Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

temakamin nima yau infita gari Dan Allah.


"Kinga rumanaa banason Neman fitini fa! Taya zakice zaki fita alhalin kinsan bawata lafiyar kirkice dakeba kokuwa so kikeyi kuje a jijjigoki ki dawo ki kwanta?


Wani irin bakin ciki da takaicine ya lullubeni Wannan ma ai wulakancine shikenan ni cikin gida zan dawwama idan lokacinda beda lafiya banje ko inaba yanzu ma babu inda zandinga zuwa kenan,Kumama idan ciwone ai shine yajamin shi tunda da lafiyata lau.


Bankuma kallonshiba na dukunkune cikin hijab dina nacigaba da kukana tunda nasan bazanyimishi dole ba.


Tashi yai ya wuce daki ya gama shirinshi niyyarshi yabarni inta kukana tunda nima na iya Neman rigima acewarshi,Saidai Sam jiyai yakasa fitar ma,Wata zuciyar ke tunamishi rumace haidar tafi karfin wani yasata kuka agabanka ma balle kai kasata.
Dagoni yai jikinshi ya rungume, Haba rumana menene abun kuka kuma daga magana iye?
Cikin sheshsheka nace nima bansaniba amma ni shikenan bazan dinga zuwa ko inaba dole saida lalura? Tunda aka kawoni gidannan bantaba zuwa ko inaba ko gida so daya nabata zuwa shima dakilin maganinba ne sannan koda ka warke banje ko inaba saida banda lafiya yanzukuma umma zanbi bani kadai zanjeba ka hana kumafa kaima aiki zaka ni kadai za abari gidan kenan?


Bakinshi ya manne da nashi yana tsotsa harsaida naji yana Neman zurmawa sannan nai saurin dafemishi hannuwa,Idanunshi sun sauya yace naji Ruma nakuma fahimceki kiyi hakuri bazan kumaba kinji? Gidama insha Allah wannan weekend din zamuje kiyi hakuri tashi ki shirya to.
Mikewa nai zuciyata cike da farinciki amma Dan kadda yagane saiban nunaba, Har zan wuce yawani jawoni jikinshi tare da marairaicewa haba mana nafa baki hakuri to kisaki ranki mana,Koso kikeyi idan naje aikin inkasa yi?
Hawayena na share tare da danyin murmushi,Kudi ya damkamin ahannuna gashinan ko zakiga wani Abu dazaiyi miki kinji ko?
Godiya nayimishi sannan yabar gidan ajiyar zuciya na sauke kamin infara taka rawa Dan gaskiya naji dadin barin da yayi koba komai nima yau naga gari kuma ya ganni ai.


Yana tafe yana murmushi kai mata kenan iyayen rikici,Ita ruman da yakeganinta shiru shiru Ashe itama ba kanwar lasa bace kallifa yanzu daga magana amma takoma gefe tasaka kuka.






*** *** ****


Sosai naji dadi fitar da mukai da umma domin takaini gidan danginta da yawa inda sukaita nunamin kauna kamar zasu cinyeni awannan tafiyarnema nafara tunanin anya ba cikine daniba domin addu'ar da duk sukebina da ita alamace ta lallai akwai ciki jikina.
Umma babu wani kunya da kanta take fadin ai ansamu k'aruwama.


Munje gidan kayatattun kawayenta 'yan gayu kamarta nasami abin arziki da yawa musamman kayan gyaran jiki dana oga uban gayya.
Nidai ai iyakata murmushi danni inajin kunyar umma sosai.


Sai yamma likis muka koma gida itama umma taimin siyayyar kayan kwalam sosai acewarta wai duk abinda nakeso inci kawai indai hankalina zai kwanta.


Kwanciyata nayi akan kafet dinta duk da inaji tana fadin lallai kadda inyi barci Sabida magriba tataho amma ina jikina kwanciyar kawai yakeso.


