra bai ƙara gigin kai wa Annur gulmar Safiyya ba kai ko da ma abin da ya danganceta ne. Annur kuwa ya dage sosai wajen ƙoƙarin fahimtar da Safiyya soyayyar da yake mata tun tana jin kunyarsa har dai ta kai ta kawo ta fara sakin jiki da shi. Shi kuma bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen gina soyayyarsa mai tsafta haɗe da tsaya wa a rai da zuciya.


Mama ta yi matuƙar yin farinciki da kasancewar Annur masoyi ga Safiyya saboda nagartarsa da kuma tsayar da ibada mutumin kirki ne da kowa yake yabonsa ko ita shaida ce a kan halaye na kirki masu nagarta da Annur ɗin yake da su mutum ne shi da kowace uwa za ta so ya kasance miji ga ɗiyarta kuma kowace mace za ta so ya kasance miji kuma uban ƴaƴa a gareta.




A ɓangaren Safiyya ta yi murna sosai da bayyanar soyayyar Annur ɗin a gareta da yake nuna mata zallar ƙauna babu algus kuma ko a gaban waye. Da farko ta ji kamar bata cancanci kasancewa masoyiya a gareshi ba kasancewar bazawara wacce ta auri maza uku ta haifi ƴaƴa har uku amma kuma nuna ta isa tana da daraja da muhimmanci shi ne abu na farko da ya kawar mata fa duk wani tunani tare da rusar aƙidar da ta ɗauka na cewa ta daina yin soyayya bare har ta kai da yin aure saboda irin ƙalubalen da take fuskanta amma shigowar Annur rayuwar da kuma yadda ya nuna cewa ita ɗin daban take ita ɗin kamar kowa take ita ta musamman ce shi ne abin da ya sanya ta ji zuciyarta ta kwaɗaitu da kasancewa tare da shi bare uwa uba nasiha da jan hankali da Mama ke mata, ita da Baba Dudu hakan ya sanya ta jefar da duk makaman yaƙinta ta bada kai bori ya hau.

Annur kuwa ji yake tamkar dai bai taɓa kasancewa a cikin farinciki ba sama da ranar da ya bayyana wa Safiyya soyayyarsa, rana ce da t kasance ta musamman a wajensa wacce ya saka a kuddin tarihin tayuwarsa da ba zai manta da ita ba ko da wasa.






Domin rana ce da ya fitar da abinda je damun zuciyarsa tsawon lokaci wanda so ya masa kamun kazar kukun da bashi da wani buri da ya wuce ya bayyana wa abar son sa ƙaunar da yake mata bare kuma ranar da ta nuna ta amince da shi sai ya ji tamkar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha dan farinciki. Daddy kuwa sai ya ji kamar babu wanfa ya fishi jin daɗin hakan domin ya yaba da hankalin Safiyya kuma tun kan ya san Annur ɗin yana son Safiyyar ya masa sha'awar aurenta sai dai kasancewar ƴaƴan zamani kar ya masa tayin hakan ya watsa masa ƙasa a ido shi ya sa ya ƙyale shi yanzu kuma da ya bayyana sai ya ji ya yi frinciki kasancewar yana ganin nagartar Safiyya yayaba da hankali da tunaninta dan ba kamar sauran mata take ba gashi dai yarinya ce mai ƙananan shekaru amma kuma hankali da tunaninta na manya ne.


