Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawo na uku duk na san jarabawa ce ko damuwar da nake shiga a sanadin mutuwar aurenki ina yi ne saboda damuwar da kike samun kan ki a ciki da kuma kalmar da mutane suke jifanki da ita ta MAI FARAR ƘAFA. Sai dai na san akwai lokaci, lokaci zai zo wanda komai zai zama tarihi lokaci zai zo wanda komai zai zama kamar ba a yi ba dan na san iya tsawon rayuwa na miki addu'a kuma na san Allah maji roƙon bayinsa ne sannan a duk lokacin da ɗan adam ya roƙi Allah wata buƙata to kuwa Allah ba ya maido wa bawansa addu'a face ya amsa masa ita ko dai ya samu jinkirin amsuwarta ko kuma addu'ar tashi ta tsaya a sama tana kokawa da wata musiba da za ta afka masa ma'ana addu'arsa tana tare wani abu marar kyau da zai same shi. Dan haka na san ko aure goma za ki yi to akwai wanda za ki aura wata wanda burina zai cika ki samu kwanciyar hankali dan haka ke ma ki kasance cikin yi wa ƴaƴanki addu'a da ke kan ki ma" Mama ta kai ƙarshen maganar tana kallon Safiyya.


"In sha Allahu Mama na gode ƙwarai kuma ina alfahri da kasancewarki mahaifiya a gare ni, kuma uwa ta gari domin kowace uwa mahaifiya ce ce amma ba kowace uwa bace ta gari, uwa ta gari da ban take"
Mama murmushi kawai ta yi sai ta ce






"Ki kira Rabi'u a waya ki sanar masa cewa kin haihu amma ɗan bai zo da rai ba"


"Mama ba lallai ya ɗauki wayata ba saboda da zan taho har gargaɗi ya mini cewar ko kaya za a je ɗauka kar na je masa gida...


"To ai yanzu ba gidansa za ki je ba a waya za ki faɗa masa kin ga kar a binne ɗan bai sani ba kuma daga baya a zo ana A'i ina indo dan zai iya yin ƙaranki ma ya ce ki fito masa da ɗansa ko ya ce kashe masa ɗan kika yi da gangan"


"Yo Mama ai ina da hujjar da zan kare kaina tun da ba a gida na haihu ba a asibiti na haihu ko masu asibitin za su shaideni"


"Haka ne amma dai gwara ki kira shi yanzu maganin kar a yi kar a soma"


"To" Cewar Safiyya tana fito da wayar daga pos ɗinta.






*ANNUR*


Tun da ya kai su Mama ya ajiye ledojin hannunsa ya fito part ɗin Daddy ya nufa yana jin wani nishaɗi a ransa ganin irin tarin baiwar da Allah ya masa a yau na kawo masoyiyarsa abar ƙaunarsa har cikij gidansu lallai yau rana ce da ba zai taɓa mantawa ba a cikin tarihin rayuwarsa domin ko a mafarki bai taɓa kawo hakan ba, kai bai ma taɓa tunanin a kwana kusa zai haɗu da ita ba amma sai gashi cikin hikimar ubangiji komai ya zo masa da sauƙi ko da ya same ta a matsayin matar aure sakakkiya sai ga shi cikin awanni ƙalilan idda ta fita daga kanta.


"Assalamu alaikum" Ya faɗa yana daga bakin ƙofar falon mahaifin nasa yana jiran ya amsa masa kuma ya bashi damar shiga domin koyarwar mahaifiyarsa ce tun yana yaro ƙarami in zai shiga wuri sai ya yi sallama sannan idan aka amsa aka masa iso sai ya shiga.


"Wa alaikumus salam wa rahmatullah, shigo" Ya tsinkayo muryar Daddy daga cikin falon.


A hankali ya ɗaga labule ya kutsa kai cikin falon mahaifin nasa wanda ya ƙawatu ƙwarai da kayan alatu na more rayuwa. Ƙamshin freshner da sanyin AC ya haɗe falon. Zaune Daddyn yake a kan lallausan capet ya ringisa a kan tuntu sanye yake da yadin kufta wanda aka yi wa aikin hannu sai alkyabba marar nauyi wacce ta sha aiki na lafarma carbi ne ɗan dannawa (Counter) Maƙale a yatsan hannunsa na dama sai kuma hoton matarsa abin faharinsa a gefensa a jingine domin a duk lokacin da hoton yake kusa da shi ya kan ji tamkar ita ce a kusa da shi hakan yana rage masa kewar rashinta a tare da shi duk da ganin hoton ba ya rage masa raɗaɗin rashinta a zuciyarsa amma dai ya fi so hoton ya kasance a kusa da shi sai ya ringa jin tamkar dai ita ce domin a lokacin tana raye bata yin nesa da shi ta kan zauna su yi ta hira abinsu cikin so da ƙaunar juna tamkar sabbin amaren da suka tare a satin farko.