Tsaye tai saman kaina tana sakin murmushi tare da jeromin addu'o,I cikin zuciyarta mamaki takeyi wai haidar dintane yaima mace ciki lallai Allah shine gwanin hikima.
[4/2, 3:09 PM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 44




Shigowar Abba gidan ya tilastamin tashi domin dama har anfara kiran sallar magriba.
Tashinai zaune ina murje idanuna sannan najawo glass dina na saka na gaidashi.
Be amsa gaisuwarba sai sannu dayaita jeromin kamin yace"Kinbi ummanku yawo aigashinan duk kin gaji ko?


Murmushi kawai nayi tare da sadda kaina k'asa.


"To sannu,Allah yaimuku albarka yabaki juriya da hakuri Ya Albarkaci zuri'arku.
Ahankali na amsa da amin kamin umma ta k'araso wajenmu,Sannu da zuwa taimishi kamin ya wuce dauro alwala cikin d'akinta.
Kallona tai " Tashi kije kema ki shirya kamin yadawo saikuci abinci kinji ko? Idan kuma akwai abunda kike buk'ata saiki gayamin ga tsarabarkinan cikin Leda karki manta.


Saida nai wanka sannan nayo Alwala banda hautsinawar ciki babu abinda ke damuna.
Saida na idar da sallar sannan na zauna lissafin lokacin al'adata,Cikin ikon Allah naga ai duka kwana takwas na kara shine alamun cikin kenan?
Jinai idanuna sunciko da hawaye kenan tun randa haidar yafara kwanciya dani ya zubamin cikin da amincewar Allah, Sai lokacin na tuna abinda yaitacewa wai be shigeniba rakine kawai kalar nawa, toko yina biyune dagayi sai ciki innalillahi yanzunan cikin cikina akwai kwayar halittar mutun? Kenan shiyasa naga su umma sunnunka kulawar da suke bani? Kai ko haidar din kulawar dayake bani yanzu tafi tada nesa ba kusaba.


Idanuna na lumshe inajin yanda cikina da kirjina keta zafi Sabida tashin zuciya.


Da gudu na mike nai bayi aiko nan nafara sheka amai gwanin ban tausayi dama kuma nacika cikin da ruwa danashiga wanka.


Tundaga falo yakeji kakarina da sunan inna danake kira tsabar wahala,Fatali yai da kayan hannunshi ya nufi inda yakejin sautina da gudu.
Bedamu da yanda nabata jikinaba ya rungumeni jikinshi yana shafar bayana sannu yake jeramin cike da tausayi.


Kuka na sakamishi ina kuma shigewa jikinshi, Dan sosai naji na galabaita dagayin Aman.


Shiiii, Sorry yi hakuri kinji yanzu zakiji dadi tunda kinyi aman kinji sannu.


Rigar ya ciremin ya watsamin ruwa sannan na dauro wata alwalar Sabida isha'i ta k'arato.


Shima wankan yayo bayan ya zaunar dani gefen gado.
Zama yai kusa dani bayan ya fito ya riko hannuna yanadan matsawa "Sannu kinji ina kemiki ciwo yanzu?


Kaina kawai na girgizamishi wasu sabbin hawayen na ziraromin.


Jiyai duk hankalinshi yatashi ko wani mummunan Abu ke damuna,Matseni yayi jikinshi yana shafar bayana,Kiyi hakuri kinji gayamin mezaki yanzu in samomiki kadda dare yayi ko?


Jinai kawai bakina ya furta tuwo zanci shi nakeso.


"Idanunshi ya fiddo kamin ya shafa kaina" Tuwo Ruma?
Cikin shagwaba nace eh ko bazan samuba?


"A a jira insa kayana inje wajan umma nidai wallahi bansan inda zansami tuwoba yanzu ni nama manta da munada nau'in abinci mesunan tuwo jira ina zuwa.


Kwanciya nayi tare da lumshe idanuna,Inajin shi ya sumbaci goshina lokacinda zai fita.



Cikin damuwa ya k'arasa wajan umma.
Zama yai yana sauke numfashi iyayen duk suka bishi da kallon kauna,Kamin umman tace " lafiyarka kuwa?


