Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri Moddibo ya Girgiza kai tare da cewa.
“Subhanallah Abba kada kace haka kada zafin damuwa yasa mu kaucewa lissafin hankali da na Musulunci Abba kayi addu'a dan Allah ka karɓi maganin kasha Abba. shin yakakeso nayi idan har kaima ka faɗi ciwo ya kwantar da kai”.
Cikin tausayawa ya kalli Abba idanunsa cike da ruwan hawaye kana yace.
“Abba na tabbatar ko da J na nan bazai yi farin ciki da haka ba Abba dan Allah kayi haƙuri kasha maganinka, ganinka cikin dauriya shike bani ƙarfin gwiwa Abba bazan so ganin wani mugun abu yasa Meka ba. Idan har wani abu ya sameka Abba ya zanyi da rayuwata!?”.
Ya ida Maganar tare da miƙawa Abba maganin karɓa Abba yayi tare da kaiwa bakinsa ya haɗiye miƙewa Dr Muktar yayi kana yace.
“Alhj bari a maka Allura”.
Kai Abba ya gyaɗa kana Dr Muktar ya masa bayan ya masa ya juya ya fice.
Sannu Ahankali Abba ya fara maida numfashi kana ya jingina bayansa da jikin kujera ahankali numfashinsa ya fara dai-dai-ta Atake zufa ya shiga tsats-tsafo masa agabaki ɗaya ilahirin jikinsa.
Moddibo kuwa ganin haka yasa ya miƙe ahankali tare da ɗaukan remote ɗin AC ya kunna kana ya dawo ya zauna agefensa.


Matsawa kusa da Abba Hajiya Turai tayi kana ta ɗauki hankief ta shiga goge masa zufa,
cikin sanyin murya tace.
“Sannu Alhj Ubangiji ya sawwaƙa maka, ka kwantar da hankalin ka insha Allah babu abinda zai samu Jameelu sai al'khairi”.
Kallonta yayi amma baice komai ba.
Moddibo ma ahankali ya dawo kusa dashi ya zauna kana cikin sanyin murya yace.
“Abba ka kwantar da hankalin ka insha Allah babu abinda zai samu J Abba yanzu fa abinda ya kawoni da mukayi waya kace ansamu kudin kwata kwata Abba yanzu fa Million biyar ne ya rage akan kuɗin da muke nema ai abu yazo ƙarshe insha Allah babu abinda zai samu J,
Kuma ma kafin inzo nayi waya da Ummi tace akwai wasu gwala-gwalai guda biyu gobe zata kaisu Taraba, da akan yau zata kaisuma to dare yayi, ta kuma cemin in sha Allah zasu iya kai two million.
Kajifa alamomin nasara Abba meye zai tayar maka da hankali!?”.


Ahankali Abba ya ɗago jajayen Idanunsa tare da kallon Moddibo kana ya kalli Hajiya Turai sai kuma ya maida kallonsa kan Hajiya Karima dake tsaye cikin rauni ya nuna ta da yatsa kana yace.
“Karima ce nashiga wanka suka kira.
Karima ta ɗauka wai tana musu maganan ragin kuɗin nace ta nema min ragi ne?
Tabarni mana Jameelu ba ɗana bane ai zan fashi ɗana amma Meyesa Karima zata min haka!?”.
Moddibo kuwa cikin wani azabebben tsinkewar zuciya ya riƙe kansa tare da cewa.
“Innalilahi wa'inna ilahi rajiu'n.
kika nemi ragin kuɗi kuma Aunty Karima amma gaskiya baki kyauta mana ba”.
Cikin tsananin tsoro da fargabar abinda hakan zai haifar yaci gaba da cewa.
“Amma gaskiya baki kyauta manaba, ai wannan mugunta ne an saki ne ko kuma annemi wani temako awajenki fisabilillahi? wallahi kin cutar damu wannan shine cuta mafi muni da kika mana bayan kinji gargaɗin da sukayi”.
Ya ƙarashe mgnar cikin raunin murya yana jin zuciyarsa na wani irin zafi da karaya.


