Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inda baki gane ba saiki tambayeni jeki ina nan ina jiranki.''


Jikina a sanyaye na mike duk da cewa d'azu sai da na leka ko'ina. Yana nan zaune na dawo yace min.


"Akwai matsala?'' Muryata tayi laushin dole sabida kuka nace.


''Eh akwai kayan da ban san yanda zanyi amfani dasu ba a kitchen d'in.'' Mikewa yayi tare da cewa.


''Muje ki dai yi hakuri Haidar beda uwa ne agidan na san da itace zata zama madadina, to kinga bata nan dole nine zan tsaya miki ko gobe kadda kijira a kawo miki abinci kiyi abinki da kanki akwai komai na buk'ata sannan koda wata ta kawo miki abinci ban yarda kici ba kinji ko? kome kikeso ni zaki nema insha Allah zuwa jibi kingama hutawa zamu yi wata muhimmiyar magana dake.''

Kaina nakuma sunkuyarwa kasa ba tare da nayi magana ba.


"Kidinga min magana Ruma ki d'auke ni amatsayin mahaifinki kinji ba siriki ba domin nima matsayin d'iya na d'aukeki kinji?" Cikin jin kunya nace.


''Toh.'' Yafe min.


"Yauwa ki dinga kirana da Abba sabida mijin kima haka yake ce min kinji ko?''


"To.'' Itace kalmar dana kuma amsawa da ita, gabaki d'aya wata irin soyayyar dattijon ce ta kamani domin gaskiya yana da kirki sosai ga kamala.


Da kanshi ya nuna min komai harma sai da yasa na gwada had'a tea sannan ya ajiye min ledar dake hannunshi ya kunna min TV sannan yayi min sai da safe ya tafi.


Wani tsalle nayi na antaya kan gadon ina murna bayan na cika cikina da naman kazar daya ajiye min.


''Oh ikon Allah wai yau nice cikin wannan daular?''


Sai da na shiga bedrooms d'innan duka wai zab'en wanda zan kwana a ciki, duk shegen tsoron da nakeji haka nayi kwanciyata bayan nayi sallar godiya ga Allah tare da tarin addu'a wadda har sai da narasa mema zance.


*****


Zaku yi matukar mamakin yanda na tashi domin sai mutum ya rantse bani bace jiya aka kawo ina ta koke-koke ba. Tunda nayi sallah da asuba ban koma ba to dama ban saba komawa d'inba, saina d'ora da karatun alkur'ani mai girma har sai da gari ya waye sannan na jiye tare da nad'e sallayar da hijab din jikina na gyare d'akin tsab na saka turaren da nagani birjik a saman madubi sannan na koma parlour, nan ma sai da na share na kakkabe na goge sannan na shiga kitchen ina tunanin mai zan dafa musamman dana lek'a store d'in na ganshi shake da kayan cima kala-kala ammafa duk na 'yan gayu ne.

Ruwan tea na dafa sai kwai dana soya saina d'auki biredi na koma can wani d'an keb'antaccen waje da aka malaleshi da wani kafet mai kyawun gaske dama an tanaji wajen ne domin cin abinci kamar yadda Abba ya gaya min jiya.

Shigewa bedroom nayi, wanka nsyi sannan na gyara jikina hoda kawai na shafa amma ko kwalli ban saba, danni dama kwalliya bawai damuna tayi ba.


Karfe goma da wasu mintina na gama karyawa sai lokacin naji an kwankwasamin kofa. Mayafi na d'ora saman doguwar rigar dake jikina na nufi k'ofar. Kallon sama da kasa tayi min kafin tace.


"Kece amaryar?''

A kunyace na d'aga kaina ba tare dana bari mun kuma had'a ido ba, domin ban san wacece ita ba sannan na lura daga ganin kallon da take yi min inaga banyi mita ba.


Zama tayi bayan na gaisheta taci gaba da karewa falon kallo tana yatsina fuska. Lallaikam alhaji ashe uban kud'i ya kashema wajennan shi yasa ya hanamu mu shigo ko gani muyi lallai ma.