*RABI'U*


Tun bayan da ya saki Safiyya yake zaton zai samu hauhawar arziƙinsa da bunƙasar kasuwancinsa sai dai abin ya ci tura dan yana ganin kamar ya jefar da ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda ashe abin ba haka bane. Dan bayan rabuwarsu sai da komai nasa ya ƙare wasa-wasa sai ga shi hatta ƙananan abubuwa suna neman gaggararsa shi da yake da yara a shagonsa har ta kai ta kawo ya dawo shi ne yaron shagon, daga baya ma sai komai ya ɓalɓalce masa dan hatta kayan ɗakin Safiyya da yake ikirarin idan za a zo kwasar su kar a zo da ita sai gashi ko ɗaukan kayan babu wanda ya zo har ya siyar da kayan ɗakin da tufafinta ya ja jari da su dan ya samu labarin an ce tun daga ranar da ya sake ta ubanta ya koresu daga gidansa ita da uwarta. Hakan ya sanya ya ƙara ji a ransa dai dai ya yi da ya sake ta tun da ga shi uban da ya haifeta ma ya gujeta. Wani ɗan wuri ya samu ya haɗa rumfa a umguwarsu yana siyar d kayan miya su tumatur tattasai albasa da sauransu yana ji yana gani duniya ta juya masa baya lokaci ƙanƙani arziƙi ya koma talauci.




Tun yana ganin sakin Safiyya mafita ce har ya dawo yana da na sanin sakinta dan wata bazawara da ya aura sai dai ya gwammace kiɗa d karatu ga rainuwar tsiya komai ya mata bata godewa saɓanin Safiyya mace mai haƙuri da kawar da kai, duk abin da kaa bata sai dai ta karɓa ta yi godiya da addu'ar samun buɗi kuma ba za ta taɓa cewa abin bai mata ba ko kuma ba zai ishe ta ba sai ga shi ya yi gamo da dai dai da shi wata rana ko magana yake idan tana masa jaraba kamar uwarsa ko ta ding nuna masa yatsa wataran har tsone masa ido take idan tana masa faɗa. Da na sani dai duj da ƙeya ce amma RABI'U ya yi ta tafi cikin carbi dan yana ganin samunsa da yake raguwa kamar daga gareta ne ai gashi Allah ya nuna masa ishara da bata nan ma talaucin ya fi baibayeshi har ta kai da zuwa kasuwa ya gagareshi ya dawo siyar da kayan miya.


*MALAM SADIQ*


Bayan korar su Mama daga gidansa ko sau ɗaya bai taɓa yin nadama ba, dan yana ganin abinda ya yi shi ne dai dai musamman ma da mutanen unguwa suke nuna masa ko waye ma hukuncin da zai yanke kenan har da masu cewa ai ita Mamar ita ta ga za ta iya tun da ta zaɓi bin ƴarta a kan zaman aure da yake ibada. Ko da wasa bai taɓa neman inda suke ba dan sai karensu suke ci ba babbaka shi da Umma. Kafin daga baya wata ƙaddara da suka rasa mafarinta ta fara afka musu dan duka ƴaƴan Umma mazajensu suka sake su suka dawo gidan banda bala,in faɗa babu abin da suke a tsakaninsu iyayen basu isa su tsawatar musu ba sai su dinga nuna wa kansu ɗaya da su, ga masifaffa yawon jaraba dan dama ba tarbiya ce da su ba ga babu ilimin addini abin sai ya taru ya musu yawa wai shege da hauka.