Cikin nutsuwa ya ƙarasa wajen mahaifin nasa ya zauna tare da naɗe ƙafafunsa.


"Daddy...


"Annur wani irin abu ne ya faru da kai wanda ya sauya yanayinka gabaɗaya daga mai damuwa zuwa mai annushuwa tun a sallamarka na fahimci kana cikin farinciki a muryarka, yanayin tafiyarka da ka shigo yanzu fa ma zaman da ka yi duj cikin zumuɗi ne na ƙara fahimtar daɗin da ke lulluɓe ɓoye a cikin ranka ta yadda na ga walwala shinfiɗe a fuskarka ka sai wani walwali take tamkar sabon angon da ya dawo daga wajen ɗaurin aurensa" Daddy ya katse masa maganar cikin nuna tsantar farinciki yana son sanin mene ne ya canja shi lokaci guda Annur ɗin da har shi yake bashi umarnin ya fita ya zaga gari dan kawai ya rage damuwar ransa tun mutuwar mahaifiyarsa lokacin ya dawo daga ƙasar Ingila ya kammala karatunsa har yau bai ƙara ganin farinciki a tare da shi ba ya fahimci yana cikin damuwar da ba mutuwar mahaifiyarsa kaɗai bace damuwar tasa, ya fahimci akwai wani gagarumin abu da yake damunsa a zuciyarsa wanda ya ƙi sanar da shi sai dai a yadd ya fahimta ya yi ƙiyasin kamar dai soyayya ce yake fama da ita sai dai kasancewar Annur ɗin ba ma'abocin kula mata bane babu ruwansa da ƴan mata shi ya sa ya watsar da wannan tunanin a ransa amma kuma ya tabbata koma mene ne a yau ya samu warwarewarsa dan ba haka ya fita ba.






"Daddy za mu yi maganar daga baya yanzu baƙi ne na kawo gidan nan wasu mutane ne masu kirki da karamci kuma suna buƙatar taimako na wurin zama shi ne na kawo su gidan nan"


"Ma sha Allah, Annur hasken rai da zuciyata ai babu wani wanda za ka kawo gidan nan kai ko da a ce dabba ce bare kuma mutum ɗan adam mai cike da karamci da martaba da kuma daraja a ƙi karɓarsa dan haka ka kai su masauki ko da shekara nawa za su yi a gidan nan ba za a ƙyamace su ba kai ko da za su rayu a nan ne tsawon rayuwarsa babu wani abu da za su nema su rasa matsawar ina raye kuma kaima kan numfashi sai inda ƙarfinmu ya ƙare wajen taimakon bayin Allah"


"Godiya nake Daddy" Annur ya faɗa farincikinsa ya kasa ɓoyuwa.


"Babu godiya ai yi wa kai ne kuma aikin lada ne matsawar mutum na taimakon mutane masu buƙatar taimako to tabbas ba zai taɓe ba kuma arziƙinsa ba zai gushe yana ƙaruwa ba domin Allah na taimakon masu taimako"


"Haka ne Daddy"


"Maza ne ko mata, ko kuma maza da mata, sun kai kimanin nawa?"


"Mata ne su biyu ne"


"Ikon Allah mata, Allah sarki ashe ma masu rauni ne ka san mata suna da rauni, kuma ma a she su biyu ne basu da yawa ma Allah bamu ikon kyautata musu"


"Amin ya rabb, amma Daddy uwa da ƴa ne kuma daga asibiti muke yanzu ƴar ce ta haihu dama a hanyarsu ta zuwa asibiti na haɗu da su ƴar tana naƙuda shi ne na kaisu asibiti to yanzu dai ɗan bai zo da rai ba shi ne nake so a masa sutura "


"Allahu akbar kabiran ina alfahri da kai ƙwarai saboda taimakonka ga jama'a"


"Daddy ai a wajenku na koya"


"Mu je yanzu na gansu sai ka fita ka sanar da mutane a waje domin a sallace shi"


"To Daddy"