"Sunana hajiya Saude nice uwar gidan Alhaji ina yi miki barka da shigowa wannan gidan, sannan ina yi miki jaje na auran mahaukaci da kika yi.''

Binta nayi da kallo yayin da zuciyata taci gaba da wani irin bugu ban san lokacin da ta karasa ficewaba, sabida tunanin da yasha kaina. Ina nan jigum dani duk wani karfin gwiwa ta ya gudu, saiga Abba ya shigo bansan lokacin da na mike na nufeshi ba sabida fargaba.


Ganin yanda na taso cike da damuwa yasa shi jin jikinshi yayi sanyi domin ba haka yaso ba, yaso ya taddani cikin walwala. Zama yayi ni kuma na zauna wajan k'afafunshi ina gaida shi tun kafin ya gama amsawa na d'ora da tambayarshi.


''Abba wai mahaukaci nake aure?'' Idanunshi ya rantse kamin ya kalleni.


"Ki kwantar da hankalinki Rumana yanzu zan baki labarin komai, amma ina so dan Allah kiyi min uzuri tare dajin tausayina kadda kiyi fishi sannan kadda kik'i yadda da kaddara kinji ko?''


Idona harya cika da hawaye na san shikenan tawa ta kare daga yanda yake maganar nan na san cewa gaskiya matar nan ta fad'a.


"Kamar yadda kika sani sunana Alhaji Yusuf ni haifaffen garin bakori ne amma bayan na gama karatuna saina koma garin katsina na cigaba da aiki. Nafara aiki da shekara biyu mahaifina ya rasu dama kuma mun dad'e da rasa mahaifiyarmu domin ta rasu ne tun bani da wayau. Dagani sai yayana Alhaji Yahaya iyayen mu suka haifa amma muna da dangi sosai babu laifi. Bayan rasuwar baban mu sai yayana ya tilastamin yin aure sabida yace shi dai hankalin shi be kwantaba da in zauna jiran sai nayi gidana na kaina, nufinshi na kawota nan bakori kamin na mallaki muhalli a nan katsinan. Saudatu itace matata ta farko kanwar wani abokina ce da mukayi karatu tare, na aureta tun bata gama mallakar hankalin kantaba, sai dai tunda na aureta ko b'atan wata bata tab'a yi ba, tsawon shekara shida sai yayana yace na kuma yin wani auren,

''Saina nemi auran Saratu nan da nan aka bani domin alokacin ina da muhallina a cikin katsina sannan ina da kudina danni ban yarda da aikin gwamnatiba kawai, ina had'awa da kasuwancina. Itama Saratu duk hakan take domin shekara hudu itama shiru ba haihuwa sai hankalina ya fara tashi sabida tuni na fara tunanin matsalar daga jikina take kila nine bana haihuwar gashi zullumi ya hanani zuwa ganin likita sabida ina jin tsoron abinda za'a ce min,

''Ban hakura ba saina auri Bilkisu itama dai shiru, banyi niyyar yin wani auren ba daga mata uku din nan sai dai a ranar danaga Fatima naji idan ban aure ta ba har mutuwa zan iyayi, Nasha wahala sosai kafin na samu iyayenta subani ita domin sunce baza suba me mata har uku 'yarsu ba haka kawai aje a nakasa musu yarinya tunda yanzu ba wani tsoron Allah ake jiba. Amma na jajirce na like har sai da suka gamsu da kalar son da nake mata sannan suka amince min na aureta. Matana sun nuna b'acin ransu sosai da wannan auran musamman da suka ganta yarinya ce sosai kuma a lokacin duk ta fisu ilmin addini dana boko.''

Numfasawa yayi kafin yaci gaba, nima zamana na gyara tare da kuma bud'e kunnuwana domin na fahimce sosai yaci gaba da cewa.