"Ajiyar zuciya ya sauke kamin yace " Umma ruma tafara amai duktai laushi kuma wai yanzu tuwo zataci.


Wata kabbara Abban ya dauka kamar meshirin kiran salla duk suka bishi da kallo kamin ya kauda kanshi yana murmushi ganin yanda duk suka zubamishi ido.

Jinjina kai umman tayi kamin tace to yanzu ina zamu samu tuwo? Indama inada garine sai inyimata ko?


Shiru sukai kowa da tunanin da yakeyi,Kamin Abban yace bari inje wajan malam habu megadi nasan baza a rasaba tunda ina gani yaranshi na kawomishi wani lokacin.
Bayan fitar Abban sai ya lalubo wayarshi ya dannama harun kira, "Kai ango yane?
Cikin basarwa yace oho maka Dan Allah yau hajiya tayi tuwo?


Wani uban ihu Harun din yayi kamin ya tashi Yakama rawa duk da cewa shine Wanda ya tabbatar da samun cikin amma beyi tunanin za afara wannan artabun da wuriba, Shi kanshi yanason aure to Amma daya tuno irin wahalar da yayunshi kesha wajan laulayi da yanda mazansu ke zarya tsakanin gidansu saiyaji kasala da tsoro Dan kaf yayunshi babu meyin laulayi me sauki watama saidai ta dawo gida.
"Hello kana jina? Cewar haidar jin Harun din shiru.


" Eh inajinka,Aikasan hajiya bata rabo da tuwo bari inkawo yanzu kace babynmu me karfine tunda yafara bukatar tuwo tun yanzu.

Kallon Umma yayi wacce ta zubamishi ido tanajiran taji ansamu kokuwadai tatashi ta saba hijab.
Cikin Dan basarwa yace umma Harun zai kawo yanzu.


Saida me gadi ya idasa addu'anshi Sannan Abban yaimai bayanin abinda ke tafe dashi.
Cikin farinciki malam habu yace Alhamdulillahi,Ashe munsamu k'aruwa to Allah ya inganta yasa arabu lafiya bari inleka gidan nasan baza a rasaba insha Allah.


Godiya Abban yaimishi Sannan yakoma cikin gida bayan yaji megadin ya rufe kofar gidan tabaya.




Wata matsanciyar sha'awar tuwon ta tasomin jinake kamar idan banciba zan mutu,Hijab dina na sagala na nufi wajan umma ina kuka ko fahimtar haidar din yana ciki banyiba Sabida yanda idanuna suka rufe.

Tuni umman ta mike jikinta har rawa yake haka Abba da haidar, Jikinta nashige ina sauke numfashi.
Lallashina tafara kamin tace menebne?
Cikin sheshsheka nace umma nace zanci tuwo amma har yanzu bedawoba nikuma yunwa nakeji cikina harya fara ciwo.


Kusan atare Abba da haidar din suka mike daalama jin cikina yafara ciwo yasasu rudewa.


Atare suka fice daidai lokacin Megadi yashigo da k'aramar kula hadda hajin jego.
Abban ya karbo sukaimai godiya atare suka dawo falon har lokacin umma na rungume dani tana lallashi bakinta har kunne surukarta tafara laulayi.


Kular Abba ya ajemin tare damin sannu,Ko jiran umma data tafi dauko filet banyiba na bada yajinnan nakama cin tuwon kamar Allah ya aikoni ni kaina bansan inacin tuwo hakaba Dan damacan bawani damuna yaiba.
Hatta 'yan kasusuwan dake ciki saida na taunesu tas Sannan nai gyatsa wani irin sukuni da kwanciyar hankali naji yana saukomin,Bansan lokacinda na lumshe idanuna ina murmushiba.


Sukansu dake kallona ko wanne sai fuskarshi ta cika da murmushi musamman Abba Wanda har wata kwalla ke tarar mishi cikin ido Anya befi haidar son cikinnan ba?


