Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amsa har tana ɗan inda -inda tare da ƙoƙarin maye gurbin damuwar da murmushin yaƙe wanda ya yi ƙoƙarin hakan amma abin ya faskara. Mama kuwa da yake ba yarinya bace duk iya ƙoƙarinsa na ya ɓoye mata a matsayinta na mace mai yawan shekaru ta fahimci akwai gagarumar damuwa a tattarw da shi dan an ce labarin zuciya a tambayi fuska. Dan haka ko da ya yi ƙoƙarin yaƙi da fuskarsa wajen yin murmushin yaƙe bai samu zarafin yin hakan ba dan haka sai ya yi ƙoƙarin kawar da maganar da cewa.


"Ba a fito da ita ba?" Ya tambaya dan ya nuna wa Mamar shi fa zuwansa wurin kenan.Ƙaran buɗe ƙofar ɗakin tiyatar shi ne ya dakatar da su daga maganar da suke a kiɗime su duka suka juya da sauri suka nufi wajen
gadon Safiyyar da aka garo ta.




Har rige-rige ake da Mama da Annur wajen zuwa wajen gadon da aka garo Safiyya da ke kwance lifet a kai. Daga Mama har Annur babu ma wanda tunanin ina babyn yake kawai hankalinsu gabaɗaya a kan Safiyya yake. Annur ne ma ana dab da shiga ɗakin hutun da za a kaita ya juyo zai yi wa likitan tambaya sai ya ga ashe saboda saurin da yake yana biye da gadon har ya ba wa likitan tazara, dan haka yana juyo wa ya sauke idanunsa a kan likitan da wacce take riƙe da babyn suna tahowa. Ganin zai ɓata wa kansa lokaci ma sai ya juya ya shige ɗakin dan dama so yake ya rage fargabar zuciyarsa dan tambayar likitan zai yi bata mutu ba? To kuma dai sai ya ga gwara ya bi su in ya so gani ga kori ji. Suna shiga aka kwantar da ita a kan gado, Mama da Annur idanunsu a kan cikinta suna ganin yadda cikin nata ke ɗaga wa alamar numfashi wanda hakan ke nuni da tana nan a raye bata mutu ba. Wata nannauyar ajiyar zuciya da Annur ya sauke wacce sai da kowa na wurin ya kalle shi aikuwa ya murtuke fuska yake muzurai.


"Alhamdulillah!" Cewar Mama a zuciyarta tana ƙara gode wa Allah.


Likitan da suka shigo ne, hankalin Mama ya koma kan babyn da ke hannun nurse ɗin wanda ke naɗe da ɗankwalin atamfar Mama da aka ce ta bada zanin da za a saka baby ganin basu zo da komai ba ya sanya ta ciro ɗankwalin ta bayar da yake ɗankwalin da girmansa kuma atamfar ma sabuwa ce wankinta ɗaya. Sai lokacin ma Mama ta tuna da ashe fa ɗa aka ciro dan ita gabaɗaya Safiyyar ce a ranta.




"Ah ga babyn nan da ta haifa namiji ne, da kanta ma ta haihu dan ana shiga naƙudar ra zo gadan-gadan to da muka ga haka sai aka dakata ba a fara aikin ba, da yake Allah ya rubuta ba za a yanka ta ba sai ta haihu da kanta" Likitan ya kai ƙarshen maganar yana kallon Mama, sai kuma ya maida kallonsa kan Annur wanda fuskarsa take washe kamar auduga sai ka ce an masa albishir da gidan aljanna.


"Za ka bini office ka bani acc no in maida maka kuɗin aikin da ka tura tun da ba a mata aikin ba"


"Na bar maka" Annur ya faɗa cikin halin ko in kula.




MMN AFRAH






MAI FARAR ƘAFA
(JAHILCI NE)


NA


MAMAN AFRAH


FCW
GAJERAN LABARI


FREE BOOK🥳


Page 1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣


"Ban gane ka bar mini ba, kuɗinka ne fa kuma na ce ba a kai ga mata aik...


"Idan baka buƙata za ka iya ba wa wanda yake buƙata" Annur ya katse likitan cikin halin ko in kula hankalinsa ma na ga Safiyya da ke ta faman bacci. Daga Mama har likitan da kallon mamaki suka bi shi, amma shi ko a kwalar rigarsa.


"Sai dai ina jimamin sanar da ku yaron bai zo da rai ba" Cewar likitan da ke kallon Mama tana karɓar babyn a hannun Nurse ɗin.