Cikin sauri Hajiya Turai ta kalli Hajiya Karima tare da Girgiza kai cike da takaicin halayyar ta tace.
“Idan har ba tayi haka ba ai bata cika Yadukko ba, ai dama baka sanin mai sonka da gaskiya sai kashiga wani hali, wasu kuma burinsu su samu hanyar da zasu musguna wa rayuwarka suke nema”.
Kallon Hajiya Turai Hajiya Karima tayi kana ta kalli Abba da Moddibo cikin Muryan kuka tace.
“Agaskiya ni anyi min bahaguwar fahimta nima Ina son Jameelu tamkar ɗa yake awajena fa, ke Hajiya Turai da kike wannan maganar nida ke waya fara zama da Jameelu ne?”.
Banza Hajiya Turai tayi da ita tana jin wani irin takaicin abinda ta aikata aranta.
Sannu Ahankali bacci ya fara fisgar Abba saboda magani da Alluran da aka masa nan take Bacci ya ɗauke sa kwanciya Moddibo ya gyara masa akan kujeran kana ya miƙe tare da ɗaukar key ɗin motarsa zuciyarsa cike da rauni damuwa da tashin hankali duk sun bayyana afuskarsa.
Yana fita yashiga motarsa tare da yimasa key yayin da hawaye suka cika kwarmin Idanunsa Driving yake yana sake try numbers din da suke kira kasancewar duk lokacin da suka kira saiya yi copy amma baki ɗaya Swich off.
Ahankali ya fito da Number M Jameel kana Yayi dearling cikin ikon Allah yaji wayar tashiga tana ringing lokaci ɗaya ya shiga cikin matsanancin farin ciki afili ya furta.
“Yau kuma wayar J tana shiga”.
Cikin sauri ya juya akalar motarsa zuwa gidan Ummi kana ya Parking awaje tare da buɗe gate ya shiga coumpund ɗin yana cewa.
“Ummi! Ummi!! Ummi!!!”.
Ummi dake tsaye Atsakiyar falo tayi saurin fitowa tare da cewa.
“Na'am Babana me yafaru?”.
Cike da walwala yace.
“Ummi wayar J ɗina yana shiga yau”.
Cike da farin ciki Ummi ta ware ido kana tace.
“Wayar Jameelu yana shiga?”.
Kai Moddibo ya gyaɗa still da murmushi afuskarsa ya gyaɗa mata kai kana yace.
“Wallahi yana shiga Ummi bari ma kiji”.
Ya faɗa tare da dearling number M Jameel aikuwa ya shiga ya fara ɗut-ɗut-dut cikin Sauri ya samata akunne da sauri Asma'u da Bashir dake Bedroom suka fito jiyo sautin su Ummi cikin farin ciki.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Bari in Kira nima".
Ta ida maganar tare da dearling number kasancewar wayar na hannunta still ya shiga yana ringing.


Cikin sanyi ta juya ta kalli Moddibo tare da cewa.
“Babana to ya baya ɗauka kuma?”.
Cikin wani masifaffen tsinkewar zuciya da tsoro Moddibo ya kalleta cikin ƙoƙarin ɓoye tsoronsa yayi Murmushi tare da cewa.
“A'a Ummi Insha Allah tunda har wayarsa tana shiga zai ɗaga mu cigaba da kira da izinin Ubangiji zai ɗaga Agaskiya Ummi yau naji sanyi”.
Murmushi Ummi haram Asma'u, da Bashir.