Sanadin abubuwan da ƴaƴan Umma suke hawan jini ya fara yi wa Malam Sadiq dirar mikiya, jinya ba ya iya zuwa ko nan da can haka Umma ta barbaɗawa idanunta toka ta ringa gallaza masa ba sa taimakonsa daga ita har ɗiyant idan suka fice yawonsu suka kawo kuɗinsu sai su ba Umma su hana Baba abu ya tare masa goma da gomiya har ta kai ya dawo yana da na sani a kan abinda ya yi wa su Mama dan ya lura abinda ke faruwa da shi ba ya rasa nasaba da alhakinsu. Dan akwai wani lokaci yana kwance a ɗakinsa aka masa sallama ya bada izini ashe Salisu ne tsohon mijin Safiyya na biyu ya zo ya bashi haƙuri a kan ya aura masa Safiyya dan ya gane kurensa na JAHILTAR abubuwan da suke samunsa ya danganta su da ita sai yanzu ya gane gaskiya na Malam Sadiq ɗin ya fashe da kuka yana bashi labarin abinda ya faru ya faɗa masa a halin da ake ciki yanzu shi ma neman Safiyyar yake ruwa a jallo. Haka Salisu ya tafi cikin ƙunar rai yana jin son Safiyya na dawowa sabo dal a zuciyarsa yana ji da a ce yau zai ganta ya mayar da ita ɗakinsa to da ya fi kowane namiji sa'a a rayuwa.
Bayan tafiyarsa da sati biyu Sani ma ya zo wajen Malam Sadiq bada haƙuri da neman bikon Safiyya dan ya samu labarin an ce aurenta ya mutu shi ma nan Malam Sadiq ɗin ya rattaba masa bayanin bai ma san inda Safiyyar take ba dan ya koreta a kan FARAR ƘAFAR d ake cewa tana da ita. Haka ya tafi yana addu'ar Allah ya bayyana Safiyyar ya mayar da ita ɗakinsa su yi zaman soyayya tare da rungumar ɗan da suka haifa wanda suka hana ta riƙe ɗan gudun kar ya raɓeta ya gogi annobar FARAR ƘAFA.






*Mama*


Abinda Daddy ya sanar da ita ne ya ɗaure mata kai, ta shiga tunani jin Daddy ya zo wajenta da ƙoƙon bararsa na soyayyarta tare da neman amincewarta a kan ta yarda ta aure shi. Ta yi mamaki tare da jin abin wani banbarakwai musamman da ya kasance Safiyya na soyayya da Annur har ana shirin yin aure. Safiyya kuwa murna take Mamarta ta samu nagartaccen miji wanda take ganin mahaifinta bai kai shi a komai ba, amma ba komai na dukiya ba ita tafi kwaɗayin halayyarsa dan dama maganar dukiya ma babu ita dan kuwa ba za ma a haɗa ba.


*BAYAN WATA BIYU*


A rana ɗaya aka ɗaura auren Mama da Dady Annur da Safiyya. Auren da ya zama sanadin wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan SARKIN SHANU auren da ya mantar da Daddy rashin mahaifiyar Annur da ke addabar zuciyarsa a kullum domin ya samu mace ta gari wacce take masa abu kwantankwacin wanda mahaifiyar Annur take masa wacce take bashi kulawa tamkar jaririn da aka haifa a daren yau!


A gida ɗaya suke rayuwa kowa yana ɓangarensa da ban dan Daddy ya ce ba ya son su Annur su yi nisa da shi. Daddy Safiyya ce tashi Mama kuma Annur ne nata kowa da wanda ke masa ɓaci. A haka har aka wayi gari da ɓullewar ciki a jikin Safiyya wanda ta ga gata da kulawa daga wajen Daddy Annur kuwa tamkar ya goyata a haka ta haifi ɗiyarta mace wacce aka saka mata sunan Mahifiyar Annur Fatima suna kiranta da Timo.


Wata rana Daddy da Annur suka ce Mama da Safiyya su shirya domin zuwa wani waje haka suka shirya Mama ta ɗauki Fatima suna baya ita da Daddy Annur da Safiyya a gaba Annur yana jan motar Safiyya sai murna take wata unguwa suka ga an nufa da su wani gida madaidaici a nan suka sauka suna shiga gidan suka tarar da Mahaifin Safiyya Malam Sadiq kwance ba lafiya yana ganinsu ya fara kuka yana neman yafiyarsu Mama da sanin babu abinda ya haɗa ta da shi tun da auren wani take yi yanzu dan haka ta ce dama bata riƙe shi ba Safiyya kuka take tana cewa ta yafe masa.




Ashe Annur ne ya siya masa gidan da yake ciki ya ɗauki wani saurayi yake kula da shi dan Umma da ƴaƴanta sun guje shi dan Umma har sai da ta sanya ya sake ta ta bar shi da jinyar da suka yi silar samuwarta a jikinsa ita da ƴaƴanta.






