Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suke neman abin hawa da kuɗinsu suka rasa amma ga shi zai kai su kyauta ba tare da su suka nemi taimakon ya kai su ba sannan ma wai asibitin kuɗi kuma zai ɗauki ɗawainiyar lallai hanyar Allah yawa gareta. Mama da ke ta jinjina alkairin da zai musu a ranta take faɗa.


"Amin ya hayyu ya qayyum" Haka kawai ya faɗa.

Safiyya kuwa tana jin duk abin da suke cewa sai dai ciwo ya hana ta magana.






A dai dai get ɗin asibitin mai suna FHARAHA ya tsaya, yana tsayawa Mama ta buɗe ƙofar ta fito ta gewaya ta buɗe wa Safiyya.


"Sannu Safiyya, Allah raba ku lafiya"


"Safiyya kenan sunanta Safiyya" Annur da fitowarsa kenan sunan Safiyya da Mama ta ambata ya yi wa majiyar sautinsa dirar mikiya. Yana ta maimaita sunan a zuciyarsa ya ga Mama ta fito da ita ƙarasa wa ya yi ya mayar da ƙofar ya rufe.


"Mama ba zan iya hawa ba benen ba" Muryar Safiyya da ke cikin tsananin ciwo ta furta a hankali, Annur da ji ya yi tamkar ta masa busa da sarewa a kunne sautin muryarta tamkar wanda aka zuba wa zuma kan daɗi wai a hakan ma tana cikin halin rashin lafiya ne ina ga tana da lafiya ga muryar a hankali.


"Matar aure ce" Wani ɓangaren na zuciyarsa ya katse shi lokacin da suka shiga get ɗin yana biye da su, kuma da yake gabaɗaya asibitin a saman bene yake dan ƙasan shaguna ne a wurin.


"Ki daure ki hau kin ji" Annur da bai san da zaman fitowar maganar ba sai jin ta ya yi ta kufce masa ta fito ba tare da ya shirya ba.


"Eh haka za ki daure ki hau" Muryar Mama ma ta ƙara da faɗin hakan. A hankali a hankali suke tafiya har suka hau saman Annur yana biye da su.

Bayanan faɗa masa duka kuɗin ya biya ita kuma nurses sun shiga da ita labour room Mama tana nan tsaye ta kasa zama kana ganita ka san tana cikin damuwa.


"Innalillahi wa inna ialaihir raji'u, La'ilaha ilallahu muhammadur rasulullahi S.A.W" Muryar Amminsa ta dawo masa a lokacin da take halin naƙuda tana ɗakin haihuwa ita ce magana ta ƙarshe da ta zauna daram a kunnensa maganar da ita ce maganarta ta ƙarshe a duniya haka ta tafi da cikin jikinta bata haihu ba. Wannan tunanin da ya faɗo masa wanda lokacin da abin ya faru suna tsaye a dai dai windown ɗakin haihuwar da mahaifiyarsa take ciki a wani asibiti na kuɗi yanzu kimanin shekara biyu kenan. Da sauri ya juya ya sakko daga saman benan jin hawaye suna neman zubo masa yana zuwa ya buɗe ƙofar motar ya shiga ya zauna ya rufe ya kifa kansa a sitiyarin yana jin ƙunci da damuwa suna yi wa zuciyarsa ƙawanya.


"Shin ita ma kar dai ta je ta mutu" To ina zan sanya rayuwa ta, ko bata mutu ba ta haramta a gareka matar wani ce fa. Ina mijin nata yake mahaifiyarta ce kaɗai za ta kawo ta asibiti haihuwa shi wanda ya mata cikin ina yake ko ba ya muradi da murnar haihuwar da za a masa kamar yadda wasu mazan JAHILCI ke yi wa katutu a kan ba sa son haihuwa? Ko dai ba ɗan sunna bane ɗan gaba da fatiha ne?"


"Noooooooo" Ya faɗa a fili yana ɗago kansa daga kan sitiyarin.






Neman agajin da waya take yi shi ya dakatar da shi yana mamakin ina aka samu waya a mota dan ya san tashi tana aljihunsa. Cigaba da ƙaran wayar a motar ne ya so ya addabi majiyar sautinsa kuma ƙaran yana ƙara masa damuwa da ɓacin ran da yake ciki. A fusace ya juya yana kallon bayan motar aikuwa idanunsa suka sauka a kan wata ƙaramar pos da ke kujerar da Safiyya ta zauna. Ƙaran dai yana katsewa wani kiran ke shigowa, da sauri ua miƙa hannu bayan ya ɗakko wayar lokacin kiran ya ƙara katsewa wani ya shigo.