*SAFIYYA*


Tun da ta fara kiran wayar Rabi'u yake katsewa har ta gaji ta ajiye sai Mama ta ce ta ƙara gwada wa ko Allah zai sa ya ɗauka dan Mama ta fi so a sanar da shi cewar ɗansa bai zo duniya da rai ba tun da dai har ya san ta taho da cikinsa to dole ya san halin da ake ciki. Haka Safiyya ta daure ta ƙara kiran nasa har ya katse bai ɗauka ba sai da ta yi sau huɗu a na biyar ɗin ya ɗaga da wata muguwar tdawa da ta sanya Safiyyar razana bata shirya ba kafin ta dawo daga razanar da ta yi ya kawo wata ashariya ya luƙa tamkar ɗan maguzawa.


"Wai uban me zai miki da kika nace da kirana, bayan abin da ya haɗa mu da ke ya raba kuma ko cikin mafarkina bana fatan dake ko haɗa hanya da ke yanzu ma na ɗauka ne dan in miki kashedi a kan kirana da kike to ki sani ni dai na fi ƙarfinki a yanzu domin wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa kuma ina gama wayar nan da ke zan yi blocking ɗinki ke hatta wayar bayar da ita zan yi gudun kar muryarki ta sa wani abunki na FARAR ƘAFA ya shafe ni ko sim ɗin ma zan cigaba da amfani da shi ne saboda customer na da suke da number...


"Ina son sanar da kai ne na haihu kuma ɗan bai zo da rai ba... Cewar Safiyya da ta katse shi daga munanan kalaman da yake faɗa mata domin zuciyarta zafi takw mata in banda ma Mama ta matsa da babu abin da zai sa ta kira wo shi, dai dai tun kan ta kai aya ya katse ta da faɗin.


"Alhamdulillahi! Allah na gode maka da hakan ta faru shikenan ma na huta da baƙar jaraba don haɗa zuri'a da MAI FARAR ƘAFA ba ƙaramin jafa'i bane gwara ma da ɗan bai zo da rai ba shikenan a ja a je an hana tsohuwa shiga mota, ko suturarsa na yafe ba sai na zo ba ku binne shi Allah sa ya ceceni a lahira amma ba zan zo ba in raɓi inda ahalin masu FARAR ƘAFA suke"


MAMAN AFRAH😍
MAI FARAR ƘAFA
(JAHILCI NE)


NA


MAMAN AFRAH


FCW
GAJERAN LABARI
FREE BOOK


Page 1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣


Gabaɗaya jikinta ne ya yi wani irin sanyi zuciyarta ta karaya ta shiga mata wani zugi na maganganun fa yake faɗa mata ta cikin wayar kafin ta samu ƙwarin gwiwar furta komai ya ja wani uban tsaki tare da yanke kiran. Hawaye ne suka shiga malalowa daga idanunta ko wayar ta kasa cire ta daga kunnen nata bare a yi zancen yin magana.




Mama ce ta aro jarumta tare da ƙarfin gwiwa ta ce


"Kar ki damu ai tun da kin faɗa masa kin fita haƙƙinsa, dama ni burina ya san da haihuwar da kuma komawar abin da aka haifar to tun da kin isar da saƙo baki da haƙƙinsa ko a wurin ubangiji kin fita" Cewar Mama tana dake muryarta dan bata so ƴar tata ta fahimci raunin da zuciyarta ta yi na sauraren maganar abin da aka mata ta waya dan akwai volume Mamar tana iya jiyo duk abin da Rabi'un ya ce


"Danne zuciyarta ta yi tare da maida hawayen da ya yi wa idanunta tsinke, ta ce


"Babu komai Mama" Saboda ta ji daɗin yadda mahaifiyarta take kwantar mata da hankali ko ba komai ai soyayya da kulawar mahaifiya sama take da kowa a cikin mutane.


*BAYAN AWANNI BIYU*


Mama, Safiyya, sai kuma Baba Dudu mai aikin gidan SARKIN SHANU su ne zaune a falon lokacin Safiyya har ta yi wanka da ruwan zafin da Baba Dudun ta haɗa mata tana zaune tana cin abincin da Baba Dudu da kuma Mama suka matsa mata. Dan ko Daddy da ya shigo sosai ya yi farinciki da ganinsu domin kana yin tozali da su za ka gane mutane ne masu karamci.


Sannan shi ma Annur ya sake shigowa bayan sun dawo daga maƙabarta ya ƙara jajanta wa Mama tare da yi wa Safiyya sannu da jiki haka ta amsa tana jin kunya saboda kallon da ta lura yana jifanta da shi wanda ta kasa gane takamaiman dalilin yin kallon.