"Allahu akbar kabiran " Cewar Mama da Annur da suka haɗa baki wajen faɗa. Cikin sanyin jiki Mama ta buɗe yaron da ke cikin ɗankwalin tana kallonsa kamar su ɗaya da mahaifinsa sai dai shi yaron ya ɗakko hasken Safiyya.


"Allah sa mai ceto ne" Cewar Annur yana kallon Mama.


"Amin ya Allah" Mama ta amsa cikin sanyin murya, ƙwalla na zubo mata ta saka hannu ta goge.


"Allah sarki ta san ya mutu fa, babu rabon ta gan shi yana raye haka Allah dama yake yi wani mai gajeran lokaci ne sai dai Allah sa mai ceto ne" Cewar Nurse ɗin da ta miƙa wa Mama babyn.


"Eh wallahi kuma kwa ga shi ta fi shan wahala a haihuwarsa"Cewar Mama tana kallon Safiyya da ta ɗan motsa.


"Ta biyu ce haihuwar?" Nurse ɗin ta tambaya.


Dudummm! Sautin ƙirjin Annur ya buga da mugun ƙarfi jin ana batun ba haihuwarta bace ta farko.


"Kenan tana da wani ɗan? Za ta iya yin auren kisan wuta ta koma gidan mijinta dan saboda ɗanta ba la...


" Wannan haihuwarta ta uku ce"


"Uku?" Sautin maganar Annur ya daki majiyar sautin Mama kallonsa Mama ta yi ganin duk ya wani diririce sai ma ta rasa mene ne dalilinsa na yin wannan tambayar mai kama da titsiye?"


"Allah sarki ni duk tunani na ma haihuwar fari ce" Ya wayance dan kar Mama ta fahimci inda ya dosa duk da yana ganin hakan da hawala amma kallo ɗaya za ka masa ka fahimci maganar ta buge shi.


"A'a haihuwarta biyu wannan ce ta uku" Mama ta bashi amsa.


Nurse ɗin kuwa bin su Annur take da kallon mamaki dan duk tunaninsu Annur mijinta ne amma kuma ga shi ta ji ya yi tambayar da ta fahimci ko yawan ƴaƴan mai haihuwar bai sani ba wanda a ƙiyasi ko da a ce ɗan uwa ne na kusa zai iya sanin yawan ƴaƴanta.




"Allah raya"


"Amin"


"Ya kamata wannan a tafi da shi gida a masa sutura, ita ma idan ta falka muka ga babu abin da ke damunta za mu sallameta tun da lafiya ta haihu" Maganar likitan ta ratsa kunnuwan Safiyya da ke jin ta ita ba ido biyu ba ita ba mai bacci ba tana jin maganganun su Mama sama-sama. Jin wannan maganar sai ta buɗe idanunta dakyar dan ta san dai ita da Mama ne suka zo asibitin kuma su kaɗai suke da junansu idan Mama ta tafi da gawar ina za ta je a yi suturar tun da Baba ya kore su. Tana buɗe idanunta ta fara ƙarfin halin tashi zaune duk da ba wai gajiyar ta barta bane, dan bata gama jin ƙarfin jikinta ba amma ya zama tilas ta tashi dan idan an sallameta su tafi tare da Mama dan ta san yanzu za a fara cewa su kira ƴan uwansu.


"Sannu" Cewar Annur da ke tsaye idanunsa ƙurrr a kanta.


"Yawwa" Ta faɗa a hankali tana maida idanunta da suka mata nauyi ta lumshe saboda nauyin da suka mata tana buƙatar ta huta akwai bacci a idanunta sai dai damuwar da take ciki da kuma zuwan abin da ta haifa babu rai duk ya ɗauke baccin.


"Sannu Safiyya" Cewar Mama tana matsawa ganin bayan ta rufe idanun ta sake buɗe su. Wannan lokacin bata amsa wa Mama sannun da baki ba, kanta kawai ta iya ɗaga mata tana kallon mahaifiyarta wacce tausayinta gabaɗaya yake mamaye zuciyarta ga shi a yau sanadinta mahaifinta ya sake ta duk da cewar dama ba wai tana jin daɗin zaman gidan bane amma dai ko yaya gidan aure rufin asirin mace ne kuma aure garkuwa ne ga kowacce mace. Duk da cewa wau matan na ganin wani auren ne ke amsa wannan sunan amma dai ko ma yaya ne aure ibadah ne.