"Kai ina dalili wannan mai kiran da naci yake ni yanzu su da suke cikin halin nan ma na nufe su da waya?" Cewar wani ɓangare na zuciyarsa.


Kawai ka kashe wayar dan mai kiran ba zai daina kira ba in ya so daga baya ka sanar da su" Wani sashen na zuciyar tasa ya ƙara raya masa hakan.


A ɗan fusace ya kai hannu ya zige zip ɗin, yana zigewa wata takarda ta faɗo wacce ba a linke take ba.


"Na sake ta saki uku" Shi ne abin da idanun Annur suka sauka a ka. Cikin sauri ya ajiye jakar dai ko wayar da ke faman ruri bai fiddo ba, hannunsa har karkarwa yake wajen miƙar da takardar gabansa na bugawa da mugun ƙarfi dan tun da yake a rayuwarsa bai taɓa ganin takardar saki ba.


*Ni Rabi'u na saki Safiyya saki uku, ba dan ta min laifin komai ba sai dan tana ɗauke da FARAR ƘAFA da kuma ƙashin tsiya a tattare da ita kullum samuna raguwa yake ba ya ƙaruwa*


Shi ne abin da ke ƙunshe a jikin takardar.


"Safiyya, saki uku"
Su ne kalam da suka fara kai kawo suna safa da marwa a ƙwaƙwalwar Annur.


MAMAN AFREH
09030283375
MAI FARAR ƘAFA
(JAHILCI NE)


NA


MAMAN AFRAH


FCW

FREE BOOK🥳


Page 9️⃣➡️1️⃣0️⃣




"Mene ne kuma MAI FARAR ƘAFA? Tana da ƙashin tsiya shin mai waɗannan kalamai ke nufi, amma ai ya ce bata masa komai ba" Cewar wani sashe na zuciyar Annur har lokacin idanunsa kafe a kan takardar kamar wanda aka ce zai gano asalin tambayar fa yake jefawa kansa domin shi bai san ma'anar kalmar FARAR ƘAFA ba bare mai ƙashin tsiya.


"Shin dama kuka take mijinta ya sake ta? Kenan son sa take bata son ya rabu da ita shi ya sa har take yin kuka...

Tun kan ya kai ƙarshen maganar zucin ya ji kishi ya turnuƙe shi, gabaɗaya ransa ya ɓaci tuna wa fa ya yi tana ƙaunar mijinta ashe ma ba shi bane a zuciyarta shi kaɗai yake kiɗansa yake rawarsa.


"Ka manta bata sanka ba, ka manta bata sa ma kana sonta ba, to ma wai ko da ta sanka kana da tabbacin za ta soka, an sha samun namiji yana ƙaunar mace amma ita bata ƙaunarsa ko a samu mace na ƙaunar namiji amma shi ba ya ƙaunarta.




"Ɗif bugun zuciyarsa da ke faman yi da sauri da sauri ya tsaya cikin ƴan sakanni kafin ya cigaba da bugawa da ƙarfi.


"To kenan duk ganin da nake mata da akwati sakinta yake shi sa take kuka, to amma wannan ne karo na uku da nake ganinta a irin halin kuma dai yanzu saki uku na ga ya ce, ko dai sauran yaji ne take tahowa wannan karon ne ya sake ta?" Takardar ya tuƙunƙune ya ɗauki jakar ya tura a ciki haɗe da wayar ya ja zip ɗin jakar tamkar zai tsinke shi, jakar ya ɗaga ya jefa kan kujerar da ya ɗauka yana jin wani abu a ransa da ya kasa gane mene ne. Kansa ya mayar kan sitiyarin ya kifa tare da mayar da idanunsa ya lumshe.




Gabaɗaya ya rasa wane kalar tunani zai yi ƙunci damuwa duk sun taru sun masa katutu a ƙahon zuciya, na rashin takamaiman abin da zai yi a gefe ɗaya kuma halin da take ciki na naƙuda yana karyar masa da zuciya. Sai dai wani tunani da ya masa dirar mikiya yanzu a ciki sakkani shi ne abin da ya sanya shi ɗago da kan nasa daga sitiyarin.