"Ina son Fatima sosai domin tana da matukar tarbiyya a zaman da muka yi bazan ce ga ranar da ta sab'a min ba, saima nine wani lokacin idan aka kawo zugarta tai kaza zanyi mata fad'a koda batai laifin ba. Kwatsam sai Fatima ta fara laulayi bayan watanni takwas da auren mu. Babu wanda ya kawo mata cewa ciki ne domin ni a lokacin na riga na saddak'ar da cewa lallai bana haihuwa. Tsabar sa ido na hajiya Saude yasa ta fahimci akwai matsala domin ni dai ban sani ba wata rana ina kwance cikin d'akina sai gata ta shigo, zama tayi kusa dani tace.


''Alhaji wai kakai matar ka asibiti kuwa?'' Ba tare da na bata wata kulawa ba nace.


''Ban kai taba amma tace min ita taje.''


"To katashi kaje ka bincika idan ba haka ba kakusa d'aukar shege a hannunka tunda kowa yasan baka haihuwa ita kuma ai laulayi take yi.''


Ban san lokacin da nakai d'akin Fatima ba a lokacin, aikuwa saina tarar da ita tana ta amai duk ta galabaita, ban yadda cewa Fatima zata iya cin amanata ba domin koda na aureta budurwa na sameta sannan suna da duki ya dai-dai bakin gwargwado bare nace kwadayi zaisa tayi min haka. Da kaina na taya ta tagyra jikinta sannan nace muje asibiti. Likita ne ya tabbatar min da cewa ciki ne da ita na wata uku.


A wannan lokacin rasa abinda zanyi nayi shin farin ciki zanyi ko kuwa bakin ciki. Yayinda ita Fatiman naji ta saka ihu harda birgima ita wallahi ba ta son cikin ya za'ai ace duk cikin matana babu wacce naiwa ciki sai ita, ita wallahi sai dai azubar dashi. Na shiga tashin hankalin jin kalamanta wanda yasani fallamata mari sai dai kuma tana kukan najawota jikina na rungume sabida tunanin da gaskiyarta fa kuma dole ta shiga damuwa.

Bayani naima likitan tun daga farko har karshe yayi min tambayoyi sannan yace zai min awo. Gado aka bata domin ta huta nikuma a lokacin naga likita, sai dai iyakar binciken su sun gaya min cewa iyakar kwan haihuwata guda d'aya ne kacal kuma na fitar dashi akan Fatima.


Kusan ban yadda da maganar su ba saina shirya mana tafiya nida Fatima a wannan lokacin zuwa India, nanma maganar d'aya ce domin har cikin Fatima sai da suka bincika min cewar lallai cikin nawa ne kumama namiji ne jinana ne. Saudiyya muka wuce nan ma saida suka gama binciken su amma duk maganar d'aya ce dan haka anan na zauna nayi addu'a-nayi addu'a tare da nuna godiya ta ga Allah. A lokacin jinake babu abinda nake kauna sama da Fatima da abinda ke cikinta.


Matana sune suka fara sheganta min yaro sabida suna ganin aisu basu haihu ba sun manta cewa Allah shine mai tsara komai kuma a sanda yaso. Sai da mukai masifa dasu harma nayiwa Bilkisu saki d'aya sannan suka saduda suka bari alokacin ne nayi musu bayanin duk abinda ke faruwa tare da musu bayanan da likita yayi min a lokacinma harna basu zabi cewa duk wacce ke bukatar haihuwa to tayi min magana na sallameta sabida kadda na shiga hakkin su. Amma sai suka nuna zasu ci gaba da zama dani.


A lokacin da aka haifi Haidar kowa sai ya kara tabbatarwa da cewa lallai yaron jinina ne domin beyi kama da maman shi ba dani yayi kama kamar nayi kaki sai dai ya dauko farar fatar mamarshi domin tafini fari nesa ba kusa ba. Nasami haihuwa Ruma a lokacin da na fidda rai da samu shi yasa nayi shagali iyakar shagali sannan na saki kudi sosai aka yi taron suna.