Tun daga wannan rana Safiyya kan zuwa ta gaishe da mahaifinta, ta kai masa abin arziƙi Daddy ya biya aka kai shi asibiti cikin ikon Allah ya samu lafiya yanzu bashi da wani abu da yake alfahri da shi sama da ƴarsa Safiyya wacce ya wulaƙanta a baya ya koreta gata yanzu ta zame masa sanyin idaniya. Malam Sadiq har malamin sunna ya sanya ya yi wa,azi a game da JAHILCIN da mutane suke na jifan wasu da masu FARAR ƘAFA Alhamdulillahi kuma saƙo ya je inda ake buƙatar zuwansa domin kuwa mutane sun falka daga duhun JAHILCIN da suka yi nutso a ciki sun gane cewar komai Allah ne yake bayarwa kuma shi yake ƙwacewa a duk lokacin da ya so babu wani ɗan adam da FARAR ƘAFAR sa za ta yi sanadiyyar rugujewar katangar samun mutum. Ibra yanzu an fahimta an daina gulma da tsegumin MAI FARAR ƘAFA dama komai ta yi farko yana da ƙarshe.


Tafe suke a mota su biyu ne a ciki Annur yana gefe inda Safiyya take jan motar dan shi da kansa ya koya mata har ta iya ita kuma da ta iya in za su fita tare sai ta ce ita za ta tuƙa su. Duk da ita ma tana da mota yanzu ga kasuwanci da take wanda Annur ya bata jari mai kauri take yi. Daddy kuma ya biya musu aikin Hajj su duka suka je bayan ta yaye Fatima.


Suna cikin tafiya ta ga wurin da suke siyar da goba (Guiva) Irin manyan nan.


"Sweet hearta kanga irin gobar da na ce ja siyo min jiya amma ka siyo mini wannan nunanniyar ni na fi son wanda basu nuna ba"Ta ƙare maganar tana wani zumɓuro baki.


"Takawarki lafiya Annurin zuciyata, yo ni in ma cewa kika yi in nemo bishiyar gobar ai sai inda ƙarfina ya ƙare, mu tsaya mu fita ki zaɓi irin wacce kike so da kan ki dan na fara fuskantar dab kije da yi wa Timo ƙani ko ƙanwa" Ya faɗa yana kanne mata ido ɗaya murmushi ta yi bata ce komai ba dan ita ma tana zargin ciki ne da ita. A dai dai wajen ta yi parking kafin ta buɗe ƙofar har ya fito daga cikin motar ya zagayo ya buɗe mata yana jiran fitowarta, kallonsa kawai ta yi tare da yin murmushi ta sako ƙafafunta ta fito suna yi wa juna murmushin so da ƙaunar juna.




Rabi'u da ke zaune daga can gefen mai siyar da goba yana gyaran takalmi domin yanzu shoe shainer ne. Tun da motar ta tsaya ya ji tamkar dai akwai wani abu nasa a cikin motar hakan ya sanya ya dakata daga gyara takalminda yake yi wa wani saurayi d ya kaɗe mas hankali sai sanabe yake masa a kan irin gyara da wankin takalmin da yake so ya masa. Idanunsa suka sauka a kan Annur da ya fito ya kewaya yana shirin cigaba da gyaransa ya ga ya buɗewa wata mace kyakkyawa ƙofa wacce yanayin farin fatarta da irin hutun da jikinta ya nuna tana samu ya yi zaton ko balarabiya ce. Amma kuma ƙayataccen murmushin da ya ga tana jifan wanda ya buɗe mata motar shi ya ankarar d shi Safiyyarsa ce. Da hanzari ya yi jifa da takalmin hanunnsa ba shiri ya miƙe tsaye ya nufi wajensu hankali tashe dan har hawaye sun fara zarya a fuskarsa ganin yadda Safiyyar ta ɗaukaka shi kuma ya ƙasƙanta hakan ya nuna masa halih rayuwa da kuma fawwala komai ga Allah domin kuwa ga shi ya gujeta saboda gudun talauci amma kuma bai tsira ba saboda haka Allah yake son ganinsa kuma lokacin karayar arziƙinsa ya yi hakan ya sa bashi da tsumi bashi da dibarar tserewa ƙaddarar da ta tunkaro shi.