"Tana haihuwa fa ta gama idda" Shi ne abin da zuciyarsa ta raya masa wanda hakan ya sanya shj ɗago da idanunsa wanda suka masa jawur ya sauke a kan saman benen asibitin tamkar dai wanda aka ce Safiyyar ce a wajen. Wani murmushi ne ya saɓuce masa yana jin wani yanayin mai daɗi na ziyartarsa har wani nishaɗi-nishaɗi yake ji saboda tunowa da ya yi cewar idan Safiyya ta haihu ta gama idda kenan za ta iya zama mallakinsa. Da sauri ya buɗe ƙofar ya fito cikin asibitin ya koma yana hawa matakalar da bibbiyu tamkar dai wanda aka sanar da shi Safiyyar ta masa alƙawari za ta aure shi, dan yana raya wa a ransa cewar zuwa yanzu ta haihu dan ya kwashe awa biyu a wajen.




Yana hawa saman idanunsa suka sauka a kan Mama da ke ta safa sa marwa a santar wurin, idan ta je ta dawo sai ta ɗaga hannu sama alamar addu'a. Jikinsa ne ya yi sanyi daga ƙwarin gwiwar da ya shigo da shi a sanyaye ya nufi wajenta. Mama kuwa da juyowarta kenan ta sauke idanunta a kansa da sauri ta ɗan juyar da fuska gefe ta goge ƴar ƙwallar da suka taru a idanunta, a hankali ya ƙaraso wajenta yana jin tausayinta duk da bai santa ba a yau ya fara haɗuwa da ita sai ya ji tamkar mahaifiyarsa, ga shi ya lura mutuniyar kirki ce.


"Ya jikin nata?" Ya jefa mata tambayar a ladabce lokacin da ya ƙaraso wajen.


"Da sauƙi"


"Bata sauka ba?"


"Eh ana can ana fama, sun ce idan ta ƙara awa guda bata haihu ba tiyata za su mata sabo da sun lura ba za ta iya haihuwa da kanta ba"


"Innalillahi wa inna ialahir raji'un"


"Ina mijin nata ina son ganinsa a office" Likitan da ya fito daga ɗakin haihuwar wata nurse na biye da shi ya faɗa lokacin da ya zo wajen su Mama.




Mama da tashin hankali ya bayyana ƙarara a fuskarta jin kalaman likitan ta buɗe baki da niyyar magana sai ta ji Annur ya ce


"Ga ni, to bari na zo" Tsabar mamaki ma ya hana Mama magana dan ita tunaninta ma ta ce mijinta ba ya nan tun da dai ta san a halin yanzu babu wani miji da Safiyyar take da shi tun da ya sake ta duk da ɗansa ne za a haifa amma dai bata ga kyan wuri a kunnen jaka ba, dan ta san babu mutunci a al'amarin Rabi'u bare ta yi tunanin ma sanar da shi halin da ake ciki dan ta san neman da likita ke yi wa mijinta na sanya hannu ne a takardar da za a mata tiyatar da kuma biyan kuɗin aikin wanda ta san ko sama da ƙasa za ta haɗe Rabi'un ba zai taɓa biyan ki ƙwandala ba ko da bai sake ta bare kuma yanzu da ya san ya yanke alaƙar auratayya a tsakaninsu babu ruwansa ta yi rai ko ta mutu. Bare kuma mahaifinta wanda zai maye gurbinsa tun da duj inda aka nemi miji ya saka hannu in baya nan uba za a nema in ba ya nan wa ko ƙane ko wani shaƙiƙi wanda ta san basu da su gabaɗaga dan ita Mamar ita kaɗai iyayenta suka haifa kuma sun rasu sannan ita ma Safiyya ita kaɗai ta haifa sai ƴan uwanta mata wanda suke uba ɗaya wanda ko jituwa ma basa yi bare a yi zancen ƴan uwantaka dan duk sun ware Safiyya a cikin dangi a cewarsu annoba ce kar ta goga musu kashin kaji na FARAR ƘAFA. Kafin Mama ta ce wani abu sai kawai ta ga Annur ya bi bayab ɓɓn daktan da sauri.
"Ah wannan yaro Allah maka albarka lallai mahaifiyarka ta baka tarbiya na taimako, kuma kana da zuciyar tausayi" Cewar Mama a zuciyarta tana kuma yi wa Allah godiya.


Bayan an masa izini ya shiga office ɗin ɗauke da sallama. Amsa masa daktan ya yi ya masa nuna da wurin zama hannu ya bashi suka yi musabiha duk da shi Annur burinsa kawai ya ji mene ne dalilin kiran dan zuciyarsa cike take da tsabar fargaba dan tsoronsa ɗaya kar ma Safiyya mutuwa ta yi shi ne daktan zai faɗa masa.