To nidai bazance ga abinda ya dinga faruwa ba a tasowar Haidar sai dai dole tasa na kai Fatima wani gidana sabida a lokacin tace in dai ban raba musu gida ba to wallahi gidan su zata tafi, gashi nayi-nayi ta gaya min menene matsalar amma taki, dole na kaita wani k'aramin gidana. A nan Haidar ya taso ba sai nace komai ba akan kulawar da yake samu sabida ban had'a sonshi da komai ba. Shekaran shi goma na fitar dashi waje karatu, sai dai dawowar shi ne mummunar kaddarar nan ta afku.''














*MAMAN KHADY*🙇🏻‍♀
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: 💞💞💞 *RUMANA* 💞💞💞


Na


*MAMAN KHADY*🙇🏻‍♀
(Mk)


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert and perfect writer's)




Page 6






Kai tsaye b'angaren sauran abokan zamanta ta nufa hankali a tashe, razana tayi sosai lokacin da taga babu kowa a babban falon. Wayarta ta jawo ta danna musu kira d'aya bayan d'aya akan gatanan a babba falo tana jiransu. Mata ne mugayen mata suna da tsananin kishi tsakanin su amma sai suka had'ewa mahaifiyar Haidar kai, har sai da sukai yanda suka yi suka rabata da gidan bayan sun nakasa mata yaro.

Sunayin tarayya wajan ganin sun ruguza shi Haidar d'in gaba d'aya wannan dalilin ne yasa lokuta da dama suke danne kishin su, ammafa ko wacce cikin zuciyarta akwai wani mugun nufi dake makale wanda inda ko wacce zata samu dama tofa sai inda karfinta ya kare, amma a haka bazaka tab'a ganewaba domin ko wacce ta iya takunta.


D'aya bayan d'aya suka dinga shigowa cikin parlourn ko wacce taci gayunta sai kamshi ke tashi kai baka ce akwai wani mugun nufi a cikin zukatan suba. Hajiya bilkisu ta dai-daita nutsuwarta hanci a sama tace.


''Kun kuwa san meke shirin faruwa cikin a gidan nan?'' Hajiya saratu ta yatsina fuska tare da cewa.


"Babu abinda muka sani Bilki sai dai idan ke zaki gaya mana yanzu.''


"To akwai matsala babba ba k'arama ba domin kuwa alhaji na nan yana shirin yiwa Haidar aure wanda bamu san wace kala yarinyar zai auro mishi ba.''


Duk cikinsu babu wacce maganar bata doketaba amma da yake 'yan duniya ne babu wacce ta nuna, Saima hajiya Saude ce da tayi murmushi tace.


''Lallai daga gani makwad'ait ne idan ba haka ba waye zai ba mahaukaci d'iyarshi? kai bama haka ba anya ansan ya Haidar d'in yake kuwa da zasu bashi auran 'yarsu? kodai rufa-rufa aka yiwa iyayenta?''

Nanfa sukai shiru bayan sun tsayar da magana d'aya cewar duk wacce ta samu dama to lallai ta bugi cikin alhajin har sai ya fad'i gidan su yarinyar ta yanda zasuje su kashe maganar domin suna so su tona abinda shi alhajin ya rufe kowa yasan babu wani me hankali da zai d'auki d'iyar shi ya dankawa mahaukaci ita, kai ina bama zai yiwu ba.


*****


Bayan sati d'aya. A ranar muka dawo BAKORI bayan na gama zagaye dangina na uwa dana uba sunata nanata min sai sunzo biki insha Allah. Ni dai iyakata ido da murmushi domin gani nake yi kamar labari ne na kanzon kurege.

Aranar da muka dawo aranar alhaji Yahaya yazo gidan mu ya kuma ce wajena kawai yazo yana son magana dani. Rashin sabo tsakanin mu yasa duk hankalina ya tashi inna da kanta takai mishi tabarma har zaure sannan ta dawo gida bayan sun gaisa. Ban yarda na kalleshi ba a haka muka gaisa dashi sabida kunya inda ya fara da ce min.