Safiyya da suke tsaye gaban mai goba hannunsu cikin na juna kallo ɗaya za ka musu su baka sha'awa domin dacewar da suka yi da juna. Kawai sai ganin mutum suka yi a gabansu tamkar an jefo shi.


"Safiyya dama kina raye? Ina ta fafutukar nemanki har gidanku na je amma mahaifinki ya sheda mini bai san inda kike ba dan Allah ki yi haƙuri ki dawo mu cigaba da rayuwarmu Safiyya na yi nadamar sakin ki yanzu ina matuƙar sonki da...


"Dakata Malam! Ka adana kalamanka wataƙila idan ka je wani wajen za su maka amfani wannan matar aure ce tana tare da mijinta idan ka zauce ne ka dawo hankalinka" Cewar Annur yana mau shiga tsakanin Rabi'un da Safiyya dan gadan-gadan ya tunkareta. Baki sake Rabi'u ke kallonsa dan shi duk tunaninsa ma Safiyyar yawon banza take domin ganin yanayin shigarta ya nuna tana samun kuɗi hakan ya sanya ya ɗauka ko daduronta ne Annur ɗin dan bai taɓa tunanin ko a mafarki za ta samu miji kamar wannan ba bare har ta samu kulawa kamar wata sarauniya mijin ma wani yaro ɗanye sharaf da gani ya san saurayi ne duk da dai zai fi Safiyyar a haife.


"Tabbas ni matar aure ce kuma da mijina nake tare, sannan idan maye ya ci ya manta uwar ɗa ba z ta manta ba, shin ka manta saki ɗai-ɗai har uku ka mini, babu kome tsakaninmu to wallahi ko da akwai kome kuma bani da aure ba zan koma gidanka ba, bare wani hanin ga Allah baiwa ne dan ni yanzu wallahi wutsiyar taƙumi ta yi nesa da ƙasa" Safiyya ta faɗa tana karɓar ledar gobar bayan Annur ya miƙa kuɗin ko canjin basu karɓa ba suka juya hannunsu cikin na juna dan Annur har da riƙo ƙugunta suka je ya buɗe mata ta shiga ya shiga tana shirin tada motar sai ga Rabi'u kamar an jefo shi ya zo yana kuka wiwi wai ta daure ta kashe auren ta dawo gidansa wani kallon raini ta watsa masa ta tada motar ta tada ƙura ta bar wajen a 360 Saurayin da Rabi'u je yi wa gyaran takalmi ne ya biyo shi yana cewa ya zo ya ƙarasa masa gyaran amma Rabi'u ko kallonsa bai yi ba ya juya ba tare da ya ɗau kayan gyaran takalmin ba ya nufi gida, yana jin ɗaci da kishin Annur a zuciyarsa ya gwammace ya je gida matarsa in tsikareshi ma za ta yi ta tsikareshi da bala'in da yake jinsa a ciki yana ta mamaki dan bai taɓa zaton akwai ranar da za ta zo ba shi da kansa ya nemi Safiyya ya rasa ba! Dama ai ɗan hakin da ka raina shi ke tsone maka ido.




BAYAN SHEKARA BIYAR


Yanzu Safiyya yaranta uku biyu mata ɗaya na miji, Fatima ce babba sai na miji Abubakar wanda ya ci sunan mahaifinta suna kiranshi da Sadiq sai kuma ƙaramar Munawwara. Soyayya suke nuna wa juna tamkar su haɗiye junansu

Please Login or Register in order to submit comment