"Ku barta ta samu hutu domin ta wahala" Cewar likitan bayan ya duba wata marar lafiyar da kan wani gadon daga gefe ya saka kai ya fita.


Mama kuwa da Annur kallonta suke da tausaya wa dan tuni bancin har ya ƙara kwasarta. Annur kuwa fita ya yi da takardar magungunan da likitan ya bashi wanda za a siya mata. Yana fita masallaci ya wuce ya gabatar da sallar la'asar dan dama lokaci da ya je ƙofar gidan su Safiyya daga masallaci yake wanda suke gabatar da sallar azahar sha biyu da rabi. Bayan ya yi sallar ya je ya siyo magungunan a parmacy na asibitin ya dawo da ledar maganin. Lokacin Safiyyar ta tashi ma tana zaune ta jingina da filo a kan gadon.


Biyar da rabi likitan ya basu takardar sallama bayan ya tabbtar da babu wani abu da yake damunta. Da kanta a ta fito Mama tana riƙe da jaririn da har lokacin Annur cike yake da mamakin ganin babu wani nasu da suka kira kai ko da mahaifin yaron. Suna fitowa suka shiga motar Annur kuwa wani shago ya shiga jim kaɗan ya dawo niƙi-niƙi da ledoji. Ya buɗe gefen mai zaman banza ya saka ledojin ya shiga ya tada motar suka fara tafiya. Babu wanda ya ce komai sai Mama da ke ta saƙa da warwarar inda za su nufa a gefe ɗaya Safiyya tana jin nauyin ƙirjinta na ita ce silar damuwar mahaifiyarta.


Tun da ya hau kan titi Mama take ta faman tunanin inda za ta ce ya ajiye su dan ta san shi a nashi tunanin gidan da ya ɗakko su zai mayar da su.


"Bawan Allah ka gangara gefen titi mu sauka"




Kalaman Mama suka sauka a majiyar sautin Annur. Safiyya kuwa bata yi mamakin furucin Mama ba, dan dama ta san an rina wai an saci zanen mahaukaciya.


"A nan zan sauke ku kuma? Dama ba gida zan kai ku ba, ai ba damuwa indai dan ni ne zan kai ku har gida" Annur da tunaninsa ya basa cewa ko suna ganin da takura ne shi ya sa suka ce ya sauke su dan tunaninsa ko ɗan sahu za su hau.


"Ba sai ka kaimu gidan ba, nan ma mun gode Allah saka da alkairi" Muryar Safiyya da ta fara keta hazon ta shiga gajimare har ta isa cikin kwararon kunnuwansa cikin sanyi da sanyaya wa.


"Dan Allah ku barni in ƙarasa ladana mana ina ne gidan, ga shi ina buƙatar a sallaci gawar amma sai ku ce in ajiye ku a titi haba" Annur ya faɗa cikin sanyin murya idanunsa kafe a kan titi.


"Kar ka damu ai ba gidan da ka ɗakko mu za mu je ba, kuma ma inda za mu je layin mota bata shiga" Mama ta faɗa tana kallonsa.


Shiru ya ɗan yi yana nazarin magmar Mama amma kuma dai ko mota bata shiga layin ai dai ya rage musu hanya.


"Ni ma ina son a yi wa yaron sutura tare da ni ga shi yanzu la'asar ta yi sosai ya kamata a je a sallace shi ko a miƙa shi makwancinsa" Ya faɗa yana waiwayo wa baya idanunsa kafe a kan jaririn da ke a naɗe yana hannun Mama. Safiyya ma kallon gawar yaron take idanunta cike taf da hawaye dan ita kukan zuci take wanda ya fi na zahiri ciwo, yaron da ko mahaifinsa bai san da zuwansa duniya ba ga shi yanzu ba komai take tunani ba sai waɗanda za su yi wa yaron sutura har su miƙa shi inda kowane ɗan adam yake dakon jiran ranar tafiya can. Dan wataƙila ma sai sun je sun nemi taimakon wanda zasu yi jana'izarsa.


"Wace unguwa ce za a kai ku wane layi ne kuma" Muryar Annur ta katse shirun.


"Haba Malam ba wai bamu ji daɗin taimakonka bane, tabbas mun ji daɗi kuma mun gode sannan ba za mu gushe ba muna maka fatan alkairi a kan alkairinka gare mu sai dai ba sai ka kai mu can ɗin ba a nan za mu sauka" Cewar Safiyya da zuwa lokacin abin ya fara ɓata mata rai domin ta fara ganin kafiyar mutumin hakan na neman nuna yana neman sanin sirrinsu da suke ɓoye wa babu wanda ya sani sai junansu.