"Ina so ne ka saka hannu domin za mu yi wa matarka aiki mu ciro baby saboda babyn a kwanciyarsa ba a daidai take ba kuma mun yi ƙoƙarin mun juya shi sai dai abin ya faskara sai wahala take sha babyn ma na wahala amma haihuwar ta ƙi daɗi daga kan babyn ya taho sai ya koma dole sai an mata aikin dan ceton ranta da na abin da za ta haifa" Maganar dakta ta dakatar da Annur daga zancen zucin da yake.




"Haba likita a kan me za ka kira mata mutuwa, bayan numfashi Allah ne kaɗai yake busawa kuma shi kaɗai ya san ranar mutuwar bawa ai kamata ya yi ka ƙarfafa gwiwa ba wai ka saka sarewa a zuciyar ɗan uwan marar lafiya ba" Annur da kalmar mutuwa ta daki zuciyarsa har ya fusata har ɓacin rai ya sanya shi faɗa wa likitan magana, kana kallon idanunsa ka san ransa a ɓace yake kuma yana cikin matsananciyar fargaba.


"Ba haka nake nufi ba kuma ko ni ai ba zan so ta mutu ba kawai ina faɗa maka abin da zai faru ne idan aka ɗauki tsawon lokaci nan gaba ba tare da an cire babayn ba, tun da a halin yanzu an saka mata ruwan naƙuda ya ƙare duk wasu ƙwayoyin da za su taimaka mata wajen naƙudar an bata amma shiru duk ta bi ta galabaita dan haka yanzu ba surutanka nake buƙata ba ka yi saurin saka mini hannu ai ko ma me na faɗa a kan aikina nake"


"Ko da shi aka haifeka" Annur ya faɗa yana jan takardar ya sanya hannu, wayarsa ya fito daga aljihu ya masa transper kuɗin da ake buƙata, shi dai likitan bai ƙara tanka masa ba dan ya san yana cikin damuwa ne kawai.




Gaba ma ya iyo ya bar Annur ɗin a cikin office ɗin dan yana so a shiga da ita yanzu, shi ma Annur ɗin bayansa ya biyo yana jin dakyar yake iya ɗaga ƙafarsa saboda yadda jikinsa ya mutu. Yana fitowa ya ga Mama tsaye wacce ta rasa inda ma za ta sanya ranta, suna nan tsaye Annur ya jingina da jikin windown sai ga wata nurse ta kira Mama, haka Mama ta bi bayanta da sauri shi ma Annur bai san ma ya bi bayanta ba sai da ya ji wata nurse tana dakatar da shi a kan cewa maza ba sa shiga ɗakin haihuwa. Mama tana zuwa ta ga halin da Safiyya take ciki gabaɗaya ta galabaita ƙarfinta ya ƙare.


"Mama ki yafe mini dan Allah"




"Babu abin da kika mini Safiyya za ki samu sauƙi da yardar Allah za a yi aikin cikin nasara" Cewar Mama hannunta na cikin na Safiyya bayan nurse ta bata wata rigar yadi blue da huta mai raga-raga ta saka mata su ne uniform ɗin da ake saka wa wanda za a yi wa aiki.


"Ni Mama kawai so nake a cire cikin in huta" Cewar Safiyya tana magana dakyar sai wani uban gumi ke tsatstsafo mata. Suna cikin wannan maganar likita ya dakatar da su ya sanya aka tura gadon Safiyya zuwa ɗakin tiyatar Mama tana biye da gadon idanunta kafe a kan ɗiyarta wani tausayinta na mamaye zuciyarta Alah sarki soyayyar uwa da ban ce babu wanda zai maka soyayya sama da ta mahaifiya shi ya sa ma Allah ya ambaci a yi wa mahaifiya biyayya mahaifiya sau uku sannan ya ambaci uba sau ɗaya. Annur da ke jingine a inda aka dakatar da shi ganin an garo Safiyya da ke kwance lifet a kan gadon sai ya ji hankalinsa ya yi bala'in tashi idanunsa a kanta ko ƙiftawa ba ya yi gani yake kamar kallon ƙarshe yake mata ganin Mama ta yi sauri ta riƙe hannunta sai shi ma ya nufi gadon idanunsa jawur ya ce