"To Alhamdulillah *RUMANA* na san cewa babu wanda ya tuntub'e ki domin jin ta bakinki akan kina son auran Haidar ko bakya son shi, sabida ana ganin an isa dake. Toh nima ba tambayarki zanyi ba Rumana sai dai nayi miki godiya da amincewar da kika yi domin yin wannan jihadi, insha Allahu nasan zuwa gaba zakiji dad'i sannan zaki yi alfahari da hakan ina fatan Allah yai mana jagora kuma ya shigemana gaba a cikin wannan lamarin.''


Kaina a kasa na amsa da 'amin' ba tare dana bari ya jiba.


"Ga wannan waya ce Yusufa yace a baki ko zaku dinga gaisawa tsakaninku dashi, sannan dan Allah kadda kidamu da rashin ganin mijinki a yanzu domin sainan da watanni biyar zai dawo, ke kuma kinga yanzu saura satittika ya rage ayi bikin ku, zan turo miki Usman na wajena ai na san kin sanshi, to abokin shi Haidar d'in ne saiku dinga aiwatar da komai dashi na hidimar bikin kinji ko? Koda kina bukatar wani abun shi zakiwa magana kin fahimceni ko?''


Kaina a kasa nace ''Ehh nagode Allah ya saka da alkhairi.''


Komawa nayi cikin gida jikina duk ya gama yin sanyi, jinai kawai hankalina be kwanta da wanda zan aura din ba to inba haka ba shi ace zamu gaisa din dashi mana amma sai ace da mahaifinsa zamu yi, gaskiya nifa dama can bana kaunar na auri wanda baya sona sabida idan namiji baya sonka wallahi komai zai iyayi dan ganin ya wulakantaka, bare shi wannan daga yanda naga labarinshi kudi sun gama bud'e mishi idanu, wai tsaya ma wani kalane shi mijin da zan aura..? Tambayar da bata da amsa a yanzu kenan.


******


''Alhaji kayi hakuri kamar yadda na gaya maka a wancan lokacin kaki yadda to yauma daka dawo maganar zan nanata maka, yaronka kwakwalwar shi lafiya lau take, sannan bashi da wata lalura mai alama da tabin hankali, kawai dai an kauce hanya ne aka had'ashi da mugayen aljanu wad'anda suke zuwa suna bidirinsu ajikin shi wani lokacin, shine zakaga ya koma kamar mahaukaci amma sam ba mahaukaci bane. A tun lokacin da nayi maka wannan bayanin idan da ka amince inaga da yanzu Allah ya bashi lafiya domin Allah zamu rok'a kuma shine zai yi maganin komai, Amma lokacin saika nuna kai a'a ba zai yiwu ba sabida kana tunanin baka nufin kowa da sharri dan haka babu wanda zai nufeka dashi ko? To yanzu ba k'aramin kuskure bane, dan wanima bakasan shi ba amma yana nan yana neman hanyar da zai cutar dakai balle kuma wanda kasani kuma yake jikinka, Bawai ina nufin wani naka bane yaiwa yaronka wannan sharrin a'a kawai dai inaso in nuna maka cewa k'addarar Allah yawa ne da ita sannan zakaga komai yana da sila da sanadi yanzu dai fatan mu Allah ya shige mana gaba ya kawowa yaron nan sauki.''


Muskutawa yayi kafin yace. ''Amin ya Allah, nagode malam to yanzu wane mataki ya kamata afara bi?''

''Yauwa to maganar danake son ji kenan daga bakin ka, yanzu abinda ya kamata anan shine da farko dai za'a fara da almajirai yara ayi sauka ta alkur'ani sau d'aya, sannan za'a bawa mabuk'ata sadaka, Sai a fara bashi rubutu na sha da shafawa insha Allah wata rana sai labari. Sannan bayanin dakai min na auran da zaka yi mishi shima wannan naji dad'i kuma nayi farin ciki domin indai ita matar tashi ta fahimci lalurar tashi to lallai ko maganin zaifi tafiya yanda ya kamata ajikin shi, Amma ka daina maganar sha'awarshi eh gaskiya ne yana da yawan bukatar mace kuma koda bakin shi yasha gaya maka amman yanzu ma da lalaurar ta kamashi su aljanun basu tab'a mishi wannan b'angaren sha'awar tashi ba shi yasa take tashi lokaci zuwa lokaci amma dan Allah kadda kaba da kofar da zai kusanci yarinyar mutane alhalin baya cikin hayyacin shi dan lallai za'a iya samin matsala wacce bama fata.''