"Allah sarki ku yi haƙuri dan Allah ba wani abu nake nufi ba da ban" Annur ya faɗa kamar zai yi kuka dan yadda ya ga Safiyyar na maganar sai ya karanci akwai ɓacin rai a kwance a fuskarta shi kuma tausayinta ma duk ya bi ya addabi zuciyarsa ya lura da tana cikij dakuwa duk da bai san takamaimao damuwar ba sai dai ya san hakan ba ya rasa nasaba da sakin da mijinta ya mata har guda uku lokaci guda ga shi tana zuwa gida ba tare da ta huce daga ɓacin ran sakin ba naƙuda ta tashin mata wani ƙarin damuwar ɗan da ta sha wahalar haihuwarsa wada ya fi so da ƙaunarsa ya karɓi abinsa.


"Bawan Allah gidan can da ka ɗakko mu haya muke kuma mai gidan ya sallame mu a kan bamu biya kuɗin hayar da yake binmu ba" Cewar Mama cikin hikima dan ta lura yana son taimaka musu bai kamata su watsa masa ƙasa a ido ba duk da cewar bata ƙaunar sanar da kowa cewar mahaifin Safiyyar ya kore ta daga gidan ita kuma ya sake ta duk da cewar zance ba ya ɓuya ko da kuwa rami aka haƙa aka saka shi sai an samu mai tono shi amma dai ita ba zaa ji mutuwar sarki a bakinta ba kuma ko dan a yi saurin yi wa yaron sutura ya kamata su sanar da shi cewa korarsu aka yi daha gidan haya a ƙalla dai ko ba komai ba zai ga laifinsu na ɓoye masa wani abu ba tun da dai zai fahimci basu da wurin zuwa bare ya takura sai ya kai su.






Tun da Mama ta fara magana yake kallonta da tausaya wa, ashe dai basu da wurin zuwa shi ya sa suke ɓoye- ɓoye yake raya hakan a ransa. Safiyya kuwa tun da ta ji Mama ta fara magana sai ta sunkuyar fa kai dan ta ɗauka Mamar za ta sanar da shi asalon maganar a ganinta kuwa ai ba ƙaramin abin kunya bane a ce uba ya kori ƴarsa daga gidansa saboda wata manufa fa bata da madogara, kai ko da kuwa ƴar cikin shege ta yi gudun abin kunya ai uban ba ya koreta ba dan idan ya koreta bai san inda za ta je ba kuma bai san wace rayuwa za ta ƙara faɗa wa ba. Amma jin Mama ta yi hikima wajen faɗa masa sai ta ji zuciyarta ta yi sanyi ko ba komai maganar sirrinta ne.


"Allah sarki ai da kin min bayani Mama da abin bai kai nan ba" Annur ya faɗa yana kiranta da Mama kamar yadda ya ji Safiyya tana kiranta. Mama na shirin magana sai ta ga ya ja motar ya hau kwalta a tunaninta ma ko gidan zai kai su ya ce zai biya kuɗin hayar hakan ya sa ya ji babu daɗi a ranta dan ta san zai ji ta masa ƙarya idan ya je zai biya kuɗin hayar aka tabbatar masa da cewa ba gidan haya bane ga shi kuma yana ganin girmanta hakan ya sanya ta ji duk ta shiga damuwa. Amma ganin ya ɗauki wata hanyar da ban sai suka shiga kallon kallo ita da Safiyya. Hanyar fada ya nufa sai da ya je wajen gidan sarki a karya kwanar da za ta sada shi da unguwar WAZIRAWA a dai dai ƙofar wani katafaren gida ya tsaya wanda gidan aka masa ado da dagi irin na sarauta. Ya shiga danna horn mai gadi ya buɗe musu get mamaki ne ya cika wa Mama zuciya ganin ya kawo su gidan Alhaji Anas Aliyu (SARKIN SHANUN GUMEL) Gidan hakimin da yake ji da tashen dukiya wanda kaf garin da wasu garuruwan da ma jihohi da dama sunansa ya shahara kasancewarsa mutum mai yawan alkairi da ƙaunar talakawa da kuma tausayin marayu.