Saida nagama hutuna sannan na bude idanuna aiko wata matsananciyar kunya ta kamani ganin yanda duk suka zubamin ido suna kallona.
Boye kaina nayi cikin cinyoyina ina murmushi saikace banice nagama kukaba.


Harun ne yashigo falon,Duk aka gaisa sannan ya zauna na gaidashi shima bakinshi har kunne yakemin sannu kamin ya ajiye kulolin dake hannunshi.
Tare duk suka fice Sabida sallar isha'i da ake niyyar kabbarata.
Nima anan nayi sallar wajan nakoma na zauna jin cikina nakeyi har kirji Sabida yanda nai cin tsiya to ban sababa ni bammasan nayiwannan mugun cinba saidaga baya danaji cikin yaimin wani hake hake.


Harun wucewa yai gida Abba kuma fita hai haidar ne kawai yadawo kuma nan wajan umman yayi zamanshi bayan yaci abinci suka dasa hira,Nidai inajinsu kawai.


Wani uban nama Abba ya dire agabana sai baza kamshi yakeyi,Yace gashinan Ruma kici ki koshi megadi nabiya Wanda kika cinyemai saina karo miki.
Boye kaina nayi ina dariya,Suma duk dariyar sukeyi.


Haidar ya daukar min ledar da kulolin tuwon da Harun ya kawo mukai bangarenmu.




*** ****




Hanani cin naman yayi wai cikina zaiyi nauyi da yawa Saidai na wanko bakina nazo kusa dashi na kwanta.

Mun kwanta shiru naji babu wani bayani da alama yau yayi niyyar barina sainaji duk babu dadi bansan abinda yahau kainaba naji kawai shinake bukata.
Kirjinshi nafara shafa Ahankali ina lumshe ido aiko nan da nan bugun zuciyarshi ya sauya amma danya tabbatar saiya kama hannuna ya rike.
Kukan shagwaba na sakarmishi tare da murza kafafuna cikin nashi domin dama aharde suke.


Rungumata yayi yana jijjiga tare da furta sorry kinaso ne?


Kuma shigewa nayi jikinshi batare danace komaiba saidai salon danakemishi shiya tabbatar mishi da abukace nake domin bantaba kwatantamishi hakanba.


Idanunshi alumshe yace"Ruma karfa ki amayemu da tuwonnan wlh!!


Nidai banza nai dashi shima dole yai shiru yafara biyamin karatun danakejin shi kadai zangane alokacin.


Saida tafiya tai nisa sannan nasakamishi kuka,Aiko yanajina amma yai biris saima murmushi dayasaki danya lura rigimace kawai irinta masu yaronciki.
[4/2, 3:09 PM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 47






Tallabeni jikinshi yayi yana sakin k'aramin kuka betaba tunanin cikina biyu bane domin kusan so hudu yanamin scanning amma saidai yaga guda daya amma k'ato.


Hawayen wahala keta ziraromin ga wancan yaron nata son fara kuka gakuma na jikina yaki fitowa duk kokarin da yakeyi.


Muryarshi na rawa yace daure Ruma kadda ya mutu rikeni sosai kiyi nishi me karfi zai fito saiki huta kinji.
Cikin muryar kuka nace "bazan iyaba haidar mutuwa zanyi"


Da sauri ya sakeni yakoma cikin kayan da yake ajewa sabida tsaron lalura irin Wannan saigashi da allura,Acinya yaimin ita kamin wani lokaci nai wani mugun nishi daya fiddo ragowar babyn,.


Wani irin barcin wahalane yai gaba dani kokuma sumewa nayi oho dai nidai bankuma sanin inda kaina yaiba tunda nasamu wannan azababban ciwon ya sakeni.