*BAYAN SATI BIYU*


Duk yadda Mama da Safiyya suka so su bar gidan amma Daddy ya hana su dan shi Annur ma daga Mama ta fara masa maganar barin gidan sai ya faɗa wa Daddy, haka Daddy zai yi ta musu nasiha yana jan hankalinsu a kan kar su damu ko su saka wani abu a ransu domin nan gidan babu wani abu da za a musu shamaki za su rayu ne a cikinsa tamkar dama a nan suke tun asali. Ganin hakan sai su Mama suka saki jiki suka zauna suke sabgoginsu ko rayuwarsu ta baya basa tunawa ga komai nan na buƙata babu abin da suka nema suja rasa dan ko aiyuka akwai masu yi da mai girki Baba Dudu dan ko Mama ta ce za ta tayata girkin bata yarda sai ta ce ta sha zamanta ta huta. Kwanci tashi asarar mai rai a haka har Safiyya ta zubar da wanka. Sun yi ƙiba abinsu sun yi kyau sosai jin daɗi da kwanciyar hankali ya bayyana a jikinsu. A haka har Mama ta kammala iddarta.


Zaune yake a mota ya sako ƙafafunsa waje fa yake ƙofar a buɗe take. Ya yi nisa wajen kallon hoton Safiyya wanda ya ɗauketa ba tare da ta sani ba, suna zaune da Mama suna hira ya shiga gaishe da Mama bayan Safiyyar ta gaishe da shi ya amsa yana ɗan danna waya a haka ya saita fuskarta ya ɗauki hoton ba tare da Safiyyar da Mamar sun fahimci ya ɗauka ba. Ya kafe hoton da ido yana zooming kyakkyawar fuskarta ma'abociyar kyau wacce a koyaushe ba ya gajiya da kallonta har kullum ganin Safiyya yake tamkar sabuwar halitta a idanunsa duk da wani lokacin yana ta tunanin ina dangi da ƴan uwansu suke. Duk da cewar har yau Safiyyar bata wani saki jiki da shi ba iyakarsu gaisuwa ko zuwa ya yi ya tarar suna hira da Mama ko da Baba Dudu daga lokacin da ya shigo ɗakin za ta saka wa bakinta linzami ta rufe ruf tamkar ɗakin da aka kulle da ɗankwaɗo. Haka za ta yita sunkuyar da kai idan ma ta ga sun fiya haɗa ido da shi sai ta tashi ta shige ɗaki ta barshi da Mama a falon.


"Ranka ya daɗe ga kukar kaɗin an samo kuma wallahi tana da kyau sosai" Cewar Ibra direban gidan su Annur.


Ɗago kai ya yi daga kallon wayar da yake na ganin hoton Safiyya tare da sauke wata ajiyar zuciya ya kalli Ibra ya ce


"Ka shiga da ita gida ka ce a mini ɗanwaken amma ka faɗa wa Baba Dudu Safiyya ce za ta mini ɗanwaken" Ya faɗa yana kallon Ibra da ya ɗan rissina cikin girmama wa dama ɗanwake ya ce a masa sai Baba Dudu ta ce babu kukar da za a yi shi ne ya aika direban ya siyo a kasuwa.


"To ranka ya daɗe an gama" Cewar Ibra yana juya wa ya shige cikin gidan.








Can kicin ya nufa inda ya san zai samu Baba Dudu. Zaune ya same su da wata wacce bai ga fuskarta ba dan ta bashi baya ne.


"Hajiya Dudu an buga an barki"


Dariya ta yi tana kallon Ibra ta ce


"Aikuwa dai sai dai a barnin"


"Ga wannan in ji yallaɓi ƙarami ya ce amma Safiyya ce za ta masa ɗanwaken"


"To sannunka da ƙoƙari Safiyya lambarki ta fito" Cewar Baba tana dariya ta miƙa wa Safiyya ledar kukar da Ibra ya miƙo mata. Ita Safiyya rasa bakin magana ma ta yi sai kawai ta miƙa hannu biyu ta karɓa tana sakin murmushin yaƙe. Ibra da ke ta son ganin fuskar Safiyya sai kuwa aka yi sa'a ta ɗan juyo a nan ya yi gamdakatar na ganin fuskarta saboda bai san fa zamanta a gidan ba dan ya ɗan yi jinya ne ya daɗe ba ya zuwa aiki.