“Har naji hankali na ya dan kwanta wayar J ɗina ya shiga, kinga farko kafin mu rasa shi kiran wayarsa muka fara rasawa Ummi, yanzu kuma Insha Allah mun samu kiran wayarsa shi zamu ƙara samu next da izinin Ubangiji”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da cewa.
“Ameen”.
Cikin jin sanyi Asma'u tayi murmushi kana tace.
“Alhamdulillah wayar Yah Jameel ya shiga gaskiya munyi farin ciki”.
Malam Ahmad daya fito daga wanka ya fito coumpund ɗin fuskarsa ɗauke da murmushi kana yace.
“Alhamdulillah Asma'u maza kawo musu abinci suci tunda mun samu wayar Jameelu ya shiga maza kawo musu abinci”.
Moddibo kuwa kallon Malam Ahmad yayi kana yace.
“Nikam ma Malam baki ɗaya cikina ya cushe baki ɗaya farin ciki ya cika min cikana”.
Murmushi Ummi tayi kana tace.
“Nima cikina ya cika baki ɗaya farin ciki nake ji”.
Jinjina kai Malam Ahmad yayi tare da cewa.
“Dan Allah ku zauna kuci abinci wayarsa muka fara rasawa yanzu kuma wayarsa muka faru samu insha Allah shi ma zamu sameshi nan kusa ”.
Dai-dai lokacin Asma'u tazo ta ajiye musu abincin.
Tun ɓatan M Jameel sai yau Ummi da Moddibo sukaci abinci mai nauyi acikinsu duk da ba dayawa suka ciba.
Miƙewa Moddibo yayi kana yace.
“Ummi bari naje in faɗawa Innayi ta tayamu farin ciki”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da faɗin.
“Aikam dai gwara kaje”.
Ficewa yayi tare da tafiya Driving yake Cike da farin ciki har ya isa gida yana zuwa ya shiga sashen Innayi.
Innayi dake ki shimfiɗe ta miƙe kana tace.
“Alhamdulillah Moddibo naga kana cikin farin ciki da alama akwai labari mai daɗi?”.
Kai ya gyaɗa still Fuskarsa ɗauke da murmushi yace.
“Innayi wayar J ɗina ya shiga yau”.
Kai Innayi ta gyaɗa tare da cewa.
“Alhamdulillah gaskiya munyi farin ciki. Allah ya bayyanar mana dashi”.
Ameen ya amsa tare da wucewa sashen sa cike da farin ciki yana shiga ɗaki ya kira layin Malam Arɗo.
Malam Arɗo na dagawa yace.
“Malam Alhamdulillah yau wayar J ɗina yashiga a cigaba da taya mu da addu'a a masallacai da makarantu”.
Cike da farin ciki malam Arɗo yace.
“Masha Allah da izinin Ubangiji zai fito Insha Allah zamu cigaba da addu'a”.


Awannan daren haka Moddibo Ummi, Asma'u Bashir malam Ahmad da Innayi suka kwana cike da farin cikin shigar wayar M Jameel.


Yayin da Aɓangaren Abba ya kwana cikin taraddadi da tashin hankali koda ya farka tsakiyar dare kuka yayi ta yi yayin da Hajiya Karima ke kuka tana basa haƙuri kana tana cewa bada niyya tayi ba.


Aɓangaren gidan Lamiɗo ma haka Khausar da Mommy suka kwana azaune da Ramadan da kansa ke masifar ciwo da zaran an bashi maganin da Lamiɗo ya kawo yasha ciwon zai ɗan lafa jimawa kaɗan kuma zai sake tashi tsakiyar dare ya farka ya riƙa kuka dole Ummi ta kira Abba ya kawo masa magani cikin ikon Allah yana sha ciwon kan ya lafa.


Washe gari; Moddibo, Malam Arɗo, Ummi Innayi duk wani makusancin M Jameel na cikin farin ciki kana duk wanda ya kira wayarsa zai shiga sai dai ba aɗagawa Wunin wannan ranan haka Moddibo yayi yana kiran layin M Jameel still ba amsa.
Zuwa yamma jikin Moddibo ya fara sanyi da lamarin ganin yana kiran wayar M Jameel baya shiga lokaci ɗaya tsoro ya fara kamashi hankalinsa ya tashi Misalin ƙarfe goma na dare yana gidan Abba zaune sun kira Jameel kuma sama da sau ashirin kuma duk kiran yana shiga, sau dai ba'a ɗagawa, su kuma masatan basu kiraba.
Yayin da idanun Abba ke kumbure alamar har yanzu jinjinsa bai sauƙa sosai ba.
Cikin mutuwar jiki Moddibo ya koma gida kai tsaye sashen Innayi ya nufa bakinsa ɗauke da Sallama ya shiga.
Innayi dake zaune riƙe da carbi ta amsa masa cikin raunin Murya yace.
“Innayi”.
Kallonsa tayi cike da kulawa kana tace.
“Na'am”.


Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana cikin sanyin murya yace.
“ Innayi hankalina ya soma tashi wayar J yana shiga ba'a ɗauka sannan mutanen nan basu sake kira ba”.
Ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe tare da cewa.
“Ba komai Moddibo Insha Allah ka kwantar da hankalin ka”.
Girgiza kai yayi kana yace.
“Anya kuwa Innayi?”.
Cikin bashi ƙwarin gwiwa tace.
“Ba komai Insha Allah ka cigaba dayi masa addu'a da izinin Ubangiji zai fito yanzu idan sun sake kira kuce musu an samu kuɗin Insha Allah Million biyar bazai gagara ba koda a masallatai anemi temako za'a samu su haɗu”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Toh Innayi Allah yasa su kira ɗin dan yanzu kam ma cikon Million ukune”.
Cikin jin daɗi Innayi tace.
“Alhamdulillah Allah ya bamu sa'a”.
Amin yace
Sanna ya miƙe ya koma sashen sa cike da damuwa. Washe gari jin sauran kuɗin da ake buƙata, Lamido ya bawa Mommy da kanta ta kaiwa Ummi su sau dai sam basu kuma kiraba.


Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya yau kusan kwana ki shida kenan duk lokacin da aka kira wayar M Jameel zai shiga sai dai ba'a ɗauka.


Yayinda Ramadan kuwa ke kwana da azabebben ciwon kai idan aka bashi magani yasha ciwo ya lafa anjina kaɗan kuma ya sake dawowa.
Ga ɗaya Mommy da kwausar sun shiga damuwa, sun kai asibiti har cikin Taraba anyi hoton kan da duk wani gwaje-gwaje amman babu wani ciwo dake kansa, dan da farima likitocin sunyi zaton brain cancer ne.
baki ɗaya yaron ya fita hayyacinsa saboda tsananin ciwon kai.
Yau kimanin kwana shida kenan da aka fara samun wayar M Jameel na shiga.
Washe garin rana ta bakwai.
Da safe bayan an idar da Sallar Asbah Moddibo na fita a masallaci ya kira wayar M Jameel.
Cike da mmki tsoro ya janye wayar a kunnenshi sabida jin ance masa Switch off.
cikin mutuwar jiki ya nufi gidan Ummi yana shiga ya samu Ummi zaune akan Sallaya hannunta riƙe da Carbi.
Cike da ladabi ya gaisheta kana cikin sanyin murya yace.
“Ummi”.
Kallonsa tayi tare da cewa.
“Na'am Babana”.
Cikin raunin murya yace.
“Ummi na kira wayar J ɗina baya shiga”.
Ahankali Ummi ta jingina kanta da jikin kujeran falon kana tace.
“Nima na kira wayan Jameelu na baya shiga bansan Meyesa ba Allah yasa al'khairi ne”.
Cike da sanyi Middibo yace.
“Amin ya Allah in sha Allah ba komai Ummi”.
Cikin raunin murya Ummi ta lumshe Idanunta tare da cewa.
“Hmmm,Hmmm Ubangiji Allah yabamu ikon cinye jarrabawar da zai jarabce mu”.
Cikin sanyi Moddibo yace.
“Ameen”.
Miƙewa Moddibo yayi kana yace.
“Ummi bari naje gidan Abba naji koshi ya kira ya shiga”.
Kai Ummi ta gyaɗa Muryanta cike da rauni tace.
“Toh”.
Cikin sanyin jiki zuciya cike da karaya Moddibo ya nufi gidan Abba yana shiga coumpund ya ga Abba na ƙoƙarin shiga falo dawowansa daga masallaci kenan.
Ƙara sawa Moddibo yayi tare da miƙa masa hannu sukayi musabaha kana cikin sanyin murya Moddibo yace.
“Abba wayar J ɗina baya shiga”.
Ahankali Abba ya sunkuyar da kansa hawaye masu zafi suka shiga bin kuncinsa Shar-shar-shar kamar ƙaramin yaro baki ɗaya ya rame cikin raunin murya yace.
“Aliyu dama wayar Jameelu da kira yake shiga. Wani sanyi ne dama hankalina ya tashi tun jiya nake kiran wayar baya shiga, dama ni banyi farin ciki da shigan wayar Jameelu ba. Aliyu inaji Ajikina kamar akwai wani abu da bamu san menene ba jikina na bani ko ina Jameelu na yaje baya cikin walwala na rasa tudun dafawa”.
Cikin sauri Moddibo ya runtse Idanunsa zuciyarsa na bugawa da masifaffen ƙarfi kana cikin raunin murya yace.
“Abba insha Allah J yana cikin ƙoshin lafiya mu cigaba da masa addu'a amma nima baki ɗaya hankalina yayi masifar tashi”.
Cikin rauni da tsanananin tashin hankali suka ci-gaba da tattaunawa.