"Sofy ki yi haƙuri kin ji yadda kika shiga lafiya za ki fito lafiya" Ya faɗa cikin sanyin murya da ido ta bi shi tana son karantar yanayin da ya mata magana duk da tana cikin wani hali amma kuma sai ta ji daɗin yadda ya mata magana da taushi da tausaya wa, hakan ya sanya ta ji wani sanyi a ranta dan ta san bayan mahaifiyarta bata da wani wanda yake mata magana mai daɗi cikin sanyin rai ta saba da jin baƙaƙen maganganganu mararsa daɗin saurare wanda basu da tushe daga bakin mutane mabanbanta.




tabbas ta gane shi, shi ne ya kawo su asibiti a mota ya kuma biya mata komai tabbas da ganinsa mutumin kirki ne hakan ya sanya ta fara ƙoƙarin buɗe baki ta masa magana amma kuma wani uban koma wa da babyn cikinta ya yo gefe guda sai qata azaba ta ziyarceta wacce ta kasa tantance wa da sauri likitan ya bada umarnin a wuce da ita dama an dakata ne dan mijin nata ya mata sallama saboda kar ta Allah ta kasance. Hannunta ta ɗaga a hankali ta haɗe da ɗayan alamar godiya a haka aka shige ɗakin da ita Mama kuwa bata ma san mai ake ba dan ta juya tana ta faman share hawaye. Har sai da aka shige da ita ya daina hango ta sannan ya dawo hayyacinsa, jin wami danshi a fuskarsa ya yi saurin kai hannu wurin a take danshin ruwa hawaye ya yi wa hannunsa sallama.


"Kuka?" Ya jefa wa kansa tambayar cike da mamaki.


"Tabbas kuka kake, ai Safiyya ta wuce matsayin wasa a wurinka soyayya ce ta haƙiƙa kake mata in baka sani ba ma ka sani" Wani sashen na zuciyarsa ya bashi amsa.
MAI FARAR ƘAFA
(JAHILCI NE)


NA

MAMAN AFRAH


FCW


Page 1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣



"Ya rabb ka dubi baiwar nan taka ka raba ta da abin da ke jikinta lafiyaka fito mini da ita cikin aminci ka raya abin da za ta haifa" Cewar Mama a fili tana tsaye a ƙofar ɗakin tiyatar, da yake akwai wani benci a wajen idan ta zauna sai ta tashi tsaye gabaɗaya ta rasa abin da za ta yi. Allah kaɗai ne ya san irin fargaba da tashin hankalin da take ciki domin bata son ta rasa Safiyya tana ƙaunar tilon 'yarta duk da kasancewar mutane na ƙyamatar ta ita kuma sai ta ji duk duniya bata da sanyin idaniyar da ya wuce Safiyya daa Bahaushe ya ce abincin wani gubar wani


A hankali yake ɗaga ƙafafunsa da ya ji zuwa lokacin sun masa nauyi har suna barazanar kasa ɗaukan gangan jikinsa tabbas da a ce za a buɗe zuciyarsa babu yadda za a yi ba a ga an rubuta damuwa ba a nasa ganin kenan saboda irin ɗinbin damuwar da ta baibaiye masa ruhi ji yake kamar ya hankaɗa ƙofar ɗakin tiyatar ya shiga ya je ya ganta ko ya samu salama domin ya fi so ko mutuwa za ta yi ta mutu a kan idanunsa. Saboda a halin da yake ciki yanzu idanunsa ita kawai suke kallo gizo suke masa da ita ganinta yake lokacin da aka tura ta aka shige d ita tana haɗe masa hannayenta wanda ita ta yi ne a matsayin godiya shi kuma tasa zuciyar tana faɗa masa cewar sallama take masa tare da nuna masa ya yi haƙuri idan ta Allah ta kasance saboda yaudararsa da zuciyar tasa take tana nuna masa ta san yana ƙaunarta dan a yadda yake jinta a ransa gani yake zai yi wuya a ce bata san da zamansa a gogin zuciyarta ba.




"Yanzu Annur idan ka ga sun fito da ita a mace ya za ka yi? Wane irin yanayi za ka shiga wani hali za ka kasance a ciki bayan barinta duniyar?" Wani sashi na zuciyarsa ya jefa masa tambaya dai dai da halin fargabar da yake ciki.


"Ba za ta mutu ba, ba za ta mutu ba ba za ta mutu ba" Shi ne abin da yake maimaitawa a fili kamar wani zautacce. Mama da bata san ma yana wurin ba saboda ruɗanin da take ciki ita ta ɗauka ma yana wani wurin da ban ko ma ya yi tafiyarsa tun da ya musu mai wuyar amma jin kalaman da amon muryarsa ya isarwa majiyar sautinta shi ne abin da ya sanya ta juyo a firgice domin gane wa idanunta, shin waya yake yi shi ma wata yar uwarsa tana cikin wani hali dan da alama shi ma yana cikin irin halin da take ciki na fargabar mutuwa ko shi ma 'yar uwanrsa take cikin yanayi na halin rayuwa ko mutuwa kamar yadda ita ma take ciki.