"Safiyya!" Ya faɗa da mamaki. Juyo wa ta yi gabaɗaya sai ta sauke idanunta a kan fuskar Ibra. Cikin fargaba ta ce


"Na, na, na'am" Har tana inda-inda dan ganin Ibra ya mugun tasar mata da hankali dan ta san shikenan yanzu sai ya yi sanadin barinsu gidan fa suke ganin sun samu kwanciyar hankali har suna mantawa ma da wani abu wai shi ɓacin rai ko baƙinciki na jifansu da magana da jama' a dan tun da suna samun komai na buƙata babu inda suke zuwa ko nan da can bare Safiyya dama bata da yawo ko da na gidan ƙawaye ne bare kuma da mutane suka canfa cewar ita MAI FARAR ƘAFA ce sai kowa yake gudunta ita ma kuwa sai ta daina zuwa wajen kowa bare ma har a wulaƙantata.


"To iko sai lillahi! Wato dama a nan gidan kike ake ta raɗe-raɗin...


"Ibra dakata dan Allah! Ni fa ban tambayeka koma mene ne ba dan haka duk wasu maganganunka ka riƙe kayanka" Safiyya ta faɗa tana ɗaukan ledar kukar ta tafi cikin kicin ɗin dan yin ɗan waken dan ta san Ibra tauraruwa mai wutsiya ne ganinsa ba alkairi bane.


"Baba Dudu wai ko dalilinki ta zo gidan nan? Shin ta daɗe ne a nan gidan ko yanzu ta zo har na ji yallaɓi Annur na cewa a bata ta masa ɗanwake, ko dai ita ma aiki aka ɗauketa" Ya faɗa yana wani ɗaga wuya dan ya hango Safiyya da ta shige kicin yana wani waiwaye-waiwaye kamar marar gaskiya.


"Ibra ka je ka tambayi masu gidan ni ma dai ai ka san aiki nake a gidan nan tun da kana buƙatar a maka ƙarin bayani sai ka tuntuɓi masu gida tun da dai ka san babu zai shiga gidan mutum ba tare da mai gidan ya sani ba" Baba ta faɗa tana ɗaure fuska dan dama ta san Ibra da shegen gulmar tsiya kuma tun da dai har ta ga Safiyya ta ɗaure fuska kuma ta nuna bata buƙatar yin magana da shi to tabbas akwai wata gulmar da yake son aiwatarwa duk da ita bata ga wani aibi a kan Safiyyar da mahaifiyarta ba , amma ɗan adam tara yake bai cika goma ba.


Ganin Baba ta yi banza da shi ya juya yana waiwaye har yana yin tuntuɓen da ya nemi faɗuwa.


*SAFIYYA*


Tun da ta yi ido huɗu da Ibra gabanta yake faɗuwa dan ta san idan har Ibra ya yi wa masu gidan bayanin wacece ita to tabbas za a kore su daga gidan kuma bata san inda za su je ba. Dan Ibra unguwarsu ɗaya da shi babu abin da bai sani a kanta ba game da jifanta da ake na cewar ita MAI FARAR ƘAFA ce. A haka ta yi ɗanwaken cikin sanyin jiki fa saƙe-saƙe har ta gama ta sanya masa a foodflaks ta masa miyar jajjage dan da miya yake ci ba ya ci da yaji. A kicin ɗin ta bar masa dan ta san Baba za ta saka a kai masa part ɗinsa, fitowa ta yi daga kicin ɗin amma sai ta tarar Baba Dudu ta tashi daga wajen tunaninta ko ta tafi ɗakinta ne dan a gidan take kwacakam da zama tana aiki.


Ɓangarensu ra nufa dama ta fito wajen Babar ne dan ta ɗan huta da zaman ɗakin sai ta bar Mama tana kallo. Da sallama ta shiga falon Mama ta amsa mata da kallo Mama ke binta ganin ta sauya jikinta sanyi ƙalaw ba kamar lokacin da ta fita ba.


"Safiyya lafiya dai na ganki haka?" Mama ta jefa mata tambayar. Shiru ta ɗan yi da ba za ta faɗa wa Mama ba dan kar hankalinta ya tashi sai kuma ta yi tunanin gwara dai ta faɗa mata dan idan ta san da maganar ko da an kore su abin ba zai ɗaga hankalinta ba duk da ta san mahaifiyarta jarumar uwa ce tana tunkarar matsalar da ta tunkarota a koyaushe.