Acan gidan Lamiɗo kuwa Mommy, Khausar da Lamiɗo basu rintsaba a wannan daren.
A kan Ramadan suka kwana yanata kuka baiyi bacci ba.
Washe gari Bayan an idar da sallan Asbah Hajiya Bunayya ta shigo falon Mommy ahankali Ramadan dake kuka ya miƙa mata hannu kana cikin wata raunan'niyar murya mai cike da wahala yace.
“Ummah! Ummah! Kaina zai fashe kaina zai faɗi Wayyo Allah na Kaina! kaina”.
Baki daya jijiyoyin kansa sun tashi sunyi ruɗu ruɗu dasu yayinda idanunsa sukayi ja.
Cike da tausayawa Khausar ta ɗaura tafin hannunta na dama akan goshinsa Idanunta cike da ruwan hawaye kasa riƙe hawayen ta tayi jin yanda kan ke harbawa da masifar ƙarfi.
Kuka sosai Ramadan keyi kana cikin tsananin radaɗin ciwo ya riƙo hannun Mommy kana yace.
“Wayyo Mommy Kaina zai fashe. Mommy Kaina Wayyo zan mutu Mommy Zan mutufa”.
Wani irin miƙa Ramadan yayi tare da cewa.
“Momyyyyy zan mutuuuu”.
Cikin sauri Lamiɗo da yanzu ya shigo ya karɓesa ganin yanda idanun yaron suka juya da sauri ya fara ɗan bubbuga kumatunsa yana cewa.
“Ramadan! Ramadan!”.
Wani irin juyawa Idanun yaron yayi tare da wulƙitawa kana yaja dogon numfashi....!






*Zuwa yanzu dai mun gama ratsa tsakiyar labari babi-babi na zaren na dab da fara warware wa.*




By
*GARKUWAR MARUBUTA*
*Littafin nan dai ba free book bane, na kuɗine ko kin gashi a wasu wuraren da ba Group na da ake biya insa mutum, littafin 1k ne kacal in sha Allah zaki karanta shi daga forko har ƙarshe akan 1k kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki yar uwa*






Sbpndegoo. Lamiɗo kuwa cikin yanayin, tausayi da jinƙai da ƙauna mai haɗe da taraddadi da tsoro, ya sanya tafin hannunsa na dama ya tallafo, fuskar Ramadan ya juya gefe da gefe ga mmkinsa gaba ɗaya uwayan yaron ya koma lagob-lagob cikin yanayi da kiya da son aro Jarumtaka ya runtse Idanunsa tare da maimaita kalmar Hasbunallahu wani'imal wakil. Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n.
Cikin sauri Hajiya Bunayya dake zaune ta buga hannunta aƙirji tare da kallon Lamiɗo daya zubawa Ramadan ido tace.
“Mai Martaba ya rasu ko?”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗago ido ya kalleta kai ya girgiza mata batare da yace komai ba.
Da sauri Mommy dake tsaye tayi baya tare da zama da ɓas akan kujeran dake bayanta, baki ɗaya jikinta ya saki Atake ta fara Maimaita kalmar.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin”,ta faɗa hawaye na bin kuncinta Shar-shar.