"Kar dai yaron nan ɗan gidan SARKIN SHANU ne?" Mama ta jefa wa kanta tambayar a zuciyarta kasancewar ta san alkairin mutumin a bakin jama'a daga shi har tilon matarsa wacce ta rasu kowa ya yi jimamin mutuwarta. Duk da bata taɓa shiga gidan ba amma tana ganin SARKIN SHANUN a kan doki idan ana hawan sallah dan in bata manta bama waccen sallar azumin shi ne ya lashe hawanda aka yi saboda tsaruwa da hawan masa ya yi ga dawakansa ƙosassu wanda aka ƙawatasu da kayan kwalliya na alfarma daga su har mahawan nasu.


"Kenan shi ne ɗan gidan sarkin shanu ɗansa da ake faɗa tilo? Mama ta jefa wa kanta tambayar.


"Dole ka yi tausayi, dole ka yi taimakon, dan ba a ƙasa ka ɗauka ba tabbas hali zane" Mama ta faɗa a z ranta idanunta taɓ da hawayen taimakon da Annur ɗin ya musu, ga kuma gawa a hannunta. Yana gama parking ya fito ya buɗe wa Mama ƙofar ta fito ita kuma Safiyya ta buɗe ɗayan ɓangaren ta fito tana ƙarewa gidan kallo sai lokacin ma ta lura da no motar Annur ɗin mai ɗauke da sunan SARKIN SHANU 3 a jiki.






Mai gadin da wasu a wurin suka shiga masa barka da dawo wa da hannu ya musu alamar amsa wa ya buɗe ƙofar ya ɗauko ledojin da ya siyo wa Safiyya kayan shayi da abubuwan buƙata wanda ya yi niyyar basu idan ya sauke su a gidan dan da ya san ma gidansu zai taho da su ba sai ya tsaya ɓata lokacin siyan komai ba dan akwai komai da za su buƙata. Wani daga cikin mazan da ke zaune a get ɗin ya taso yana yi wa Annur ɗin kirari irin na saraita zai karɓi ledojin amma Annur ɗin ya dakatar da shi ya ɗauka a kansa dan yana ji a ransa cewar babu wanda ya dace ya ɗauki kayan Safiyya sama da shi.
MAI FARAR ƘAFA
(JAHILCI NE)


NA


MAMAN AFRAH


FCW
GAJERAN LABARI
FREE BOOK


Page1️⃣5️⃣➡️1️⃣6️⃣


Tafiya yake su Mama suna biye da shi a baya suka shiga cikin gidan tsaruwa da kyan cikin gidan har ya fi ƙofar gidan ma. Gida ne mai girman gaske ga kyau kamar ma ba a Nigeri'a ba. Can wani ɓangare ya nufa da su ya buɗe ɓangaren ya kai su wani babban falo ya ce su zauna zai je ya ce su shiga zai je ya sanar da Daddynsa, da to Mama kawai ta amsa suka shiga ɓangaren suna ta ƙarewa wajen kallo.






Bayan sun zauna Mama ta kalli Safiyya da ta yi nisa cikin tunani pos ɗinta a kan cinyarta ta ce


"Safiyya kar kike saka damuwa a ranki komai ya same ki a rayuwa ki zama mai fawwala wa ubangiji domin shi ne majiɓancin dukkanin al'amura. Yana sane da dukkan abubuwan da suke faruwa da ke dan haka ki ɗauki hakan a matsayin jarabawa sai dai ki yi fatan Allah ya baki ikon cinye wa. Shi kuma yaron nan dama Allah ne ya baki kuma yanzu ya karɓi kayansa, dan haka ki saka a ranki dama can Allah bai rubuta shi cikin wanda za su shaƙi iskar duniya ba , kuma ko da a a ce ya rayu tsawon lokaci yo akwai ranar fa ubangiji zai karɓi ransa domin alƙawarin Allah ne sai kowace rai ta ɗanɗani mutuwa kowa zaman jiranta yake wanda ya tafi bai yi gagggawa ba wanda ya yi jinkiri shi ma ranar ƙarewar kwanakinsa tana nan zuwa sai dai mu yi fatan cika wa da imani" Mama ta faɗa tana kallon Safiyya da zuwa lokacin hawaye ne suke ta zirya a fuskarta saboda sai ta ji tamkar Mama ta tsokano mata inda yake mata ƙaiƙayi.




"Ba komai Mama dama bawa ba ya wuce ƙaddararsa, sai dai sakin da Baba ya miki ne a dalilina ban ji daɗi ba dom...