Jikinshi babu inda be rawa sabida tsabar rudewa sai shafa yaran yakeyi gasu zabga zabga kamar haihuwar daya daya,Saima kokarin kuka da sukeyi.
Dakyar ya jawoma kanshi dauriya ya goge yaran dayake dama kayan haihuwar ashirye suke saida ya gama gyarasu tsaf sannan yaima hasan din sheda sabida kwata kwata babu abinda ya banbantasu.
Kuma saka hannunshi ahancina yayi yaji ina numfashi sannan ya kwashe yaran bayan yasakamusu riguna ya nanndesu cikin bargunansu masu taushi,Addu'a yaimusu sannan ya koma wajena lokacin tuni barcina yai nisa.


Ruwa me zafi yafara hadamin sannan yatasheni,Wani kuka nasakamishi ina kwace hannuna"Nika kyaleni inyi barci"


Cikin lallashi yace "To aidama barcin zakiyi zo ki gyara jikinki yanda zakiji dadin barcin ko?


Saida yaimin allura sannan yaimin wankan da kanshi hatta jinin saida ya rageminshi sannan na idasa gyara jikina nafito. Shikuma ya tsaya wanke bayin Dan na zubar da jini sosai.


Riga da zani nasa na daura kallabina sannan na lallaba kusa da yaran na kwanta wata irin azaba nakeji gabana nayi Wanda dacan banjishi sai yanzu.


Idona biyu har yagama gyaran ko ina ya wanke kayan dana bata da nashi danshima mugu mugu yayi saikace shima haihuwar yayi.
Saida yasa turare sosai bayan ya lullube har fuskar yaran sabida zai iya yimusu karfi,Sannan yadawo kusa dani ya zauna yana sauke numfashi.


" Hannunshi nakamo na rike gam ina hawaye.
"Hannun nawa yacigaba da mirzawa cikin lallashi yace" Kiyi hakuri kindan k'arune shiyasa kikejin ciwo bari in inyimiki dinki yanzu saimuyi barci kinji ko?
Nidai ba baka sai kunne.


Saida yaimin allurai har biyu sannan yaimin dinkin banwaniji zafiba sannan ga allurar hadda ta barci danhaka bankuma sanin me akecikiba.


Ajiyar zuciya yaita saukewa akai akai kamar Wanda yaga halaka ya kufce sai kallon yaran yakeyi wa inda keta barci har hawayen dadi yayi tsabar farinciki jiyake kamar canzashi akayi.


Wanka yakumayi sannan ya dauro alwala yafara nafilfili yana godiya ga Allah dayaimishi wannan kyauta lokacinda beyi zatoba sannan kyautar da babu wani mahaluki daya isa yaimaka irinta.


Saida yai sallar asbahi sannan yasamu ya tsallaka can karshe ya kwanta yaran na tsakiya saidai su motsa su koma.






*** ***




Umman haidar ko zaki leka yarancan ne nifa bansan inji shiru banji motsinsuba kinsan bawani hankali garesuba ko?
Farfesun dake gabanta ta ture kamin tace "Alhaji kadaisan halin haidar da shiririta yaufa lahadi tunda yasan ba aiki zashiba aidama da wuya sutashi yanzu"


"Uhumm kofa sallar asuba bejeba kidaije ki lek'a kokuma ni inje.


Tashi tayi tana " Kai alhaji ko bari inje tunkamin katashi kai gaba,Cikin nan dai ko kai za ahaifar mawa iyakarta kenan!!! Ficewa tayi tana dariya yayinda shima yabita da kallo yana dariya.




Tajima tsaye tana bugun kofar amma shiru babu wani bayani,Da sauri ta juya Dan dauko key din dake wajanta Dan lokaci guda zuciyarta tafara gayamata ba daidaiba.


Ganin tashiga amatukar rude yasashi biyota data dauko key din,Ko ina lif babu haske duk da cewa Tara na safe yama wuce.
Tsaye sukai tsakiyar falon suna sallama nan ma shiru.
"Bafa tsayawa zakiyiba binta shiga zakiyi kiga ko lafiya nikuma zanjira nan.


Dakin datasan munfi amfani dashi ta nufa zuciyarta inbanda matsanancin bugu babu abinda takeyi,Fatanta daga alkhairi ba sharri ba.