Khausar kuwa juyawa tayi ta kalli Hajiya Bunayya kana ta mayar da kanta kan Mommy da hawaye ke bin kuncinta ahankali ta sake maida kallonta kan Lamiɗo da yayi shiru yana jan yatsun Ramadan alamar yana dai-dai-tasu.
Cikin wani irin yanayi tace.
“Abba mu tafi dashi asibiti,Abba mu kaisa asibiti”.
Jujjuya kai Lamiɗo yayi kana yace.
“Khausar ki nutsu”.
Kallon Hajiya Bunayya da Idanunta ke kan Ramadan yayi yace.
“Hajiya Bunayya kama khausar ki zaunar da ita”.
Mommy kam tana zaune akan kushin babu abinda take maimaitawa face kalmar Innalillahi still hawaye na bin kuncinta.


Ganin haka yasa Lamiɗo fesar da numfashi kana ya miƙe tare da ɗaukar Ramadan awuyansa ya fice.
Da sauri Khausar ta miƙe tare da bin bayansa tana cewa.
“Abba inzo mu tafi Asibitin ne!?”.
Tsintsiyar hannunta Hajiya Bunayya ta riƙe tare da gyara zamanta tace.
“Khausar ki nutsu mana ki dawo ki zauna?”.
Kai khausar ta girgiza cikin rawan murya tace.
“Ki sake ni zamu tafi asibiti ne kiga Ramadan fa”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da faɗin.
“Ki zauna mana ba kiji Abbanku yace ki zauna ba.
Kai ta gyaɗa cikin wani irin yanayi ta koma ta zauna.


Lamiɗo kuwa yana fita kai tsaye sashen Gimbiya Dadu ya shiga bakinsa ɗauke da Sallama zaune ya samu Gimbiya Dadu afalon.
Ganinsa Rungume da Ramadan yasa cikin sauri tace.
“Ya dai lafiya Lamiɗo meke faruwa?”.
Cikin sanyin murya yace.
“Ramadan ne fa ki duba min shi”.
Kai ta gyaɗa tare da Matsawa gaban Ramadan dake kwance ƙasan ɗakin yatsunta biyu ta kai saitin hancinsa sannan ta riƙe jijiya hannunsa kallon Lamiɗo tayi cike da mamaki tace.
“Ha'a bashi da rai ai ajikinsa?”.
Araunane Lamiɗo ya ɗago idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur jijiyoyin kansa ya tashi cikin raunin murya yace.
“Nima dai kamar haka na gani ahannuna na ya cika kamar babu rai atare da shi.
Jinjina kai Gimbiya Dadu tayi cikin rawan murya tace.
“Tabbas ba Rai atare dashi Ramadan ya rasu fa”.
Ta ida maganar tare da ɗago hannunsa ta juya sangalam duk ta inda ta juya sai ya tafi luuuu zai fadi kana ga bakinsa dake aɗan buɗe idanua kafe.


Ahankali Lamiɗo ya sunkuyar da kansa akan Ramadan hawaye masu ɗumin gaske suka shiga zubo masa asaman kincinsa, suna ɗiga kan fuskar Ramadan tal-tal yayinda jinkinsa ya shiga tsuma.
Gimbiya Dadu kuwa bayanta ta jingina da jikin kujeran cikin sanyin murya tace.
“Allah sarki Ramadan ashe dai ciwon kan nan na ɗauka ne? Ciwo lokaci ɗaya!?”.
Akuma dai-dai lokacin Uncle Naseer ya shigo falon ganin yanayin da suke ciki ne yasa ya zauna gefen Gimbiya Dadu tare da cewa.
“A Lafiya meke faruwa?”.
Ahankali Gimbiya Dadu ta ɗago kai tare da Kallonsa tace.
“Wallahi Ramadan ne Allah ya masa rasuwa!”.
Arazane Uncle Naseer ya Kalli Gimbiya Dadu tare da kallon Ramadan dake kwance cikin wani irin yanayi yace.
“Ha'a wani irin magana ne Gimbiya Dadu ya zakice Ramadan ya rasu!? Ko ke Dr ce ya za ayi kice ya rasu taya kika gane hakan?”.
Kallonsa ya mayar kan Lamiɗo daya zubawa Ramadan ido kana yace.
“Yah Lamiɗo mu kaisa asibiti”.
Kallonsa Lamiɗo yayi tare da Girgiza masa kai still Idanunsa na nan ja jawur ruwan hawaye na kwance acikinsu yayinda jikinsa ke cigaba da tsuma zuciyarsa na harbawa da masifan ƙarfi.