"Haba Safiyya yanzu a ringa maimaita magana dai sakin nan fa ba wai laifinki bane kuma ki sani ba ke ce sila ba shi aure da kika ji da gani rai gareshi tamkar mutum shi ma akwai ranar da kwanakinsa za su ƙare dama can Allah ya rubuta cewa yau ne ranar da aurena da mahaifinki zai mutu kuma ko da a ce baki zo gidan ba tun da Allah ya ƙadarta zai sake ni a yau to dole sai ya sakie ni! Shi ya sa a rayuwa za ko ga ma'aurata suna zaune tsawon lokaci kuma suna samun saɓani wata rana ma saɓanin ya zama mai yawa kuma mai rikitarwa, wanda rikitarwasa da kuma ɓacin ran da aka fuskanta sai ki ɗauka a ranar auren nan zai mutu to amma kuma tun da Allah bai ƙaddara mutuwarsa a ranar ba sai ki ga duk girman laifin sun manta sun daidata sun cigaba da zama dama mata da miji sai Allah. Amma wani lokacin kuma sai ki ga wani abu ya gifta wanda bai taka kara ya karya ba, wanda bai kai ya kawo ba amma sai ki ga an kasa haƙuri an kasa jurewa sai ki ga abu ƙalilan ne ya kashe auren wanda an yi ta gumurzu a zaman sama da wanda ya yi sanadin mutuwar auren amma auren bai mutu ba sai a kan abu kalilan wanda za a yi ta cewa a kan abu kaza ya sake ta, to ba haka bane dama ranar Allah ya ƙaddara auren zai mutu dan haka ki daina ɗora wa kan ki laifin mutuwar aurena" Mama ta kai ƙarshen maganar idanunta kafe a kan ƴar tata ganin duk jikin Safiyyar ya yi sanyi.




"Haka ne Mama ba zan ƙara tunanin hakan ba na yarda haka Allah ya ƙaddara"


"Yawwa Safiyyata kar ki damu Allah zai baki miji na gari mai ƙaunarki wanda ba zai taɓa ƙyamatarki ba. Wanda zai yi sanadiyyar shigarki aljanna, saboda kullum na kai goshina ƙasa a matsayina na mahaifiyarki ba na ɗagowa har sai na roƙa miki miji na gari wanda zai riƙe ki amana wanda ba zai taɓa wulaƙanta ki ba tun kina ƙarama nake miki addu'a kuma kin san addu'ar mahaifiya tana da tasiri ƙwarai a kan ƴaƴanta bakin mahaifiya yana da kaifi shi ya sa ake so a koyaushe ya zamana abu mai kyau ne zai fito daga bakin mahaifiya ya zamana addu'ar alkairi ce ga ƴaƴanta ba wai sai a sallah uwa take yi wa ƴaƴanta addu'a ba ko aiki suka mata ko aikensu ta yi sai ta musu fatan alkairi ta musu addu'ar dacewa duniya da lahira. Ta nema musu tsari da mugayen abokai da mugayen ƙawaye ta musu fatan haɗuwa da mutanen kirki wanda za su zame musu farinciki ba wanda za su gurɓata musu tarbiya da rayuwarsu ba ta nema musu samun ilimi mai albarka ke hatta ƙoƙari uwa ce take yi wa ƴaƴanta addu'ar fin sauran ɗaliban ajinsu ƙoƙari da gane karatu hatta position uwa take yi wa ƴaƴanta addu'ar su zo su ne na ɗaya a cikin ajin islamiya da boko.






Dan haka na jajirce wajen miki addu'a tun baki san inda yake miki ciwo ba ke tun kina ƙarama idan na ga kin zo ta biyu a ajinku to na kan ƙara zage dantse wajen dagewa da addu'a har sai na ga kin doke kowa kin zo ta ɗaya kina kawo kyaututtuka gida sannan hankalina yake kwanciya bare ɓangaren addu'ar samun abokin rayuwa na ƙwarai tun kina ƙaramarki mitsitsiya nake miki addu'ar hakan har girmanki dai dai da rana ɗaya ban taɓa fashin faɗa wa ubangiji hakan ba ke ko da ina al'ada (Fashin sallah) Nake to kuwa na kan yi alwala in hau sallaya in yi addu'o ina dan kar wannan rana ta wuce ban faɗa wa ubangiji buƙata ta ba. Ko aiki nake a zuciyata ina miki addu'a da kaina baki ɗaya dan haka ko da na ga kin yi auren farko baki dace ba kin fito ban damu ba haka aurenki na biyu ma, har

Please Login or Register in order to submit comment