Innalillahi wa inna ilaihirraji'un Alhaji zokagani Dan Allah.
Lokaci guda salatinta ya karade gidan,jikin Abban har rawa yake wajan afkawa cikin dakin wani irin burki yaja lokacinda ya fahimci metake nunamishi.


Nice ta farko sai yaran kudundune atsakiya saikuma haidar din Wanda ke daf da yaran yo ai dole ai ramuwar barci wannan artabu da akasha cikin dare.


Duka umman ta bugama haidar Wanda yasashi tashi agigice yana lalubar yaran Dan karma ya kasance mafarki yai duk wannan wahalar dayasha.


Jikinsu har rawa yakeyi wajan daukar yaran wayyo murna Abba hadawa yayi da Umma da yaran ya rungume yana godema Allah tare da jeramishi kirari.
Lamo haidar din yayi yana sakin murmushin farinciki dama yasan burin iyayeshi kenan suja jininshi yau gashi Allah yabashi har guda biyu.


Hannu Abban ya mikama haidar din Wanda yaketa kallonsu yana murmushi tare da share kwallar farinciki,Tashi yai yashige jikin mahaifinshi suka rungume juna,Itama umman hadasu tai ta rungume fuskarta jage jage da hawaye.


Saida suka natsa sannan tace "Hardar ita uwar lafiyarta lau ko?


" Lafiya lau Umma amma saida naimata dinki.


"Allah sarki baiwar Allah ai dole wa innan yara haka manya manya gashi ta fari Allah yabata lafiya bari mukoma falo kadda atasheta,Tasamu ta huta sosai ,Ammadai tai wanka ko?


Kai ya dagamata yana lumshe ido wani irin barci yakeji shima.


Komawa falon sukai suka zubama yaran idanu kowa sai sakin murmushi yakeyi ko magana sunkasa yima juna tsabar farincikin da suke ciki.
" Ammadai haidar yaso yai wauta meyasa be kirakiba kin temakamishi?


"Uhumm Aiko gashinan shima duk ya zube dare daya kawai daga gani kwana sukai Abu daya,Mudai ai anyi barka tunda anrabu lafiya"


"Hakanekam Allah shine abun godiya Allah yaimata albarka ai tayi kokari sosai wallahi yarinyar akwai ta da dauriya,Cewar Abban bakinshi har keya,Sai faman liliyar hannun yaron dake hannunshi yake.






Zubamin manyan idanunshi yayi ganin yanda fuskata tadan tasa sabida gumurzun jiya lallai ba k'aramar juriya nayiba,Wani murmushine ya kufcemishi lokacinda ya tuno da fitsarin daya saki lallai yayi abin kunya Allah ma ya rufamai asiri lokacin ban cikin hayyacina lallai dayayi abinda zanta tsokanarshi dashi.


Fuskata ya dinga shafawa har saida na bude idanuna nai wata doguwar mika gwanin dadi na juya yanda raina keso,Ai bansan lokacinda na rungumoshi jikinaba cike da farinciki" Shikenan yanzu nima zandinga barci yanda raina keso"


Murmushi yayi tare da sumbatar kuncina"Allah yaimiki Albarka matata Allah ya farantamiki Ruma Allah ya jikan iyayenki yai musu rahma,Ina rokon Allah yabani iko da damar farantamiki har karshen numfashina nagode sosai Allah yabarmu tare.


Cikin sanyi jiki na amsa da Amin ya haidar nima nagode da kyautatawarka gareni.


Wani murmushin kauna yabini dashi kamin yace muje in nunamiki yanda zaki gasa jikinki saiki karya nasan dai akwai yunwa cikinki tunda kinfitar da wa incan basawan,Kamin kuma sufara Neman abincinsu.


Kusan wankan ma da kanshi yaimin duk da irin shagwabar da nake zubamishi,Umma shigowarta biyu amma bamu fitoba saidai tanajin maganarmu,"Kai yaran zamani sai abarsu.