A kansa ta sauke idanunta ganin babu waya a kunnensa hakan ya dagula lissafinta, dan bata ga alamar ma ko wani yake faɗa wa maganar ba. Ƙafarsa ya tako ya nufo wajenta dama a can gefe yake yana zuwa ƙwallar da ke kwarmin idanunsa ta gangaro masa hawayensa suka riga furucinsa fitowa dan a lokacin yana cikin damuwar da yake son a lallashe sa, a faɗa mas kalma mai daɗi wacce za ta rage masa fargabar da yake ciki ko ma a maye masa gurbin damuwar gabaɗaya duk da ganin fitowar Safiyyar cikin ƙoshin lafiya shi ne ai haifar masa da hakan amma yana buƙatar ko yayana ne ya ɗan samu salama.


"Ba na so ta mutu" Ya yi yaƙi fa bakinsa kafin ya samu damar fito da kalaman ya wannan da ya isar da su ga Mama wacce ke masa kallon rashin fahimta dan ita ta kasa gane mai yake faɗa a kan wa kuma yake furta maganar tasa domin kallo ɗaya ta masa ta ga damuwa ƙarara haɗe da tashin hankali marar misaltuwa kwance a kn dakalin fuskarsa.


"Wacece???" Mama ta jefa masa tambayar a kiɗime dan tunaninta ya bata ko waya aka masa mahaifiyarsa ko wata 'yar uwarsa bata da lafiya shi ne ya shiga damuwa. Annur kuwa da ganin fuskar Mama da damshin hawaye sannan duk ta wani birkice kana ganinta za ka fahimci akwai matsala a tattare da ita, sai haka ya ƙara ɗugunzuma damuwar tasa. Dan sai yake kallon fuskar Mamar tamkar ta mahaifiyarsa dan ya san ita ce take lallashinsa duk lokacin da yake cikon damuwa bata taɓa bari ya shiga ƙunci duk runtse bata bari hawayensa ya zuba ɗan gata ne amma kuma bai rasa tarbiya da nagartattun halaye ba. Sai dai kashi mai raba wa ta raba, ƙasa ta rufe idanunta yadda ba zai sake ganinta ba ma bare ya tunkareta da damuwarsa har ta masa maganin matsalarsa tabbas uwa -uwa ce, kuma duk wanda bashi da ita ya yi kuka wanda yake da ita kuma ya kyautata mata ya ƙara yi wa Allah godiya saboda mahaifiya sanyin idaniya ce baka da kamarta baka da masoyi duk duniya saboda ita duk wanda zai nuna maka so ko ya baka kulawa to tabbas a bayanta yake.




Tambayar da Mama ta jefa masa ita ce ta warto shi daga duniyar da ya lula a ciki sai lokacin ya ɗan dawo hayyacinsa, sai lokacin ya fahimci shi ke kiɗa da rawarsa babu wanda ya san abin da yake cikin zuciyarsa sai Allah.


"Wacece ba za ta mutu ba, wata ce ba lafiya ne, kalli yadda kake kuka" Cewar Mama da tausayinsa ya baibayeta tana ganin shi ma ya yi ƙoƙari matuƙa wajen taimakonsu su ma ya kamata su tausaya masa tun da dai ta san ba ƙaramin abu bane zai sanya namiji kamar wannan zubar da hawaye. A take ita ma Mamar ta ji tata zuciyar ta ƙara shiga damuwa damuwar da take ciki ta ruɓanya kasancewarta mace kuma duk mace an santa da rauni.


Annur kuwa hannu ya kai duka biyu ya yi saurin shafa wa aikuwa ya yi gam da katar na taɓo ruwan hawayensa da ke kwance yana gamgarowa a dakalin fuskarsa. Da sauri ya sanya tafukan hannun ya goge kamar mai gudun kar wani ya gani har sai da ya ji babu sauran hawayen a fuskar sai dai ya tabbatar ko babu kuka zahiri akwai na zuciya wanda ya fi na zahirin ciwo da kuma ƙuna a zuciyar mai yinsa.


"Ba, ba, babu kowa" Ya ba wa Mama

Please Login or Register in order to submit comment