Uncle Naseer kuwa hannu yasa a aljihu tare da ciro wayarsa yayi dearling number family Dr su yana ɗagawa yace dan Allah yazo ya duba yaro agida Dr ya amsa da toh.
Bayan minti 16 minute Dr yazo bayan ya duba ya tabbatar musu da Ramadan ya rasu kimanin minti talatin da suka wuce.
Sai asannan Uncle Naseer ya yarda kana ya raka Dr ya tafi yana dawowa.
Sashen Gimbiya Dadu ya hadu da Lamiɗo ya fito da Ramadan Rungume akafaɗarsa bayansa yabi Lamiɗo kuwa kai tsaye Falonsa ya nufa yana shiga ya kwantar da gawar Ramadan Atsakiyar ɗakin kana ya cire masa suturar jikinsa ɗen oh foɗimo.


Cikin rauni da tsinkewar zuciya ya nufi ɗakin Mommy a inda yabar Mommy zaune anan ya dawo ya sameta still Idanunta na zubar da hawaye masu zafi da ƙuna a zuciya.
Khausar dake gefenta ta kalleta tare da cewa.
“Mommy Meye faru me yasamu Ramadan?”.
Ahankali Mommy ta janyota jikinta tare da kwantar da ita akan cinyarta kana ta sanya hannunta akanta tana shafawa cikin sanyin murya mai cike da rauni tace.
“Khausar muyi haƙuri Ramadan kam ya tafi ya barmu.
Ubangiji Allah yajiƙan sa Allah ya masa rahma Allah yasa mai cetone”.
Cikin tsananin tashin hankali Khausar ta fashe da matsanancin kuka me tsuma zuciya yayin da ta shiga girgiza kanta kallon Mommy tayi Muryanta na rawa tace.
“Mommy Ramadan kike cewa ya rasu!? Mommy wannan wani irin magana ne!?
Dan Allah Mommy kice mafarki nake Mommy kice ba gaskiya bane!”.
Girgiza kai Mommy tayi still Hawaye na bin fuskarta amma ta gaza furta komai.


Cikin sauri Khausar ta toshe bakinta jin wani matsanancin kuka ya taho mata.
Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauƙe tare da ƙarasawa cikin falon ya zauna kusa da Mommy, kasancewar akan 3sitter take.
Cikin sanyi murya yace.
“Khausar kiyi haƙuri kinji ko?”.
Kallonsa tayi da jikaƙƙun Idanunta kana tace.
“Abba da gaske wai Ramadan ya rasu!?”.
Nunfashi Abba ya fesar tare da jinjina mata kai yace.
“Da gaske ne Khausar ya muka iya da hukunci Ubangiji, dama shi ya bamu Ramadan kuma shi ya karɓesa, kiyi haƙuri ki daina kukan nan kinji ko!?”.
Girgiza kai tayi tare da sake fashewa da matsanancin kuka mai gunji.
Dafa kanta Lamiɗo yayi cike da tausayawa yace.
“Kiyi haƙuri yanzu ma Naseer ya kira Dr yazo ya dubasa sannan ya tabbatar min da cewa ya rasu!”.
Cikin wani irin yanayi mai cike da ruɗu Khausar ta miƙe da gudu tare da shiga Bedroom ɗinta ta faɗa kan gado tare da sakin marayan kuka.
Lamiɗo kuwa bayan ya sake rarrashin Mommy tare da bata haƙuri da kuma nuna mata muhimmanci tawakkali da haƙuri ya mike ya fita.


Bayan angama shirya Ramadan an masa wanka an suturtasa yanda addinin Musulunci ya tsara aka kaisa gidansa na gaskiya.