Abba na rungume da yaran gaba daya sai kiran waya yakeyi yana fadi yayinda umma keta shige da ficen ganin ta kammala abinda zan karya dashi ga yaran harsun fara Neman abincinsu.


Saida nafara shafa mai sannan shima yashiga wankan,Mamaki nakeyi wai yara biyu na Haifa duk maza lallai Allah shine mabuwayi gagara misali.
Riga da zani na sa wa inda rabon da insasu harna manta sabida girman ciki,Amma gashi yanzu sun shige tsaf sai kirjina dayacika sosai.


Saida tagama shiryamin abinda zanci sannan taima yaran wanka ta shiryasu cikin wasu kaya masu matukar kyau da Tsada saidai kalarsu daban sabida babu Wanda yai tunanin biyu zan haifa duk da mutane da yawa na fadin gaskiya da wuya idan dayane Sabida girman da cikin yayi.


Lokacinda shadaya na safe yayi ai tuni gidan yafara dinkewa da 'yan barka.
Falona cike yake da dangin umma sabida itace 'yar gari kamin dangina su iso duk da dai duk Wanda yakirani sai inji yace sai suna zaizo amma innata kam tace tana nan tafe yau dinnan kuma sai anyi suna sannan zata koma.



Niyyar kwanciya nake sabida har kaina yafara ciwo sabida hayaniya saigashi ya shigo da yaran daga bangaren Abba yake sabida abokanshi dana Abban daketa zuwa ganinsu.


Duk kuka suke yanata jijjiga da lallashi saikace sunsan abinda yakeyi.
Hararata yayi kamin yace anya kinada kai kuwa?Ya za ai ki hana yaran abincinsu tun jiya haba Dan Allah"


Cikin marairaicewa nace kayi hakuri Allah da umma ta kawosu dazu bansan yanda zanyibane kuma sainaga sunkoma barcin saina kyalesu.


Zee din rigata yaja kamin yace to ai saikiyi magana anunamiki amma yara sai kuka sukeyi rike ki gani.
Yai maganar yana mikemin daya sannan ya kwantar da dayan acinyarshi ,Da kanshi ya zaro nonon yana tambayata kin gogo da nace ki goge?


Kaina na dagamishi tare da tayashi gyara yaron.


Wani k'aramin ihu nasaki lokacinda yaron ya damki nonon,Bansan lokacinda na dafe hannun haidar dinba ina hawaye.
Cike da tausayawa yake cewa"Sannu kinji ahankali zai bari sannu kadda ki ciremishi kinga sosai yakeja yunwa yakeji.


Ummace ta shigo da sallama,Tana kallonmu "Sannu Ruma zafi ko? Kiyi hakuri zai bari bari inje indawo dama bakine sukazo.


" Dan Allah kabarshi hakanan yafa koshi!!!


Hararata yayi kamin yace gidanwa ya koshi kina gani saisha yakeyi.


Saida yaron ya saki Dan kanshi sannan ya amsheshi ya dorashi akan kafadarshi yabani dayan,"Yauwa bashi wannan yanda kikaima wannan din dasun koshi saikiyi barcinki kinji 'yar albarka.
Yana zaune duk saida yaga suncika cikinsu sannan yace in kwanta shikuma ya fice da yaran.


Sonake inyi barci kamin inna ta iso musha hira.
[4/2, 3:09 PM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 46




Sallamar Abba yasani kokarin gyara zamana,Amma saiya kalleni cike da tausayawa "A a yi zamanki rumana sannu kinji Allah yarabaku lafiya yabada masu albarka"
Sadda kaina k'asa nayi Sabida kunya inason tsohonnan wallahi sosai yake kaunata.
Naman dake hannunshi ya ajiye gabana yana fadin ga sakonki da zafinshi sosai.


Godiya naimishi sannan najawo ledar na bude bayan barinshi falon.


Haule itace yarinyar da Umma

Please Login or Register in order to submit comment