Kuma numfasawa alhaji Yusuf yayi jiyake jikin shi kamar anyi mshi duka sabida tashin hankali shi kam duk wanda ya yiwa Haidar haka bazai tab'a yafe mishi ba idan kuwa zai ganshi kila sai ya zama ajalin shi. Sallama yayi akan sai ya dawo sai a fara abinda ya dace ammafa har lokacin tunani yake anya kuwa gaske ne wani ne zai kauce hanya domin ya cutar da d'an uwansa musulmi?


Jiki a sanyaye ya koma gida ko b'angaren shi bai nufa ba sai dai ya fara nufar na Haidai d'in. Kwance yake yana bacci, shi kuma Mudi na saman kanshi yana ragemai sumar kanshi a hankali gudun kadda ya tashi yayi ta borin daya saba.

Zama yayi ragwaf tare da d'agawa Mudi hannu wanda yake gaidashi, Lumshe idanunshi yayi yana tunani wanda yanzu ya zame mishi jiki.

Yana zaune yana kallon Mudi har k'umba sai da ya rage mishi sannan ya gyara mishi sajen shi nan da nan fuskarshi tai wani fayau kai baka ce yana da wata lalurar ba.


"Mudi aure zan yiwa Haidar.'' Cewar alhaji Yusuf yana kallon yanayin Mudin, cikin washe baki yace.


''Kai alhamdulillah alhaji hakan yayi kyau wallahi Allah ya bashi ta gari wacce zata kula dashi tsakaninta da Allah.''


Bayan sati shida.Zuwa wannan lokacin gidanmu ya kacame da hidima sabida karatowar biki. Zaune nake inna tana ta lailayemin jikina da lalle dagani sai wata bak'ar bes a jikina, inna da kanta ta siyota a kasuwa sabida wannan aikin da take mim. Kirjina na kalla wanda yayi wani cirko-cirko kasancewa babu bra a jikina, har kirjin nawama be tsira ba tunda bani takeyi tace na shafa idan tagama.

Fatata ta canza sosai wani uban laushi da santsi takeyi sannan ga kamshi domin akwai wata madarar turare da ake zubawa cikin kwabin lallan yanzu wajan wata daya kenan dafara yi min wannan gyaran ammafa na canza nayi kyau ta yadda daka ganni zaka san cewar ni din amarya ce.

"Dan Allah duk gyaran nan da nake miki ki daure idan anyi auran nan kiciga ba da yi domin wallahi ba k'aramin temakawa jiki yake yiba, kune dai yaran zamani da sai kuce ku dole sai kayan shafe-shafe shi yasa da an kwana biyu sai jiki ya jeme ya lalace.'' Ban kalleta ba nace.


''Toh inna.''


Shigowar dije da wasu k'awayenmu yasa inna barin d'akin mukuma mukaci gaba da shirya yanda za'a yi duk da dai ni ina zaune iya kaci na dasu kallo.


Usman shine wanda yayi ruwa yayi tsaki wajan ganin komai ya tafi dai-dai an shirya walima kadai kamar yadda mahaifin ango ya tsara sannan aka bani wadatattun kud'i koda zan buk'ata lefena kwananshi hudu da kawowa babu abinda babu akwatina shida masu shegen kyau da tsada sannan ga uwa uba kayan da aka zuba a ciki.

K'awayena sunata tayani murna tare da nanata suma Allah ya mai dasu kamar ni, Ni kam jinsu kawai nake yi domin ina cikin wani yanayi wanda ni kaina bazan ce ga kalarshi ba......
