"Ki faɗa mini mana kar ki manta baki da wacce ta fini a rayuwa ni ma kuma haka to mai za ki ɓoye mini Safiyya"


"Mama Ibra ne ya ganni a gidan nan"


"To sai aka yi yaya?"


"Mama ina ga fa aiki yake a gidan nan kuma kin san shi da gulma saboda shi faɗi ba a tambayeka bane, yanzu na san dakyar ne in bai faɗa wa masu gidan cewar ni MAI FARAR ƘAFA bace"


"To mene ne na damuwa? Kowane lamari fa Allah ake miƙa wa, kuma nan ɗin ma ba yin kanmu bane Allah ne ya sa masu gidan suka amincw da mu har suka yarda muka zauna musu a gida to haka in suka koremu Allah ba zai hana mu wani wajen da za mu zauna ba dan mutum komai yake ya saka Allah to kuwa Allah zai zame masa jagora!"






"Haka ne Mama"


"To ki kwantar da hankalinki komai muƙaddari ne daga Allah, ko yanzu aka zo aka ce mu tafi kar ko ɗaga hankalinki ai duniya da faɗi maye ba ya ci kansa ba"


"To Allah iya mana"


"Amin Safiyyata"


Murmushi kawai Safiyyar ta yi.



*IBRA*


Ƙafafunsa har wani wani rawa-rawa suke tsabar sauri da yake yana son ya je ya barbaɗa wa Annur gulmar wacece Safiyya dan ya san duk wanda ya san cewa ita MAI FARAR ƘAFA ce ba zai bari ta raɓe shi ba.


"Taɓ MAI FARAR ƘAFA a gidan SARKIN SHANU yo wannan kwana kaɗan ya rage duk wannan ɗinbin dukiyar da kuka tara sunanta ƘURMUS dan duk inda MAI FARAR ƘAFA ta raɓa sai komai ya lalace"Cewar Ibra a ransa bakinsa har wani mutsu-mutsu yake na son faɗin gulma da ɗumi-ɗumi.




Yana fitowa sai ya ga Annur a kan mota a zaune amma lokacin ba wai waya yake latswa ba carbinsa na dannawa yake dannawa.


"Ranka ya daɗe an isar da saƙon" Cewar Ibra yana ɗab rusunawa idanunsa kafe a kan fuskar Annur ɗin dan yana so ya ga fuskar da zai faɗa masa abin da ke ci masa tuwo a ƙwarya wanda ya gani yanzu, dan yana ganin idan har ya ɓoye kamar bai riƙe alƙawari ba ya ci amanar zaman tare. Ganin Annur ɗin ya tsare gida dan ko maganar ma bai amsa masa ba kawai hannu ya ɗaga masa.


"To fa! Yallaɓai sarautar ta motsa ya wani haɗe rai gashi ni kuma ina son faɗa masa akwai MAI FARAR ƘAFA a cikin gidansu.


"Am,um ranka ya daɗe dama akwai magana da nake son faɗa maka" Cewar Ibra a ɗan ɗarare yana kallonsa.


"Ibra ba na son damu ka yi abin da ke gabanka ni ma ina da abin yi"


"Yallaɓai wallahi tallahi maganar tana da matuƙar muhimmanci matuƙar ban faɗa maka ba hankalina ba zai kwanta ba gani nake kamar ma na ci amana ne f...


"Ibra! Ka faɗi abin da ya kawo akwai abin da nake yi ne tun da har ka ji na bafa uzurina amma tun da har ka faɗi hakan ka gaggauta faɗa mini domin in cigaba da abin da ke gabana" Cewar Annur da bai so ya katse azkar ɗin da yake ba domin azkar ne da yake na neman Allah ya bashi ikon furta wa masoyiyarsa Safiyya kalmar so tare da dacewar ya samu ta amsa masa ta karɓi tayin da zuciyarsa za ta yi wa tata zuciyar dan ba ya fatan ta watsa masa ƙasa a ido ta hanyar ƙin karɓar kalmar so daga gare shi idan har haka ta kasance bai san makomar damuwarsa ba zai rayu ne cikin damuwa da ƙuncin zuciya saboda ya yi nisa ya yi nutso a cikin kogin sont d ƙaunarta wanda ba ya jin akwai wata mace da za ta samu kwatankwacin irin ƙaunar da yake yi wa Safiyya daga wani ɗa namijin dan shi ita kaɗai ce a zuciyarsa kuma da ita kaɗai yake

Please Login or Register in order to submit comment