Bayan andawo Lamiɗo da ƴan Uwansa da kuma Abokan arziƙi aka zauna zaman Makoki.
Wunin wannan ranan haka Mommy da Khausar suka yini cikin alhini da jimamin rashin Ramadan Hajiya Bunayya kuwa sosai tayi farin ciki sai dai kallo ɗaya zaka mata ka fuskanci mutuwar ta shigeta domin ayanda take nunawa tafi Mommy damuwa wani abin ma Mommy ke tausarta tana bata haƙuri.
Washe gari Khausar ce zaune a ƙasa Mommy na Kan kujera gabansu Kuma kayan Breakfast ne.
Cikin sanyin murya Mommy ta kalli Khausar tare da cewa.
“Khausar ki matso kici abinci”.
Girgiza kai Khausar tayi tare da kallon Mommy da kumburarrun Idanunta kana cikin sanyin murya tace.
“Mommy ba najin yunwa”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da rintse Idanunta kana tace.
“Khausar ki matso kici abinci bana son haka zamuyi fushi da abinda Ubangiji ya jarabcemu da shine Allah daya halicci Ramadan yafimu son sa shi ya bamu Ramadan kuma shi ya ɗauke mana shi!”.
Wasu hawaye masu masifar zafi ne suka zubowa Khausar akuncinta cikin matsanancin kuka tace.
“Mommy shikenan!, Shikenan Ramadan ya tafi baza mu sake Kallonsa ba shikenan mun ransa shi har abada. Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Kallonta Mommy tayi still Idanunta cike da ruwan hawaye Akuma dai-dai lokacin wayarta ya ɗauki ruri.
Kallon screen ɗin wayar tayi nan taga sunan Hajja Nana na yawo.
Cike da ladabi tayi Picking tare da kaiwa kunnenta tace.
“Hajja ina yini?”.
Daga ɗaya ɓangaren Hajja Nana tace.
“Lafiya lau ina Khausar!?”.
Cikin sanyin murya Mommy ta kalli Khausar da hawaye ke zuba a Idanunta kana tace.
“Gata nan”,
“Toh ki bata wayar”, cewar Hajja Nana ta.
Kai Mommy ta gyaɗa tare da miƙawa Khausar wayar.
Amsa Khausar tayi cikin Muryan kuka tayi sallama.
Cike da kulawa Hajja Nana tace.
“Ke kuma lafiya ya naji muryanki haka kukan me kike!?”.
Cikin sheshsheƙan kuka Khausar tace.
“Hajja Nana Ramadan ɗin mune ya rasu”.
Hajja Nana kuwa cikin sauri tace.
“Innalillahi Wa'inna Ilahi rajiu'n Ayyah Allah sarki Ubangiji Allah ya jiƙansa da rahma Allah yasa maicetone ai bamu da labari bamu sani ba bawa Mommy naki”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da miƙewa Mommy wayar.
Jin Mommy ta amshi wayar yasa Hajja Nana cewa.
“Wai ashe Ramadan ya rasu!?”.
Kai Mommy ta gyaɗa kana cikin sanyin murya tace.
“Eh Wlh”.
Ajiyar zuciya Hajja Nana ta sauke tare da cewa.
“Ikon Allah Meye sameshi haka?”.
Numfashi Mommy ta fesar tare da gyara zaman ta kana tace.
“Wallahi ciwon kai ne mako ɗaya”.


Cikin sanyin murya da tausayawa Hajja Nana tace.
“Allah sarki Allah ya gafarta masa Ubangiji yasa maicetone! Dama yanzu Malam Liman zai shigo Gembulan Insha Allah zan biyo shi muzo”.
Jinjina kai Mommy tayi cikin sanyin murya tace.
“Toh Allah ya kawo ku Lafiya mungode sosai”.
Bayan Mommy ta kashe wayar ta kalli Khausar data zubawa kayan Breakfast Ido Cike da tausayawa ta shiga lallashinta.


Acan gidan Ummi kuwa Moddibo ne zaune afalon ya tsurawa waje ɗaya Idanu yayin da Ummi kanta ke ƙasa hawaye zira-zira baki ɗayan sun zurfafa acikin tunanin da suke Asma'u ta fito daga kitchen cikin mutuwar jiki ta tsugunna kusa da Ummi kana cikin sanyin murya tace.
“Ummi”.
Ahankali Ummi

Please Login or Register in order to submit comment