*MAMAN KHADY.*🙇🏻‍♀
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 16






Zaune nake ina tilawar alkur'ani me girma shikuma yana gefena yai zugudun saikace mai tunanin wani abu.


Inuwa kawai nagani saman kaina,Kusan atsorace na dako kaina aiko wata mace nagani tsaye saman kaina tana taunar cingam tare da wani girgije girgije saikace karuwa agefen titi.
"Wani miyau na hadiye kamin ince sannu da zuwa ki zauna mana.


Wani kallon banza taimin kamin tace" Ke dallah dakata kekuma awa da zakice in zauna ko kina tunanin wani matsayi gareki?


Da mamaki nake kallonta,Kamin ince ikon Allah to Dan Allah kadda ki zauna kiyita tsayuwa.
Sabida raina tuni yafara baci dama wani lokacin fadane dani balle wannan ko sallama bataiminba kuma Dan iskanci naimata tayin wajan zama zata nunamin itama wata shegiyace.
Hannun haidar nakama na kaishi daki sannan nai zamana acan Dan banga amfanin dawowata falon ba.


Bansan ya akaiba saidai naji banbamin masifa natashi acikin falon,Mamaki da tsoro ya hanani ko motsin kirki Saida naji ana kwalamin kira da cewa ke matar mahaukaci kina ina fito.


Hijab dina na d'auka nasa sannan nafita.
Uwargidan Abba ce tsaye da wannan me zubin 'yan duniyar.
Duk'awa nai tare da cewa hajiya ina yini?


Wata shegiyar harara ta sakarmin kamin tace"Dallah can matsa bani guri algunguma kawai ubanme k'anwata taimiki kika zageta?


Idona waje na furta zagi kuma?Wallahi hajiya ban zagetaba itacema tashigo ko sallama bataima tana gayamin maganganu shine sai nikuma natashi nabata wuri dama ko zama bataiba.
"Mitsw aikin banza to Dallah dama ancemiki zama tazo to bari kiji wannan itace nafeesa wadda haidar zai aura kamin yazama mahaukaci kuma koyau ya warke itace matarshi nasan kedai kozai mutu bazai zauna dakeba domin yafi karfinki garama ki kama kanki ankawokine domin ki wahalamishi kamin yaji sauki ya sallameki wawuya kawai,Kenan har wata mace ce?


Hawaye share share idanuna nakebata hakuri yayinda zuciyata nakejin kamar zatayo waje tsabar tafarfasar da takeyi.
Saida tagama masifarta ta zagemin iyaye tas tare da kirana da kwadayayya sannan sukabar falon.


Kuka nacigaba dayi sosai hadda sheshsheka saiga Harun ya shigo.

" Subhanillahi Amarya meya faru?


Muryata ashake nace wallahi wannan hajiyarce tazo da kanwarta wai wacce zata auri ya haidar shine suka zagemin iyaye wa inda basusan me akeyiba.


"Kanshi ya dafe kamin yace ammadai kinban haushi wallahi shine kika tsaya kina kuka bakici uban shegu ba?Toma tsaya idan ita hajiyar kin ragamata shikenan sai itama wannan Mara kunyar ki kyaleta?
To bari kiji wallahi kinji na rantse matukar kuka zaki dinga musu to ki tabbata kwanan nan hawan jini zaikamaki domin ta dinga shigomiki kenan tunda dama takanzo idan sunyi hutun makaranta kuma tana dadewa danhaka ki kankaroma kanki mutunci tunkamin dare yaimiki.
Ina mutumin nawa? Yaya kike ganin jikin nashi?

" Alhamdulillahi da sauki sosai gaskiya domin komai yafara sauki.


"To Alhamdulillahi ai haka akeso yanzu abinda yai saura shine kiyi k'okarin ganin umma ta dawo k'asar nan kema hankalinki nasan saiyafi kwanciya.


Haidar ne ya fito da cup ahannu da kallo duk mukabishi Sabida ganin abinda zaiyi.
Yana zuwa saitina ya

Please Login or Register in order to submit comment